NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   44 / 54

129K to 132K   out of 160.7K words

"Ana buk'atar Kara musu jini nawa za a d'auka" Cikin Sauri Arman ya ce "nau mana Dr Dan Allah ka taimakamun kar wani Abu ya samu yarana " Cikin gaggawa aka Auna jinin Arman akaga Yayi daidai Nan aka d'auka Inda likitan ya bawa su Naila Gado ya sanya musu a lokacin duk sume suke Shi kanshi yayi mamaki ace jinin yara ya zuke haka lokaci guda gashi yaran baiga Alamun Rashin jini a tattare dasu ba wani tunani ne ya fad'o masa Tabbas yaga yanda ake dora yaran nan a media Dan ya sansu shi kanshi farin sani Tabbas y'an shan jinine suke neman Shanye musu jini dayake musulmi ne Wani malaminshi ya kira Akan Dan Allah yazo yayi wani taimako ta Cikin wayar yayi mushi bayani da yake malamin mai taimakone ya ce gashinan zuwa su Aira sunyi jugum jugum sai risgar kuka take Arman shinema mai k'arfin halin Lallashinta Suna tsaye sukaga wucewar Malam Cikin office d'in Dr d'in binshi sukayi Dan sungaji da jira A tare suka shiga cikin kuka Aira ta ce. "Dr kar yarana su mutu Dan Allah Dr ina sonsu wlh ka taimaka mana" kallonsu Malam din yayi ya ce "Karku damu Kuyi musu addua Sannan ya kalli Dr Bayan sunyi musabaha ya ce " Ina yaran suke"Mikewa Dr yayi ya ce "Bari muje d'akin da suke a tare suka shiga d'akin harsu Aira Hango yaran nata yashe gadon marassa lafiya karasawa tayi ta fashe da kuka tana sabbatu Dak'yal Arman ya tadota Kallon Dr yayi yaa ce " akawo ruwa a cup"miko masa akayi ya jima yana tofa adduo'i a cikin ruwan kafin ya k'arasa Inda yaran suke ya yayyafa musu Nan take suka kawo numfashi tare fara kikkifewa Rikesu Malam yayi Inda ya shiga tofa musu Adduo i da karatu yayi minti Talatin a kansu dayake Babban malamine su Aira duk sai kallon ikon Allah suke Chan sukaji sun tashi tare da Fara tari sai kuma suka fara kuka "Cikin farinciki aira taje ta rungumesu tace " Alhamdulilla Allah nagode maka"Ajiyar zuciya Malam ya sauke ya ce " Alhamdulilla a Gaskiya yaran nan sun Auna arziki wlh inbanda dr kayi tunanin gane kan matsalar da Saidai wani ikon na ubangiji masu shan jini ne suka kamasu suka fara Shanye musu jini amma sun sakesu yanzu insha Allahu Saidai a cigaba da musu adduo'i Sosai sannan a kiyaye da yawa iyayen yanzu kuna sakaci da Yaranku saikiga yaro gashi bud'e ko anyi kitso yayi kyau an bud'e ko kaga ana d'ora yara social media Wanda hakan duk ba dacewa bace ta wannan hanyarce har ire_iren mutanen nan suke samun daman Shanye jinin Yaranku ku daina Sakaci da Addua Allah ya kiyaye gaba "Ameeen dr da Arman suka fad'a sosai suka shiga yiwa malamin Godiya Inda ARMAN ya bashi check din one million da farko kin karba yayi ya ce Ai aikin Allah ne yayi Dak'yal dai ya samu ya amsa Inda ya rubuta musu Adduo i sosai Wanda zasu dinga yiwa yaransu dasu kansu na tsaro.
