NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   25 / 54

72K to 75K   out of 160.7K words

ta samu ta ce "Dan Allah Alh kayi hakuri insha Allahu zamuyi mata fad'a zata daina sannan ina neman Alfarmar da ka bani na tafar mata da yaron insha Allahu kome mukayi gobe zaka jimu" Jinjina kai Abba yayi ya ce "Bakomai Ramlat amma yaron ki barshi a nan tunda ta iya tafiya ta barshi a tunaninta ko bazan iya Rikesu bane ko me gwara ki barmunshi " dak'yal Dai ta samu har Abba ya sauko ya ce "ta tafi da Amer d'in a tare da Amer Aunty Ramlat suka tafi gidan Yayansu suna zuwa sosai Aunty Ramlat ta shiga yiwa Mamy fad'a Inda ta shiga batanan take fita ba itadai Mamy batace uffan ba Hamdalarta d'aya kawai da Ta amso mata Ameer Dan tunda ta taho shi kawai take tunani " Kiyi Hakuri Aunty Insha Allahu hakan bazata k'ara faruwa ba ya hanya kunsha hanya "Allah sa hmm hanya Alhmdllh Aira dai ana Chan gidan miji" Badai taci gaba da kukanba Aunty "Kuka kuma da sauki to amma har muka taho tanayi" Goge hawayenta Mamy tayi ta ce "Amma Aunty kina ganin ba matsala gida d'aya aka had'asu da kishiyar?tab'e baki Aunty Ramlat tayi ta ce " to da sauk'i dai za ace Amma banga Alamun mutunci a tattare da wannan kishiyar tata ba ga Aira ba Wayau ba dad'in abun kawai da dangin mijin da mijin na sonta sun hana Wani abun Amma a yanda naga Alamun kishiyar nan da yaranta banga Alamun arziki a tattare da su ba "Innalillahi Mamy ta fad'a tare da Fara kuka ta ce " wlh Alhaji ya cuceni kawai sayarmun da y'a ne yayi yanzu Dan Allah akwai adalci a abunnan kuwa Aunty Aira za akai uwa duniyar nan kawai kashemun d'iya ne za ayi"tsaki Aunt Ramlat taja tace "daman ban fad'a maki ba rikitacciya kawai ke Ko karar nan ma na y'an fari bakyayi wai d'iyarki da agaban wasu manyan ne zasu miki d'aukar marar Kunya ko Dan ai baki da itama ai wasu ko sunan d'iyan farinsu basa fad'a wlh " ni bawani karar y'ar fari da zanyi akanme masu yinma sun daina wahalshe da kansu ne suma suke ai maganar Gaskiya Ce nidai kawai an cucemu Allah saka mana Mamy ta fad'a tare da d'aukar Amer dake mata kuka tayi ciki Daren ranar da tunanin halin da Aira ke ciki Mamy ta kwana ko baccin kirki batayi ba....Aira ita ce bata tashi ba sai wajen 12 jiri na dibarta haka ta tashi tana tashi Wanka ta shiga tayi tana fitowa ta shirya cikin Atamfarta Riga da sicket cikin k'arfin hali ta shirya ganin ana kiran salla ne ya sanyata tashi ta koma tayo alwala ta tada salla harta gama tana addu'ar Allah yabawa Arman lafiya ta jima tana mashi Addu'ar neman samun lafiya tukwana ta koma Gado ta kwanta yinin ranar a rufe ta yini a d'aki ba tare da taci komai ba yunwar ma batajinta saboda tashin hankalin da take ciki Saidai idan taji kishirwa ta tara ta sha a tap d'in toilet Alh Yusuf ko sosai Rashin fitowar tata ya dameshi sau Ukku yana turawa laila takai mata abinci Saidai ta koma tace mai a rufe shi da kanshi yaje Dan yakai mata amma bata bud'e ba cike da damuwa ya yini Hajiya saude ko mamakin al'amarin nan take Gashi tana son tambayar Alh Saidai kuma tace ba ruwanta idan tayi tsami saji....washegari Aira da azababbiyar yunwa ta tashi ga ciwon kai dak'yal ta iya mik'ewa taje tayi wanka saboda yanda jiri ke