Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
a kusa da ita hakan yasa tunda ya tashi ya shiga damuwa yinin ranar bai samu ya leko ko palour ba saboda azabar ciwon da kanshi ke mashi Sosai ya zurfafa tunanin Aira Inda daga karshe ya yanke shawarar da yake tunanin indai yabita idan yaci sa a zata b'ulleshi a lokacin karfe Tara na dare Mikewa yayi kamar Wanda aka zabura cikin Sauri ya d'aga locker Kayanshi Tare da bude k'aramar had'ad'd'iyar box dinshi Kala hud'u ya sanya cikin Kayanshi Tare da saka abunda yake ganin zai buk'ata na yau da kullum Yana gamawa ya ja akwatin ya rufe takarta da biro ya ciro tare da zaunawa ya fara rubutun doguwar wasik'a yana gamawa ya linke sannan ya k'ara bud'e wata ya sake wani rubutun Wanda baikai na wancen ba Shima ya linke saida ya lek'o palour yaga ba kowa Ajiyar zuciya ya sauke tare da saurin komawa yaje ya janyo akwatinshi harya fita daga Part d'insu bai hadu da koawaba saida ya fito ne yaci karo da securities D'aya daga cikinsu ta nufa wajenshi Wanda yasan Daddy Ya aminta dashi fuskarshi a daure danma kar wani cikinsu yayi mashi wata tambayar rainin hankali cike da gadara ya je ya mik'awa security d'in tare da mik'a mashi takaddun nan guda biyu ya ce "Gashi gobe da safe ka bawa Daddy d'ayar kuma Mummy zaka bawa"to ranka ya dad'e zan kai musu amma ina kake shirin zuwa da Daren nan na ganka kamar kana shirin tafiya" wani banzan kallo Arman ya watsa mashi tare da cewa "is not your business " yana gama fad'ar haka ya kira d'aya daga cikin driver d'in gidan umartarshi yayi da ya sanya mishi akwatinshi cikin boot din motar sannan ya bud'ewa Arman back sit ya shiga Shima ya shiga ya tada mota cike da girmamawa ya ce "ranka ya dad'e ina muka nufa" Airport zaka kaini"Koda suka isa airport Bayan driver ya fitowa da Arman da akwatinshi Kallon Arman yayi ya ce "Allah ya tsare hanya ranka ya dad'e " Ameen Arman ya fad'a tare da cewa"duk Wanda ya tambayeka Inda ka kaini kada ka bashi amsa a Daren nan ka fad'awa wani ka kawoni Airport kaima kasan sauran"insha Allahu hakan bazata faru ba ranka ya dad'e a dawo lafiya"Arman bai Kara cewa komai ba ya bar wajen cikin k'ank'anin lokaci aka shirya mishi tafiya sokoto kamar yanda ya umarta Dan a lokacin ma babu jirgin da zaije sokoto mak'udan Kud'i Arman ya kashe Dan bayason ya k'ara kwana d'aya a garin nan ba tare da ya isa garin da masoyiyarshi take ba ba ayi 1 hour ba jirginsu ya d'aga sokoto Wanda cikin k'ank'anin lokaci suka isa a lokacin kusan 11pm saura Koda suka isa a hankali Arman ya dinga Saukowa Daga benen jirgin Wani farinciki da annashuwa ya mamayeshi harya gama Saukowa k'ayaitaccen murmushi ya saki ya ce "Yau Gani a garin da ban tab'a mafarkin zuwa ba Amma soyayya ta kawo ni Alhmdllh yau gani garin da masoyiyata Take cikinshi a halin yanzu nima ina cikinshi Tabbas Gaskiya ne da y'an magana sukace Garin masoyi baya nisa..........โ๐ฟ
*Garin masoyi baya nisa๐๐๐๐๐juyo ki ganni gani a kusa๐๐๐๐a kanki ba abunda zana fasa๐
๐
ba Wanda Zai magana in jisa...๐
ku k'arasa da kanku Fans aikin nan naku ne*๐๐๐
