NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   24 / 54

69K to 72K   out of 160.7K words

sakarai kawai "Mik'a mishi Amer d'in tayi tare da Kayanshi na d'ayar akwatin ta ce " ga shinan Ai daman bance zan tafar maka da yara ba Shima Dan naga mama yakesha Gashinan Inma kashesu zakayi saika gamu ka kashesu daman ai ka kashe rayuwar d'ayar suma saura su "Mama da Aysha Da suka fito Aysha tayi saurin rik'e hannun Mamy tana hawaye Dan sai yanzu take kukan tafiya da Aira bata iskesuba tana zuwa akace suntafi sosai ta sha kuka kallon Mamy tayi ta ce " Dan Allah Mamy karki tafi kiyi hakuri Dan Allah nasan kina cikin fushi ne kiyi hakuri ki dawo "Mama ko Abba ta Kalla ta ce " Bazaka hanata tafiya ba Alhaji"Tsaki Abba yaja ya ce "ta tafi d'in mana aiba wani abu akayi mata ba bare na bata hakuri sannan ya mik'awa Mama Amer ya ce " Amsarshi ku koma ciki "Haba Alhaji wannan fa ba daidai bane Ku dinga kai zuciyarku nesa sannan ta kalli Mamy ta ce " Ke yanzu Rahama yaron shekara guda zaki tafi ki bari "Ai bani nace bazan tafi dashi ba shiyace na Aje mishi d'a Dan haka bazan tsaya jayayya ba Allah ya raya" Tana gama fad'ar haka Mamy taja akwatinta ta saka a motarta ta zagaya tashiga tayiwa maigadi horn ya fito ya bud'e mata taja ta fice Amer dake Kuka Hannun Mama Aysha ta Goge hawayenta ta amsa Mama ce ta ce "Haba Alh wai meyasa baku sassauta Abu ka maida mata d'anta akwai zalinci fa me yaro karami yayi" cike da b'acin rai Abba ya ce "Ina ruwanki ko bazaki rik'emunshi ba na nemi Inda zan kaishi" Jan bakinta Mama tayi ta ce "Allah ya baka hakuri" Sannan ta juya Kallon Aysha yayi ya ce "zanba Driver yanzu ya kawo muku irin abincin da yakeci ki lallabashi yayi bacci Sannan Anjima ki tafi gidanki bansan wannan zaryar da kike tunda an k'are biki ya isa kuma" To Abba "Aysha ta fad'a tukwana itama ta koma ciki tana jijjiga Amer dake Kuka harta samu yayi bacci sosai Abba yayo sayayyar irin abubuwan da Amer ke sha na yara damanshi bai fiya rigima ba Sosai inba yunwa ba Dan Ya saba da y'an gidan sosai Musamman Haidar dake yawan daukarshi Haidar Bayan dawowarshi daga school ya samu labarin Tafiyar Aira da kuma tafiyar Mamy Sosai ya sha kuka Shima harya hakura ya daina tukwana ya d'auki Amer ya dinga mashi wasa Mamy ko koda ta isa gidan Yayanta kallonta yayi ya ce " ya na ganki da akwati Rahama "Cikin kuka ta ce " Yaya gida na dawo na gaji ya ce ma zai aikomun takardata gida"Dak'uwa yayi mata ya ce " Bansan shiririta Rahama wuce ki koma gidanki"Kuka Mamy ta fashe dashi ta durkushe ta ce "Dan Allah yaya kayi hakuri amma Bazan komaba Saidai na tafi Agadez indai kace saina koma " Matar Yayanta Hindatu ta ruk'ota ta ce "To bar kukan wuce muje ciki " Hindatu bansan irin wannan ki barta ta koma gidanta dukda ban bincika ba nasan ita ce bata da Gaskiya "Haba Alh aikama ka bari ka bincika ko sannan ai bata tab'a zuwa ko yaji ba Tunda kaga haka kila da abunda aka mata " hindatu kenan saikace baki zauna da Rahama ba bakisan halinta ba kinsan halinta fa sarai inta rikice to muje Naji abunda ke faruwa?Bayan sun zauna ya Kalleta ya ce “fad'amun abunda ke faruwa"Cikin kuka ta ce "Yaya maganar Aira ce sanin kanka ne har kashe kanta tayi kokarin yi amma Abbansu bai saduda ba yanzu haka sun tafi da ita sokoto yaya gidan