NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   14 / 54

39K to 42K   out of 160.7K words

ta barmun gidana bansan ganinta"Aira kuka ta k'ara fashewa dashi ita kam ta shiga ukku dak'yal Mama da Mama Halima suka dinga bawa Abba hakuri suka samu ya zauna Mama Halima ta ce "Dan Allah yaya ka saurareni muyi magana munsan sunyi laifi amma kayi hakuri saika yanke mata hukunci cikin nutsuwa ai hannunka bai rub'ewa ka yanke shi ka yar" Abba na huci ya zauna ya ce "wani hannun tuni kake yardashi karya isheka da Wari ku maza ina Sauri ku fad'amun me ke tafe daku" Ajiyar zuciya Mama Halima ta sauke ta ce "Daman yaya akan maganar Mamana ce nazo mu baka hakuri Dan Allah kayi hakuri ka yafe mata Allah ma munayiwa laifi ya yafe mana " Ai babu wani zancen daidaitawa Nida wannan yarinyar tunda bazatabi umarni na ba to fa nima bazan sassauta mata ba Ai tunda har ta iya d'aukar kafa ta tafi har kaduna wajenki nikuma ai tafi k'arfi na ta koma wajenki da zama bani ba ita "cike da damuwa Mama Halima ta ce " wannan laifi na ne Yaya wlh ni na sanya Mujahid ya kaimun ita saboda nasan kayi fushi daman jira nayi ka huce amma kayi hakuri Dan Allah ina neman alfarma Dan Allah Dan darajar iyayenmu da suka haifemu suna k'asa ka taimakamun ka yafe mata wlh tayi nadama bazata sakeba "ta k'arasa fad'a tana hawaye " shiru Abba yayi yana daidaita nutsuwarshi na y'an sakanni.kafin ya d'ago ya ce "Wlh taci darajarki da kuma darajar iyayenmu da kika Ambata zan yafe mata ta zauna a gidana Amma saida sharuddan nan da zan lissafo guda hud'u kuma cikinsu ba d'aya da za a kuskure idan kun amince dasu to zata zauna a gidana idan kuma baku amince su ba to na hakura da ita ta koma gidanki ko kuma taje duk Inda zata na hakura da ita" Cikin Sauri Mama Halima tace "munyarda zamu amince insha Allahu wasu sharudda ne" Aira ko duk ta tsure tana like da Mamy sai kuka ta ke Itadai Mamy batace uffan ba Yaya Umar ma saurara kawai yake Dan baisan case d'inba daga Mama Halima sai Abba kadai suke magana "Abba ya ce " sharad'i na farko shine "zata zauna a gidannan bazata k'ara lek'a ko bakin get ba hatta ko Tahfex na cireta bazata k'ara zuwa ko ina ba sannan zata dawo nan part din ko bangaren Inna nayi mata iyakar shiga kun yarda da wannan?Ajiyar zuciya Mama halima ta sauke ta ce " Mun yarda,na biyu kuma "Babu zancen jonawarta Makaranta Kamar yanda ko wani d'ana nake tsaye musu harsu kammala Degree d'insu kuma shine Babban burina da tsarina tundaga kan yayyinta to banda ita ko Diploma bazatayi ba " Kallon Aira Mama Halima tayi ta ce "Kinaji kin yarda " gyad'a kai Tayi tana kuka Alamun ta yarda "Kallonshi Mama Halima tayi ta ce " Shima mun yarda " Na Ukku babu ita ba Yaron Chan Nayi mata katangar karfe dashi babu wace alaka ko a fili ko a boye da zata k'ara shiga tsakaninsu Shima kun yarda da shi?Mama Halima cikin damuwa ta ce "Haba yaya d'an uwanta ne fa " d'aga mata hannu Abba yayi ya ce "na fiki sanin hakan amsa kawai kun yarda eh ko a a " Kallon Aira Mama Halima tayi Ta ce "Kinaji abunda yace Amsa na wajenki kin yarda?Sosai Aira ta shiga tashin hankali amma kuma ba yanda zatayi muddin tanason zaman lafiya da