NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   54 / 54

159K to 160.7K   out of 160.7K words

Dariya "Cije baki yayi tare da karkada hannu Alamun zata gane kuranta Gwalo ta k'ara masa Hada yi da hannu Marairaicewa yayi tare da Kallon Mummy ya ce " Mummy Kinga gwalo take yimun"Harararshi Mummy tayi ta ce "Tayi maka d'in " Dariya Ayra tayi Ganin haka ya sanya Arman tashi zai chafkota tayi saurin Mikewa tare da zuwa ta lafe jikin Mamy tana Dariya "Kudai bazaku daina shiriritaba wlh kun girma harda yara amma Abunda yaran suke Shi kuke Allah shiryeku ta fad'a tana Kiran Wanda zai fara yiwa Aira registeration din cikin sa a ko ta sameshi A ranar Aka je da Aira tayi registration din jamb sai murna take Daga nan gidansu ta wuce Bayan sun gaisa da y'an gidan Ta wuce gidan Amma Inda aka shiga Firar yaushe gamo cikin y'an uwanta Ranar suna yaro yaci suna Sani ana ce masa Sultan Haka akayi taron suna Lafiya aka gama lafiya Inda Aira ta koma gidansu a lokacin twins Sunje suna ganinta da gudu Suka ruga suka Rungumeta suna oyoyoy cutie D'aya Bayan d'aya ta daddagasu ta ce " oyoyoy my Angels "I miss you mom Suka fad'a a tare " Miss you tooo "ta fad'a tana sama da Haidar dake Dariya ya ce " Mom amma dai Kindawo nan ko"Dariya tayi ta ce "Sarkin wayau nufinka na dawo nan ku bazakujeba Chan kenan Saidai ku ku koma Chan badai ni ba " Mak'ale kafada yayi yayi ya ce "um um nidai bazan koma ba Saidai ke ki dawo" Dariya Ayra tayi ta ce "nak'i wayan " dak'yal Aira ta samu ta zauna saboda yanda suka yayyabeta Mamy da Mama ta Gaida suka Amsa cikin mutuntawa Mamy ta ce "Y'an suna sai yau ake ganinki tun Randa kikazo" Dariya Aira tayi ta ce "Wlhko Mamy hidima ta boyemu Ina su Sadeq da shureim " sai yanzu ma kike Tambayarsu Dan gidanku Kawai daga zuwa ki tafi kibar yara suta Rafkawa mutane kuka saidai babansu na kira Yazo ya d'aukesu kinsan k'iyiwa ce dasu daman zaki barsu ke raguwa Biyun ma kin kasa kula dasu tsabar ragwanci ai wlh naso ace Biyar d'innan hannunki suke muga ta tsiya"Dariya Ayra tayi ta ce "Chab Mamy Ai bazan iya dasu ba Kuma kunsani shiyasa kuka amshesu ina ni ina Iyawa da Yaran nan Ai Saisu ida doramun hawan jini Kinga idan sukaje Hutu suka had'u Su Biyar d'innan Kullum da ciwon kai nake yini Dan B'arna da Irin tijarar da suke mun kare baici wancen hutun fa k'atuwar plasma d'inmu ta palour wlh Suna fad'a suka fasata saida tayi ragwa ragwa kuma Da gangan Wancen uban zuciyar ya fara fasata ta fad'a tana nuna Haidar saida muka sake sabuwa"girgiza kai Mamy tayi ta ce " Sun aika Wlh Shiyasa da na gansu kaffa kaffa nake da kayana b'arna yaran nan garesu Allah dai ya kyauta "Ameen Aira ta fad'a ranar ta kwana gidansu tukwana tayi musu bankwana Ta wuce gidan Mummy Dan yau zasu wuce tana zuwa ta samu Arman da Twins suna ganinta suka Ruga suka Tareta daukarsu tayi tare da zaunawa ta ce " Shine kukayi tayiwa Mamy kuka ko"Dariya sukayi suna wasa da Sarkar gold din jikinta shureim ya ce "Mom mu chafi(tafi)Dariya Mummy tayi ta ce " bagwaran nan Baisan mutane ja iri tunda sukazo saidai babansu wai dole.sai an tafi gida"Dariya Aira tayi ta ce "Wlh Mamy sarkafa garesu shiyasa Na gudu ba dasu ba " Harararta Arman yayi ya ce "Ai wlh sa a kikaci ina y'an mutuncin da kaimiki su zanyi kawai kika tafi kika barmun yara Suna kuka Kika kashe wayarki saini Mamy ta kira " Dariya Aira tayi ta ce "To ayi hakuri ai gwara da kake a y'an mutunci ba y'an tsiyarba ta fad'a tana Dariya" Shima dariyar Arman yayi ya ce "Mummy zamu wuce " Okay Allah ya kiyaye Amma bamu minti biyu ta fad'a tana kama hannun Ayra bedroom d'inta ta nufa da ita Bayan ta rufe kallonta tayi ta ce "Shawarace nayi akan karatun da zaki Fara idan kika samu wani cikin zakusha wahala Shiyasa na sayo Allurar planning zanyi maki ta shekara Ukku Kina ganin ba matsala?Ajiyar zuciya Ayra ta sauke Dan daman a tsorace take karta kuma samun wani cikin Dan data samu ko tasan ko giyar wake Tasha Arman bazai barta tayi karatu ba cikin farinciki ta ce " Mummy kawai kiyimun nima inaso"To Mummy ta fad'a tare da had'a allurar ta ce "Karki kuskura ya sani nima bazan fad'a masa ba " Insha Allahu Ayra ta fad'a Nan Mummy tayi mata allurar A tare suka fito Arman bai damuba Dan Mummy da Aira An saba sirri har parking space Mummy ta rakasu tare da musu bye bye.

