NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   16 / 54

45K to 48K   out of 160.7K words

Gida kinsan Mummy ta dameni akan tana son ganinki"y'a fad'a yana tada mota"murmushi tayi ta ce "Allah sarki Mummy nah nima inason ganinta nayi kewarta" .
b'angaren gidan su Aira Baba mai gadi yana dawowa yaga wayam ba Aira sallama yayi cikin gidan Dan a tunaninshi ciki ta koma Mamy ce ta lek'o ta ce "Lafiya Baba" kati ya mik'a mata tare da chanji ya ce "gashi sak'on da kika Aiko maman Alhaji da yake haka cewa Aira na sayo" Cike da mamaki Mamy ta amshi katin ta ce "Ita Airar ta ce Na aikota ina take ita d'in" sosai mamaki ya kama Baba mai gadi ya ce "Hajiya yanzu fa ba jimawa ta zo ta ce kince na amso maki kati nikuma na tafi na barta a nan" tab'a hannu Mamy tayi tare da salati ta ce "Aiko wlh Baba wayau kawai tayi maka ta fita ba wani Aikenta da nayi sannan ta jinjina kai ta ce " Allah ya shiryeki Aira har kin iya dabarar fita "Sosai Baba mai gadi yayi mamaki ya ce " lallai yaran zamanin nan a gansu a kyale karamar yarinya tayimun wayau "Dariya mamy tayi ta ce " Allah dai ya shirya mana zuri'a kawai za ace ka koma kan aikinka kawai Baba "itama ciki ta koma tana mamakin Fitsarewa irin ta Aira ashe kudin da ta amsa duk shirine girgiza kai kawai tayi taci gaba da Al'amuranta.
suna isa Government house a tare suka fito security na Sara musu har suka isa Babban Palourn gidan Mummy ta taho da fara'arta ta ce "oyoyoyo ga y'ata ta fad'a tana Rungume Aira cike da farinciki ta kama hannunta ta ce " Sannu da zuwa tunda kika tafi kika barni da kewa"murmushi Aira tayi ta ce "Nima nayi kewarki sosai Mummy nah " Sosai Mummy ta dinga nan nan da Aira kamar zata maidata ciki sosai hakan yake yiwa Arman dadi yanda Mummy ke son Airanshi sai wajen magriba Aira ta fara tunanin Gida sai sannan ma ta tuna a yanda ta fito kallon Arman tayi ta ce "Yaya Mamy tace kar muyi magriba " ta fad'i hakane Dan Mummy tayi zaton da sanin Mamy ta fito "Mummy ce ta ce " Au har ina tunanin kwana zakimun "Murmushi Aira tayi ya ce " Mummy ai zandawo nayi maki kwana biyu"To shikenan Aiko da Naji dadi sannan ta tashi ta ce "jira ni ina fitowa Mummy na shiga Arman ya dawo kusa da ita ya ce " Yanzu sai yaushe zamu k'ara had'uwa"Turo baki tayi ta ce "Saina duba" Dariya yayi ya ce "irin wannan wulakancin na y'an mata ko" Dariya tayi ta ce "To me yafi son raina badai kace kana soba ai gwalaka ma fa zan fara"Dariya Arman yayi ya ce " Haba yarinya munga Wanda zai gwala wani cikinmu"ganin fitowar Mummy ya sanya Aira harararshi ta ce "To ka tashi sai Mummy ta ganmu" Meye Dan ta ganmu kefa har yanzu kink’ii ki waye saina wayar dake"harara Aira ta galla mai ta ce "Ai nice ma na wayar dakai ta fad'a tare da tsinkuninshi d'an Kara yayi tare da tashi yana Dariya " Mummy na isowa ta mik'awa Aira k'atuwar kwali bag mai d'auke da hoton Mummy da na Daddy ga alamu dai na siyasa ne ta ce "Amshi ki kaiwa maman naki kice ina gaishe ta sosai Dan Allah" Amsa Aira tayi ta ce "To Mummy zan fad'a mata nagode sosai " Tukwana sukayi bankwana lokacin da Suka isa unguwarsu Ana kiraye kirayen magriba a Inda ya d'auketa ya sauketa har ya wuce ta na Mashi bye bye saida taga wucewar motarshi tukwana ta nufi