Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
me yasa tun lokacin da nace inasonki kika k'i amincemun meya kaiki Auren sa an babanki Aira dan bakisan kalar son da nake maki ba....cike da masifa daddy ya ce "Banson iskanci Sadiq na k'arajin makamanciyar Kalmar nan a bakin ka a gidan nan wlh ranku zaiyi mugun b'aci Nakarajin ka k'ara danganta Kalmar so mata ta zakusha mamakin abunda zan muku " Aira kamar wacce kwai ya fashewa haka ta tashi al'ajabi duk ya gama cika mata kai kenan mahaifin Sadiq ne Aka auramata chabdi A zuciyarta ta ce "Allah yasa daman banyi wata soyayya dashi ba Chan ta matse musu wahalallu wucewa bedroom d'inta tayi batare da ta kuma waiwayar suba harta b'acewa Sadiq gani yana kallonta cike da bala I Daddy Ya ce " Na rantse da Allah Na kusa korarku kaida Mubarak daga gida na ku duk iskancinku akan matata ma ya k'are kaida nake maka kallon mutumin kirki shine kaima zaka b'ullo da wani sabon iskancine to wlh ko kallo karna sake ganin Wanda ya kuma kallonta tunda ku mutanen banza ne"Sakato saude tayi tana Kallonshi ta ce "Ikon Allah to saika kori Y'ay'anka saboda mace Sannu salamamme to wlh karka k'ara aibantamun y'ay'a d'iyan kirki y'an albarka Chan kuje ku karata da amaryarka amma kar a sakamun y'ay'a"a bakin duniya" Tsaki Daddy yaja tare da mik'ewa "ya ce aina fad'a muku dai kuci gaba kuga hukuncin da zan yanke" Yabar palourn cikin fushi Sadeq ko ya jima yana mamakin wannan al'amarin har saida ya goge hawaye dan ba karamun so yakeyiwa aira ba abunda aka shirya mashi dinma dak'yal mama ta lallabashi yaci danshi wannan zuwan nashi bai mashi dad'i ba Aira ko Tana komawa salla tayi ana kiran isha I ma tayi tabi ta haye Gado Dan daman baccin gajiya ya kwasheta washegari itace bata tashi ba sai Takwas Sosai tayi mamakin makara Sallar asuba da tayi abunda bata saba ba Cikin gaggawa Tai salla tayi wanka ta fito kenan Daga wanka jikinta daure da towel ta tsaya jikin mirror tana busar da gashin kanta Daddy Ya shigo tunda ya shigo ya kafeta da idanu bako k'iftawa har wani Had'iye yau yake Aira na juyowa sukayi ido hud'u dashi Ai batasan sanda ta fasa uban k'ara ba tare da durk'ushewa a wajen Matsowa Alh Yusuf yayi ya ce "Subhanallahi meke faruwane beauty ko wani abun ne ya sameki" Kuka Aira ta fashe ta ce "Dan Allah Daddy ka fita" Sakato yayi yana kallonta ganin yana Matsowa Kamar zai Rungumeta ya sanya Aira kwasar k'afarta a guje ta koma toilet tare da rufewa ta sanya key Huci kawai take tare da dafe k'irji ta ce " nashiga ukkuna ni Aira " Alhaji Yusuf ko girgiza kai yayi tare da barin d'akin dukda ba haka yasoba Dan a yanda yaga Aira sosai ta rud'ar dashi yaso ace ko rage zafi ne yayi Aira tafi minti Talatin a toilet saida taga dai da gaske yabar d'akin tukwana ta lek'o tana ganin bainan ta sauke ajiyar zuciya Tare da fitowa ta maza ta je ta rufe d'akin sai huci take kamar wacce tayi wani aiki Cikin Sauri ta shirya daman tunda tazo gidan ba make up take ba ko hoda bata shafawa Turare kawai ta fesa sannan ta yafa beil din doguwar rigar a sanda ta fito daga d'akinta Takoyi sa a laila kad'ai ta tarar a palour zaune a kan sopa earpiece mak'ale a kunnenta tana bin wak'a Hartaje tayi break fast ta dawo palourn tana zaune Inda ta barta zaunawa Aira tayi tana son ta tambayi Laila ta ara mata wayarta ta kira