NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   32 / 54

93K to 96K   out of 160.7K words

sha d'aya tayi saida Arman ya duba agogo wara idanu yayi ya ce "Maza cutie tashi ki koma kalli agogo " Turo baki tayi ta ce "Ni nan zan kwana" wara idanu yayi sai kuma yayi murmushi ya ce "Kiyi hakuri ki koma ciki ai koda yaushe muna tare banason a fara samun matsala tun ba Aje ko ina ba" tana gunguni Aira ta mik'e Shidai lallab'ata yake Shi ya rakota har wajen Haske tukwana ya juya tana waiwayen shi Harta k'arasa part d'insu Arman tun a hanya ya fara istighfari Dan yasan a yanzu Aira da Auren wani a kanta amma babu yanda zai iya da zuciyarshi D'aga hannu yayi ya ce "ya Allah ina neman gafara da yafiyarka ya Allah na kasa jurewa ne a kanta koda ya koma ya kwanta bacci mai dadine yayi awon gaba dashi saboda tsananin farincikin da yake ciki Airako koda ta koma cikin sand'a ta shiga gidan Allah ya taimaketa ba kowa kowa yana Dakinsu cikin sand'a ta nufi part d'inta tana shiga ta sauke ajiyar zuciya Cike da farinciki ranar tayi baccin da har ta manta rabon da tayi bacci cikin kwanciyar hankali haka y'an gidan ko kasancewar sunsan Aira gwanar zaman dakice ta kulle kanta ya sanya basu damu da Rashin ganin nata ba Alhaji Yusuf ko lokacin daman dakin Hajiya saude yake kuma fushi yake da Airar ya sanya baibi ko ta kanta ba washegari Aira cikin farinciki ta tashi Wanda har Laila saida ta gane hakan tambayar ta tayi ta ce " wai Sis ya akayi yau naganki cikin farinciki Dariya Aira tayi ta ce "kawai Hakanan nima najini cikin farinciki" Dariya Laila tayi ta ce "kodai Anfara son dadynmune" Harara Aira ta galla mata tare da tilla mata Pillow ta ce y'ar air kawai"Murmushi tayi tukwana sukaci gaba hira Arman ko Alhaji Yusuf ne ya kawo mashi wasu kaya Zasukai kala shida ya ce "ga shi ya dinga sawa Ya daina shigar buzayen" Godiya yayi mishi a yana fita ya ja tsaki tare da Wulli da kayan wai yau shine ARMAN har wani banza zai bashi jace"Saikuma yayi murmushi ya ce "a saboda so ne Ai " Hakan ya karamai kwarin gwuiwar Dan bayajin ciwon kome zaiyi kome zai sameshi indai a soyayyar Aira ne daga kayan yayi yaga suna da tsafta kuma basu sha jikiba kamar sabbi Tsaki yaja Dan daman ya gaji da kayan buzayen koda yayi wanka shiryawa yayi cikin wani black yadi da yasha d'inkin Kufta sosai ya fito yayi kyau ya dawo asalin Arman d'inshi koda ya fito domin kai Laila school kasa Daina Kallonshi yayi Wanda har saida yaja tsaki shiyadawo da ita daga duniyar tunanin data Lula sosai ya tafi da imaninta Dan ita a yanda ta ganshi baiyi mata kama da driver ba kwata kwata ya koma kamar wani basarake ko kuma hamshak'i Dan yanayin fatarshima daka gani kasan Hutu ya zauna a ciki da wannan tunanin har ya kaita school koda ya maido da ita d'akin Aira ta nufa a lokacin tana linke kayanta kamo hannunta tayi ta ce "Sis wai kinsan wani abun mamaki kuwa wlh sabon driver d'innan kwata kwata baiyi kama da kaskantacce ba Karkiga yau da yasa kayan hausawa yanda yayi masifar kyau har tuntube nasoyi Dan Kallonshi Gaskiya guy din ya had'u wlh tunda nake bantab'a ganin guy