Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
Daddy Ya ce " Inna wace yarinyar kike maganar yayiwa cikin ?yo wa ka sani mana idan ba Hajara ba tunkan ayi Auren ashe da ciki taje bai kyaleta ba a haka ba saida ya bita har gidan Aurenta shiga d'an iska yaje a matsayin matuki yaje ya dinga nanikarta har saida mijin suka kamasu karshe dai ya kashe mata Aure kuma ya gudu da ita to wlh Kaine ubanshi saika nemo munshi Tare da jikata zan nuna masa na fisa iya shak'iyanci "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai Mummy da Daddy ke furtawa Dan hands free Wayar take taji komai kashe wayar Daddy yayi ya ce " Kinji abunda d'anki ya aikata ko?Keda kike d'aure mashi Ga abun kunyar da ya aikata mana to wlh kisani daga yau babuni babushi dukda shi kadaii na Haifa na gwammace nayi rayuwa batare da kowaba sannan duk Inda Yake zansa a kamasu sainasa an rufeshi Su kuma ya maido musu y'arsu sosai Daddy Ya shiga Surfa masifa Mummy ko hawaye kawai take tana Nazarin Arman bazasu aikata haka ba Saidai ance ba a yabon d'an kuturu duk irin masifar da Daddy yayi mata tanka shiba saboda ance d'an goruba mai jawa uwarshi jifa Dan har ita Daddy Ya hada yake surfawa masifa Saida ya gama tukwana ya fara kiraye kirayen Airport tare da tura hoton Arman ya ce da sun ganshi su kamashi sannan ya Ce har gidan nashi na Abuja zansa Aje Duk iskancinshi zan nuna masa k'arshenshi Mummy ko sosai tashiga tashin hankali ta ce "Alhaji karkayi haka karkasa a kama d'anka idan rai ya baci hankali baya gushewa " Daddy baima kulataba sai barin d'akin da yayi cikin tsananin tashin hankali Mummy ta shiga cikin d'akinta Tare da janyota wayarta number Arman kawai take Kira amma a kashe Tana hawaye tayi ta tura mashi text kala kala dukta rude Hankalinta duk ya k'ara tashi Dan bazata juri A rufe mata d'a a banza ba Dan ta lura Daddy da gaske Yake kuma idan yayi irin wannan kafiyar Babu mai tankwarashi hakan yasa hankalinta tashi gashi duk ta kira layukan Arman Amma a kashe zama tayi bakin Gado tare da tafka uban tagumi Tana hawaye.
Arman koda ya dawo bacci ya tarar da ita tanayi Wanda hakan sosai yayi mishi dadi Take away d'in da yayo mata ya Aje tare da maganin ya nufi bedroom d'inshi yaje yayi wanka Bayan ya fito ya shirya sosai yayi kyau cikin Dakakkiyar light blue din shaddarshi sai maiko take d'akin Aira ya koma yaga har lokacin Bacci take zaunawa yayi kan sopar Dake gefen gadon tare da kafeta da idanu bako k'iftawa wutar sonta na k'ara fisgarsa Yakai one hour yana kallonta sai wajen la'asr ta tashi A hankali take bud'e idonta ta saukesu a nashi murmushi tayi mishi Shima ya mayar mata Brush taje tayi shiya taimaka mata taci abinci tukwana tayi Salla maganin da ya sayo ya b'alla mata tana Yatsine fuska ta sha kallonta yayi ya ce "To ya jikin naki? Dasauki yanxu banajin zazzabin Saidai ciwon ciki Kad'an " Insha Allahu Shima zai daina dia Allah ya k'ara miki lafiya"Ameen Aira ta fad'a tana jingina kanta ga jikin gadon Wayarshi Arman ya lalubo ya ce "Kinga Tunda mukazo ban kira musa ba