Mamy tana tsoro tadβau minti ashirin zaune tana sak'e sak'en dak'yal dai ta tattaro jarumta ta ce "Laila Dan Allah wani taimako zakimun" Kamar bazatayi magana ba Saikuma ta cire earpiece d'in ta ce "Ina jinki" Kamar mai shirinyi kuka Aira ta ce "Dan Allah wayarki nake so ki aramun zan d'anyi kira minti biyu inba damuwa" Kallonta Laila tayi sama da k'asa kamar bazata bataba saikuma ta Mik'a mata ta ce gashi"Cike da farinciki Aira ta ce "Nagode sis " Tab'e baki Laila tayi tana wani girgiza k'afa "Aira na amsar wayar Number Arman ta fara dialing Tajita kashe sosai taji wasu hawaye sun zubo mata Goge number tayi tayi dialing number Mamy Tare da karawa a kunnenta " Ringing Biyu Taji an d'aga Daga bangaren Mamy ta ce "Assalamu alaikum" Wani sanyi Aira taji a ranta jin muryar mahaifiyar tata tsawon wata guda kenan bataji muryarta ba tuni hawaye sun wanke mata fuska tama kasa magana "Mamy ce ta k'ara cewa Hello Yadai an kira anyi shiru" Cikin shashekar kuka Aira ta ce "Mamy...Ai Mamy Mikewa tsaye tayi jin muryar y'artata cike da farinciki ta ce " Aira ta kece kuwa "Cikin Kuka Aira ta ce " Nice Mamy "kina lafiya kuwa Naji muryarki haka Aira ko bakyajin dad'in zaman" Kuka Aira fa fashe dashi kamar wacce akayiwa mutuwa "Sosai hankalin Mamy ya tashi cikin damuwa ta ce " Karki k'ara tayarmun da hankali please daughter me yake damunki kukan me kike maimakon ki kwantarmun da hankali Aira ko so kike jini na ya hau"cikin shashekar kuka Aira ta ce "Mamy Please kizo ki tafi dani Dan Allah Mamy nasan ke kina sona" Dafe goshinta Mamy tayi ta ce "To Naji amma fad'amun ba abunda ya faru dake are you okay dear ko wani abun ake maki a gidan" Girgiza kai Aira tayi kamar tana gabanta ta ce "a a a Mamy nidai gida nakeso bazan iya zama a nan ba Dan Allah Mamy kizo ki tafi dani"ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka " Itama mamyn hawaye take amma Dan son kwantarwa da y'artata hankali ta ce "Ki kwantar da hankalinki daughter Allah na tare damu ki dage da addu'a kinji sannan idan kinsamu waya ki dinga kirana Inajin muryarki ko Naji sauk'i damuwar dake tare dani Kidaina tayarmun da hankali ko so kike hawan jini ya kama mamyn naki ta mutu" Cikin Sauri Aira ta fara Goge hawayenta tare da girgiza kai ta ce "A a a Mamy Nadaina banason komai ya sameki " To kidaina kuka kinji ki dinga addua itace takobin mumini"To Mamy bazan sakeba Mamy ina Haidar da Aunty Aysha Da Amer nasan yanzu Amer ya manta dani"Haidar yana school Amer gashinan yana wasa Waneshi wane mancewa da Babbar yaya yana nan yana kewarki Aysha Da kowa Duk suna lafiya""Murmushi Aira tayi tanajin wani sanyi Cikin zuciyarta jin muryar mahaifiyartata a hankali ta ce "Ki gaishemun da su Mamy sai anjima karna cinye mata credit"" zasuji wayar wacece kika samu"cikin k'asa da murya Aira ta ce "ta y'arshice" Okay to sai Anjima ki dinga kirana kinji Allah maki albarka "Ameen Mamy nagode I miss you" Miss you too daughter ki dinga kulamun da kanki kinji"murmushin da Aira tajima batayiba tayi ta ce "Nima ki kulamun da kanki kinji Mamy na" Tukwana sukayi Bankwana Laila duk tana jinsu gwanin burgewa take kallon Aira Aira na gama wayar murmushi tayi mata ta ce "Gashi sis nagode" Itama murmushin Laila ta sakar mata ta ce "DM Dear Amma na tambayeki mana Dan Allah" Sosai Aira tayi mamakin