NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   42 / 54

123K to 126K   out of 160.7K words

i sosai yakejin k'aunar yaran na shigarsa ta musamman Bayan yayi musu addua jin sun fara kuka ya sanyashi kallon Mummy ya ce "Ba abunda za a basu Mummy " Zamzam ta ciro tare da Dabino mai laushin nan irin na makka ta mik'a masa tace tauna musu Kad'an ka basu saika basu ruwa daga nan zaka iya musu hud'uba "hakan yayi Bayan nan yayi musu hud'ubar kiran salla Kamar yanda manzon Allah ya koyar tukwana ya rad’a musu suna Dagowa yayi ya kalli Mummy tare da Yin murmushi " Kallonshi tayi ta ce "Me ka sanya musu" Mik'a mata Hasanar yayi ya ce "ga takwararki Fatima zahra d'ayar kuma Rahama"Cike da farinciki Mummy ta amsa ta ce " masha Allah Allah ubangiji ya raya manasu sosai Aira taji dad'in sunan da ya sanyawa yaran sunan mahaifiyarshi da nata Hakan ya mata dadi sosai nurse dinne suka bukaci da Akai Aira d'akin Hutu Dan yanda tasha wahala saita huta sosai haka ko akayi ita kadai aka bari ba b'ata lokaci bacci ya d'auketa Arman da Mummy suna waje sai liliyar yaran suke Dan yanzu sunyi shiru Har sha biyun Dare sunanan dak'yal Mummy ta lallaba Arman ya koma gida Bayan ya sayowa Aira abubuwan da zataci su Kaza fresh milk fruit Da sauransu Baiso ba ya koma Dan bayason abunda zaiyi nesa da yaranshi da yakejin kaunarsu ta musamman Mummy dakinda aka kwantar da Aira ta nufa da Yaran har lokacin Bacci take ga yaran sunfara kuka Alamun sunajin yunwa Haka nan tayi ta jijjigasu Inda Hasanar ta rude da kuka Wanda kukan ya tashi Aira har cikin Ranta takejin kukan yaran ganin ta tashi ya sanya Mummy saurin zuwa tare mik'a mata ita ta ce "Kinga tund'azu ita tafi rigimar" Amsarta Aira tayi tare da Fara jijjigata tad’an lafa da kukan Amma bata dainaba Alamun yunwa takeji sanyata Mummy tayi ta fito da Mamanta ta sanya mata a baki dukda kunyar da Aira takeji Amma me babu ruwa "Cikin Sauri Mummy ta hadawa Aira tea mai kaurin gaske Mik'a mata tayi Tasha Bayan nan ta zuba mata Farfesun naman da Arman ya sayo Shima tadanci sosai Fresh milk da Malta Mummy ta k'ara had'a mata marairaicewa tayi ta ce " Mummy wlh na k'oshi" a a a Aira daurewa zakiyi kisha Dan asamu abincin yaran nan yazo Kinga sai kuka suke ki daure jin Haka ya sanya Aira saurin shanyewa "yawwa to Mummy tafada tare da cewa " to gwada bata insha Allahu ruwan zaizo yanzu"cike da jin kunya Ta Kara gwadawa Tana sanya mata taji yazo ta kama ta fara tsotsa Sosai Aira taji wani irin zafi d'an k'ara tayi tare da saurin fusgewa "Tana hawaye ta ce " Mummy zafi"Matsawa kusa da ita Mummy tayi ta ce "Daurewa zakiyi ko so kike kibar yaranki na kukan yunwa Daga yanzu bazaki sakejiba " Jin haka ya sanya Aira mayar ma da Hasana taci gaba da sha Dukda zafin da takeji haka ta daure gashi yarinyar da ancire zata hau kuka tafi minti ashirin tana tsotsa Ganin d’ayarma ta fara kuka ya sanya Mummy saurin karbeta ta ce "ba d'ayar itama Amsarta tayi itama ta fara bata tanajin tana tsotsa tayi shiru Babbar ko kuka ta fara Jijjigata Mummy tafara ta ce " Haba takwara karfa kiyi Rashin hakuri Kinji "Sosai Mummy ta shiga jijjigata Inda ta samu har bacci ya d'auketa itama d'ayar tana cikinsha bacci ya d'auketa kwantar dasu kan gadon tayi itakuma Aira ta koma gefen karshen gadon ta kwanta.