Bayan barin Malam wajen Kallon Arman Dr yayi ya ce " Bro Gaskiya Ku daina d'ora Yaranku a media baki da ido yayi musu yawa "da mamaki Arman ya ce " media kuma dr ai yaran nan bama Dorasu media Ko what's app ba Dorasu mukeba ko Ya fad'a yana kallon Aira dake feeding d'in yaran gabantane ya bada daram shikenan yau asirinta ya tonu"Kasa da kanta tayi gabanta na fad'uwa Lalubo Wayarshi Dr yayi ya shiga shafin Oum twins Naila&Nihal nan take Abubuwan yaran suka bayyana mik'awa Arman Wayar Dr yayi ya ce "Wannan ba su bane " Da mamaki Arman ya amsa Inda ya shiga Dubawa Tabbas sudinne Post d'insu yafi d'ari Ukku Kome suke ana d'auka ana dorawa Hatta shigarsu ta yau da safe yaga an d'ora sosai ranshi yayi mugun b'aci"idanunshi da har sun sauya launi ya kalli Aira datayi kasa da kanta ya ce "Uban waye yake doramun Yara a tsinannan abunnan " kasa tayi da kanta gabanta na fad'uwa ta kasa magana "Tsawa ya daka mata da ta mance rabon da yayi mata ya ce " nace ubanwa Yasa ki dinga doramun y'ay'a a duniya tallarsu nake ,ko me Da izininwa kika bud'e tiktok ?tuni Aira harta fara hawaye Cikin rud'u ta ce "Dan girman Allah yaya kayi hakuri?zuciyar ARMAN banda tafarfasa ba abunda take sosai ta bata masa rai to yanzu da yaranshi sun mutu fa a saboda dorasun da take har y'an shan jini zasu kashe musu yaya Tabbas saiya d'auki mataki bazai kyaletaba (hakan yana Faruwa sosai wlh Iyaye a dinga kiyayewa Allah ya kara kiyayewa ameeen)Tsawa ya daka mata ya ce " Ajemun yara na "Cikin rudu tana hawaye ta mik'e Dan baitab'a mata haka ba tsawon rayuwarsu tare da Jan baya hanyar kofa ya nuna mata ya ce " Get out."Yay....tsawar da ya daka mata ya sanyata saurin barin dakin hada tuntube tana kuka waje ta samu kofar D'akin ta durkushe tare da fashewa da kuka itakam ta bani Kenan yanzu da masu shan jini sun kashe mata yara bata tab'a tunanin hakanba ga ARMAN yanda taga yayi mugun fushi kuka take sosai Tana danasanin d'ora Yaranta da take Arman ko zuwa yayi ya Rungume yaran daman sunsaba da Daddynsu hakan yasa sukayi shiru jikinshi suna wasa da gemunshi yana musu wasa a haka har jinin ya k'are Inda Dr d'in yazo ya cire tare da rubuta musu magani Godiya sosai Arman yayiwa Dr d'in Inda ya amshi number shi Shima yayi mashi alkhairi sosai Rungume Naila datayi bacci a kafad'arshi yayi tare da d'aukar Nihal da idonta biyu ta lafe jikinshi yayi a haka ya fito Kallon Aira yayi data hade kai da guiwa tana kuka ya ce "Wuce mu tafi" cikin Sauri ta mik'e tana kuka ta ce "Dan Allah yaya....d'aga mata hannu yayi ya ce " banson jin komai daga bakinki Goge hawayenta tayi tare da bin bayansu zasu shiga mota mik'a masa hannu tayi zata amshi Naila tsaki yaja tare da kallonta ya ce "Ai bazaki Kara daukarsuba tunda bakya sonsu ni inason abuna kuma zan kula dasu daga yanzu kika k'ara daukarmun yara duk abunda na maki ke kikaja" Jan bakinta Aira tayi tana Hawaye Dan tasan sahibin nata yayi fushi sosai da ita a baya ya kwantar da Naila Inda ya na rik'e da Nihal ya shiga matuk'ar driver ya sanyata gabanshi yana tukawa ganin zai tada motar ya sanya Aira saurin shiga gaba tare da rufewa harsuka isa gida baice uffan ba itama sai hawaye take suna isa ya zagaya ya d'auki Naila da ta tashi ta fara kukan yunwa a palour suka baje Inda ya had'a musu madararsu ya basu daman suna sha sosai nan suka shiga sha a lokacin kasancewar magriba ya sanyashi Zaunar dasu yasa musu abun wasa yaje yayi alwala ya tada salla Yana gamawa yaje ya lalubo turaren da goggo ta taba basu basu taba amfani dashi ba na miyagu da iska nan ya hada boner ya sanya take dakin ya bide da kaurin maganin inda daya bayan daya ya turare yaran saida yaga sun fara tari alamun hayakin ya fara musu yawa tukwana ya dauke Aira ya kalla da duk tayi jugum tana hawaye ya ce "Bani wayarki ?Jikin charge ta cirota Dan daman tana chaji suka tafi mik'a masa tayi Daman ba security Tiktok din ya shiga ya shiga bincikawa yaga itadince duk gashinan ta daddora Wasu frnds d'inta