layinsu Tsit ba kowa unguwar Cikin Sauri take tafiya Harta isa gabanta na fad'uwa ta na zuwa Knoking tayi mai gadi ya fito ya na K'are mata kallo Aira bata Ko Kalleshi ba ta yi Sauri ta shige cikin Sauri har tuntube take ta nufi hanyar Part d'insu Daga bayanta taji muryar Abba na cewa "daga gidan uban wa kike"Shock Aira tayi a wajen ta kasa koda motsi gwalo idanu tayi ta ce " na shiga ukku "Abba ko tsawa ya k'ara daka mata daga Inda yake kan farar kujerar roba ya ce " ba dake nake ba".......✍🏿


*Ni da yaya Arman Littafin kud'ine akan Naira #200 kachal katin Mtn ta wannan number 07026166536*

*Takun ce dai mai k'aunar farincikinku*

_*Miss Hajo_*🤙🏿
[6/14, 20:47] Hajo hajo: 🅿️.......*45&46*





Cike da firgici Aira ta juya ta saki jakar hannunta bin jakar Abba yayi da kallo Mamy ce daga palour tajiyosu cikin Sauri ta fito ta na fitowa kallon Aira tayi cikin basarwa ta ce "Harkin dawo kenan Kinko kyauta baki wuce magribar ba bani sak'on ta fad'a ta na amsa jakar hannunta kallon Abba tayi ta ce " Ni na aike ta" Ajiyar zuciya Aira ta sauke a zuciyarta ta ce "Amma Mamy ba k'aramun ceto na ba kikayi tayi saurin daidaita nutsuwarta ta ce "Eh Mamy na dawo" Abba ne ya kalli Mamy ya ce "Da izininwa kika aiketa ba gabanki na yanke hukuncin hana ta fita ba shine zaki aiketa Raini ne ko me" Danne zuciyarta Mamy tayi cikin ladabi ta ce "Kayi hakuri D'an aike na rasa ita kad'aice gidan shiyasa banjima da aikenta ba " Shiru Abba yayi saikuma ya ce "Daga wannan ya zama first and last ko kin rasa d'an aike duk Mahimmancin abun ki jira wani yazo ko ki kira driver kika sake Aikenta ranki zai b'aci" Ikon Allah Mamy ta fad'a a cikin zuciyarta a fili kuma cewa ta yi "To Allah huci zuciyarka" tana gama fad'a ta kama hannun Aira ta jata sukayi ciki suna Zuwa bedroom d'in Mamy ta saki hannunta Tare da d'aure fuska ta ce "Daga ina kike?" Gidan....saikuma tayi shiru"Bansan k'arya kinsan kikamun ganeki nake ki fad'amun Gaskiya kai tsaye Daga ina kike"Aira ba yanda ta iya tasan dole ta fad'awa Mamy tunda ma harta taimaketa a wajen Abba k'asa tayi da kanta ta ce "Mamy yaya Arman ne yazo shine.." shine me"Mamy ta fad'a a tsawace"Shine naje muka gaisa kuma wlh ba Inda mukaje gidansu kawai mukaje Kuma daga Chan ya maidoni wlh kingama abunda Mamanshi ta bada na kawo maki "ta fad'a tana nunawa Mamy jakar" shine ke har kin iya dabarar fita kiyi mana wayau ki fita kodan kinga na daina matsa maki shine kike nema ki rainani To yanzu da babanki ya kamaki kice Ubanme inbanda na taimakeki ke kinfison kullum ke kad'ai akejin kanki Da mahaifinki Aira"Cikin hawaye Aira ta ce "Bazan sake ba Allah Daga yau kiyi hakuri mamy Allah ban rainakiba " Hmmm ai hakurinki da bazan sake d'inki ba Inda sabo mun saba Allah ya shiryeki "Sannan ta d'aga jakar ta fiddo kayan ciki Turamen atamfofi ne Ukku sai Turare da sabululluka masu kyau " kallonta tayi ta ce "Ai da ina da number ta da nayi mata Godiya Angode" Murmushi Aira tayi ta ce "Wlhko mamy Ai tana da kirki sosai Mummy ba ruwanta kuma karkiga yanda take sona har cewa tayi na koma nayi mata kwana" hmmmm naga alamu ni da zan samu numberta ma akwai maganar da mukeso muyi"Cikin Sauri Aira ta ce "Ko nace yaya Ya turo maki" Ta ina zakice ya