NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   47 / 54

138K to 141K   out of 160.7K words

yarda ki tafi cikin halin nan ba Ni uwace zan iya fuskartar ko wani irin Abu amma Bazan barki ki tafi ba " Durk'ushewa Aira tayi tare da fashewa da kuka ta ce"Mamy Dan Allah ki koma ni banason na dinga zama silar rugujewar farincikinku zan tafi kamar yanda Abba ya fad'a duk ranar da ya huce zan dawo tana gama fad'ar haka ta kama hannun twins tana kuka sosai ta fita daga gidan Gaba d'aya Mamy ko binta tayi dak'yal Mama ta lallabeta ta maida ita ciki ta hanata fita Sosai take kuka tanajin haushin Abba Aira ko na fita dakalin kofar gidansu ta zauna tare da fashewa da kuka sosai takejin zafi a cikin zuciyarta twins ma kukan suke sosai a jikinta Naila nacewa "Mom kiyi hakuli Mu tashi mu bal musu gidanchu Tunda Dad enki baya chonki muma I hate him kuma duk sanda na gilma saina rama maki" rufe mata baki Aira tayi tama kasa koda magana sai kuka Yaran abun tausayi suma kukan suke Ganin mamansu na kuka a haka ARMAN yazo ya samesu cikin wannan halin sosai Shima hankalinshi ya tashi a mota ma Aira kuka kawai take ta kasa koda magana Twins ne suka ce"Hero Dad en mom ne ya chanyata kuka sai sannan arman ya gane Dalilin kukan na Aira Lallashinta ya fara amma taki magana sai kuka kai tsaye gov house suka wuce saboda yayi waya da mummy ta ce suzo nan suna isa Bayan sunyi parking a harabar Part d'insu suna fitowa Aira na hawaye har lokacin a harabar gidan suka ci karo da Mummy da Daddy sun fito Da gudu twins suka Ruga suka Rungume Mummy itama rungumesu tayi tana farincikin ganin jikokin nata Daddy ko tsaye yayi yana binsu da Kallon mamaki Kallon Mummy yayi ya ce "me ya kawo wadannan gidana" Ajiyar zuciya ta sauke ganin cikin nutsuwa yayi maganar ta ce "zanyi maka bayani idan ka nutsu Wannan yaran da kake gani jikokinkane yaran Arman ne Wanda suka Haifa da Aira Yaran sunna ne kuma y'an halak "sosai dad yayi mamaki Nihal ce tazo wajenshi tana Dariya ta ce " Dad en hero"Murmushin k'arfin hali yayi mata tare da daukarta Dan yanason yaran sosai tun kafin yasan jinin shine amma hakan bai hanashi tunowa da abunda Arman yayi masa ba Kallonshi yayi ya ce "Fitarmun daga gida karna k'araga kafarka ka tako cikin gidan nan bani bakai na Riga na shafe da labarinki Ubanme ya kawoka gidana" Rumtse ido Arman yayi yanajin zafi a ranshi zuciyarshi na tafarfasa cikin zuciya ya kalli Aira ya ce "Shiga muje " Shiga tayi tana Hawaye Kallon twins yayi dake hannun iyayen nashi ya ce "Ku taho mu tafi" mak'alewa jikin Su sukayi Alamun basu zuwa Cikin fad'a Mummy ta ce "Banson iskanci Arman bazaka bawa mahaifinka hakuri ba kai uban zuciya shine ma zakayi fushi to ka tafi d'in ko warce yaran zakayi a hannumu ka nuna mana kai ka haifesu ba muba" Arman baicewa Mummy komai ba sai Juyawa da tayi tare da bude mota da karfi ya shiga tare da tada motar ya figeta da gudu Tsaki Mummy taja tanajin haushin Arman yanda taga Daddy Ya sauko da ya bashi hakuri zai iya hakura Daddy ko sosai ranshi ya b'aci fasa fitar da yayi yayi ya kalli mom ya ce "Muje ciki " suna shiga Mummy ta bashi labarin abunda ya faru na hada Auren su da tayi sosai Abun ya bashi mamaki yanda ta rik'a boye mai Abubuwa har a zuciyarshi baiji zafin Mummy na hada