Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
karki ci Amanata ki rik'emun Amanar Komai dake tattare dake na baki Amanar kanki Da kanki ke tawace ni kad'ai kiyi hakuri kiyiwa mahaifinki biyayya kafin na dawo ina tare dake duk rintsi duk wuya alk'awarin mu na nan i love you .....Duka a hankali yake maganar cikin k'arfin hali Dan a rarrabe yake maganganun " Goge hawayenta Aira tayi tace "I love you too yaya kai nawa ne ni kad'ai nima takace kai d'aya plx ka tashi a ciwon nan meya sameka yaya" tari ne yazowa Arman Cikin Sauri Aira ta Dagashi cike da tashin hankali ta fashe da kuka ganin Arman na tari jini na zubowa daga bakinshi "Dr ne yace " ku maza ku turashi a sakashi mota ciwon yana worse "cikin Sauri aka tura Arman Dan a sakashi mota a tafi Airport Kuka Aira ta fashe dashi tare da Rik'e k'arfen gadon ta ce " ina zaku kaimun shi ku barmunshi zai tashi ba abunda ya sameshi yanzu muka gama magana dashi ku barmun miji na dak'yal wasu nurse tare da Mama Halima suka rik'eta tana fusgewa tana kallo har aka fitar da Arman daga asibitin Sulalewa a wajen Aira tayi summammiya.........βπΏ
_*Miss Hajo ce*_π€πΏ
[6/23, 18:57] Hajo hajo: π
ΏοΈ.......*61&62*
Sulalewa a wajen Aira tayi summammiya kuka sosai Mama Halima da su Aysha su Mama suke sosai suka tausaya musu Emergency aka k'ara wucewa da Aira Mama Halima ko cike da b'acin rai Ta fice daga asibitin Tana kuka tana zuwa gidansu Aira Cike da b'acin ran da tajima batayishi ba ta samu Abba ta ce "Hankalinka ya kwanta ka sanya su cikin wani hali Arman yana Chan rai hannu Allah daman haka kakeso yaya baku da imani baku da tausayi ba yanda bamuyi dakai ba kar ayi Auren nan amma ka dage sai anyi Daga yau na tafi bazaka k'ara gani na da idonku ba bazan k'ara zuwa garin nan ba Yau ina kukan rashinku iyayena amma kuma ina tayaku farincikin tafiya da kukayi ba tare da kun iske wannan bakin tashin hankalinba" tana gama fad'ar haka zata fice Abba yayi saurin janyo hannunta ya ce "Haba Halima yau kece kika fad'amun magana haka" cikin kuka ta ce "Yaya dole na fad'a maka bakuyi mana adalciba a rayuwa" Sosai Abba ya shiga Lallashin kanwar tashi dak'yal ya samu ta hakura ta fasa tafiyar amma da niyyar da tayi gida zata koma Daga wajen Abba kai tsaye wajen Mamy ta nufa Inda ta sameta sai hawaye take yayyinta sai Lallashinta suke Dan tunda akace Aira bata mutu ba hankalinta ya kwanta Saidai hawayen tausayinta da take ta so taje taga jikin nata amma ta kasa Dan zuciyarta zata karaya bangaren su Arman Cikin sauki akayi clearing d'in komai jirginsu ya d'aga Egypt koda suka isa sosai asibitin aka karbesu cikin girmamawa nan manyan likitoci suka shiga Duba lafiyar Arman Inda suka duba sukaga zuciyar tashi ta kumbura sosai Dan Kad'an Ya rage ta buga nan suka shiga bashi taimakon gaggawa cikin kwarewar aiki irin nasu.Aira ita ce bata farka ba sai wajen Tara na dare da sunan Arman ta farfado ba abunda take In banda kuka sosai Aysha Da Aunty Fadila yayar Mamy suka shiga Lallashinta Sannan Dr ya k'ara musu bayani da cewa jininta ya hau a kiyaye b'acin ranta shi kanshi Dr mamaki yake garinya karama kamar wannan ta kamu da hawan jini duk yanda akai da Aira ta ci wani Abu kasawa tayi ko ruwa bata sha ba tun tana kukan harta dawo tana hawaye tana tausayin halin da ta tarar da