NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   45 / 54

132K to 135K   out of 160.7K words

nashi hakuri Dak'yal ya samu suka hakura Shima saida ya kaisu shan ice cream da wajen wasa tukwana suka sauko Aira a lokacin tana d'aki ta tashi dak'yal ta yunkura tayi wanka tana fitowa ta sanya rigar bacci ganin magriba nayi tana fitowa palour ta samesu suna shigowa da kayayyaki a hannunsu " tana ganin haka tasan wajen wasa ya kaisu Dan kullum suna hanyar park Sannu da zuwa tayi musu tare da kwantawa Sannu Arman yayi mata Twins ko sai kallonta suke sunason suje Wajenta suna tsoron karta musu fada irin na d'azu Take away din da yayo mata ya bud'e tare da nufar ta ya ce "Cutie bakici komai ba Yau ki daure kici ko Kad'an ne zakiji sauki" Hero amma kasan zan iya maidosa"girgiza mata kai yayi ya ce "Bazaki maidosa ba " Ya fad'a yana kai saitin bakinta Tare da Fara bata ci spoon hud'u ba Taji zuciyarta ta tashi da gudu ta mik'e kafinma ta isa toilet din palour ta fara amai sosai take yi kamar zata amayar da y'ay'an cikinta Arman yaje cike da tausayawa ya taimaka mata ta gyara jikinta shiya gyara Inda ta bata tare da sanya k'amshi twins ko sosai suka rude ganin mamansu cikin wannan halin musamman Naila da har ta fara kuka Wajen Aira data fito daga toilet din taje tare da Rungumeta tasa kuka Shafa kanta tayi tare da karasawa palourn ta zauna dasu a tare da ita Nihal ma jikinta ta fad'a tana hawaye a tare suka ce "Sorry cutie mom bazamu sakeba" Gyada musu kai kawai Aira tayi tare da kwantawa kan sopa "Jikinta suka haye Naila ta dinga shafa fuskar mamantata ta ce " Sorry mom sannu"Murmushi Aira ta sakar musu tare cewa "yawwa" Ganin sun damu sosai ya sanyata K'arfin halin nuna lafiyarta qalau ranar dak'yal ta samu sukayi bacci da anjima anjima saisu zo wajenta suna mata Sannu Aira saida tayi hawaye ganin yara dai kanana yanda suke tattalin uwarsu kamar wasu Manya '"Allah sarki d'a da uwa kenan sai Allah sosai itama ta shiga kogin tunanin tata mahaifiyar Arman ma sosai yake jera mata Sannu da tattalinta.
Yau da lafiya gobe babu haka har cikin Aira yayi wata takwas Inda ya fito amma baiyi girma sosai ba Yau suna zaune a garden din gidan Su Duka Twins na Danna tab D'insu Mummy ce ta kira Arman Bayan sun gaisa yabawa Aira itama suka gaisa Jin Mummy da gudu twins suka amshe wayar suna rigen cewa "Mummy Mummy " murmushi bangaren Mummy tayi ta ce "Iye yaran Mummy yakuke " am Very fine mom how are you"Nihal ta fad'a cikin Muryar yara'alhmdllh Mummy ta fad'a "Naila ce ta amshe ta ce " Hello takwala "Dariya Mummy tayi ta ce " na am my takwala yakike "Lafiya qalau takwala yauce jakijo munyi missing d'inki" ni bazanzoba Saidai ku kuzo ganina Mummy ta fad'a "Shagwaba Naila ta dinga mata akan saitazo daga karshe danson kwantar mata da hankali ya sanya Mummy cewa 'to shikenan zanzo " tsallen murna Naila tayi tare da wulla wayar ta Dare Arman ta ce "Hero Mummy zatazo am very happy"shafa kanta yayi yana murmushi ya ce " kice takwararki ta kusa zuwa Me zaki shirya mata"Abinci me nice "Naila ta fad'a tana zillo jikin Arman " dauko wayarshi yayi da ta fashe dan tunda aka haifi twins waya kusan biyar suka fasa masa saidai ya sauya wata Nihal ko kuka ta fashe dashi Duk kallonta sukayi Aira ta janyota ta ce "Lafiya kukan me kike" Cikin kuka ta ce "Nima cutie ina takwala ta kullum takwalal Naila kadai take zuwa muke waya da ita ni hal yanju banga takwalata ba " Jikin Aira ne yayi sanyi harshi Arman Naila ce tayi mata gwalo ta ce "yeyeye yalinya to ai ke sunan maman cutie gareki Mummy maman Hero ce ko?ta fad'a tana kallon Arman?cikinsu ba Wanda yayi magana " Nihal ce cikin shagwaba ta kalli Aira da har ta fara hawaye ta ce "Cutie wai gaske sunan mom enki galeni?gyada mata kai Aira tayi tana Hawaye " a tare kamar sun had'a baki Nihal da Naila suka ce "Cutie ke ina mom En taki bamu tab'a ganinta ba mom En hero kadai muka sani sannan bamusan Dad enki ba Dad ein hero kadai muka chani "Aira kamar daman jira take Wani kududune taji tundaga zuciyarta sosai yaran Suka tayar mata da hankali bata tab'a jin tashin hankali tunda tabar gidansu ba irin na yau bata tab'a sha awar waiwayar gida ba sai yau kuka ta fashe dashi sosai Rungumeta Arman yayi ya ce " Subhanalla cutie meye haka kukanme kike"Sosai take kuka a jikinshi Inda twins duk suka tsaya suna kallonta suma harsun fara hawayen ganin mom d'insu na kuka Arman duk ya rud'e ganin irin kukan da Aira take ya ce "Kiyiwa girman Allah cutie kibar kukan nan daga yara sunyi magana zaki tashi hankalinki " Cikin kuka ta ce "Yaya Mamy nakeson gani Dan girman Allah ka kaini na ganta......✍🏿