Auren nan da tayiba tunda gashi hada zuri a da dole dai sai an haifi yaran amma Yaji zafin Arman yanda yayi masa hakan yasa ya karajin zafi a ranshi Idan kuma ya kalli yaran sai yaji soyayyarsu a ranshi ga yanda Nihal ta lafe jikinshi kamar daman ta sanshi sosai Mummy taji dad'in yanda Daddy bai nuna wani b'acin ranshi ba sai shiru da yayi Yana nazarin abubuwa da dama Jin ana kiran Magriba ya sanyashi Aje Nihal zai tafi masallaci taki barin jikinshi murmushi yayi mata ya ce "Amaryar tawa uwar son jikice kenan salla zanje inyi" Dariya Nihal tayi kamar tasan me yake nufi ta ce "Dad en hero kai bazaka dinga yiwa hero fad'a ba shi dad en Cutie mugu ne Kuka ya sanya mom Kuma bama sonshi saina halbeshi da bindigata" Girgiza kai dad yayi tare yimata murmushi ya ce "Eh bari na dawo daga salla saimuyi labarin" Mummy ko girgiza kai tayi gsky abunda Abba yake baya kyautawa gashi har yara kanana zasu kullaceshi Nihal ko dining ta nufa tare da Fara b'arna da abinci Kallon Naila da tayi shiru kamar mai tunani Mummy tayi ta ce "My takwara me ya faru kinyi shiru yau ba surutun kenan" Hawaye Naila ta fara ta ce "Mom ina cutie zataje kuka take dad enta baya chonta ya sata kuka Please kije ki bashi hakuli kice Yadaina sanya mom enmu kuka kuma mu bajamu k'ala juya wajensa ba"
Saida zuciyar Mummy ta karye jin yarinya k'arama na irin maganganun nan Gashi damuwa k'arara a fuskarta Goge mata hawayen tayi ta ce "Dad d'inta itama yana sonta Naila laifi tayi mashi shiyasa yayi mata fad'a kuma yanzu ya hakura sunje su dawo muje kici abinci Kinga y'ar uwarki wasanta take ko " ta fad'a tana nuna mata Nihal dake b'arna dak'yal ta samu Naila itama ta waske Inda take ta basu abinci sukaci sosai suka saki jiki da ita suka dinga mata surutu da labarai Wanda tare da Daddy suka dinga musu dimi Saidai suyi Dariya Dan labarin gida kowanne saisun basu.
Arman ko cikin fushi kai tsaye hanyar Kaduna ya d'auka ranshi na Mashi mugun zafi shi abunda yafi damunshima irin yanda yaga cutie d'inshi hankalinta ya tashi sun wuce Zaria Aira ta farajin ciwon baya da mara tun tana daurewa har ta kasa cije baki tayi tana Salati da mamaki Arman ya ce "Kina lafiya cutie me ya sameki" Kallonshi tayi yana nukurkusa ta ce "Cikina yaya bayana kamar zai balle" Sosai ya shiga damuwa Cikin kid'imewa ya tsaida motar Mummy ya kira tana d'auka cikin tashin hankali ya ce "Mummy kinganmu nan hanyar Kaduna Aira ba lafiya bayanta da cikinta wai ciwo" Subhanalla Mummy ta fad'a ta ce "ku hanzarta isa Kaduna ka kaita Asibiti zankira Halima ta sameku nakuda ce take" Da mamaki ya ce "Amma Mummy ba watan Haihuwarta bane" Eh inaga tashin hankalin da ta shigane ya turo nakudar ka maza ku tafi karta galabaita"Cikin Sauri yace to mom tukwana ya tada motar harsuka isa Kaduna Aira na Abu d'aya suna isa ya wuce da ita wani private hospital.........✍🏿


*Ni da Yaya Arman littafin kudine akan 200 kachal ta wannan number 07026166536*


_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[7/21, 09:47] Hajo hajo: 🅿️........*117&118*