yabi Wanda suma suka d'ora yaga wata Rahama ta d'ora yafi sau goma sai lemart da yaga ta d'aura sau Ukku sai wata Jannat Abuja Itama ta d'ora so biyu duk saida ya k'ara biccinkawa yaga su kadai suka d'ora Kallonta yayi fuska babu wasa ya ce " wacece Rahama Lemart Jannat?tana shashekar kuka ta ce "Kawayenane ?tsaki yaja ya ce " zoki amsa ki kirasu kice su sauke abubuwan yarana da suka d'ora yanzunnan"cikin Sauri taje ta amshi wayar tana kuka Rahama ta fara kira tana d'auka ta ce "Mom twins yau wata sabon gani kece hada kirana" Cikin muryar mai kuka Aira ta ce "Momcy Dan Allah hotunan su twins da kika D'aura ki sauke Yanzu Dan Allah a tiktok" lafiya mom twins nagama kamar kuka kike"Da sauki dai ki sauke Yanzu Tana gama fad'ar haka ta kashe kiran kallon Arman tayi d'aya kafeta da idanu Jannat ta dannawa kira itama ta fad'a mata haka A na lemart ne gabanta ya dinga fad'uwa karta ganeta Harararta yayi ganin takasa kiran d'ayar ya ce "jiran me kike" Goge hawayenta tai tare da Danna mata kira lemart na na d'auka sosai tayi mamakin ganin kiran Muryar da ba tataba Aira ta ara ta ce "Sis Dan Allah hotunan su twins da kika d'ora zaki hau yanzu ki sauke plx" subhanalla lafiya"da sauki ki sauke Dan Allah"too yanzu kuwa Amma meya faru Naji kina kuka"Bata bata amsa ba Aira ta katse kiran mik'awa Arman Wayar tayi da ya mik'o hannu amsa yayi tare da Kara shiga yana shiga Yaga Rahama. Da Jannat harsun sauke nasu tsaye tayi yaga saukewar na lemart itama tana nan yaga ta sauke ajiyar zuciya ya sauke Tare da shiga daman shi ya kware a computer a take ya lalata account din nata yayi harking dinsa yana gamawa Ya goge tiktok din gaba d'aya Tare da kashe wayar yasa a Aljihu D'aukar twins d'inshi yayi da suka fara bacci yayi ya wuce Bedroom d'insu Aira dai ta zama hoto dak'yal ta iya Jan kafarta ta shiga dayan bedroom d'in Sallar itama tayi har isha i da taji ankira Tana gamawa itama Sosai tayiwa yaran nata addu'ar neman tsari Tana nan zaune har 12 duk daukarta Arman zai huce da wuri Kodan susha abincinsu ai ya kawo mata su Amma taji shiru tunowa da bak'ar zuciyar Arman tayi ya sanyata saurin Mikewa ta fito d'akin ta shiga a hankali Inda ta samesu kwance akan Gado Arman a lokacin ba bacci yakeba yanajinta ya rufe idonshi Kamar mai bacci Ajiyar zuciya Ta sauke tare da Yin sanda a hankali taje ta d'auko Nihal tare da zama Gefen gadon Zage zif din rigarta tayi ta fito da Mamanta tare da sanya mata abaki Nihal da daman abunda take buk'ata kenan a take ta tashi tare da kamawa ta dinga tsotsa Dukda duhune hakan bai hana Aira yi mata wasa ba Takai 15 minutes tana sha tukwana taji ta saki Alamun tayi bacci a hankali ta yunkura Ta maida ita makwancinta tare da rufa mata bargo Arman duk yanajinta yana kallonta ta wutsiyar ido sosai yaji tausayinta Allah sarki y'a da uwa kenan ya fad'a yana jinjina kai Aira ko a hankali ta d'auko Naila Tana daukarta Ta yage baki zatayi kuka Cikin Sauri ta sanya mata abaki Wanda hakan yasa tayi shiru Ajiyar zuciya ta sauke daman yunwa Naila takeji nan tashiga tsotsa Sosai saida tayi 30 minutes tana tsotsa Aira harta fara gyangyadi Chan kuma taji ta saki Alamun tamayi bacci Daman Naila tafi Nihal tsotsa a hankali ta maida abunta tare da kwantar da ita Tana shirin Mikewa tabar dakin taji Arman ya janyota tare da rungumeta jikinshi Dan tuni zuciyarshi ta karye Yama fasa horata din da yace zaiyi Aira jin Haka kamar me jira ta sanyata sanya mishi kukan shagwaba ta ce "Yaya Dan Allah kayi hakuri Allah bazan sakeba nima nayi nadama dan Allah karkayi fushi dani bazan iya jurar fushinkaba yaya please ka yafemun"Rungumeta yayi ya ce " Na hakura my cutie nima ai bazan iya fushin dakeba ta maza ce nayi na daure amma kin b'atamun Raine Kinga yanzu inbanda Allah ya taimaka malamin nan yazo dafa zamu iya rasa yaranmu"Cikin kuka ta ce Bazan sakeba yaya "to my cutie na hakura ya fara yana fara romance d'inta Kamar basu tab'a fada ba daganan suka Lula wata duniyar ta daban.
