Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
harararshi Tayi ta ce "Ni ba hali na ba tayo wannan ai gulmace take kuma Zakisan ni kika Zagarwa uba daga yau ba ruwana dake" Ta na gama fad'a ta zauna Kan Gado tana girgiza k'afa "girgiza kai Arman yayi ya ce " Yanzu dai yi hakuri tashi ki shiryasu mu fita"Turo baki tayi ta ce "Allah wlh kaji na rantse bazan shiryata ba Saidai kai ka shiryata" Dariya yayi ya ce "ta turo maki baki kema kinturomun kinga an fanshe 1-1 kenan to ni bari naje na shiryata kafin na shiryata kishirya sauran" Bata ko kallesu ba harya fita sai Haushi takeji a haka ta shirya Nihal da Haidar itama ta shirya sosai sukayi kyau gwanin burgewa nan d'akin Arman yazo ya shirya Naila dake like dashi kar Aira ta daketa A tare suka fito gwanin ban sha awa kai tsaye wani katafaran mall suka wuce Inda kowa ya jibgi abunda yakeso daga nan ya wuce dasu ya kaisu park sosai ya nishad'antar da iyalin nashi suka ci sukasha sannan sukasha hotuna sai wajen isha i suka koma gida har lkcn Aira zafin maganar Naila takeji ko magana bata mata abun ne ya isheta suna zaune a palour Naila da Nihal na Game a tab d'in d'insu suna gefen Arman Haidar ko na hannunshi yana masa wasa yana Dariya janyo wayarta Aira tayi ta lalubo number Mamy tana d'auka ta fashe da kuka sosai hankalin Mamy ya tashi ta ce "Lafiya Aira meya faru" Su Arman ma da twins duk kallonta suka tsayayi cikin kuka Aira ta ce "Mamy Dan Allah yaushe zakizo kinganninan har yara sun fara yimun gori wai iyayena bakwa sona ta k'arasa fad'a tana rushewa da kuka " Arman sosai yayi mamakin maganganunta ya k'ara tabbatarmai da airantashi dai har yanzu ta da d'ince dai "mamy ko cewa tayi wasu yaran ne suka maki gorin" Mamy Naila ce Hada cewa wai babana mugu ne "Tsaki Mummy taja ta ce " nazata ma wacen macen arzikice akan jariran yaran nan kikemun wannan kukan Allah ya shiryeki ni ban iya shiririta ba sanda kika dawo daidai munyi waya "tana gama fad'ar haka ta katse kiran " Fashewa da kuka Aira tayi sosai "Arman ne yaje tare da Rungumeta ya Ce " Haba Aira akan Naila ne duk zaki d'aga hankalinki kiyi shiru kinsan ba abunda na tsana sama da kukanki bazata sakeba daga yau"To ba kaibane ka goyi Bayan ta rainani ba kuma ko Ka bani hakuri"Murmushi yayi tare da "Goge mata hawayen ya ce " to yi hakuri bazamu sakeba"Nihal ce tazo tare da hayewa kan Aira tana Goge mata hawaye ta ce "Sorry mom
" Goge hawayenta Aira tayi tare da d'aukar nilah ta ce "Na hakura yarinyar kirki Allah miki albarka" Amen Nihal ta fad'a tana Lafewa jikin Aira Naila ce ta taho tana Hawaye ta ce "Sorry mom bajan zakeba" Harararta Aira tayi tare da d'aukar Nihal tayi sama da ita ta ce "Muje mu kwanta my Beloved Daughter kuma Mummynah " Dariya Nihal tayi tana yiwa Naila gwalo Suna barin Wajen Naila ta fashe da kuka Lallashinta Arman ya dingayi amma ta tubure Dak'yal ya samu bacci ya d'auketa tana bacci Dakinsu yaje ya kwantar da ita Shikuma ya wuce d'akin cutie d'inshi .
Washegari ayra Tarairaiyar Naila ta dingayi Dan Naila taji Haushi yanzu ma tana cinyarta tana bata choculate ta kunna mata game a wayarta tanayi Naila na gefe tana hawaye Ganin Haka ya sanya naila fashewa da kuka tare da zuwa taje ta haye Aira ta ce "Dan Allah mom kiyi hakuri Allah na daina bazan sakeba" Shafa kanta Aira tayi ta ce "Na hakura Amma kika sake me zan maki" Dagowa tayi tana Hawaye ta ce "Ki dakeni Mom Allah bazan sakeba " Murmushi Aira tayi tare da Rungumeta Itama ta ce "To yi shiru my prince's d'ina " Sosai Naila taji dad'i .
