NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   51 / 54

150K to 153K   out of 160.7K words

fad'a tana yunkurawa tacewa twins ku taho mu tafi" Ba Inda zaki koma ki zauna Mamana "Suka tsinkayi Muryar Abba " Sosai Ayra tayi mamakin jin kalaman Abba da batayi tsammani ba Bama ta San yana wajenba Kallonshi tayi hawaye na zubowa daga idonta sai kuma tayi k'asa da kanta ta ce "Dan Allah Abba kayi hak....shit Abba ya fad'a tare da cewa " banason jin komai ki huta Sannan ya kalli Mama ya ce "A bata abinci taci sannan Tasha magani " To Mama ta fad'a Abba na gama fad'ar haka yabar palour kowa saida yaji dadin ganin saukowar ta Abba Bayan fitarsa Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da Kallon Mama ta ce "Allah yasa Abba ya yafemun" murmushi kawai ta mata nan kowa ya shiga yi mata Sannu Inda Amma Cikin farinciki ta kira Aysha Da Ummy ta fad'a musu samun lafiyar ta Ayra A lokacin da Aysha Tazo sosai Ayra tayi farincikin ganinta da tsohon ciki nan suka Rungume suna suna murna Ummy ma tana da wani k'aramun cikin Dan d'anta harya girma Itadai Aira shiru tayi tana son ta tambaya ina Haidar d'inta tana jin nauyi ga ARMAN da takeson taji yana ina Dan bata gansa ba Da dare Suna daki ita da Amma suna ta hira Ta ce "Sis wai ina Haidar " yana wajen babanshi jiya da ya kawo twins Ya tafi dashi gobe zai maidosa ya ce Ai kullum saiya kira ta wayarki ni nake d'auka yaji halin da kike ciki"Shiru Aira tayi tana nazari kenan Arman wata biyu bai ganta ba kenan Tasan Tabbas daman indai tana gidansu ne bazai tab'a taka kafarshi gidan ba yanda yake da bak'ar zuciya Shiru tayi bata Kara cewa komai ba washegari tunda Safe Abba ya sanya Driver ha kaisu Aira Asibiti Wanda Mama tayi mata rakiya Inda akai checking lafiyarta da abunda ke cikinta Alhmdllh komai normal Jikinta yanzu watanshi biyar Ya shiga na shidda nan aka rubuta musu magunguna suka dawo gida Suna zazzaune twins na bangaren Abba Suka jiyo sallama Amsawa sukayi Haidar babba ya je ya bud'e Mummy ce ta shigo Tare da Haidar A hannunta sosai Su Mamy suka tarbeta cikin girmamawa da mutuntawa Nan aka shiga gaisawa sosai Mummy tayi farincikin samun lafiyar na surukar tata Sosai tayi hamdala nan suka Rungume juna ita da Aira Haidar ko Amma ta amsheshi Dan tayi kewarshi sosai Nan aka shiga jajinta abunda ya faru Aira dai na like da Mummy Arman ko yana kawo Mummy yajuya ya koma A hankali Aira take kallon Haidar d'inta taga Ya girma masha Allah ga ya k'ara wayau ganin Yanda ya lafe jikin Amma kamar itace mamansa "Murmushi tayi musu Tana kallonsu Shima ita d'in yake kallo" Amma ce ta nuna masa ta ce "Ga Mom je ku gaisa" Lafewa yayi jikin Amma yana tsotsar yatsa Alamun bazaijeba "Murmushi Aira tayi sosai taji dad'in yanda taga y'ar uwar tata tana kula mata da d'anta Dan yanda taga ya like mata to Ta tabbata ba k'aramar kula ta bashiba a kwanciyarta.
