NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   41 / 54

120K to 123K   out of 160.7K words

shine albishir din da zanyi maki ai yau ranace ta musamman a garemu dole ne na fara baki k'aramun tukuici Babban kuwa Sai my unborn ya fito"ya fad'a yana shafa cikinta"Alhamdulilla Aira ta fad'a Sosai itama ta shiga farinciki marar musaltuwa shidai Dr Dariya yayi musu Dan sosai love d'insu ta burgesu Shi kanshi Dr d'in saida ya shaida Dan Arman barin kudi yayi mashi Ranar saida yabi Duka marassa lafiyan asibitin yayi musu Alheri Na nuna godiyarshi ga ubangiji "(Haka ake so idan abun alkhairi ya samu mutum ya godewa Allah Sannan yayi alkhairi Bawai kida da sauransu ba Allah sa mu dace)Koda sukabar asibitin basu zarce ko ina ba sai wani katafaran shagon sayar da waya IPhone 14 ya saya mata a kwali savuwa dal wacce ko wata batayi da fitowa ba A mota ya sameta Bayan yashiga Kallonta yayi tare da mik'a mata kwalin ya ce " ga tukuicinki my cutie na rasa dame zan saka maki bani da abunda zan saka maki a duniya Saidai nace Allah ya Barmu tare har Abada"Murmushi Aira ta sakar masa ta ce "Nima bani da abunda nake dashi da zan saka maka mijina kaid'in haske ne a cikin rayuwata Bud'e wayar tayi Zaro ido tayi ganin wayar da Batayi tsammaniba Ai batasan sanda ta Rungumeshi saida tayi hawayen farinciki ta ce " Thnks Thnks you so much My hero Allah ya k'ara budi da arziki mai amfani "Shittt Arman ya fad'a yana rufe mata baki ya ce " banason Godiya cutie kin chnachanci fiye da haka wannan bakomai bane "Sosai Aira tayi farinciki sai zumudi take sim din d'aya saya na k'asar ya sanya mata a wayar Koda sukabar wajen joint suka wuce Inda Arman ya sanya Aira ta zaba abunda ranta yakeso saida suka cika cikinsu tukwana suka dawo gida Suna isowa ana magriba Bayan sunyi sallah a palour Cikin zumud'i Aira ta fiddo wayar Ta ce " yaya sanyamun number su mummy"murmushi yayi tare da Amsar wayar ya sanya mata number su mummy da Murja da su Hasina Bayan nan ya shiga ya d'auko mata apps da abubuwa masu amfani what's app kawai ya d'aukar mata danshi kadai yakeson tayi yana cikin saita mata Mummy ta kira cikin zumud'i ya d'auka ya ce "Mummy albishirinki" Goro "Mummy ta fad'a cike da zak'uwa" An dace Arman ya fad'a tana Dariya"Itama dariyar Mummy tayi ta ce "Kai Alhmdllh son kace an dace wata nawa kuma?Dariya sosai Arman yayi yana mamakin yanda Mummy ke biye musu ya ce " Mummy 4months hada sati d'aya"Alhamdulilla Ai yau da ina da hanci da nayi gud'a kai Allah mungode maka Mummy tafada tare da cewa "bani y'artawa " Aira na jinsu duk sai kunya ta kamata a kunyace ta amshi wayar 'Sosai Aira tayi mamakin yanda Mummy ta shiga sanya mata Albarka da jera mata adduo i ita duk kunyama ta kamata Daga karshe Mummy ta ce "Yanzu bake kadai bace daughter ki k'ara kula da kanki Da abunda zaki dinga ci sannan karki Kara shan ruwan sanyi ki yawaita shan fruit,Zuma,Dabino da dai sauran kayan lambu sannan banda wasa da ciki karki zauna da yunwa kinji Daugher na" murmushi Aira tayi cikin jin kunya ta ce "To Mummy insha Allahu" Baki buk'atar komai?Eh Mummy "idan kina buk'ata ki fad'amun " murmushi aira tayi ta ce "Bakomai Mummy" masha Allah to Allah ya raba lafiya ya baki lafiya "Amen Aira ta fad'a kasa kasa tare da mik'awa Arman wayar nan suka shiga tsara abubuwa shida Mummy itadai tana jinsu tana mamakin yanda suke k'aunar cikin tun baizo duniya ba ".
