NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   19 / 54

54K to 57K   out of 160.7K words

ba mijinkiba wlh in banda kece da babu wacce ta isa tamun abunda kikemun na kyaleta amma ke bakya gani ganinkima ke ake chuta yanzu wannan Abun da kike shi zaki koyawa y'arki taje tanayiwa miji" Tsaki Mamy taja ta ce "Ai daman ka saba Cemun mai k'aramar kwalwa to wannan Karin zakaga aikin k'aramar kwalwar tana gama fad'ar hakan fuuuu ta fice daga d'akin tana komawa d'akinta ta kira Mama Halima tana kuka ta ce " yanzu Halima haka zamu zuba ido Abun nan ya faru wlh yanzu haka daga wajenshi nake naje mai da lalumarma amma karshe ba arziki muka kwashe yanzu ya zamuyi halima"da yake Mama Halima Tabawa Mamy wannan shawarar numfasawa Mama Halima tayi ta ce "To ni yanzu wlh kaina ma ya kulle Banmasan ya zamu b'ullowa yaya ba Nima fa Dana kirashi ba irin magiyar da ban mashi ba Amma ya murje ido yanzu yanda za ayi kawai kiyi hakuri mu zubawa sarautar Allah ido sannan ita kuma Mamana ki lallabeta kice mata kunyi magana dashi ya ce ya janye Dan a kwantar mata da hankali karta shiga wani hali" goge hawayenta Mamy tayi ta ce "To shikenan Halima nagode Bari nace mata hakan " sai wajen Azahar Aira ta tashi tana tashi taji saukin ciwon kan wanka taje tayi tana fitowa Mamy ta shigo da abinci saida Mamy ta bata fuska tukwana ta yarda taci abincin cikin lallashi Mamy ta ce "ki kwantar da hankalinki Mamana Munyi magana dashi kuma yace zai hakura amma saiyaga nutsuwarki har zuwa lokacin ki kwantar da hankalinki kinji" cikin farinciki Aira ta d'ago ta ce "Mamy da gaske " gyada mata kai tayi ta ce Gaske mana"Alhamdulilla Aira ta fad'a tare da Rungume Mamy ta ce "Nagode Mamy Allah tsundumaki a aljanna nikuma insha Allahu zankiyaye nagode Gaskiya Mamy kincika uwa ta gari Allah saka miki da alkhairi " murmushi Mamy tayi ta ce "Ameen yanzu ki kwantar da hankalinki ki dinga bacci kina cin abinci kinji" gyada kai Aira tayi tana murmushi ta ce "Insha Allahu Mamy kai ashe addu'a ta ta amsu " murmushi kawai Mamy tayi a zuciyarta ta ce "tukunna dai" Tun daga ranar Aira ta d'an kwantar da hankalinta take cin abinci amma walwalarta taki dawowa Tana waya da Arman akai akai ta kasa fad'a masa abunda ke faruwa Abba ko dabara yayiwa inna ya tura ta umrah dan yasan halinta haka zatayi ta cewa dan ba ita ta haifeshi ba shiyasa bayajin maganarta Yaya Umar ko tuni ya koma wajen aikinshi tare da matarshi dan yace ko bikin bazaizo ba a haka har akayi sati Ukku Ranar Litinin Aira na baccin rana Haidar yazo cikin tashin hankali ya dinga Bugata ya ce "ya Aira ki tashi " tana tashi ta ce "ya akai haidar ina bacci kanamun wannan tashin hawaye haidar ya fara ya ce "ya Aira kije palour ki gani wlh ashe Abba da gaske yake Auren nan Lefenki ne aka kawo yanzu daga sokoto firgit Aira ta mik'e ai bata gama Jin Abunda Haidar zai fad'a ba tayi palour cikin tashin hankali tana zuwa ta tarar da Wasu mata tare da su Mama hada su Mama Halima Akwati Sunkai guda ashirin baje a palourn tashin hankalin da ta shiga bai misaltuwa tsaye tayi tare da kama k'ugu tana k'arewa y'an d'akin da akwatinan kallo Wata mata ce daga