Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
mik'awa wayar ta ce " gashi Mama "Kallonta Mama tayi ta ce " ba kince zaki ara wayarba tafi da ita"Sosa kai tayi tana murmushi ta ce "Shikenan Mama" Daman shine zaki kira kuma ya kira ko?Mamy tafada tana Harararta b'ata rai Aira tayi tayi ta ce "Ai nidai bance ba sannan ta d'auko Ameer dake k'asa yana rarrafe ya Mike zai Fard'o kayan kwalliyar dake mirror ta ce " wannan D'an naki mab'annaci ne Wlh""Ai bai kai k'afar b'arnar da kikayi ba "inji Mamy " kai Mamy nidin kuma ta fad'a tare da barin d'akin tare da Amer suna fita Mama Halima ta kalli Mamy ta ce "Kidinga janta a jiki Dan Allah inba wajenki ba ba ina zataje taji sanyi " Girgiza kai kawai Mamy tayi ta ce "Ina bakin kokarina Halima wlh ni abunda yasa ma tun farko na nuna banason tarenta dashi karya lalatamun y'a shiyasa nidai tawa addu'a ce kawai Dan wlh yarinyar nan tayi nisa yanda baki tunani" ba abunda zai faru sai alkhairi insha Allahu addua zamuyi tayi Ai nice shaida wlh yaran nan ba k'aramun so sukeyiwa junansuba ranar sunjima suna tattaunawa akan Lamarin su Aira.washegari mama Halima suka shirya zasu tafi harsun fito da kayansu Aira sai magiya take abar Hafsat itama Hafsat din tana so a barta Mama ta ce "a a a ita takemun aiki wlh itace k'arfin aikin gida kunsanni ba maid house nake daukaba " Mamy ta ce "kedai kin k'iwace wlh Halima ki barta ta d'an huta ko sati biyu ne" Dariya Mama tayi ta ce "bazakiganeba wlh Ban iya aikin gidan nan ni kadai anma zatazo kwanannan"Yaya Umar ne sukayi sallama shida matarshi Kallon Mama yayi ya ce "Mama badai tafiya ba" wlhko babana wucewa zamuyi wai"Kallon Hafsat yayi ya ce "Amma ba da ita ba zaki tafi ko" Dariya tayi ta ce "Tare " haba Mama Ki barta mana ta kwana biyu wai meyasa bakyason barinta tana zumunci"Mamy ce ta ce "kaima dai ka fad'a " Hafsat ce ta ce "Dan Allah Mama ki barni ko 1week ne nayi" Mamy ce ta amshi Jakarta ta kaya ta ce "mun rinjayeki ba Inda zata " Dariya Mama tayi ta ce "Ai dole ma na barmuku ita Anyimun chaaa Hafsat sai murna take Ita da Aira Airace ta rad’a mata ta ce " wai Sis bakiga yanda yaya Umar ke kallonki matarshi sai Aiko miki harara take"Dariya Hafsa tayi ta ce "Kai Aira sharri Juyawa sukayi suka koma ciki Mama Halima ta tafi.
Washegari Wajen la'asar kasancewar girkin Mama ne gashi Y'ar aikinsu batajin dad'in bata zoba Mama ta shiga kitchen tana girki Khady tana ganin yanda take aiki da zirga zirga ko Sannu batacewa Mama ba bare har ta tayata " Itako Mama bata damuba Dan ta saba Aira ce ta Hafsa suka fito palour suka zauna Sukace "Sannunku da hutawa Yaya" Yawwa Y'ar Inna Sosai Umar ya dinga Jan Hafsa da Hira Khady ta cika tayi Fam Airako Kad'an Ya hana tayi dariya hakan yasa take tsunkunin Hafsa akan ta k'ara chusa mata Haushi itama Hafsat da Jan magana tashi tayi taje kujerar kusa dashi ta ce "Yaya please ka kaini naga gari Dan na shaida nazo Hutu nima" Cike da farinciki Umar ya ce "Aiko yanzu zaki shiga gari kanwata jeki shirya" Khady ce ta mik'e cike da b'acin rai Ta ce "wannan wani irin iskanci ne to ba Inda zaka kaita wlh ta tari napep mana ta hau inbanda tsabar iskanci ka tashi mu tafi ni gida nake so muje mu huta da bakazoba da wa zai kaita " Bata fuska Umar yayi ya ce "Meye haka Khady banson iskanci gaban yara idan gidan zaki ga hanya nan ki tafi ko dole saidani" Aira me zatayi inba Dariya ba hada durk'ushewa Amma kasa kasa take yanda bamaiji Hafsat ko itama ji take kamar ta fashe da dariyar Aira Dan ta k'ara chusa mata Haushi ta ce "Haba Aunty ki bari mana ya kaita bakuwace kafin su dawo ma Kinga kin kara hutawa naga kamar gajiye kike" harara Khady ta gallawa Aira tare da Jan tsaki Hafsa ce ta tashi ta ce "Daman da wasa nake wlh " Tashi sukayi ita da Aira suka koma bedroom d'insu suna kwasar Dariya.
