Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
ba Ga wata had'ad'd'iyar agogo dake Juyawa a Gaban wajen Rik'e hannunta yayi Tare da wuk'a a hannunsu.
Mutanen wajen ne suka hau lissaafi daidai lokacin da 12 ta kusa Bugawa 1,2,3,4,5,6,7,8,9,10 Arman ya kama hannunta suka Yanka cake Duka wajen tab'i ya d'auka tare da wakar Happy Birthday Aira sosai wak'ar tayi Bala'in dad'i Aira zata iya cewa cikin rayuwarta bata tab'a shiga farinciki irin wannan ba kwata kwata ta ma mance yau ne ranar birthday d'inta sai yanzu ta tuna .
Ita ta fara bashi cake d'in a baki tukwana Shima ya bata ya na Gama bata Ya amshi Abun magana tare da kallonta duka camera na kanshi
k'asa da kanta Aira Tayi Ya fara magana cikin zazzak'ar muryarshi kamar haka "Alhamdulilla Alhmdllh Alhamdulilla My Love sister she's +1 year God bless you for many more years Happy Birthday Lover for you is the real,real,real,a deal a really ,really really big deal You are my North Star and help me know my direction in life you make me happier and a better person Happy Birthday to you My cutie Aira I Love I Love I Love you so much My Cutie Please Love Me my Aira sannan ya durk'usar da gwuiwarshi har k'asar Inda take tare da kallonta ya had'e hannayenshi biyu Alamun rok'o ya ce " will you marry me?...........โ๐ฟ
*Tofa ya kenan Arman ya k'ara ringimo wata rigimar ya kuke tunanin iyayensu zasuyi idan sukaga wannan birthday d'in a duniya*???
*Wani irin mataki kuke tunanin Abba Da Daddy zasu d'auka Kuna tunanin zasu bari wannan Abun ya tafi a banza kuwa*??
*Yau dai Arman ya fito ya bayyanawa Aira tare da duniya Kalar son yake mata tilon dโan governor guda ya dukursawa mace cikin bainar Jamaโa*
*Iyayensu zasu samu daman raba su kuwa*???
*ya makomar soyayyarsu zata kasance nan gaba Zasu mallaki juna ko akasin haka*
*Idan iyayensu suka samu damar rabasu ya kuke tunanin halin da wannan masoyan zasu shiga yanda suke jin bazasu iya cigaba da rayuwa ba ba tare da d'ayansu ba*
*Shin Abba da Daddy Zasu shirya kuwa*?????
*Duka wannan Amsoshin zaku samesu ne kai tsaye idan kin biya 200 kachal zaku karanta cikin kwanciyar hankali karku bari kice sai an sata a kawo maki ki karanta ba girmanki bane Hajiya ki biya ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali darajarshi tafi ta kudin na barshi hakane a saboda k'auna da soyayya Masoyan Asali*๐๐๐
*wannan shine last page na free page na wannan littafin kamar yanda na fad'a daga yanzu sai Wanda suka biya ne suke da damar ci gaba da karanta wannan k'ayattacen littafin mai cike da salon burgewa sannan duk Wanda zata saya ta saya da zuciya d'aya Karki saya ki fitar mun da Littafi kud'in karantawa kika biya ba na mallaka ba Kunsan dai mahimmanci hak'k'i Sarai bazanyi Allah ya isa ba Ammafa ban yafe ba akwai hak'k'i ni da yaya Arman koda kudinka saida rabonka nasan babu wacce zataso ayi tafiyar nan babu ita ga masu bukatar saya ga tsarin yanda biyan yake*
*Normal group Transfer Ko hoton katin MTN #200 kachal*
*PC Wanda basa buk'atar sakasu group ta PC zandinga tura musu zasu biya #300*
*VTU 300*
*Zaku turo ta wannan number 07026166536*
_Saimun had'e a Paid group_
