Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
wuri ka kama kanka kasan Daddynku ya ji maganar nan ba k'aramun hukunci zai yanke maka ba Sannan karna karajin ka fad'i Kalmar kana sonta kasandai ko sakinta Daddynku yayi babu Aure tsakaninku Dan Haka karna karajin haka ta fito daga bakinka"Cike da jin Haushi Mubarak ya Mike yana gunguni tare da barin palourn yana sharce kanshi da masharcin dake mak'ale cikin sumarshi Haka rayuwa taci gaba Aira kullum cikin k'unci take ga aikin abinci da take azabtuwa Dan Hajiya saude har girkinta Aira take sanyawa tayi mata ita kuma Aira na tsoro dole haka zata dirtsawa katti abinci wani lokacin ma ba ci take ba kullum Saidai ta yini d'aki tana kuka gashi Hajiya saude ta ce ta sake ta fad'awa Daddy tana aiki ita kadai tasan abunda zata mata abun duniya duk ya isheta ga Mubarak da yake takurawa rayuwarta shiyasa yanzu ko Kad'an bata fitowa Daddy ko saita kwana biyu bata ganshi ba Dan har yanzu kulle d'akinta take tabar key din jiki Daddy kullum cikin damuwa yake Dan ko Kad'an Aira taki sakin jiki dashi ko tana palour da taga shigowarshi zata maza ta koma daki ta kulle kamar dodo hakan ba k'aramun damunshi yake ba a haka dai da dad'i ba dad'i har Aira tayi wata guda a gidan Wanda cikin k’unci tayishi Dan Hajiya Asabe da y'ay'anta sosai suke musguna Mata Saidai tayi kuka ta gode Allah duk ta rame lokaci guda Yau Aira ganin Daddy Ya fita wajen la asr ya sanyata fitowa Farfajiyar gidan Sai sannan take karewa gidan kallo tana nan zaune sanye take cikin atamfarta mai golden doguwar Riga rigar ta d'an dameta kallabi kawai ta yafa Mubarak ne ya shigo gidan tunda ya hangota ya sauke ajiyar zuciya Dan Yajima bai gantaba sosai yake kallonta yana k'ara yaba kyau da zubin halitta irin tata harya karaso kusa da ita ya zauna Aira da batasan da wanzuwarshi ba saida taga zaman mutum kusa da ita ya sanyata Juyawa ido hud'u sukayi Da Mubarak gabanta na fad'uwa saurin matsawa tayi murmushi yayi ya ce "Ina yini Auntynmu" Harararshi Aira tayi tare da turo baki "Y'ar Dariya yayi ya ce " tofa Aunty daga gaisuwa sai harara"Kallonshi Aira tayi saikuma ta ce "Lafiya" Yawwa ko ke kefa beauty hutawa kike kenan"ba tare da Aira ta Kalleshi ba ta ce "ummmmm" nan Mubarak yayi ta janta da hira tana kaucewa tun tana harararshi tana fad'a mashi magana harta dawo tana Dan maida mas dan takula Dan naci ne kuma ga alamu duk cikin gidan ya fisu mutunci cikin hirar ne ya ce "Amma na tambayeki mana Aunty" inaji"Aira ta fad'a cike da kosawa Dan ta fara gajiya da surutunshi "Dan Allah wai garin ya kika auri old man d'innan yanda kike da kyau da diri d'innan me ya kaiki Auran tsohon mutumin nan Allah yayi miki kyau da fari kamar baturiya aike matar Manyan Yara ce masu jini a jika y'an tashe ba tsaffi ba " Cike da mamaki Aira ta juyo tana Kallonshi ta na mamakin wai ubanshi yake fad'awa haka Sai sannan ta lura da tsaf d’an duniya ne ma "tsaki taja tare da cewa " Saikaje ka tambayi shi uban naka ya baka amsa"Daddy ne tunda ya shigo yake kallonsu Yasan sarai halin d'an nashi cikin zafin nama ya nufi wajensu kallon Mubarak yayi ya ce "Ubanme kake A nan " Tashi yayi yana wani babbasarwa ya ce "Hutawa nake Nida Beauty " Daukeshi da Mari Daddy yayi cike da b'acin rai ya ce "Matar tawa Dan ubanka d'an iska to wlh na k'ara ganinka kai da ita ni kad'ai nasan Abunda zan maka xakaja in koreka daga gidana " Sannan ya kalli Aira tare da daka mata Tsawa ya ce "Wuce ki koma ciki" Aira sarkin tsoro tuni ta rud'e tare da rugawa tayi ciki Dan yanda taga ranshi ya b'aci kamar zai daketa tana shiga da gudu ta fad'a d'akinta sai huci take kulle d'akin tayi tare da kwancewa ta fad'a Gado tare da fashewa da wani irin kuka mai cin rai ta ce "Yaya Arman ina kashiga ka barni har tsawon wannan lokacin yaya idan baka dawoba zan iya mutuwa ka dawo Ina cikin wani hali yaya ina cikin begenka yaya kazo ka fitar dani daga rayuwar k'uncin nan ina cikin wani hali yaya ba uwa ba uba ba d'an uwa a kusa dani sannan babu kai........✍🏿