*tofa ya kenan Twins sun Tayarma da Mummynsu hankali harta fara tunanin Gida*


.
_*Miss Hajo ce*_
[7/18, 17:31] Hajo hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN*🍏
_Hot love story_β™₯️

MALLAKAR
Hajara L Sadeq

*Bonus page*πŸ’ƒπŸΎπŸ˜‚

πŸ…ΏοΈ.......*113&114*



....Dan girman Allah ka kaini na ganta"ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka"Lallashinta ya fara ya ce "Kiyi hakuri cutie kibar maganar nan ki bari ba yanzu ba na kaiki ki ganta d'in amma ki bari saikin haihu" Mikewa Aira tayi tana Hawaye ta ce "Dole kace haka tunda bakai ne kake cikin halin da nake cikiba amma kasani ina k'aunar mahaifiyata kuma inason ganinta kamar yanda kowani d'a yakeji game da mahaifiyarshi Daurewa kawai nake tunda nake dakai na tab'a cewa ka kaini naga mahaifiyata yanzu nace ka kaini shine zaka k'i kaini" tana gama fad'ar hakan ta bar wajen tare da nufar hanyar Palour binta yayi yana kiran sunanta tayi mishi banza "Tana shiga Aira d'aki ta shige tare da rufewa da durkushe ta fashe da kuka abubuwan da suka faru a baya suka shiga dawo mata cikin kwalwarta kuka sosai take kamar ranta zai fita Arman da twins ba irin bugawar da basu mata ba dansu har sun fara kuka amma taki bud'ewa sai kukanta da suke juyowa sosai Hankalin Arman ya tashi palour ya koma Tare da dafe kanshi da yake Sara masa twins ne suna kuka suka ce " Hero kaba cutie hakuri bazamu sakeba mu muka chanyata kuka ko dad?rungumesu yayi ya ce "Ba ku kuka sanyata ba kuka My twins Karku Damu kinji" nan ya shiga Lallashin su har ya samu sukayi shiru duk sunyi sanyi Naila uwar iyayi harda tagumi "Arman ba irin yanda baiyiba Aira ta bud'e amma taki Mummy ya kira cikin damuwa ya fad'a mata abunda ke faruwa " Cewa tayi "ka lallab'ata Ta hakura ta Bari idan ta haihu saiku taho din yanzu ina zata da tsohon ciki" Cike da damuwa ya ce "to Mummy amma banajin zata hakura" ka jaraba idan Bata hakura ba saimusan yanda za ayi"To ya fada ranar Aira kulle ta kwan a d'aki tana kuka har bacci ya d'auketa su ARMAN ko a palour suka kwana shida yaranshi Da safe Bayan ta tashi idonta yayi jawur saboda kukan da tasha cikin k'arfin hali tayi wanka ta shirya cikin Doguwar Riga marar nauyi parasitimol ta b'alla Tasha saboda ciwon da kanta ke mata "bud'e d'akin tayi ta fito Inda ta samu Arman yana bawa yaranshi abinci a palour duk kallonta sukayi musamman Arman Cikin tausayawa ya ce " Sorry cutie Kintashi lfy "Alhamdulilla ta fad'a tana zama tare da kauda kai twins suka tashi sukaje suka hau kanta a tare sukace " Good morning cutie mom ya jikki"morning too my angels how was your night "ta fad'a tana shafa kansu" Very fine suka fad'a Sannan nihal ta marairaice ta ce "Cholly mom bazamu chakeba"murmushi Aira tayi musu " Arman ne ya taso ya ce "Taho muje kiyi breakfast" Kauda kai tayi tana shan magani ta ce "Na koshi" Amma dai kinsan bakici komai ba tun jiya banson irin haka cutie ki taho muje kici abinci kodan Abunda ke cikinki"ya fad'a cikin