me kyanshi ba sis Kinga kuwa fatarshima kuwa Yanda take shining Gaskiya guy d'innan ya had'u iya had'uwa Dan a ko novel da nake karantawa yanda ake zuzuta mazan novels to zan iya ce maki wannan yafi Namijin novels kyau tak'amaimai dai in fad'a maki sis Ki kirashi da mijin novel kawai (lol😝)Dan yakai duk Inda baki tunani.Sosai Aira taji wani wutar kishi na taso mata wai Arman dintane wata mace ke yabawa haka lokaci guda taji tsanar Laila tatsargu cikin zuciyarta Danne b'acin ranta tayi da zafin da takejin cikin zuciyarta ta ce " Uhm su Laila manya"Harararta Laila tayi ta ce "haka ma zakice wai meyasa jiyama na kawo maki maganarsa kin shareni" Tab'e baki Aira tayi ta ce "To me kikeson nace maki Laila" Bata fuska tayi ta ce "Tayani zakiyi ko zanji dadi sannan ki bani shawara Dan wlh sonshi nake" A matuk'ar zabure Aira ta mik'e ta ce "so so fa kika ce Laila" Da mamaki Laila take kallonta ta ce "Meye naga kin tada jijiyoyin wuya saikace wacce ta ce tana son mijinki"ko saurayinki ?Rumtse ido Aira tayi ganin zatayi baram baramma ya sanyata saurin gyarawa ta ce "Amma dai Laila baki da hankali ki rasa Wanda zakiso sai Wanda yake K'ark'ashin mahaifinki driver d'inki ne fa Haba Is not your class ke ai Matar manyace" Ajiyar zuciya Laila ta sauke ta ce "Daman a saboda wannan ne ni har kin tsoratani Ai ba wani Abu bane Dan kaso Wanda yake k'asa dakai Sai Abba ya mayar dashi mai kud'in wannan ba wani Abu bane tunda dai ina sonshi nasan shima zai soni ta fad'a tare da tashi tace “Kinga bari naje na watsa ruwa na Shawo rana" Tana fita Aira taja dogon tsaki tare da Wulli da Kayan linkin ta ce "Chabd'i wlh bazai yuba Kujimun wani sabon iskancin Tama rasa Wanda zataso sai Arman d'ina Wanda mallakin nawa ni kad'ai sosai ta karajin tsanar Laila a ranta kasa daurewa tayi cike da jin Haushi tana cika tana batsewa ta fito farfajiyar gidan Hangoshi tayi a wajen parking space Shima ita yake kallo yana mamakin yanda ta wani had'e rai wajenshi ta k'arasa yana ganin haka yayi saurin janta wajen lambu Dan kar a gansu kallonta yayi cike da kulawa ya ce " Yadai naganki haka my prince's me ya faru"Kama k'ugu tayi tare da turo baki ta ce "Nidai Gaskiya Yaya daga yau karka k'ara kai Laila school banason ganinka da ita cewafa tayi tana sonka dan iskanci" Shi maganar ma dariya taso ba Arman saida ya d'an dara tukwana ya ce "Ummm cutie manya Wannan kishi haka kamar zaki tashi sama" Harara ta galla mai ta ce "wasa ka d'auka ko?Kama hannunta yayi ya ce " inbanda abunki cutie ina ruwana da ita keda kikasan halina ai Saidai kiba wani labarina Me zanyi da wata Gaki kalloma ni bata isheni ba haryau bazan iya ce miki ga kalartaba saboda ko kallonta ban tab'a yiba calm down ki nutsu karki damu da wannan kisa a ranki danke kad'ai akayini " Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da turo baki ta ce "To nidai na k'agara mu tafi mu bar garin nan yaya" gyara mata gashin kanta yayi da ya bazo ya ce "Karki damu akwai lokaci ai" Sun tab'a Hira sosai a nan Saida Aira ta Hango Motar Daddy Ya sanyata tashi cikin Sauri ta bar wajen shikuma Arman ya koma BQ.
