Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
insha Allah " Goge hawayenta tayi ta ce "To yaya Amma Dan Allah karka maidani gida yaya Dan Allah Abba kasheni zaiyi kokuma ya sake rabamu bana son komawa kano kwata_kwata yaya " kan wani dakali ya zaunar da ita Shima ya zauna tare da cewa "Bazamu komaba cutie guduwa zamuyi" Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da hade kanta da gwuiwa "lalubo Wayarshi Arman yayi ya dannawa musa kira Bayan ya d'auka yayi mashi kwatancen Inda suke tare da cewa Dan Allah duk Inda yake yazo yayi gaggawar zuwa " Minti Sha biyar me kyau musa yazo ya samesu a wajen da mamaki yake kallonsu Ya ce"Yadai Abokina yana ganku haka ku biyu kuma yanayinku kamar ba dad'i"Kama hannun Aira Arman yayi tare da mik'ar da ita ya ce "Muje kawai munyi maganar later" A back sit ya sanya Aira shi kuma ya shiga gaba har suka isa gidan musa bamai cewa Uffan saida suka isa Arman ya fito tare dabudewa Aira ita ta fito a palour gidan suka d'auka Inda matarshi ta tarbesu hannu bibbiyu dukda k'in sakewar da Aira take kallon Sarat Arman yayi ya ce "Maman boy Dan Allah toilet zaki nuna mata ta tayi wanka kafin mu dawo" da to ta amsa tare da kama hannun Aira ta ce "Sis muje " ba musu Aira ta bita toilet d'in ta nuna mata tare da bata towel tabar d'akin Saida ta cire kayan jikinta tukwana ta d'aura towel din daman daga ita sai kayanta ko Hijab babu jikinta haka sukazo Arman ko fita sukayi tare da musa Kallonshi musa yayi ya ce "baka ban labari ba Abokina meya faru" Numfasawa Arman yayi ya ce "ya saketa" wara idanu musa yayi ya ce "Serious Abokina" Da gaske mana muna irin wannan wasan dakai"Wow amma natayaku murna wlh congratulation Amma garinya harya yarda ya saketa"ya gaji da Zama da itane bata da amfani a gareshi shiyasa kawai ya saketa "ya bashi amsa a takaice don baijin zai iya Fad'ar gaskiyar Lamarin abunda ya faru kamar ya tozarta cutie d'inshi ne dukda har yanzu zuciyarshi bata lamunta da zargin cikin da ake mata ba a wani boutique dake kusa dasu sukaje Arman ya sayowa Aira doguwar Riga wacce zatasa sannan suka biya suka sai mata yadin hijab suna tsaye aka d'inka mata hijab d'in yadi hud'u tukwana suka koma gidan a lokacin Aira harta fito daga wanka Sarat sukaba kayan akan ta kai mata Zaune ta sameta tayi tagumi " Mik'a mata kayan tayi ta ce "Gashi y'ar uwa kisanya" Nagode Aira tafada tare da amsa saida ta fita tukwana ta bud'e rigar ta sanya ko madubi bata tsaya kallaba bare taga ma yanda tayi mata hijab din ta warware Blue har kasa tare da sanyawa ta fito palour anan ta tarar da Su Arman Mikewa Arman yayi tare da mik'awa musa hannu ya ce "Abokina zamu wuce nagode nagode Allah yabar zumunci Kayimun abunda bazan tab'a mantawaba dashi a rayuwaba Allah ya saka da alkhairi" Bakomai Abokina ai yiwa Kaine bazaku bari Kuyi break fast ba tukwana ku wuce "a a a Gaskiya Sauri muke Abokina kallon Aira yayi ya ce Taho muje Godiya Aira tayiwa Matar musa tukwana ta bisu musa ya kaisu Har airport saida yaga sun yanki ticket sunyi clearing d'in komai jirginsu 12 zai tashi zuwa Abuja ganin lokacin ya kusa ya sanyashi yi musu bankwana akan zai koma Account number shi Arman ya amsa tare da yi mashi Transfer 10 million" Sosai musa yayi mamaki yaji dadi sosai sannan yayi mishi