_*Miss Hajo Ce*_🤙🏿
[6/29, 14:10] Hajo hajo: 🅿️.........*69&70*
......Sannan kuma Babu kai yaya Ya kukeso nayi da rayuwata ne Wai sosai take kuka tana cikin kukan ta jiyo bubbuga k'ofa Banza tayi ganin yanda ake buga mata da k'arfi ne ya sanyata Jan tsaki ta ce "waye wai" Nine kizo ki budemun kuma wlh kika bari na balle k'ofar na shigo da kaina zakisan sauran"Wara idanu Aira tayi jin muryar Daddy saikuma ta mik'e tare da dauro jarumunta kama k'ugu tayi ya ce "idan kuma nak'i bud'ewar saikayi me" Ki bud'e nace na fad'a maki"Bud'ewa Aira tayi tare da ja da baya Cike da b'acin rai Alh Yusuf ya shigo Aira ko ja baya tayi sosai gabanta ke fad'uwa amma ta fusge"na k'ara ganinki ke da Mubarak ko Wani Abu ya had'aku ranki zaiyi mugun b'aci kina jina"Kallonshi Aira tayi daga sama har k'asa taja tsaki ta ce "da Allah Malam in ka gama zaka iya fita ni ina da aikinyi"kwantar da murya yayi ya ce " Wai meke damunki ne Beauty kin manta ni mijin kine aljannarki tana k'ark'ashin k'afata idan na take bazaki shiga ba meyasa kikemun Rashin kunya ko ba wannan ba aikin darattani Dan girmana da kuma matsayina na abokin mahaifinki"iyeeee Aira tafada tana kama hab'a tare da mashi wani irin kallo ta ce "anzo wajen to kai bakaji kunyar Aure na ba matsayina na y'ar cikinka sai nice zanji kunyar gaya maka magana ai wlh tunda harka nace ka Aure ni ka rabani da Masoyi na to ba wani sauran mutuncinka a idona ya Riga ya zube sannan kuma ni Aljannata bata k'ark'ashin k'afarka in kaga dama ma ka take tana k'ark'ashin k'afar yaya Arma.....Kasa k’arasa maganar tayi sakamakon Rufe mata baki Alh Yusuf da yayi tare matseta jikin Bango cikin zafin rai ya ce " Karna sake na k'arajin kin Ambatarmun sunan wani kato a cikin gida na sannan Aurenki da nayi aiba haramun bane raya sunnanar ma'aikice zaki dinga daukarwa kanki zunubi a banza sannan shi kanshi rufemun k'ofa da kike ba k'aramar azaba kikesha ba sanine bakiyi ba Ga kuma hak'k'ina dake kanki tsawon lokacin nan nayi Aure amma Nida Wanda banyiba duk d'aya muke d'aga miki k'afa ne kawai nake bawai Rashin kunyar da kikemun bace tasa na kyaleki a yau naga damar amsar hakkina dole na amsa kota tsiya ko ta arziki"gwalalo ido Aira tayi a lokacin da za a auna jininta to yahau d'ari Ukku kirjinta in banda dabdab ba abunda yake a zuciyarta ta k'ara jinjina lamari na Alh Yusuf lallaima baida kunya wlh wai haryake mata maganar wani hakki sosai tsoro ya kamata Dan a duniya bata da burin da ya wuce ta kaiwa Arman budurcinta ba wani banza ba Hakan ya sata tsorata Dan tayi alk'awarin ko zata mutu Bazata tab'a bawa wani budurcinta ba Bayan yaya Arman kwantar da murya tayi cikin muryar tausayi ta ce "Dan Allah kayi hakuri Daddy bazan sakeba na daina Dan Allah tadani numfashina na daukewa" Matsawa Alh Yusuf yayi daga jikinta ganin haka ya sanya Aira saurin tashi tare da matsawa "Kallonta yayi ya ce " Daga Yau karki sake kulle d'akinki kinji na fad'a maki ba kulle d'akin zaisa nak'i miki abunda nayi niyya ba "Cikin tsoro Aira da har tafara hawaye ta gyad'a