Kullum Arman da Aira saisun kebe sun zuba love d'insu kamar saurayi da budurwa Dan Arman mancewa ma yake da Akwai Aure a kanta itako Aira daman bata daukin Auren da komai ba Dan bata tabajin kanta a Matar Aure ba Satin Arman guda kenan Kullum saisun had'u batare da wani ya tab'a ganinsuba Dan Daddy yayi tafiya kwana huduma bare ya takurawa Aira ranar da ya dawo Aira Sun shirya fita da Arman Ta rasa yanda zata tambayi Daddy haka nan tayi shahada ta je palourn da yake yana zaune yana shan fruit nesa dashi ta tsaya tana wasa da zoben hannunta shiko tunda ta shigo ya zuba mata Idanu ba ko k'iftawa sun kai minti biyar ba Wanda ya ce uffan da kyal Aira ta iya d'ago baki ta ce "Ina yini Daddy andawo lafiya" Ajiyar zuciya tajo ya sauke Tare da cewa "Alhamdulilla my Beauty kin fara hankali ko" Tsaki Aira taja a ranta a fili kuwa murmushi tayi Wanda baikai cikiba sosai Alh Yusuf yayi farinciki ya ce "Inaga beauty ta hakura " Cikin y'ar in ina ta ce "Uhm Uhm Daddy Daman fita nake so nayi tunda nazo banje ko ina ba gashi ina son naga gari" Cikin fara a ya ce "Ai ba matsala Beauty gashi na gaji ai dani da kaina ma zan kaiki Na kaiki ko ina amma ba matsala Bari nayiwa driver magana saiya kaiki duk Inda kikeso Ko" Hamdala Aira tayi a cikin ranta Murmushi tayi tare da mik'ewa ta ce "Thnks Daddy Bari naje na shirya" murmushi yayi ya ce "Bazaki daina Cemun wannan daddyn ba ko" k'asa da kanta tayi tare da barin D'akin cikin Sauri ta shirya cikin Abaya doguwar Riga black da tayi mugun amsarta ta yafa belt din rigar sosai yayi mata kyau Ga gaban lallausan gashin kanta da ya kwanta ya fito Tunda ta fito Alhaji ya kafeta da idanu bako k'iftawa sosai yake godewa Allah daya bashi zuk'ek'iyar mata kama hannunta yayi ya ce "kinyi kyau my baby" Sosai Aira taji haushin rik'e mata hannu da tayi Dan ba yanda zatayi a tare suka fito shida ita hannunsu rik'e Dana juna Arman dake cikin mota tunda ya hangosu yaji wani irin bak'inciki Ya mamayeshi Ji yake kamar yaje ya fisge Aira daga hannun Alhaji Yusuf Rumtse idanunshi yayi da karfi Dan bai buk'atar Kara ganinsu har mota Alhaji ya kai Aira tare da bude mata back sit ya sanyata Tare da rufewa zagayawa yayi ya kalli Arman ya ce "Ka bimun ita a hankali kaji Dan daman ya fad'a mashi Inda zai kaita sannan ya bashi kudade dan ya mata sayayyar abunda take buk'ata Dak'yal Arman ya iya d'aga baki ya ce " To tare da Jan motar Horn yayi mai gadi yazo ya bud'e masu a guje sukabar gidan........✍🏿




_*miss hajo_*🤙🏿
[7/5, 22:01] Hajo hajo: 🅿️.........*83&84*





.....A guje suka bar gidan Aira har tsoron gudun da ya sharara tayi Sun d'an bar layin taji ya tsaya ba tare da ya kalletaba ya ce "Dawo gaba" A sanyaye ta fito ta koma gaba tare da rufe k'ofar Kallonshi tayi taga yanda ta had'e girar sama da ta kasa a hankali ta ce "Ina yini Yaya" Ba tare da ya kalletaba ya ce "Lafiya" Cike da nuna Rashin jin dad'i ta ce "Yaya ko nayi maka wanin abun naga kana b'ata rai" Kallonta yayi yaga yanda tayi bala in kyau lokaci guda yaji tsananin kishinta na k'ara ninkuwa cikin zuciyarshi tab'e baki yayi ya ce "Shine Dan ki nunamun kinyi Aure hada Fitowa hannunki mak'ale da nashi ?Cikin marairaicewa ta ce " Yaya nima bani nace ya rik'emun ba Bafa kuma nima banso ya rik'emun hannuba abunda yasama na Kyaleshi Dan Karya hanamu fita"Uhm