Washegari safko Arman ya buga musu a lokacin Aira sunfito Daga wanka Wanda mummy ta gargasata doguwar riga ta sanya tare da zaunawa kan kujera Lokacin shigowa yayi tare da kayan break fast d'aya shirya Bayan ya zauna Kallon Aira yayi ya ce " Sannu cutie ya jikin naki"Murmushi Aira tayi ta ce "Alhamdulilla" Mummy ina kwana "Lafiya qalau son ta fad'a tana d'aukar Rahama da ta tashi don yi mata wanka Plask din d'aya shigo dashi ya Tsiyaya ruwan tea din tare da sanya madara millo da bounvita a ciki sosai yayi kauri mik'a mata yayi ya ce " Amshi maman twins kisha"Wara idanu tayi kasa kasa ta ce "Uhm harna tashi daga cutie na koma maman twins kenan" Dariya yayi ya ce "Ai Duka sunankine my cutie " Amsa tayi tare da Fara kurba a hankali Inda take hadawa da wainar kwan da ya kawo kallon Mummy yayi da take yiwa Rahama wanka yace "Sannu Mummy ga break fast d'innan a hada maki ko saikin gama" Bari dai na gama tafada tana Tsaneta a towel Dan ta gama mata "Gado taje ta kwantar da ita tare da zaunawa kan chairs din dake d'akin Arman ya had'a mata tea din itama da wainar kwai tana cikin break fast Zarah ta kwala Kuka da duk saida suka Kalleta Cikin Sauri Arman ya d'auketa tare da Fara jijjigata ya ce "Mummy ko bata lafiya?Lafiyanta qalau wlh inajindai takwarar tawa zatayi kukan banza bata ta bata Tasha " sorry my Mummy karkiyi Rashin hakuri Kinji takwararki hakuri gareta ki taimaka "Arman ya fad'a yana kallonta " Duk Dariya sukayi har Aira data kusa kwarewa ta ce "Yaya kamar irin tanajin naka nan ko" Kallonta yayi da murmushi a fuskarsa ya ce "tanaji mana ai tasan daddynta tama Cemun bazata sakeba " Girgiza kai Mummy tayi tare da amsarta ta dorawa Aira kan cinyarta ta ce "Karki biyema mashiririncinnan Bata Tasha " Amsarta Aira tayi tare fara feeding d'inta Arman ko d'aukar Rahama yayi yana kallonta tare da Fara mata wasa Kallon Mummy yayi ya ce "Wai Mummy baza a sanya Musu Nick name ba" ku zan tambaya ai me kuka zaba musu"Kallon Aira yayi ya ce "Cutie wannan zab'inkine wani suna kike tunanin za a dinga kiransu dashi? Yaya duk sunan da yayi muku nima yayimun ku zaba kawai " Mummy ce ta ce "a a a baza ayi haka ba ke zaki zabawa yaranki ne Ai tunda yayi na farkon ke kuma saiki zab'i sunan da yayi maki ko zuwa kafin suna ne Kinga sai a sanya" Kasa tayi da kanta ta ce "To Mummy " Bayan tagama bata itama Amsarta Mummy tayi itama Bayan tayi mata wanka ta shiryata Nan Arman ya shiga yiwa yaran nashi hotuna masu kyau a waya ranar aka sallamesu Bayan sun koma gida Nan Mummy ta shiga kiran y'an uwa tana shaida musu haihuwar tare da tura hoton yaran groups d'insu na y'an gida kowa sai Farinciki yake Sosai yaran tun a hoto suka shiga ran mutane murjace ta kira Aira Bayan ta d'auka ta ce "Congratulation kawata Allah ubangiji ya raya mana twins wlh Kinga Dana gansu a hoto kamar na sace Ji nake kamar nayi tsuntsuwa na taho" murmushi Aira tayi ta ce "Ai gwara ki tahoma tun wuri