Godiya cike da kewar abokin nashi ya koma gida"K'arfe 12 daidai jirginsu Ya tashi Bayan y'ar takaitacciyar tafiyar da sukayi jirginsu ya sauka Abuja Taxi suka hau A lokacin Jikin Aira yayi rauu zafi sosai Sannu kawai Arman ke mata har suka isa katoton gidanshi dake G R A Sosai gidan ya burge Aira Dan ya had'u karshen had'uwa Aljannar duniya kenan Knoking Arman yayi mai gadi ya leko yana ganin Arman yafara fara a tare da washe baki ya ce "Ranka ya dad'e kaine tafe Sannu da zuwa ya fad'a yana bud'e musu tare da basu Hanya " Alhmdllh kawai Arman ya fad'a ya shige ciki Aira na biye dashi a makeken Palourn gidan da fad'ar tsaruwarshi bata baki ne suka yada zango Kallon Aira yayi da duk tayi sanyi tare da kamo hannunta ya ce "kodai jikin ne cutie mu wuce Asibiti " girgiza mashi kai tayi ta ce "a a a yaya ni bansan zuwa Asibiti bazan k'ara zuwaba tunda basa fad'ar alkhairi" D'an murmushi yayi tare da cewa to shikenan yanzu ki kwanta anan naje na had'o maki break fast"Na koshi yaya Banajin yunwa"Hararar wasa yayi mata ya ce "Baki isa ba inke bakyaso ai baby na yaso ya fad'a yana kallon cikinta da yake a shafe" Hawaye Aira ta fara ta ce "Cikin da ba asan ubanshi ba Kake dangantawa da babynka yaya Dan Allah ka kaini a ciremun please" murza hannunta yayi ya ce "Baza a cire ba cutie Har yanzu bangama yarda akwai ciki a tattare dake ba sannan koda ace da gaskene to kisani a soyayyar da nake maki ko Kad'an bazata ragu ba saima karuwa da zatayi sannan ni zan amshi cikin a matsayin nawa koda kuwa duniya zata tsinemun Amma ki bari please muje Asibiti a gwada " cikin hawaye take Kallonshi tana Kara godewa Allah da yabata masoyi na Gaskiya hakika Arman da wanine a wannan lokacin ne zai gujeta amma gashi ko a kanshi sannan bai nuna mata kyama ko hantara ba "Girgiza kai tayi ta ce " Yaya bazanje Asibiti ba nan gaba kila su fad'amun abunda zai tarwatsarmun da zuciya"ta k'arasa fad'a tana hawaye "To shikenan bar kukan my cutie kinsan ba abunda na tsana sama da kukanki abunda nake so dake ki kwanta ki huta kinji kafin na fito" gyada mishi kai tayi tanajin soyayyarshi na k'ara ratsata Har ya bar wajen tana Kallonshi saida taga shigarshi kitchen tukwana ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ka kawo mana mafita cikin wannan rud'addiyar rayuwar da muke ciki Arman yana shiga kitchen yaga basu da kwai ta k'ofar baya yaje ya bawa Mai gadi kudi akan yayi Sauri ya samo mashi kwai ba b'ata lokaci kuwa yana tsaye har yaje ya dawo"itadai aira tana kwance yayinda idanunta suke a bude ba ayi 30 minutes ba taga ya fito hannunshi rik'e da plate zuwa yayi ya Aje gabanta sannan ya koma ya d'auko Cup d'in tea da yasha Had'in kauri Shima ya Aje gabanta cike da kulawa yaje ya ruk'ota tare da cewa " Mike to kici kinji my prince's zakiji k'arfin jikin naki"A hankali Aira ta mik'e Plate d'in soyayyar wainar k'wai sai k'amshi yake tashi ya bud'e mata tare da gutsuwa yayi saurin kai bakinta ya ce "ha a bud'e bakin" Murmushi Aira tayi mishi tare da bud'e bakin shi ya dinga bata tare da tea din sosai taji dad'inshi har batasan taci da yawaba Kallonshi tayi tare da marairaicewa ta ce "Yaya na koshi kaima kaci please" Murmushi yayi ya ce "a a ni na k'oshi ki daure ki k'arasa cinye wannan zakiji k'arfin jikinki" girgiza