mashi kai ta ce " bazan sakeba Daddy amma Dan Allah bazakamun komai ba idan na bari a bud’en "Murmushi yayi Dan sosai yarintar Aira ke burgeshi komai yarinyar tayi burgeshi yake cike da kulawa ya ce "Ba abunda zan maki Amma kidainamun rashin kunya Kinsan dai ba kyau yiwa na gaba dakai rashin kunya ina son ki saki jikinki da ni da mutanen gidan nan d'in gidankine banason d'ari d'arin da kike banajin dadi ko ana k'untatawa maki idan bana nan idan ana maki wani abun fadamun" Ajiyar zuciya Aira ta sauke ta ce Bazan sake maka Rashin kunya ba daga yau Daddy ba abunda akemun "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " ba abunda kike buk'ata"Hawaye na bin k'umcinta Aira ta ce "Bakomai Daddy amma Dan Allah Dan girman Allah Dan darajar fiyayyan Halitta ka sakeni na koma gidanmu Dan soyayyarka da manzon Allah " kallon baki da wayau Yayi mata ya ce "idan kina wannan mafarkinma ki daina ban aureki Dan na sakeki ba Karki k'ara rokata akan wannan idan kina buk'atar wani Abu ki dinga sanar dani yana gama fad'ar haka yabar d’akin durk'ushewa Aira tayi a wajen tare da fashewa da kuka mai cin rai....Inna koda ta dawo daga Umrah ta samu wannan Bak'in Labarin sosai ta shiga surfa ruwan masifa da bala'i Kuka ko ta shashi ba iyaka tsare Abba tayi da masifa akan saiya kaita ta taho da Aira shidai Abba banda lallashi ba abunda yake sosai Inna ta tubure ta rude jin y'an lelen nata Duka biyun na cikin wani hali Kuka ta dinga rafsawa tare da had'a kayanta ta ce " Garin zata bari Bazata cigaba da chusar bak'inciki ba Duk yanda Abba yaso ya shawo kan Inna kasawa yayi da kyal dai saida ya had'a da dangin Abbansu ana ta bata hakuri tukwana ta hakura ta zauna Amma kullum saitayi mita da kukan kewar Arman da Aira shidai Abba Saidai yayi ta Lallashinta Dan ba yanda ya iya....Mummy saida tayi sati Ukku a gida batare da Abba yaje ba Sosai hakan ya b'atawa Yayanta rai Itako kullum da tunanin zullumin halin da y'arta take ciki take Dan ko ta Abba batayi...Abba dai ganin Abun na Mamy ba mai ci ba mai cinyewa bane A daddafe yayi kwanakinnan ba tare da ita ba Ganin zaiyi sakakka ya sanyashi shiryawa cikin sati na hud'u yaje bikon Mamy Sosai Yayanta ya nuna mashi rashinjin dad'inshi da kyal dai Abba ya bashi hakuri ya sauko kiran Mamy akayi Dan ayi musu sasinci tana zuwa ta ce "Yaya nidai ba wani sasinci kawai yabani takardata daman ai yace zai biyoni da ita " Kallon baki da hankali Abba ya mata yo ko giyar wake yasha ya saketa ina zai samu kamarta ga kyau ga tsafta ga gayu ga yanda take da d'an jikinnan ba a tab'a cewa ma ta haifi kamar Aira sai ace Amer ma shine d'anta na fari Dan saika rantse bata jima da Auren fari ba Ai ya saketa tuni wani zai aureta Kwantar da kai yayi ya ce "Babu saki A Aurenmu Rahama mutu ka raba insha Allahu idanma nayi miki laifin kiyi hakuri ki shirya ki koma d'akinki" Jin haka ya sanya Mamy yin sanyi Da Abba da Yayanta suka sasinta abun Yayanta yacewa Abba "ta fad'amun ta ce batajin dad'in zaginta da kake gaban kowa Dan Allah ku daina ba girmanku bane Alh kusan kun girma wannan ai Saidai yara ku masu yiwa wasu fadane" nan Abba ya shaida mashi Bazai sakeba umarta Mamy Yayanta yayi da taje ta shiya tabi mijinta su tafi Bayan yayi mata fad'a akan karta k'ara magana akan duk hukuncin da zai yankewa y'ay'anshi ba ruwanta yaranshine shike da hakki a kansu "insha Allahu bazan sake ba yaya "Mamy ta fad'a cikin ladabi a ranar Abba ya mayar da Mamy a mota ma sai cika take tana batsewa shidai ABba in Banda Lallashinta ba abunda yake..