yanda Laila yau tayi mata murmushi cike da kulawa ta ce "Inajinki" Dan Allah Ko zaki d'anban labari sai a kwanannan na lura da kamar bakya son Daddy Kuma Naji kina waya nasan mamankice akan tazo ta tafi dake""Murmushin takaici Aira tayi tare da Goge hawayenta Ta ce "Banason Tuno da labarin da ya wuce kamar zan k'ara fama raunin da yakasa warkewane a cikin zuciyata " Dan batajin zata fad'awa wani cikin gidan sirrinta Dan bata gama sakewa dasu ba"kad'a kai kawai Laila tayi ta ce "Shikenan badamuwa" Nagode Aira ta fad'a tare da tashi"ta koma bedroom d'inta Aira na barin wajen Laila d'akin mamanta taje ta ce "Mama wai kin lura da abunda na lura kuwa Amaryar Daddy fa kamar batason Daddy sainakega kamar ma ba da son Ranta ba akai auren nan ta bata labarin maganar da taji Aira tayi da Mamanta" Hajiya saude ce ta ce "Nima na lura da hakan koma dai meye idan tayi tsami Maji.....Arman tundaga lokacin nan yaci gaba da samun sauki amma har yanzu tunanin Aira na nan mak'ale a cikin zuciyarshi tausayin mahaifiyarshi ya sanyashi fara Rage damuwa a ranshi ana samun cigaba sosai Dan yanzu har yana Mikewa yayi sallah dukda a zaune yakeyinta Magana ce dai ba Sosai yakeyiba a zaman arman asibiti Daddy sun kashe kud'i sun haura 30 million's sati biyu da Farkawar Arman aka Sallamesu dan jikin nashi Alhmdllh Bayan ambasu magunguna ankuma fad'a musu dokokin da zasubi Dan kula dashi Arman jinshi yake cikin farinciki Dan tunda ya farka ya gaji da zaman Asibitin ga kuma farincikinshi na komawa k'asar da sahibarshi take Dan yayiwa kanshi alk'awarin ko birnin sin Aira take saiya nemo ta.........Alh Yusuf sosai ya fara gajiya da Abubuwan da Aira take mashi duk yanda yaso ko d'an rage zafi ne yayi da ita amma ta kafe tak'i yarda ko yatsanta ya rik'e yaudai ya gaji wata kusan biyu da Aure amma Ba abunda ya shiga tsakaninsu da Ita hakan yasa yadβau D'aurarriyar aniyar kota arziki kota tsiya saiya Nemi hakkinshi.....da misalin Sha d'aya na dare Aira harta kwanta bacci Dan yau a gajiye take ta mantama ko rufe d'akin batayi ba Alh Yusuf sosai yayi hamdala lokacin da ya zo d'akin Aira ya ganshi a bud'e hamdala yayi tare da shigowa ganin tana bacci ya sanyashi murmushi Ya ce "Yau Ranar tawace komai yazomin a sauk'ak'e daga yaudai beauty Zamu zama d'aya Cikin Sauri ya cire babbar rigar jikinshi cikin sand'a ya haye gadon Tare da janyota a hankali ya fara sarrafata cikin wani irin salo Aira cikin bacci takejin Abu kamar a mafarki ga wani nauyi da takejin an hayeta Jin Abu nayin gaba Ya sanyata farkawa koda ta farka taga mutum a kanta ihu ta fasa iya k'arfinta ta ce " wayyo kwart.....saurin rufe mata baki Alh Yusuf yayi ya ce "Ba kwarto bane nine mijinki"wara idanu Aira tayi tuni harta Fara kuka ta ce "Daddy me keke shirinyimun na shiga ukku Dan Allah ka rabu dani ka tadani wayyyo ni Aira shikenan na mutu'" K'ara mirginawa Alh Yusuf yayi kanta tare da Fara k'ok'arin Rabata da rigar jikinta ya ce "Hak'k'ina zan Amsa wajenki beauty kinsan dai na d'aga maki k'afa to yau hakuri na ne yazo k'arshe Gwarama ki bada kai kawai bori ya hau Dan yau babu mai kwatarki a wajena Karkiyimun gardama Naji maki ciwo my beautiful bride a hankali zan biki........βπΏ
*Tirk'ashi*ππΏββοΈππ½ββοΈ
*_Miss Hajo ce_*π€πΏ
[6/29, 22:56] Hajo hajo: π
ΏοΈ..........*73&74*