turo Makin keda ba waya kukeba sannan Mamy ta kama hab'a ta ce "Ke wai ko har yanzu wayar nan na cikin gidan nan taya ma akayi kikasan yazo har kika fita inba kuna communication ba " cikin tsurewa Aira ta ce "Na janyowa kaina garin ilata Cikin Sauri ta ce " a a wlh Mamy na mayar mashi da Wayarshi a wayar Inna yakirani shine fa dazu da tazo take fad'amun"kindai tabbata kin maidamai wayar"cikin basarwa tace "Haba Mamy tun yaushe idan baki yarda ba Kuma ki tambayi innar" a a ni ba saina tambayeta ba jeki"Ajiyar zuciya Aira ta sauke ta ce "Na sila" cikin Sauri ta bar d'akin a palour ta tarar da Amma na salla zama tayi Dan fashin Sallah take saida Amma ta gama ta tambayeta ta ce "Y'an makaranta kenan sai yanzu" Wlhko ai yau munsha wahala Kinsan sai six muke fitowa daga lecture to yau driver baizo da wuri ba shiyasa nakai magriba"Amma ta fad'a tana cire hijab tab'e baki Aira tayi ta ce "Tofa Allah takaita wahala" Kamarya Allah takaita wahala Amma ta fad'a tana Harararta "Dariya Aira tayi ta ce " To me zance inba Allah takaita wahala ba to Allah k'aro wahala shikenan"girgiza kai Amma tayi ta ce "Kede kika sani Ai zaki shiga University d'in zakiji yanda mukeji kema" Tab'e baki Aira tayi ta ce "Uhm Aiko kina ruwa inkinganni lahira kaini a kayi karatu ba shine gaba na ba" Mama ce da ta fito tayi charaf ta ce "To meye gaban naki" Rufe baki Aira tayi tare da zare idanu ta ce "Kai Mama waida kinajina Sannan ta tashi tayi dariya ta ce " Ina nufin ba yanzu ba sai Abba ya huce tukwana"girgiza kai Mama tayi ta ce "Ai nazata ko Aure kike nufi keda sahibin naki" Rufe fuska Aira tayi tare da rugawa bedroom d'insu tana Dariya Itama Mama Dariya tayi ta girgiza kai.
Tana shiga Aira wanka tayi ta sauya kaya ta haye Gado Arman ne ya kirata tana d'auka ta fad'a mashi cewa "Mamy ta ce yayiwa Mummy Godiya sannan ta bashi labarin taimakonta da Mamy tayi a wurin Abba" cikin jin dad'i ya ce Allah sarki Mamynmu Allah mata albarka Gaskiya ta taimakemu yanzu dai Matsalarmu tayi sauki tunda Mamy ,Mummy, Mama Halima, Inna duk sun goya mana baya Saura Abba da Daddy kawai suma kuma muyi ta addu'a Insha Allahu Zasu amince kinsan ni fa harna k'agara Dan wlh bansan Aurenmu ya wuce nan da 3Months a k'agare nake "wara idanu Aira tayi kamar yana gabanta ta ce " 3months kuma yaya"Eh mana ai yamayi kusa ai kwanciyar hankali ace ranar da aka daura aranmu gani Gak.....cikin Sauri Aira ta katse wayar tana Dariya ta ce "Kai yaya wlh yanzu baida kunya yanzu da magana tayi nisa sai ya saki layi ta fad'a tare da yimai text da cewa " Good Night ka kwanta kayi bacci saida safe"tana turamai tayi saurin kashe wayar Dan karyayi ma ta kira Kwanciya tayi Bayan tayi Addua Dan bacci take ji Ba b'ata lokaci bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita cike da mafarkin sahibin ta.washegari Bayan tayi Sallar asuba komawa bacci tayi Dan bai isheta ba ita ce bata tashi ba sai 10 da wata muguwar yunwa ta tashi da ita brush kawai tayi cikin Sauri ko wanka bata tarka ba ta fito palour bata tarar da kowa ba Alamun amma da Haidar suna School Dining ta nufa ta bud'e cooler soyayyar Doya da kwai ta gani a plate ta zuba da yaji ta fara ci dukda ta fara sanyi tadanji dad'in ta tana cikin ci