Wani private hospital suna isa kai tsaye labour room aka nufa da ita ya nan yana safa da marwa yaji kiran Mama Halima Bayan ya d'auka ya shaida mata asibitin da suke ba ayi minti goma ba sai gata cikin rudu ya nuna mata d'akin da take Kallonshi tayi ta ce "kun taho da kayan haihuwarne?a a Mama bamu taho da komai ba " To.ka maza kaje ka sassayo da abunda za asa jaririn da komai nikuma bari naje "To ya fad'a duk ya rud'e tare da tafiya neman abunda Mama Halima ta fad'a ita kuma ta shiga ciki Inda ta samu Aira na labour sosai Sannu ta dinga mata a lokacin Tara na dare Karfe sha biyu Aira ta haifo d'anta namiji kyakyawa dashi mai tsananin kama da ita Bayan ta haihu a lokacin Arman ya kawo jibgin kayan da ya sayo hamdala kawai yake da yaji ance ta haihu Bayan anshirya jaririn itama Aira anshiryata d'akin Hutu aka wuce da ita saboda galabaita da tayi Gashi kuma taso tayi ikilamsiya saboda jininta da yahau Allah dai ya kiyaye Arman sosai ya ji soyayyar yaron a ranshi koda ya daukeshi cikin farinciki Yayiwa Allah Godiya Yau shine da yara har Ukku Tambayar Mama Halima Aira yayi ta ce " bazai samu ganinta ba saita huta sannan ta amshi jaririn ta ce "sauran kayan da ka jibgo ka wuce dasu Gidana sannan kace Hafsa ta gyara d'akinsu " to Arman ya fad'a nan takura ya shaida wa Mummy haihuwar itama Sosai tayi farinciki marar musaltuwa Aira ko sosai ta huta duk galabaice take Dan bama tasan abunda ta Haifa ba Mama Halima Tabawa jaririn ruwa gashi baiyi kuka sosai ba ranar Aira kwana tayi tana bacci Dan Dr d'in saida yayi mata allurar bacci saboda jininta da yau ya sauka washegari itace bata tashi ba sai 10 koda ta tashi Su Hafsa sunzo duk Sannu suka dinga mata Har Arman da yake tausayawa cutie d'inshi ganin yanda tayi firi_firi Mama Halima tayi mata wanka ta gasata sosai Bayan sun shirya ta bata yaron akan tayi feeding dinshi sosai Aira ta tsaya Kallon Yaran tanajin soyayyar shi kamar yanda takeson twins a zuciyarta ta ce "Allah ya raya munkai " a fili kuwa shiru tayi saboda nauyin Mama Halima da takeji Bayan an b'ata tayi Kari me kyau A yammar ranar aka sallamesu ta koma gida duk tayi shiru bata son magana sosai saboda ciwon kan da take "Wanda saida aka rubuta mata magunguna akan ta dinga sha.
Washegari Mummy tazo ita da twins a lokacin Aira na D'aki tana kwance Kanta banda ciwo ba abunda yake Dan tunda ta haihu take wannan ciwon kan Mummy ta shigo Tare da twins dak'yal ta tashi tana kirkirar murmushi ta ce " Sannu da zuwa mom"yawwa daughter ya jikin naki barka ko Allah ya raya k'asa da kanta Aira tayi Twins ne sukaje Wajenta Suna mata murmushi itama mayar musu tayi Naila ta ce "Sannu cutie mom ya jiki baby boy d'in da muka gani namu ne ko"? Itama Nihal cewa tayi " Mom ai boy dinmune ko wai Mama tace bazata bamu ba ta fad'a tana turo baki"Dariya Aira tayi ta ce "sarakan surutu " Dariya Mummy tayi ta ce "Kunga kubar maman taku ta huta" k'iyawa sukayi suka D'are Aira Girgiza kai tayi sannan ta Kalleta ta ce "Ki fad'a abubuwan da kike buk'ata a sunan daughter saina taho maki dashi Dan anan za ayi sunan tunda naga jikin naki ba adinga yawo dake ba " Kasa tayi da kanta ta ce "ba komai Mummy duk yanda Mummy tayi Aira ta fad'a abunda takeso kiyawa tayi ta ce komai ma ta yanke yayi " Ita Mummy duk sai ta bata tausayi ganin irin sanyin da tayi Lallashinta ta dingayi gami da nasiha Cikin hikima "Da yamma Mummy suka wuce tare da twins dan yanzu sunyi mugun sabawa da mum " da dare Aira na kwance tana kallon boy d'inta Arman ya