karsuyi fushi da Mummyn su " ah suyi hakuri ina hanyar tahowa my twins ki shafa mun kansu Sis Zadai ki bani su kyauta ko Dan wlh ina sonsu"Hasina ce tayi saurin amshe wayar ta ce "Rabu da ita sis Me ya kaiki ba wannan mahaukaciyar yara Ni zaki bawa su yanda zankula dasu " Dariya Aira tayi tanajin irin yanda suke drama A waya Bayan sunyi bankwana hotonsu tahau what's App ta tura musu tana ganin yanda suke ta status Ana hadama yaran tiktok sak daka kalli yaran zakace musu turawa grps suka bude su hudu waidan tattaunawa akan sunan Aira ce tayi voice ta ce "Manyan iyayen twins wani suna kukeganin za a dinga kiransu dashi nidai wlh na kasa ganowa Ku zaba musu suna mai dadi" Voice maryam tayo ta ce "Gaskiya kam kyanta a naima musu nick name mai dadi bari hasina ta fito itace Gwanar sanin sunaye nima ita ta zabawa hanif" Hasina ce tayo voice bayan nasu ta ce "a gaskiya inaga a kirasu da Nihal da Naila ko ya kikace sunan yayi kuma Kunga baiyi yawa Ba sosai" kowa yayi na am da sunan Hakan yasa Aira ta ce "sunan yayi sis kawai a kirasu da hakan amma yaushe zakuzo" Insha Allahu zuwa jibi mukeson tahowa tare da su goggo"Sosai Aira tayi farinciki sosai take chat da su ana raha da Hira A lokacin Aira na Gado Arman ya shigo da Rahama dake Kuka mik'a mata ita yayi tare da zaunawa ya ce "wani sunan kuka zaba musu za a bugo musu abubuwan suna "Nihal & Naila yayi ko Yaya?Wow ya fad'a tare da Jinjina mata hannu ya ce " sunan yayi mom.twins "takwarar Mummy sai a kirata da Naila takwarar Mamy kuma Nihal ko " Eh my hero ta fad'a tana feeding d'in Nihal Kallonsu yake gwanin sha wa Shafa sajenshi yayi ya ce "Kinsan me cutie" Dagowa tayi ta ce "Saika fad'a hero" Nifa mamaki nake har yanzu Wai kece da yara saina tuna kema yarintataki gani nake kamar haka kece da kina yarinya"Dariya sosai Aira tayi tare da mik'ewa ta ce "Lallai hero Allah kana maidani baya da yawa sannan tayi Farr da ido ta ce " Me yafi son ranka Ganikwa dak'au kamar ban haihuba ko yanzu sai a dasa daga Inda aka tsaya"Dariya yayi ya ce "Au to bari na yi taste naji da gaskene zai chafkota ta ruga da gudu tayi palour "Rufamun asiri karki kadamun y'a ya fad'a yana binta a palour Kallon Aira da ta shigo da gudu Mummy tayi ta ce " Subhanallahi meye haka Aira Da yarinyar zaki dinga gudu Dan shirme jaririyar saikin kada ita kodai harkin manta zafin nakudar da kikasha ?Sosa kai Aira tayi ta ce "Yi hakuri Mummy bazan sakeba " Hararar Arman d'aya biyo bayanta Mummy tayi ta ce "Kaikuma Dan shirme na meye zaka biyota Wlh indai wannan shiririta zakuyi bazan yardaba wannan kunma iya kula da Yaran har yanzu baku Aje shirmeba" Sorry Mummy Arman ya fad'a tare da Kallon Aira ya kashe mata ido Alamun zasu hade gwalo tayi mishi tare da zaunawa gefen Mummy duk tana kallonsu girgiza kai kawai tayi Ywwa Mummy Sun zaba musu Nick name takwararki Naila za akirata dashi takwarar Mamy kuma Nihal sunan yayi ko?Masha Allah eh sunan yayi kam