cikin Wanda suka kawo kayan ta ce " Ah masha Allah itace amaryar kenan ba shakka Allah Sanya alkhairi ya bada zaman lafiya"Ba Ameeen ba Aira ta fad'a tare da Jan tsaki cike da Rashin kunya tare da nuna yatsa ta ce "Na rantse da Allah kuka yarda Aka d'aura Auren nan kun saiwa kanku tashin hankali wlh tun wuri ku kwashi tsiyarku ku koma Inda kuka fito kunzo kun wani jugum jugum bako kunya tsaffin banza kawai uban Waye za a aurawa tsohon najadun nan ko nayi muku kama da kalar tsaffi kuje chan ku nema mishi tsohuwar zawara ko sa’anninku ne itace mate dinshi ba niba wlh ko ku fita da Kayan nan ko na zagi tsohuwa har uban tsoho da uwarsa zan zaga dan haka ku kwashi tsiyarku ko in sawa kayan fetur wlh “Lokaci guda Aira taji jinta da ganinta sun fara gushewa kwalwarta ta fara juya mata Duka matan da suka kawo kayan sororo sukayi suna mamaki wace mata ta ce " lallai yusuf yau ya kawomu inda za a wulakanta mu Daman yarinyar bataso kenan to Aiko da sake "Kanwar Alh Yusuf ce ta mik'e ta ce " Ku tashi mu tafi munfasa daman yasan yarinyar bata da tarbiya shine zaisa muzo ayi mana Rashin mutunci "Mama ce ta ce " Dan Allah Kuyi hakuri yarinta ce Mama Halima ko d'auke Aira tayi da Mari ta ce "Daman baki da mutunci Aira Rashin kunya zakiyiwa mutane Dan iskanci wadannan waye bai haifekiba" kuka Aira ta durkushe ta fashe dashi ta ce "Mama kuyimun rai wlh banason shi sannan ta Ruga wajen Mamy ta jijjigata kamar mahaukaciya ta ce " Daman Mamy k'arya kikamun kikacemun Amfasa Mamy dake za a had'a baki a kashemun Rayuwa"Tsawa Mama Halima ta daka mata ta ce "Wai baki da hankali Aira uwar taki kike cewa ta miki karya ki wuce kiba mutane wuri" Durk'ushewa Aira tayi kuka kawai take kamar ranta zai fita Wanda suka kawo kayan nan wata dattijiwar mata ta ce "ku bita a hankali Dan Allah mu bamusan yarinyar bataso ba Gaskiya a hakura da abun nan tunda Kunga halin da yarinya ke ciki" Abba ne ya shigo da ya samu labarin Abunda Aira tayi da belt ya shigo ya hau lafta mata ihu da kuka Aira take tana neman a kawo mata d'auki tashi Mamy tayi tabar d'akin gaba d'aya dak'yal matan da suka kawo Lefe suka kwaci Aira a hannun Abba su suka dinga bawa Abba hakuri Aira ko da gudu ta Ruga Dakinsu tana kuka Wayarta ta janyo cikin tashin hankali ta shiga kiran Arman.
Arman yana kwance a kan sopa Idonshi bud'e amma ba bacci yake ba Hakanan kawai tun satin nan gabanshi ke fad'uwa jin Kiran Aira ya tasheshi kiranta yayi tana d'auka ya jiyo kukanta cikin tashin hankali ya mik'e tare da cewa "Lafiya cutie me ya sameki kukan me kike " shiru Aira tayi sai kuka ta ke "cikin tashin hankali ya ce " please cutie ki fad'amun abunda ke faruwa kin tayarmun da hankali ki fad'amun me yake faruwa"Cikin kuka Aira ta ce "Yaya nashiga Ukku shikenan mutuwa zanyi Aure Abba zaiyi mun cikin satin nan yaya har ankawo Lefe yau wlh bansaniba yaya sai yau na shiga ukku shikenan an kasheni " What Arman yafada cikin tsananin tashin hankali ya ce "Bansan irin wannan wasan kinfi kowa sani Aira ki fad'amun Gaskiya" Cikin kuka ta ce "Wallahi tallahi da gaske Yaya abokinshi zai auramun tsoho ne kuma" Ai Arman baisan lokacin da..........✍🏿

