NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   20 / 54

57K to 60K   out of 160.7K words

ba gashi munason junanmu ba harda zuri'a ke akanme bazakiyi hakuri ba baki da tawakkali kenan kuma Arman din da kika likewa ai gwara da Abba zai miki Auren Dan ubanki daman hak'e nake dake harkuje Kuyi birthday a idon duniya kuna Rungume_Rungume ke inkina da zuciya me zakiyi da Arman yaronda ubanshi ya tsaya takara da ubanki a gaban idonki wani irin wulakancin da cin mutunci ba ayiwa Abba ba dukda yana Dan uwanshi ya take shine ke Dan Rashin zuciya kika likewa d'anshi to ai yanzu ta k'are saikiyi hakuri ki tsaya a gyaraki ko kinje kiyi daraja gidan mijin naki"Aira ji tayi kamar ta shak'e Aunty Maryam tsaki taja da batasan tayi ba cikin kuka ta ce " Aike saurayine aka Aura miki Nifa sa'an ubana ne za a auramun ko kece ai nasan saikin damu Kuma yaya Arman da kike magana Nidashi mutu ka raba insha Allahu babu Wanda ya isa ya rabamu kuma ni shi nakeso sannan in kinga anyi Auren nan Saidai in baya numfashi ke daman Aunty Maryam ai nasan ba k'auna ta kike ba "Rik'e hab'a Aunty Maryam tayi ta ce " Eyye lallai Aira Tabbas na yarda yanda aka ban labarinki kin wuce nan Harni zaki d'aga baki kiyiwa Rashin kunya tare da tsaki to wlh ni ba Ummy da su Aysha bane sai in tsiinkeki da Mari ko inyi maki dukan tsiya "Aysha ce ta shigo ta ce " Haba Haba Aunty wai meye haka ki bartama da abunda ke damunta kinzo kin hauta da wani fad'an "ai daman ke da ita halinku d'aya" inji Aunty Maryam Rungume Aira Aysha tayi ta fara Lallashinta tacewa Aunty Maryam "eh munji mudai ki tashi ki tafi" Lallashi sosai Aysha ta shiga yiwa Aira harta samu tayi shiru wajen magriba Aira ta fito palour ganin kowa na harkar gabanshi masu salla nayi daga ita sai doguwar Riga da kallabin rigar hanyar fita tayi ba Wanda yayi mata magana Dan a tunaninsu alwala zatayo a tap din waje tana fitowa taga mai gadi na alwala hamdala tayi tare da basarwa taje tap ta fara alwala Tana ganin fitar Baba mai gadi tayi Sauri ta bar wajen Allah ya taimaketa farfajiyar gidan ba kowa a guje ta Ruga ta fice daga gidan gudu ta shigayi sosai kamar wacce aka biyo saida tayi nisa sosai tana hak'i ta kira Arman yana d'auka tace Yaya na gudo kayi Sauri ina daidai inda ka d'aukeni rannan kayi Sauri"Ai Arman na shirin shiga Salla fasawa yayi a sukwane ya d'auko mota ya nufi unguwar su Aira yana zuwa ya sameta a wajen sai waige waige take tana ganinshi aguje ta shige Motar Tana Shiga Arman ya ja motar a guje Dukansu Ajiyar zuciya kawai suke saukewa Kallonshi Aira tayi ta ce "Yanzu ina zamu yaya " shiru yayi itama shirun tayi Dan ta lura da yanayinshi sai huci yake a wani katafaran hotel yayi parking Bayan ya biya ya sai mata hijab tasa tare suka fito d'aki ya kama musu mai kyau da komai room45 itadai Aira Ajiyar zuciya kawai take tunda ta samu ta kub'utowa daga gida ai alhmdllh suna shiga d'akin ya Umartar Aira da tayi salla Shima anan sukayi Sallar har isha'i itadai Aira ta rakube kamar munafuka sai yanzu takejin tsoron idan gida aka nemeta aka rasa Danna belt din d'akin akai Arman ya lek'a ya amso plate din abinci d'aya gaban Aira ta Aje ya ce "oya ci" d'agowa tayi cikin hawaye ta ce "Yaya bazan iyaci ba" d'aure fuska yayi ya ce "ji yanda kika rame kamar bakeba