na shaida masa mun Iso lafiya Nasan yana ta nema na bari na kira shi ya fad'a yana bud'e wayar Yana bud'ewa yaji text message na shigowa Rututu daga sama kuma yaga number Mummy ce message d'in farko ya shiga Inda ta rubuto'" Son ka bud'e wayarka zamuyi magana dakai Dan girman Allah"Na biyun kuma ta ce "Arman ka taimakeni indai naci darajar haihuwarka da nayi ka kirani akwai matsala Arman " Na ukkun kuma ta rubuta"Na hadaka da girman Allah Arman idan na kiraka ka amsa kirana nasan duk kiran da nake maka kwanaki kana gani kake kin d'auka wannan Karin muddin baka daukaba zanyi fushin da..bai k'arasa karantawa ba yaji kiranta cikin Sauri Arman ya d'aga cikin damuwa ya ce "Mummy kina Lafiya" nauyayyar Ajiyar zuciya yaji Mummy ta sauke wanda har a waya saida yaji ta ce "Ba lafiya ba Arman kuna ina kaida Aira ?Kallon Aira yayi da hankalinta na kanshi ya ce " Muna Abuja Mummy please karki fad'awa kowa"Cikin Sauri Mummy ta ce "akwai matsala ka maza ka d'auketa Kushiga Mota ku tafi Adamawa Karku sake Kuhau jirgi Daddynka ya sanya a kamaka sannan har nan Abujar ya sanya azo gidanka sannan ka sanya face marks yanzunnan ba sai gobe ba ka maza ku tafi Adamawa gidan Mahaifina Zan sameku a Chan ko zuwa gobe ne" Cikin marairaicewa ya ce "Mummy Dan Allah ba wani shirin kukayi mana ba baso kuke ku Kara rabamu ba"ba Numfasawa Mummy tayi ta ce " Arman ba ka yarda dani ba kenan Babu wani shiri da na shirya wlh ina son kawo karshen matsalar nan ne Kayi abunda nace maka yanzunnan cikin gaggawa"To to Mummy yanzu zamu tafi nagode ya fad'a tare da Kallon Aira ya ce Cutie maza ki shirya Adamawa zamu tafi"Adamawa kuma Yaya wajen me"yanzu Mummy ta kirani ta ce "Muje Chan itama zataje karmu tsaya bata lokaci tashi mu tafi " a sanyaye Aira ta mik'e tare da sanya Hijab d'inta ta ce "Muje Yaya" Makullin motarshi mai tinted ya d'auko Suna zuwa parking space ya bud'e mata gaba tana shiga ya zagaya yaja motar Horn yayi mai gadi ya fito Cikin Sauri ya bud'e Zage glass din motar Arman yayi ya ce "Duk Wanda yazo nemana karka shaida musu nazo garin kace rabona da gidan amfi wata hud'u kuma wlh ka sake ka fad'awa wani nazo gidan nan nadawo a bakin aikinka" Yana gama fad'ar haka ya zuge Glass din baijirama amsar mai gadin ba ya figi motar a guje Sosai Arman ya dinga sharara gudu Suka d'auki hanyar Adamawa a lokacin hud'u Harta gota sosai suke sharara gudu Wanda Aira a lokacin zazzabinta ya dawo sunyi nisa sosai taji Tanajin Amai Kallonshi tayi cikin k'arfin hali tace Yaya "Amai nakeji" tsaida motar yayi tare da bude mata Ta sauke kafafunta waje nan ta shiga Yin aman saida ta gama tukwana ya mik'a mata ruwa ta kuskure bakinta Tare da wanke fuska Kallonta yayi ya ce Sannu Allah baki lafiya"gyad'a mishi kai tayi ta ce "Amen yaya " Fitowa yayi tare da rik'eta ya mayar da ita back sit tare da kwantar da ita saman kurerar ya ce "Ki kwanta ki huta" gyada mishi kai tayi Dan daman hutawar take buk'ata shi kuma ya zagaya ya koma Tare da tada mota ba ayi minti goma ba bacci ya d'auketa tafiyar awa Hud'u