....A hankali zan biki"Aira jin maganganun take tamkar a mafarki kuka ta fashe da shi ta ce "Ka tadani Daddy Dan soyayyarka da annabi muhammad (s a w) Karkamun komai " Ai Alh Yusuf baimasan tanayiba tuni harya zuge mata zif din rigarta yana kokarin raba ta da rigar jikinta ganin da gaske dai yake "ki rik'emun Amanar Komai dake tattare da ke na baki Amanar kanki Da kanki" Tunowa da maganar Ta da Arman Ta k'arshe Ai batasan sanda wani k'arfi yazo mata ba hannun Alh Yusuf ta samu ta gantsarwa cizo iya k'arfinta har saida Fatar wajen ta fara fita Ai Alh Yusuf najin azabar cizon da Aira ta gallamai ba baisan lokacin da ya yi k'ara ba Ya mirgina gefe Aira na ganin ya d'agata cikin sauri ta mik'e cike da tashin hankali hawaye duk sun cika mata fuska Kallonta Alh Yusuf yayi ya kalli hannunshi ya ce "Tunaninki wannan cizon da kikamun shi zai kwaceki daga wajena sainaga ta Inda zaki fice daga d'akin" Cikin kuka Aira ta ce "Wlh baka isa kayimun komai ba mugu azzalumi macuci tsohon banza kawai" Alh Yusuf cike da zafin rai ya tunkarowa zai Kara chafketa Cikin rud'u Aira ta fara waiwayen neman mabugi Kwalbar turarruka da aka jera mata akan Mirror d'inta ta kwaso Tare da Jefa mashi katuwa a goshi"Alh Yusuf ba k'aramar azaba yaji ba tuni goshinshi harya fashe ya fara fitar da jini Durk'ushewa a wajen yayi yana sauke numfashin wahala Aira ganin hakan ya sanyata saurin Rugawa tayi hanyar kofa tare da Fara k'ok'arin bud'ewa "ni kika fasawa goshi Illatani kike son kiyi Aira to Karki fice daga d'akin nan kome na miki ke kikaja" cikin kuka Aira tana bud'e k'ofar ta ce "idan ka tashi ka kasheni sannan wlh saika sakeni" Ganin Alh Yusuf ya Mike jini nabin goshin shi sosai ya fashe ya sanya Aira saurin bud'ewa cike da tashin hanki ta Ruga a guje Alh Yusuf ya Mara mata baya yana ina zakije Ai Aira bata zarce ko ina ba sai d'akin Hajiya saude taci sa a ko a bud'e A guje ta Ruga tayi d'akin sai hak'i take tana kuka Hajiya saude da har ta kwanta Jin Banko k'ofar ya sanyata tashi cike da mamaki take kallon Aira ta ce "Me ya kawoki nan ke kuma" Kafin ta k'arasa maganar Alh Yusuf ya shigo rik'e da goshin shi dake fitar da jini cikin kid'imewa Saude ta mik'e Aira ganin ya biyota ai da gudu ta Ruga ta boye Bayan Saude tare da kankameta ta fashe da kuka ta ce "Dan Allah Mama ki taimakeni " Cike da masifa daddy ya ce "ki fito na fad'a maki " Mama saude tsaye tayi ta kalli wannan ta kalli wancen "ta ce " wai meke faruwane Alh yanaga jini a goshinka ka"Matsowa yayi yana cije baki ya ce "Ba ruwanki ke kuma ki fito Daga bayanta idan kuma kika bari na kwaceki da kaina zaki yabawa aya zak'inta " Kuka Aira ta fashe dashi tare da kankame Mama saude ta ce "Mama Dan Allah karki bari ya tab'ani kasheni zaiyi kimun rai Mama Dan Allah kisa ya sakeni Daman bana sonshi aka auramunshi Dan Allah ki taimakeni Mama "Rik'e Aira saude tayi tare da gallawa Daddy harara ta ce " Ficemun daga d'akin Alhaji"bazan fita ba ina ruwanki wai ba mata ta bace wlh ranku Duka zai b'aci"Aira najin haka ta k'ara fashewa da kuka ta ce "Mama Dan Allah karki bari ya tafi dani " Mama saude mamaki duk ya cika mata kai kwantar da murya tayi ta ce "Kayi hakuri Alhaji ka fita na turo maka ita Sannan kaje a duba maka goshin naka kafin nan zan lallaba maka ita" Badan Alh yaso ba Kamar Wani sakarai ya ce "to" yana