kulawa "kamar me jira tuni ta fara hawaye Cikin fushin da bata tab'a masa irinsaba ta juyo ta ce " nace na k'oshi bazanciba Ta fad'a tana Mikewa tana kuka tayi hanyar bedroom taku biyu tayi zatayi na Ukku ya ce "kika k'ara taku d'aya ban yafe maki ba " Chak ta tsaya bata juyoba Batayi gaba ba "Ajiyar zuciya ya sauke tare da Cewa dawo ki zauna muyi magana " ba musu ta janyo kafafunta tana hawaye ta dawo ta zauna "Matsawa Inda take yayi cikin damuwa ya ce "Meye haka cutie wani sabon salon ne kika samo Wanda baki dashi fushi kike dani me nayi maki?Kuka ta fashe dashi tare da Fad'awa jikinshi tana kuka ta ce " yaya na fad'a maka Mamy nakeson gani ka taimakamun ka kaini Wajenta Dan Allah na hadaka da girman Allah"sosai yayi sanyi Cikin sigar lallashi ya ce "Kiyi hakuri cutie idan kika haihu yanzu bakiga yanda kike Bafa k'aramar tafiya bace daga nan zuwa 9ja " Cikin kuka ta ce "Yaya Dan soyayyarka da Annabi Muhammad (S A W) ka kaini yanzu banajin komai ba abunda ke damuna nidai ka kaini na ganta"to shikenan Bar kukan insha Allahu zan kaiki shikenan ko" Dagowa tayi fuskarta jab'e jab'e da hawaye ta ce "da gaske " murmushi yayi mata ya ce "Ehmana cutie jibi insha Allahu saimu tafi" Cike da farinciki Aira ta Rungumeshi ta ce "Thnks you so much My husband " murmushi yayi yana shafa kanta Aira sosai taji farinciki Wanda harta k'agara jibin tayi koda Arman ya kira Mummy ya fad'a mata cewa tayi Allah ya kawosu lafiya Aira ko tun ranar ta fara shiri da parking d'in kayan twins kayanta kala biyar kawai ta zuba a akwati sauran duk na twins ne da kuma na Unborn da suka fara sayayya twins ma sai murna suke zasuje 9ja Washegari Arman ya bata wayarta da ya amshe tare da mata kashedin wani Abu ya k'ara faruwa ba ita ba k'ara rik'e waya cikin farinciki ta ce Insha Allah ba abunda zai k'ara faruwa yana bata tana bud'ewa what's app ta hau taga voice din mutanenta da kawayenta da suka had'u saboda twins Sai voice suke mata lafiya D'aya Bayan d'aya ta shiga ta dinga maida musu da alhmdllh "Rahama ce ta kirata " murmushi Aira tayi ta d'auka ta ce "My momcy ykk" Cikin murna Rahama ta ce "Haba daughter saikuma muka jiki shiru wlh karkiga yanda na damu kusan wata nawa anriga an saba Saina jiki shiru ga wayarki bata shiga kullum saina kira yanzuma ina gwadawa Naji ta shiga " Murmushi Aira tayi ta ce "Sorry my mom.wlh matsala aka samu ranar nan da na kiraku d'innan wlh kwana a gaba ya tayar da su twins masu shan jini suka kamasu To dadynsune da ya gano ina Dorasu ya b'ata account din sannan ya amshe wayar sai yanzu ya maidomun harma na hakura banyi zatoba nima nayi kewarki wlh" Cikin damuwa Rahama ta ce "Subhanallahi ai bamusan abunda ke faruwa ba Allah ubangiji ya tsare gaba ya k'are gsky gwara da aka lalata account din mutane ba gsky ina twins nasan yanzu an girma" murmushi Aira tayi ta ce Bari na had'aki dasu daga Inda take ta kwala musu kira da gudu Suka rigo Nihal ta ce "Cutie what happend? zaunar