shigo Dagowa tayi ta Kalleshi da murmushi a fuskarsa ya zauna tare da d'aukar jaririn ya ce "Sorry my boy yau bamu gaisa ba ko to ya jikin mom d'in taka" ya fad'a yana kallon Aira ya ce "ya jikin cutie" Murmushi ta masa ta ce "Alhamdulilla" "Allah ya k'ara maki lafiya uwar y'ay'ana yasa kaffarane " Ameen ta fada "Huduba tayima yaron Bayan ya gama Kallonshi Aira tayi ta ce " wani suna ka sanya masa "Aliyu Haidar " Munyiwa Bappa takwara Saboda shi ya zama silar samun wannan farincikin namu "Murmushi Aira tayi Tabbas hakane ta ce " Allah ya raya my hero ka kyauta kuwa "Sun tab'a Hira cikin so da k'aunar juna sai wajen 11 yabar D'akin da Haidar a hannunshi saboda yaron baida rigima Sosai Arman keson Haidar saboda kamannin cutie d'inshi da yayo " Hafsa ce ta shigo d'akin da farfesu a hannunta ta ce "Sis gashi Mama ta ce kisha karki sake tazo bakici ba" Dariya Kad'an Aira tayi ta ce '"Uhm my Mama kenan"Zaunawa Hafsat gefenta tana mata hira Bayan Aira ta cinye Kallon Hafsa tayi ta ce "Hafsa Dan Allah aroman wayarki zanyi kira banda layin nan k'asar" Mik'a mata wayar tayi number Aysha Ta dannawa kira Bayan ta d'auka "Aysha ta ce " Sis kina lfy dazu amma ke fad'amun Abunda Abba yayi maki wlh banji dadi ba yanzu kina ina?Goge hawayen da suka zubo mata Aira tayi ta ce "Ina Kaduna sis Na haihu ina gidan Mama Halima" Cikin farinciki aysha ta ce "Wow masha Allah me muka samu" Baby boy "ta fad'a kasa kasa" kai amma nayi farinciki wlh Allah ya raya insha Allah gobe Nida Ummy zamu taho har sai anyi suna tukwana bari nafadama honey Babban Albishir murmushi Aira tayi Bayan ta katse kiran number Mamy ta kira a lokacin Mamy sun gama fadansu da Abba tana d'aki Taga kiran Hafsa jin muryar Aira ya sanyata sauke ajiyar zuciya ta ce "Kina lfy Aira tunda kika tafi hankalina bai kwanta ba" Ajiyar zuciya Aira ta sauke ta ce "Ina lafiya Mamy ina Kaduna Ma gidan Mama Halima" Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce "Alhamdulilla gwara da kikaje Chan Dan Allah kici gaba da hakuri ki kwantar da hankalinki ba ason mai juna biyu na damuwa Kinga yanda kike " Murmushin K'arfin hali Aira tayi ta ce "Mamy ai na...sai kuma tayi shiru tanajin nauyin abunda zata fad'a " Dariya Hafsat tayi tare da Amsar wayar ta ce "Mamy so take ta ce maki ta haihu tun jiya mun samu baby boy" Cike da farinciki Mamy ta ce "Kai Alhmdllh amma nayi farinciki wlh Allah ya raya yanzu wannan cikin nata Har isa haihuwa nazata da saura " eh wlh Mamy Naji Mama tace ba watan Haihuwarta bane kawai tension ne ya kawo nakudar kuma ma tunda ta haihu bata da lafiya ciwon kai take kullum ikilamsiya taso ta sametama Allah ya kiyaye Amma yanzu da sauki "cikin tashin hankali Mamy ta ce " Subhanalla Oh ni Rahama Kenan Bata da lafiya bata wayar"Hararar hafsat Aira tayi ta ce "wa yace ki fad'a mata kinsan zata tashi hankalinta " A lokacin Mama ta shigo "Amsar wayar Aira tayi ganin yanda Mamy ta damu ta ce " Mamy lafiya ta fa qalau karya take"Sosai ta kwantarwa da Mamy hankali ganin yanda ta rude Hartana cewa kodai ta taho dak'yal ta samu hankalinta ya kwanta "Bayan sun gama wayar mik'awa Mama Halima wayar Aira tayi nan suka shiga gaisawa da Mamy Inda Mamy tayi mata Godiya Ta ce " bakomai ai Aira y'atake a Wajenta abunda zatayiwa Hafsat dole shi