😂Team Aira and Arman how market 🤣yaudai Aira ta zage tsaffi 😅😭Arman yau zaiji mugunji 😭😭where is team Abba🙄



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/19, 22:52] Hajo hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

*MALLAKAR*
*Hajara L Sadeq*

*BONUS PAGE*💃🏾💔😂

*This page is dedicated to all lovers of this book as much as they love this book I love them in my life I am so grateful for the way you show love to my book wanda sukayi paying da wanda basuyi ba duka ina godiya ina muku son fisabilillah shafin nan naku ne masoya a duk inda kuke I am very proud of you*♥️❤️♥️❤️❤️❤️❤️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

🅿️..........*53&54*



Ai Arman baisan lokacin da wayar ta sulale a hannunshi ba Sakinta yayi Tim a k'asa "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai yake maimaitawa dafe kanshi yayi kamar Wanda Aka tsikara haka ya tashi ya ce " no bazaiyu ba wlh impossible wlh duk abunda yake kusa dashi ya hau wullawa cikin tashin hankali ya kwashi wayoyinshi yayi waje yana zuwa ya kwalawa mai gadi kira ya ce "Ka maza second biyu na baka ka budemun get yana gama fad'ar haka ya tafi ya d'auki motarshi 360 ya jata yana zuwa bakin gate har mai gadi ya bud'e a guje ya figi motar ikon Allah ne kawai ya kaishi Airport lafiya cikin k'ank'anin lokaci ya yanki ticket zuciyarshi ba abunda take In banda zafi kamar zata fashe kowa ya Kalleshi lokacin zakasan yana cikin tsananin b'acin rai idanunshi sunyi jawur kamar garwashin wuta k'arfe bakwai da wani Abu jirginsu ya d'aga zuwa kano.Aira ko ganin Arman shiru tayi ta magana shiru ya sanyata fashewa da kuka jikin kofa ta durkushe kuka kawai take gwanin ban tausayi Bangarensu Abba ko sosai ranshi ya b'aci matan da suka kawo kaya suda aka batawa rai saiyadawo su sukebawa Abba hakuri sukace ai d'ane ka haifeshi baka haifi halinshi ba ba yanda ba suyiba akan a janye maganar Auren nan tunda bata so suka kira Alh Yusuf sukayi mashi bayani shi ko da yake Allah ya d'ora mai son Aira cewa yayi ba abunda za a fasa idan an d'aura Auren zata soshi Ai Abba ma ko haka yace shi da Mama Halima suka basu hakuri akan Abunda Aira tayi musu sukace ba komai sosai akayi musu sha Tara da arziki Da zasu tafi Mama Halima ce Bayan Tafiyarsu ta je ta samu Mamy Tagumi ta iske tayi ta na hawaye dafa ta Mama Halima tayi ta ce "a Gaskiya zan fad'a maki Rahama kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki fawwalawa Allah komai wannan damuwar da kike bata sa komai bata hana komai kila Allah ya nufa matarshi ce ba abunda za a fasa kiyi hakuri sannan kiba y'arki hakuri kiyi mata fatan Alkhairi kawai ki bari tayiwa mahaifinta biyayya tunda Kinga ya kafe idan kika nuna Rashin sonki kamar kina k'ara zuga tane ki mata fad'a ta nutsu ta rabu da mahaifinta lafiya sannan ta cire Mujahid a ranta tunda Allah ya nufa kila bashi bane mijin dukda dukanmu ba haka muka so ba ki saki jikinki ayi hidimar biki dake naga ko gayya bakiyiba dan Allah Rahama ki kwantar da hankalinki ki kwantar da na y'arki hakuri zamuyi mu barwa Allah sauran tunda munyi abunda zamu iya" Haba Halima taya zan kwantar da hankali na bama wannan ba yanzu abunda yafi tadamun hankali idan na tuna gidan kishiya za a kaita da y'ay'a ta yaya Aira a y'an shekarunta zata iya da kishiyar da ta haife tamayi kusan jika da ita ina zataji da d'iyan miji ki duba fa kiga nisan sokoto Halima nifa