mai kai tayi tare da Amsar plate d"in itama ta gutsuro takai saitin bakinshi "murmushi ya sakar mata Itama ta mayar mai a haka itama ta dinga bashi har wainar kwan ta k'are Mikewa Aira tayi ta ce " Yaya salla zanyi"Shima mikewar yayi ya ce "Muje na nuna maki bedroom d'inki binshi tayi ya gwada mata d'akin tare da fita Dan Shima yaje yayi salla Dan lokacin ta ya wuce sai a gida yayi Aira ma cire hijab din tayi tare da Shiga Toilet taje tayi alwala Ta fito ta sanya hijab d'inta tare da shimfida abun salla raka'a biyu tayi tare da nafila biyu saboda k'asaru ce Tana gamawa ta jima tana adduo'i a haka Arman ya sameta Saida ta gama tukwana ta juya ta Kalleshi murmushi ya sakar mata ya ce " Fatan an sakamu a Addua'ar "Uhm yaya Ai Addu'arma gaba d'aya taka ce " ta fad'a tana rufe fuska murmushi yayi ya ce "Ah kice Duka tawace to Allah ya amsa mana" Ameen Aira ta fad'a kasa kasa tare da Yin kasa da kanta Kallonta yayi ya ce "ki kwanta yanxu ki huta Dan Allah zanje na samo maki magani kinji cutie sannan kiyimun alk'awarin bazakiyi ta kukan da kika saba ba ke bakyama gajiya da kuka kanki yayi ta ciwo a Banza"Mikewa tayi tare da Kallonshi ta ce " to yaya insha Allahu bazanyi kuka ba karka jima please "to y prince's kafin in dawo ki tabbatar kinyi bacci" murmushi tayi ta ce "To my yaya" yana barin d'akin ta cire Hijab d'inta jikinta tare da hayewa Gado Ba jimawa bacci ya d'auketa Dan daman a gajiye take.
Abba na zaune a palour da misalin karfe Tara na dare yana kallon labaran N T A News Kira ya shigo Wayarshi duba mai kiran yayi yaga Alhaji Madugu ne Amsawa yayi tare da Kara wayar a kunnenshi ya ce "Assalamu alaikum" Wa alaikumussalam Alhaji Madugu ya amsa daga ganin kasan yana cikin fushi cikin Fushi ya fara magana "A Gaskiya Alh bukar ka cuceni ka zalince ni daman Kasan y'arka y’ar iskace baka bata tarbiya ba dan tayi cikin shege shine ka lik'amun ita to kasani asirinku ya tonu dan asibiti mukaje dr ya tabbatar mana da tana dauke da juna biyu na wata hudu Bayan aurenmu da ita wata ukku da kwanaki ne hasalima ni wani abu baitab’a shiga tsakanin ni da ita ba sannan nakirakane Dan na fad'a maka a halin yanzu y'arka bata hannuna na saketa tabi Tsohon Saurayinta da ya yaudare ni kusan wata guda yake Aiki a karkashina ashe shirine sukayi da ita Bayan mun kamasu dumu dumu dazu da safe na saketa saki Ukku Ta bishi sun tafi Dan karma ka bincika y'arka wajena bata hannuna tabi tsinannan saurayin da yayi mata Cikin da bakinshi ya fadamun cikinshine daman sone kukayi ku likamun cikin shege shiyasa ka lakabamun ita sannan kuma ka sani duk abunda na kashe tundaga neman Aurenta har zuwa yanzu saika biyani Dan bazanyi asara a banza ba "Tunda Alhaji Yusuf ya fara maganar Daddy Ya shiga tsananin tashin hankali har yakai karshe " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ya fad'a wayar tuni ta sulale a hannunshi A tsayen da yake ya dire kan kujera tare da dafe saitin Zuciyarshi a rarrabe ya ce "Ci ki Aira " Ai tuni Yaji hankalinshi ya fara gushewa Ya fara ganin jiri Mama ce da tafito taga yanayin da yake cikin cikin tsananin tashin hankali Ta nufe wajenshi tare da cewa "Alhaji lafiya? Me ya faru " Wayarshi ya nuna mata a rarrabe ya ce "Ki ki ra mun Dr cikin Sauri Mama ta dauki wayar tare da Nemo