*Shafin nan na sadaukar dashine ga kungiyata daya tamkar da dubu jarumai Writerโs Association bisa ga cikarta shekara biyu da kafuwa Allah ubangiji ya kara daukaka wannan kungiya mai albarka tare da jaruman dake cikinta yan uwa da suka tayamu murnar anniversary muna godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci*
*_Miss Hajo Ce_*๐ค๐ฟ
[7/4, 15:35] Hajo hajo: ๐
ฟ๏ธ.........*79&80*
Garin masoyi baya nisa wani farincikine yaji ya mamaye zuciyarshi ji yake ai matsalarshima ta kusa zuwa karshe tunda dai gashi a garin da masoyiyarshi take cikinshi Tunani yayi yanzu ina zai dosa shida bai tab'a zuwa garinba baisan ko ina ba na garin wani abokinshine musa ya fad'o masa a rai Wanda sukayi karatu a Misra d'an sokoto ne Wayarshi ya lalabo tare da kunnawa Dan tajima kashe Contact d'inshi ya shiga ya shiga laluben sunan Cikin sa a kusa yaga yana da number Dannawa number kira yayi kiran farko saida ya katse a na biyu aka d'auka Daga d'ayan b'angaren musa ya ce "Yau wace rana ce wannan Arman ka kirani da kanka kaida ka yada mutane" Murmushin da baikai ciki ba Arman yayi ya ce "Yau Juma a kaga ko babbar rana ce Shiyasa" hhhh Gaskiya ne manyan k'asa to ya garin"Alhamdulilla Yanzu haka ina garinku shine nace bari na kiraka kazo ka d'aukeni ina Aiport"Cike da mamaki musa ya ce "da gaske Abokina ko wasa" da gaske mana muntaba wasan nan haka dakai da Allah Malam kazo ina Aiport bansan doguwar magana"Murmushi musa yayi ya ce "Har yanzu halin nan naka na nan kenan Abokina Gaskiya nid'in yau d'an baiwa ne mr Arman guda a garinmu gani nan zuwa yanzu yanzu" murmushi kawai ARMAN yayi ya ce "Saikazo ina jiranka" tukwana ya katse wayar minti Ashirin me kyau tayiwa musa a aiport Sosai yayi mamakin ganin Arman Rungume juna sukayi cike da farincikin sake ganin juna Dan rabon da su had'u tun a makaranta musa da kanshi ya sanyawa Arman jakarshi a boot Bayan Arman ya shiga Shima ya shiga ya jasu suka nufi hanya Kallonshi Arman yayi ya ce "Hotel zaka kaini" Hotel kuma Abokina Nazata ai gidana zaka sauka?A a ka kaini hotel me kyau kawai "ka bari yanzu ka fara sauka gidana muje ka huta kaga harna sanya iyalina Ta yi maka girki" da mamaki Arman ya ce "Wai kana nufin har kayi auri" Dariya musa yayi ya ce "Hada yara ma biyu kuwa zauna anan har tsufa ya fara kama
Ka" Murmushi Kad'an ARMAN yayi ya ce "Soon nima zanyi Saidai kuji a bazata" To Allah ya yarda Kace ka fara soyayya kenan Dan a sanin da maka ko kallon mata bakayi "ai soyayyar ce ma ka kawoni garin nan harka samu ganina?da mamaki Musa ya ce " kana nufin wai saboda budurwa kazo garinnan"of course "ya fad'a yana basarwa "da mamaki Musa ya ce 'Chabd'i amma wannan wace y'ar baiwarce nan garin take kenan" cikin kosawa da magana Arman ya ce "Nifa bazan iya da surutunka ba kamar mace gobe mayi Maganar" Dariya musa yayi ya ce "bazaka chanza ba Abokina?Kaima bazaka tab'a chanzawa ba " Arman ya fad'a yana kallon hanyar da ssukebi har suka isa gidan musa cikin girmamawa matarshi ta tarbi Arman tare da ajemai drinks kala kala Kad'an yasha baijima ba musa ya wuce dashi wani
hotel dake ba nisa dasu Bayan Arman ya biya daki Musa ya koma gida da niyyar gobe zai dawo suyi magana Arman kasancewar akwai gajiya tattare dashi sosai yayi baccin da ya jima baiyi irinshi ba Dan jinshi yake cikin Wace irin nutsuwa marar musaltuwa.
