NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   39 / 54

114K to 117K   out of 160.7K words

I love you so much My everlasting"sannan ya Mike ya nufi kitchen cikin.kankanin lokaci ya had'o mata lafiyayyan breakfast din soyayyan dankalin turawa da kwai sai kazar jiya d'aya dumama mata Yanzun ma da kanshi ya dinga feeding d'inta Inda daga karshe itama tayi feeding d'inshi yinin Ranar dai haka suka yishi cike da k'aunar juna Dan tuni Aira harta mance wahalar da tasha soyayya kawai suke zubawa ba kama hannun yaro washegari a tare sukayi wanka Bayan sun fito Aira na gaban mirror daure da towel jikinta Ya fito Shima daure da towel ta baya ya rungumota tare da far'a sinsinar wuyanta Ta madubi yake kallonta murmushi ta sakar masa ta madubin "Uhm baby yaza ayi dani" ya fad'a yana y'ar shagwaba "y'ar Dariya Aira tayi ta ce " Zumah na kenan ko yunwa kakeji"Jujjuya kai yayi ya ce "Ummm amma bata abinci ba" jin hakan ya sanyata Jan bakinta tayi shiru"Bakice komai ba my cutie ya fad'a yana shafa lallausan hannunta dake d'auke da kunshi"turo baki tayi ta ce Uhm yaya Me zance to"sorry my babe ki taimakawa Yayanki mijinki kinji"yaya zafi fa."Daukarta yayi tare da Yin sama da ita ya ce "Wannan Karin bazakijiba Kad'an zan miki" bai direta ko ina ba sai kan bed lokacin nan ma Aira ta dansha azaba gogan naku ko abunki ga sabon shiga Shine bai kyaletaba sai 12 na rana Shima saida yaga ta dinga yimai ihu hakan yasa ya rabu da ita Da kanshi yayi mata wanka sannan sukayi wankan tsarki suka fito Aira sai turomai baki take ala dole yayi mata laifi shiko bawan Allan lallashi kawai yake yana bata hakuri saida suka koma ya k'ara gasata sosai tukwana suka fito shi ya shiryata cikin shalauliyar wata k'aramar Riga Ganin ana kiran salla ne ya sanyashi kallonta cikin marairaicewa ya ce "Cutie naje masallaci nayi salla ko nayi a gida" tana tutturo baki ta ce "Kaje am okay" Kama kunnenshi yayi ya ce "a'm sorry my love nayi laifi ko yi hakuri" kamar mai jira ta fashe da kukan shagwaba ta ce "Aishine kamun wayau kace bada yawa zakayiba yanzu haka zafi nakeji" Rungumota yayi ya ce "Sorry my prince's ayiwa Yaya hakuri bazai sakeba kinji my love " turo baki tayi ta ce "Uhm Uhm " Saukowa yayi tare dayin knell down ya kama kunnanshi ya ce "Sorry my cutie to ki zaneni indai zaki huce" Sosai hakan yabawa Aira Dariya saida tayi dariya sosai kafin ta mik'e ta ce "Kai my Zumah Inani ina dukanka wace ni na hakura ka maza kaje karka makara salla" Murmushi yayi mata tare da mik'ewa yayi hug d'inta tare da bata peck a kumatu ya ce "ki kulamun da kanki kafin na dawo" Nima ka kulamun da kanka my hero Allah ya tsare munkai a cikin tafiyarta da kuma dawowarka sannan banda kallon y'an mata ta fad'a tana aika mishi da Hararar wasa"Dariya yayi yana karajin soyayyar Matar tashi sosai yaji dadin addu'ar da ta masa ya ce "Ameen Matar aljanna sannan yayi dariya ya ce " Ina ni ina kallon y'an mata ina da wannan zuk'ek'iyar a gida ai kowace mace kallon namiji nake mata ke kad'aice nakeyiwa kallon mace my prince's zuciyar Arman takice ke kad'ai ko kin manta ne"Murmushi tayi tana jin dad'i sosai ta ce "Hakane my hero a dawo lfy" yana fita