mahaifinta dole ta amsa ta ce " Eh na yarda"Amma har cikin zuciyarta ba wai ta yarda zata rabu dashi d'inba ta amsa ne kawai Dan ta samu sassauci.Kallon Abba Mama Halima tayi ya ce "mun yarda " To hud'u kuma na k'arshe shine "Aure zanyi mata?Cikin tashin hankali Mamy ta mik'e ta ce " Aure kuma Alhaji Sadakarta kake nufin zaka bada ko me?Eh Aure Kamar yanda na fad'a Tunda shi take so kuma shi zanyi mata bazata daukomun magana ba sannan ko sadakar ta kama sai inbadata abunda ya dace da ita ai"Tashin hankali ba a gwada maka rana Aira ita bama zata iya cewa ga halin da take cikiba kuka kawai take " Mamy ce ta ce "Wlh Ba a isa ba Daman na lura duk cikin gidan nan ka tsani Y'ata Duka cikin Y'ay'anka wa kayiwa Aure a age d'inta sai ita Dan tsana me ta tsare maka a gidan shekarar sha 18 ma bata ida ba to Allah bazan yarda ba laifin me tayi ko cikin shege tayi ai sai haka Inbanda lalacewa akan d'an d'an uwanka ake wannan Abun laifine Dan sunyi soyayya dashi matsafine ko d'an giya ne ko kuma wani mashahurin boka ne da za a sanya mun y'a cikin wani hali dan tana sonshi ai ba sab'on ubangiji bane Ku barsu mana Suyi soyayyarsu inma Aure ta kama ni ina bada goyon baya d'ari bisa d'ari tunda suna son junansu amma wlh bazakayiwa y'ata Aure ba yanzu " ta k'arasa fad'a cike da masifa "Tashi Abba yayi ya nuna ta da yatsa ya ce " Sau nawa zan fad'a maki idan ina yanke hukunci akan y'ay'ana ki dainamun katsalandan Ke kike da iko akanta ko ni Na rantse da Allah idan ba so kike ranki yayi mugun b'aci ba na kowa ya b'aci ki k'ara shigarmun idan na yanke hukunci "ran nawan ya b'aci na kowama ya b'aci sai me ko me zakamun yau kamun a shirye nake wlh " Mama Halima ce ta kama hannun Mamy ta ce "Dan girman Allah Rahama kiyi shiru tun d'azu da muke magana bakisa bakiba yanzu ma kiyi shiru kiwa girman Allah da darajar iyayenki ki wuce d'aki "Dakyal Mama Halima ta samu Mamy ta wuce ciki " Mama Halima tace "Yaya ku rik'a sassauta zuciyarki Dan Allah kayi hakuri ka janye maganar ka ta k'arshe sauran Duka mun amince dasu na karshen ne yayi tsauri" Cikin fad'a Abba ya ce "to ku tashi ku bani wuri daman na ce muku ai d'aya bazan hakura cikin hudunnanba idan baiyi mukuba babu dole ku tashi ku barmun gida Aira da take shan kuka Muryarta harta dishe ta ce " Na amince Abba "ta fad'a tare da tashi tana kuka ta wuce Bedroom d'in Mamy tana Zuwa ta haye kanta ta fashe da kuka Kamar wacce akayiwa mutuwa " sosai kowa dake palourn saida ya tausayawa Aira sai sannan Yaya Omar yayi magana ya ce "Dan Allah Abba kayi hakuri ka janye na karshen" Na gama magana kuma babuja da baya Abba ya fad'a tare da tashi ya fice part d'inshi"Girgiza kai Mama Halima tayi ta ce "Nima Allah ya kawoni Allah ya kyauta tukwana ta wuce d'akin mamy ta samu Aira na kanta sai risgar kuka take Mamy ko tayi tagumi sai huci take " Zaunawa gefen gadon Mama Halima tayi ta ce " Kuyi hakuri Rahama Kalar tamu jarabawar kenan Allah ya bamu ikon cinyeta "Cikin hawaye Mamy ta ce " Yanzu Halima ki duba kiga Akwai adalci a maganganun Alhaji kuwa"numfasawa Mama Halima tayi tukwana ta ce "Ni fa a ganina duk wannan maganganun yayi su ne cikin fushi Amma bazai