Da sassafe Mummy da Daddy na break fast Daddy yayi shirin Tafiya office Security ya shigo Bayan ambashi izinin shigowa saida ya bari suka gama sun fito palour ya Gaishesu cikin mutuntawa suka Amsa Mik'a wa Daddy takardar yayi ya ce "ga shi Ranka ya dad'e ya bani jiya da dare akan yau da safe na kawo muku" Amsa Daddy yayi da mamaki Dan yasan Arman ne suke ceman ranka ya dad'e sannan ya kalli Mummy ya ce "gashi kema Hajiya ya ce Wannan a baki" Da mamaki Mummy ta amsa Sallamarshi sukayi ya zuya ya tafi Daddy ne ya fara bud'e takardar cin karo da dogon rubutu da yayi kuma note d'in Arman Cikin k'asa da murya ya fara karantawa kamar haka " ```Assalamu alaikum Mahaifina na rubuta maka wannan letter badan komai ba saidan fitar daku daga wasi wasin ina na tafi na bar garin nan tafiya mai nisa ka gafarceni mahaifina bazan iya Aurar wacce ka zab'a munba ni namiji ne ina da right d'in kaina Dan haka idan ma kun d'aura na saketa saki Ukku I m so Sorrry my dear father karkayi fushi dani duk sanda ka huce zandawo gareku daga tilon d'anka Mujahed Kabir``` sosai Daddy Ya shiga rud'u da tashin hankali da tsananin b'acin rai Bayan ya gama karanta takkadar cikin bakin ciki ya ce "Ni Arman zai kunyatani,ni zai nunawa ban isa dashi ba Aiko kamar yanda yabar gidan nan yakiyimun biyayya ya barshi har abada bani bashi" cike da damuwa Mummy ta ce "Alh lafiya me Arman din yayi tana rik'e da takardar dake hannunta tama kasa karantawa" Cike da b'acin rai ya ce "Guduwa yayi Amshi ki karanta abunda Ya rubuto mun " Amsa Mummy tayi hannunta na karkarea tsabar rud'u tana gama karantawa ta fashe da kuka ta ce "Shikenan Alh ka sanya ya gudu Arman me yasa zaka mana haka me yasa " ta k'arasa fad'a tare da bude takardar da ya rubuto mata hannunta har karkarwa yake ta fara karantawa kamar haka "```Assalamu alaikum Mahaifiyata d'aya tilo da babu kamarta a duniya ina mai baki hakurin Tafiya da nayi please Mummy ki gafarceni ki yafemun nayi hakan ne badan komai ba saidan nemawa kaina y'anci nasan ke uwace kuma bazakiso wani Abu ya samu d'ankiba ki tayani da addua tare da sanyamun albarka Tabbas albarki ita ce kawai abunda nake buk'ata a koda yaushe sannan ina rokanki akan karki tayar da hankalinki please mummy nah kada ki shiga damuwa a saboda ni ni ba yaro bane bazan shiga wani hali ba I love so much I really love you so much My first love```sosai Mummy take kuka Bayan ta gama karantawa ta ce " me yasa zakayimun haka ARMAN ka gudu ka barni Bayan kasan irin tarin k'aunar da nake maka me yasa zaka zabi guduwa ka barni amma bakomai a duk Inda kake Allah ubangiji ya tsare munkai yayi maka Albarka "Cikin b'acin rai Daddy yabar gidan tare da fushin Arman Mummy ko number Arman ta dinga dialing amma a kashe Tasha kukanta Har ta gode Allah sannan ta bishi da Addu'ar Allah ha tsare matarshi aduk Inda yake daddyko hakuri yabawa Abban husna sannan yace subar duk abinda ya kashe har lefen yabar musu bainuna mishi komai ba Abban husna yace Allah sa haka shi yafi alkhairi ..