Twins Nada shekara daya da Rabi sosai suka Tashi da baki magana rai rai ga shegen wayau ga gudu ko ina Komai aka fad'a saisun maimaita A lokacin ne kuma Aira ta fara wani irin zazzabi da amai ga tashin zuciya arman yayida ita suje Asibiti ta kiya yauma tana kwance jikinshi Tana sauke ajiyar zuciya twins na tsaye suna wasa su biyu da teddy Shafa cikinta arman yayi ya ce " Cutie kodai nayi ajiya ne a cikin nan yake sanyaki amai da tashin zuciya"cikin shagwaba ta ce "Hero ka manta wancen cikin na twins banyi wani lauyayi ba sai nakega kawai ciwo ne fa " Naila ce ta rugo da gudu ta fad'a jikin Aira nihal kuma ta fad'a jikin Arman cigaba da hirarsu sukayi ARMAN ya ce "Amma ai saikanakega baizama lalle Duka biyun ya zama iri daya d'aukar cikinsu sainakega kowanne da banbancinsa nidai ban yarda ba cikine dake cutie" Uhm Nidai ka daina cewa haka hero ciwone kawai"Naila ce dake tsotsar yatsa Duka sunajinsu ta kalli Aira ta ce "Cuty(Cutie) itakuma Nihal ta kama Sajen Arman ta ce " Helo(Hero) Wara idanu a tare Aira da Arman sukayi Arman ya ce.....✍🏿


*Ki biya naki ki karanta cikin nustuwa da kwanciyar hankali akan Naira 200 kachal to 07026166536*



_*Miss Hajo ce*_

[7/18, 13:05] Hajo hajo: 🅿️........*111&112*







Ya ce "Chab Kwaiwayonmunefa sukayi?Dariya Aira tayi ta ce " Aidaman shirun nan danaga sunyi sunajin me akecewa "Dariya twins sukayi Naila ta kama rigar Aira zata d'aga ta kasa turo baki tayi ta Ce " Cuty mama ansha"Itama jin Haka ya sanya Nihal saurin Rugawa ta Dare Aira ta ce "Cuty nima ansha"Dariya sosai Aira da Arman suke Arman ya ce " Kinga yara karfa su sa mana suna"Dariya itama Aira tayi ta ce "Ai na yayeku tunda kuka iya gulma daga yau " kamar sunsan me tace sukahau kuka Arman da bayason kukan yaran nashi saurin yiwa Aira magana yayi akan tabasu susha tukwana ta basu tana jin haushin yanda Arman yaki bari ta yayesu gasudai tubarakalla saika d'auka sun haura shekara biyu ita har kunyar Shayar dasuma take wlh.