dasu tayi ta ce " ga Auntynku zaku gaisa"sannan ta fara karawa Nihal wayar ta ce "good Afternoon Aunty yakeke" Dariya Rahama tayi ta ce "Lafiya qalau my namesake ashe kunyi baki to ygd ya mom " tana lafiya ta fad'a tana shirin kada wa Aira waya ta maza ta amshe tana Harararta Dan ita ba Arman bace da zasu mata asara Naila ta karawa a kunne wayar na hannunta Bayan sun gama gaisawa ta ce oya to ku tafi Aje ayi wasa "ta cikin wayar Rahama ta ce" kai ji yanda yaran nan sukayi baki gsky anjima ba a hadu ba wlh k'ilama yanzu har anyi musu k'ani ko"Dariya Aira tayi ta ce "Zadai ayi musu gobe fa zamu shigo k'asar" Cikin farinciki Rahama ta ce "da gaske sis kice muna da manyan baki ina zaku sauka " Kano ina sa ran insha Allah"Allah ya kaimu insha Allah Ko bakizoba ni zanzo naga my twins har yanzu dai banga pic dinkiba bare inmun hadu mu gane juna"murmushi Aira tayi tare da tura mata pic d'inta me kyau ta what's app ta ce "Yau dai kinganni momcy" Sosai Rahama tayi mamakin yarinya ce ma Airar ashe "voice tayo "ta ce " wow daughter Ammafa kin hadu ba k'arya wlh dole twins suyo kyau dukda naga ba kamarki suke ba Ammafa bamai cewa kina da Aure wlh bare har ance kina da su Naila"murmushi kawai Aira ta yi ta tura mata da stiker Dariya Itama tambayarta tayi hotonta ta turo mata soi sannan taganta itama kyakyawa ce Masha Allah ga wayewa zatayi irin 21 years "voice Aira ta tura mata ta ce " Kaiii ashe dai momcyn tawa ba wasa Wajen kyau masha Allah insha Allah gobe damun Iso zankiraki da layin 9ja "Kawarta Jannat ta kira dake Abuja Itama sosai ta ja jinta shirun da tayi kamar yanda tayima Rahama bayani haka tayimata ita daman suna da hotunan juna Dan ita kadai Aira ta yarda take da hotonta itama Dan ta yarda da nutsuwartane Itama budurwace wayayya Nanko ta shiga murna Akan Aira idan tazo Itama zatazo ta ganta da twins amma ce da tayi mata message a what's app duk na jajanta ne take tura mata voice tayi cikin. Make murya tayi mata bayanin abunda ke faruwa " Sosai Amma ta damu kiranta a waya tayi Bayan sun gaisa ta ce "wayyo Allah ya k'ara kiyaye gaba wlh karkiga yanda na damu sosai wata da watanni ba a tare" Murmushi Aira tayi ta ce "Karki damu sis insha Allah kinkusa ganin twins dinki kusa dake" cike da zak'uwa amma ta ce "da gaske sis " Dariya Aira tayi ta ce "Kedai kisa ido kawai zamuyi surprise d'inki amma badan ta yarda ba Dan a tunaninta zolayanta ne take.
Washegari Aiport na gano su Aira sosai tayi kyau cikin pink d'in Abaya Mai mugun tsada Fuskarnan tata ba komai sai asalin kyan da Allah yayi mata Ga cikinta d'aya turo saiya Kara yi mata kyauma hand bag rataye a hannunta Arman ke rik'e da k'aramar akwatinsu yana ja Twins ko wasa kawai suke suna tsalle A haka har aka fara kiraye kirayen suna Suka shishiga ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga 9ja Wanda Aira jinta take cikin Farinciki Twins ko a jirgima wasansu kawai suke suna harkar gabansu wasa suka dingayi da yara Wanda