Taku har kullum
๐
*_Miss Hajo ce_*๐ค๐ฟ
[6/11, 16:49] Hajo hajo: ๐
ฟ๏ธ....*35&36*
........."Will you marry me??Aira da jin kalaman Arman kawai take tamkar a mafarki " Dagowa tayi ta Kalleshi batasan lokacin da wasu zafafan hawayen farinciki suka fara zirarowa daga idanunta ba "Cikin saurin Arman ya tashi tare da d'aukar handchiep ya fara Goge mata hawayen ya ce " Kinsan bansan kukanki My Love ki bari"d'agowa Aira tayi ta Kalleshi Shima itad'in yake kallo idanunsu suka sartse Cikin na juna Aira batasan lokacin da ta fad'a Jikinshi ba har yanzu ji take kamar mafarki yau Itace Arman ya bayyana mata kalar son da yake mata kuka ta fashe dashi Arman jin kukan nata Yake har cikin ranshi daddab'a bayanta ya fara cikin sigar lallashi ya ce "I m sorry cutie bansan ranki zai b'aci ba ko baki sona ?cikin muryarta mai kama da wacce ta sha kuka ta ce " I love you too yaya I love you so much I can never live without you yaya I love you more "Duka wajen tab'i ya dauka tare da sakin wak'ar love sosai suka burge mutane da dama dake wajen Ai Arman baisan lokacin da ya k'ara kankameta ba cike da farinciki ya ce " Thnks you thank you thank you so much My Love Bazan tab'a iya kwatanta maki farincikin da nake cikiba "Aira ko shiru tayi jikinshi tana shak'ar daddan k'amshin turarenshi Mai narkar da zuciya Sosai Akayi bishasha a birthday din kamar wani biki Wanda wadanda sukajema saida suka.shaida arziki daga k'arshe ARMAN yayiwa Aira kyautar Sark'ar gold tare da Dan kunnenta da zobenta wadda a k'alla ta haura sama da 3million A matsayin special gift d'inta na birthday Aira jinta take kamar a mafarki tama kasa kwatanta kalar farincikin da take ciki 12:40 aka tashi daga kayataccen birthday d'in a Mota d'aya Aira da Arman suka shiga Driver ya jasu tana baya ta lafe jikinshi Tayi shiru Arman ko yau jinshi yake kamar ya sauke wani katoton dutsi a kanshi ya fad'awa Aira abunda ke ranshi A mota sai zolayanta yake itadai tayi shiru Dan wata kunyarshi kuma take ji.
B'angaren gidan Su Aira Mamy harsun kwanta Aunty Maryam ta kira Abba saida ta kusa Katsewa tukwana ya Dauka cikin rud'u Maryam ta ce " Abba kuna ganin abunda nake gani yanzu kuwa"Abba ya ce me kenan "ku kunnan tashar Haske Television(k'irk'irarrar Tasha ce )yanzunnan zakuga abunda nake gani Mamy ce ta tashi ta ce " Lafiya Abbansu "To kawai Abba ya cewa maryam sannan ya fad'awa Mamy abunda maryam ta ce mashi "
A tare da Abba da Mamy suka fito palour suna shigowa sukaga Mama da su Amma suna kallo Duk a tsaitsaye Alamun abun al'ajabi suke kallo A sanyaye Abba da Mamy suka kai dubansu TV sosai hankalinsu ya tashi ganin abunda ake nunowa a tashar kuma Live tundaga lokacin da Aira da Arman suka Yanka cake har zuwa Maganganun da Arman yayiwa Aira na soyayya da Rungumeshin da Aira tayi Da ita ma Kalaman da ta mayar mashi komai saida suka gani har zuwa kyautar da yayi mata "d'ora hannu a ka Mamy tayi ta ce " na shiga Ukku Abbansu me nake gani kamar Aira "Abba da ranshi ya gama b'aci Zuciyar shi tafarfasa kawai take cikin tashin hankali ya kashe t v safa da marwa ya fara kafin ya bar palour cikin tashin hankali Mamy kuka ta