aiwatar ba tunani na kawai zai tsorata ta da haka ne amma sai nakega bazai mata Aure ba Ki duba kiga yayyinta Duka saida suka kammala Degree d'insu A kanta bazai karya akidarshi ba ku kwantar da hankalinku kawai tsoratarwa ce sannan ma idan yace zai mata Auren itada yanzu ya hanata fita ina ma zata fita bare har wani yace yana sonta " bakiji me yace Ba sadakarta zai bada Mamy ta fad'a tana hawaye "Duka fad'ine yayi Dan mu tsorata Amma bazaiyuba zai sauko nan kusa" Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce "kila kuma hakanne Allah dai ya shige mana gaba " Ameen Mama Halima ta fad'a Aira duk tanajinsu sai sannan hankalinta ya Dan fara kwanciya Dagowa tayi cikin kuka ta ce "Mama Dan Allah ki rok'eshi ya bari mu koma Kadunan tare" Chab Inani ina wannan Mamana kina ganin dak'yal ma muka samu ya amshemu idan nace xan koma dake ai rikicewa abun zaiyi ki bari idan aka kwana biyu Zan dawo nayi yanda nayi na shawo kanshi ya bani ke sannan ya huce sannan kuma ki kiyaye ki hakura da Mujahid na wani lokaci "Gyada kai Aira tayi tana Hawaye taje ta Rungume Mama tana kuka Dak'yal Mama ta lallasheta harta samu ta hakura.

Wajen la asr tana kwance a d'akin mamy kanta sai ciwo yake mata Amma ta shigo ta ce " Aira kije ya Umar na Kiranki"to ta fad'a tare suka fita a palour ta sameshi shi kadai Alamun Khady ta fita daga ita saishi yace Amma ta wuce ta basu waje kusa dashi taje ta zauna "Cikin nutsuwa ya ce " Hajara Naji Duka abunda kikayi yanzu Halimatu ke bani labari bani da labari sai yanxu na samu labari Dan kyautawa baku kyautaba Amma Duka ya wuce sai a tari gaba ke yanzu fad'amun Gaskiya kina son Mujahid ko a a magana ce tsakani na dake"Dagowa Aira tayi ta kalli ya Umar daman tasan shi baya da matsala Dan halin Mama yayo yana da hakuri ga nutsuwa komai cikin kwanciyar hankali yake binshi k'asa tayi ta kanta batasan lokacin da wasu zafaffan hawaye suka zubo mata ba ta ce "Yaya ina sonshi sosai kuma Shima yana sona banason a rabamu " ta k'arasa fad'a tana hawaye "Girgiza Kai Umar yayi ya ce " Arman bashi da Aibu Aira da zance wai ki rabu dashi amma ina baki shawarar kisan yanda kikayi kika rage sonshi a cikin zuciyarki sannan duk yanda zakiyi ki hakura dashi na y'an wani lokaci ki samu Ki shawo kan Abba ya barki ki jona makaranta kinajina duk abunda Abba yace kiyi kidinga yi ki dinga barin abunda ya hana saboda Kinsan dai Halin Abba mu Kanmu da girman mu da komai kiyaye umarninshi muke bareke Duka yaushe kikazo duniyar"Goge hawayenta tayi ta ce "Insha Allahu Yaya zanyi duk abunda kace nagode " Yawwa ko kefa y'ar wajen Inna sannan bance ki tada hankalinki ba kiyi rayuwarki.kamar yanda kike a baya kidaina sa damuwa a ranki ko so kike y'ar k'aramar kanwarmu ace ta kamu da hawan jini so kike tsufa ya kamaki da wuri"Murmushi Aira tayi ta ce "A a ayaya nadaina daga yau " To shikenan ko kefa yanzu kije kici abinci kinji y'ar kanwata"To yaya ta fad'a tare da tashi sosai taji d'an sanyi a ranta a ranta ta ce "Nidai nayi sa'ar yayyu Duka suna sona Allah na gode Maka da ka bani y'an uwa masu sona Nidai bansan wani Abu wai y'an ubanci ba har mamaki take idan a makaranta ana firar