Yau Aira na kwance a d'aki tana karatun alk'urani Dan yawaicin kwanakin nan kullum shi take karantawa kuma sosai takejin damuwa da kadaicinta sun ragu Laila ce ta shigo ta shaida mata Mama ta ce taje Mikewa tayi tare da ninke Quran din ta bi Bayan Laila tana zuwa Bayan ta gaishe da Mama ta amsa mata ba yabo ba fallasasa sannan ta ce " Daman aikine zaku shiga kitchen Kuyi tare ke da laila na musamman Sadiq ne zaidawo yana hanya yanzu haka daga Paris kuyi mashi komai na musamman plx"To Mama Aira tafada tare da tashi a tare da Laila suka shiga kitchen suka fara girke_Girke kala_Kala sai wajen la'asr suka samu suka gama Wanda Aira duk ta gaji tana gamawa ta fad'a d'akinta Tare dayin wanka Ta shirya cikin lace d'inta riga da sicket da yasha d'inkin zamani....
Arman jikin nashi ba acewa komai sai Alhmdllh Dan kullum cikin samun sauk'i yake dukda har yanzu bai farfadoba tsawon wata guda kenan Saidai komai a mashi danma ya gamu da kwararrun likitoci Mummy ta kasance a wajenshi yayinda Daddy yake komawa 9ja Duk weekend yake zuwa yaga jikin nashi Bayan a nan ma ya rabawa malamai mak'udan kudi akan su tayasu addua Allah yabawa d'an nashi Lafiya Yau Akesa ran farkawar Arman Wanda Mummy tun safe take zumudi ta kasa matsawa daga Inda yake Wajejen 6Pm Arman ya farka Wanda jinshi yake tamkar wani sabon mutum Mummy ganin yayi motsi ya sanyata matsawa kusa dashi cikin farinciki marar musaltuwa ta kama hannunshi ta ce "My son ka farka ka tashi ka kalleni mummynka ce " A hankali Arman ya fara bud'e idanuwanshi da sukayi mashi nauyi yana bud'ewa ya maza ya maidasu ya rufe "Alhamdulilla Allah na gode Maka Mummy ta fad'a tana daga hannu sama nan likitoci suka shigo suma sosai sukayi hamdalar farkawar ta Arman Dan Gaskiya su kansu sunsha tsananin fama akan wannan ciwon nashi Dan su kansu basuyi tunanin zai tashi ba Dan wad'anda zuciyarsu har takai stage d'innan ba lafiya tashi ba congratulations sukayiwa Mummy Akan farkawan yaron nata Dan su kansu sun yaba da irin k'auna da soyayyar da Mummy ke yiwa Arman Cikin farinciki Mummy ta kira Daddy tayi mishi wannan Babban Albishir Ai Daddy farincikin da ya shiga bai musaltuwa a lokaci ya mike tare da cewa a shiryamai tafiya Egypt Arman ko jinshi yake kamar bashiba Abubuwan da suka farune suka dinga dawomai ji yake tamkar a mafarki Mummy ce ta ce " son ka bud'e idonka ka kalleni mummynka ce"jin haka ya sanya Arman bud'e idanuwanshi ya kalli Mummy Rungumeshi Mummy tayi cikin farinciki ta ce "Alhmdllh Allah abun Godiya Allah ya k'ara maka lafiya my son " Gyad'a mata kai kawai Arman yayi Dan bayajin zai iya wata doguwar magana Tea me kauri Mummy ta had'a mashi da taimakon Dr da sukazo tare da shi suka tayar da Arman a hankali Mummy ta shiga bashi tea din Arman na kurba kamar wani k'aramun yaro yasha sosai Inda hakan yayiwa Mummy Dad'i Kallonshi tayi ta ce "ba abunda kake buk'ata son" Gyada mata kai kawai yayi tare da komawa a hankali ya kwanta "Ba wacce ta fad'o masa a rai idan ba Aira