d'ibarta shiryawa tayi cikin doguwar rigar lace d'inta black da yasha kyau d'inkin Street gown sosai kayan suka amsheta simple d'aurin dankwali tayi zaunawa tayi bakin Gado tare da tagumi sosai ta Lula duniyar tunani ga yunwa da take ji cikinta banda k'ululu ba abunda yake knoking Tajiyo Hakanan dai ta tashi saboda yunwa a hankali ta bud'e k'ofar Tare da Yin tsaye k'arewa Aira kallo laila ta tsayayi sosai ita kanta ta tsorata da ganin kyau irin na aira kafin ta tab'e baki ta ce "Kije Palour Daddy na nemanki " Sosai gaban Aira ya fad'i idanunta duk sun firfito kamar mai shirin yin kuka ta ce "To gani nan zuwa " Juyawa laila tayi tana Jan tsaki tana komawa Ta zauna kusa da Mamanta sai tsaki take ja "Kallonta mamanta tayi ta ce " Yadai Auta naga kin dawo kina tsaki"Haba Mama wlh Dan bakiga ba yarinyar da Daddy Ya auro ba Duka cikin gidannan ba sa anta hatta ni na girmeta nesa ba kusa ba Duka bata wuce 16to17 ba wannan ai abun Kunya ne Wlh a k'awayena ma sai sumin gori dukga mata nan manya birjik a gari amma ya rasa wacce zai auro sai wannan kamar fara da k'ilama ko fitsarin kwance bata gama ba "Girgiza kai Mama tayi ta ce " Uhm bari dai ta fito nima na ganewa idona takaici"Suna ganin shigowar Daddy sukayi shiru kallon laila yayi ya ce "ta bud'e " Cike da jin Haushi laila ta ce "Eh ta ce gata nan" Cike da farinciki Alh Yusuf ya ce "Bari naje na gani" Cike da takaici Saude ta mik'e ta ce "Ai saika dawo ka zauna ba ankira maka ita ba sai wani rawar k'afa kake gaban yaranka ko kunya" Shidai Alh baice komai ba yadawo ya zauna itama Saude ta zauna tana cika ta na batsewa Laila na wucewa Aira ta saki Ajiyar zuciya tare da Goge hawayen da ya zubo mata ko saboda yunwa yau dole ta fita gyalenta ta janyo tare da d'oroshi a Samar ka flat shues ta sanya sosai tayi kyau a haka ta fito tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki harta Iso katoton palourn gabanta na fad'uwa tana isowa tsaye tayi tare da Kallon Matar da ta tabbatar kishiyartace sosai ta k'ara tsorata Dan girman Matar ya tsorata cike da tsoro tayi k'asa da kanta Daddy ko tunda ta shigo yake kallonta yana Kara godewa Allah da ya bashi wannan zuk'ek'iyar Matar yasan ba k'aramun sa a yayi ba cike da farinciki da annashuwa ya ce "Ki k'arasa ki zauna Baby" sai sannan Aira ta Kalleshi tsaki taja a cikin ranta ta ce "tsohon najadu kawai ba ko kunya wai baby" a hankali ta k'arasa shigowa palourn tare da zaunawa kujerar nesa dashi"baby ki matso mana nan"ya fad'a yana nuna mata Inda yake "bata Kalleshi ba Aira Haka bata matsa daga Inda take ba a hankali ta d'ago ta kalli kishiyartata cikin murya mai shirin yin kuka ta ce " ina kwana"Hajiya saude da tunda ta shigo take kallonta Sosai kyan Aira ya tsoratata amma kuma tayi mamakin yarinya k'arama da kyau da komai ta auri wannan tsohon gashi tasan mahaifinta Shima me kud'i ne bare tace Auren kud'i tayi sosai tashiga kogin tunani jin Aira na gaisheta ya sanyata saurin fusgewa ta ce "Lafiya ya bakunta" k'asa da kanta Aira tayi ta ce "Alhamdulilla" Alh Yusuf ne yayi gyaran murya ya ce "to Alhmdllh ba komai yasa na had'aku anan ba sai Dan kusan juna sannan ku had'e kanku Nunawa Aira Hajiya saude yayi ya ce " wannan ita ce Saudatu