kishiyane fa za a kaita da y'ay'an miji ina Aira ina zama da kishiya yarinyar da bata da wayau ko fad'a bata iya ba" tsaki yaja tare da tashi ya ce "nama zaci ko keda shi ne daman baki hakura da maganar nan ba duk abunda nafada maki baki yarda dashi ba to wuce ki koma gidanki badani ba daurewa karya gindi dama ace wani laifin yayi miki shine da saina d'aukar maki mataki" Kuka Mamy ta fashe dashi ta ce "Yaya ai ban k'arasa fad'a maka ba " a tsaye ya ce inajinki yi Sauri bansan jin shiririta cikin kuka ta ce "Yaya Kuma kullum daya tashi bai kunyar zagi na Gaban kowa har gaban yara na ya dinga Cemun mahaukaciya mai k'aramar kwalwa "To Ai ita d'ince Rahama na rasa me yasa har yanzu bakya girma Abunda zakiyi wani d'an shekara goma ma bazaiyi ba yanzu kin tashi kin taho Ina Amer d'in yake dallah ki wuce ki koma gidanki zanyi magana dashi bazai sake zaginkiba shikenan ko" kuka ta fashe dashi ta ce "Yaya Dan Allah ka bari ko zan koma ba yanzu ba Amer shi ya amsheshi ya ce Bazan tafar mashi da yaro ba " Hindatu ce da ke Dariya ta mik'e tare da kama hannun Mamy tayi ciki da ita dawowa tayi wajen mijin nata ta ce "Kaida kasan Rahama y'ar rigima ce idan tak'i duk bakai ba ka ja da ka shagwaba ta ba Alhaji itafa har yanzu jinta take kamar wata y'ar shekara sha takwas Bata girma Rahama Harta Aurar da Y'a Amma batabar shiririta ba yanzu kawai tunda ta kafe ka barta ta d'an huce zata Huce ai fushi ne "Girgiza kai Yayi tare da murmushin manya ya ce " Allah ya shiryeta Ki dinga mata nasiha da nuna mata rayuwa Dan Allah"Insha Allahu Alhaji zan nuna mata ai dole duk kai ka ja mana wannan aikin da ka dinga shagwabata da yawa ai yanzu Rahama da me fad'awa wanice"murmushi yaya yayi ya ce "Hindatu kenan gata da soyayya ne na nunawa Rahama bawai shagwabata nayi ba kin manta amana ce ita da iyayenmu suka barmana Kingakwa dole na nuna mata soyayya da gata " asalinsu! Mamy su shidda kenan wajen iyayensu Babban yayansu Safiyanu,Ramlat,Asma'u,Aisha,Fadila ,sai autar su Rahama mahaifinsu Alhaji Ibrahim sanannen mai kud'ine a garin Agadez mahaifiyarsu Hajiya Saratu haifaffiyar garin katsina ce Aure ne takaita Niger amma y'an uwanta duk suna Chan suntasone cikin Had'in kai da k'aunar juna Babban yayansu tunda yazo karatu kano yaga wuri Inda ya fara kasuwancinshi a nan kano har yayi Aure ya auri matarshi Hindatu y'ar nan kano ce itama yayyun mamy ma mata duk sunyi aure a nan niger kasancewar sun bata shekaru sosai iyayenta da yayunta suna ji da rahama sosai kasancewar ita ce autarsu musamman iyayensu da suka shagwabata komai ance Auta kwatsam wata rana iyayensu zasuyi tafiya zuwa k'asa mai tsarki Dan yin Umrah A lokacin Rahama na da shekara Bakwai a duniya da tare dazu tafi da ita amma tasa kuka ta ce ita bazata k'ara zuwa ba saboda tsoron jirgi take sun taba tafiya da ita ta tsorata sosai hakan yasa ko jirgi taji an ambata a lokacin sai tasa kuka ana gobe zasu tafi yaya Safiyanu yazo daga kano Dan suyi bankwana Hannunshi iyayenshi suka damk'a da na Rahama suka ce "ga Amanar Rahama nan a hannunka amana amana amana ka rik'e mana Ita amana karka yarda tayi kukan rashinmu ko Bayan ranmu ka zame mata uba kaji ka dauki nauyinta sannan kuma ka jajirce a kanta ka bata ilimin zamani da na arabi " Sosai Safiyanu yayi sanyi ya