Ranar Aira ta kira Su Murja Inda suka shiga yi mata tsiya Abunka ga sun saba itama Aira ta biyesu Sosai taji dad'in yanda suka sha waya Inda daga karshe sukace saisun hade a what's app nan suka turo mata number Maryam Dan tayi mata barka ta haifi baby boy d'inta kiranta tayi ta mata barka nanma sunsha waya sosai Inda Har Maryam ta ce Zata bada numberta a sanyata wani grp na karuwa hakan ko yayiwa Aira dad'i Dan koda akasakata taga grp din Akwai karuwa sosai musamman akan zamantakewar Aure Ganin yanda ta shagala ya sanya Arman amshe wayar tare kasheta Kallonshi tayi ta ce " Honey..."Janyota jikinta yayi ya ce "Wayar nan naga alamar Kade maki hankali take nemanyi Bayan mijinki na bukatarki" Cikin shagwaba ta ce "Uhm honey Ammafa kasan babynmu zai wahalta ko kaida ba saurarawa kakeba" Dariya yayi tare da Fara Aika mata sakwanni ya ce "nak'i wayan ai babyna yanason jin d'umin Daddynshi Zai k'ara kwari bata karacewa komai ba Dan itama tuni ta fara kawo wuta Daga nan labari ya sauya salo suka Lula wata duniyar.
Kulawa ta musamman Arman yake bawa Aira da cikinta taban mamaki saika rantse ba a tab'a haihuwa ba a duniya a kansu za a fara ga Mummy data daure musu kullum itama cikin kira take jin lafiyar Aira Ita kanta Aira abun har mamaki yake bata Dan ta zama wata y'ar gata ta musamman Tarairaiya kuwa ba a magana Dan Arman Ko nan Danan saiyace bazata taka ba sai dai ya d'auketa saida sukaje Asibiti ne ma awo dr yake cewa Hutu yayi mata yawa ta dinga exercises tukwana aka d'an samun saukin yake barinta tafiya da kanta cikin Aira ya shiga wata shidda Inda Yayi girma kamar Lokacin haihuwar ne A lokacin kuma wani kwadayi ne take na ban mamaki " yau ta tashi da son Cin d'an wake hada hawayenta ta kalleshi ta ce "Honey d'an wake nakesonci wlh" Cikin Sauri ya Mike ya ce "Karki damu Prince's sorry bani minti biyu " Mummy ya kira ya ce "Mummy Dan Allah ya ake d'an wake please koyamun cutie ce Ke son ci " Dariya Mummy tayi ta ce "Aifa abun nema ya samu Abu yazo ga ma iya" Sosa kai Arman yayi ya ce "Uhm Mummy ke nake jira" Cikin kankanin lokaci ta koya mashi Katse kiran yayi tare da nufar kitchen yaje ya fara hada d'an waken fulawa Mummy ko Aira ta kira Video call Bayan ta daga kallonta tayi cikin so da k'auna ta ce "Sannu daughter ya jikin naki normal ne dai ko har yanzu"murmushi Aira tayi ta ce "Lafiya Qalau Mummy Saidai Nauyi da nakeji sosai da motsi yayi yawa Kuma banajin dad'in hakan" ta fad'a cikin shagwaba "cike da kulawa Mummy ta ce " Sorry daugher Ai sai hakuri indai ciki ya fara girma Kidage da addua safe yamma dare karki sake da adduo I kinji sannan zanturama son adduoin da zai dinga tofa maki kinasha Insha Allah za a rabu lafiya Ga cikin naki naga yayi girma kamar mai yara biyu a ciki anyi scanning kuwa? Insha Allahu Mummy A a a ba ayi scanning ba ya hana ya ce Wai yafison Muga koma meye a surprise kuma Dr dinma yace ayi "girgiza kai Mummy tayi ta ce " Rabu dashi Allah saukeki lafiya Ai naso zuwa wlh hidimar Siyasa data taso ta hanamu zaune da tsaye Kinsan saura wata biyu zab'e to ko nace zanbar k'asar Daddynku bazai bari ba Har sai munga wucewar zabe lafiya insha Allahu ana gama zabe zan taho"Murmushi Aira tayi ta ce "Bakomai Mummy Allah yasa ayi zaben cikin nasara ya bawa Daddy nasarar komawa next level Insha Allahu" Ameeen ameeen Mummy tafada ta ce "Sai anjima ki kulamun da kanki" Murmushi kawai Aira tayi a haka ARMAN yadawo ya isketa tare da plate din Dan wake a hannunshi "sorry dia Sannu ko" Aira ta fad'a zaunawa yayi yana shafce zufa ya ce "ywwa my prince's Angama ci kawai ya rage" Amsa tayi tare da bud'ewa Masha Allah danwake yasha mai da yaji da Yanke yanke Shi da kanshi ya chakuda mata tare da Fara bata tanaci sosai taji dad'inshi Kallon Arman tayi tare da "Jinjina mai hannu Alamun good" Murmushi yayi ya ce "Thnks wiffey yayi dadi kenan?Uhm ai in ana salla ba a magana Honey Girkinka na musamman ne bantaba cin girki mai dad'in haka ba ta fad'a Dan yaji dadi " sosai yaji dadin yanda take yaba masa koda ya dandana yasan Dad'in bai kai chanba kawai tana fadane Dan ta faranta masa Wanda hakan sosai ya karajin kaunarta na k'ara shiga Ransa Shidai Ana cewa mutum Tara yake bai cika Goma ba Amma ya kasa gano Inda aibun d'ayan na Aira yake kodan kyawawan halayyarta sunyi yawa koma dakwai dayan ba za a tab'a ganewa ba.