Arman idan ta tuna kuma da maganganun da ya fad'a mata sai tayi murmushi ta ce "Ina nan jiran ranar dawowar taka my yaya nasan bazaka bar da'd'addiyar alak'armu ta tafi a banza ba Ganin Aira na hawaye kuma tana murmushi ya sanya Wanda ke wurinta tsorata sukace kodai ta zauce cike da tashin hankali Aysha ta kira Mama dayake sunkoma gida sai suka bar y'an matan Wajenta tana kuka ta ce " Mama Aira fa kamar ta zauce wlh kinganta nan tana kuka kuma tana Dariya "cike da tashin hankali Mama ta ce subhanalla Aysha kin tabbatar kuwa" wlh Mama da gaske kinganta nan yanzu haka hawaye take kuma tana murmushi"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Mama ta fad'a sannan ta ce"Bari na tafi gidan Malam Hassan(k'anin mahaifinta ne malami ne) ayi mata rubutun dakewa insha Allahu idan akayiwa mutum ana dacewa tunda ayar Allah ce"to Mama "Mama bata fad'awa kowaba saboda tasan hankalin Mamy k'ara tashi zaiyi Mama Halima kadai ta fad'awa itama tayi na am da hakan tare sukaje wajen Malam din suka yimashi bayanin komai cikin k'ank'anin lokaci yayi musu rubutu a Allo ya wanke ya zuba musu a leda ya ce Aje a bata ta sha gobe insha Allahu zai rubuta da yawa azo a amsar mata tana sha insha Allahu ko meye zata dake " Godiya Sosai su Mama sukayiwa Malam a Daren wajen shad'aya Mama da Mama Halima suka wuce asibitin A lokacin ma Aira na zaune ta kalli wannan ta kalli wancen sai kuma ta fashe da kuka ta ce "Yaya ku kaini wajenshi akwai maganar da zamuyi" Mama.Halima saida tayi hawaye ganin k'iri_k'iri yarinya na neman haukacewa "Zama Mama Halima tayi tare da daure fuska ta ce " Kiyiwa mutane shiru bansan shirme ke baki da tawakkali ne "kuka Aira ta fashe dashi ta ce " Mama yaya Arman ne fa munyi alk'awarin bazamu rabu da juna ba to me yasa suka tafarmun dashi"dafota Mama Halima tayi ta ce "Kiyi hakuri zai dawo nan kusa anje nema mashi magani ne dazuma munyi waya dashi ance ya farka yana ta tambayarki ya ce ki kwantar da hankalinki zai dawo saikuyi aurenku ko" lokaci guda Aira ta washe hakora ta ce "da gaske Mama sannan ta Rungumeta cike da farinciki ta ce Amma Naji dadi Mama yanzu yana dawowa Aure kawai zamuyi meya sameshi wai plx ku kiramunshi " bata rai Mama Halima tayi ta ce "zazzabi ne kawai sannan kuma Yanzu yayi bacci " bata fuska Aira tayi ta ce "wayyo Allah bashi lafiya To gobe kin kiramunshi " gyad'a mata kai Mama Halima tayi daman tayi mata wannan karyar ne Dan son kwantar mata da hankali"mik'a mata rubutun tayi ta ce "Amshi kisha yanzu " na meye Mama"banason tambaya cewa nayi kisha"Amsa Aira tayi ba musu ta Shanye rubutun tas"Ajiyar zuciya Mama Halima ta sauke sannan ta kalli su Aysha Da su mama ta ce "Zan kwana Wajenta kawai ku tafi gida" tafiya sukayi tare da Addu'ar Allah bata lafiya a hanya Haidar ya ce "Mama ya Aira fa ta zare wlh maganganunta duk na zararru take" Harararshi Mama tayi ta ce "karna karajin maganar nan a bakinka kayiwa y'ar uwarka fatan samun lafiya kaji" gyada mata yayi ya ce "To Allah ya bata lafiya "Mama Halima ita ta kwan wajen Aira sosai ta dinga kwantar mata da hankali harta samu taci abinci sannan ta samu har bacci ya d'auketa sai sannan tayi nata kukan tajima ta na Addur Allah ya kawowa yaran nan sassauci cikin rayuwarsu tukwana itama tayi bacci.washegari aka Sallami Aira