Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
nan sai anzauna kin sanyani a duhu da yawa" murmushin k'arfin hali Aira tayi suka shiga ciki a palour suka tarar da mijinta gaisheshi Aira tayi ya amsa mata cike da mamaki Bayan sun zauna Aysha ta kawo musu abun Tabawa twins ko tuni suka kama wasansu a wajen dining harsuna shirin yiwa Aysha b'arna tashi mijin aysha yayi yabar gidan dan yabarsu su sake kallon Aira tayi tare da kama hannunta ta ce "Sis yaran waye bani labarin abunda ya faru" Goge hawayenta Aira tayi tare da bawa aysha labarin komai da ya faru tundaga rayuwar gidanta ta Alh Yusuf har Zuwan Aurensu da Arman da yaran su Sannan sharrin da Akai musu Tayi mata rantsuwa akan basu tab'a aikata Alfasha ita da ARMAN ba"Aysha na kuka ta Rungume y'ar uwar tata ta ce "Allahsrk sis wlh na tausaya maki Abba mahaifinmune amma baiyi miki adalci ba Abba yana tsananta Abu da yawa fushinshi yana yawa yanzu Kinga ba bincike ba komai ashe haka abun yake"Aira na kuka ta ce " Sis Dan Allah fad'amun Gaskiya Bayan tafiyata Abba da Mamy basu tsinemun ba"Goge hawayenta Aysha tayi ta ce "basu tsine maki ba sis amma Abba ya Ce ya cireki a jerin yaranshi nan Tabawa Aira labarin komai da ya faru har Rashin lafiyar da Mamy ta dingayi a dalilinta" Sosai Aira ke kuka ta ce "Na shiga ukku ni Hajara sis ya zanyi da rayuwata wlh nayi nadama Yanzu kenan Abba ya cireni a yaranshi sannan ya rabaku dani" girgiza mata kai aysha tayi tana Hawaye ta ce "Sis fadarshi ta yarabamu bashi ke nuna zamu rabu dake ba muna tare da ke har gobe ke y'ar uwarmuce babu yanda zamuyi dake sannan koda ace zargin da aka maki Gaskiya ne bazamu rabu dake ba bare sharrine jibi da ikon Allah hada rabon yara Har biyu ga na Ukku " Sosai Aysha ta shiga Lallashin Aira harta samu ta daina kuka suka hirar yaushe gamo Waiwaye Aira ta dingayi ko zataga yaran Aysha amma shiru kasa daurewa tayi ta ce "Sis ina Yaran ko suna makaranta" Murmushi Aysha tayi ta ce "Bani da yara ko d'aya har yanzu sis Gaki k'anwarta ta Ukku hada yara biyu ga na Ukku Kinga ikon Allah Ko" Sosai Aira taji tausayin y'ar uwar tata cewa tayi "Allah ya baki kema me amfani sis"Ameen Aysha ta fad'a " rugowa Nihal tayi wajen Aira tare da hayewa kanta tana boyewa ta ce "Cutie Kinga Naila zata doken " Kallon Naila da ta biyota Da wayar chazar Aysha tayi sai huci take tana hawaye Aira tayi ta ce "naila bansan zalinci y'ar uwar taki zaki doka da abun nan Dan iskanci Ta fad'a a tsawace tare da amshe chazar tace " wuce kiban waje sarkin fad'a"kuka Naila ta fashe dashi tare da durk'ushewa ta fara burgima Aysha ce tayi saurin daukarta tana Dariya wai Aira ce da raba yara fad'a kallon Aira tayi ta ce "Ke kuma haka ake rabon fad'a saikiji me tayi mata kafin ki sasinta" Turo baki Aira tayi ta ce "Allah Aunty fad'ane da ita Dan taga ta fita k'arfi ita kuma sakaran tsorantama take ta fad'a tana dungurarwa Nihal kai data lafe jikinta " Dariya Aysha tayi tana Lallaba Naila harta samu tayi shiru ta ce "Uhm su Aira iyaye Ashe dai twins dinkine amma ta rude a kansu hhh kaji y’an soyayya yarankuma cutie suke cemaki kenan “Dariya Aira tayi ta ce "Ai har yanzu batasan ni bace sai ta ganmu k'watsam amma Aunty kina ganin naje gida ba