number Dr bashir ta kira ring Ukku ya d'aga cikin tsananin damuwa ta ce " Dr kazo gidanmu yanzu ka taho tare da kayan aiki ina tunanin jinin Alhaji ne ya hau sosai "Tana kashewa ta kwalawa Mamy kira " Rahama ki fito Alhaji ba lafiya!Cikin tsananin tashin hankali Mamy ta fito tare da nufar wajen ta ce "Subhanallahi me ya sameshi yanzu fa muka rabu dashi lafiya" wlh ko nima haka yanzu na sameshi"Su amma da su Haidar ma duk sun fito Cikin tashin hankali sunyi jugum jugum a haka Dr ya shigo cikin Sauri ya nufi Inda Abba yake tare da Fara Dubashi Abun awon DP ya fara mashi yana dubawa yaga jininshi yahau sosai irin yanda yake bada matsala cikin Sauri ya sanya mishi semomitre a harshe tare da saurin had'a allura Yayi mashi su mama dr ya Kalla yace su taimaka a kaishi daki Mama da Mamy suka taimakamai aka kwantar dashi a kan gadon Mama Wanda tuni bacci ya daukeshi Dan allurar ta bacci ce Daman kallonsu Dr yayi ya ce "wani Abu aka fad'amai kafin ya fara haka Dan kadan ya hana ya samu heart attack" Subhanalla heart attack kuma Dr Gaskiya nidai bansan anyi mashi wani ba Saidai ko Yaya idan ta sani "Mamy ta fad'a tana kallon Mama " itama cewa tayi bata saniba magunguna Dr ya rubuta musu akan a sayo daya tashi ya cigaba da shansu sannan su barshi shi daya ya huta a dakin har zuwa sanda zai tashi kar a tasheshi jinin zai sauka Daman yasan Abba yana da hawan jini amma irin na manyanta ka ne bamai matsala ba magani kawai yakesha "Godiya su Mamy sukayiwa Dr Bayan ya tafi suma Duka barin d'akin sukayi Dan kar ayi hayaniya kowannensu ya shiga kogin tunanin meye ya sanya jinin Abba hawa a take.
Washegari sai wajen goma na safe Abba ya farka jinin nashi ya sauka Saida Dan Rashin jin dad'i da bayayi a lokacin Duka iyalannashi na dakin Sannu kawai suke jera mishi da kanshi ya Mike " Kallon Mama yayi ya ce "Banyi asuba ba ko?Eh Alhaji bakaiba Dr yace a barka ka tashi da kanka shiyasa" Cewar Mama "Aida kun tasheni ya fad'a tare da shiga toilet ya dauro alwala yaxo ya gabatar da salla Mamy ce tayi k'arfin halin cewa Ya jikin" Da sauki ya bata Amsa Kallon Mama yayi ya ce "Ki kira su Aisha da Ummy Dukanku karfe sha biyu ku sameni a palour na yana gama fad'ar haka Ya fice daga d'akin ya koma part d'inshi sosai duk sukayi sanyi Basusan me yake faruwa ba kamar yanda Abba ya fad'a haka Mama ta kirkira su Aysha karfe sha biyu tayiwa kowa na gidan a Babban palourn Abba har Inna saida yasa aka kira idan aka cire yaya Umar da Maryam sai Aira Bayan kowa ya zauna Aysha Abba ya Kalla ya ce " Kiramun Maryam a waya kisa hads free "Sannan ya kalli Ummy ya ce " Ke kuma kiramun Umar Duka inason kowa ya saurari abunda zan fad'a "hakanko akayi Duka aka kirasu Gyaran murya Abba yayi ya ce " To ba bakomai yasa na taraku anan ba Saidai In kafa hujja sannan ku shaida ku sani a gaban kowa daga yau Ni Abubakar Umar na cire Hajara a cikin jerin y'ay'an da na Haifa daga yau babu ni babu ita Sannan duk d'an Dana Haifa Shima na rabashi da ita babu ku babu ita Na yanke zumuncin dake tsakaninku ko a boye wani yayi mu’amula da ita ban yafe mashi ba daga yau kar a k'ara alak'antata da y'ar da na Haifa na yafeta a cikin jerin y'ay'an da na haifa ...........✍🏿
*Jumaat khareem*