sukayi Karfe 8pm tayi musu a garin Adamawa Wanda sai lokacin Aira ta tashi Sannu yayi mata ta amsa da yawwa tare da cewa "Amma yaya munyi Sauri harmun Iso kenan " Murmushi ya sakar mata ya ce "Kina baccinki ai dole kice Munyi Sauri tunfa biyar kike bacci " Wara idanu tayi ta ce "Kaiii Ammafa nasha bacci shiyasa da na tashi Naji ba ciwon kan" Koda suka isa gidan Wazirin Adamawa mahaifin Mummy kenan a bakin get d'in gidan yayi parking Ya fita itama Aira bud'ewa tayi ta fito tare da Kallon get d'in da bangon gidan an kawatashi da zanen sarauta tundaga get d'in gidan Har bangon gidan irin na al'adarsu kama hannun Aira yayi ya ce "Muje ciki" A tare suka shiga cikin gidan Wanda Aira sai kallon gidan take tana kallon yanayin tsarin gidan sosai ya burgeta Kai tsaye bangaren Mahaifiyar Mummy Hajiya Zaituna Arman ya nufa da ita ita dai Aira na biye dashi da Sallama suka Shiga palourn Kallon y'an d'akin Aira tayi tsohuwace d'aya sai y'an mata guda Ukku"Cike da farincikin Ganinshi Hajiya Ta Mike tace "lale marhaban mai Gidan " murmushi Arman yayi ya ce "Tsohuwar daman baki gangara ba har yanzu?Uwaka ce zata mutu bani ba ja iri ta fad'a tana tashi tare da kamo hannun Aira ta ce " Sannu da zuwa kishiyata kunshawo hanya"ta fad'a tana zaunar da Aira gefen ta"K'asa da kanta Aira tayi ta ce "Ina yini Mama" Lafiya qlau y'ar nan ki saki jikinki nan d'in gidankune kinji"gyada mata kai Aira tayi y'an matan dake wajen ne suka gaishe da Arman ya amsa a takaice d'aya daga cikinsu ce ta kalli Aira tare da cewa "Wow waida tare kuke da Auntyn tamu yaya Ita ce ko?Harara Arman ya maka mata bata damuba Dan tasan Halin sauran ne suma suka kalli Aira sukace wow she's beautiful Yaya Gaskiya ta had'u Auntyn tamu ta fad'a Tare da zuwa ta zauna gefen Aira Ta kama hannunta ta ce " Sannu da zuwa Auntynmu ansha Hanya ya gajiya"Murmushi Aira tayi mata cike da kunya ta ce "Alhamdulilla" Sauran biyun ne suka mik'e D'aya ta je ta janyo hannun Aira ta ce "Muje ciki ki huta Karki biyewa tsohuwar nan ta k'ara miki Gajiya " ta fada tana kama hannun Aira dukansu sukayi cikin wani daki da ita Ja irai Hajiya tafada tare da kallon Arman ta ce "oh ni Mujahid yaushe rabonka da garin nan........โ๐ฟ
*Barka da Salla fatan kowa yayi sallah lfy Allah amshi ibadunmu ya nuna mana badโi da rai da lafiya*
*Masu fitarmun da littafi ina sane daku kuma ku sani na barku da Allah saboda hakkinane Ni da Yaya Arman na kudine akan Naira 200 kachal ku tuntubeni akan number wayata 07026166536 ki saya naki ki karanta cikin kwanciyar hankali ba sai an sata an kawo maki kikaranta ba ba girmanki bane hajiya*๐
๐ปโโ๏ธ
_*Miss Hajo ce*_๐ค๐ฟ
[7/12, 14:52] Hajo hajo: ๐
ฟ๏ธ.......*91&92*