taga fitowar Mamy da hijab Tare da Amer a hannunta "ina kwana Mamy ina zaki naga kinfito kamar kina shirin fita" Aira ta fad'a tana cin doyarta "Wlh ko wai Aysha ce suke Asibiti tun jiya da dare bamu saniba sai dazu mijin ya kira tayi miscarriage ne Wai harma anyi mata wankin ciki Su Mama sunyi gaba shine zan bisu " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Aira ta fad'a tana hawaye sannan ta ce "Kaico Aunty Aysha Allah bata lafiya Mamy Dan Allah inzo mu tafi" Ta fad'a tana hawaye ganin yanda ta damu ya sanya Mamy cewa sanya hijab d'inki tare da Abbanku ai zamu idan ya yarda saimuje "cikin Sauri Aira taje ta sanyo hijab da takalmi suna fitowa farfajiyar gidan Abba na mota harsun fiddo mota Zagayawa Ta glass Mamy tayi ta ce " Abbansu wai Aira tace itama zataje ta dubata da naga a mota ne kuma tare zamu ta bimu ko ?Ba Inda zata ta koma tayi mata addu'a a gida ke kuma kiyi Sauri ki shigo mu tafi Sauri nake"Kallon ta Mamy tayi ta ce "Kinji abunda ya ce " ki koma"Goge hawayenta Aira tayi ta ce "To Mamy Allah bata lafiya barmun Amer Dan Allah ya tayani zama tunda ni kad'aice"Mik'a mata shi Mamy tayi ta ce " idan yaji yunwa ki had'a mashi abincinshi ki bashi saboda zamu jima"Amsarshi tayi daga hannun Mamy ta ce "To Allah kiyaye kice ina duba ta Dan Allah Mamy" Su Mamy na tafiya Aira ta koma ciki tare da Amer dake mata gwalamgwamtu sosai ta damu da Rashin lafiyar Aunty Aisha taso taje ta ganta Amma ba dama a gida tayi mata addu'a ta ce "Allah baki lafiya Aunty" tana komawa Aje Amer tayi da niyyar taje tayi wanka Amma fir ya k'iya ya fara kuka ba yanda ta iya sai daukarshi tayi ta fara jijjigashi Dabara tayi ta goyashi ba b'ata lokaci ko bacci ya daukeshi saukeshi tayi a hankali ta shinfid'ar dashi gadonta taje tayi wanka tana fitowa ta shirya cikin Doguwar Riga Atamfa ta d'aura kallabin atamfar Wayartace tayi ringing d'auka tayi Daga bangarenshi Arman ya ce "Shine jiya kika gudu kika barni ko" Dariya tayi ta ce "Ai kai dinne yaya Naji kana neman sako wata maganar yanxu dai ya kake ka tashi lafiya" Alhmdllh sai kewarki kawai"Zaro idanu tayi ta ce "Jiya fa muka rabu" Eh mana ai nafison koda yaushe muna tare da juna"Murmushi tayi ta ce "Nima da so samune hakan amma ya zamuyi" me kike Arman ya fad'a "Bakomai ni kad'aice ma a gidan sai Amer Duka sun tafi duba Aunty Aysha " Subhanalla Me ya sameta"miscarriage tayi"wayyo Allah ya bata lafiya ya musanya musu da mai amfani "Ameen yaya" kince ke kad'aice ko"Eh yaya"To ganinan zanzo mu gaisa "gabantane ya fad'i ta ce Yaya ai mai gadi bazai bari na fita ba" eh na sani lek'owa zanyi daga bakin gate ganinki kawai zanyi na koma"murmushi Aira tayi gabanta na fad'uwa ta ce To yaya saika zo"ganin ana kiran Sallar Azahar ya sanyata tashi taje kitchen ta dafa indomie Da egg cikin 30 minutes ta gama komi ta fito a palour ta Aje jiyo kukan Amer ya sanyata tashi tana zuwa Taga ya tashi yana shirin fadowa kasa ta tareshi tare da daddaukarshi ta jijjigashi ta ce "To yi shiru" Kuka ya cigaba dayi dafe kai tayi ta ce "Nima naga ta kaina fitowa tayi dashi palour dakin Mamy taje ta had'o mashi custard da madara cikin Sauri ta dawo palour Tana fara bashi yayi shiru Ajiyar zuciya ta sauke taci gaba da bashi