NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   37 / 54

108K to 111K   out of 160.7K words

suka wuce Inda fitacciyar mai K'unshin ta Zane Aira tasss sosai tayi mata kunshi mai bala in kyau abunka ga farar fata sosai K'unshin ya k'ara fito da ita a lokacin daka kalli Aira dole kayi sha awar Kara kallonta saboda kyan da tayi Saidai kawai a tofeta da wala haula su Murja ma da su Maryam sai santin lallan Aira suke a gajiya suka koma gida Suna komawa kuma aka dasa da gyaran jiki akan Inda aka tsaye ciki da bai tsaf ake gyara Aira.
Washegari aka shirya walima Wanda aka kira manyan manyan malaman sunna Dan suyi wa azin mata A wani Babban Hall Wanda wannan shirin Mummy ne Dan ta ce Batason ayi bidi'a a bikin yaron nata Dan yayi albarka Aira sosai tayi kyau cikin tsadaddar doguwar Riga pink wacce ta Cikin lefentane da Mummy ta sayo a k'alla Rigar zatayi Sama sa dubu d'ari biyar banmayi k'arya ba Ba make up fuskarta sai ainahin kyaun da Allah ya bata Sosai rigar tayi mata bala in kyau a haka malamai mata suka shiga wa azi ba kama hannun yaro Wanda yawaici duk akan aurene da hakkin mace akan mijinta da hakkin miji akan matarsa da azabar da Allah ya tanadarwa Wanda basa yiwa mazajensu biyayya sosai aka shiga wa azi mai ratsa jiki Wanda jikin kowa saida yayi sanyi hatta iyaye Aira ko saida tayi hawaye haka aka k'are walima lafiya aka k'are Inda aka raba kyaututtuka na ban mamaki sosai wajen yayi mutane ni da Yaya Arman fans ma ba abarsu a baya ba dan sosai suka cika wajen wanda bama zan iya Gane wasu ba Dukda naga cikinsu wasu na gunguni akan mummy ta kwafsa musu da bata Bari suka chasheba sunajin haushin duk training din rawar da sukayi ya tafi a banza suna shirin yin warrrrr kawai an warware su (🀣)tukwana kowa ya koma gidanshi Wanda mota d'aya Mummy da Aira suka shiga Gidan Baba Nasir aka wuce da Aira Dan Chan y'an matan suke Hidimominsu.
Washegari da misalin k'arfe 1:PM Aka d'aura Auren *Hajara Abubakar Umar* tare da Angonta *Muhajed Kabir Umar* Akan sadaki Naira Dubu d'ari Dan ance sadaki Kad'an yafi Albarka bayan nan aka daura na Maryam da angonta Salis Baffa shi ya zama wakilin Auren Aira shikuma Arman maimartaba Sarkin Adamawa shi ya zama wakilin shi d'aurin Auren da ya samu halartar manyan mutane Sosai wajen d'aurin Auren ya cika da mutane Saidai kuma an hana koda a waya ne a d'auki hoto ko vedion d'aurin Auren Arman sosai yayi kyau cikin Farar shaddarshi da Tasha surfani na ban mamaki sai kyalli yake duk Inda ya gitta zaka gane shine Angon saboda ya fita da kowa a wajen koda yaji an d'aura Auren rasa Inda zai sanya kanshi yayi saboda Farinciki A wajen yayi sujjada Ya jima yana kwararo yabo da Godiya ga ubangiji cousin d'inshi duk Dariya suke mai yayi minti goma yana sujjada tukwana ya d'ago cikin fara a ya ce "Alhamdulilla Allah na gode Maka daka nuna mana wannan rana daga hannunshi yayi sama sosai ya ce " Alhamdulilla Allah nagode nagode nagode Ka gamamun komai ya Allah Alhamdulilla "murna saida ta kusan zautar da Arman Y'an uwanshi sai Dariya suke mai cikin Sauri ya ja hannun Suleman ya ce " ta Ho mu wuce gida ".