d'aga bakin na baki" Arman shiya dinga bawa Aira abinci sosai kuma taci taji dad'inshi har saida ta k'oshi Kallonshi tayi ta ce "Yaya kai kaci mana kaimafa karkaga yanda ka rame" girgiza mata kai yayi ya ce "Bazan iyaciba " Ruwa Tasha a fridge din d'akin tare da zama bakin gadon ta cire hijab din jikinta Dan ta takura mata Kallonshi tayi tace "Yaya me yasa ka kawoni nan wani zai iya ganinmu yayi mana wata fassarar ko a zargemu daman gidan Mummy ka kaini" cike da yanayin b'acin rai Arman yace "Daman ai bamuyi ba suke zarginmu suke cewa munyi dukdai ba dalilin hakan bane yasa har zai miki Aure shiyasa na kawoki nan muyi abunda da bamuyi ba wlh bantaba sonki da wani Abu na jikinkikiba Aira Amma har Gobe kallon d'an iska mahaifinki yakemun why tunda nake bantab'a zina ba na tsaneta na tsani masu aikatata amma mahaifinki da laifin wannan yake dangantamu To Yau abun yazo karshe yau d'innan zan rabaki da virginity d'inki sai Inga ta yanda zasuyi miki Auren Tunda su basu tunanin halin da zamu shiga nan gaba ya k'arasa fad'a yana cire kayan jikinshi ya rage Dagashi sai singlet da gajeran wando sosai Aira ta tsorata da maganganun Arman sosai tashiga tashin hankali ja da baya ta fara tare da girgiza mai kai tana hawaye shiko tuni ya hayo gadon tare da chafketa yabi ya hau kanta ya danne sosai Aira ta shiga tashin hankali marar musaltuwa cikin hawaye ta ce " yaya karkamun hak.....bata k'arasa maganarba ya had'e bakinsu waje d'aya tare da Fara musu wata irin tsotsa kamar mayunwacin zaki a zafafe yake Aira ko tuni numfashinta taji ya fara d'aukewa fusfusgewa ta fara iya karfinta amma Arman ko motsi baiba daga kanta.................✍🏿


*NI DA YAYA ARMAN it's not free it's for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*
*ki biya 200 d’inki kachal ki karanta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa duk Mai buk’atar saya ya tuntub’e ni kan number wayata 07026166536*


*_Miss Hajo ce_*
[6/21, 19:23] Hajo hajo: 🅿️.........*55&56*





... .....Tashin hankalin da Aira ta shiga yafi Wanda ta shiga lokacin da Aka ce za ayi Auren ta da Alh yusuf Arman ko tuni ya fara fita daga hankalinshi Aira batasan lokacin da ta sume ba tsabar firgici Arman yad'au minti ashirin yana kissing d'inta jinta shiru ta daina hafre hafre ya dawo dashi cikin nutsuwarshi tashi yayi a matuk'ar firgice Rik'eta yayi yaga ta koma "Innalillahi meyake shirin faruwa da nine me nake shirin aikatawa " Arman ya fad'a yana kallon jikinshi cikin Sauri ya mayar da manyan kayan jikinshi tare da dauko ruwa a fridge a d'imauce ya shiga watsa mata Ajiyar zuciya yaji ta sauke Shima Ajiyar zuciyar ya sauke Aira na bud'e idonta Maganganun Arman da abunda ya mata suka shiga dawo mata tashi tayi a matuk'ar firgice tare da rugawa tayi hanyar fita girgiza k'ofar ta farayi taji a kulle Kuka kawai take Arman ko binta yayi ya ce 'please cutie ki saurareni"d'aga mishi hannu tayi ta ce "Babu abunda zaka Cemun yaya ka cuceni ka zalince ni banyi tunanin zaka yimun hakaba kaikad'aine na yarda dashi na bashi amana ashe kaimad'in zaka iya cin amana ta yaya me nayi maka tukuicin soyayyar da nake maka da haka zaka sakamun ashe Ta k'arasa fad'a tana durk'ushewa a wajen tare da sakin kukan takaici girgiza mata kai Arman ya fara tuni idanunshi sun