Allah ya raya"Mikewa Arman yayi tare da Kallon Aira ya ce "Jeki fito musu da kaya masu kyau mai hoton na waje zai shigo ya d'aukesu Ki fito musu da Kamar kala biyar biyar?to Aira ta fad'a tare da mik'ewa ta shiga d'akinta drawer da aka jera kayan Yaran ta fiddo Inda ta zaba musu masu kyau iri daidai ta fito dasu palour a lokacin har mai hoton ya shigo Mik'awa Mummy kayan tayi tare da zaunawa gefe Nan Mummy ta shiga shiryasu da anyi musu hoton su sauya musu wasu kuma sosai hotunan sukeyin kyau a haka har aka gama Mai hoton ya tafi sosai Mummy ta shiga tofe yaran da Addua Dan yaran nan a kyansu sai an dage da addu'a saboda bakin mutane Kallon Aira da Arman tayi ta ce " Karku sake Kuyi sake da Addu'ar nan Safe dare ko fita zakuyi dasu Karku kuskura ku tab'a mancewa Ta zauna a bakinku ku dinga Tofa musu "A'uzu bikalmatillahi tammati min sharrima halak'a " ku tofa musu a kansu sau Ukku ko sau Bakwai insha Allahu babu abunda zai samu Yaranku tundaga kan sharrin mutum da aljan ba abunda zai samu Yaranku sannan Karku dinga Dorasu a social media bakin mutane idan kasan wani bakusan wani dukda idan kun rik'e addu'ar nan babu Wanda ya isa yataba Yaranku koda maye ne kuwa Amma ance hanyar lafiya a bita da shekara Karku dinga d'ora Yaranku a social media Ya wuce what's app a barshi kunjidai na fad'a maku"To Mummy insha Allahu suka fad'a Sannan ta k'ara kallon Aira ta ja mata kunne cikin sigar wasa"Dan Kara Aira tayi ta ce "Auch mummy" Sannan ta d'an dankwasheta aka ta ce "kekuma na k'araga kina gudu da su a hannu Ko shan ruwan sanyi ko zaki ko yaji na hana" Dariya Arman yayi ya ce "Mummy kamar kinsan ta da shegen shan choculate gwara ki mata warning" Shima dankwashinshi Mummy tayi a ka ta ce "Kaikuma ina ruwanka d'an sa ido" Dariya Aira tayi mai tare da mashi gwalo Marairaicewa yayi ya kalli Mummy ya ce "Kinganta ko Mummy gwalo takemunfa" tayi maka d'in Mummy ta fad'a tana Kara masa dankwashi"Dariya Aira tayi sosai hada rik'e ciki Tare da Kara mashi gwalo ganin ya Mike Ya sanyata saurin Aje Nihal kan sopa tare da rugawa tayi ciki ya Mara mata baya"Girgiza kai Mummy tayi ta ce "Ana magani kai yana k'aba Allah ya shiryeku yaran nan kuma zakusha renon mashiriritan iyaye ta fad'a tana Dorasu kan kekensu na kwanciya Dan sunyi bacci tukwana ta mik'e ta shiga bedroom d'in da ta sauka tayi wanka ta shirya.tana tunanin yanda zata kankare da Daddy idan ta koma.
Ana jibi suna y'an Yola suka tattaho sunfi su sha biyar hada Gwaggo Sosai Aira tayi farincikin ganinsu ita dasu Hasina tsalle sukayi suka Rungume juna suna farincikin had'uwa da juna Sosai suka tahowa da Aira dinkuna Wanda Mummy ta sanya a kai mata d'inkin a tafo dasu kala goma kuma Duka masu masifar kyau nanfa kowa ya shiga d'aukar yaran da riritarsu kowa ji yake inama nasune musamman su Hasina da suke zuba musu hotuna a wayar Aira saboda wayar badai camera ba idan ka kalli yaran saika rude kaji inama nakane (lol).
