NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   28 / 54

81K to 84K   out of 160.7K words

Aira na barin d'akin Laila cike da mamaki Tace "wai Mama Lafiya naga kin sauya lokaci guda" Hmmm kede bari Laila ai dole kiga haka Ashe duk haukan banzan mu muke.....tas ta kwashe komai da Aira ta bata labari ta fad'awa Laila itama Laila sosai ta tausaya wa Aira tasan Tabbas ko itace akayiwa haka saita girgiza...Aira na fitowa a palour taci karo da Sadiq Kallo d'aya yayi mata ya kauda kanshi ganin haka ya sanyata saurin wucewa bedroom d'inta tana shiga ta rufe tabar key din jiki tare da hamdala wanka tayi ta sauya kaya ta haye Gado cike da tunanin Arman bacci ya kwasheta itace bata tashi ba Sai wajen 10 Shima Knoking d'in Laila ne ya tayar da ita tana bud'ewa murmushi Laila tayi mata ta ce "Baccin kikasha kenan sis muje muyi break fast " Murmushin Aira ta mayar mata ta ce "banma San nakai lokacin nan ba muje to" a tare da Aira da Laila suka fito Aira ganin Daddy a dining d'in sosai gabanta ya fad'i zata juya Laila tayi saurin rik'e mata hannu ta ce "matsoraciya kawai daddyn namu ne ya zame miki dodo" A sanyaye aira tabi Laila gabanta na fad'uwa kujerar kusa da Mama Laila ta ja ta zauna gabanta sai fad'uwa yake cike da kulawa Mama ta ce "Harkin tashi kenan " Kanta a k'asa tana wasa da zoben da yaya Arman ya sanya mata ta ce "Eh Mama" Laila kiyi serving d'inta "to Laila tafada tare da Fara serving d'in Aira Daddy ko idonshi nakan Aira ko k'iftawa baiyi Ga kuma mamakinshi na yanda yaga Saude na nan nan da Aira Cike da fargaba Aira tafara tsakular abincin d'ago idonta tayi a hankali Suka hada ido da Daddy saurin k'asa da kanta tayi sosai gabanta ya fad'i ganin irin ciwon da taji mashi Batare da ta k'oshi ba ta mik'e Mama ta ce " Badai harkin koshiba"murmushi Aira tayi ta ce "Wlh na k'oshi Mama " To shikenan"Daddy ne shima ya Mike cike da gadara ya kalli Aira ya ce "Muje zamuyi magana" Aira tuni harta fara hawaye Kallon Mama tayi ta ce "Dan Allah Mama kice karya dakeni " dan ita a tunaninta rama ciwon da tajimai ne zaiyi "Kallon Daddy Mama tayi ba wasa ta ce " Alhaji koma ka zauna"Cike da jin Haushi Daddy Ya ce "waike ina ruwanki saude Nifa na kawota gidan nan aurota nayi kamar yanda na auroki Dan haka ki daina shiga tsakanin Nida matata idan ba so kike ranki ya b'aci ba" kallon Aira Mama tayi ta ce "Wuce ciki Aira" Aira hada gudunta ta Ruga "Laila ma tashi tayi tabar wajen Kallon Daddy Mama saude tayi ta ce " Kaidai kaji kunya wlh Alh ashe tirsasawa yarinyar nan kukayi Auren ka to Naji komai da bakaso Naji kuma daga yau karka k'ara takurawa yarinyar mutane kaiko kunya ma bakaji Yanzu wa gari ya waya bagashi nan taji maka ciwo ba to wlh nan gaba saita illataka indai kaci gaba da Haye mata Dan Idan mace batason namiji komai tana iyayi wlh ni mamakima kakeban godai godai dakai da tsufanka da komai amma baka hakura da duniyaba har kake k’ok’arin fad’awa yarinya k’arama kusan sa ‘ar jikanka kadaiji kunya wlh "Cike da masifa ya ce " Ohhh wai