chuko da k'walla duk'ursawa yayi gabanta ya ce " Kiyi Hakuri ki yafemun cutie shed'an ne yaso yayi galaba a kaina nayi tunanin wannan ce kurin mafitarmu ta k'arshe saida nadawo hayyacina na gane ba haka bane Dan Allah kiyi hakuri nasan ni mai laifi ne a gareki amma kiyi hakuri ki yafemun please "Cikin kuka da jaraba Aira ta ce " shed'an ko son zuciya Yaya kaban mamaki nayi tunanin kai mai tsareni da tsare mutunci na ne a ko ina amma da kanka zaka lalatamun rayuwa nayi danasanin biye maka da nayi yaya ka bud'e mun k'ofa na fita tunda burinka ya cika ka rabani da mutunci na ka bud'e mun nace "Wlh tallahi babu abunda nayi miki cutie na rantse da girman Allah banyi maki komai ba kiyi hakuri mu fahimci Juna ya fad'a yana ruko hannunta ta fusge hannun tayi ta ce " karka sake tab’ani ka bud'emun kofa nace ba abunda zaka Cemun na tsaneka na tsaneka yaya bansan ganinka I hate you "ta fad'a tana rumtse ido " Ai Arman jin Kalmar yayi kamar an d'iga mishi Darmar wuta "na tsaneka Na tsaneka" Ai baisan lokacin da ya fashe da wani matsanancin kuka ba da tunda uwar da ta haifai bai tab'ayi irinshi ba ita kanta Aira sosai Cike da mamaki take Kallonshi shiru tayi tana sauraren kukan shi sosai Arman yake kuka kamar Wanda aka cewa uwarshi ta mutu Mik'ewa yayi tare da d'auko wuk'a zai chakawa kanshi Aira ta maza a matuk'ar rud'e ta rikeshi tare da rik'e wukar ta ce "Meye haka yaya kashe kanka kake shirin yi kana hauka ne? cikin b'acin rai ya ce "ki saki ki rabu dani na kashe kaina rayuwata bata da amfani Aira tunda kema baki sona bani da wani amfani a duniya ki bari na mutu itace kawai tafi chanchanta dani meyasa bazaki fahimceniba Aira Duka abunda nayi na yine a saboda son da nake maki wlh banyi da wata manufa ba Kuma nayi nadamar abunda nayi shirinyi Meyasa bazaki fahimceniba kince baki sona kin tsaneni Aira bakin da ya furta mun so yau shine ya furtamun kalmar k'i da kanki yau Kika furtamun Kalmar tsana" kuka Aira ta fashe dashi ta ce "I love you yaya bazan tab'a daina sonka ba Ina sonka har yau har Gobe har jibi har abadan abada bazan tab'a iya daina sonka ba"Ai Arman baisan sanda wuk'ar ta sulale a hannunshi ba Ganin haka ya sanya Aira fad'awa jikinshi tare da fashewa da kuka ta ce "please yaya karka k'ara attempting kashe kanka Nima mutuwar zanyi ka daina banso ina sonka sosai yaya Amma me yasa zakace saita haka ne kawai mafita akwai mafita da yawa zamu iya guduwa muje a d'aura mana Aure a wani wajen " Daddab'a bayanta Arman ya fara ya ce "Kainane ya kulle Aira Bansan wani irin so ne nake maki ba har shed'an yaso galaba a kaina kiyi hakuri ki yafemun na mance da wannan mafitar ta mu gudu I love you so much Aira please karki gujeni duk rintsi duk wuya " Lafewa jikinshi Aira tana sauke ajiyar zuciya Dan sai yanzu ta fara dawowa daidai sosai Arman ya tsoratata a hankali ta ce "Nima karka gujeni duk rintsi mu rik'e alk'awarin juna yaya da gaske Bakayimun komai ba " Gani kawai tayi ya tashi tare da d'auko Quran hizif sittin dake gefen Gado ya rik'e ya ce "na rantse da Quran d'innan Mai girma babu abunda nayi maki" Saurin tashi Aira tayi tare da amshe Quran din ta ce "Ni bance ka Rantsemun ba na yarda " Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "kin hakura kenan" gyad'a mashi kai tayi tana zumburo