Tundaga ranar twins suka sanyawa iyayen nasu suna ba irin yanda basuyiba su hanasu amma suka hanu saidai wani gamun sucewa Aira "Cutie mom" Shikuma Arman "Hero dad" sosai yanzu jikin Aira ya k'ara tsanani kome taci saita maidoshi Koda sukaje Asibiti gwajin farko likita ya tabbatar musu da tana d'auke da juna biyu na Wata biyu zokuga farinciki wajen wannan masoyan haka suka dawo gida suka ci gaba da rainon cikin su Wanda kuma lokacin Mummy da taji Aira Nada ciki ta yiwa Arman magana akan a yaye twins sun girma da kansu suka yaye yaran nasu daman sunacin abinci sosai hakan yasa basu sha wahalar yayensuba Mummy ma tazo ta duba jikin na Aira Inda taso tafiya da twins saboda rage musu wahala Amma sukak'iya subita suka dinga rafka kuka hakan yasa Mummy ta ajesu tace karma mutane suce satosu tayi daman iyayen baso suke ba Dan Aira bata nuna ba Amma Arman Saida ya nuna bayason Dan ko Kad'an bayason abunda zaiyi nesa da yaran nasu a lokacin ya kaisu school saboda shegen wayau da garesu da baki ya sanya malaman amsarsu Dukda sai ansha dagu suke zuwa school d'in musamman Naila danma sayayyar Choculate da kayan makuleshen da ya ninka saya musu ya sanya suka Dan yarda suke zuwa makarantar kullum idan zasu tafi sai sun tofe su da adduo'i Dan idan ka gansu da kayan makarantar zakayi mamakin irin kyan da sukayi yau Aira na kwance saman bed Dan da zazzabi ta tashi ga ciwon kai Arman ya bata maganin da Dr ya rubuta musu ta sha Rungumeta yayi akan bed Dan twins na palour suna wasa kasancewar yau weekend Yana shafa bayanta yace "sorry cutie Cikin nan Yana baki wahala da sauki d'auko" gyada mashi kai tayi tana Lafewa jikinshi dan bacci takeji"Kwantawa sukayi a tare Rungume da juna ya dorata saman ruwan cikinshi irin yanda akema yara idan sunaso suyi bacci tare da Daddab'a bayanta yana zuba mata kalamai masu zafi Itadai Uhm kawai take cemas shikam arman a hanksli ya dinga shafa ta tare da sanya hannunshi a rigarta yana mata wani irin salo twins ne jin iyayen nasu shiru ya sanyasu rugawa d'akin suna banka k'ofar suka samesu a haka Kallon juna sukayi tare da wara idanu Saikuma suka k'ara kallon iyayen nasu ido hud'u sukayi da Aira da Arman Saurin Juyawa sukayi suka koma palour Aira ko cikin saurin ta mik'e Ta ce "Yaya me suke nufi jifa kallon da suka mana" Shima Mikewa yayi tare da kama hannunta Suka fita a palour suka tarar dasu sun had'e waje guda suna kallo"Wajensu Aira ta nufa ta ce "My twins Kallo ake " banza sukayi da ita kallon Arman tayi tamai nuni da yazo yana zuwa Ya ce "my twins Me yasa kuka kyale mummynku naila uwar iyayi da tsiwa tana turo baki ta ce " Ba luwanmu daku mu"Wara idanu a tare sukayi suka kalli juna sannan suka kallesu Aira ta ce "Me mukayi muku" suna turo baki Nihal miskila ta kauda kai Naila kuma ta ce "ku Daina kaji Hero ba chauu"Kallon juna Arman da Aira sukayi saikuma Aira ta fusge Dan ta lura yaran nata abunda suka nufi tsaki taja ta ce " yara sai shegen sa ido mu wlh daman mummyn ta tafi dasu suka barmu muka huta ba damar Mu sake muda gidanmu yara sai gulmar tsiya "Dariya Arman yayi ya ce " ai shiyasa kikaga na sanyasu school a a gwara da Mummy ta barmu da abunmu ai sakacinmunema da muke barin d'akin bud'e"Turo baki Aira tayi tare da kallonsu ta daure fuska ta ce "Kuka k'ara shigo mana d'aki batare da kun nemu iziniba saina zaneku uban me ke hanaku knoking Dan iskanci ku fadowa mutane d'aki ba ko sallama haka nakoya muku?kamar jira suke Dan a rayuwarsu basason fad'a aiko suka fashe da kuka rungumesu Arman yayi tare da Hararar Aira ya ce " Kinga kin sanyamun su kuka wa yace ki musu fad'a "tab'e baki Aira tayi tare da barin palourn taje ta haye Gado tare da kwanciya Dan bacci takeji Arman ko sosai yasha dagu wajen bawa yaran

44 / 54