gani nake kamar sayarmun da y'a ne wannan Abun Sokoto fa ina zata iya kishi da sokkwatawa me ta sani game da kishi "Ajiyar zuciya Mama Halima ta sauke ta ce " ai akwai Allah shi zai tsareta insha Allahu ki daina damuwa da wannan nima Inajin wannan din amma Addua zamuyi tayi mata sannan muyi mata nasiha ta zauna da kowa lafiya"Sosai Mama Halima ta dinga bawa Mamy baki.Arman koda ya Iso kai tsaye Gida ya wuce cikin tashin hankali Mamy ta tareshi tace Lafiya son na ganka da dare tsaka Baka sanarmun kuma zaka zoba naga kamar ma baka cikin nutsuwa Arman bai iya magana ba Dan in yana irin cikin wannan tashin hankali bai iya magana lura da haka ya sanya mummy shiga damuwa kamo hannunshi tayi kamar yaro tare da zaunar dashi itama ta zauna kwantar dashi tayi saman cinyarta tare da Daddab'a bayanshi ta ce "Calm down my son yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi " Dan haka take mashi idan ya shiga damuwa Arman huci kawai yake tare da lumshe ido yanason yayi control d'in zuciyarshi Sosai Mummy take Abu d'aya dukda batasan meya sanyashi cikin wannan halin ba ta kwashi kusan Awa guda yana kan cinyarta tana lallaashinshi sai Chan taji ya na sauke ajiyar zuciya hamdala tayi azuciyarta alamun ya dawo daidai kenan cike da damuwa ta ce "me yake damunka Arman ka fad'aman please" Arman yana daga kan cinyarta ya lumshe idanunshi tare da bud'esu a hankali kamar mai koyan magana ya ce "Mummy wai Aure zasuyi mata" Wacece za a yiwa Auren "Aira Mummy wlh Mummy inasonta sosai please karki bari a rabamu itad'in rayuwa ta ce Bazan iya cigaba da rayuwa babu itaba " Sosai gaban Mummy ya fad'i tasan abunda Arman yake fad'a Gaskiya Dan son da ya ke yiwa Aira ya zarce misali sosai ta shiga damuwa cikin damuwa ta ce "Aure kuma son Waza a aura mata Bayan sunsan kuna son junanku" Arman baisan lokacin da wasu zazzafan hawaye suka zubo mashi ba ya ce " wani ne Abokin Abbanta Ranar Friday Auren Mummy Dan Allah karki bari ayi Auren nan wlh ni nake sonta nasanke uwace ki tausaya mun nasan Daddy bazai saurareniba ammake zaki saurareni Yin Auren nan daidai yake da rasa rayuwata idan ba so kuke ku rasa ni ba to kusa a hana auran nan please ya k'arasa fad'a tare da mik'ewa ya rik'e hannayenta biyu "Rufe mashi baki Mummy tayi karo na farko kenan da ta tab'a ganin hawayen d'an nata da girmanshi Sosai itama ta shiga damuwa Dan a duniya ba abunda take so sama da Arman d'a daya tilo da Allah ya bata girgiza mashi kai tayi tare da Goge mashi hawaye ta ce " ka kwantar da hankalinka kaji Arman d'ina Insha Allahu Aira taka ce zansamu Daddynku yanzu yaje suyi magana da d'an uwanshi fatan mudai ya yarda"yawwa Mummy Dan Allah kuyimun kokarin wannan "Mummy duk yanda taso da Arman yaci abinci kasawa yayi har a baki ta bashi amma ya cije sosai ya bata tausayi lokaci guda ya zama wani so silent A Daren ta samu Daddy ba irin magiyar da batayimai ba akan yaje wajen Abba suyi magana Dan Allah a janye Auren nan Ya nemawa Arman Auren Aira amma Daddy fir yaki cikin hawaye Mummy ta ce " Ammafa kasan d'anmu zai shiga cikin wani hali me yasa kuke zafafa Abu ne ku bari yaran nan su Auri junansu tunda suna so za a sanya rayuwarsu cikin wani hali"ko zai mutu wlh bazanje ba akanshi wace irin Maganace mahaifinta bai fad'amun ba shine kukeso na je a k'ara fad'amun maganar da zan kwana ban rintsa ba to badaniba bazanje ba idan ke kin matsu kije "Daddy na