Yau ta kama Friday ranar sunan twins manyan manyan raguna tirka tirka saida aka yanke takwas uwar jego Aira sosai tayi masifar kyau ita da yaranta Haka uban gayya Arman sosai aka shiga musu hotuna masu masifar kyau Mummy ma anmata hotuna masu kyau ita da y'an jikokin nata da takejin kaunarsu kamar ita ta haifesu sosai akayi bishasha a bikin sunan nan Anci ansha Sannan aka raba su calendar, bags kala kala na hotunan Yaran da sunansu jiki,su cups,memo,littatafai manya da hoton yaran jiki,sannan da kayan yara da aka buga da hotonsu jiki Babban Hall Aka kama Inda akayi lunch Akaci aka sha akayi hani an Hall din sosai ya cika da mutanen Arziki Dan abokanan Mamy dake nan London hada Wanda suke Dubai da aminanta dake 9ja manyan masu kudi saida sukazo sannan kowannensu saida ya cika jariran da kayan arziki Sosai na dinga kyalla idona naga ko zanga Ni da yaya Arman fans a bikin sunan nan amma shiru kakeji nace kaico Nasan kila jirgi suka rasa hakan yasa na d'auko musu rahoto yanda ya kamata anyi taro lafiya ankwashe lafiya kowa sai dai Sam barka........✍🏿


*nida Yaya Arman littafin kudine akan Naira 200 kachal ta wannan number*


_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[7/17, 11:09] Hajo hajo: 🅿️........*107&108*




.....Washegari Bayan anyi soye y'an uwan Mamy wasu suka tattafi garage daga Murja sai Hasina da goggo sai Mummy kawai da dare Suna kan Gado su Ukku suna ta fira yayinda Hasina ke kalle_kalle a tiktok Amsar wayar Aira tayi ta ce " wai muga iktok d'innan ya yake " Amsa tayi tayi ta kallon videos da na kirkin da Wanda bana arzikiba saitaji abun ya burgeta kallon hasina tayi ta ce "Sis amma Wlh abun yayimun kyau ka d'ebe kewa " Wlhko ga kinci Dariya Ko na bud'e maki kuma Kinga kina d'ora hoton twins wlh zakiyi mamakin followers din da zasu jawo maki"Allah sis Saidai yaya Ya ce whats app kadai yakeson inayi ga karkiga yanda ya tsani tiktok d'innan"Yo sani zaiyi kinayi shida bayinshi yakeba bare yagani inaga yaya what's app kadai yake ki bud'e abunki wlh"Mik'a mata wayar Aira tayi ta ce "Anshi budemun " Amsa tayi ta bud'e mata account da Oum_twins_Naila&Nihal (Karfa Kuyi search fans k'irk'irarren account ne😂dan naga kun k'agu ku samu shiga wajen Aira lol😉😝)
Ana gama bud'ewa ta d'ora mata hotunansu sannan ta nuna mata yanda akeyi ai Aira abun nema ya samu Nan tayi ta shiga Inda ta fara d'ora hotunan twins da photographer yayi musu rannan wa iya zubillahi fad'ar kyan da sukayi bata bakine walahaula ta tofa a hoton su kansu su Hasina saida suka d'auka suka daddaura a nasu shafin dan su kansu twins sun isa su janyo musu followers a cewarsu (Nima dai inaga hoton twins din Aira zankoma post Ko sunjayomun followers lol)Boye mata account din sukayi Inda bazai ganiba koya d'auki wayar.
Washegari Suna zaune a palour ana fira twins na hannun Mummy da goggo Magungunan miyagu da na iska goggo ta mik'awa Aira ta ce "Amshi ku dinga turarawa duniyar nan ba yarda " Amsa Aira tayi tayi mata Godiya goggo Ce ta kalli Mummy ta ce "Ke yanzu fatima haka za abar yaran nan su kadai Nidai Dan kinji tawa amma da muntafi dasu idan tayi arba in sai ta dawo" jinjina kai Mummy tayi ta ce "Goggo bazaki gane bane yaran ne basuyi kwariba AC jirgi ba wasa bace illa zatayi musu sannan ayita yawo dasu da kafin ta haihu ne za ayi wannan din" Hakane.kuma to yanzu wa zai zauna wajensu kenan nidai Kinga jibi zamu wuce da ina da lfy da ni saina zaunama tunda dai ba ambar yarinya haihuwar farko ita kadaiba"goggo ni zan zauna daman har tayi arba'in din wa garesu Wanda ya fini "Haba Fatima dukga y'an uwanki nan da d'iyan yayyinsu har a rasa Wanda zai zauna saike ki zauna a a baza Ayi hakaba a kira hadiza ta dawo (kanwar Mamy ce tana Aure a Yola)saita zauna har suyi arba'in din?banki taki ba goggo amma kiyi hakuri na zaunadin nasan bawai mai rasa zaman akaiba a a nafison su samu kulawar tawane yaran Dan Yaran nan saina taka musu birki ta fad'a tana Hararar Arman " Dariya kawai sukayi ita Aira suna jinsuma amma hankalinsu nakan hirar da suke" jinjina kai goggo tayi ta ce "To shikenan amma gsky bazakiyi kwana arba'in ba mijinki baisan Inda kikeba kidaiyi sati biyu gasu Hasina nan Saisu zauna Har suyi kwarin" To goggo Hakanma yayi "Su Hasina da Murja ko tsallen murna suka daka Za a barsu Aira ma sosai tayi farinciki suka Rungume juna Dariya Mummy tayi ta ce "

42 / 54