matata ce uwar gidanki kenan Ki girmamata sannan kiyi mata biyayya "Sannan ya kalli saude ya ce " ita kuma basai na miki bayanin komai ba kinsan komai abunda nakeso Dan Allah ku had'e kanku sannan ku zauna lafiya sai magana ta k'arshe maganar raba kwana kowa saita fad'a yanda takeso Ayi"cike da gadara Hajiya saude ta ce "Masha Allah yayi kyau Ango Nidai bani da matsala da kwana na bar mata nau da nata Har wata Ukku Asha amarci lafiya tana gama fad'ar haka ta mik'e cike da b'acin rai Ta bar wajen " Aira ko gabanta banda fad'uwa ba abunda take tuni harta Fara hawaye Alh Yusuf ko d'age kafada yayi yayi tare da tashi yaje ya zauna kujerar da Aira take suna gogar juna a hankali ya ce "Beauty na kinajin yunwa ko" Laila ko ganin wannan kayan takaicin ya sanyata tashi cike da b'acin rai tabi mamanta cike da masifa ta ce "Wlh akwai d'anyen aiki a gidan nan Mama Dan waccen Amaryar Area take ko uwar wa wlh wataran saina mata d'an banzan dukan da zata kasa tashi yanzu haka fa Daddy ba ko kunya Yaje kamar zai runguemeta ita kuma y'ar duniyar har wani sissine kai take " Tagumi Hajiya saude tayi ta ce "Duka zanyi maganinsu barni dasu ni nama zaci wace macen kirki ce aka auromun har ina tayar da hankalina Ashe wannan figaggiyar ce yo in tsaya kishi da wannan abar ma ai Naji kunya " Wlhko Mama ai zataci ubanta da mu take zancen Ammafa Mama naga kamar tsoro gareta bakijin yanda take magana kamar zatayi kuka "nima na kula da hakan barni dasu...Saurin tashi Aira tayi cike da tsoro Dan ta lura mutumin nan kwata kwata baida kunya tana zumburo baki " murmushi yayi ya ce "Sorry me zaki ci " Komai ma ta bashi amsa tana kauda kai Alh Yusuf da kanshi ya tashi yaje dining ya hadawa Aira break fast tukwana ya dawo cike da kulawa ya ce "na had'a maki Prince's muje " tana cika tana batsewa Aira ta tashi Bayan ta zauna a dining shi ya zuba mata yana kokarin fara bata ta mik'e tare da zare dara daran idanunta ta ce "Wai meye haka Daddy Nifa har yanzu Kallon uba nake maka meye haka d'in ka bari zanci da kaina idan ba so kake Duka na fasa cin abincin ba wlh kaiko kunyama baka da ita " ta k'arasa fad'a tana hawaye "Sorry sorry beauty kici da yawa bari ma na bar wajen tunda bakyaso yafada yana komawa palour tsaki Aira taja Dan ta tsani mutumin Chan Tare da Fara yin break fast d'inta.........✍🏿

*NI DA YAYA ARMAN it's not free it's for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*




_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/27, 22:01] Hajo hajo: 🅿️.........*67&68*







...Saida ta tabbatar da cikinta ya cika tukwana ta sha ruwa tare da Goge hannunta da tissue satar kallon Daddy tayi ta ga hankakinshi Duka yana kanta tsaki taja tare da mik'ewa tayi hanyar bedroom d'inta ya ce"Beauty bazaki zauna muyi hira ba"Tsaki Aira taja tare da galla mai harara ta ce "Kayi hira da Television badai niba kai ko kunya ma bakaji Auren y'ar cikinka mugu kawai azzalumi ka rabani da Masoyi na Allah ya isa tsakani na dakai ta fad'a fashewa da kuka tare da rugawa tayi bedroom d'inta ta fad'a Gado taci gaba da kuka Soyayyarsu da ARMAN ta shiga dawo mata cikin kwalwa tajima tana kuka yinin ranar ma a d'aki ta yini tare da kulle d'akinta bata fito