ce "kidaina fad'ar haka Mama sainaga kamar wani abun ne ko bazaku dawoba insha Allahu na amshi Amanar Rahama har abada" sosai suka dinga yi musu nasiha a lokacin Rahama bata da wayau bata ma sanin abunda Suke cewa ba Sosai a ranar da zasu tafi har aiport suka yi musu rakiya duk sunyi sanyi har suka tafi suna juyowa sunayiwa yaransu bye bye harzasu shiga jirgi Rahama ta Ruga tare da rungumesu sai kuma tasa kuka hakan yasa hankalin y'an uwanta tashi duk tafiyar da iyayensu suke basu tab'a jin ba dadi ba irin wannan tafiyar shafa kanta iyayenta sukayi sukace "Allah yayi miki albarka Rahama kibar kuka kinji ko bakison idan muka dawo mu taho maki da d'iyar roba mai tafiya tana wak'a " Cike da murna Rahama ta ce "Ina so Mama Allah maidoku lafiya" a wannan tafiyar ne aka samu hatsarin jirgi da akayi asaran rayuka Wanda ciki hada iyayensu Rahama cikinsu babu Wanda ya fita Sosai y'ay'ansu suka sha kuka daga karshe suka yi hakuri sukacigaba da yiwa iyayensu addua tundaga lokacin Rahama ta koma kano wajen yayanta da zama Inda shida matarshi suka rik’eta amana sosai Yayanta ke bata kulawa tare da bata dukkan abunda take so bai tab'a yarda daidai da rana d'ayaba Rahama tayi Rashin iyaye Komai takeso mata yake musamman idan ya tuna da wasiyar da iyayenshi suka bar mishi a kanta Ya sanyata makaranta mai tsada tun daga Primary har secondary Wanda da kyal ta k'arasa secondary saboda samari da suke yi mata chaaa saboda masha Allah Rahama akwai fari ga kyau Alh Safiyanu yana da yara hud'u Duka maza ne ana hakane har Daddy Ya shigo rayuwarsu soyayyarsu da Daddy da kuma yanda akai ta koma wajen Abba Wanda son farincikin Rahama ne ya sanya Yayanta yarda akan Amincewa da Abba a lokacin tana da shekara sha takwas akayi mata a yanzu Kuma tana da shekara talatin da bakwai *Wannan kenan*
K'arfe Shida da wani Abu tayi musu a sokoto a jirgima Aira har suka iso Kuka take motocine na alfarma su kusan goma suka zo taryar su Aira a ta tsakiya aka sanyata Mama Halima na rik'e da ita tare da Yayar Alh Yusuf a haka har suka isa katafaran gidan Alh yusuf dake Arkilla quarters har lokacin fuskar Aira na lullub'e cikin laffaya gabanta banda fad'uwa babu abunda yake jin abun take tamkar mafarki A haka aka kamo hannunta suka fito ita dai Aira bata ga gidanba saboda fuskarta lullub'e ta ke ta na dai jin dai bud’ar mutane da zasu shiga cikin gidan Mama Halima ta ce "Kiyi bismillah ki shiga da k'afar dama Au'zubillahi minashshaid'ar Rajim Aira ta fad'a tare da shiga da k'afar hagu.......✍🏿


before the writer starts typing she knows what will happen at the beginning of the story in the middle and at the end I can't change my writing style as I originally planned so I'll go with it it was their love style that came with it😢😻

*Ni da yaya Arman it's not free it's for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*


_*Miss Hajo ce_*
[6/27, 09:57] Hajo hajo: 🅿️.........*65&66*