hademun Kaine nan zakuyi to ina ruwanki Inma batasona aidai Nina aurota"Tsaki taja tare da barin Wajen tace "Chan ta matse maka " Daddy cike da jin haushin matan nashi ya bar gidan duk sungamu sun chaza mashi kai ....tun daga lokacin nan Aira da Mama saude suka had'e kansu sosai Aira take yiwa Mama saude biyayya yanzu bata aikin komai ga kuma Ita da laila sun zama kawaye Saisu zauna susha hirarsu kamar basune ba ga kusan kullum Laila saita kirawa Aira Mamy Dan Wani lokacin ma da kanta take cewa baza a kira miki kowaba Sosai hakan ya farawa Aira dadi Dan yanzu Bata da matsala da mutanen gidan idan ta amshi wayar Laila takan kira layin Arman Amma koda yaushe switch up Saidai tayi kukanta a d'aki ta gode Allah Alhaji Yusuf kuwa ido ya sanya musu yaga gudun ruwansu hakan ko sosai yayiwa Aira dad'i Dan ko gaisuwa Bata had'ata dashi Ammafa duk Inda ta gitta idonshi a kanta.......Sanye yake cikin K'ananan kayan da sukayi mugun karb'ar shi dukda Ramar da ya d'anyi Fuskarnan tashi tayi fayau ta k'ara kyau da haiba Sumar nan tashi lufluf kamar wacce ake shafama mai A hankali yake Saukowa daga matattakalar benen jirgi Mummy na gefenshi kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin farinciki rik'e take da hannunshi tana binshi a hankali kamar wani yaro har suka k'arasa Saukowa Kallon filin jirgin ayayi garin yayi lufluf Kamar za ayi ruwa Alhamdulilla finally yaudai gani a 9ja K'asar da Masoyiyata take cikinta Murmushin da harya mance yaushe rabon da yayishi yayi a hankali yanda ba wanda zai ji ya ce "a duk Inda kike a fad'in duniyar nan ko da kuwa nisan wajen ya kai birnin sin saina nemo ki masoyiya............✍🏿



*Ni da yaya Arman it's not free it's for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*


_*Miss Hajo ce_*🤙🏿
[7/1, 23:00] Hajo hajo: 🅿️..........*75&76*




....Saina nemo ki masoyiya ya k'arasa fad'a yana murmusawa ta gefen baki"Daddy ne ya taryoshi Rungumeshi yayi ya ce "highly wellcome my son I m very happy to see you Allah ya k'ara maka lafiya"Ameen Arman ya fad'a Shima yana Rungume Daddy Mummy ta matso cike da farinciki Dan yau jinta take cikin farincikin marar musaltuwa Dan samun lafiyar yaron nata a yanzu ta fiye mata komai cike da farinciki suka bar airport d'in koda suka isa gida sosai goverment house din ta cika da mutane Dan ko a Chan Egypt d'in mutane sundinga tururuwar zuwa y'an uwan Mummy ma dake yola duk sunzo domin duba jikin na Arman gidan saiya kasance kamar ana wani shagali Arman ko dayake baisan damuwa da hayaniya tunda ya shiga katafaran bedroom d'inshi bai lek'oba Dan wasu idan suna son ganinshi Godiya Mummy takeyi musu tace ya samu bacci Dan tana kiyaye dokokin da likita ya dorasu a kansu Arman ko kwance yayi a makeken Royal bed dinsa ya d'ora kanshi bisa hannunshi yana kallon sama tunanin Inda Aira take kawai yake tare da tunanin yanda zai nemo ta dan baitab'ajin ya karaya ba ko sau d'aya indai akan Aira ne lokacin shan maganinshi nayi Mummy tazo da kanta ta b'alla masa ta bashi yasha.