zata mata nan suka jajinta abunda ya faru a baya Mamy ta ce "Wai kina sanin kema bakisan abunda ke faruwa ba sai yanzu" Girgiza kai tayi ta ce "Wlhko banida masaniya komai Kawai sai kirana Hajiya Fatima tayi akan naje Asibiti sai jiya da tazo take fad'amun abunda ke faruwa na ce " ai da ta fad'amun tunda dai nima da Bayan goyon abun zan bada Allah dai ya kyauta ya kawo mana karshen AL amarin nan"Ameen Mamy ta fad'a Bayan sunyi bankwana Mama Halima ta Kali Aira ta. Ce "ki daina sanya damuwa a ranki Mamana jifa kin haihu keda zakiyi k'iba kiyi kyau amma ramewa kike " Kasa tayi da kanta ta ce "To Mama" Bayan fitar Mama kulli Aira ta kaiwa Hafsat ta kauce tana Dariya Hafsat ta ce "Wlh sis mamaki nake wai muna sa anni amma kece hada yara ukku" Dariya Aira tayi ta ce "me yafi son ranki kema ki fito mana da miji kawai musha biki" murmushi Hafsa tayi tana far da ido ta ce "Ah bakisan an sanya aure na ba ni da yaya omar" wara idanu Aira tayi ta ce "wanne yaya Umar din " Dariya tayi ta ce "naku mana " Sosai Aira tayi mamakin ashe soyayyar Hafsa da yaya omar kamar wasa ta zama gaske sosai kuma tayi farinciki da hakan suna cikin hirar ya kiraa Inda Hafsa daman ta fad'a masa komai a waya Aira Tabawa wayar sosai yayi farincikin jin muryar y'ar uwar tashi nan yayi mata barka tana jin kunya Daga karshe ta ce ya gaishe da Aunty Khady Dariya yayi ya ce "Abokiyar fad'ar taki zakice zataji insha Allah gobe zuwa jibi zanzo naga jikin naki kinji y'ar kanwata Allah ya raya mana boy" Dariya Aira tayi ta ce "To yaya Allah kawoka lfy tukwana ta mik'awa Hafsat wayar saida suka gama shan love d'insu tukwana suka yi bankwana Kallon Hafsa Aira tayi tana Dariya ta ce " zakici gidanku hannun basamudiyar Matar nan Dan wlh ta zauneki saikin hango k'abari ni zan baki labarinta"Sosai Hafsat ke Dariya hada rik'e ciki ta ce "yarinya kedai zatayiwa taganki haka kamar fara amma ni kam Saidai mu chashi juna sannan ma ina zan ganta muda ba gida d'aya zamu zaunaba ya ce " gida zai raba mana"Nan suka cigaba da Hira har bacci ya kwashesu .
Washegari kamar yanda su Aysha suka fad'a ita da Ummy sukazo daga gidajen mazajensu Sosai Aira tayi farincikin ganin y'an uwan nata nan suka shiga d'aukar Haidar suna yabawa da kyan yaron Aysha ji take inama nata Har saida tayi hawaye a b'oye Mamy duk sanda taso tazo Abba ya hana Dan ta fad'a masa Aira ta haihu ya ce "bazataje ko ina ba cikin su Duk Wanda yaje a bakin aurenshi Mamy Kad'an Ya hana ta tafi in banda Aunty Ramlat da ta kira ta dinga mata nasiha akan ta zauna ita zasuje gobe ayi komai dasu ta kwantar da hankalinta a haka suka samu Mamy ta zauna Amma taso taje Amma ganin yanda Abba ya hana iyayensu ma zuwa ina ita ina tunkarar zuwa.
Yayyun Mamy Duka saida sukaje kd din Har Matar Yayanta ana jibi suna sukaje Wanda hakan sosai yayiwa Aira dad'i koba komai wannan Karin akwai dangin mahaifiyarta da na mahaifinta a sunan y'an uwan mummy ma na yola duk sunzo Ranar suna yaro yaci suna aliyu Haidar k'aton sa Arman ya yankawa d'an nashi sosai a wannan sunanma yayi b'arin kudi Aira ko shigar da tayi ma fad'ar tsadar da kyaun kayan b'ata baki ne Sosai tayi kyau dukda bata da walwala saboda batajin dadi tunda ta haihu k'arfin hali ne kawai take haka akayi taron suna aka gama

47 / 54