*After 5 years*

Cikin shekarun nan Aira ta kammala degree dinta a nan abuja tayi inda bayan gamawarta ta k'ara haihuwar y'arta kyakyawa Aka sanya mata halimatu takwarar inna ana ce mata Amal.
***
A hankali suke Saukowa daga matattakalar jirgi k'aramar baby da bata wuce 5months ba a hannunta Kyakyawa mai tsananin kama da Ita Ansha mata gayu babyn tare da mata two babies sosai tayi kyau Uwar kuma sanye take cikin shigar doguwar Riga Blue ta yafa beilt din rigar sosai tayi kyau ta fito kamar wata baturiya Dak'yal na gane ta saboda wani kyau da fresh da wayewa da ta k'ara Arman ne a gefen ta hannunsu cikin na juna Shima sosai yayi kyau cikin Farar shaddarsa da tayi masa bala in kyau Ta Kara fito da kyawunsa suna tafe suna hirar soyayya har suka sauko suna Saukowa sukaji a rungumesu su Duka an zagayesu "Murmushi sukayi Ganin yaran nasu ne su biyar suka rungumesu Cikin farinciki Arman ya shiga daukarsu d'aya Bayan daya banda twins da suka girma yanzu sun tafi shekara Tara shagwaba suka fara Naila ta ce " Dad saurani "Dariya yayi tare da d'agata itama ya maidota tana Dariya Sannan itama Nihal ya d'agata Naila ce Ta Rungume Aira ta ce " Highly wellcome my cutie mom "Dariya Aira tayi Wanda ya fito da fararen hakoranta Dake d'auke da zinarin hakorin makka sosai naga ya k'ara fito nata da wutar kyanta Ta ce " Thnks my angels "Nihal ce itama ta matso ta ce " Sannu da zuwa mom ya makka"Dariya itama ayra tayi mata ta ce "Yawwa my angel makka Alhmdllh" Amsar Amal Naila ta mik'a zatayi Yarinyar ta mak'ale jikin uwarta "Turo baki Naila tayi ta ce " rabu da ita wai ita nan ji take ta dawo daga makka shine zatayi mana rainin wayau to tun kafin kije mu muka fara zuwa Y'ar rainin hankali"Dariya iyaye sukayi Sai sannan suka Hango Mummy mamy da Daddy tare da Abba Wajensu suka nufa d'aya Bayan d'aya suka rungumesu kowa nayi musu Sannu da dawowa suna amsawa Mummy ce cikin fara a ta ce "Masha Allah yaudai su Aira anzama Hajiya" Dariya Aira tayi tare da murmushi ta ce "Ai jina nake cikin farinciki Mummy ashe duk zuwan da zakayi idan ba hajji kayiba bakajinka cikin nutsuwa kamar haka nidai Alhmdllh yanzu kuma banida da wani sauran buri anan duniya Duka burika na Sungama cika Saidai Fatan samun aljanna kawai Sannan ta juya ta kalli Mijin nata ta ce " ka gama yimun komai a duniya my hero Kaid'in miji ne da kowace mace zata so samun irinsa Allah ya barmu tare har mutuwa "Ameen Arman ya fad'a yana lakutar kumatunta kamar ba gaban iyayensu suke ba ya ce " Nima kingamayimun komai my cutie matata a duniya kuma a Aljanna uwar y'ay'ana Allah ya biyaki da gidan Aljanna Alhmdllh nima bani da wani saurin buri a duniya burina kowanne ya gama cika Saidai kuma fatan samun aljanna Allah ya had'amu a aljanna baki d'aya mudaku "ameeeeeeen duk suka Fad'a Zuwa Aira tayi ta Rungume Mamy Itama Rungumeta mamyn tayi ta ce " Highly wellcome my Beloved daughter Alhmdll ko buri ya gama cika "Murmushi Aira tayi tanajin gumin mahaifiyartata ta ce " Thnks Mamy na Yanzu kam bani da wani sauran buri duka burika na sungama cika tsakanina da ubangiji har kullum sai Godiya Saidai kawai muce Alhamdulilla Allah ya barmu tare har mutuwa *Ni da Yaya Arman*.......✍🏿