dukurshe tanayi Mama ta lallasheta ta ce " Kiyi Hakuri Ni kaina nayi mamakin al'amarin nan garin Yama ta fita cikin Daren nan "Mamy cikin kuka ta tashi tabi Bayan Abba Bangaren inna Abba ya nufa cikin tashin hankali ya dinga buga mata k'ofa Inna cikin bacci ta fito ta na wanene " Abba yace nine "tana bud'ewa cikin tashin hankali Abba ya. Ce " Ina Aira??Sosai gaban Inna ya fad'i ta ce "basu dawoba" Cikin tashin hankali da zafin rai Abba ya ce "Daman da saninki ta fita" Kuka Inna ta fashe dashi ta ce "Kai amma yaran nan sun chucheni daman basudawo ba" Abba da ranshi ya gama b'aci yasan wata maganar ma ya kumayi ran Inna zai iya b'aci a yanda yakeji baice komai ba ya juya Mamy ko cikin kuka ta ce "Inna ina sukace maki zasu" Inna bata bada amsa ba sai sharb'ar hawaye take inna ganin Mamy ta dameta cike da borin kunya ta ce โto ni ina zan San inda take kema uwarta baki saniba bare ni ta fada tare da rufe dakinta ta koma ciki sai rarrabe ido take Itama Mamy Juyawa tayi cikin tashin hankali ta koma gida Mamy tun tana kukan har ta dawo tana zubda hawaye Abba wajen mai gadi yaje yayi ta surfamai masifa akan ubanwa ya bashi umarni budemai gida har wani ya fita shi kanshi mai gadin saida ya tsorata hakuri ya dinga bawa Abba Komawa ciki Abba yayi Wanda Da za a shiga zuciyarshi a fito da ita tofa da za aga tana ci da wuta tsabar bacin ran da yake ciki Safa da marwa kawai yake Mamy ko tayi tagumi sai hawaye take "Nikam ya Aira takeso dani mutuwata takeson gani kome" ta fad'a tana hawaye.
B'angaren gidan su Arman ma haka ta kasance Duka abunda ya faru Mummy da Daddy sun Kalla sosai ran Daddynshi yayi kololuwar b'aci itadai Mummy hakuri kawai take bashi.
Aira bata tsorata ba saida sukazo bakin get d'in gidansu Sai sannna ta tuna da tashin hankalin gida idan suka gani"Kallon Arman tayi cikin hawaye tace "Yaya tsoro nakeji" karki damu ba abunda zai faru "Shiya kama hannunta suka fito Sukayi knoking mai gadi yazo ya bud'e musu " Kallon Arman mai gadi yayi ya ce "yallab'ai da zakubi shawarata Karku shiga gidan nan ka kaita wani waje ta kwana dukda bansan abunda ya faru ba Amma muddin ta shiga komai zai iya faruwa Dan ran me gidan ya b'aci sosai'"Kuka Aira ta fashe dashi tace" ka gani ko yaya"kama hannunta Arman yayi suka juya suka shiga mota driver ya umarta da ya wuce government house har suka isa Aira kuka take shikuma sai aikin lallashinta yake a tare suka shiga makeken Babban palourn gidan Aira na baya tana hawaye tana biye dashi Mummy da Daddy suka gani tsaitsaye Sosai Aira ta tsorata Arman ko ajikinshi "Kanshi Daddy yayo cikin Masifa ya ce " Daman kalar tarbiyar da na baka kenan,hakan da kayi me kenan me kake nufi ka fa sani bamu kadai muka kalli abun nan ba duniya ce gaba d'aya me kake tunanin mutane zasu d'auki Lamarin nan Mujahid kana cikin hankalinka kuwa ka rasa wacce zaka durkusawa cikin bainar jama'a sai mace macen ma wacce bazaka tab'a Auranta ba har abada muddin ina numfashi"Sosai ran Arman ya b'aci jin Kalmar Daddy ta k'arshe ya ce "Daddy ina sane nayi hakan Dan na gwadawa duniya Kalar son da nake mata kuma duniya ta shaida kuma ku shaida idan kuna