Yau Aira ita kad'ai a gidan Laila ta tafi school Suna da evening lectures yayinda Daddy baya nan Mama ta fita biki a palour ta yini tana kallo cike da kad'aici kad'aicin ne ya isheta ya sanyata fitowa Farfajiyar gidan Hakanan yau take jinta cikin y'ar annashuwa da ta rasa dalili Sosai ta fad'a duniyar tunani gata nan ita da ARMAN sun zama miji da mata ya kaita bitch sai wasan ruwa suke haka dai tayi ta wasik'ar jakkanta ita kadai daga karshe kuma ta hade kanta da gwuiwa ta fashe da kuka inama ace tunaninta ya zama Gaskiya,ina ma ace Yau Arman ne mijinta,Sosai take kuka daga karshe ta Goge hawayenta tare da mik'ewa D'anta koma ciki taga ana kiraye kirayen magriba tana Mikewa taga Mubarak a gabanta kamar Wanda Yasha ya Bugu" Tsoro ya bata hakan ya sanyata saurin kaucewa zata tafi saurin shan gabanta yayi ya ce "Haba my Beauty ina kuma zaki Bayan saboda ke nazo nan d'in" ya fad'a cikin muryar bugaggu"Cike da b'acin rai Aira ta ce "Ka matsa ka bani hanya nace" k'ara wara hannunshi yayi tare da tare mata hanya ya ce "Bazan matsaba ya fad'a ya na kamo hannunta" Kallonshi Aira tayi ta kalli hannunshi wani mugun b'acin Raine ya zo mata Ta fusge hannunta Tare da wankeshi da Mari "rik'e kumcinshi Mubarak yayi ya ce " ni ni ni kika Mara"An marekad'in d'an iskan banza marar mutunci "" d'aga hannu Mubarak yayi zai shararawa Aira Mari yaji an rik'e hannunshi ta baya Tare daukeshi da Mari"Da mamaki Aira take kallon Sadiq da idanunshi suka fara sauya launi tsabar bacin rai"Kallonshi Mubarak yayi ya ce "Ni ka Mara" An mareka Dan ubanka marar mutunci Matar uban naka zaka tara harkayi kokarin marinta Dan kana Dan iska marar mutunci"Cije baki Mubarak yayi yana jin zafin Marin da yasha biyu tare da Kallon Aira yayi mata nuni da yatsa ya ce "zamu had'e Dan ubanki" Sadiq ne zai k'ara kai mishi wani Marin yayi saurin barin wajen Dan Duk iskancinshi yana shakkar Sadiq "Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da K'asa da kanta ta ce " na gode mai sunan Abba"Badamuwa Aira kiyi hakuri haka yake baida d'a a ki dinga kiyayewa idan kin ganshi kinji"gyada mishi kai Aira tayi tana Hawaye"Sosai yayi mamakin hawayen dake zubowa daga idanunta ya ce "Kukan me kike Aira ko wani abun ya faru ne" Girgiza mashi kai tayi tana Hawaye ta ce "Dan Allah Mai sunan Abba ka sanya Daddynku ya maidani gidanmu"da mamaki Sadiq yake kallonta ya ce " gidanku kuma Keda kikazo Aure Aira "Kuka Aira ta fashe dashi " Wlh Auren dole ne akayimun da Daddynku bana sonshi ina da Wanda nakeso Kawai Dan yana abokin Abba shine ya aura munshi "ta fad'a tana rushewa da kuka"Sosai Sadiq yayi mamaki Dan saiyau ya tabโajin maganar nan ya ce "da gaske kike Aira Haba ai konima kaina nayi mamakin da kika auri Daddy " Cikin kuka ta ce "Dan Allah kasa ya sakeni ko kai ka maidani gidanmu nasan kai kana da tausayi mai sunan Abba" Numfasawa Sadiq yayi tare da cewa"Bani da ikon da zansa Daddy Ya sakeki Aira mahaifinmu mutum ne mai kafiyar bala I zaiyi wahala ya sakeki amma zan tayaki da addua akan Allah zaba miki abunda yafi zama Alkhairi sannan daga yau ki daina jin kunya ta tun lokacin da Na samu labarin Kece wacce Daddy Ya auro na hakura dake Aira saboda babu Aure tsakaninmu akwai zumunci insha Allahu zan taimaka maki wajen rage maki kadaici "Goge hawayenta Aira tayi ta ce " Nagode mai sunan Abba "masallaci Sadiq ya wuce yayinda ita kuma Aira ta koma gida kasancewar tana fashin salla D'akinta ta shige ta kunna kallo a plasma d'in dake manne a d'akin.