taci komai ba Daren ranar ma ba irin bugawar da bai mata ba Amma taki bud'e mashi rayuwar Aira gidan Alh Yusuf cikin k'unci taci gaba dayinta Kullum tana rufe a d'aki Saidai idan taji yunwa ta fito taci abinci ta koma bata yarda tana had'uwa da mutanen gidan Alh Yusuf ko hakan sosai yake damunshi a haka har akayi sati guda Aira duk ta rame saboda zullumi da tunanin Arman da misalin k'arfe hud'u na yamma zaune take bakin gadonta tayi tagumi tunanin halin da take ciki kawai take siraran hawaye na zubo mata ita so take ko sau d'aya ne tama ji halin da Arman yake ciki amma ba hali Jiyo knoking tayi a d'akinta Kamar bazata bud'e ba saikuma ta mik'e zuwa tayi bakin Kofar ta ce " wanene"Idan kika bud'e ai zakiga wacece "Laila ta fad'a tana Jan tsoka jin Haka ya sanya Aira bud'ewa " Cike da Kallon rainin wayau Laila ta ce "Kije Palour Mama na nemanki yanzu yanzu sannan kuma batasan jira"To Aira ta fad'a tare da komawa ciki ta sanyo hijab ta d'ora doguwar rigar jikinta kasancewar me d'an d'amewar nan ce a palour ta tarar da Su mama tare da wata mata da yara su hud'u "durk’usawa ar k'asa Aira tayi ta ce " Ina yini Mama"Tsaki Mama taja ta ce "Kinga bansan kinibibi da salon barikanci a ina na zama mamanki idan na haifeki ai bakin auremun miji ba Dan haka ki rik'e sanabe da kinibibinki kina jina " Kasa Aira tayi da kanta hawaye nabin kumcinta "Zuhura ce ta ce " Kan uban Chan Amma wlh Daddy Ya gama damu daman wannan abar ce ya auro har yake wani rawar k'afa wannan ai zubda girma ne Wlh ki dubeta fa Mama da Kad'an ta girmi Intesar babbar y'ata a jikima intesar ta fita idan za a had'asu dambe saita kada ita ma.wlh me yasa Daddy zaiyi mana haka bama sa'ar autarsa ba Laila kanta fa ta girmi yarinyar nan Inma Auren zaiyi yaje ya nemu manyan mata mana wlh Mama har amfara fad'amun magana cikin kishin Sauri na wai ubana ya auro sa ar jikarshi wannan ai raini ne Daddy Ya saya mana wlh "ta karasa fad'a cikin Masifa " Dariya mama tayi ta ce "Kema kya fad'a Zuhura ai tunda har ta iya Aure mun miji Saidai ta zama y'ar boyi boyi na amma nafi k'arfin nayi zaman kishi da wannan abar "Aira dai na jinsu Goge hawayenta tayi cikin ranta ta ce " Da kunsan yanda na tsaneshi da bakun fad'a haka ba ni kaina a ra ayin kaina ina zan auri ubanku sosai takejin da tana da dama da saita fad'a musu magana amma ita harga Allah tsoronsu take Dan karsu jibgeta a banza "Tsawa Mama ta daka mata ta ce " d'ago ki kalleni Munafuka cikin rud'ewa Aira ta d'ago hawaye na bin k'umcinta "ki bud'e kunnanku ki saurare ni da kyau Daga yau babu Wanda zai Kara maki girki kici a gidan nan kamar yanda kikasan Aure Har kika auremun miji to haka zaki saki jiki kiyi aiki daman na Daga maki kafane na sati guda Dan haka daga yau zaki Fara girkinki kina jina" Cikin rudewa Aira ta ce "Eh naji" yawwa to yanzu tashi ki Mike ki shiga kitchen ki girka mana abincin Dinner"Mikewa Aira tayi ta ce "Me za a girka tsaki Mama taja ta ce " tuwo zakiyi mana da miyar agushi"Kamar zatayi kuka ta ce "Wlh Mama ban iya ba kidai fad'a wani abun" Ohhh baki iya ba Aiko yau zaki koya ai Aure kikazo ba Hutu ba saiki koya daga yau"Kuka Aira ta fashe dashi Sakato duk sukayi suna kallonta cike da mamaki Zuhura ta