matsala?Ajiyar zuciya Aysha ta sauke ta ce " bazance kije ko karkije ba sis amma zaki iya zuwa kidai je a b'oye kar Abba ya ganki firstly "Gyada mata kai Aira tayi wajen 3 Sukaji order Arman Bankwana Aira tayima Aysha Wanda twins harsun saba da ita suka fito Inda ta basu choculate sannan tacewa Aira Dan Allah ta dawo bayanin sanya mata number ta" da to Aira ta amsa mata cike da kewar y'ar uwar tata ta bar gidan suka shiga mota sosai gabanta ya fad'i koda suka shiga layin gidansu sosai gabanta ya shiga fad'uwa ta shiga jero duk addu'ar da tazo bakinta kallonta Arman yayi da suka kusa get d'in gidan ya ce "Kisa a ranki akwai nasara insha Allahu kinji my cutie" Cikin k'arfin hali ta gyad'a masa kai tare da bude kofar zata fita kallonta yayi ya ce "Da yaushe zanzo na daukeku "? Wajen 5 ko 6 ko?gyada mata kai yayi ya ce " ki kulamun da kanki Da my unborn nd my twins"murmushi ta sakar masa ta ce "kaima ka kulaman da kanka my hero a tare da twins suka fito da suke daka tsalle yau zasuga mom d'in Cutie Kallonsu tayi tayi murmushi ta kauda kai " Kallonsu yayi ya ce "My angels ba a yiwa hero bye bye" Dariya sukayi tare da d'aga masa hannu suka ce bye bye hero bakache mu gaishe maka da mom En cutie ba Kuma ma har dad enta yau jamu gani suka fada suna tsalle"y'ar Dariya yayi musu tare da cewa "To ku gaishemun da su" kama hannunsu Aira tayi tare da d'aga masa hannu ya wuce Tayi minti biyar tsaye tana tunanin yanda zata tunkari get d'in gidansu haka nan dai tayi shahada tare da nufar bakin get d'in gidan gabanta na tsananta fad'uwa Dak'yal ta iya d'aga hannunta ta yi knoking mai gadi ne ya leko tare da bud'ewa turus yayi ganin Aira gabanshi wara idanu yayi cike da mamaki ya ce "Hajiya kece da gaske" Murmushin K'arfin hali Aira tayi ta ce "Ni ce Baba Su Mamy na ciki?........✍🏿
*Tofah yau ga aira a gida me kuke tunanin zai faru ABBA zai yafe mata kuwa koko yana nan kan bakanshi*??
*Ni da Yaya Arman it’s for sale akan Naira 200 kachal to 07026166536 ki biya ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali nida yaya Arman ko da kudinka saida rabonka har yanzu kuna da damar sayanshi akan garabasar da na saki 200 daga randa ya zama complete document zai koma 400 ne*
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[7/20, 23:17] Hajo hajo: 🅿️........*115&116*
....Ni ce Baba Su Mamy na ciki"?Eh suna ciki Alhaji dai naga ya fita"Ajiyar zuciya Aira ta sauke jin Abba bayanan cikin Sauri ta shiga cikin gidan twins na biye da Ita "sosai take kallon gidansu tana jin wani dadi gidan da rabonta dashi shekara kusan hud'u A bud'e ta tarar da Palourn Cikin fargaba da shiga twins na biye da Ita suna surutansu Tana tura kofar amma da Mama Sai Haidar ta tarar a palourn ja tayi ta tsaya suma duk Kallon mamaki suke binta dasu amma Ce tayi k'arfin halin cewa " Sis kece da gaske ko gizau ne nake gani"Tuni hawaye suka wanke fuskar Aira gyada mata kai tayi "ai da gudu ta rugo ta Rungumeta Itama Rungumeta tayi tana jin kewar y'ar uwar tata sun jima suna kuka kafin suyi shiru wara idanu amma tayi ganin twins Bayan Aira da mamaki ta isa garesu tare da dukursawa ta ce "naila Nihal kune nake gani gabana kodai mafarki nake" Dariya Aira tayi ta ce "sunedai gabanki sis" da