Dan jikin nata yayi sauk'i wajen 12:PM suka dawo gida a d'akin Mamy ta sauka Dan bata kulawa jikin nata ya k'ara murmurewa Sosai Mamy ta d'an kwantar da hankalinta ganin y'artata taji sauk'i nan nan kawai take da Aira ga kuma tunaninta na Tasan kila Abbansu ya hakura a farke Auren nan yinin ranar Abba baiko lek'o Inda Aira take ba bare yayi mata ya jiki hakan ko ba k'aramun. K'ara konawa Mamy rai yayi ba ranar sau Ukku ana kawo rubutu daga gidan Malam ana bawa Aira kuma akayi sa a ba musu take sha Sai takejin zafin rad'ad'in dake cikin zuciyarta ya fara raguwa Kwana Ukku akai Aira na shan rubutun nan sosai ta d'an fara rage damuwa Saidai har yanzu tunanin Arman daidai da second d'aya yaki barin kwalwarta Saidai kuma abunda ke bata mamaki yanzu ya fara nutsuwa kuma ta rage kukan da take akai akai gashi Abba baiyi maganar kaita sokoto ba fata kawai take Allah ya wargaza Auren nan ta huta b'angaren Arman an d'an samu cigaba Kad'an amma har yanzu bai farfadoba hatta abinci Saidai a bashi ta hanci ko motsi bayayi Mummy kullum cikin kuka take Daddy ma sosai hankalinshi ya k'ara tashi sosai suka shiga damuwa lokaci guda harsun rame Kullum addua kawai suke Allah ya bawa Tilon d'ansu lafiya Daddy ko k'iyayyar Abba ce ta k'ara ninkuwa a cikin zuciyar shi Dan yasan shine silar shigar d'anshi cikin wannan halin.Bayan kwana hud'u ranar Alhamis Aira sosai ta fara wartsakewa Saidai kewar Arman da tayi mata yawa har lokacin Mama Halima bata tafiba Dan Mamy ta hanata tafiya ta ce itace kawai ke k'ara kwantarwa da Aira hankali Dan Allah ta jira ta Bari aga yanda Allah zaiyi hakan yasa Mama Halima ta zauna Aunty Maryam ko tuni ta koma gidan mijinta yayyun Mamy ma duk sun koma sai yayarta Aunty Ramlat kawai da ta tsaya suna zazzaune a palour Abba ya shigo nan ya shaida musu su shirya gobe Friday dangin Alh Yusuf zasuzo su tafi da amarya daman ya hakura ne shi mijin nata har taji sauk'i yanzu kuma tunda taji sauk'i Alhmdllh haka akeso Ku fara shiri"Sosai hankalin Aira ya tashi amma kawai batasan ya akayiba saitaji wani tawakkali ya zo mata idanunta dake zubar da hawaye duk kallonta mutanen dake wajen sukayi suga wani hali zata shiga sai sukaga kawai ta mik'e cike da hawaye ta ce "Allah ya kaimu" tana gama fad'ar haka ta wuce d'akin su tare da Fad'awa Gado ta jima tana kuka tana tunanin rayuwar da suka tsara Bayan auransu itada Arman k'watsam K'addara ta gifta musu Wannan shi ake kira ka na naka Allah na nashi Goge hawayenta tayi ta yi ta ce "ban isa na ja da ikonka ba Allah Kaine ka tsara duk wannan Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawar da ka jarrabemu da ita ya Allah idan har kasan mutuwa hutuce a gareni ya Allah ka kasheni kafin gob.....saurin rufe mata baki Aunty Ramlat tayi da ta shigo ta ce " ki daina fad'ar haka y'ata a farko kinyi magana me kyau daga karshe kina neman ki b'ata kiyi hakuri ganin kin cinye wannan jarabawar ki daina sanya damuwa a ranki ki nutsu kiyiwa mahaifinki biyayya zakiga fa'idar abun nan gaba"Cikin kuka Aira ta gyad'a mata kai ta ce "To mama" Mama Halima da Aunty Ramlat su suka gamu suka dinga yiwa Aira nasiha mai shiga gami da wa'azi sannan sukayi mata nasiha akan Wanda ya kashe kanshi direct d'an wuta ne karta k'ara yunkurin kashe kanta "Sosai nasihar ta shige ta