Da Mummy zata tafi Bayan ta Aje sayayyar da tayo Sosai tayi wa su Mamy Godiya sannan ta ce a rakata su gaisa da Abba Mamy ita ta rakata har part din Abba Suna tafe Mamy nayi mata Godiya akan Abubuwan da Aira ta bata labarin ta dinga mata cewa tayi ba komai ai Ayra da Arman duk d'aya suke a waje na " Suna isa palourn Abba Inda suka tarar twins Na cinyarsa suna Danna laptop suna ganin Mummy da gudu Suka tashi tare da Rungumeta "daukarsu d'aya Bayan daya tayi ta ce " Oyoyoy yaran Mummy ya weekend din "Alhmdllh suka fada a tare da tsallen murnar ganinta Mamy ta Ce " to ku bar mummyn taku ta zauna ko "Sai sannan suka bar Mummy ta zauna " Kallon Abba tayi da ita yake kallo ta ce "Ina yini Yaya munsameku lafiya" Lafiya qalau Fatima ya Gida"Alhmdllh Abba Mummy ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya jin ga Alamun Abba zai saurareta "Madalla " ya fad'a Mamy ce ta fita tare da twins Dan su basu wuri su tattauna "Bayan fitarsu cikin ladabi Mummy ta ce " Daman hakuri muka zo baka yaya akan laifin da mukayi maka ni da yarana Dan Allah kayi hakuri ka gafartamana "shiru Abba yayi kamar mai nazari sai kuma ya ce " ai babu abunda zance kin tab'ayimun na b'acin rai Fatima tsakani na dake Sai mutunci da mutuntawa bakiyimun komai ba Allah yafe mana tare"a a a yaya Munyi maka laifi babba Wanda nice mai laifin ma dai a Gaskiya Dan ni na had'a Auren yaran nan bada saninku ba ?Aure!!!!Abba ya fad'a mamaki k'arara a fuskarsa "Shiru Mummy tayi Chan kuma ta ce " Eh Yaya Aure.....tas ta basa labarin abunda ya faru a yola Har zuwa yanzu "Sosai Abba ya shiga kogin tunani kenan yaran nan yaran sunna ne " a fuska bata iya Tantance yanayin da yake ciki b'acin rai ko akasin haka amma a fili cewa yayi "Allah yasa haka shi yafi zama alkhairi " Ameeeen Mummy ta fad'a tare da Yin shiru ganin Abba bai sake cewa komai ba ya sanyata rasa abun cewa Mikewa tayi ta ce "To zan wuce Yaya mungode Allah Kara girma zan wuce da twins Gobe za a koma makaranta" Ai nazata zasu kwanan mana biyu to shikenan Allah tsare hanya "Ameen Mummy ta fad'a tare da fitowa bata gane dai abunda Abba yake nufi ba Tana fitowa Mamy ta kira a waya ta ce " Twins su fito mu wuce ?To gasunan Mamy ta fad'a tare da Kallon Aira ta ce "Zata tafi da su Naila saboda Makaranta daman weekend ne suka zo mana " To Mamy Ayra ta fad'a tare da mik'ewa ta sanya k'atuwar hijab d'inta ta kama su Suka fito a harabar gidan ta tarar da mummy na jiransu Murmushi ta sakar mata tare da dafa Aira ta ce "Ke kika fito da kanki kenan daughter Aida kin huta saboda yanajin jikin naki" Murmushi Ayra tayi tana kasa da kanta ta ce "Ai da sauki Mamy a gaishe da su Dady ta fad'a tana mik'a mata kayan su twins " Ansa tayi ta ce "zasuji me kike buk'ata na bada driver ya kawo maki" Murmushi tayi ta ce "bana buk'atar komai Mummy nagode Allah saka da alkhairi" Duk yanda Mummy tayi Aira ta fad'a abunda take so kin fad'a tayi "To tunda kinki fad'a na bada sako yanzu akawo maki" Mummy ta fad'a tana kama Nihal dake shirin sillewa ta ce "Ku wuce mutafi sarakan wasa" Murmushi Aira tayi tare da musu bye bye "suma bye bye suka mata Naila ta ce " Mom bakice a gaishe da Hero enki ba"Dariya Mummy tayi itama Airar Dariya tayi Tare da girgiza kai ganin sun fita ya sanyata komawa Ciki ta na tunanin sahibitin nata.........✍🏿


*Ni da Yaya Arman it’s not free it’s for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*