Aira sosai tayi kyau cikin tsatsadan white material Fitet gown da yayi mugun amsarta yayi Mata das a jiki Anyi mata nad'in headgolden wuyanta ko da hannayenta duk gold ne masu matukar tsada sosai tafito tayi wani irin masifar kyau ga make up da akayi mata tayi mugun mata kyau kasancewar bata make up A palourn Aunty Safina Y'an matan cousins din Arman duk suka baje sai tsiya suke yiwa Aira Itadai tayi shiru tayi sanyi Maryam ma sosai tayi kyau su biyun aka hadu aka dinga kashewa Hotuna Bayan anyi mata ita kadai a waya da kuma photograper wanda daya gama zai tura musu ya goge a haka sukayi dashi kuma Mummy ta ce Kar ayi posting koda a what's app ne kawai ayi saboda tarihi Itama Mummy sosai tayi kyau cikin lace d'inta mai mugun tsada hannuwanta da wuyanta shake yake da gwagwalai daka ganta zakaga asalin bafullatanar Yola Dan Mummy itama badai kyau da gayu ba shiyasa Arman yayi masifar kyau saboda biyu ya had'a ga kyan Mummy ga na Daddy Mummy na gefen Aira Ta kama hannunta nan aka shiga musu hotuna masu masifar kyau kamar y'a da uwa(kodan ai sune) ana cikin hotuna sai ganin Arman sukayi kamar daga sama ya fad'o kai tsaye wajensu Mummy ya nufa Tare da Rungumesu ita. Da Aira kamar k'aramun yaro saiji sukayi ya sanya kuka y'an palourn duk Dariya sukasa yayinda wasu suka fara musu video Aunty Safina ta ce "Haba ya haka ango da kuka kuma" wata kanwar mamy ta ce "kukan farincikine" Sosai Arman yake kuka jikin Mummy Danne zuciyarta tayi ta fara Lallashinshi Itama Airar kuka ta fara a jikin Mummy"Ikon Allah Mummy ta fad'a ta ce "To nima kukan kukeso nayi" Zaunawa tayi suna jikinta suna kuka Dak'yal Arman ya sassauta ya ce "Thnks you Mummy mungode mungode Allah saka maki da gidan Aljanna hak'ika kin cika uwa ta gari da kowani d'a zaiso ki kasance uwa a gareshi Mummy kingama mana komai Allah ya biyaki da gidan Aljanna Allah ya baki farinciki Fiye da yanda kika bamu" murmushi Mummy tayi ta shafa kanshi ta ce "Ameeen Ameen Allah yayi muku Albarka ya sanya Albarka a cikin aurenku ya baku zuri'a Dayyiba " Ameen Mummy"Arman ya fad'a yana Goge hawayen shi "murmushi Mummy tayi ta ce " Kazo ka rikitamun y'a kaga ka sanyata kuka"Dagowa Arman yayi ya kalli Aira dake jikin Mummy tana shashekar Kuka "Tashi yayi tare da zagawa gefenta Ya Rungumeta sosai tare da shafa bayanta ya rankwafar da kanshi yana sinsinar wuyanta a hankali ya ce " Alhamdulilla My beautiful wife finally dai An daura mana Aure kin zama mata ta Cutie ji nake kamar mafarkine nake Tabbas yau rana ce da bazan tab'a mancewa da ita a rayuwa ta ba"Lafewa Aira tayi jikinshi Tare da Yin shiru tana sauraran Kalamanshi itama d'in ji take tamkar a mafarki wai yau itace Matar Arman Bayan gwagwarmayar da aka sha a baya shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya Tare da Yin luff a jikinshi "Y'an palourn sim sim kowa ya dinga Zamewa yana fita Dan bazasu iyaga wannan Rashin kunyar ba Mummy girgiza kai tayi tare da barin Wajen Dan tasan Arman gaban kowa zai iyayin komai indai akan Aira ne ta Riga da tayi mishi uzuri Suko tuni sunma manta da wanzuwarshi wasu mutane a palourn musamman Arman Ganin tsayuwar bazata fishshesu ba ya sanya su zaunawa kan kujera Suna Rungume da juna Arman tuni notin kanshi ya fara sincewa Dan Aira ta gama rikitar dashi a hankali ya rad'a mata ya ce " Kinyi kyau my wife"Uhm kawai tace tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren mijin nata shinshina wuyanta ya fara tundaga kan wuyanta Yanajin wani sabon yanayi baisan lokacin da ya fara kissing d'inta ba Ta ko ina Aira ko kasa hanashi tayi Dan sak'on yana shigarta sosai jikinta tuni ya mutu batayi aune ba saiji tayi y Had'e bakinsu waje d’aya ........✍🏿