ba ?Ta na Ina?wani hali take ciki?Shin tsawon wani lokaci ya d'auka kwance?Kallon Mummy yayi da murmushi yaki barin fuskarta Nuni ya mata da ta matso yanason magana da ita cikin Sauri Mummy ta matsa tare da Kara kunnanta a bakinshi ta ce " me kake so kace son"Kamar mai koyon magana Arman A hankali ya ce "Mu m my I na A ira?Sosai gaban Mummy ya fad'i idonta tane suka cicciko da hawaye Mikewa tayi tare da girgiza masa kai tana hawaye ta ce " Karkamun haka ARMAN ni mahaifiyarkace nafi kowa so da Kaunarka karka k'ara komawa cikin wani hali a saboda ita Arman ina sonka sosai ina buk'atar rayuwarka fiye da komai dake cikin duniyar nan nasha wahala a Rashin lafiyar nan taka tsawon wata guda kenan Arman Karkamun haka karka k'ara komawa cikin wani halin a saboda ita plz son "Arman sai yaji tausayin mahaifiyartashi ya Kamashi kama hannunta yayi tare da girgiza mata kai alamar tabar kuka sannan ya lumshe ido ya bud'e tare da sakar mata murmushi Alamun bazai Kara shiga wani halinba " Ajiyar zuciya Mummy ta sauke tare da zaunawa ta ce "Nagode my son Allah yayi maka albarka ya jikin naka yanzu bakajin komai" ameen ya fad'a a hankali Dan magana yanzu wahalar masa take Sannan ya jinjina mata kai Alamun ba abunda ke idanunshi......
da misalin takwas na dare zazzaune suke a Babban pourm gidan Har Aira Dan itama tanaso taga wannan sadiq din da ake ta rid'in zuwanshi taga har daddyma sai Farinciki yake tana cikin wannan tunanin tajiyowa sallamarshi "badai ta d'ago idontaba har Taji shigowarshi sai Sannu da zuwa ake mai ana oyoyoy yana amsawa cikin barkwanci sosai Aira gabanta ya fad'i jin muryar kamar ta tab'a sanin me ita D'aga idanunta tayi Dan tabbatarwa da abunda kunnanta ya jiye mata tana d'agawa idonta karaf ya had'e Dana sadiq dake kallonta Shima a tare suka wara idanu musamman Sadiq cike da mamaki ya ce " Aira.......✍🏿
*Ni da yaya Arman it's not free it's for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*
*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/29, 15:40] Hajo hajo: 🅿️.........*71&72*
.......Ya ce “Aira ”kallon mamaki Aira ta dinga binshi dashi ba tare da ta ce uffan ba sai k'asa da kanta da tayi"Sadiq ne ya kalli Mama ya ce "Mama a ina kika San Hajara"
Kunsan juna ne daman? Mama ta bashi amsa"Sani ma kai Mama ita ce wacce na dinga baki labari lokacin zuwana kano budurwar da nayi ina sonta sosai Mama dalilin wannan tafiyar nema da nayi Yasanya ban kuma waiwayartaba amma daman niyata ina dawowa zan tashi daga Inda na tsaya Kinga Allah ya kawomun ita har gida garin yaya mama a ina kuka Santa"Tirk'ashi Mama ta fad'a tare da Kallon Daddy da ya had'e gidan sama data k'asa Sadiq ta Kalla ta ce "To ka kiyaye kanka ita ce Amaryar babanka "what Sadiq ya fad'a yana Mikewa ya ce " me kikeson kicemun Mama kina nufin daman Aira ce Daddy Ya auro"Ga Kat kuwa ka gani Dan haka saika nemi wata ubanka dai ya kasaka"Kallon Aira sadiq yayi duk mamaki ya gama kulle mashi kai ya ce "Garinya Aira kika auri tsoho