*_Miss Hajo ce_*
[7/24, 12:52] Hajo hajo: 🅿️..........*125&126*





Tana tunanin sahibin nata Koda Mummy ta koma ta fad'awa Arman samun lafiyar Aira zokuga farincikin da ya shiga Kiran wayarta yayi tayi a lokacin wayar na silent bata gani ba Da dare Aira na zaune a palour suna Hira da y'an gidansu Dukda ba wani sakewa take sosai ba Amer yazo ya ce "Ya Ayra Abba yace kije" Saida gaban Ayra ya fad'i cikin dauriya ta mik'e ta sanya hijab d'inta Kallon Mamy tayi Gyada mata kai tayi Alamun ta je gabanta na fad'uwa ta isa part din da Sallama ta yi knoking ya bata izinin shigowa tana shigowa kasa ta samu ta zauna nesa dashi tare da Yin kasa da kanta ta ce "Ina yini Abba" Lafiya qalau ya jikin naki"Alhmdllh "ta fad'a masa kasa-kasa" Jim yayi kamar bazaiyi magana ba saikuma ya ce "d'ago ki kalleni zamuyi magana dake kuma kika kuskura kikamun karya kinsan zanganeki Gaskiya nake so ki fad'amun Dazu Hajiya Fatima tazo munyi magana da ita ta fad'amun komai na shirya aurenku Da tayi to ni wannan bai daman ba Sosai Saidai Annunamun ban isa dake ba Wanda ke kika bada kofar yin haka to wannan ya wuce tunda Allah ya kadarta auren ba wanda ya isa ya Hana tunda gashi hada rabon yara Maganar da zamuyi akan Aurenki Da Alh Madugu tun lokacin da abun ya faru Ya kirani yake sanarmun Sunje Asibiti Anga ciki Jikinki Bayan nan sun kamaki keda Mujahid daki daya " To abun nan har yanzu shi yafi mun ciwo Gaskiya nakeson ki fad'amun shin maganar Gaskiya Ce haka take ko Ko?Tuni Idon Aira harya cika da k'walla ta ce "Wlh tallahi Abba ko da Al'kur ani zan iya rantse maka wlh ban tab'a zina ba Da kowa ba bare kuma *NI DA YAYA ARMAN* sharri ne kawai suka mana sannan babu wani ciki a lokacin Typord ne ke damuna suka mun sharri sukace ciki" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka"Shiru Abba yayi na d'an wani lokaci yana nazarin maganganunta A yanda tayi maganar yasan Tabbas Gaskiya take fada Cewa yayi "Kin tabbatar maganar haka take" Tana kuka ta ce "Wallahi Abba idan akwai karya a maganar nan kar Allah ya maidani Cikin gida lfy" Sosai ran Abba ya b'aci kenan sharri ne Madugu yayiwa y'arshi kenan shiyasa bai Kara kiranshi akan maganar ba Aiko cikin b'acin rai ya lalubo wayarsa tare da dannawa Alh Madugu kira Ring biyu ya d'auka tare da cewa "Alhaji Abubakar kana lafiya " Cikin fushi Abba ya fara magana da cewa "Daman kai ba mutumin kirki bane na d'auke ka na baka y'a saboda yarda da kuma amintar mu da na duba ka rasa Dame zaka sakamun saida b'acin suna Ka k'ullawa y'ata sharrin zina da kuma sharrin ciki to bari kaji wlh baka isa kaci lilis ba Saina makaka a kotu ka kawo shaidun Inda ka kamata mutumin banza da wofi kawai"Sosai Alh Yusuf ya rikice cikin waya ya fara cewa " Dan girma Allah ka tsaya ka saurare Alhaji Duka abunne yazo a wani iri Rashin bincike da zurfafa bincike yasa aka samu matsalar wannan wlh banyiwa y'arka sharri ba Daga asibitin ne suka bada result d'in ba daidai ba muma saidaga baya suke shaida mana mistake ne aka samu aka bata result d'in wata ita waccen Aka bata nata ashe typord ke damunta sannan ni bani da shaidar da zance na kama yarka tana iskanci duk Rashin bincike ne ya kawo haka har yanzu nima ina nadamar abunda na aikata Inajin kunyar zuwa na baka hakuri sannan nayi bikonta Dan wlh inason mata ta har yanzu”sosai ran Abba