Sosai suka shiga sayayyar kayayyakin jarirai gadaje,kayan wasan yara,kekunan koyan zama,keken kwantar da yara da,Abun goya Yara a ciki,Keken tura yara,Kayayyakin sawa na ban AL ajabi a Gaskiya sayayyar da suke gaban mamaki ce saikace ba a San darajar kudi ba komai saya ake daki guda an cikashi da kayayyaki kayan sanyawa jariraine kawai basu saya da yawaba kuma komai da suka saya bibbiyune saboda Dr ya shaida twins ne a cikinta Kayan sanyawa na jarirai Guda bibbiyu suka saya Masu masifar kyau da tsada bangaren Mummy ma sosai take sayayyarta.
Masha Allah anyi zabe cikin nasara Inda Daddy Ya koma Kujerarshi ta gwamna a yanzu hankali ya kwanta Mummy kuma yanzu Hankalinta ya tafi Wajen Yaranta So take.taje ta samu ganinsu.
Cikin Aira Ya shiga watan haihuwa Sosai Arman ya linka kulawar da yake mata fiye da Ga wani irin girma da cikin yayi Dak'yal take tashi take zama yauma tana zaune Dak'yal ta yunkura zata mik'e ARMAN ya yi saurin tareta tare da mik'ar da ita ya ce "Sannu mummyn twins wlh tausayi kike bani Allah ya saukeki lafiya" Murmushin K'arfin hali Aira tayi tare da cije lebe ta ce "Ameen honey Allah harna k'agara na rabu da Cikin nan karkaga yanda nakeji" Shafa cikin yayi ya ce "Dan bakisan yanda nakejiba a raina cutie ji nake daman Wahalar ta dawo kaina Dan babu yanda zanyi ne nake ganinki cikin wannan halin kici gaba da hakuri da daurewa ankusa rabuwa insha Allahu" Gyada mishi kai tayi ta ce "Bacci nakeji muje ciki" Shiya kamata Dan bazai iya daukartaba tana rik'e da k'ugu suka shiga ciki Suna zuwa ta kwanta Gado Sosai take d'anjin sauyi a tattare da ita amma batason tayarwa da habibyn nata hankali hakan yasa ta yin shiru Dan abun bai matsa mata ba Sosai ba tana daijin bayanta na sarawa Koda ta kwanta Arman toilet ya shiga tare da Dauro alwala Inda ya shiga jera salloli Akan Allah ya sauke cutie d'inshi lafiya Aira ko bacci ne ya kwasheta Chan wajen Ukkun dare taji ciwon na k'ara yawa koda ta bud'e idonta ta ganta jikin Arman Yana bacci cije baki tayi tare da daurewa ta fara adduo I a haka dai har taji kuma abun ya lafa tukwana bacci ya sake daukarta Chan wajen Asuba taji Abu ya dawo sabo Wanda ya linka na d'azu "wayyo Allah na ciki na " ta fad'a yana rik'e kugu "Cikin kid'imewa Arman ya Mike Dan daman baccin baiyi nisaba cikin tashin hankali ya ce " me ya faru cutie "Cikinta ta nunamai tana yarfe hannu Tace " yaya cikina bayana kamar zai balle ta fad'a tana hawaye "Subhanallahi Sannu dia bari mu tafi Asibiti cikin Sauri ya lalubo Wayarshi ya kira Mummy ringing biyu ta daga Dan ta tashi Sallar asuba cikin kid'imewa ya ce " Mummy Aira ce ba lafiya Kingantanan cikinta da bayanta ke ciwo sai kuka take"Ku maza ku tafi Asibiti nak'udarce ku marmaza ganinan tahowa k'asar nima yanzu yanzu"Cikin rud'u Arman ya sanyawa Aira hijab da ta fara hada gumi ya sungumeta Sai mota koda suka isa asibitin har gari ya fara wayewa Labour room aka wuce da ita duk yanda Arman yaso shiga hanashi nurse sukayi zaunawa yayi ya rafka tagumi tare da Fara jera mata adduo