Da dare Aira ta lallaba Amma ta ce "Dan Allah sis kaya na zaki daukomun a bangaren Inna wayoyina na cikin d'akin Dan Allah daukomun " Dak'yal ta samu Amma taje ta d'auko mata Allah yasa lokacin da wuta Aiko tasa wayoyinta Duka chaji k'aramar Kara d'aya tayi ta maza ta bud'e tana kiran shi saida ya katse ya kira Ajiyar zuciya ta sauke Suka shiga gaisawa cikin so da k'auna kwancewa gado Aira tayi rufda ciki tana jin farinciki ya mamaye zuciyarta Sunjima suna waya tukwana ARMAN ya tambayeta Ya sukayi da Abba Duka ta fad'amai amma bata fad'amai maganar karshe ba na Aure zaiyi mata Dan bata d'auki abun serious ba "Ajiyar zuciya Arman ya sauke ya ce " Ai wannan ni Abba ya taimaka bai sani ba ya hanaki fita bare wani ya ganemunke har yace yana so,makaranta ma hakan yayimun dad'i Daman ina kishin shigarki makaranta kowa ya dinga kallemunke a bilis"na Ukku kuma abunda bazai tab'a yiwa bane har abada Watau rabuwarmu Kinga ko ai Hukuncin mai sauki ne "Dariya Aira tayi ta ce " kai yaya kuma fa hakane sai kuma ta bata fuska ta ce "To idan munason mu hadu yazamuyi Bayan ya hanani fita" murmushi yayi ya ce "banida damuwa da wannan saboda duk sanda naso ganinki dole saina ganki ko ana ruwa ko ana iska Allah yana tare damu Insha Allahu" wani sanyi Aira taji a ranta kwata-kwata ma Arman ya kwantar mata hankali Sai takega Duka hukuncin ma da Abba ya yanke mai sauki ne sunjima suna shan hirarsu gwanin sha'awa cikin so da kaunar juna.
Hafsa satinta guda Driver yazo daukarta a lokacin Su Yaya Umar sunzo sosai yayi mata tsaraba su Mamy ma sunyi mata tsaraba sosai Airako hada kuka duk saitakejin ba dadi itama Hafsa din Har zasu tafi Aira da Jan magana ta ce "Yaya ka amshi numberta kuwa" mik'a mata Wayarshi yayi ya ce "Amshi ki sanyamun ki sanya mata tawa mundinga gaisawa a waya tunda bata da zumunci " murmushi Hafsa tayi ta ce "Yaya aikai dinne ganinka ke wuyar gani" cike da gayya Aira ta sanya musu numbobin juna Khady ji take kamar ta shak'e Aira sai aika mata da harara take da abun ya isheta tsaki taja tare da ficewa tabar gidan Gaba d'aya "girgiza kai ya Umar yayi sannan ya kalli Aira ya ce " so kuke ku haukatamun mata ko"Dariya Aira da Hafsa sukayi suka tafa Hafsa ta ce "To me aka mata kawai kishidai yayiwa Matar ka yawa " Dariya Aira tayi hada rik'e ciki Mamy dake kallonsu girgiza kai tayi ta ce "Allah shiryeku" Mama ko Addua tayi ta ce "Allahsa Umar son Hafsa yake wannan Matar zamanta ita kadai gidan dana matsala ce " Hafsa Na tafiya Aira ta koma ciki duk batajin dad'i.