ya k'ara b'aci ashe Gaskiya ne kenan Aiko cikin fad'a ya ce "Zaka maimaita Duka wannan bayanan a gaban alkali mutumin banza Sannan Kai bakaji kunyar na k'ara maido maka y'a ba a karo na biyu to idan baka sani ba ka sani tun sanda ka saketa tayi Aure yanzu haka Yaranta Ukku Dan haka kaida ita har abada sannan saina nema mata hakkinta na b'ata mata suna da kayi ka jirayi sammaci Abba na gama fad'ar haka ya katse kiran sai huci yake saboda b'acin rai Aira Duka taji abunda Alh Madugu ya fad'a Dan a hands free Wayar take sosai taji dad'in yanda Abba yayi mishi kuma ya nuna zai nemo mata y'ancinta bata gama wannan tunanin ba ta tsinkayi Muryar Abba da cewa " tashi zaki iya tafiya gobe kiyi sammako Mu tafi court saina maka Dan iskan mutumin nan a gaban hukuma "Mikewa Ayra tayi ta ce " To Abba Tare da dukursawa ta ce "Dan Allah Abba ka yafemun irin Abubuwan da nayi maka a baya nayi nadama Kuma na tuba na shirya yi maka biyaya akan duk abunda ka bani umarni a kansa amma Dan Allah ka yafe mun"Taso da ita Abba yayi ya ce " Na jima da yafe maki Mamana Allah yayi maki albarka ya shirya miki yaranki Na yafe maki duniya da lahira ko yanzu kika mutu baki mutu Da hakkin mahaifi a kanki ba sannan nima ki yafemun irin abubuwan da nayi miki na rashin Adalci zafin zuciya ne da fushi ya rudeni harna dinga maki abubuwan da namaki ki yafemun nima na yafe maki duniya da lahira Allah maki albarka mamana "Ayra harta ta manta yaushe rabon da tashiga cikin farincikin da ta shiga ba irin na yau Ai batasan lokacin data Rungume Abba ba ta ce " Nagode Abba Allah ya saka da alkhairi Tabbas kaid'in ka cika uba na gari bakayimun komai da zan yafe maka ba duka laifi nane na rashin maka biyayya da nayi nagode Abba “ta k'arasa fad'a tana hawayen farinciki Sosai Abba yakejin ninkin soyayyar yaratshi na shigarshi Dan har yanzu Aira ta daban ce a cikin yaranshi son da yake mata na daban ne"Da gudu Aira ta saki Abba Tare da rugawa part d'insu Dan tayiwa y'an uwanta da Mamy albishir tana zuwa Cikin farinciki ta Ruga ta Rungume Mamy daka Kalleta kasan tana cikin farinciki " Kallonta duk sukayi tare da cewa "Lafiya Ayra cikin " Tsananin farinciki ta d'ago ta ce "ku tayani murna Abba ya yafemun duk abunda nayi masa da bakinsa yanzu ya fad'a ya ce ya yafemun duniya da lahira" Cikinsu babu Wanda baiyi farinciki ba duk hamdala sukayi "Nan Aira ta basu labarin yanda sukayi Da Alh Madugu Dariya Mamy ta yi ta ce " Ai gwara da suka k'are a hakan shi aminta dadi hada d'aukar Y'a sukutum ka aurawa tsoho ai yanzu an k'are. Tsiya tsiya wani kotu kuma Bayan Allah ya bayyana Gaskiya "Dariya Ayra tayi Jin maganar da Mamy tayi ta ce " ai gwara a kwatomun hakkina na b'atamun suna da yayi ta fad'a tana Mikewa taja hannun Amma suka nufi daki Dan su Kara labatarwa "Mamy ko da Mama tattaunawa suka dingayi akan Lamarin Sannan sukaje suka samu Abba dak'yal suka samu suka shawo kanshi akan yayi hakuri ya barsu da Allah sakayyar Allah tafi ta kotu A haka suka samu harya hakura ya janye maganar Karan .
Aira na komawa daki wayar Ta ta lalubo nan ta shiga kiran y'an uwanta su Aysh,ummy,Aunty Maryam,Mama Halima duk tayi musu albishir da Abba ya yafe mata zokuga farincikin da y'an uwanta sukayi musamman Mama Halima daman Arman Daddy Ya yafe masa yanzu Abu d'aya ya rage Daidaituwar Abba da Daddy Shima kuma suna sa ran insha Allah zasu shirya.