kawai ya ce Tare da lalubo Wayarshi itadai Aira ta zuba mashi idanu bako k'iftawa Dan idan tana Kallonshi ji take kamar za a kwace mata shi Arman musa ya kira yayi mashi kwatancen Inda suke Ya shaida mashi gashinan yana kashe wayar kallon Aira yayi da ta zuba masa idanu hura mata iska yayi a idanu tare da cewa "wannan kallo haka ai saiki cinyeni" Firgit ta dawo cikin hankalinta tare da turo baki ta ce "Kai yaya saikace mayya" Zan Bugi bakin fa"Dariya tayi ta ce "Sorry my yaya" kinyi kyau cutie"Murmushi tayi tare da K'asa da kanta ta ce "thnks kaima kayi kyau my yaya " sosai suka shiga hira da labarai Wanda har saida ta mantar da Arman haushin da yakeji a haka musa ya samesu Kallon Aira yayi ya ce "Amma fa Gaskiya Kin rikitamun aboki da yawa kin zautashi Kotu ta kamaki ba k'aramun hukunci zata yanke maki ba " murmushi Aira tayi tare da K'asa da kanta "Kallon Arman yayi ya ce " Ammafa Abokina ba k'arya dole ka zauce ko nine na samu wannan zanyi abunda yafi naka"Wata irin harara Arman ya banka masa tare da cewa "ka iya bakinka wlh Wama yasa ka kallemun ita Dan sa ido kawai " Dariya musa yayi ya ce "Maida wukar yanzu dai ina ne za a Naji kiran gaggawa" wajen shakatawa za a kai cutie to kasan bansan ko ina a garin nan ba shine na kiraka ka mana jagora"Musa yayi musu rakiya duk wani wajen shakatawa yayinda Arman yayi wulli da kud'in da Alh Madugu ya bashi akan yayiwa Aira sayayya itadai Aira batace uffan ba Dan Tasan halin kayanta saida lallamo sosai suka shakata suka sha love d'insu kamar saurayi da budurwa Sune basu koma gida ba sai wajen isha'i sosai Aira take nishad'i Suna komawa Aira ta fito tana Dariya Shima Arman ya fito yana fara'a Daidai lokacin da laila ta lek'o da mamaki take kallonsu Sosai gaban Aira ya fad'i Arman ko fusgewa yayi cike da fargaba Aira ta nufi Inda Laila take ta ce "Ina zuwa sis" Bako ina Laila ta bata amsa tare da komawa ciki tana tunanin Me ya maida Aira gidan Gaba ?sannan tunda tazo bataga fara'arta buzu ba (Dan haka suka samai suna saboda basusan sunanshi ba Kuma babu Wanda ya tambayeshi game da sunanshi ko Tarihin shi) amma yanzu shine ta gani yana Dariya sannan tunda aira tazo garin nan bata taba sha'awar fita wani wajeba sai zuwan buzun nan zuciyarta chunkushe da tunani Aira ko tabe baki tayi tashigewarta Takoyi sa a Daddy bayanan tun daga lokacin nan Laila ta sanya musu ido Yayinda su kuma harkar gabansu suke ga kirkirar zuwa shopping ko saloon da Aira take tarka Wanda Daddy yake sanya Arman ya kaita sosai sukeshan love d'insu batare da sanin kowaba amma kuma ko hannunta yanzu arman baya yarda ya taba saboda yasan haramun ne tunda da igiyar wani a kanta ko rungumarsa tazoyi kaucewa yake hakan yasa itama tadaina yunkurin fadawa jikinshi Wanda Laila duk tana ankare da hakan hakan yasa yanzu sama sama takeyiwa Aira itako hakan bai dameta ba saboda yanzu Arman ya maye mata gurbin kowa data rasa hakan yasa hankalinta kwanciya a haka har Arman yayi wata guda a gidan yau Aira tana d'akin Arman suna ta shan Hira har Sha biyun dare tayi batare da sun sani ba saida suka Ankara tukwana Aira ta baro BQ din cikin sand'a ta shiga cikin gidan Kichibus sukayi da Laila dake kokarin shiga kitchen Dan harta kwanta bacci taji yunwa hakan ya sanyata zuwa ta had'a tea Sosai cikin Aira ya d'uri ruwa cike da Kallon