Washegari Aira ta shiryasu sukaje gidan maman noor Bayan ta turo mata address din gidan Sosai Taji dad'in zuwansu a motarta Aira ta tuk'a sukaje Twins da noor kuwa Sai wasa suke Sai magriba sukayi mata bankwana Bayan ta cika twins da abun arziki Washegari kuma kawarta Jannat ta kawo mata ziyara itama ganin twins tazo.
Hutunsu na karewa na makaranta Mummy ta aiko Aka tafi dasu Suka koma Inda Aira gidan yayi mata ba dad'i haka rayuwa taci gaba duk Hutu ana kawo twins suyo Hutu su koma A haka har Haidar yayi wata Bakwai Wanda yaron yayi wayau sosai ga kyau da shiga rai .
Yau Aira tunda Arman ya tafi Wajen aiki takejin fad'uwar gaba Hakanan kawai takejin kamar wani Abu marar dadi zai faru Haidar ne dake Kuka ta hau jijjigashi Bayan ta bashi abincinshi ta samu yayi shiru tana nan zaune Taji shigowar motar Arman Bayan ya shigo cikin shigar kayan aiki ya Kalleta ya ce "My Prince's ya dai naga Sai wani k'ara kyau da k'iba kike kwanannan " murmushi kawai tayi tare da mik'a masa Haidar ta ce Hero.Wlh gaba na ke fad'uwa tun d'az...bata k'arasa fad'a ba sakamakon ruri da wayarta ta fara Duba mai kiran tayi taga bakuwar number d'auka tayi tare da karawa a kunne Muryar amma taji tana kuka ta ce "Sis ki maza duk inda kike ki taho yanzu " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un meke faruwa sis wanine ya mutu "Aira ta fad'a tana dafe k'irji "Inna ce ba lfy muna asibitin Mallam aminu kano sunanki Dana yaya Arman kawai take ta fad'a a kira mata ku" Tuni Aira hankalinta ya tashi cikin kuka ta ce "Na shiga ukku sis gamu nan katse kiran tayi Arman da jira yake ta gama yaji meye cewa yayi " lafiya cutie ?ba lfy ba yaya kana ji Inna ce ba lfy kuma ni dakai take nema "Cikin rudewa Arman ya ce " Subhanalla maza maza sanyo hijab Cikin Sauri Aira ta Ruga ta sanyo hijab Haidar dake hannun arman ta amsa tana hawaye ta ce "Muje yaya muyi Sauri" Kai tsaye Airport suka nufa Cikin kankanin lokaci jirginsu ya tashi zuwa kano minti Talatin me kyau tayi musu a kano Inda Arman ya kira driver d'inshi yazo ya daukeshi Kai tsaye asibitin Mallam aminu kano suka nufa Duk sun rude Suna isa cikin kid'imewa Aira ta fito Inda ta Hango su Mamy ta nufa tana kuka duk kallonsu tayi ta ce "Mamy ina innar " D'akin Da take ta nuna musu itama tana hawaye ganin zata yadda Haidar ya sanya Mamy Amsarshi Tare da cewa "ki nutsu " Cikin Sauri Aira ta nufi d'akin Arman ma d'akin ya nufa batare da ya ma Gaishe da mutanen wajen ba Dan Duk ya rud'e Aira na shiga ta samu Inna Kan gadon marassa lafiya numfashinta na fita sama sama yayinda likita biyu a kanta cikin kid'imewa Aira ta nufi gadon tare da fashewa da kuka ta ce "Inna meya sameki Inna " Arman ma gadon ya isa ya kama hannunta ya ce "Sannu Inna meya sameki" Cikin murya ta marassa lafiya Inna ta murza hannunsu ganin tana motsa bakinta ya sanya su Matsawa saitin kunnansu suka saita bakinta Cikin dauriya ta ce "Allah yayi muku Albarka Allah yayi muku Albarka Ko yau na mutu Alhmdllh tunda burina ya cika na ganin kunzama ma'aurata kuma harda zuri'a Burina na karshe ne har yau ya kasa cika na Daidaituwar Iyayenku Ina fatan ko Bayan raina zaku zama silar Daidaituwar Iyayenku