itama ta mik'e Bayan ta dauro alwala ta gabatar da tata Sallar Azahar din Bayan tagama tajima tana addua nemawa aurensu albarka tukwana ta mik'e tana d'an tafiya dak'yal palour ta nufa kai tsaye kitchen ta shiga tana shiga tayi dube dubenta bataga komai ba na girki Juyawa tayi ta fito palour daidai da shigowar Arman kallonta yayi ya ce "Me ya kaiki kitchen matas" k'arasowa Inda Yayi tayi ta ce girkine zan daura kuma nashiga naga ba komai"Kama hannunta yayi tare da zaunar da ita ya Ce "wai gidanwa kikatabaga amarya tayi girki amaryarma Ta musamman kamarke babyn Yayanta aike y'ar hutuce Dan haka karna k'ara ganinki a kitchen akwai kuku da mukayi magana dashi zaidinga zuwa yana girki daga mundawo daga honeymoon Hakan yasa ban Aje komai ba saboda order zamu dingayi " Marairaicewa tayi ta ce "Amma my...rufe mata baki yayi yace " Nasan kinajin yunwa ya fad'a tare da bude take away din da yayo musu Shi ya dinga Bata a baki saida ya kosar da ita tukwana itama tayi feeding dinshi suna gama Aira ta kwanta Saman cinyarshi ta mik'ar da kafarta kan kujera wayarshice da ya saka layinshi na k'asar ba jimawa yaji tayi ringing cikin Sauri ya duba yana ganin number Mummy ce Sai sannan ya tuno laifin da yayi mata tunda sukazo bai kirataba yace mata Sun isa lafiya cikin Sauri ya d'aga tare da cewa "Hello Mummynah" ba wani Mummy ni ba kai nakiraba y'ata na kira Naji lafiyarta nasan da ita take da waya ai bazata kwana biyu bata kiraniba Kodan Naji saukarku lafiya "sorry mummynmu nayi laifi ayiman afuwa wlh tunda nazo ban d'ora layin k'asar nan ba sai yanzu shysa kiyi hakuri kinji mummynmu bazamu sakeba" Murmushi Mummy tayi ta ce "Sarkin dad'in baki to yakukaje lafiya " Alhmdllh Mummy munga gyara da akayi mungode Allah ya saka da alkhairi ya k'ara girma"ameen kawai Mummy tace tare da cewa "Ina y'artawa fatan dai kana kulamun da ita" Dariya yayi tare da shafa sajenshi ya ce "Mummy y'arki gata nan ina kula miki ita kamar kwai " Masha Allah haka nakesonji bani ita mu gaisa"Aira da tana jinsu cikin Sauri ta amsa wayar cikin zazzak'ar muryarta ta ce "Hello mummynmu nayi kewarki" Daga bangaren Mummy tace "oyoyo y'ata nima nayi missing d'inki kin tafi kin barni da kewa To ya k'asar fatan dai kinajin dad'in gidan" Lafiya qalu Mummy Alhmdllh Ya su Murja"Lafiyansu qlau su Murja na barosu Chan nadawo kano suna cewa idan kinyi waya a basu numberki suna son. Ku gaisa"murmushi tayi ta ce "Allah srk ina Gaishesu Mungode Mummy Allah kara arziki da girma “murmushi tayi ta ce "amen d'an tashi kusa dashi muyi magana" Kallonshi Aira tayi da Shima ita yake kallo"Ganin yanda ya bata fuska ya bata Dariya tare da tashi tashiga Bedrom ta ce "Mummy na baro" yawwa y'ata abubuwan nan Dana baki kina amfani dasu kuwa?kasa kasa ta ce "Nadaiyi amfani da miskin Mummy sauran ne banfara amfani dasu ba" Ajiyar zuciya Mummy ta sauke Dan daman batason ta fara amfani dasu kafin ya santa anfiso daga baya cewa tayi"to shikenan daga yanzu ki fara amfani dasu kinji suna da amfani sosai musamman Kinga sanyin nan da yayiwa AL Umma yawa "kasa da kanta tayi ta ce " to Mummy insha Allahu"Allah miki albarka maida mashi wayar fitowa palour Aira tayi tare