*chakwaiiiii yaufa chashewa zamuyi yacin kowa yau ta fito ta gwada mana kalar farincikin da ta shiga Finally dai yau Aira ta zama Mrs Arman chakwaiiiiiiii*πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒkowa ya fito yayi musu wak'a nidai ga tawa😹

_Naga amarya Aira tana ta yanga naga ango Arman yana ta burga naga Nida yaya Arman fans suna ta takuuuu_πŸ’ƒπŸ’ƒ

_Ranar kuke jira yau gashi tazo muma da tamburanmu gamu munzo Ango Arman shida Aira Amarya kuyo rawa ta murna anyi Aure_ πŸ’ƒ

_Allah ne ya had'a ba wani mutum ba_πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

*Lokaci ne gashi naku yazo aurenku anka d’aura yau kuncimma burinku a kauna Happy marriage life Aira&Arman *πŸ­πŸ¬πŸ‘πŸ€ΈπŸΌβ€β™‚οΈπŸŽˆπŸŽˆπŸŽπŸŽŠβœ‰οΈπŸ“©πŸ“¨

*Warrrrrrrrrrrrrrrrrr*πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ˜‚



_*Miss Hajo ce*_πŸ€™πŸΏ
[7/14, 12:42] Hajo hajo: πŸ…ΏοΈ.........*95&96*






.....Had'e bakinsu yayi waje d'aya Tare da Fara mata wani irin tsotsa Sosai suka shagala suka ma manta a wajen da suke Ringing d'in wayar Arman ya dawo dashi cikin hankalinshi cikin Sauri Arman ya matsa Itama Airar matsawa tayi tanajin kunya Daga kiran Arman yayi daga bangaren Mummy ta ce "Sarkin marassa kunya saika kyaleta tazo mutane su ganta Idan kayi hakuri ba kai maka ita bama za ayi ba Ka kawomun ita yanzu yanzu gidan Baffa" Sosai k'eya Arman yayi ya ce "Sorry Mummy gamu nan" kama hannunta yayi ya ce "Taso muje gidan Baffa my cutie" Kanta na kasa ta bishi suka bar palourn Duk kunya ta gama cika Aira ganin yanda Ake kallonsu yayinda shi kuma Arman ko a kanshi A motar Suleman suka shiga shi ya kaisu gidan Baffa koda suka fitoma Hannunsu mak'ale Dana juna kannen Mummy sai tsiya sukeyiwa Arman yana murmushi Itako Aira duk kunya takeji A haka suka ratsa mutane suka shiga cikin palourn Wanda cike yake da y'an uwa kai tsaye Aira wajen Mummy taje ta zauna Kasa tare da d'ora kanta saman cinyarta nan Mummy ga shiga nunawa sauran y'an uwan nata surukar tata kowa Sosai suka yaba da kyan Aira ga kuma nutsuwarta da kunya Nan aka shiga hotuna da y'an uwa Wanda Mummy na tsaka Aira da Arman na gefenta sauran kuma Su Bappa da Gwaggo da sauran y'an uwanta nan aka shiga hotuna masu kyau Alhmdll biki yayi biki Saidai ace Alhamdulilla Dan komai ya tafi yanda akeso Bayan magriba aka wuce da Maryam gidan mijinta dake nan garin Yola wajen Takwas da wani Abu Mummy ta sanya Aira taje tayi wanka da ruwan turaren da ta had'a mata Bayan ta fito ta bata atamfa me kyau ta sanya tare da yafa mata gyale kama hannunta tayi suka fito palourn Inda ta tarar da Arman anan yana gefen Gwaggo yana janta Sai Bappa da yayyun Mummy A kunyace Aira ta gaishe dasu suka Amsa cikin mutuntawa Mummy ce ta ce "To abunda yasa Mukayi zaman nan akan hukuncin da na yanke na Inda zaku zaunane bazaku zauna anan k'asar ba London zaku tafi na Riga da nasa an buga muku biza da passport d'inku nasa an yankan muku ticket gobe insha Allahu jirginku zai tashi da misalin k'arfe Sha biyu na rana bazaku dawoba har sai munga yanda hali ya bada sai mungama da matsalar Iyayenku tukwana"da mamaki Arman ya ce " Mummy London kuma Haba Mummy mu fara zama Abuja mana"Bazaku zauna ba nan Arman Na riga da na gama yanke hukunci hankalinku zaifi kwanciya a Chan"Amma Mummy Wajen aikinafa kinsan ya kamata na koma kan aiki tunda sun mana uzurin Rashin lafiyata yanzu Dana warke ya kamata na koma"Na