Haka rayuwa taci gaba Aira bata zuwa ko ina Abba ya fad'awa me gadi kar asake a barta fita Amma tuni harta fara zuwa makaranta hakan ko Kad'an bai damu Aira ba Saboda tana shan wayarta da Arman kullum Daki take rufewa susha wayarsu da video call da dare ko raba dare suke suna shan love Harsai Amma tayi fafatu akan sun hanata bacci Daman Haidar ya koma bangaren Inna yake tayata kwana.
A haka har akayi wata guda ranar wata juma'a Arman ya kirata ya ce ya shigo kano kuma yanason su hadu tasan yanda zatayi ta fito su hadu Sosai hankalin Aira ya tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye Mamy taje ta samu tana hawaye ta ce "Mamy Dan Allah gidan Aunty Aisha nake so naje ki taimakamun naje kafin Abba ya dawo Allah na dawo" Wlh Aira ba ruwana Tunda Abbanki ya hanaki fita kawai ki hakura yanzu Abun na barki ki fita ne ni kaina matsala zaki jamun ba ruwana karkije ko ina idanma Aishar kikeso Kuyi magana amshi wayata ki kirata"Goge hawayenta Aira tayi ta ce "Shikenan Mamy ba sai na kira ta ba " ta fad'a tana barin d'akin saida Mamy ta tausaya mata Aira na komawa gado ta fad'a tare da kiran Arman yana kira ta fashe da kuka ta ce " Yaya mamynma ta hana "kuka kawai take Lallashinta yayi ya ce " jeki ki samu mai gadi ki lallabashi kiga zai bari ki fito "to Aira ta ce sannan ta fita tana zuwa ta samu Baba mai gadi najin radio har k'asa ta durkusa ta gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska Zaunawa tayi gefenshi ta ce " Baba Dan Allah fita nakeson nayi "Dayake baba suke cemai tsohone sun jima dashi " kallonta yayi ya ce "Kiyi hakuri Hajiya Alhaji yayimun kashedin na sake na barki kika fita a bakin aikina ni kuma aikin nan dashi nake sha nake ci shine rufin asiri na bazanso rasa shi ba Dan haka kiyi hakuri bazan bud'e miki k'ofa ba" Cikin tashin hankali Aira ta fara kuka ta ce "kayiwa Allah da girman manzon Allah S a w Baba ka bari in fita wlh ba zanja maka matsala ba yanzu zan dawo........✍🏿
*Ni da yaya arman Littafin kud'i ne ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa #200 Katin MTN to 07026166536*
*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/14, 18:32] Hajo hajo: 🅿️........*43&44*
Gaskiya kiyi hakuri Amma bazan bud'e maki ba idan har ba mai gidan bane da kansa ya ce na bud'e maki ba "jin abunda Baba mai gadi yace ya sanyata tashi ta Ruga ciki da gudu tana kuka tana zuwa ta fad'a kan Gado tare da fashewa da kuka saida tayi kukanta mai isarta Arman ne ya kira d'auka tayi cikin kuka ta ce " Yaya Baba mai gadi ya hanani fita wlh ba irin magiyar da ban mashi ba "daga dayan bangaren Arman sosai baiji dadi ba cewa yayi " ki kwantar da hankalinki kinsan bansan kukanki kuma ke baki tashi yi sai gabana"share hawayenta tayi tare da turo baki kamar yana gabanta ta ce "To ba dole nayi kuka ba kana gari amma anhanamu ganin juna" To sai kiyi shiru mu nemi mafita ko kukan shi zai zame mana mafita"a a yaya "Numfasawa yayi ya ce " matsala ta dake baki iya dabara ba ke a y'an farin ma shugabar faranta ce Wlh ko k'aramun yaro ya fiki wayau "ya fad'a da sigar zolaya " Kamar zatayi kuka ta ce "Ni wlh ba y'ar fari bace Kaine ma za a ce d'an fari kuma auta tunda baka da yaya baka da k'ani Niko ina da yayyu ina da k'anne" ta fad'a tana turo baki "Dariya Arman yayi