gama maganar ya fice daga d'akin sosai Mummy ta shiga damuwa Mama Halima ce ta fad'o mata a rai ita ta kira ko zata samu ta taimaka mata amma maganar da taji daga bakin Halima ma ya sanyata Kara shiga damuwa Dan labarin komai Mama Halima ta bata akan ba yanda basuyi da Abba ba Amma ya kafe hatta Inna ta kasa tankwarashi Saidai kawai mu barwa Allah zab'i"washegari Arman har ya fad'a sosai ya shiga tashin hankali da Mummy ta fad'a mashi yanda sukayi da Daddy da kuma yanda sukayi da Mama Halima kamar wani zaki haka ya mik'e kamar Wanda aka zabura ya ce " impossible wlh Mummy bazaiyuba Aira tawace Dan ni kad'ai aka yita bazan tab'a zuba ido ta zama mallakin waniba itadin rayuwata ce munyiwa juna Alk'awarin bazamu tab'a rabuwa ba muddin na bari ta auri wani Tabbas munci Amanar soyayya Yana gama Fad'ar haka ya figi makullin mota kamar zai tashi sama ya fice Mummy ba binshi baiko saurare ta ba mota ya figa a tamanin a lokacin wajen karfe Takwas na dare ranar Aira a d'aki ta yini taci kuka kamar ba gobe masu Lallashinta harsun gaji ga Arman tayi ta kiranshi kashe Wayarshi tana kwance tana hawaye ga k'aramar wayarta dake hannunta taji tayi ringing cikin Sauri ta d'auka kuka ta fashe dashi ta ce "Yaya kai kadaine nakejin muryarshi a yanzu Naji sanyi a raina plx karkayi fushi dani wlh babu masaniyata " Daga bangaren Arman taji muryarshi ya ce "bana fushi dake Aira bantaba fushiba tashin hankalin da na shigane yasa ban waiwayi waya ba ki kwantar da hankalinki rabuwa ta dake abunda bazai yu bane kisa a ranki Auren nan babushi muddin ina numfashi alk'awarinmu bazai tafi a banza ba" Cikin kuka Aira tace "taya zan kwantar da hankalina yaya Bayan baka tare dani" kisa a ranki a ko ina ako wani hali ina tare dake my Aira ked'in jinin jikina ce taya za ayi na samu ganinki yanzu"Wlh yaya yanzu babu ta yanda zaka ganni Abba ya sanya mai gadi tsaro sosai babu ta yanda zan fito "Sosai Arman ya shiga damuwa cikin zuciyarshi Dan son kwantar da hankalinta ya ce " karki damu dole ne ki baro gidannan muddin munason cigaba da rayuwa kamar kowa Duk yanda zakiyi gobe kiyi ki gudo kina kub'utowa daga gidan ki fito da waya kiyi saurin Kirana "Goge hawayenta Aira tayi Dan tasan kaso ashirin na damuwarta ya ragu tunda Arman yana nan bazai bari Auren nan ya faru ba a tunaninta " To yaya zan kokarta na gani saurin kashe wayar tayi ganin Amma na nufowa k'ofar maza tayi ta boye wayar tare da kwanciya "Amma tace sis bazakije kici abinci ba " bazanciba ta fad'a tana juya mata baya.washegari ta kama laraba kuma ranar ne za a fara hidimar biki ba yanda ba ayi da Aira ba akan ayi mata lalle da saloon Amma fir tak'i su Ummy da sukazo ana musu lalle su sukace itama sai anyi mata taga zasu takura mata hauka tayi ta ce "Bazanyiba d'in nace Bazanyiba dole ne ku rabu dani mana wlh kuka Takuramun zanyiwa mutum abunda bai tunani ta fad'a tana girgiza kai " Allah baki hakuri Ummy ta fad'a Hafsa ce ta ce "kuma ku rabu da ita tunda bataso ai ba dole bane " tsaki Aira taja tare da komawa daki Ta dinga risgar kuka Aunty Maryam lokacin tazo da yaranta daga Lagos cewa tayi ina Airar akace mata tana daki tana sana'ar kukan d'akin ta nufa daman ita fad'a gareta nan ta hau Aira da fad'a ta ce "To saikiyi tayi hawan jini ya hauki kanki farau Auren dole Ni kaina ai ba Wanda nakeso aka auramunba kuma nayiwa Abba biyayya na zauna da mijina lafiya yanzu

19 / 54