nasan tawa tazo karrshe kuyimun Alk'awarin zama tsintsiya d'aya Ku rik'e juna da amana Allah yayi muku albarka" tari ne yaci k'arfin ta Kuka Aira ta fashe dashi tare da Rungume Inna ta ce "Bazaki mutu ba Inna zaki tashi muci gaba da rayuwarmu zafin ciwo ne ki daina fad'ar zaki mutu Inna bazaki mutu ba " ta Kara'sa fad'a cikin kuka mai ban mamaki Arman ma ji yake kamar yayi kukan girgiza mata kai yayi ya ce "Inna bazaki mutu ba " Bayan tarin ya tsagaita Girgiza musu kai kawai tayi Dan muryarta harta fara chanzawa ta ce "Ina Aliyun yake " Kallon Amma Aira tayi dake tsaya wajen tana hawaye itama ta ce "Amma amso Haidar wajen Mamy" Amso Haidar amma tayi wajen Mamy ta shigo dashi Amsarshi Aira tayi tare da nunawa Inna ta ce "gashinan Inna " Shafa kanshi Inna tayi ta ce "Naganshi daman shine bansaniba Allah musu albarka y'an biyu ma dazu sunzo na gansu Allah ya raya muku zuri arku yayi musu albarka" Ameen Aira ta fad'a tana kuka sosai "kallon amma tayi ta ce “meya sameta sis”Amma na hawaye ta ce “Daga zazzabi kwana biyu yau da safe ana tashi mukaga tana cikin wannan halin shine aka kawota asibiti yanzu da saukima akan dazu tun dazu sunanku kawai take kira tana cewa a kira mata ku shiyasa na kiraku”Girgiza kai aira tayi tana kuka tace “Allah bata lfy”Murmushin karfin hali inna tayiwa aira da arman tare da cewa " Kabir da Abubakar ko bayan raina zanyi alfahari daku idan kuka zama silar daidaituwas....Tari ne Inna ta fara ba kakkautawa Tare da shakuwa sosai duk suka rude har Abba da Daddy da suka shigo tsaye sukayi kanta Aira ko hannunsu gam ta kasa saki kuka kawai take Dr ne ya shigo Tare da sanya mata oxygen ganin numfashita yana daukewa "Chan kuma sukaji shiru Ba motsi ba numfashi Hannunta suka ga ya saki Wanda yake rik'e da na Aira da Arman " A firgice kamar mahaukaciya Aira ta mik'e ta ce "Inna Inna bacci ne kikayi " Dr ne ya matso tare da cire mata na urori ya rufe mata fuska kallonsu yayi ya ce "kuyi hakuri Allah yayi mata cikawa Allah jikanta da Rahama yasa mutuwa Hutu ce yana gama fad'ar haka yabar wajen " Ai Aira jin Abunda Dr ya fad'a batasan lokacin da jinta da ganinta Ya daukeba sai ganinta sukayi a sulale a wajen summammiya......✍🏿
*Allahsrk rayuwa kulli nafsin za ikatul maut Mutuwa kenan mai yankan kauna Allah jikan musulmanmu da suka rigamu gidan gaskiya idan tamu tazo yasa mu cika da imani Allah ya sa muyi kyakyawan karshe*😭😭😭
*Ni da Yaya Arman it’s not free it’s for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*
_*Miss Hajo ce_*🤙🏿
[7/22, 19:54] Hajo hajo: 🅿️.........*121&122*
Summammiya su Mamy da su Aunty Aysha su ummy amma da Mummy da twins da sukazo Sosai Suka shiga kuka mutuwar Inna ta girgiza mutane da dama musamman Arman Daddy da Abba ko ba a magana Babban bakincikinsu da Inna ta mutu Da Jimamin Rashin jituwarsu A bakinta Tabbas basuyi mata adalci ba Mummy ce tayi k'arfin halin Daga Aira taji ta sume ruwa ta yayyafa mata amma bata kawoba Kallonsu tayi cikin k'arfin hali ta ce "Addu'a ya kamata muyi mata ba wai kuka ba Ta rigamu ne Saidai muyi fatan samun Rahama Inda taje dole kowa zaijeshi muma jiran tamu muke Allah sa mucika da imani Inna kuma yayi