Tunda aka Sallamo Arman kullum gidan cike yake da mutanen Arziki masu zuwa dubiya Mama Halima ma tazo daga kaduna ita da Hafsa Dan duba jikin nashi Tunda Mama Halima tazo batayiwa Arman zancen Aira ba haka Shima baiyi mata ba dukda yana son tambayar Inda take Zaune suke a palour ya kwanta saman sopa Mama Halima da Mummy na hira jefi jefi yayinda Hafsat ke waya k'asa k'asa Shidai Arman idonshi rufe ba wacce takeyimai gizau idan ba Aira ba Shi ina ma take?ya tambayi kanshi Bud'e idonshi yayi a hankali ya sauke akan Hafsa dake lumshe ido tana waya bamaijin abunda take cewa "Tsaki yaja Tare da yunkurawa zai tashi cikin Sauri Mummy taje ta taimaka mashi ya mik'e tare da yi mashi Sannu" Gyad'a mata kai yayi a hankali ya ce "Mummy zan iya fa tafiya da kaina kije ki zauna Naji sauk'i fa" Murmushi tayi ta ce "Ka tabbatar dai ba wata matsala" gyad'a mata kai yayi tare da d'an murmusawa kad'an da mahaifiyar tashi taji sanyi"Sosai kwa hakan yayiwa Mummy dad’i ta ce "To shikenan ka kula Allah ya k'ara lafiya" Ameen ya fad'a tare da Fara tafiya ya nufi bedroom d'inshi Yana isa kan bed ya zauna tare da dafe saitin zuciyarshi dake mashi ciwo Dan tunanin Aira da ya zurfafa Kwance yayi wasu siraran hawaye na zubo mashi wace hanyace zai samu ya had'u da Aira tunani yayi Tabbas Hafsa tasan Inda take kuma zata iya fad'a mashi hakan yasanya shi janyo telephone d'in dake gefen gadon ya Danna number Mummy tana d'auka ya ce "Mummy a bawa Hafsa ta kawomun Tea " Daga bangaren Mummy Ajiyar zuciya ta sauke tare da Kallon Hafsa ta ce "Jeki had’awa yayanku tea ki kai mashi d'aki amma karki cika sugar kinji daughter" Katse wayar da suke da yaya Umar tayi tare da mik'ewa ta ce "To Mummy " Bayan tafiyar Hafsa kallon Mama Halima Mummy tayi ta ce "Ni wlh daman Hafsat Arman ya komawa Tunda dai Airar tayi Aure kuma naga Kamar ya d'an fara hakura da ita tunda ko maganarta bayayi" Cike da Rashin nuna jin dad'i Mama Halima ta ce "Aunty kibar wannan Maganar Dan Allah karma ta zame matsala " murmushi Mummy tayi ta ce "Ai daman ceewa nayi daman naga Hafsa d'inma kamar da Wanda takeso tunda na kula tunda tazo kullum tana waya" Wlh ko wai Umar nefa suke soyayya dashi ni farkon d'aukarma wasa nayiwa Abun saidaga baya na lura itama sonshi take "ikon Allah To Allah tabbatar da alkhairi kice tuwo na maina za ayi amma ai yana da mata ko" Eh yana da mata Allahdai tabbatar da alkhairi kawai Amma banson kai y'a gidan mai mata dukda dai d'an uwanta ne "Ameeeen ya Allah ai fatan Alkhairi kawai ake Wani gamin saikiga Auren mai Matar ma yafi na saurayin kwanciyar hankali Yanzu barin Kasu d'in da ta shiga zatayi kenan idan Auren ya taso" a a. Gaskiya banjin Abbanta zai cireta tunda Shima ak'ida garai cewa yayi saitagama karatu ko yana mata Aure "Nan dai sukaci gaba da tattaunawarsu Hafsat ko Bayan ta had'a tea d'in d'akin Arman ta nufa knoking tayi ya bata izinin shigowa tana shiga Ta duk'ursa ta ce " Sannu yaya ga tea d'in"yunkurawa Arman yayi ya tashi zaune tare da cewa "Ajeshi kan center Table " Nan ta Aje harzata juya ya ce "zo muyi magana Hafsa " Juyowa tayi tare da zaunawa Kujerar dake gefen gadon ta ce "Gani yaya" Numfasawa yayi kamar bazaiyi magana ba kallonta yayi ya ce "Kinsan Inda Aira take tana gidansu har yanzu kuwa ?"Sosai Hafsa tayi mamakin tambayar da Arman yayi mata cewa tayi "a a a ta na sokoto " what sokoto kuma?Arman yafada cike da mamaki"Gabanta na fad'uwa Dan tsoro take kar wani abun ya kuma samunshi ta ce "Kayi hakuri Yaya Yanzu Aira ai tafi wata guda a gidan mijinta Ammafa har yanzu tana sonka yaya dukda yanzu bama tare A dalilin Auren har kokarin kashe kanta tayi Tasha fiya fiya" Kashe kanta fa kikace Hafsa yanzu dai fatan tana lafiya ba abunda ya sameta "gyada mashi kai tayi ta ce " Eh taji sauki tun lokacin ta warke"nauyayyar Ajiyar zuciya Arman ya sauke Sosai yaji zafi da kishi da rad'ad'in jin wai Aira na gidan mijinta mijin ma bashiba "Ya sunan mijin nata?ya fad'a cikin k'arfin hali" Kamar mai nazari Hafsa tayi Dan sunan ya shige mata saikuma ta ce "Inajin dai akwai Madugu a sunan nashi Amma na manta ainahin sunan"Kallon Hafsa yayi ya ce " okay thnks u can go but don't tell anyone munyi wannan Maganar dake "gyada mashi kai tayi ta ce " Insha Allahu "tare da barin d'akin tana tunanin me Arman zaiyi da sunan mijin Aira Arman ko tana fita Sosai ya k'ara shiga damuwa wai Aira ce Ke gidan wani har tsawon wata guda Sosai wani irin kishi ke taso mashi shikenan kenan Wani banza sakarai ya rigashi sanin Airarshi sosai zuciyarshi ta dinga tafarfasa.