Zaune yake akan Kujera k'aramun littafin Alquran a hannunshi yana karantawa sosai yakejin dad'in iskan farfajiyar hotel d'in Musa ne yazo mik'a mashi Hannu yayi suka gaisa tare da cewa Ya bak'unta" Bayan sun gama gaisawa nan musa Shima yaja tashi kujerar ya zauna "yawwa Abokina inajinka ina son sanin labarin nan da kace zaka bani yau Dan a k'age na kwana da sonjin labarin" kamar bazaiyi magana ba saikuma ya fara bashi labarin soyayyarsu da Aira da abunda ya had'a mahaifansu rigima har suka rabasu haryakai karshen labarin Inda ya d'ora da cewa "Ina buk'atar taimakon Abokina wajen gano gidan da Airata take Dan Allah patan zaka bani Had'in kai" Sosai musa ya tausayawa abokin nashi Tabbas akwai abun tausayi a labarin "Numfasawa musa yayi ya ce " a Gaskiya Kunga jarabawa Abokina Allah baku ikon cinyeta Saidai abunda ban fahimta ba a nan me ya kawoka garin nan me zakayi idan ka gano gidan da take"a saboda Aira nazo garin nan ina son sanin Inda take ne bazan iya cigaba da rayuwa batare da ita a kusa dani ba tayi nesa da idanuwa na Amma har yanzu kusa take da zuciyata bazaka gane irin son da nake mata abokina ba hakan yasa na yanke shawarar zuwa Inda take Dan na nemu gidan da take Na nemu Aiki a gidan hakan ne kawai zaisa naci gaba da arba da ita "da mamaki Musa ya Mike ya ce " kana da hankali kuwa Abokina Aikifa kace Haba impossible wlh kamarkai da darajarka da komai ka kaskantar da kanka a saboda mace kana d'an governor guda kace zakayi aiki a k'ark'ashin wani Gaskiya shawarar nan da ka yanke batayi ba so hauka ne aka gaya maka"so yafi hauka Abokina Son da nakeyiwa Aira ya wuce duk yanda kake tunani kada ka kashemun kwarin guiwa inason ka karfafamun hakan yasan ban nemu taimakon kowaba ba na nemu naka Saidai idan bazata taimakamunba kawai ka fad'amun"ya fad'a cikin daga murya "kwantar da murya musa yayi yana mamakin wani irin sone wannan ya ce " ba haka bane Abokina amma Ina mamakinkane Shawarar da ka yanke ce nake ganin bata dace ba Kadubafa matsayinfa maid house zakayi Haba Abokina da iliminka da kyanka da kudi ga mulki ga matsayi ka duba fa "Numfasawa Arman yayi ya ce " Tabbas hakan ya shaidamun baka San meye so ba musa so babu ruwanshi da mulki,kud'i,sarauta,matsayi da sauransu Zan iya komai a saboda Soyayyata so ba Karya bane karka k'ara katseni akan Abunda nayi niyya idan zaka Taimakeni ka tayani neman gidan if bazaka iya ba kawai ka fad'amun bazaka iya ba na nemu taimakon wani "Sorry Abokina kayi hakuri idan ranka ya b'aci yanxu shikenan yaushe zamu fara neman Gidan" Mikewa Arman yayi ya ce "For now" Girgiza kai musa yayi Dan yalura abokin nashi yayi mugun nisa a soyayya A mota musa ya Kalleshi ya ce "kasan sunan mijin nata" Harara Arman ya maka mai tare da Jan tsaki ya ce "Wlh ka k'ara ambatarmun sunan wai mijinta a nan zakayi mamakina" Dariya musa yayi k'asa k'asa ya ce "Allah huci zuciyar manya to ya sunan shi mutumin" Tsaki Arman yaja yanajin tsanar sunan ya ce "Wai Madugu? ai Madugu suna da yawa a garin nan wanne kenan Real name d'inshi zaka fad'a" Tab'e baki Arman yayi ya ce "Bansan asalin sunanshiba nasan dai ana ce mashi Madugu " Aiki ja Kace aikin namu babba ne Aiko nemoshi a garin nan akwai aiki "bincikawa zamu tayi har Allah yasa a dace " Ganin yanda Arman ya had'e rai ya sanya musa Jan bakinshi a haka sukayi da Yawata gari suna neman mai suna Madugu amma duk kwatancen da akayi musu sai suga bashi bane Sai magriba suka Koma gida cike da gajiya musamman musa da aka tada mashi aiki tun daga ranar nan kullum Arman da musa sai sun fita neman Gidan amma sun kasa samowa saida sukayi kwana biyar suna Abu d'aya sosai sukeshan wahala ba karama ba Dan Duk Inda suka tambaya Sai ace su dai fad'i lak'anin yaudai musa ya fara gajiya Dan sun gama yawatawa amma Ba nasara kallon Arman yayi yace