gama da wajen aikinka kasan daman sunsan baka da lafiya tunda har daga Chan wajen Aikin naka wasu sunje duba ka kana kwancen wannan to zatonsu har yanzu baka da lafiya sannan jiya na samu munyi waya da Matar president Akan baka da lafiya har yanzu tace babu matsala duk sanda ka warke zaka koma kan aikinka harma Bayan nan ta bani shi mai girman president d'in Shima kuma ya maimaitamun hakan akan duk sanda ka warke zaka koma kan aikinka to ai kaga bamu da matsala da wannan sannan kaga har yanzu albashinka na shigo maka duk wata "Ajiyar zuciya ya sauke Dan daman matsalarshi wajen aikice kawai ya ce " To Mummy "mummy ce ta kalli Aira ta ce " Daugher Lefenki yaza ayi dashi ina za a kai maki shi"kasa da kanta tayi a hankali ta ce "mummy duk yanda kukayi" A a a a ke zakiyi magana kinga ai hakkinkine naga sunyi yawan da bazaku iya tafiya dasu bane shawarar da na yanke zaku tafi da akwati hudu ne kawai a saka abubuwan da suka fi important sauran kuma saiki fada inda za a aje maki"cikin jin kunya ta ce "Mummy Allah duk inda kika ajesu yayi" Arman ne ya ce "bari na ari bakinta ki aje mata a wajenki kawai mummy" Kallonta mummy tayi ta ce "kinji wai abunda yace hakan yayi miki" Gyad'a mata kai tayi"To masha Allah kowa ya ce sannan Baffa ne ya d'ora musu da nasiha akan su zauna da juna lafiya da amana Inda Mummy ta dora da cewa " Ga kuma Amanar y'ata nan na baka karka sake ka b'ata mata "Murmushi Arman yayi a ranshi ya ce " Ai Mummy bani Amanar cutie ma b'ata bakice "Nan dai y'an uwa sukayi musu nasiha tukwana kowa ya nufi wajen kwananshi kama hannun Aira mummy tayi ta nufi d'akin da ta sauka Inda lefen suke Ganin Mummy ta wuce da Aira ya sanya Arman Shima komawa masaukinshi yaso ace d'akin su Maryam Aira ta koma ya samu damar kebewa da ita amma yanda yaga Mummy ta rirrike ya sanyashi bai tanka ba Suna shiga Mummy da kanta Tare da Murja da Hasina suka kama mata ta dinga fiddo akwatinan tana bud'ewa tana tambayar Aira ta fad'a abunda take buk'atar a saka mata a Wanda zasu tafi dashi Ganin kunya takeji ya sanya su Hasina tayata zaba Kaya dinkakku kala sha biyar kawai aka saka sai English wears akwati guda sunema sukafi yawa Saisu under wears da su ineer da sauran abubuwan amfanin yau da kullum Akwati Ukku Aka cika D'an Mummy tacema hud'u tayi yawa sauran abubuwan yasai mata a Chan Saida suka gama mata Parking d'in komai tukwana Mummy ta Sallami su Murja kama hannun Aira mummy tayi ta ce " d'ago ki kalleni sannan ki saurareni da kunnen basira Nasihace zan maki ta y'a da uwa ba wai surukarki ba "Aure da kikasani d'an hakuri ne Idan kin had'a da biyayya nasanki baki da matsala Aira ki k'ara akan kyawawan halayyarki Dana sanki dasu sannan ki dage da tsafta karki sake ki yarda mijinki yaga kazamtarki duk kankantarta kuwa sannan ki dage da gyaran jiki mace y'ar gyara ce Mu Kanmu manya da kika gani gyarawa muke bareku yara ki dage da tsafta iya girki,iya kwalliya,kissa da kisisina ,Jan aji namu na mata ,ki kama mijinki a hannu kam yanda bazai tabajin sha awar kallon wata a wajeba Idan bake ba sannan zaman Aure Dan hakuri ne ki gani kiji ki kauda idanu Sannan karki yarda wata ta samu kofar Rabaki da mijinki Arman yana sonki so bana wasa ba Aira ki kama mijinki kar kisa yarinta ko shirme Kinji sannan ta janyo wata leda ta bud'e ta fiddo katoton kwalbar miski ta mik'a mata ta ce " Kinga wannan farin miskine mai matuk'ar amfani karki