ficewa daga d'akin Aira ta sauke wata nauyayyar Ajiyar zuciya Rufo d'akin Mama saude tayi tare da sa key ta juya Kallon Aira tayi dake tsaye har lokacin tana kuka Dafota tayi ta ce zauna muyi magana"ba musu Aira ta zauna gefen gadon tana kuka dukta rikice numfasawa saude Tayi ta Ce "Inason kiban labari komai bana son ki b'oyemun Naji kina cewa bakisan Alhaji to garinyaya Akayi Auren nan " Cikin shashekar kuka Aira ta ce "Eh Mama wlh bana sonshi Auren dole ne akamun dashi" Cike da mamaki saude ta ce "Auren dole Kuma tun yaushe aka wuce yayin Auren dole garinya Haka ta faru" Goge hawayenta Aira tayi ta ce "Ina da Wanda nake so tun yarinta.......tas ta bata labarin komai da soyayyar su da Arman har zuwa Aurenta da Alh Madugu " amma ta boye mata zarginsu da Abbanta yake da kuma birthday din da ya hada mata da kamasu a hotel da akayi ta k'arasa fad'a cikin kuka mai cin rai Dan sosai ta k'ara tunowa da soyayyar su da Yaya Arman"Hajiya saude sosai tayi sanyi ta kuma tausaya wa Aira a zuciyarta ta ce "Ashema haukan banzana nake Yarinyar ba sonshi take ba" Kiyi shiru ki bar kukan nan kinji a Gaskiya ni kaina na tausaya miki "Cikin kuka Aira ta ce " Dan Allah Mama ki daina kallona matsayin kishiyarki wlh ni kallon uwa nake maki Dan Allah ki sanya Daddy Ya sakeni wlh bazan iya zama dashi a matsayin miji ba ki taimakeni Mama kisanya ya sakeni"Karki damu y'ata daga yanzu nadaina kallonki matsayin kishiya duk bansan da wannan al'amarin ba sai yanzu da kika fad'amun yanzu ki koma d'akinki kije ki kwanta gobe ma k'arasa magana"Mama Dan Allah ki bari na kwana a nan wlh ni ko a k'asa Ne saina kwana Amma bazan iya komawa ba Chan tsoro nakeji zai iya bina Dan Allah Mama ki taimakeni"sosai Aira ta bawa Mama tausayi Hakan ya sata cewa "to shikenan tunda kin tsorata hau gadon ki kwanta saimu kwanta tare" Murmushin farinciki Aira tayi ta ce "Nagode Mama Allah saka da alkhairi" A tare suka kwanta Gado d'aya Aira har lokacin fargaba take Saidai kuma.ta d'anji sanyi a ranta da suka fahimci Juna da Mama saude koba komai yanzu damuwarta a gidan zata ragu Itama saude cike da mamakin al'amarin nan ta kwana (Sabon salo kwana Gado d'aya da kishiya ππ
)Alhaji Yusuf ko kai tsaye wani k'aramun clinic ya nufa Inda aka duba mashi raunin Saida akai mashi d'inki shi kanshi yayi mamakin irin yankan da Aira ta mishi saida aka gama mishi d'inkin tukwana ya koma gida takaici biyu ga bai cimma abunda yaje samuba ga azabar ciwo Washegari koda suka tashi cikin ladabi Aira ta gaishe da Mama saude ta amsa mata cikin mutuntawa Nan Aira ta shiga gyara mata d'akin dukda tayi da ita ta Bari ammata kβi tana cikin shara Laila ta shigo kallon Aira tayi cike da mamaki tukwana ta kalli mamanta ta ce "Mama wannan kuma me take maki a d'aki da sassafen nan" Janyo hannunta Mama saude tayi ta ce "Aikine take tayani Sannan ta ce " Daga yau Laila karna k'ara ganin magana marar dadi ko harara ko hantara ta shiga tsakaninki da Aira ki d'auketa tamkar y'ar uwa kinji"zumburo baki Laila tayi ta ce "To akanme Mama kishiyarkice fa" Aira ce ta ce Mama zan wuce "murmushi saude tayi mata ta ce " To Aira nagode kije kiyi bacci Naga baki rintsaba sosai sannan karkishiga kitchen nayi magana da mai aikinmu zata dawo yanzu idan ta gama break fast zanturo Laila ta kiraki kinji "To Mama nagode"