mata Rahama yasa ta huta mala'ikun Rahama su San da zuwanta" Ameeen duk suka fad'a "nan aka shirya tafiya domin ayi Jana izar inna itakuma Aira aka wuce da ita emergency Arman ko baka iya Tantance yanayin da yake ciki ba a tab'a yimasa mutuwar da ta shigeshi irin mutuwar Inna ba zuciyarshi ji yake kamar zata rabe gida biyu " Wajen ya samu ya zauna a waje yanajin zuciyarshi na masa zafi da zaiyi kuka ma shi da ya ji sassauci akan Abunda yakeji idan ya kalli masu kukan sai yaji inama shine ya samu kukan irin nasu Sosai yayi mamaki jin Daddy Ya dafoshi ya ce "Addu'a zamuyi mata Mujahid tashi mu tafi ayi mata Sutura" Kallon Daddy Arman yayi sai kuma zuciyarshi ta karye Ya fashe da kuka tare da Fad'awa jikin Daddy Ya ce "Daddy Inna ta rasu Daddy shikenan ta mutu" Rungume dan nashi dad yayi yanajin nadamar abubuwa da dama da yayi a rayuwa ya Ce"Adduarmu take buk'ata namiji da jarumta aka sanshi muje kaga antafi da ita muje ayi mata Sutura da wuri"Dak'yal Arman ya iya daidaita kanshi A tare da Dad suka shiga mota Cikin k'ank'anin lokaci aka shirya Inna Bayan anyi mata salla aka wuce da ita gidanta na Gaskiya( Inda kai da ni da ita da su da kowa zaije Saidai muyi fatan Allah ya sa mu cika da imani Wanda suka rigamu Allah ya jikansu yasa sun huta Mu dake raye kuma Allah bamu guzirin taddasu )Bayan an dawo daga Sutura Wanda dumbin mutane da dama suka Je suturar Dan kafin kace me labarin mutuwar Inna ya baza gari saboda d'iyan zumunta Mama Halima ma ta tarar da suturar Inda ta sha kuka kamar ba gobe Abba ko sosai daka Kalleshi shida dad zakasan mutuwar tana nukurkusarsu cikin gidan ma ansha kuka Inda daga karshe kuma duk aaka bita da addua sai Bayan magriba sai Sannan Mamy ta kawo a kanta Aira Na Asibiti Kallon Aysha tayi ta ce "Dawa aka bar Aira a Asibiti "Aysha da cikinta da ya fara girma ta ce " Wlh Mamy bansaniba duk nan muka taho "Mikewa Mamy tayi ta ce " Bari naje naga jikin nata "Mikewa itama Aysha tayi Ta ce " muje Tare Mamy a tare suka fito harabar gidan Daidai lokacin Abba ya dawo daga salla Kallonsu yayi da mamaki ya ce "Ina zaku" Aysha ce tayi k'arfin halin cewa "Aira ce zamuje mu gano a Asibiti ba a barta Da kowaba" ku jira na d'auko mota mu tafi tare suka tsinkayi Muryar Abba "Sosai sukayi mamaki da AL ajabi musamman Mamy Sakato tayi a wajen har Abba ya fito da mota har suka iso asibitin Mamy na.mamaki suna fitowa suka samu Amma rik'e da Haidar din Aira tayi jugum idanunta jawur a waje " Kallonta sukayi a tare sukace "Kina nan daman kenan to ya jikin nata" Juyowa Amma tayi tana jijjiga Haidar ta ce "Har yanzu basu bamu wani bayani ba Tunda suka shiga har yanzu shiru Kuma sunki barina na shiga na ganta" sosai suka damu musamman Abba da a fuskarsa zakaga tsananin damuwar da yayi Kallonta yayi ya ce "Dr din bai fito ba har yanzu" Gyada musu kai tayi "Suna nan tsaye Mummy da Arman sukazo suma daga wajen makokin sukayo nan Dan suga jikin nata Arman daka Kalleshi zakasan yana cikin tsananin tashin hankali ga mutuwar Inna ga kuma Aira ba asanma halin da take ciki ba nan suka zazzauna jiran Fitowar likitan aji halin da ake ciki " sai wajen 9 pm tukwana dr din ya fito yana shafce