I Mummy ko Cikin Sauri ta shirya kayanta akwati Lek'a Daddy tayi ta da mamaki ya Kalleta ya ce Ina zuwa da asubar nan "wata karyace tazo mata ta ce " Wlh habiby yanzu aka kira kanin mahaifinmu dake Yola ya rasu za ayi sutura karfe Tara shiyasa na maza na shirya "Subhanalla Allah ya jikansa Aida kin bari mun tafi tare " a a a dia Basaikajeba na wakilceka ai Sunsan yanayin da kake ciki na gajiyar siyasa "To shikenan Allah jikansa sannan ya mik'a mata check din kudi akan takai sadaka cikin Sauri Mummy tabar gidan duk ta rude koda ta isa airport ba jirgin da zaije London jirgin Lagos tahau Inda tana isa ta samu jirgi mai zuwa London cikin k'ank'anin lokaci ta gama clearing d'in komai jirginsu ya d'aga.
Aira sosai take shan azabar da tunda uwarda ta haifeta bata tab'a shan irinta ba Cije baki kawai take tana Salati Tana kiran sunan duk Wanda yazo bakinta gashi likitoci sun duba sunga Haihuwar da saura sosai take Abu d'aya har Mummy ta Iso wajen 1 na rana Aira na Abu d'aya Koda Mummy tazo cikin k'arfin hali Arman yayi mata kwatancen asibitin a waya Tana shigowa cikin rud'u ta ce " Ina take "Arman kamar zaiyi kuka ya ce " Mummy tana ciki tund'azu taki haihuwa"Bata saurareshiba Mummy tayi cikin labour room d'in Inda ta sameta sai yarfewa take Wajenta Mummy ta nufa cike da tausayawa Dan daman tasan yanda Aira batayi laulayin cikiba zata iyashan wahala wajen haihuwa sosai ta tausaya mata Sannu ta shiga jera mata Aira bama tasan da wanzuwarta ba cewa ta ke "Zan mutu yaya kazo ka taimakeni yaya Airanka Ce fa Gashinan ina ganin mutuwa daman haka Zafin d'aukar rai yake bansaniba wayyo ni Aira Mamy ki yafemun na tuba Abba ka yafemun zanmutu yaya Arman kazo"Saida Mummy tayi hawaye kamata tayi ta ce " bazaki mutuba haka kowa yakeji ki daure kinji y'ata"Arman jin Haka bai saurari kowa ba ya Banko k'ofar Tare da zuwa ya Rungumeta Saikuma ya sanya kuka "Ikon Allah Kowa ke fad'a itadai Mummy tana mamakin yanda Arman akan Aira Duka jarumatarshi ta tafi Ada d'an nata ko hawayen shi baka isa ka ganiba" Tasoshi Mummy tayi ta ce "Haba son meye haka ka fita mana zata sauke lafiya insha Allahu" Cikin hawaye ya ce "Mummy bakiga yanda take shan wahala Mummy ba yanda za ayi cutie na sai shan wuya take" Airako jin Arman Sosai ta karawa rakinta volume Ta ce "Yaya karka tafi kaikadai ke sona mutuwa sukeso inyi Yaya Ka taimakeni Cikina" Kama hannunta yayi tare da durk'ushewa ya ce "Zaki sauka lafiya cutie kinji kiyi hakuri ki daure " Dak'yal Aka samu Arman ya fita Inda ya tafi masallaci ya shiga jera Adduo I Aira tana nan tana Abu har magriba Har ana shirin mata Aiki Mummy dukta fita hayyacinta Dan ta tsorata da wuyar da takesha ana shirin Tafiya da ita d'akin theatre ta haifo y'arta Kyakyawa Fara Sol "Hamdala kowa yayi musamman Mummy Bayan nan nakuda ta dawo sabuwa Inda Bayan Mintuna baifi goma ba ta k'ara haifo wata d'iyar itama fara Sol kamarsu d'aya da d'ayar rai da rai ba banbanci Nauyayyar Ajiyar zuciya Aira ta sauke Sai yanzu tajita ta dawo mutum Mummy ko hamdala tayi