ce "Ikon Allah wai kodai Reno ne Daddy Ya kawo maki Mama bamu saniba" Tsaki Laila taja ta ce "wani salon barikanci ne" Mama Tsawa ta daka mata ta ce "Dukanki nayi da zaki yimun kuka Munafuka" girgiza kai Aira tayi da goge hawayenta cikin muryar shagwabar da ta zaune mata ta ce "To yi hakuri Mama Allah ban iya tuwo ba karnayi kuma ba daidai ba kimun fad'a" Tsaki Mama taja ta ce "Jeki dafa shinkafa da miya" To Aira ta fad'a tare da Goge hawayenta tayi hanyar kitchen Dariya Zuhura ta fashe da ita ta ce "Ai inaga nan gidan zandinga zuwa kallon drama Mama wannan ai fitar da ita gidan nan Abu me sauki ne bakiga yarinya ce kuma matsoraciya wannan ai ba kishiya ba Daddy Ya kawo maki y'a ce sai yanda kikayi da ita" murmushi Hajiya saude tayi ta ce "Zuhura kenan Ai kishiya kishiyace Zandai gyara musu Zama danma karkiga yanda Daddynku ke rawar k'afa a kanta ke daga zuwanta fa harya fara sauyamun saina fad'a magana ya take kingako ai matsala ce ta shigomun gida" haka dai suka cigaba da tattaunawarsu akan Aira Aira ko Tana shiga kitchen din aiki ta fara ba kama hannun yaro tanayi tana kuka Dan ita bata saba da aikin wahala a gida ba tunda Maid house ke masu Saidai wani karin Mamy ta ce tazo ta tayata Dan ta koya mata kafin magriba ta gama komai sai huci take tana hada zufa tana gamawa tahau Jerawa a dining Hajiya saude na kallon shige da ficen ta murmushin mugunta kawai take Dan da gangan ta kori me aikinta saida Aira ta gama Jerawa sai sauke numfashi take tukwana taje ta zauna Kan sopa tana sauke numfashi ta ce "Na kammala Mama" Kallonta Mama Tayi ta ce "Sannu " yawwa Aira ta fad'a tana niyyar tashi Mubarak ya shigo da earpiece a kunnenshi yana tafiya ta y'an duniyar nan "tunda ya shigo ya kafe Aira da idanu harya zauna yana kallonta Wow she's Beautiful babe Mama ina kika samo mana me kyau haka" Aira jin Haka sosai gabanta ya fad'i Mikewa tayi cikin Sauri tare da Kallon Mama ta ce "zan shiga ciki" okay kije "Haba beauty ya zaki tafi kuma bamu gaisa ba " ya fad'a yana karkace baki Kallonshi Aira tayi ta kalli Mama dake aika mishi da harara batare da tace uffan ba ta wuce ciki har tuntube take Dan Sauri tana zuwa ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ohh nima Allah ya kawoni Allah ka fitar dani daga halin nan da Nike ciki sannan ta fashe da kuka ta ce " Yaya Arman ina kaje kadawo please ga airanka nan cikin wani hali karka manta alk'awarinmu"ta k'arasa fad'a tana rushewa da kuka tana kuka taje tayi wanka tayi salla tana ta addu'ar Allah ya kawo mata sassauci Aira na barin palourn Mubarak ya bita da Kallo har wani Had'iye yau yake Kallonshi Mama tayi cikin b'acin rai Ta ce "Bansan iskanci Mubarak Meye haka" Mama please wacece wlh tana da kyau nidai tayi mun ina sonta plx Mama ina kika samota ko y'ar uwarmuce ban saniba Kai cikin danginku babu farare Mama Plx ina kika samota "Wani irin kallo ta watsa masa ta ce " To ka nutsu tun wuri ma ka kama kanka Amaryar Daddynku ce"what Mubarak ya fad'a yana mikewa ya ce "Wai Mama kina nufin wannan itace amaryar da Daddy Ya auro kai amma wlh Daddy nidai ya cuceni wannan ai dani ta dace ba shiba yayimun shigar Sauri Gaskiya nidai sonta nake" Wlh babu ruwana Mubarak tun

25 / 54