zufa duk wajenshi suka nufa tare da tambayar halin da take ciki"Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Alhamdulilla munyi nasarar ceto rayuwata da d'an dake cikinta ta so ta samu heart attack ne Allah ya kiyaye Amma dai bata farka ba zata iya farkawa zuwa gobe haka Allah ya bata lafiya" Duk hamdala sukayi ga mamakin su na jin Aira wani cikin gareta Arman ne yayi k'arfin halin cewa "yanzu zamu iya ganinta" Eh ba damuwa zaku iya ganinta amma kar ayi hayaniya a kanta Dan Allah"Arman shi ya fara shiga d'akin Inda ya sameta kwance tana numfashi sama sama "Kama hannunta yayi ya ce " Allah ya baki lafiya my cutie"Duk shigowa sukayi suka duba jikin nata Har Abba Haidar ne da ke kuka hannun Amma Mamy ta amshe shi ta ce "Ko yunwa yakeji " Eh kila ai yanama da hakuri Tun dazu ruwa kawai na basa "Arman ne cikin k'arfin hali ya mik'awa Amma makullin mota ya ce " Ki bud'e Motar da mukazo da ita zakiga Madararshi a Pida"To ta fad'a tare da amsa ta fita Abba ne ya fita daga d'akin Bayan Amma ta dawo ta bawa Mamy Madarar Inda ta shiga bashi yana sha "Mamy kawai ta kwana wajen Aira Inda suaran suka koma gida Washegari Tun safe Arman a asibitin ya tare Dan jiran farkawartata Mummy Wajen 11 tazo tare da twins Suna ganin mamansu cikin wannan halin suka hau kuka Dak'yal aka dinga lallashinsu Haidar ko bawan Allah sai madara Mamy ta dinga bashi yanzuma yana bayanta ta goyashi yayi bacci suna nan zaune jugum jugum Sukaji farkawar Aira Cikin Sauri Arman yaje tare da kamata ya ce " Sannu Mom twins"Kallonshi Aira ta tsayayi tare da Kallon mutanen wajen da kuma Inda take abubuwan da suka faru ne suka shiga dawo mata Kuka ta fashe dashi tare da d'ora hannu a ka ta ce "Na shiga ukku yaya Dan Allah ka Cemun mafarki nake ba Inna bace ta mutu" Rungumeta Arman yayi ya ce "ki nutsu Aira baki da lfy Dukkan mai rai Mamacine Addua zakiyi mata Inna ta rigamu gidan Gaskiya" basuyi aune ba saiji sukayi ta buga uban k'ara tare da Kara sulalewa a wajen Duk rudewa sukayi Inda suka kira dr nan ya k'ara dubata Kallonsu yayi ya ce "Gaskiya mutuwar nan ta girgiza ta da yawa Ta Kara suma Allah ya kiyaye karta samu wata matsalar Allah Ya bata lfy ya fad’a tare da sanya mata Karin ruwa " sosai kowa hankalinshi ya tashi twins kuka suka sanya tare da hayewa kanta suna jijjigata sukace"Cutie mom ki tashi mom ki tashi mu tafi gida"Janye su Mamy tayi tare da Kallon Mummy ta ce "Ko Aysha ta wuce dasu gida" Mummy da duk tayi sanyi cewa Tayi Eh to a wuce da su din"Arman ne yayi saurin cewa "Mummy bari na kaisu gidan aboki na nan kusa ba nisa" Duk kallon mamaki suka bishi dashi "Mamy ta girgiza kai Mummy Ce ta harareshi ta ce " gidan abokin naka har yafi gidansu"Kiyi hakuri Mummy gwara na kaisu Chan saboda Chan din za a iya korosu Nan ko damun gama abunda muke zanje na d'aukesu "Duk Kallonshi suka tsayayi cikin b'acin rai Mummy ta ce " to ba Inda zaka kaisu"Mamy ce ta ce "Ki barshi ya kaisu Chan din Hajiya Ai yana da Gaskiya Abban su baida Tabbas ka kaisu Inda yafi maka kwanciyar hankali" Girgiza kai Mummy tayi Arman ko d'aukar yaranshi yayi ya fita dasu Dan bazai lamunta ba a wulakanta mai yara tunda baisan last time