Da misalin tara na dare Zaune suke a palour ita da Laila suna Hira Laila na bata labari har Dariya take Sadiq ne ya shigo da sallama a bakinshi Kallo d'aya Aira tayi mai tayi kasa da kanta Dan nauyin had'a ido dashi ta ke " Zaunawa yayi yana sauke ajiyar zuciya Laila ce ta ce "Sannu da zuwa yaya Ga alamu kashayo gajiya" Yawwa Sadiq ya fad'a ya ce"wlhko na kwaso gajiya jeki d'auko mun ruwa"To yaya Laila ta fad'a tare da tashi tabar palourn Kallon Aira yayi da tayi kasa da kanta tana wasa zobe yayi ya ce "Auntynmu ba magana to ina yini " D'agowa Aira tayi ta Kalleshi tare da turo baki ta kauda kai"Murmushi yayi ya ce "Baza a amsa gaisuwarta tawa ba kenan Mamanmu" Dagowa Aira tayi ta Kalleshi tare da Fara hawaye Cikin shagwaba ta ce "Ni ba mamanka bace ina nazama mamanka please mai sunan Abba ka daina "Dariya Sadiq yayi ya ce " sorry to na daina Auntynmu zance kenan"Turo baki Tayi ta kauda kai"Wai ina Aunty Aysha kuwa kun bani ita tunda dai Ke yanzu kin zama mamanmu "ya fad'a cikin sigar zolaya " Murmushi tayi ta ce "Tana Chan kano Ai tayima Aure tafi 5 moths ina tunani" Cike da nuna Rashin jin dad'i Sadiq ya ce "Ayya to Allah ya basu zaman lafiya"Ameen Aira tafada" Laila ce ta dawo tare da mik'awa Sadiq ruwan kallon Aira tayi tare da mik'a mata wayarta ta ce "Natafi kuma sai Mamy ta kira zan kawo maki kuma saita katse amshi ki kirata...kafin Aira ta amsa ta sake kira" yawwa ma gashi ta sake kira Laila ta fad'a tana mik'awa Aira amsa Aira tayi tare da d'aga wayar daga d'ayan b'angaren Mummy tayi sallama "Aira ta amsa tare da cewa " Ina yini Mamy"Lafiya qlau Aira ya sokoto kindai zama basakwakwaciya"tashi Aira tayi tare da barin palourn tayi d'akinta ta ce "Haba Mamy ni har yanzu bakaniya ce Sokoton da ko ganinta bantaba ba Tunda nazo banje ko ina ba"Haba dai to ai gwara haka daman Banason yawo amma naga kamar kuna zaman lafiya da mutanen gidan ko Aira " Eh Mamy yanzu lafiya qlau muke zaune da dai suka bani wahala Amma yanzu Alhamdulilla "To masha Allah haka nakesonji daman ki hakura kiyi zaman aurenki kinji Aira tunda Allah ya kaddara miki" hawaye ne suka zubowa Aira ta maidasu "Uhm kawai tacewa Mamy" Sannan ta ce "Mamy ban Amer mu gaisa" Murmushi Mamy tayi ya ce "shidai bai magana Saidai yayi miki gwalamgwamtu ta fad'a tana Kara mishi Wayar a kunne" My boy Aira ta fad'a jin gwalamgwalamtun Amer nan ta biyeshi suka yi ta shiririta tukwana ta ce "a bata Haidar kiran Haidar Mamy tayi Shima ta bashi Sosai yaji dadi cikin farinciki suka shiga gaisawa da y'ar uwartashi ya ce " ya Aira munyi missing d'inki wlh gidan duk ba dad'i inna ma kullum saitayi kukan rashinki"Goge hawayenta Aira Tayi ta ce "Nima nayi missing naku sosai bro Kaico my Inna kenan ta dawo nima nayi kewarta"Amsar wayar Mamy tayi ta ce " "ba abunda kike buk'ata inbada ko mota ne a kawo maki...Dariya Kad'an Aira tayi ta ce " Kai Mamy yanzu ko nace inason wani Abu saiki bada a kawomun tundaga kano a a bana