baki"Murmushi yayi ya ce "Thnks you my cutie zaunawa Aira tayi tare da Yin tagumi" sai nakega kamar har yanzu baki hakura ba cutie please Dan Allah kiyi hakuri"murmushi ta kirkira ta ce "Na hakura yaya kawai tunanin mafitar da zamu samu nan gaba nake" Ajiyar zuciya ya sauke tare da zaunawa gefenta ya ce "mafita ta k'arshe itace kawai gobe muyi safko mu gudu" Kallonshi tayi ta ce "ba matsala kuma yaya" Ba wata matsala insha Allahu ita ce kawai damarmu ta k'arshe Ko zaki yarda Kinaji kina gani a aura miki wani banzan tsoho"girgiza kai Aira tayi tana hawaye ta ce "Alllah ya kaimu goben Yaya Amma please mu raba d'aki " murmushi yayi ya ce "to Prince's Angama ina zuwa " yana fita Aira ta sauke ajiyar zuciya tana hamdalar da Arman bai mata komai ba baijima ba ya dawo yace na kama wani d'akin ke ki kwanta anan kinji kiyi bacci sosai Dan Allah "murmushi tayi ta ce " Insha Allahu Yaya kaima kayi bacci"Murmushi yayi cike da so da k'auna ya ce "Good night" Arman tunda ya shiga d'akin inbanda salla ba abunda yake Airako bacci bai d'auketa ba sai wajen biyu da asuba tana tashi tayi sallah ta koma bacci saboda tsananin ciwo da kanta ke mata Arman ko Shima saida yayi Sallar asuba bacci ya daukeshi Bayan ya leko Aira yaga itama baccin take bacci mai mugun nauyi Duka ya d'aukesu kamar Wanda suka sha wani Abu saboda sunjima daman basu samu bacci ba.
B'angaren gidan su Aira sosai suka shiga tashin hankali da suka lura ta gudu musamman Mamy Daman tasan hakan zai faru sosai Tasha kuka a d'aki Mama Halima ko cikin tashin hankali taje ta samu Abba ta fad'a mashi Aira fa ta gudu a lokacin goman dare sosai ran Abba ya b'aci cike da mamaki ya ce "What Guduwa garinyaya ta gudu Bayan nasa matakan tsaro a kanta aikinme me gadin yake " To wlh yaya ta gudu batanan "cikin b'acin rai Abba ya fito wajen mai gadi ya nufa ya dinga surfamai masifa akan garinya ya barta ta fita da rantsuwarshi Baba mai gadi yace "wlh nidai banga fitar ta ba Saidai idan lokacin da naje salla ta gudu Dan daman na hangota a pampo tana alwala bankawo komai a kaina ba saboda naga alwallace take shiyasama harna fita amma wlh banga fitartaba Alhaji kamun rai karka koreni a aikin nan dashi kawai na dogara " Cikin b'acin rai Abba ya nufi parking space ya d'auko mota ganin haka ya sanya Baba mai gadi rugawa yaje ya bud'e mai Abba kai tsaye police station ya nufa ya basu mak'udan kud'i akan duk Inda Aira take Su shiga su nemota tare da tura musu hotonta a wayarshi Tun Daren y'an sanda suka fara fafutukar nemanta duk sun turawa abokan aikinsu hotunanta akan duk Inda suka ganta su sanar Abba ko ranar Kad'an Ya hana jininshi ya hau sosai Aira ta k'ara chusamai bak'inciki Daren Ranar cikin gidansu Babu Wanda ya rintsa Musamman Mamy tsoronta kawai karta fad'a mugun hannu Bayan Sallar asuba Mama Halima da yake daki daya suka kwana da mamy wani tunani ne ya fad'o mata Mummyn Arman ta kira Bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah Arman ya kwana gida kuwa" Sai sannan hankalin Mummy ya kawo ta ce "a a bai kwana gida ba rabo na dashi tun shekaranjiya lafiya kuwa Halima" da sauki dai za ace Aira ce ta gudu tun jiya da dare nasan duk Inda take suna Tare da Arman Dan Allah kid'an bincika mana nayita kiranshi Wayarshi kashe "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Mummy ta fad'a tace " Amma banji dadiba Gaskiya irin haka nake gujewa yasa tun farko naso abar yaran nan su Auri junansu tunda suna so Amma taurin hali na iyayensu sun kafe bari nayi Sauri na tura guest house d'inshi dake gra duk sanda bai gida to yana Chan nasan kila suna Chan"Wlhko Aunty kinga mamanta nan ma duk hankali tashe itama Ba irin gwagwarmayar da bata sha ba akan abun nan yafi karfinta"Ajiyar zuciya Mummy ta sauke ta ce "Allah shige mana gaba bani Rahamar mu gaisa" mik'awa mamy wayar tayi ta amsa Bayan sun gaisa da Mummy suka jajintawa juna abunda ya faru Mummy ta ce "To Allah ya kawo mafita bari na maza na tura can din zakujini " Ameen nagode "Mamy ta fad'a ba ayi minti Talatin ba Mummy ta kirasu hankali tashe ta ce " Wlh na sanya Duka anbincike cikin Chan din basanan mai gadin yace rabonshi da gidan tun Jiya da magriba "Mama Halima ta ce " ba kokontoma suna tare daidai lokacin ta gudu itama "Sosai Mummy suka shiga damuwa shawara mummy ta bada akan a sanya jami'an tsaro suje hotel_hotel d'in garin nan da kuma y’an sandan bakin hanya kila a dace Tsoronsu Kardai Aje guduwa sukayi hankali tashe Mama Halima taje ta fad'awa Abba tace Suna tare da Arman A sanya jami'an tsaro su tsaya bakin duk hotel d'in garin nan shi daman Abba baiyi mamaki ba Daman Chan yasan shi zaisa ta gudu cikin k'ank'anin lokaci Abba ya kira jami'an tsaro aiko ba b'ata lokaci Duka suka bazu duk hotel d'in da suka sani sannan Abba ya sa Mama Halima ta tura musu hoton Arman.
Aira itace bata tashi ba sai karfe d'aya na rana sosai taji ta wartsake bayan tayi wanka Salla tayi kayan jikinta ta mayar zaunawa tayi bakin Gado tayi tagumi Ta na zaune taji shigowar Arman da harta tsorata tana ganin shine Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce " ina yini Yaya "Murmushi yayi ya ce " Alhmdllh cutie yau munsha bacci ko"murmushi tayi ta ce "Wlhko banzaci munkai haka ba" Ai nima banjima da tashi ba bari naje na Samo maki kayan da zaki sauya kafin mu tafi na so ace sauko mukayi "rik'e hannunshi tayi ta ce " Yaya zan mayar da na jikina plx kawai mu tafi banson a samu matsala nasan duk Inda y'an gidanmu suke nemana ake "a a ki bari na samo maki wasu kayan cutie babu wata matsalar da za a samu tunda kina nan ba tare zamu ba Kuma ma mota ta tinted ce bamai ganinmu daga Chan saina taho maki da abinci nasan yunwa kikeji ba Dan Aira ta so ba ta bar Arman ya tafi Arman yana fitowa daga farfajiyar hotel d'in kai tsaye motarshi ya nufa ya tada Y'an sanda ko suna ganinshi suka ganeshi Dan tunda aka turo musu hoton daman sunsanshi d'an Excellency ne Abba suka kira sukace " ranka ya dad'e munyi nasarar ganin shi Mujahid d'in yanzu a harabar Grand central hotel amma shi kad'ai muka gani yanzu haka ya tada mota ya bar hotel din amma ga alamu kamar bazaiyi nisa ba "" Abba tashi yayi daga zaunen da yake ya ce "Karku saki ya gudu Kuyi yanda kukayi kuka tsayar dashi suna Tare da ita Tabbas gani nan zuwa " to ranka ya dad'e kayi Sauri Dan Gaskiya bamu da power Kamashi D'an governor guda zamu iya ta aikinmu amma kai kazo "Suna cikin wayar suka ga dawowar Arman " ranka ya dad'e gama shinan ya dawo ka yo Sauri"Cikin hanzari Abba ya d'auko mota Dan zuwa Inda suke ya ce "kusan duk yanda zakuyi ku

20 / 54