mamaki ta ce "me kike nufi Aira me ya hadaki da Yaran nan" Dariya tayi ta ce "Ai yarankine sis" Mama ko duk mamaki ya gama cika ta ga mamakinta na ganin Aira da wani cikin cewa tayi ta yi"mufa in sanyamu a duhu Aira Yaran nan dai ko ba a fad'a ba daka gansu kasan na Arman ne yaushe kika haihu bansaniba Bayan baki da Aure"Goge hawayenta Aira tayi tare da cewa "Mama ina yini" Haidar ne Shima da ya gama mamakinshi ya rugo suka Rungume juna yana hawaye ya ce "Yaya Aira me yasa kika tafi kika bar gida tsawon wannan lokaci" kama hannunshi Aira tayi ta na Goge hawayenta ta ce "Nima ba haka naso ba bro k'addarace ta zabamun haka Ina Mamy ta fad'a tana hawaye" D'akinta ya nuna mata Ai cikin Sauri Hartana hadawa da gudu Tayi d'akin tana turawa ta samu Mamy bakin Gado da gudu Aira ta Ruga tare da Fad'awa kan Mamy ta Rungumeta ta fashe da kuka Mamy da jin mutum kawai tayi a kanta ana kuka sosai tayi mamaki"Juyowa tayi ta duba fuskar aira taga ita d'ince wara idanu ta yi ta ce "Aira tace nake gani ko gizau" Tana kuka tana hawaye ta ce "Mummy Airankice Mamy Dan Allah ki yafemun " ta k'arasa fad'a cikin wani irin kuka "Itama Mamy kuka ta sa tare da Rungume y'artata tanajin soyayyarta har cikin ranta ta kasa koda magana Twins ne da suka shigo biyo mamansu Sakin rungumar Mummy tayi tare da dafa kafadar Aira Kare mata kallo Tayi Tare da Kallon cikin jikinta gabanta na tsananta fad'uwa ta ce " Aira ciki?meya hadaki da ciki Bayan ba Aure gareki ba"hawaye nabin k'umcinta Aira tayi k'asa da kanta twins ne suka zo suka D'are kanta Nihal ta ce "Cutie mom ina Mom en taki take"Nuna musu mamy tayi tana Hawaye tare da K'asa da kanta " Kallon mamy sukayi a tare Itama mamyn kallonsu take ta kasa koda magana Da zaka duba yanda zuciyarta Take tofa da kila tana Daf da fashewa saboda fargabar yaran nan nan da Cikin nan Kardai a waje ta samesu "cikin k'arfin hali ta ce " Aira ina kika samu yara da ciki keda ba Aure gareki ba fad'amun abunda ke faruwa kinsanyani cikin duhu"Goge hawayenta Aira tayi tare da kama hannun Mamy tana kuka ta ce "Mamy wlh duk abunda Alh Madugu ya fad'a muku wlh sharrine suka mana bantaba zina ba......Duka ta bawa Mamy labarin komai bata boye mata ba har zuwa Aurensu da iyayen Mummy suka hada har zuwa yaran da suka Haifa.
Koda ta gama bata labarin Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce " Amma Gaskiya Hajiya Fatima ta cika uwa ta gari ba ku kadai ta taimaka ba ni kaina ta taimakeni Allah ya saka mata da gidan Aljanna yanzu Dan Allah ina da za a akai rabon yaran nan da Saidai ku haifesu a waje Allah na gode Maka da komai yazo yanda banyi tunanin ba sannan ta kalli twins tana fara a ta ce "Ina takwarar tawa da takeson Gani na " Nihal cikin Sauri ta Ruga tare da Rungume Mamy itama mamyn Rungumeta tayi ta ce "oyoyo takwara ta yau dai Gaki ga takwararki ko?gyada mata kai Nihal tayi Ta na mata Dariya tare da shafa Fuskarta " Naila ce ganin Mamy batayi mata magana ba ta fashe da kuka tare da Fara didiira kafa "duk kallonta suka tsayayi Aira ta ce " me aka miki Naila "Tana kuka ta nuna Mamy ta ce " ba mom enki bace ta kyaleni ta dauki takwalalta Nima ki kaini wajen mom tunda itace takwala ta kuma bazan kala zuwa nanba tunda ni