Mujahed yaushe rabonka da garinnan "Dan sosa kai yayi ya ce " gwaggo kinsan yanayin aikin namu ne sai a hankali"Kaidai baka zumunci ne kawai zaka likawa aiki bikin y'an uwanka nawa akayi amma bakazoba To yanzu ba wannan ba ya jikin naka kasan munso zuwa Chan mu duba ka Allah baiyiba"Alhamdulilla Inna jiki yayi sauk'i "Masha Allah Ubangiji ya k'ara sauki Ai dazu mahaifiyar taka take kirana take Cemun Zakuzo kaida Bakuwa tafarayimun bayani kuma sai tace Saidai tazo" Sosa kai yayi tare da mik'ewa ya ce "Wlhko gwaggo bari naje na gaishe da Bappa " yana fad'ar haka yabar palourn Dan karma tayi mashi wata maganar..bangaren su Aira Suna janta a Gado suka zaunar da ita d'aya daga cikinsu ta ce "Ni suna Hasina wannan Maryam Waccen kuma y'ar bak'ar murjanatu" Ta k'arasa fad'a tanayiwa murjanatu Dariya "Hararta tayi ta ce " banza kin saba ko ina saikin nuna halinki na hauka"Tsaki Hasina taja ta ce "Kece ai za Ama kallon mahaukaciya bani ba" Tsaki Maryam taja ta ce "kudai kunji kunya gaban kowa saikun gwada halin " Itadai Aira na jjnsu batace uffan ba Maryam ce tashi sis kije ki watsa ruwa na hada maki komai na wanka "murmushi Aira ta sakar mata ta ce "To tare da mik'ewa ta shiga toilet ba ayi minti goma ba ta fito d'aure da towel jikinta lokacin da ta fito tuni hasina ta fito mata da wata rigar bacci Doguwar Riga Sanyawa Tayi Aira Bayan ta gabatar da Sallar magrib da isha i Abinci kala Ukku suka kawo mata ba yanda basuyi da itaba taci amma ta ce ta k'oshi " Mujanatu Ce ta ce Bari naje na fad'awa yaya takicin komai Tana fita ta sameshi a palourn Inna sunashan hira Bayan dawowarshi daga gaishe da baffa Kallonshi tayi ta ce "Yaya Aunty tak'icin komai fa ba yanda bamuyi da ita ba " Mikewa Arman yayi ya ce "tana ina" tana ciki "Bai jira ta sake cewa wani Abu ba ya nufi d'akin zaune ya sameta da hijab akan prayer mat Kusa da ita yaje ya duk'ursa ya ce " me yasa bakison cin abinci my cutie so kike ulser ta kama munke"Dagowa tayi ta Kalleshi tare da marairaicewa ta ce "Yaya banajin yunwa ne shiyasa zazzabin ne kamar yakeson dawomun" Tab'a jikinta yayi yaji ya fara zafi cike da damuwa ya ce "Sannu my dia Allah baki lafiya yanzu dai dan Allah idan baso kike hankalin yayanki ya tashi ba please Ki daure kici abincin ko Kad'an ne kinji y'ar lelena" Gyada mishi kai tayi ta ce "To yaya" Kallon Maryam yayi ya ce "mik'omin plate d'in" cikin Sauri ta mik'a mashi zaunawa yayi tare da Fara bata tana amsa batasaniba sosai ta ci Dan Arman na bata yana binta da zafafan kalamai bata saniba harta cinye plate din"wara idanu tayi ganin plate din ba komai ta ce "Yaya Amma tare mukaci" Dariya yayi ya ce "a a a da aljani kikaci" Hararar wasa tayi mishi ta ce "Sarkin fadan magana" Shafa sajenshi yayi ya ce "nid'in " Ehmana ta fad'a tana aika mashi da harara"Dariya Kad'an yayi ya ce "Ina son harararnan fa sosai cutie please kici gaba dayimun" Wara idanu tayi ta Kalleshi sai kuma tayi dariya magani ya b'alla mata Tasha tukwana ya Mike ya ce "ki huta sosai nima zanje na kwanta na Shawo gajiya" To my yaya have a nice dream "yana fita su Hasina suka kwashe da dariya " Hararar wasa Aira tayi musu ta ce "me kukema Dariya" Salon love mana Muma dai koba komai mun k'aru "Murja ta fad'a tana Dariya Nan suka shiga mata tsiya Inda ta Kyalesu Tayi Tare da kwanciya kan Babban gadon da saiya d'auki mutane da yawa Ba jimawa baccin gajiya ya kwasheta.