y'an uba ko ana zaginsu itadai Duka d'aya suka d'auketa" da wannan tunanin ta koma dakinsu ta tarar da Hafsa Na salla itama alwallar tayi taje tayi salla suna gamawa Amma ta zubo musu abinci a d'akin sukaci abinci su Ukku plate d'aya suna ci suna Hira Aira ce ta ce "Wai dazu daga ina kike naga kamar tare kuke da Abba " Daga B U K muke Registration mukaje Abba yayimun Bayan tafiyarki Mukayi jarabawar PUMB kuma naci sa a naci harsun bani admissions sosai na damu da bamuyi tare ba Kuma Kinga tare mukayi apply ta Online'"girgiza Kai Aira tayi ta ce "Allah ya taimaka ya baki sa'a nikam yanzu ba karatu ne gaba na ba nama fara hakura dashi " Sosai Amma tayi mamakin jin Abunda Aira ta ce "tana mata wani irin kallo ta ce " kamarya ba karatu ne ke gabanki ba to meye gabanki........✍🏿


*Ni da yaya Arman it's not free na kudi ne it's #200 via katin Mtn to 07026166536 VTU OR PC #300 kada ku fitarmun da littafi kudin karantawa kuka biya ba na mallaka ba*


_*Miss Hajo ce*_🤙🏿🤙🏿
[6/13, 23:20] Hajo hajo: 🅿️........*41&42*





Meye gabanki"Kawai haka nan ke Nifa karatun ma.ya fice a raina "Hafsa ce ta ce " Amma baki da hankali Aira to idan ba karatu ba zaman me zakiyi a gidan "Turo baki tayi ta ce " meye abun Rashin hankali ra'ayi ne kowa da nasa"to munji ra'yin ne amma me zakiyi banda karatu"Hmmm nifa wlh da so samu ne Kawai Ayi mana Aure *Nida Yaya Arman* wlh kwata kwata gaba d'aya hankalina baya kan komai yana kanshi kuma koma naje karatun Allah ba abun kirki zanyiba saboda tunaninshi ma bazai barni nayi karatu ba shiyasa ko a kaina da Abba ya ce bazanje karatu ba ni ya ma fa hutashsheni ai indai ba gani na nayi a d'akin yaya Arman ba matsayin matarshi to sannan ne hankali na zai kwanta har na samu damar yin karatu cikin kwanciyar hankali"sakato Amma da Hafsa sukayi suna kallonta Sosai ta basu mamaki Amma ta ce "Chabd'i lallai Aira waike kanki wani irin taurine dashi duk abun nan da akayi sabodake ba Aje ko ina bama Har kina tunanin wai Aure Aurenma da Arman kuma " Tsaki taja ta ce "To ina ruwanki ni bansan wani k'abli da ba Adi abar maganar" Hafsa ce ta ce "Ni banga laifinkiba Yanda Kuke baza wannan love d’in ai kawai gwara a shige daga ciki kowa ma ya huta" Dariya Aira tayi ta ce "Shiyasa nake mugun sonki sis " Dariya Hafsa tayi ta ce”Mudai a taimaka kar a samar mana D’an baba a waje a bari dai sai anshiga daga cikin dan naga dukanku ke da shi kan dancing yake “kulli a baya Aira ta kai mata ta kauce ta ce “ke dama yar iska ce wlh hafsa “Dariya hafsa tayi ta ce “Sorry uwar gida kuma Amarya a gidan Yaya Arman “insha Allah “Aira ta fada da karfi Amma ce ta ce "uhm sarkin tura turarre wannan ai ba a zuga ta" Dariya Aira tayi ta ce "da a zugani da kar a zugani duk abunda naso nake zugar bata hanani kuma bata sanyani indai akan yaya Arman ne " girgiza kai kawai Amma tayi dan kanwar tata ta riga da tayi nisa batajin kira Suna gama cin abincin Aira ta haye Gado ta kwanta Ta ce "Bacci zanyi kaina ke ciwo idan anyi magriba Dan Allah ku tasheni" kinsan dai baccin yamma ba kyau"Amma ta fad'a tana gyara Inda suka bata "ke kika San wannan Aira ta fad'a ta na jan blancket tayi kwanciyarta.