tunanin wasa ne ku daina tunani sannan kuma Aira ita ce Mata ta insha Allahu bazaku iya rabamu ba Tunda bamuda masaniya a rigimarku Dan haka bazata shafemu ba " sosai ran Daddy Ya b'aci ya d'aga hannu zai wankawa Arman mari Mummy ta rik'e ta ce "Haba Alhaji yaron nan da Gaskiya ya fad'a Akanme duk kukeso kubi ku rikitawa yara rayuwa Bayan suna son junansu Gaskiya ya fad'a babu ruwansu a rigimarku a kanme zai shafesu " Cikin fad'a Daddy ya ce "ke daman na Riga da sanin ke kike daurewa yaron nan gindi Bakijin irin maganganun da yake fad'amun bako d'a'a sannan ya kalli Aira da ke lab'e Bayan Arman ya ce " ita kuma da ka taho da ita ina zaka kaita ko so kake ka k'ara jamun wulakanci wurin mahaifinta kamar yanda ka jamun a kwanakin baya"Sai sannan Mummy ta kalli Aira Wajenta ta nufa tare da kamo hannunta ta ce "Taho y'ata " a sanyaye Aira tabi Mummy "Arman ko cewa yayi kwana zatayi kafin gobe " yana gama fad'ar hakan ya haye sama "Kallon Mummy Abba yayi ya ce " Fatima kina ganin abunda d'anki yayi ko ban fad'a maki irin wulakanci da mahaifinta yayimun ba a saboda shi shine yanzu zai kawo mana Ita gida to ba gida na ba ya maidata gidansu ko yaje ya nemu Inda zai kaita"Mummy ce ta ce "Haba Alhaji wai wannan wace irin rayuwace To babu Inda zataje da Daren nan haba wannan Abun da kuke kanku kuke wulakantawa wlh d'iyar d'an uwan naka uwa d'aya uba d'aya kake cewa ta bar maka gida idan mahaifinta yayi maka Abu ai ba ita tayi maka ko a lahira laifin wani bai shafar wani Dan haka ba Inda zata" cikin fushi Daddy Ya fice daga palourn bai kara cewa komai ba Mummy ko Aira ta Rungume tayi ta lallashi ganin kukan da take ta ce "Ki kwantar da hankalinki.kinji y'ata nid'in Tamkar uwa nake a wajenki muje kije kiyi wanka ki kwanta " makeken bedrom d'inta Mummy takai Aira Ta bata towel ta cire doguwar rigar jikinta Taje tayi wanka tana fitowa Mummy ta miko mata wata rigar bacci marar nauyi tasa Aira duk a kunyace take A Gado d'aya mummy da Aira suka kwana sosai Mummy ke k'aunar Aira har cikin ranta.
B'angaren gidan su Aira Mamy da Abba cikinsu babu Wanda ya rintsa Mamy ga Karin tashin hankalinta na k'in dawowa da Aira tayi Inna ko tana Chan duk ta tsure.
Washegari tunda Safe kiran Mama Halima ne ya tayar da Arman Cikin fad'a ta ce "Tun jiya nake kiranka bansameka ba abunda kukayi kun kyauta kenan Arman da hankalinka da komai Dan iskanci kuyi wani birthday a idon duniya to inbaka saniba tuni labari ya bazu ko ina har social media zancen da ake kenan tun jiya da daren " Murmushin gefen baki Arman yayi ya ce "Mama ai haka nakeso tunda su Daddy suna d'aukar abun wasa hakan yasa na bayyanawa duniya" Cikin fad'a Mama Halima ta ce "Mahaukatan banza ita ina Airar ta ke" Ta na d'akin Mummy,okay gidanku ta kwana kenan?Eh Mama "To Kada ka sake ka maida ita gidansu Ran Yaya ya b'aci sosai Dan na kirashi Yanzu Naji ranshi matuk'ar b'ace zai iya mata dukan da zata kasa tashi ka kawomun ita nan Kd anjima" Ajiyar zuciya Arman ya sauke Dan daman yanzu matsalarshi Hukuncin da Aira zata fuskanta Wanda bazai jurewa hakan ba "To big Mama saimunzo" ja'iri "Mama Halima ta fad'a murmushi yayi.