Sai sannan Ayra ta duba wayarta taga missed call d'in da Arman yayi mata Tana cikin liliyar wayar taji yana kira saida taja aji tukwana ta d'auka tana turo baki" Daga bangaren Arman Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "My cutie " Turo baki Ayra tayi ta ce "Uhm ba wani cutie ashe duk Rashin lafiyar nan da nayi bakazo ka ganni ba " Am Sorrry Matar aljanna farincikina Uwar yayana Macen da babu kamarta a fad'in duniyar nan tauraruwa mai Haske a cikin taurari kiyimun Afuwa sannan kiyimun uzuri kinsan dai ason samune bazanso muyi second d'aya batare da juna ba Wlh inason zuwa ganinki ina tsoron Wulakancin da Abba zaiyimun shi ya hanani zuwa Kinsan dai bazai barni na shigo cikin gidansa ba ni kaina kwanakinnan a kaya na yisu"Uhm kawai tace "Cikin damuwa ya ce " Fushi zaki yi dani My nurul khalbi kiyi hakuri Kinsan Gaskiya nake fad'a maki"cikin shagwaba ta ce "Na hakura Hero " Ajiyar zuciya ya sauke har tana ji daga waya ya ce "To ykk ya jikin naki my cutie " Alhmdllh hero "Masha Allah haka nakesonji Allah ya k'ara maki lafiya ya my unborn" Turo baki tayi ta ce "Ameeen wai ashe yaya ciki ne dani bansani ba Gashi harya girma Haidar fa ko shekara baiyi ba Yaya kamar wata kaza" ta fad'a tanajin kamar zatayi kuka "Arman saida yaso yayi Dariya Amma Dan kartaji Haushi ya fusge tare da marairaicewa ya ce " wayyo sorry cutie d'inmu Aike jaruma ce So nake ai ki cikamun gidan da kyawawan yara kamar 30 haka ba yawa"Wara idanu tayi kamar yana ganinta ta ce "Chab Yaya 30 fa saikace wata Akuya" Sosai Arman ya sanya Dariya daman Dan ya dara yayi maganar Ayra ko turo baki tayi ta ce "Dariya ko ai dole kayi Dariya tunda baka tab'a shiga labour room ba kaidai kawai ganinsu kake " daidaita dariyarshi yayi ya ce "Sorrry Oum twins d'inmu kece kika bani Dariya to yanzu dai ayi hakuri a cigaba da kulamun da unborn Allah ya saukeki lafiya Yanzu yaushe zan ganki" ameen ta fad'a tare da cewa "Albishirinnka honey tun d'azu nake son nayi maka Albishir farinciki ya hana " Cike da zak'uwa ya ce "Goro my prince's wannnan wani Babban Albishir ne " Tana murmushi ta ce "Yaya Abba ya yafemun Duniya da lahira " Arman yana daga kwance saida ya Mike ya ce "Da gaske kike cutie " Wlh kuwa yaya nan ta bashi labarin abunda ya faru"Ajiyar zuciya nauyayya ya ce "Alhamdulilla Alhmdll Allah nagode maka Tabbas komai yayi tsanani akwai sauki Nan gaba Ashe muma saukin namu na kusa Amma nayi farinciki marar musaltuwa cutie shikenan yanzu nidake gaba d'aya Bamuda hakkin iyaye a Kanmu Duka sun yafe mana Amma nayi farinciki" tana murmushi Ayra ta ce "Wlh nima nayi farinciki Sosai yaya Inajin a jikina komai yazo karshe yanzu saura Daddy da Abba kawai shiryawarsu ta rage " Insha Allahu suma zasu shirya saboda tundaga mutuwar Inna naga sun yi sanyi Allah ya nuna mana wannan ranar da cikar burin Inna "Ameen Ayra ta fad'a " Sun tab'a Hira sosai cikin so da k'auna Wanda saida bacci ya d'auke Ayra bata ma saniba tukwana Arman ya kashe kiran Washegari aka kira aka shaida musu Aysha ta haihu ta haifi y'arta mace zo kuga farincikin da wannan iyalan suka shiga kodan Aysha ta jima bata haihu ba Musamman Ayra da ta rasa Inda zata sanya ranta saboda Farinciki sati na zagayowa yarinya taci suna Halimatu ana cemata Shukura anyiwa mariganyiya Inna takwara Wanda koda

51 / 54