ya ce " yau naja gori ko to ai ni bana abubuwan y'an fari keko ko maganarki ta y'an fari ce "Allah yaya ka bari zanyi kuka" ta fad'a cikin shagwaba "Dariya yayi ya ce " sorry my cutie kar ayi kuka ayi hakuri"turo baki tayi ta ce "Kai naga bama ka damu ba da Rashin haduwarmu ko" hmmm bazaki gane bane cutie wlh nafiki damuwa kawai taurin haline kinsan maza da dauriya"Uhm tace"kinsan me za ayi"a a saika fad'a "Yanzu bari zakiyi jibi saboda gobe idan Kikayi ganewa za ai kije ki kaiwa mai gadi kudi kice Mamy ta ce ya sayo mata wani abun kinsan dai abunda zakice ke kuma yana fita ki maza ki fito " tsalle Aira ta buga akan Gado ta ce "yesssssss wlh yaya wannan dabarar tayi kwata_kwata ni banma kawo hakan a kaina ba" Dariya yayi ya ce "to kindai yarda kece y'ar farin" Turo baki tayi ta ce "Uhm ban yarda ba Kaine dai Dan fari'" sun tab'a Hira cikin nishad'i tukwana suka kashe suna gama waya Hafsa ta kira tana d'auka ta zolayeta da "Matar yayaana" Dariya Hafsa tayi ta ce "Mrs Arman ake gaya muku" murmushi Aira tare da dafe saitin zuciyarta ta ce "wayyyyo har kinsa Naji wani sanyi a cikin zuciya kai Gaskiya kinci katin 1k " Dariya Hafsa tayi ta ce "Allah shiryeki" Ameeen indai akan Yaya Arman ne Kuyi tayimun Addu'ar ya ake ciki ne wai har yanzu yaya Umar na Kiranki"ke inaso na baki labari kullum fa sai yaya Umar ya kirani musha hira kawai jiya ingaya maki Matarshi ta kirani ta dinga surfamun zagi ta uwa ta uba hada cewa wai "na k'ara kira mata miji saita sa an sauyamun kamanni" Hafsa ta k'arasa fad'a tana fashewa da Dariya "Dariya Aira ta fashe da ita ta ce " wayyo Allah cikina amma Gaskiya abun nan ya bani nishad'i Ai daman Nasan Bazata barkiba shegiya y'ar wahala"Dariya tayi ta ce "Ai na dinga chusa mata Haushi kenan tunda mahaukaciya ce" cikin dariya Aira ta ce hhhh kici gaba da gasa mahaukaciya Wai yace yana sonki kuwa"Uhm ke wlh baice yana sona ba shifa kawai a zumunci yake kirana ita kuma ta d'auka sona yake"haba Hafsa Ai yaya Umar sonki yake kawai wlh kawai fad'a maki ne baiba"Uhm kawai Hafsa tace tukwana suka saki hirar suka koma wata sunjima suna waya tukwana sukayi bankwana.kamar yanda Arman ya fad'a ranar Da wajejen Ukku Aira ta shirya cikin doguwar Hijab d'inta purple me hannu sosai tayi mata kyau a palour ta tarar da Mamy tana kallo "Sannu da hutawa Mamy" ta fad'a tana zama kusa da ita"kallonta Mamy tayi ta ce "Yawwa " Mamy Dan Allah 1k zaki bani"me zakiyi da 1k"Sosa kai tayi tama rasa k'aryar da zatayi sai chan ta ce "Uhm Mamy awara zan bada a sayoman "hmm jeki jikin drawer kayan Amer akwai jakata ciki ki d'auka saiki maidoman chanjin" Cikin murna ta tashi ta ce "Thnks you my dear mom ta fad'a tare da shiga taje ta d'auko zata fita Mamy ta ce Ina kuma zaki keda Abbanki ya hanaki fita" kamar zatai kuka ta ce "Mamy Bafa wani waje ba zani Ba Bala mai bawa flower ruwa ne zanba ya sayoman"to dan Allah karkije ko ina" To Mamy ta fad'a tare da fita tana zuwa ta tarar da Baba me gadi zaune cewa tayi "ina yini Baba Sannu da hutawa " yawwa y'ar kirki "Baba gashi inji Mamy ta ce Ka amso mata kati Dan Allah " Amsa yayi yace "to bari a amso na nawa" na d'ari biyar "yana fita Aira tayi Sauri ta lek'a taga ya danyi nisa a guje ta fice tayi d'ayar center saida ta daina Hango gidansu tukwana