......Tare da shiga da k'afar hagu girgiza kai Mama Halima tayi batare da tace mata uffan ba harsuka shiga cikin gidan itadai Aira idonta lullub'e yake sai yanda akayi da ita tana ta jin bud'ar mata har aka shiga da ita tana jin an zaunar ita ta tabbatar da an kawota d'akinta kenan sosai ta fashe da wani irin kuka mai cin rai wai yau itace aka kawo d'akin miji amma mijin ba yaya Arman ba wannan wace irin yankan k'auna ce sosai ta fashe da kuka yayyun Alh Yusuf da suka d'aukota saisuka d'auka kukan rabuwa da gida ne Lallashinta suka shigayi sukace "ki kwantar da hankalinki insha Allahu mudin zamu zame maki tamkar iyaye" Mama Halima ce ta rada mata a kunne ta ce "Karna sake Naji ko kin nuna bakisan Auren nan ko kiyiwa mutane rashin kunya ki saki jikinki kinji kibar kukan nan" gyad'a mata kai Aira tayi Alamun to ta daina kenan sosai dangin alh yusuf suka tarbesu da tarba ta musamman abinciccika kala kala wata yayar Alh Yusuf tazo ta ce ya kamata Aje a kaita wajen uwar gidan A had'a su "Sosai gaban Aira ya fad'i " to Mama Halima ta ce "Sannan suka kama hannun Aira suka tafi da ita bangaren uwar gida Suna isa suka isketa ita da Y'ay'anta da y'an uwanta sai cika suke suna batsewa Hakanan suka zauna gaishe da Matar sukayi wacce zatakai sa annin Mama Ta amsa ciki ciki Mama Ramlat ce ta ce " Amarya muka kawo miki y'ar uwa Amana dan Allah ku hada kanku sannan ita munyi mata nasiha insha Allahu Zata girmamaki "Tab'e baki Hajiya saudatu tayi ta ce " Wanda ya kawota zaku ba Amanarta ba niba sannan zaman lafiya za ayishi indai ta zo dashi"Sosai gaban Aira ya tsananta fad'uwa jin kalaman Matar a zuciyarta ta ce "Na shiga ukku an kawoni wajen wata matsalar nidai ina ganin rayuwa" Su Mama Halima sosai ransu ya b'aci tashi sukayi tare da Aira batare da sunce uffan ba yayar Alh Yusuf Hadiza ta ce "kedai saude baki da mutunci wlh iyayen yarinyar nan fa y'an mutunci ne ba da tashin hankali sukazo ba Amma abunda kika fadamusu kin kyauta kenan" Tsaki saude taja tare da tashi tabar palourn Ana komawa da Aira a lokacin ana kiran Sallar magriba sai sannan ta daga idonta ta kalli d'akin dakine babba na gani na fad'a ga kuma tantsara tantsaran kayan da aka zuba mata karewa d'akin kallo tayi Sosai Tasan Abba ya kashe mata kudi a kayan dakinma kansu dukda bataga sauranba Sallah ta tashi tayi suma su Mama Halima sukayi salla Bayan sun. Gama sosai suka shiga yiwa Aira nasiha gami da wa azi akan ta zauna da kowa lafiya kuma tayiwa mijinta Biyayya Allah ba ruwanshi da bakisan auren nan zai kamaki da laifi Aira na jinsu yanda suke fad'a mata maganar na shiga kunnenta haka take fita ta d'ayan kunnen Sannan suka Mike sukace Zasu koma Dan dama ba kwana zasuyiba fly din dare zasubi sosai Aira ta fashe da kuka ta rirrikesu ta ce "Dan Allah Mama Karku tafi ku barni na shiga ukku kuma yanzu Tafiya zakuyi...sosai take kuka su kansu su Mama Halima saida ta sanyasu kuka Dak'yal kannen Alh Yusuf suka bambare Aira dake jikin Mama Halima tana kuka harsuka tafi Aira ihu take tana kukan karsu tafi su barta dak'yal y'an uwan mijinta suka dinga Lallashinta harsuka samu tayi shiru nan mutane da y'an uwa suka shiga shigowa ganin Amarya Aira in banda hawaye ba abunda take wajen karfe goma Wata kanwar Alh ta sanya Aira tayi wanka ta shirya cikin tantsanemen lace d'inta da tasha d'inki ta sanya mata Turare sosai dukda hawayen da Aira take sosai tayi kyau Saida ta gama shiryata tukwana ta mik'e ta ce " to nima na tafi yanzu ba jimawa angonki zai shigo Allah ya bada zaman lafiya "Aira bata iya ce mata komai ba saboda k'ududun bakin cikin da take ciki tana ganin fitarta ta maza taje