har maman wata noor suka k'ulla kawance da Aira saboda jinin yaransu da yazo d'aya harsukayi musayar number itama y'ar Abuja ce karfe d'aya tayi musu a 9ja kasancewar asubanci sukayo koda suka fito daga jirgin Aira jinta take cikin farinciki marar musaltuwa sai kuma fargabarta na had'uwa da Abba sosai gabanta ya fad'i Kasancewar a Lagos Suka fara sauka hakan yasa saida suka hau wani jirgin tukwana suka isa kano around 3 suna kano Sosai gaban Aira ga tsananta fad'uwa Hakanan ta fusge driver Arman ya kira ya kawo masa mota twins Sai tsalle suke suna murna zasuga Mummy "gaban Aira na tsananta fad'uwa ta kalli Arman ta ce " yaya ina muka nufa"gida cutie muje ki huta tukwana"Kasa tayi da kanta "Kai tsaye gidan Arman dake GRA suka nufa Bayan sunyi wanka sun huta Twins ne suka damu Arman da cewa " Hero ka kaimu muga mummy"Lallashinsu yayi ya ce "Sorry my twins ku bari sai gobe " Tuburewa sukayi hakan yasa ya kira Mummy wayarta kashe batamason zuwansu ba kallonsu yayi ya ce "Kunga wayarta a kashe ku kwanta ku huta Wanda ya Riga bacci shi zan fara kaiwa Wajenta " cikin saurin suka Haye kan sopa Tare da rumtse ido wai bacci yazo"Dariya Aira tayi kasa_kasa ta ce "Ai gwara da kayi mana maganinsu Dandananko baccin gaske ya kwashesu a lokacin ana isha I Aira salla tayi Bayan ta ciccibi twins ta kaisu bedroom Gado ta kwantar dasu Bayan tayi musu addua itama ta kwanta dandanan baccin gajiya ya kwashesu Arman koda ya dawo ya samesu Gado daya addua yayi musu tare da wucewa d'ayan bedroom d'in ya kwana.
Washegari wajen 12 na rana Aira ta shirya ita da twins d'inta sosai tayi musu gayu cikin y'an kanti d'insu Riga da wando da suka matse red ba hula kansu sai Gashin kansu da akayi parking sai shek'i yake Itama shiryawa tayi cikin doguwar riga ta d'ora hijab d'inta mai hannu har k'asa green sosai hijab din tayi mata kyau A harabar gidan suka tsaya Arman ya fito da mota Suka shiga Kallonta yayi ya ce " ina muka nufa mom twins"gabanta na fad'uwa ta ce "Mu fara zuwa gidan Aunty Aysha hero" To ya fad'a tare da kama hanyar gidan Aysha Dan bai manta ba Suna isa suka fiffito da twins Kallonta yayi ya ce "zanshiga gari around 3 zanzo na daukemu" gyada mishi kai tayi a sanyaye tare da kama twins dake shirin nufa wani wajen knoking gidan ta fara minti Ukku taga anbude kallon mamaki Aysha ta dinga binta dashi ji take kamar mafarki itama Airar Kallon y'ar uwar tata ta tsayayi wara idanu Aysha tayi ta ce "Sis kece" Murmushi Aira tayi ta ce "Nice sis" Rungume juna sukayi a tare saikuma suka sanya kuka Aysha ta ce "Aira ina kika tafi kika barmu da kewa tsawon shekara Ukku da rabi" kasa magana Aira tayi sai kuka da take janye jikinta Aysha tayi tare da Kallon cikin jikin Aira wara idanu tayi ta ce "Sis ciki" Bata rufe bakinta ba taga twins Suna kallonsu"janyosu tayi tana mamaki taa ce "tare kuke sis" gyada mata kai tayi "D'aukar d'aya Aysha tayi tare da kama hannun Naila tace taho mu shiga ciki labarin

45 / 54