Washegari da misalin Goma na safe tayiwa Mummy a garin yola Wanda Bata fad'awa Daddy dalilin zuwantaba tadai cemai ne zataje zumunci wajen y'an uwa shi kuma daman baya hanata kasancewar Jirgi tahau yasa tazo da wuri Bayan tazo ta huta Inda y'an uwanta maza da mata suka dinga zuwa gaisheta tare y'ay'an yโan uwanta Dan masha Allah gidansu badai yawaba kasancewar mata hud'u Bappa ya jera Allah yayiwa biyu rasuwa yanzu saura biyu sannan mutane ne masu zumunci da girmama na gaba dasu kasancewar Mummy itace ta ukku a Duka gidan cikinsu Talatin a lokacin da tazo Aira bata saniba tana Chan sun baje dasu hasina sai hira ake Dan tuni ta saki jiki dasu kamar daman sunsan juna Dan sudin suna da wayau sosai irin wannan mutanen ne masu saurin sabo Arman ma baisaniba saida wani cousin d'inshi Suleman yazo ya fad'a masa Dayake part d'aya suka kwana Bayan ya shirya around 12 ya shigo Palourn a lokacin daga mummy sai gwaggo da Baffa saikuma Babban Yayan su Mamy Nasiru har kasa ya duk'ursa ya gaishe da mutanen palourn yayinda Mummy idonta nakan d'an nata Yana Dagowa suka hada ido biyu Harara ta maka mai da ta sanyashi yin kasa da kanshi '"Sanyawa bappa yayi aka kira Aira fitowa tayi cikin doguwar hijab d'in Hasina saboda kayantane ma ta sanya kasancewar irin jikinsu daya A sanyaye ta fito Kallonta mummy tayi tare dayi mata fara a ta ce "taho nan y'ata " a sanyaye Aira taje wajen Mummy tare da zama k'asar kujerar da take a kunyace ta gaishe da mutanen dake d'akin gaba d'aya suka Amsa mata cikin sakin Fuska"gyaran murya Baffa yayi tare da Kallon Arman ya ce "Yanzu mahaifiyarka tayi mana bayanin komai dake faruwa Wanda mu bamu da labari sai yanzu kamar yanda kukasani bana magana me yawa Saidai nayi Kad'an walau tayi dad'i walau kada tayi yanzu kai Mujahed maganar da Aka fad'a Gaskiya Ce Kai kayiwa y'ar uwarka ciki Dan Rashin Imani" D'agowa Arman yayi ya kalli vappa tare da Kallon Aira da tayi kasa da kanta tana hawaye ya ce "Wallahi tallahi Bappa ni wani Abu bai tab'a shiga tsakani na da itaba kuma gata nan a gabanku ku tambayeta" Kallon Aira Bappa yayi ya ce "Kinji abunda Yafada jikata da gaske yake ko Karya karkiji nauyi ko kunyar kowa ki fadamana Gaskiya" Ba abunda Aira take inbanda hawaye Cikin k'arfin hali ta gyad'a kai ta ce "Da gaske yake " Kallon Arman Bappa yayi ya ce "To meyasa akace ka amsa cewar kai kayi mata Bayan ba haka bane" Kanshi na kasa ya ce "Na amsane kawai baffa banason Ana cira magana d'ayane shiyasa " Kallon Aira Baffa yayi ya ce "To ke jikata Wa yayi miki Tunda dai tsohon mijinki ya ce " ba shi bane,sannan Mujahid ya ce bashi bane "Kukan da take rikewa Aira ta fashe dashi tare da cewa " Wlh Baffa zan iya rantsewa da alquran mai girma akan ban tab'a zina ba Nima bansan ya akayi hakan ta faruba amma wlh bantaba ba Banmasan ya ake ba ta k'arasa fad'a tana rushewa da kuka"Rungumeta Mummy tayi tare da Lallashinta ta ce "ki kwantar da hankalinki y'ata ni kaina ina tantama akan Abunnan kallon Bappa tayi ta ce " Bappa inason ka bamu izinin mu kaita Asibiti yanzu a k'ara gwadata Dan Gaskiya ni banga alamar wani ciki a tattare da itaba sannan ban yarda zata aikata hakanba"To Fatima kuje asibitin dan a tabbatar din ba matsala kallon nasir yayi ya ce "Nasir gashi ka rakasu asibiti Gwaggo ta ce " Gaskiya kam gwara Aje asibitin amma ni banga Alamun ciki a tattare da yarinyar nan Mai ciki kama da wa yake kowa yayi na am da wannan shawarar har Arman A tare da Mummy da Arman da Aira tare da Baba Nasir dake tukasu suka nufi general hospital Adamawa Suna zuwa basu bi wani layina Nan aka Auni jinin Aira tare da fitsarinta Dan Mummy ta ce awon komai za ayi mata itadai Aira tayi tagumi Sundau minti ashirin Tukwana Result ya fito Bayan Dr ya duba ya karanta kallonsu yayi ya ce "Ba wani Abu ke damunta ba face Typord ya kama ta sosai tun baikai haka ba Rashin shan magani yasa ya fara tsanani Sannan aman ma da take typord dinne shike sanya wannan Amma yanzu zan rubuta muku magani insha Allahu tayi sati Tana sha zata samu sauk'i Allah ya k'ara lafiya ya fad'a tare da Fara rubuta musu maganin" Sosai sukayi mamakin jin Abunda dr ya fad'a Arman ko wata nauyayyar Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Alhamdulilla daman nasan cutie bazatayi irin wannan Abun ba" Aira ko Itama Ajiyar zuciyar ta sauke Dan