Sai Bayan magriba suka tasheta tana tashi taji kanta ya daina ciwo sallah tayi ta fito palour Ta tarar da Inna cikin Sauri Inna ta tashi ta tarbeta ta ce " y'ar lelena Shine kika tafi kika barni duk nayi kewarki gidan bayamun dad'i sai yanzu da nake tambayar Zainab ke ban labarin Abunda ya faru wai ubanki ko gidana ya hanaki shiga rabamu yake so yayi"Inna tafada tana kwakuro hawaye "Dariya Aira tayi ta ce " Haba My Inna aikinsan ni Dake mutu karaba ki bari kawai ya huce nasan zai barni"yawwa y'ar kirki ai daman Nasan ke y'ar arziki ce Bazaki juyamun bayaba "Itadai Aira murmushi tayi tare da tashi tace bari na shiga wajen Mamy tashi Inna tayi ta ce " nima bari na wuce daman ganinki kawai nazo"Hug din inna Aira tayi tare da shigewa d'akin Mamy a Gado ta tarar da Mamy da Mama Halima saishan hira suke daman Chan tunda aka Auro Mamy k'awayene saboda sa'annine "Tsayawa tayi tare da gyaran murya kallonta sukayi Mamy ta ce " lafiya"sosa kai tayi ta ce "Lafiya Mamy sannan ta kalli Mama Halima ta ce " Mama Dan Allah wayarki zaki aramun"Mamy ce tayi karaf ta ce "Uban me zaki mata da waya" Bakomai Mamy "wayar Mama Halima ce tayi ringing duba mai kiran tayi saikuma tayi murmushi ta d'auka Daga d'ayan b'angaren ARMAN ya ce " Haba Mama tun d'azu nake kiranki bata shiga ina my cutie tun d'azu na kasa samun sukuni kwata_kwata banji muryarta ba Yau idan banji muryarta ba ban iya bacci wlh Mama please ki kai mata wayar"Kallon juna Mamy sukayi saboda wayar a hands free take girgiza kai Mamy tayi Mama ta ce "To sarkin y'an Rashin kunya aikama tambaya mun Iso lafiya" Kamar Wanda zaiyi shagwaba ya ce "Nasanma kunje lafiya insha Allahu nidai bani ita please" Aira duk tana tsaye jin muryar sahibin nata sai taji wani farinciki ya mamaye zuciyarta Mama ce ta ce "zo ki amsa Aira hada tuntub'enta taje ta amshi wayar Ta Kara a kunne kamar wadda zatai kuka ta ce " My yaya "Ajiyar zuciya bangaren Arman ya sauke ya ce " My cutie are you okay "gyada mai kai tayi kamar yana gabanta " Alhmdll kunje lafiya ya hanya fatan baki wahala ba ko?gyad'a mishi kai tayi ta ce "Alhamdulilla " kallonsu Mama tayi zata tashi ta tafi "Mamy ta ce " Dawo ba Inda zaki gama wayar a nan "ta fad'a ta na Harararta " Chan gefe Aira taja ta tsugunna ARMAN ne ya ce "Yadai naga kinyi sanyi ko Abba ya dake ki" a a a yaya baimun komai ba su Mamy na wajen shiyasa kaji haka"ta fad'a yanda bazasuji ba "wai kina nufin a gaban Mamy muke waya kenan yanzu itama ta hakura muyi tare" murmushi tayi ta ce "Abunda nake tunani kenan Dan ko fad'a batayimun ba" Alhamdulilla Arman ya fad'a sannan ya ce "Gaskiya nayi farinciki daman ba na fad'a maki ba Ai wannan Abun da mukayi zai iya sawa suyi sanyi" murmushi Aira tayi Arman ya ce "to ban labarin ya kukayi da Abba" Kallon su Mamy tayi taga hirarsu suke ta ce "Yaya zan fad'a maka amma ba yanzu ba sai basa wajen" to yanzu ina wayarki wai Duka biyun fa basa shiga"tana part d'in Inna dukansu Idan na samu ko zuwa gobe zansa a d'auko mun sainayi chajinsu nasan mutuwa sukayi ba chaji"okay ke bazakije ki daukoba yanzu kinsan bana jure Rashin jin muryarki "Zanfada maka duka yaya sai anjima" okay bye dia take care of yourself"murmushi tayi ta ce "Don't mention my yaya" I love you my cutie ya fad'a cikin kasalalliyar murya k'asa k'asa ta ce"I love you too "tukwana sukayi bankwana Mama ta

14 / 54