buk'atar komai ganinku kawai nake buk'at....kasa k'arasa maganar tayi sakamakon ganin shigowar Alh Yusuf da tayi a murtuke Ihu ta fasa tare da wulli da wayar ta ce "Na shiga ukku Daddy Dan Allah fita" k'arasa shigowa Daddy yayi ya ce "Bazan fita ba ke nifa ba haka nan na auroki Dan na dinga kallonkiba ba biyan buk'ata shine kuka hademun kai keda saude ko to yau zanga ta Had'in kai saitazo ta kwaceki" ya fad'a yana rufo d'akin tashin hankali ba a gwada maka rana da gudu Aira Ta Ruga ta shige toilet tare da sanya key ta ciki ta rufe durk'ushewa tayi jikin kofar tare da fashewa da kuka Alh Yusuf ko sosai ya shiga buga kofar toilet din kamar zai ballata ya ce "ki bud'e nace Wlh karki bari raina ya b'aci" Aira ba abunda take inbanda kuka ta ce "Bazan bud'e d'inba mugu azzalumi" Alh Yusuf ya dau minti ashirin tsaye yana mata magiyar ta bud'e amma takiya sai kuka take jin bazata bud'e d'inba ya sanyashi Juyawa cike da jin Haushi Mamy cikin waya ta dinga cewa Hello hello amma taji shiru ta cikin waya ta dinga jin Abunda ke faruwa cikin Sauri ta maza ta kashe wayar gabanta na fad'uwa Laila ko ta biyo Aira Dan amsar wayata tajisu saurin Juyawa tayi cikin Sauri cike da kunyar abunda mahaifin nasu yake Aira ko sosai take kuka a toilet d'in ta durkushe ita wannan wace irin jarabawace Allah ya jarabceta ita kwata_kwata tsohon najadun nan ya takurawa rayuwarta Arman kawai take kiran sunanshi tana kuka tana cewa "Yaya ka kawomun d'auki plx " tana kuka har bacci ya d'auketa a toilet d'in saida asuba ta farka ta ganta a toilet cike da tsoro ta mik'e ta ce "Na shiga ukku yau nice da kwanan toilet abubuwan da suka faru Daren jiya suka shiga dawo mata A hankali ta bud'e k'ofar toilet din ta tura taga ba kowa cikin Sauri ta fito tare da rugawa taje ta rufo d'akinta tasa key tabarshibu jiki Juyawa kan Gado tayi taga wayar Laila Na vibration Cikin Sauri taje ta d'auka tana ganin number Mamy ce " Cikin Sauri ta d'auka tare da fashewa da kuka cike da tsoro Mamy ta ce "Kina lafiya Aira kukanme kike what happend to u " Cikin kuka ta ce "Mamy Dan Allah kizo ki tafi da ni wallahi nagaji Mamy nasan ke kina sona kizo ki tafi dani Dan Allah kafin mutumin nan ya kasheni wlh Mamy kusan kullum sai yayi k'ok'arin yimun fyad'e Allah yake tsareni yanzu haka yau a toilet na kwana Mamy Allah Abba d'an iskane kawai ya auramun Mamy kizo ku tafi dani kafin na mutu" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka.
Mamy ita bada magana ba Amma sai kunya ta kamata ruwa yabi ya cinyeta Daman tun jiyan ta kasa bacci tana tsoron ko wani abun ne ya samu Airan hakan yasa tunda safe ta kira Sosai a ranta tayi mamakin kenan tunda akayi Auren wani Abu bai shiga tsakaninsu ba"murtukewa tayi kamar tana gabanta ta ce "Bansan shirme da shiririta Aira karna k'arajin maganar nan kin fad'awa kowa waike har yanzu bazakiyi hankaliba waya gaya miki kowace magana ake fad'a daga yau karna k'arajin maganar nan

28 / 54