ta sanyawa k'ofar key tare da barin key din a jiki Da gudu ta fad'a Gado tare da fashewa da kuka mai cin rai tunanin Arman yaki barin kwalwarta Alh Yusuf da murnarshi ya taho bangaren Amaryarsa sai fara a yake tare da ledarshi katuwa yana zuwa ya yi knoking yaji rufe sosai ya shiga Bugawa Aira na jinshi tayi banza ta kyale sai kuka take key ya d'auko ya gwada bud'ewa amma ya kasa hakan ya nuna mai tabar key din jiki kenan sosai ya damu cikin k'asa da murya ya ce " Haba Amaryata ki bud'e mana nasan kina jina please ki budemun kofa kinji"Aira na jinshi tsaki taja tare Kara fashewa da kukan takaici cike da damuwa.Alh Yusuf ya ce "Da Allah na had'aki baby ki bud'emun k'ofar please" cike da jaraba da masifa Aira ta ce "Bazan bud'e d'inba karka dameni Malam Karka takurawa rayuwata tun da sauran mutuncinka a idona bazan bud'e ba Saidai ka kwana a tsaye " tana gama fad'ar haka ta fad'a Gado tare da cigaba da hawaye"Alh Yusuf bai hakuraba haka yayi ta tsayuwa a wajen yana bubbuga mata ko Allah zaisa ta bud'e Hajiya saude ce ta fito cike da masifa ta ce "Da Allah Alhaji ka damemu meye hakan da kake ko kunya babu tunda tak'i bud'e maka ai sai ka hakura Amma wannan Abun da kake zubda girma ne y'ay'anka na jinka wannan wace irin jaraba ce " ta fad'a ta na Jan tsaki "Kallonta yayi ya ce " kinsan dai bansan katsalandan ko saude"to Naji yanzu dai kayi hakuri kaje ka kwanta "Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya nufi part d'inshi tsaki saude taja tare da komawa Bedroom d'inta !*Asalinsu*??Alh Yusuf Sanannen d'an kasuwa ne a nan Jahar sokoto da ma ketaran ta Matarshi d'aya Saudatu yar asalin Garin sokoto ce yaransu hud'u Babbar d'iyarsu Zuhura tana nan tana aure anan sokoto yaranta hud'u sai mai biya mata Abubakar Sadiq shi har yanzu baiyi Aure ba,sai Mubarak shi kuma yana matakin Deegree ne anan Sokoto yake karatu sai Autarsu Laila me shekaru Ashirin da d'aya a duniya tana matakin Deegree level 2 Hajiya saude sosai take juya Alhaji sai yanda tayi dashi tunda suke da ita bai tab'a yunkurin ma Kara Aure ba Dan sosai yake shakkarta irin matan nan ne jibga jibga masu jiki da k'iba itama bak'a ce koda Alh zaiyi Auren nan sosai aka sha dagu da ita Dan y'ar bala'i ce suko danginshi daman so suke ya k'ara Aure hakan yasa suka k'arfafa abun tayi shige da ficen ta wajen malamai da Bokaye amma ba nasara Y'ay'antama sosai suke takaici da bakincikin auren da Daddynsu zaiyi musamman Zuhura da laila dan Sadeq baya k'asar shiko Mubarak ba ruwanshi Dan irin y'an duniyar nan ne shiko Alh Yusuf da yake Allah ya d'ora mishi k'auna da soyayyar Aira hakan yasa ko girgiza baiba sai ya jima tsoron Matar tashi da yake ya ragu wannan kenan.....Daren ranar Aira kwana tayi batayi bacci ba kwanan bak'inciki tayi Bayan tayi Sallar asuba wani masifaffan zazzabi ya rufeta da ciwonkai cikin bargo ta shige sai rawar sanyi take hawaye na bin k'umcinta a haka har wani wahalallen bacci ya kwasheta....k'arfe Tara tayiwa Su Mama Halima a Kano Kai tsaye gidan Abba suka sauka suna isa nan ne suka samu labarin Tafiyar Mamy Dafe kai Mama Halima tayi ta ce "ohh muna ganin rayuwa wlh harna gaji da kashe kashen case nidai gobe zan tafiyata Nida garin nan kuma sai an ganni " Aunty Ramlat ko sosai taji haushin Mamy Abba

24 / 54