sannan tayi musu alk'awarin insha Allahu bazata k'ara attempting kashe kanta ba " Sunkai wajen 1 suna mata waβazi da nasiha tukwana suka rabu da ita sukace ta kwanta Daren ranar bacci kauracewa idanunta yayi tashi tayi tayi alwala tayi salla Addua kawai take akan Allah ya bawa Arman lafiya sannan Allah ya bata hak'urin Auren nan da za ayi dukda ta d'auki alwashin k'untatawa Alh Yusuf har saiya gaji ya saketa Mummy ko haukane kawai batayi ba Bayan barin Aira palour masifa da ruwan bala'i ta shiga surfawa Abba ta ce "Wlh Alh baka da imani baka da tausayi Ka sanya yaran nan cikin wani hali kai wani irin mugu ne ka fiya son kanka da yawa kai mutum ne mai sonkai wlh na gaji da zaman gidan ka yau d'innan saika sawwakemun Ka sakeni kawai " Shima Abba cike da masifa ya ce "Ni zaki dinga zagi Rahama Dan Kinga ina Miki lakwa lakwa harkina samu daman fad'amun magana mahaukaciya kawai wacce batasan abunda take ba" Sosai fad'a ya kaure tsakanin Mamy da Abba Wanda dak'yal Mama Halima da Yayar Mamy suka samu suka basu hakuri Dan Aunty Ramlat saida tayi kamar zata bugi Mamy tukwana ta samu Ta koma daki Nan suka bawa Abba hakuri saida suka kashe case d'innan ne ma suka samu damar zuwa wajen Aira Daren ranar Aira bacci k'auracewa idonta yayi ga wani masifaffan ciwon kai da ya addabeta sai wajen karfe ukku wahalallen bacci ya kwasheta ko Sallar asuba bata samu tayi ba sai wajen Tara ta tashi Shima Dan Ummy ce ta tayar da ita da tazo ba jimawa tana tashi salla Aira tayi tana gama salla ta koma ta kwanta ta Lula duniyar tunanin Arman shin yana wani hali ya yake ta jima tana tunani batasan lokacin da wasu zazzafan hawaye ke zubo mata ba Mama da Mama Halima da Aunty Ramlat su suka shiga shiryen shiryen tafiya da Aira Mamy ko lek'owa batai ba Dan bak'inciki Daman tun last week akaje akayi jere maza sukayi jeren sosai Abba ya kashewa Aira kud'i a kayan daki kayan kitchen da sauransu gara ko ba a magana duk wani Abu da uwa zatayi shi yayi bai bari Mamy tasai ko chokali ba Dan daman yasan bazata sayaba tunda ba son Auren take ba wajen k'arfe biyu na rana y'an uwan Alh Yusuf sukazo su shidda manyan mutane domin tafiya da Amarya Sosai aka musu tarba ta musamman Mama Halima ita taje ta sanya Aira tayi wanka ta had'a mata ruwan Turare Aira na kuka ta na wanka Bayan ta fito kallonta Mama Halima tayi tare da fito da wata tantsetsiyar farar laffaya ita da kanta Mama Halima ta shiryata ba make up ba komai amma tayi bala in kyau dukda damuwar da Aira ke ciki ana shiryata tana hawaye farfesun y'ay'an ciki Aunty Ramlat ta kawowa Aira ita da kanta ta dinga bata tana ci dak'yal Tana ci tana hawaye Wajen k'arfe Hud'u da wani Abu Su Mama Halima suka kama hannun Aira suka fito da ita idonta Rufe cikin laffaya Amma ganin an fita da Aira kuka ta fashe dashi a d'akin bata tab'a jin damuwar Auren nan ba sai yanzu da za a tafi da Aira sosai ta dinga risga kuka Itama Airar kuka take Kama hannunta sukayi sukayi da ita d'akin Mamy suna shiga Kafin su k'arasa Mamy ta ce "ku tafi da ita kawai na yafe mata karku k'ara tayarmun da hankali" Jin haka ya sanya Aira saurin fusgewa tare da rugawa taje ta Rungume Mamy ta fashe da wani irin kuka itama mamyn Rungumeta tayi tana kuka sosai suka shiga rera kuka hatta su Mama Halima saida suka sanyasu kuka