bata so na"Dariya mamy tayi tare da janyota ta Rungumeta ta ce "Sorrry Mamy tayi laifi ayi hakuri ina sonki sosai kema kinji" Lokaci guda Naila ta fara Dariya tare da Fara tsalle jikin Mamy ta ce "I love you so much mom En cutie" Dariya mamy tayi tanajin soyayyar yaran a ranta ta ce "I love you too yaran kirki" Nihal ko Lafewa tayi jikin Mamy kamar daman ta Santa tana Tsotsar yatsa kallon Aira Mamy tayi ta ce "Karkiga yanda Halima ta rude kullum bata da zance sai Oum twins Da twins ashe dai yarantanema Akwai lokacin da ta nunamun hotonsu har ina fad'a ina cewa baki da magaya Aira me ya kaiki d'ora yaranki a media " Murmushi tayi ta ce "Mamy ai yanzu na daina" Ai tun lokacin da kika daina karkiga yanda ta damu lafiya dai ko"Wlhko y'an shan jinine suka kamasu twins nan ta bata labarin abunda ya faru"Subhanalla Mamy ta fad'a ta Ce "Aidaman nasan anrina Allah ya kiyaye gaba sannan ki dinga sanya musu hula in zaku fita jifa gashinsu waje tubarakalla sunyo gashinki Sai a cinye miki yara a banza " murmushi kawai Aira tayi tana wasa da yatsun hannunta Amer ne ya shigo Bayan dawowarshi daga Tahfex Wara idanu Aira tayi ganinshi da mamaki ta kalli Mamy ta ce "Mamy amer ne ya girma haka" Dariya Mamy tayi Dan yau cikin farinciki ta ke ta ce "Wlhko ai yaushe rabonki dashi" Amer ko kallon mamaki yakewa Aira Dan baisan taba wajen Mamy ya nufa Tare da Kallon twins dake cinyarta Dariya yayi musu Suma suka mayar masa kallon Mamy yayi ya ce "Mamy ina kika samo mana yara masu kyau" Dariya Mamy tayi tare da nuna masa Aira ta ce "yaranka ne auta kaga mamansu ka ganeta?Kallon Aira yayi da itama shi take kallo Ya girgiza kai ya ce " a a a Mamy bansan taba amma naga tana kama da Abba kuma ina ganin hotonta"to yayarkace itama Nina haifeta wannan kuma yarantane aidai kasan Ayra a baki ko?wara idanu yayi ya ce "Lah Mamy Aunty Ayra ce Sannan ya Ruga ya Rungumeta Itama Rungumeshi tayi ta ce " Ah lalle autan Mamy ya girma "Dariya yayi Inda yaje Yayi tayiwa Su twins wasa suna Dariya sunk'i sauka daga kan Mamy sai liliyarta suke Haidar ne ya shigo shida amma tare da plate a hannunsu Amma tazo ta zauna jikin Aira tana kallonta ta ce " sis oum twins ga abincinan kici ga ya Ummy na kirata hada saurinta ta ce tana hanya Ashe dai surprised Dina da akace za ai da gaske ne"Dariya Aira tayi ta ce "Ai cewa nayi a bazata zanyi maki yaudai gaki ga twins dinki"mikawa twins hannu Amma tayi tana musu murmushi Naila ce ta Ruga Wajenta Nihal ko tayi luf jikin takwararta daman ita uwar son jiki ce fita amma da Naila sukayi Kallon Haida Ayra tayi da yayi tsaye yana Danna waya ta ce "Hmmm su Haidar manya tunda nazo sai daddauremun kake" Mamy ce cikin fad'a ta ce "Rabu dashi uban bak'in hali kamaga y'ar uwarka ko farincikin ganinta bakayi ni wuce ka bani waje kazo kayima mutane tsaye kana Danna waya" Murmushi Haidar yayi ya ce "Sorry Mamy sannan ya kalli Aira ya ce " Tunfa a palour muka gaisa sis "Amsar wayarsa Aira tayi ta ce " Kayi waya kenan bari na d'auki number ka D'aukar number tayi save Shidai Haidar mamaki yake Inda Aira ta samu yara Suna haka Ummy ta shigo da gudu Suka Rungume juna itada Aira sai murnar ganin juna suke dukda abokiyar fadantace itama saida tayi mamakin jin