*ina yiwa yan uwa musulmai murnar nuna mana wannan rana ta Arafa mai Cike da albarkoki Allah yasa muna daga cikin masu dacewar wannan rana ya yafe mana kura kuranmu ya amsa mana adduoin mu da ibadinmu Allah bamu ikon zuwa wannan k’asa mai tsarki don muma mu sauke farali Ameen ya Allah*
*zamu shiga hutun sallah koda na kwana biyu ne kuyi hakuri kunsan hidimar sallah bazata bari nasamu damar typing ba Ayi salla lfy sannan kowa ta ajemun nama na yawan nama yawan typing*😂
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿🤙🏿
[7/11, 12:53] Hajo hajo: 🅿️............*89&90*
.....Na yafeta a cikin y'ay'ana sannan koda wasa na sameta a cikin gidan nan ta shigo naga akwai sa hannun wani cikinku wlh zakuyi mamakin matakin da zan d'auka kowaye Shima Saidai ya bita hatta mahaifiyarta"kowannensu idan ka kalleshi zakasan yana cikin tsananin tashin hankali musamman Mamy cikin tashin hankali ta ce "Me kuma tayi Alhaji na shiga ukku ni Rahama " Ai zakiji kome tayi "Inna ce ta mik'e ta ce " Amma wlh habu baka kyautaba Kazo ka zauna ka dinga tsinewa y'arka To tukunma me tayi "Ban tsine mata ba Inna na bartane da duniya Sannan Abunda tayi ba abunda Zan d'aukeshi bane ciki taje dashi gidan Aurenta" Cikin tsananin tashin hankali kowa ya mik'e kamar sun had'a baki wajen fad'ar ciki?Tabbas ciki Jiya da Daren mijinta ya kirani yake shaidamun Sunje Asibiti bata da lafiya likita ya shaida musu Cikine da ita harna wata hud'u kuma ba nashi ba saboda ba abunda ya shiga tsakaninsu sannan Bikinsu kowa ya duba invitation yasan wata ukku ne Sannan Yaron nan Arman ashe Had'in baki sukayi ya bita Gidan a matsayin Driver suke cigaba da mu amula dashi karshe dai ya ce sun kamasu a d'aki Wanda Dalilin hakan ya sanya ya saketa saki Ukku Bayan Arman d'in ya tabbatar mashi shi yayi mata Cikin shine ita kuma ta bishi to shiyasa na yanke wannan hukuncin daga yau ko ambatar sunanta kar a k'ara mun a gida "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai suke Ambata sosai kowa dake wajen yayi mamakin irin abunda Aira tayi musamman Mamy da takejin zuciyarta kamar zata rabe gida biyu Aisha ko ba abunda take inbanda kuka haka Amma mamy ko cikin k'arfin hali Ta ce " Sakayyar da Aira zakayimun dashi kenan ta kyauta ta cika y'a tana gama fad'ar haka ta shige cikin d'akinta tayi tagumi sosai take hawaye tanajin zafi da rad'ad'in abun Tabbas Aira ta kunyata k'untatawa.mafi muni kuwa ai yanzu kuma bata da bakin magana a cikin gidannan innako Salati ta rafka ta ce "Na shiga ukku ni Halima cikin Shege a gidannan Amma mujahid Anyi lalatacce daman saida ya lallaba ya kumsawa yarinyar nan Ciki Goge hawayenta tayi tare ciro wayarta cikin Dan tofi Haidar ta mik'awa tace amshi maza maza kiramun Kabir " Amsa Haidar yayi a sanyaye ya kamo mata number Daddy saida yaga ta fara ringing tukwana ya mik'a mata ta k'ara a kunne Daddy na d'auka cikin Masifa ta fara cewa "Kabir ina Mujahid" a lokacin Daddy na tare da Mummy a palour Dan hutawa yau ya ke ya ce "Inna Mujahid kuma ai rabona dashi anfi wata " Eh Mujahid duk Inda yake ka nemo munshi wlh bai isa ba munafuki ina ganinshi kamar mutumin arziki ashe da abunda ya taka Saida ya yi yanda yayi ya kumsawa yarinyar nan Ciki ai wlh bai isa ba ya maidomun jikata duk Inda ya kaita ko inyi rashin mutuncin da na jima banyiba "Cikin tsananin tashin hankali