tare da godewa Allah Bayan anshirya yaran an sanya musu kayansu iri d'aya mik'o wa Mummy su akayi sosai Take farinciki ta ce " Alhamdulilla Allah na gode Maka wai yau nice rik'e da d’iyan Arman shida Aira Allah mai iko"Aira ko Bayan Angama shirayata Aka ajeta gadon hutawa Kallon Mummy tayi da take Ta murmushi tare da Yaran A hannunta Kallon nurse din tayi ta ce "Meye na Haifa Dr " Murmushi tayi ta ce mata "Twins Mata " Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da Yin hamdala Mummy ce ta mik'e tare da Yaran ta ajesu Gefenta ta ce "Daugher Kinga Abunda kika Haifa Ikon Allah kenan Twins lokaci guda kuma Duka mata masu zafin rabo " Kallon Yaran Aira tayi sosai taji wata irin soyayyarsu ta mussaman na shigarta dukda jariraine daka kallesu sak kaga ARMAN Saidai haskensu irin na Aira amma rai da rai Arman ne "Rungumesu tayi batasan lokacin da wasu hawayen farinciki suka zuba mata ba wai yau ita ce Da Yara yaranma har biyu lokaci guda kuma ita da masoyinta Arman suka haifesu Goge hawayenta tayi ta yi a hankali ta ce " Alhamdulilla Allah abun Godiya Allah ya raya munku bisa sunnar ma aiki"Ameeeen Mummy ta fad'a tare da daukarsu ta ce "Son baisan kin haihu ba bari naje na masa albishir Murmushi kawai Aira tayi tana karajin soyayyar Mummy koda ta fita Mummy da Yaran a hannunta daidai lokacin da Arman ya shigo harabar asibitin dawowarshi kenan daga masallaci cikin Sauri ya karaso Inda Mummy take da sai fara a takemai cikin zumudi ya ce " Mummy ta haihu?Mik'a mashi ta farkon Mummy tayi ta ce "Ta haihu congratulations son An samu twins duka mata kagansunan a hannuna.........✍🏿

*Ni da Yaya Arman nakudine akan naira #200 kachal ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali da nustuwa 07026166536*


*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[7/17, 11:09] Hajo hajo: 🅿️.........*105&106*






...Ka gansu nan a hannuna "Cike da farinciki Arman ya ce " Alhamdulilla Mummy kina nufin Duka yaran nan nawa ne"Lakutar kumatunshi tayi ta ce "nakane son halak malak" mik'a mata d'ayar yayi tare da sujjudul shukur Yajima yana Godiya da yabo ga ubangiji itadai Mummy murmushi yaki barin fuskarta yana Dagowa Amsar d'ayar yayi ya ce "Allahu Akhbar Mummy kamata sukayo sak" Wlhko naga Duka Kaine ni harna rikice ma Bana banbancesu Inbanda naga ta farkon tafi K'aramar girma ta haka kawai na bambance su"Hawayen farinciki suka zuboma Arman amsar d'ayar yayi tare da rungumesu gabaki d'aya ya ce "Allah yayi muku albarka yarana" cikin Sauri ya ce Mummy ina cutie tana lafiya"lafiyanta qalau muje ka ganta Mummy tafada suna shiga Inda suka tarar da Aira kwance Tana hawayen farinciki cikin Sauri Arman ya nufi gadon tare da rungume ta tare da Yaran ya ce "Thnks You so much My cutie kin gama yimun komai a rayuwa kinbani abubuwan da bazan tab'a mantawaba dasuba ked'in haskece cikin rayuwata Allah yayi miki albarka ya baki lafiya" murmushi Aira tayi tana Goge hawayenta ta ce "Ameen hero" zaunawa yayi tare da kafe yaran da idanu Inda ya shiga musu Adduo

41 / 54