tuhuma Laila ta bita ta ce "Daga ina kike da Daren nan ke kuma" Cikin muryar Rashin Gaskiya Aira ta fara in ina saikuma ta ce "Uhm mura ce ta kamani wlh shine na D'an lek'a na ga ko naga Wanda zai sayo man magani" tunda ta fara maganar Laila tasan karya take tab'e baki tayi ta ce "hmmmmmm " Tare da shigewa kitchen Aira ko tsaki taja tare da Wucewa d'akinta Tana zuwa ta iske Alh Yusuf sai safa da marwa yake Sosai ta tsorata Juyowa yayi cikin b'acin rai tare da daka mata Tsawa ya ce "Daga ina kike" Sosai Aira ta rude cikin in ina tace ba ko ina yanzu na fita fa"na kusa awa d'aya a d'akin nan shine zakicemun yanzu kike fita daga gidan ubanwa Kike"Ganin ya na hayayyak'o mata ya sanya ta murgudamai baki tare da Jan tsaki Saurin Juyawa da gudu tayi bedroom d'in Laila kallonta Laila tayi ta ce "Lafiya kuwa" rufo d'akin tayi ta ce "Nan zan kwana tare da nufar gadon ta kwanta" Mamaki duk ya gama cika Laila Tab'e baki tayi tare da Gama shan tea d'inta itama taja ta kwanta a lokacin Bacci har ya d'auki Aira washegari koda ta tashi bataga Laila ba fitowa tayi a palour ta tarar da Mama tare da Daddy da ya kura mata Idanu kasa tayi da kanta ta ce "Ina kwana Mama" ba yabo ba fallasa ta amsa Da lafiya Qalau"Kallonshi tayi ta ce "Ina kwana" Lafiya qalau my Beauty Kintashi lafiya"Harara Mama ta gallamai tare da Jan tsaki Aira ko alhmdll kawai ta ce ta wuce cikin Sauri sosai tayi mamakin yanda bai mata magana akan jiya ina taje,
Da Yamma Aira na zaune a lambu sai Hirarsu sukesha Dan wajen babu kowa Aira hira tayi dad'i ta d'ora kanta saman kafad'arshi duk yanda Arman yayi ta tadashi kiyawa tayi "Aira ce ta ce " wai yaya zaman me muke haka har yanzu kak'i sama mana mafitar da zai sakeni ni wlh nagaji yanzu fa watana ya kusa hud'u gidannan ni wlh na gaji "Nima tunanin hakan kawai nake my cutie Saidai kuma har yanzu na kasa Nemo mana mafitar da zai sakeki din muje muyi Auren mu nafiki damuwa da hakan cutie Dan bakisan yanda nake kishin zamanki a gidan nan ba"Lumshe ido Aira tayi ta ce " Uhm My yaya wai ina Mummy Dan Allah kiramun ita nayi kewarta " cutie kenan so kikema su gane muna tare asirinmu ya tonu Bayan na baki labarin ta yanda na taho ai ko sim d'ina sabo na sauya saboda karma a nemeni a wancen Dan nasan Mummy zata neme ni"dafe goshi Aira tayi ta ce "Kuma fa hakane Amma fa yaya nayi mamakin dabarar nan taka Gaskiya kaid'in na musamman ne basirarka tayi yawa" Murmushi yayi tare da shafa kanta ya ce "Ko my Quen " Murmushi tayi tare da Lafewa jikinshi ta ce "Eh mana my Zuma na" Wara idanu yayi tare da cewa "Wow Yau na samu sabon suna kenan" Dariya tayi tare da rufe fuska Hango Laila Da Aira tayi tana nufo wajen ya sanyata saurin tashi gabanta na fad'uwa duk ta rikice sai sannan Arman ya lura Inda take kallo tsaki yaja tare da saurin barin wajen Laila ko tana isowa da wani irin banzan kallo ta dinga bin Aira dashi Tare da Jan tsaki ta ce "a juri zuwa rafi dai kuma ki sani a tafin hannuna kike yawo zanga gudun ruwanki idiot kawai da Aurenki da komai" Da mamaki Aira take kallonta ta ce "Me kike nufi wai " duk yanda kika d'auka "Tsaki Aira taja ta ce " Kanki akeji "Tare da barin Wajen Laila ko cike da b'acin rai Ta koma ciki tare da zuwa d'akin mamanta ta na hak'i ta ce Wlh Mama akwai matsala gidan nan" wace matsala kenan Laila?"Mama

32 / 54