da Kallon Arman dake shshsan magani Kara mishi wayar a kunne tayi amsa yayi cikin shagwaba kamar wani yaro ya ce "Shine Mummy Dan ba Aso inji abunda zakuce shine zaki ce ta tashi yanzu fa naga duk wariya ake nunamun ''Ai sirrin y'a da uwa ne ba dole saikajiba sarkin y'an sa ido sai anjima Ka dai dinga kulamun da y'ata sannan kar a takurata " tana gama fad'ar haka ta kashe Kallon Aira Arman yayi ya ce "Baby gulmata kukayi ko" Dariya tayi tayi da mashi gwalo tace "sarkin wayau badai zakajiba Mikewa yayi zata Ruga kamu d'aya yayi ya chankofa tare da dorata kan kujera nan ya shiga kissing dinga ba kakkautawa Aira ganin Abu na neman wuce goma da iri ya sanyata fashewa da kuka dolenshi ya kyaleta sati guda sukayi suna zuba love d'insu a gida Arman tuni ya fara mayar da Aira yar hannu Dan yanzu hartafara sabawa dashi Dan ta lura mijin nata Yana da tsananin bukatuwa ita kuma a duniyar nan bataga abunda zata hana Arman ba ga kuma magungunan da take amfani dasu na wajen Ummy Wanda suke Kara rikitashi Satinsu guda suka fara fita outing cikin gari sosai Arman yake zagayawa da ita wajejen shakatawa love sukesha ta ban Mamaki yauma sanye suke sunyi ankon K'ananan kaya amma rigar ta Aira irin polo dinnance Shima irinta a jikin rigar tata an rubuta Quen shi kuma an rubuta Princess ta yafa black din mayafi a kanta tayi rolling d'inshi sosai tayi kyau a bakin ruwa suka zauna sunata shan love d'insu tare da wasanni ta Ruga ya bita sosai suka shagala suke nishad'i sunyi ciye ciye sosai su ice cream komai ya burgesu saya suke yayinda suka biya mai hoto ya dinga kashe musu hotuna Inda daga karshe ya durk'ursa Aira ta Dare bayanshi tana Dariya Kowa na wajen harkokinshi yake kunsan rayuwar turawa ba ruwan kowa da kowa Ganin da gaske Arman a goye zai tafi da ita ya sanyata Fara zillo cikin shagwaba ta ce "Honey please saukeni" Dariya yayi ya ce "Ai tunda kika hau keda sauka sai a mota" Rufe fuskarta Aira tayi tare da tutsata a bayanshi"Dariya yayi sosai ya ce "Ai kunyarki a nan wajen ta banzace ba 9ja bace nan kowa Rayuwarshi yake a haka har saida ya kaita mota tukwana ya direta dukda kowa Harkarshi yake amma saida suka burge wasu mutanen a wajen,
Da dare tana jikinshi suna kallon hotunan da sukayi a wayar Arman sosai hotunan sukayi bala in kyau karewa hoton kallo Arman yayi ya ce " Ammadai na fara zama mijin tace wlh cutie da har na biyeki kika sanya wannan kayan kartan banza na ganemun surarki"Dariya Aira tayi ta ce "Yaya Ka manta kowa Rayuwarshi yake ba ruwan wani da wani" Harararta yayi ya ce "Kin manta a musulunce haramun ba maganar right ake ba" Jan bakinta Aira tayi shiru"janyota jikinshi yayi ya ce "Daga yau a gida kadai za a dingamun irin shigarnan cutie ki daina cewa Na barki ki sanya kinsan wani ganin ba komai nake iya hanaki ba saboda bansan b'acin ranki plc karki sake cewa zakisa kinji" tohm my prince's insha Allah bazan sakeba dazun ma naga kayan iri d'ayane kuma sunyi mana kyau shiyasa"Halshenshi ya sanya a Bayan kunnanta tare da Fara mata wani irin Abu marar fassarawa lokaci guda Aira itama ta kawo wuta Sosai sukayi ta abubuwansu a palour Inda daga karshe ya sungumeta sukayi bedroom d'insu".