_Laifin dad'i karewa_😭😭


*Nima Miss Hajjo anan nake cewa Alhamdulilla*


*TAMMAT BI HAMDULILLAH ALHMDULILLAH INA GODIYA GA ALLAH (S W A) DAYA BANI IKON FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA NA GAMA LAFIYA A YAU NE NI HAJARA L SADEQ NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI MAI TAKEN NI DA YAYA ARMAN KURA KURAN DA NAYI A CIKINSA ALLAH YA YAFEMUN ALLAH YA BAWA AL UMMA DAMAR AMFANUWA DA FADAKARWAR DA NAKESON ISARWA*

*SAKON GAISUWA DA JINJINA GAREKU NI DA YAYA ARMAN FANS A GASKIYA BABU ABUNDA ZANCE GA MASOYA SAI GODIYA NAJI DADI SOSAI YANDA KUKA AMSHI LITTAFIN NAN HANNU BIBBIYU KU KA SOSHI KUKA KAUNACE SHI DA YANDA KUKE NUNAMUN TSANTSAR SOYAYYA NAGODE NAGODE ALLAH YABAR ZUMUNCI DA KAUNA KU SANI NI HAJARA L SADEQ INA KAUNARKU FIYE DA YANDA KUKESON LITTAFINA DA WANDA SUKA SAYA SUKA KARANTA DA WANDA BAMA SU SAYA BA SUKA KARANTA DUKA INA GODIYA KUMA KU SANI INA MUKU SON FISABILILLAHI LOVE YOU ALL MY FANS IRIN SOSAI DINNAN WOLLA INAJI DAKU HAR CIKIN KOKON ZUCIYATA ALLAH YABAR KAUNA DA SOYAYYA*

*SAIMUN HAD'E A SABON BOOK DINA MAI TAKEN AUREN WATA TARA WANDA ZAI FARA ZUWA MUKU RANAR 20/AUG/2022 WANDA INA DA TABBACIN SHIMA ZAKU SOSHI BAZAN KODASHI BA SABODA KUNSAN ANCE WAKA A BAKIN MAI ITA TAFI DADI AMMA DAI NASAN KUNSANI ZAZZAKAN ALKALAMIN MISS HAJO BAYA RUBUTA LABARIN BANZA KUDAI KAWAI ACIGABA DA GASHI GA MAI BUKATAR SHIGA GROUP DINA NA WHATS APP KO SHARHI,KO TAMBAYA HANYA A BUDE TAKE KU TUNTUBE NI AKAN NUMBER WAYATA KAI TSAYE 07026166536*

*ALBISHIRINKU MASOYA HAJARA L SADEQ TA SHIRYA GIVE AWAY NA MURNAR KAMMALA WANNAN KASAITACCEN BOOK DIN NA NI DA YAYA ARMAN KOWA DA KOWA YANA DA DAMAR SAMUN WANNAN GARABASA ZAKUYI SAVE D'IN NUMBER TA KUYIMUN MAGANA KAI TSAYE ZANYI SAVE NUMBERKU ZAN D'AURA GARABASAR KATIN MTN A STATUS A YAU K'ARFE 8:00 NA DARE WANDA ALLAH YA BAWA SA AR CI ZAICI ALLAH YA BAWA MAI RABO SA A AMEN GA NUMBER WAYAR DA ZAKUYI MAGANAR 07026166536*

*Littafin Ni Da Yaya Arman ya kammala ya zama complete document zaku sayeshi cikin farashi mai rahusa ga mai buk'atar sayan cmplt document na Ni DA YAYA ARMAN ku tuntub'eni akan number wayata 07026166536*

*Sayan na gari maida kudi gida*

*_MA'ASSALAM MISS HAJO CE_*🤙🏿

54 / 54