Driver ya aika ya sayowa Aira rigar da zata saka ya ba da aka Aiko mata Bayan tayi Wanka ta shirya cikin kayan da ya Aiko mata sosai sukayi mata kyau sannan ta yafa Belt din rigar ko hoda bata shafa ba kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tashin hankali Mummy tazo ta ce " Daughter harkin tashi kenan "k'asa da kanta Aira tayi ta ce " Eh Mummy ina kwana"Lafiya qalau Kintashi lafiya "Alhmdllh ta fad'a a sanyaye kama hannunta Mummy tayi ta ce " kindaiki sakin jiki da ni ko Daughter keda gidanku amma sai bakunta kike"murmushin da bai kai ciki ba Aira tayi ta ce "Ba haka bane Mummy" to yaya ne"shiru tayi tama rasa abun cewa A dining suka tarar da Arman yana breakfast cikin kwanciyar hankali kallo d'aya Aira tayi mai tayi kasa da kanta Kujera taja ta zauna Mummy ma ta zauna Mummy tayi serving d'in Aira Kad'an taci ta ce ta k'oshi"Mamy ta ce "a a a baki isa ba saikin cinye wannan D'an dankalin da kikaci zakice kin koshi ha a d'aga bakin Mamy ta fad'a tana d'auka a spoon ta Saka mata a baki " murmushi Aira tayi sosai taji Mummy ta shiga ranta cikin shagwaba Arman ya ce "Mummy Nifa''Harararshi tayi ta ce " y'ar tawa zan fasa ba na baka d'an karere "b'ata fuska Arman yayi ya ce " Kai mummy "Sannan ya kalli Aira dake yar dariya cikin so da k'auna ya ce " My cutie bazakicewa Mummy nima ta bani ba "mak'e kafada Aira tayi ta na wurgamai Harara ta ce " kayi girma da yawa "Dariya Mummy tayi ta ce " Fad'a masa dai Shi inaga baisan ya girma ba "cikin raha har suka gama cin abincin Sosai Aira ta fara sakin jiki da Mummy Dan ta lura kwata kwata bata da wata matsala a rayuwa ga yanda take nuna mata so wannan ne lokaci na farko da ta tab'a ganin Mummy saboda Daddy baya barinta zuwa Chan suma kuma Abba baya barinsu zuwa nan shiyasa basu San juna ba sai a Hoto idan Arman ya nuna mata itama mummyn a Hoto take ganin Aira.
Arman ya fad'awa Mummy yanda sukayi da Aunty Halima akan yakai Aira Chan " cewa ta yi "Me makon ka barmun ita nan" a a Mummy Chan din yafi kwanciyar hankali kafin komai ya lafa"jinjina kai tayi ta ce Hakane kuma Allah dai ya kyauta "Sosai ta had'a Aira da tsaraba Turamen atamfofi shida ta ce ta kaiwa Mama Halima biyu hud'u nata banda kayayyakin makuleshe da turarruka har Parking space Mummy ta rakasu Hug din juna Mummy da Aira suka yi tukwana Shima Arman yayi hug din Mummy ta shafa kansu ta ce " Allah ya kiyaye yayi muku Albarka "Da ameen suka Amsa har suka fice tana musu bye bye sosai Aira ta shiga ran Mummy Daman ita a rayuwarta tana son y'a mace sai taji Aira tamkar y'arta muddin Arman ya samu Aira a matsayin mata da saitafi kowa farinciki.
Kai tsaye Airport suka nufa duk Inda suka gitta ana kallonsu wasu hada cewa" Wallahi su d'inne "wasu kuma suce " laila majnon kenan"wasu kuma na gardamar couple's ne wasu na cewa a a saurayi da budurwa ne "kowa na fad'ar albarkacin bakinshi Dan cikin k'ank'anin lokaci video d'insu ya baza duniya duk Inda suka wuce ana kallonsu (๐nikam nace Aira da Arman fa kunzama cele)Cikin kankanin lokaci Arman yayi musu clearing d'in komai jirginsu ya tashi Cikin kankanin lokaci suka isa Kaduna Aira daman ba wannan ne lokaci na farko hawan jirginta ba idan zasuje garin su Mamy ko zasuje lagos gidan Aunty maryam a jirgi suke zuwa Aunty Halima ya kira yace sun iso suna Airport ta ce " su jira ga driver nan zaizo ya d'aukesu sosai sukayi mamakin anan d'inma kaduna sai kallonsu ake Itadai Aira duk ta tsure ga tunanin Gida Dan batasan irin hukuncin da Abba zai yanke mata ba driver yazo ya d'aukesu A hanya Aira ta kalli Arman ta ce "Yaya Saboda me kayi haka kasan Abba bazai kyaleniba" karki damu cutie nayi hakan ne saboda na gwadawa su Daddy kalar son da mukeyiwa junanmu Susan Soyayyarmu tayi k'arfin da bazasu iya rabamu ba hakan zai iya sawa su hakura su barmu mu mallaki juna"Aira badan ta gamsu da