Washegari jirginsu ya d'aga Paris Dan fara yawon honey moon Tunda sukaje k'asar kullum saisun fita Dan a hotel suka sauka haka zasu fita suyi ta hotuna a gurare da snap Sosai suke zuba love ta ban AL ajabi Satinsu Biyu a Paris suka wuce England Chanma sosai k'asar tayiwa Aira dadi Dan kullum Chanma saisun fita sun shakata saida sukayi wata guda a England Dan Aira k'asar sosai tayi mata dadi daga Chan kai tsaye Dubai suka wuce Ai Aira zuwanta Dubai ji tayi kamar karsu koma Dan k'asar tayi mata bala in dadi a nan ma har tayi wata kawa Zainab balarabiya ce sunje shakatawa suka had'u har tab'ata numberta kasancewar Aira najin labarci hakan yasa sukayi saurin sabo Saida suka kwashe wata biyu a Dubai Wanda Allah keda kullum saisun fita Daga nan k'asa mai tsarki suka wuce Dan gudanar da Aikin Umrah Sosai Aira taji wani sanyi da annashuwa a ranta jinta a kasa mai tsarki saitaji ai Duka k'asashen da taje ba Inda yafiyi mata dadi kamar saudiya sosai ta Zage damtse ta dinga gudanar Da ibadodinta Da kuma addua a kan Allah ya daidaita tsakaninsu da mahaifanta Satinsu Biyu suka gama aikin Umrah lfy suka wuce London Gidansu suka sauka Wanda kullum sai anshiga a gyarashi a lokacin watansu biyar da Aure Bayan sun huta sunci abinci Lafewa Aira tayi jikin Arman Ta ce "umm baby wai yaushe zamu koma 9ja nasan Mamy ma yanzu fushi take dani" shafa cikinta yayi ya ce "Ba yanzu ba Honey sai Babynmu yayi kwari sannan saisun Kara hucewa" k'asa tayi da kanta Tare Goge hawayenta ta ce "Yaya banda komai fa har yanzu" K'ara shafa cikinta yayi ya ce "Nidai ban yarda ba Inajin kamar nayi ajiya a cikin nan"Dagowa tayi ta ce " Yaya serious yanzu haka perioud nake"na yarda my prince's insha Allahu soon munkusa zama iyaye"wayarshice tayi ringing dubawa yayi yaga mummy ce kiranshi video call kasancewar ya bar data bud'e d'auka yayi tare da Kallon mahaifiyartashi ta Cikin waya ya ce "mummynmu"Aira ma murmushi tayi ta ce " mummynmu ina yini"Cikin fara a Mummy ta ce ''lafiya qalau ya gajiya sarakan yawo kunje sai wahalarmun da jika kuke daga dai yanzu saiku nemu waje ku zauna"kallon juna Aira da Arman sukayi sai suka kalli Mummy kasa da kanta Aira tayi yayinda Arman ya ce "Mummy wani jikan kenan" cikin jikin daughter mana nasan k'ilama ya fara girma b'oyemun kawai kuke ko?A a a Mummy ai kinsan da tana da ciki kece zaki farajin wannan albishir din wlh bata da komai yanxu haka perioud take"Jikin Mummy ne yayi sanyi Dan duk daukarta tuni Aira ciki gareta har tafara sa ran Dan sosai ta matsu taga y'an jikokin nata murmushi tayi ta ce "To Allah ya kawo mai amfani" Ameen Arman yace yayinda Aira ta tashi tana Goge hawaye tayi bedroom da kallo Arman ya bita Nan suka cigaba da Hira Mummy Wanda hankalinshi Duka yana kan Aira saurin yiwa Mummy bankwana yayi tare da binta yana zuwa ya sameta ta hade kai da gwuiwa tana kuka subhanalla meye haka cutie me akayi miki kike kuka kin.manta ked'in amanace a wajena kukanki kamar yana nufin ban rik'e Amanar da aka bani ba ya k'arasa fad'a yana zuwa tare da rungumota "Cikin shashekar kuka ta ce " Yaya wata biyar Da Aurenmu amma har yanzu bansamu ciki ba nasan kaida Mummy Duka kunaso karfa naki haihuwa ka daina sona"Rufe mata baki yayi ya ce"Banyi tunanin haka daga bakinkiba cutie ko da haihuwa ko babu bazan tab'a daina sonki ba sannan haihuwa da kika sani ta Allah ce Duka yaushe mukayi Auren wata biyar nefa har zaki Fara mita sannan Nida Mummy Duka munasanki wa ya ce maki baki haihuuwa da zaki zauna kina kuka Cutie bantaba fushi dake ba Amma kika k'ara irin haka zanyi fushi ki maza ki Goge hawayen nan"Cikin Sauri ta Goge hawayenta tare da cewa "Sorry my hero bazan sakeba daga