twins yaran Aira ne Palour Aira ta fito Nan Mamy tayiwa Su Mama bayanin da Aira tayi musu sosai suka jinjina Abun kuma sukayi farinciki da abunda akayi tunani bashi bane Mama ma sosai tayi fad'a ta ce "da yanzu ina za akai rabon yaran nan Haidar ma sai yanzu yaji sanyi harma ya d'auki twins Dan dazun dukda yayi farincikin ganinta amma Yaji haushin Ace yayartashi tayi abunda ake zargi ashe ba haka ba nan aira ta tambaya ina inna akace mata batanan tayi tafiya kauye ziyarar yan uwa sosai aira taso ta hadu da inna Suna palour ana jajinta abunda ya faru Amma na bawa twins abinci Aira ce ta ce “sis wai Ina makarantar kin gama?Murmushi amma tayi ta ce “two months kenan da kammala degree dina sai jiran result kingani abunda nake fada maki yanzu fa bakinki sec sis Da yanzu kema kingama degree dinki “Dariya aira tayi ta ce “Ni kinga degree dina nan “ta fada tana nuna Twins duk Dariya akai Mamy tace “kujimun marar kunya’duk Dariya akai sosai aira ta tsinci kanta cikin farinciki ganinta cikin yan uwanta da mahaifiyarta ana wasa ana dariya ana haka Suka ji sallamar Abba sosai gaban Aira ya fad'i Ganin shigowar Abba Mikewa tayi a matuk'ar firgice Shima a mamaki Abba yake kallonta cikin tsananin b'acin rai ya nunata da yatsa ya ce Uban me ya kawo wannan abar gida na da izininwa " Tuni Aira ta fara hawaye Bayan Mamy ta boye ta ce "Dan girman Allah Abba kayi hakuri ka yafemun na tuba " Mama ce ta mik'e ta ce "Kayi hakuri Alh ka sauraremu’’ Tsawa ya daka mata Tare da nuna Aira da yatsa ya ce "Minti d'aya na baki ki fitarmun daga gida bana k'aunar ganin bak'ar Fuskarnan taki a cikin gidana " Sosai Aira take kuka ta ce "Dan girman Allah kayi hakuri Abba Mamy ma tana hawaye ta ce " Kayi hakuri Abbansu Ka yafe mata ka nutsu kaji komai a sannu"Tsawa ya daka mata ya ce "Na karajin bakin wani cikinku yana ban hakuri wlh zakuyi nadamar abunda zanyiwa mutum Sannan ya sakewa Aira Tsawa ya ce " bazaki kwashi rubabbun kafufunki ki barmun gida ba saina sauya maki kamanni y’ar iska a zatonki kingama yawon karuwancin naki zaki dawomun gida na karbeki ai nariga na dade da cireki a jerin yaran da na haifa ki gaggauta barmun gida ko na kira jami’an tsaro su fitarmun dake "Cikin Sauri Aira ta mik'e dak'yal tanajin zuciyarta kamar zata rabe gida biyu ta ce "Abba zan tafi kamar yanda ka koren kuma bazansake dawowaba har saika yafemun amma Bazan gaji da neman yafiyarka ba " Kallon twins tayi da duk sun rude ganin Abba na yiwa mom D'insu Tsawa ta ce "ku taho mu tafi" Da Sauri suka taho Wajenta suna boyewa Dan sun tsorata da Abba hanyar kofa ta nufa tana kuka Suma Duka y'an d'akin kuka suke musamman Mamy cikin kuka ta ce "Alhaji ba Inda zata fushinka bazai rabani da y'ata ba " Saidai ki bita Abba ya fad'a yana nuna mata hanya"Cikin fushi Mamy ta mik'e zuciyarta na zafi ta ce "Aira jirani wannan Karin bazan lamunta irin abubuwan da akayimun a baya ba na Shanye Saidai hakan ya zama silar lalacewar alak'armu tana gama fad'ar haka ta dauki hijab d'inta " Juyowa Aira tayi tare da girgiza mata kai ta ce "Dan Allah Mamy kiyi hakuri ki koma banason na zama silar Mutuwar aurenki kiyi hakuri zantafi ni kad'ai amma Dan Allah ki koma" girgiza mata mai Mamy tayi ta ce "Aira bazan