saida ya koshi har yana kauda kai tukwana ta rabu dashi abun wasa ta Aje mishi nan yahau wasanshi yana dariya"(Nikam nace Aira ashe an iya raino😂) sai sannan ta samu damar cin nata abincin tana gamaci ta gyara wajen Wayarta ta d'auko ta hau what's app Ta fara chatting wajen la'asr Arman ya kirata ya ce " ki lek'o ina bakin gate"cikin Sauri Aira ta ce "To yaya ganin har yanzu y'an gidansu basu dawoba ya sanya hankalinta kwanciya ta ce " nasan kila ma ba yanxu ba zasu dawo"Fuskarta kawai ta gyara ta janyo doguwar Hijab d'inta tasa Tana fitowa Amir ya fara kuka yana mik'a mata hannu Alamun ta daukeshi tsaki taja tare da dungure mai kai ta ce "saikace cewa nayi zan barshi d'an rigima kawai" shiko shiru yayi tare da Lafewa jikinta yana tsotsar yatsa suna fitowa bakin gate ta nufa Baba mai gadi na zaune gaisheshi tayi ta ce "Baba zan gaisa da wani ba fita zanba ina bakin kofa yana waje " Baba mai gadi ya ce "To kiyi sauri dan Allah maman Alhaji karsu dawo su sameki" murmushi tayi ta ce "To Baba nagode" Tana lek'awa Ta Hango Arman a.mota yana hangota ya taho sosai yayi.mata kyau cikin shigar k'ana nan kaya Fuskarnan tashi sai shek'i take ga sajenshi lufluf dake zagaye da kyakyawar fuskarshi gashin kan nashi sai shek'i yake Dan yau baisa hula ba Alamun yana shan gyara"murmushi Aira tayi ta ce "Amma fa wankan nan ya tafi dani yaya" Haba my love ya fad'a yana karasowa bakin kofar"murmushi tayi ta ce "Ai.kaima ka sani sannan ta bata fuska ta ce " Allah sa wasu basu gama ganemun kai ba"Dariya yayi Kad'an dake k'ara mishi kyau cikin sigar zolaya ya ce "Ai kinsan babu wacce ta isa ma ta tsaya kalle miki miji kinsan kwarjini yake yiwa y'an mata basa iya kallona su k'ara "Uhm yaya kenan sarkin kod'a kai" Ai kema kinsan Gaskiya na fad'a "Sannan ya ce " Wai Amer ne ya girma haka masha Allah kawoshi mu gaisa"ya fad'a yana mik'a mata hannu "Mik'a mishi shi tayi daman Amer ba kiyiwa garai ba Sajen Arman ya kama ya dinga ja yana kyalkyalewa da dariya" Dariya Aira da Arman suma sukayi Arman ya ce "Ina son yara sosai my Aira nasan zaki Haifa mun yara kyawawa kamarki Allah yasa wataran d'anmu ne ni Dake na d'auka haka"Rufe fuska Aira tayi " Murmushi Arman yayi ya ce "bazakice Ameen ba" Dariya tayi ta ce "uhm To ameen my ya...muryartace ta sartse sakamakon Ganin motar su Abba da tayi a bakin gate din Alamun sun dawo suna Horn Cikin rudewa Aira ta amshe Ameer dake.hannun Arman ta Ruga ciki Kad'an Ya hana ta fad'i Arman ko Juyawa yayi yaga Inda take kallo" Girgiza kai yayi tare da Juyawa ya nufi Inda motarshi take Aira cikin tashin hankali ta shiga cikin gidan Tuni ta fara hawaye tace "Shikenan yau karyata ta k'are na shiga ukku " Batayi minti Ukku ba tsaye taji shigowar su Mamy Tare da su Mama hada Amma Cikin Sauri ta Aje Ameer Kasa tare da rugawa tayi cikin Dakinsu ta kulle sai hak'i take"Mamy ko d'anta ta d'auka tayi d'akinta Abba koda ya shigo bai tambayi Aira ba Kuma baice ina take ba bai nuna Alamun ko damuwa a fuskarshi ba Aira ko ta na Chan kulle Ranar bata fito ba Amma ma dak'yal ta bud'e mata ta shiga Washegari saida taga fitar Abba ta window tukwana ta sauke ajiyar zuciya ta fito palour Mamy ta tarar da Mama Gaishesu tayi suka Amsa Ya jikin

16 / 54