Sun dβau minti goma suna kuka ganin abun nasu ba mai kyalewa bane ya sanya Mama Halima zuwa ta kama Aira Fusgewa Aira tayi cikin kuka ta ce "Mamy Mamy karki bari su tafi dani Mamy nasan ke kina sona " Itama sosai Mamy ke kuka Mama Halima ce ta ce "ki mata addu'a ki yafe mata ba kuka zaku zauna kunayiba" Cikin kuka Mamy ta ce "Na yafe mata duniya da Lahira Allah yayi miki Albarka Allah yayi miki Albarka Aira na yafe ma..kasa karasawa tayi sakamakon kukan da yazo mata kama Aira sukayi Dan tafiya da ita sosai Aira ke kuka tana ruk'o Mamy tana cewa" Mamy karsu tafi dani Mamy Mamy......Dak'yal suka samu suka Bambareta suka fito da ita Kai tsaya dakin Mama suka Nufa da ita itama Sosai sukasha kuka tukwana suka wuce da ita wajen Abba "Ganin irin kukan da Aira take karo na farko kenan da Abba yaji tausayin y'ar tashi tunda aka fara abun nan Danne zuciyarshi yayi ya ce " Allah yayi miki albarka Mama na na yafe miki duniya da lahira Allah ya bada zaman lafiya kutafi da ita kawai"Rik'e k'afar Abba Aira tayi dake kuka kamar zata mutu ta ce "Abba karka bari su tafi dani Dan Allah Abba" Rungumota Abba yayi tare da mik'ar da ita ya kalli su Mama halima ya ce Muje Abba da kanshi ya saka Aira mota dake kuka Kallonsu mama Halima yayi da yan uwan Alh Yusuf ya ce "muje na Muku rakiya Airport d'in Abba da kanshi ya tuk'a Aira har Airport......βπΏ
πππππππ
*NI DA YAYA ARMAN it's not free it's for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*
_*Miss Hajo ce*_π€πΏπ€πΏ
[6/26, 09:43] Hajo hajo: π
ΏοΈ..........*63&64*
....Suna isa Airport Abba da kanshi ya kama Aira ya fito da ita Yana gaba itadashi da take Rungume jikinshi tana shashekar kuka sauran y'an rakiyar na baya daman an Riga Angama musu komai ba ayi minti goma ba akace jirginsu zai tashi y'an uwan Alh Yusuf su suka amshi Aira da ke hannun Abba dak'yal suka Bambareta sai risgar kuka take cikin sanyi Abba ya ce musu "Ga amana nan na baku dan Allah ku rik'emun ita amana bata da kowa a chan na damk'ata a hannunku ku rikemun ita amana"a tare suka ce insha Allahu mun karb'a hannu biyu Alhaji mungode Allah ya saka da alkhairi Aira na kuka tana kiran sunan Abba har suka kamata suka shiga jirgin Mama Halima da Aunty Ramlat sukayi mata rakiya a tare suka tafi ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga sokoto Abba ko cike da kewar y'artashi ya koma gida har yanzu duk cikin y'ay'ashi ba Wanda yakeyiwa son da yake yiwa Aira a cikin zuciyarshi ba yanda zaiyine dole sai hakan yana komawa gida ya ci karo da Mamy tana fitowa da akwatinta tare da Amer a hannunta kallonta yayi ya ce " ke kuma ina zaki"Cike da masifa ta ce "Gidanmu zan koma kuma.wlh saika sakeni tunda ka rabani da y'ata ka turata uwa duniya cikin kishiyoyi mararsa imani inma kashemun ita za ai ayi kai ba ruwanka ka cuceni wlh Alhaji sakayyata dakai sai lahira Sannan ka bani takardata na koma gidanmu yau ba Inda zani saida takardata tunda kayi abunda kakeso hankalinka ya kwanta nima kuma zanyi abunda nake so ka bani takardata Alh tun muna mu biyu " sosai maganganun Mamy suka b'atawa Abba rai Danne zuciyarshi yayi ya ce "Kije na aika Miki takardar taki gida sannan ya mik'a hannu ya ce " bani d'ana ai ba da shi kikazo ba ba yaro d'aya ba zaki tafarmun dashi ba Tunda ke mahaukaciya baki da hankali