sake kiyi wasa dashi koda ya k'are karki yarda kwalbar duk shagon da kika nuna musu zaki sameshi Ya kasance kullum kina matsi dashi kindai gane "K'asa Aira tayi da kanta cike da kunya ta gyad'a mata kai Aje kwalbar Mummy tayi sannan ta fiddo wasu magunguna cikin hikima duk ta shiga yiwa Aira bayanin yanda zatayi amfani dasu Inda ta hade mata su waje guda Dan karta manta ma rubuta mata yanda ake amfani dasu Cikin wata akwati ta sanya mata su ta ce " Kingansu nan sannan karki yarda ya gani ko yasan kina amfani dasu kinji da kunje ki samu waje ki boyesu "gyada mata kai Aira tayi tana goge hawayen da suka zubo mata Tabbas tasan tayi sa ar suruka mai kaunarta Kallonta Mummy tayi ta ce " Kiyimun alk'awarin Duka zakiyi amfani da abunda na baki "Cikin muryarta mai shirin yin kuka ta ce " Insha Allahu Mummy "wanka ta k'ara sanyata tayo da ruwan turarruka Bayan ta fito ta sanya slepping dress Gado Mummy ta ce ta kwanta sannan tace ki huta sosai saboda Kinga gobe zakuyi tafiya bacci ne me dadi ya d'auke Aira Bangaren ARMAN ko kusan kwana yayi yana Sallar Godiya da ubangiji .
Washegari k'arfe Goma sha d'aya tayi musu a Airport Mummy ta rik'e hannun Aira sosai Aira tayi kyau cikin tsatsadar laffaya black kunsan yanda bakin abu yakeyiwa fari sosai tayi kyau haskenta ya k'ara fitowa sanye take da dogon takalmi Fuskarta a rufe itama mummyn sanye take cikin laffaya itakuma fara itama Sosai tayi kyau shikuma Arman sosai ya hakimce cikin babbar riga milk koban fad'a kyau da tsadar shaddarba kunsandai Arman baya sa karamun kaya sannan baya rainanniyar shiga fadar kyaun da sukayi ma bata nakine a lokacin sosai aka shiga daukarsu hotuna Wanda saboda tarihi ake d'auka badan ayi post ba Su Baffa ma da su Gwaggo sunyi musu rakiya tare da kannen Mamy jirginsu zai tashi har amfara kiraye kirayen suna Hakan ya sanya Arman ya fara bankwana da iyayen nashi har k'asa ya durkusa ya tab'a k'afar Mummy murmushi tayi tare da tasoshi ta shafa kanshi ta ce "Allah yayi mukua albarka ya sanya Albarka a cikin rayuwar aurenku ya sanya badi ya haka suna mukazo ina Kara fad'a maka dai ka rik'emun y'a amana" murmushi Yayi ya ce "Amen nagode Mummy bazan tab'a gajiya da gode maki ba mungode insha Allahu kuma zanrike maki y'a da amana"had'a hannunshi da na Aira Mummy tayi ya ce " Allah yayi muku Albarka ku rik'e juna da amana "Rungume Mummy Aira tayi ganin za a tafi ta fashe da kuka " Daddab'a bayanta Mummy ta fara cikin sigar lallashi ta ce "Kiyi shiru kinji Daugher Allah muku Albarka kuje jirginku zai tashi Insha Allah idan na samu dama zandinga zuwa ganinku Allah muku Albarka" Cikin shashekar kuka Aira tace "Mungode Mummy Allah saka maki da gidan Aljanna bamu da bakin da zamu iya gode maki Ked'in uwace ta gari Mummy " ta k'arasa fad'a cikin kuka "Duk yanda Mummy taso daurewa saida suka sanyata kuka Dak'yal Arman ya samu ya raba Aira da Mummy Wanda Shima ji yake kamar yayi kukan har suka shiga jirgi Mummy na Daga musu hannu Shima yanayi mata bye bye Airako tana jikinshi tana mashi kuka ko a jirginma dak'yal ya samu ya lallasheta tayi shiru kasancewar kujerarsu na kusa na juna ya sanyata Lafewa a jikinshi ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga sararin samaniya...✍🏿

*Kibiya ki karanta cikin kwanciyar hankali akan Naira 200 kachal 07026166536*



_*Miss Hajo ce*_πŸ€™πŸΏ
[7/14, 12:43] Hajo hajo: πŸ…ΏοΈ.........*97&98*




.....Lagos

37 / 54