ta tsaya tana hak'i kiran Arman tayi ta ce " yi Sauri yaya kazo ina daidai karshen layin gidanmu kwanar wannan ta biyu zaka ganni"To cutie ganinan "Huci kawai Aira take Dan tayi gudu ba ayi minti goma ba saiga Arman saboda gudu ya sharara tana ganin motarshi cikin Sauri tana waige ta shige gidan Gaba sai hak'i take" Ajiyar zuciya dukansu suka sauke a tare kallonta Arman yayi ya ce "Badai gudu kikai ba" haba yaya meye ma banba muje dai kar wani ya ganmu ta fad'a tana rufo kofa "Jan motar Arman yayi suka bar unguwar sai kallonta yake itama tana Kallonshi a hankali ya ce " kinyi missing Dina kuwa cutie"cikin shagwababbiyar murya ta ce "my yaya ai ko ban fad'a ba fuskata kanta ta isa ta shaida maka kalar missing dinka da nayi" murmushi yayi ya ce "kuma zuciyoyinmuma sun isa su shaidawa junansu kalar kewar juna da sukayi ko" Eh mana my yaya ai yau jina nake kamar salla fa"Dariya yayi ya ce "Nikuma ji nake kamar Anyimun Albishir an yafe mani Duka laifuka na" Dariya tayi ta ce "Yaya kenan "Shima cikin murmushi ya ce " cutie kenan ina sonki fa sosai"murmushi tayi ta ce "Nima ina sonka sosai yayana sonda bana kwatantashi da komai" d'ayan hannunshi ya mik'o ya kama lausassan hannunta kamar auduga murza hannun ta yake cikin wani irin salo ita kanta Aira jin sak'on nashi take Sunkai tsayin minti kusan Ukku ba Wanda yayi magana ji tayi Arman yayi parking tare da kallonta cikin Wace irin murya mai cike da kasala ya ce "Mu yiwa juna Alk'awarin bazamu rabu da juna ba duk rintsi duk wahala please cutie" Aira batasan lokacin da wasu ziraren hawaye suka fara zarya daga idanunta ba Cikin muryar dake shirin fashewa da kuka ta kalleshi ta ce "my yaya" juyowa yayi ya Kalleta idanunsu suka sartse Cikin na juna kafe juna sukayi da idanu bako k'iftawa kama d'ayan hannunshi tayi hawayen dake idanunta suka zubo a hannuwansu ta ce "Alk'awarin mu ya na nan yaya karkatab'a kawowa a ranka cewar zan manta dakai bazan tab'a iya rayuwa babu kai a tare dani ba kaid'in ka zamemun wani bangare na jikina kamar yanda mutum baya rayuwa ba tare da zuciya ba to kamar haka rayuwata take muddin idan babu kai a cikinta bata da amfani" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka tare da Rungumeshi "daddab'a bayanta Arman ya fara tuni zuciyarshi ta karaya da jin kalamanta Shima jin yake da zai samu damar da yayi kuka cikin sigar lallashi ya ce " nima ta bangare na hakan take Aira kullum fad'a nake ina Kara fad'a. Sonki daga Allah ne na kasa iya misalta kalar son da nake maki a cikin raina Inajin a jikina duk ranar da su Abba sukayi sanadiyar rabamu to ranar ce ranar ajali na.."rufe mai baki Aira tayi cikin kuka ta ce "Ka daina fad'ar haka yaya bazasu iya rabamu ba banason kana maganar rabuwar nan tana tayarmun da hankali"daddab'a bayanta ya fara Dan son kwantar mata da hankali ya ce " Ai daman Nasan abunda bazai tab'a yiwa bane tashi ki yi shiru ki kalleni"kamar yanda ya fad'a tashi tayi daga kanshi tare da Kallonshi murmushinshi mai tsada ya sakar mata batasan lokacin da ta mayar mashi da kayataccen murmushin ta yake Kara mata kyau "mu yiwa juna alkawari" ya fad'a ya d'ora Hannunshi ya Aje itama ta d'ora nata a kan nashi tare suka ce " Alk'awarin mu na nan har abada"Goge hawayenta Aira tayi Ta ce "Yaya ina zamu"