yau kayi hakuri please" gyada mata kai yayi ya ce "na hakura cutie na y'ar gatan Yayanta" murmushi tayi tare da Lafewa jikinshi tana jin dad'in daddad'an k'amshin turarenshi A haka bacci ya kwasheta Arman ya jima Rungume da ita yana Kara tunanin yarinta irin ta Aira wai kawai ta zauna ta dinga kuka sai kace wacce ta shekara goma bata samu haihuwa ba murmushi yayi tare da kwantar da ita a hankali ya ce "Allah ya shiryamun ke my cutie Gefenta ya kwanta yana kallon kyakyawar fuskarta mai cike da kwarjini da haiba wutar sonta na k'ara fisgarsa shafa fuskarta ya fara a hankali tare da Rungumeta yayi kissing d'inta a goshi a haka Shima bacci mai dad'i ya kwasheshi cike da gajiya Dan akwai gajiya sosai tattare dasu......✍🏿


*07026166536 domin magana da marubuciyar*



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[7/15, 18:39] Hajo hajo: 🅿️.........*101&102*




......Sune basu tashi ba sai washegari karfe Tara Arman yayi farkon tashi Kallon Aira yayi dake baccinta hankali kwance kallon agogo yayi yaga Tara hada wani Abu cikin Sauri ya Mike yayi saurin fad'awa toilet Dan baisan har yakai hakaba batare da yayi salla ba Bayan ya gabatar da salla kallon Aira yayi yaga baccinta take har yanzu kin tadata yayi Dan yasan tana fashin salla kuma tana buk'atar Hutu palour ya fito Inda ya samu sabon kuku din da ya d'auka A palour ya tarar dashi Yana mopping har ya gama shara jinjina mashi da hannu Arman yayi shikuma baturen ya gaisheshi cikin girmamawa Bayan Arman ya amsa zaunawa yayi tare da komawa ya d'auko paper da biro ya rubuta duk wani kayan abincin da zasu buk'ata Mik'a mashi yayi ya ce "yaje ya sayo " Arman yana zaune harya dawo sosai ya shigo da jibga jibga kayan abinci Inda ya shiga sintiri dasu store din Gida har ya gama Kallonshi Arman yayi ya ce "Idan kazo da safe zaka gyara iya palourn kawai da kitchen iyanan zaka dinga gyarawa 6am ya kasance kazo ka gama sannan daka gama ta kitchen zaka dinga fita idan kana buk'atar wani Abu ka kirani a waya kawai basai ka shigo cikiba " Jinjina kai Yayi Alamun ya fahimta "Check din kudi sosai ARMAN ya rubutamai sannan ya yanke albashin da zai dinga biyanshi mai tsokar gaske daga lokacin nan kukun ya shiga kitchen ya fara aikinshi.
Arman ko dayan bedroom d'in yakoma Bayan yayi wanka ya shirya d'akin da Aira take ya nufa Inda ya sameta ta fito daga wanka daure da towel jikinta hand drayer a hannunta tana busar da gashin kanta da ta wanke ta baya ya rungomata " Dan Kara Aira tayi Dan ta tsorata"Dariya Arman yayi ya ce "Sarkin tsoro nine fa" Cikin shagwaba ta ce "Shine ka tsoratani hero" Murmushi ya sakar mata ya ce "Sorry Prince's" amsar hand drayer din yayi tare da Fara yi mata "Dariya Aira tayi ta ce " Kai Zumah me ina ka iya gyaran gashi"yau xanfara akan matas kede kawai kisa ido kiyi kallo yarinya"murmushi Kawai Aira tayi suna kallon juna ta madubi shiya gyara mata kan nata yayi mata stretching ya shafa mata mayiyyuka masu k'amshi Bayan tayi mata Parking "Sosai yayi kyau sai kyalli gashinan yake ya dirar mata har gadon bayawow yaya Amma fa yayi kyau kamar naje saloon" Murmushi yayi ya ce "da kina wasa ne da mijin naki" jinjina mai hannu tayi ta ce "Thnks mijin da yafi na kowa" Peck a kumatu yayi mata ya ce "Nagode Matar da tafi ta kowa a duniya" Saida sukayi shiriritarsu nan ma tukwana ya rabu da ita ya fita palour ita kuma ta shirya Cikin doguwar rigar atamfarta green Street gown sosai ta matseta d'an a jiki D'aurin zarah buhari tayi Ita kanta data duba kanta madubi tasan tayi masifar kyau Turarruka masu k'amshi ta faffesa palour ta fito Inda ta samu Arman yana kallon ball Kallonta yayi tare da sakar mata smiles ya ce

39 / 54