Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
Gaskiya Abokina na fara gajiya haka fa zamuyi ta gararanba a gari batare da mungano gidan ba"Kayi hakuri nasan ina sanyaka wahala insha Allahu jikina na bani yau za a dace "to waikai bazaka iya tuno sunan ba?wlh bansan sunansa ba amma me zai hana mu zagaya unguwowin masu kud'in garin nan tunda Shima yana da kud'i" na am da wannan shawarar musa yayi nan suka zagayawa unguwowin masu duk Inda sukaje su tambaya Dan Allah Ko sunsan gidan Alhaji Madugu sai ace musu basu saniba a haka har Allah ya kaisu Arkilla quarters Inda suka hangi wani wajen chaji Musa duk ya gaji a tare suka fito Dan tambayar mai chajin ko Allah yasa a dace Dan haka suke duk Inda suka samu tambaya suke Suna isa mik'a mishi hannu sukayi musabaha musa ya ce "Dan Allah Abokina tambaya muke ko Allah zaisa a dace" To inajinku Allah yasa na sani"mai chajin ya fad'a yana fuskantarsu"Dan Allah gidan wani Alhaji Madugu muke nema ko ka sanshi" Ciza yatsa Mai chajin yayi ya ce Madugu,Madugu,Madugu To mudai Madugu anan Unguwar Biyu ne akwai Alhaji Yusuf da kuma Alhaji bukar" Cikin Sauri Arman ya ce "Eh shine Alhaji Yusuf sai sannan ya tuno da sunanshi da aka fad'a a lokacin da Aka fad'a a gidan television " Kallonshi mai chajin yayi ya ce "Wanda ya auri wace Yarinya k'arama kwanaki Y'ar kano shi kake nufi kuwa"Eh shine Dan Allah gidan mukeso ka nuna mana" ya fad'a cike da zak'uwa "Kallonshi musa yayi ya ce " Daman kasan sunan ka bari muke ta shan wahala"mancewa nayi sai yanzu da aka fad'a na tuna da sunan"Kallon mai chajin musa yayi ya ce "Dan Allah Abokina zo zaka gwada mana gidan" Badamuwa me chajin ya fad'a tare da rufe wajen chajin ya ce "da y'ar tazara Saidai muje Tare na muku rakiya" Cike da farinciki suka yi mashi Godiya suka shiga mota Shima ya shiga A baya ya dinga nuna musu hanyar gidan Har yakaisu daidai kofar gidan tukwana ya ce "nan yayi ga gidan nan ya fad'a yana nuna musu kofar gate d'in " a tare suka kalli kofar Wani farinciki na shiga zuciyar Arman wai yau shine a kofar gidan da Cutie d'inshi take hamdala yayi a zuciyarshi ya godewa Allah Kallon musa yayi ya ce "Ka gane gidan daiko" Eh ai nama San unguwar muke ta shan wahala ya fad'a su suka maida mai chajin Inda suka daukoshi sosai sukayi mashi Godiya Inda Arman ya rubuta mishi check d'in Dubu d'ari biyar ai mai chajin nan godiyar da ya shiga kwararawa Arman bata lissafuwa harda kukan farinciki yayi wai yau shine akayiwa kyautar har Rabin million.kudin da ko kwatarsu bai tab'a kamawaba sosai ya shiga kwararawa Arman addua shi arman har gajiyawa ma yayi da amsawa a hanya musa ya Kalleshi ya ce "to mungama me wahalar yanzu meye shirin ka na gaba"shirina na gaba daga gobe zai fara kaidai abunda nakeso dakai inason ka nema mun irin abun nan na nad'in buzaye tare da kayan buzaye wad'anda suka d'an sha wahala " Dariya musa yayi ya ce "kace buzu kuma zaka koma" tsaki Arman yaja ya ce "matsalata dakai Maida serious magana wasa" washegari wajen 4 PM musa ya kawowa Arman abunda ya buk'ata Suka d'auki Hanya Suka nufi Arkilla quarters nesa da gidan sosai Arman ya ce "ya tsaya nan ya isa" Sannan ya amshi kayan ya ce Ka fita zan sanya a cikin mota"musa na mak'e dariyarshi ya fita kasancewar motar mai tinted ce hakan yasa cikin Sauri Arman ya cire kayan jikinshi ya mayar da kayan buzaye nan Duk da a k'yamace ya sanyasu amma idan ya tuna da A saboda masoyiyarshine saiyaji ma ya daina kamar kayan yana gama sanyawa tare da nad'in Buzaye bud'e motar yayi ya fito ai musa tunda ya Kalleshi yake kakkabewa da dariya hada rik'e ciki ,tsaki Arman ya ce "da yake mahaukacine ni da zaka dinga mun Dariya" Cikin Dariya musa ya ce "Sorry Abokina wlh shigarkace taban Dariya Sak ka fito wani buzu" tsaki ARMAN yaja ya ce "Bansan wulakanci lokaci na kurewa muje kawai ka rakani saida ya rakashi Har kofar get d'in sannan kuma ya juya da niyyar zasuyi waya duk yanda sukayi" Arman ya jima tsaye yana karewa unguwar kallo kafin ya fara knocking d'in get d'in gidan mai gadi ne ya fito tare da bud'ewa Karewa ARMAN kallo yayi ya ce "Malam lafiya" lafiya qalau Mai gidan yana ciki"Arman ya bashi amsa cikin muryar buzaye daya kirkira "eh yana ciki wa yake nemanshi"? ni nake nemanshi Dan Allah Ko zakamun iso da shi" Tsaf me gadin ya k'ara karewa Arman kallo ya ce "Ikon Allah yau kuma buzu ne a gidan Ya fad'a tare da shiga cikin gidan a lokacin Alhaji na palour yana Danna lapton mai gadi ya shigo ya shaida mashi yana da bako Okay ina zuwa ka shigo dashi Alh yafada tare da mik'ewa mai gadin na komawa yabawa Arman hanya ya ce " ka shigo"a hankali Arman ya shigo gidan daidai lokacin da Alhaji magudu ya fito da Kallon tsana Arman ya bishi dashi yana jin dama da dama da saiya kashe mutumin Chan da ya rabashi da masoyiyarshi Karasowa Alh yayi da mamaki yake kallon Buzun mutumin Tare da cewa "Malam lafiya" Dagowa da idanunshi Arman yayi ya sauke a na Madugu dak'yal ya iya yak'i da zuciyarshi yanda yakejin kamar ya Fard'o mutumin cikin muryar buzanci ya ce "Ina wuni Alhaji ni bak'one a garin nan ina neman Aiki ne ko da gadi ne indai zansamu inci insha shine kawai burina koda bansamu albashi ba" Kallonshi kasa da sama Alh yayi kafin ya ce "to nidai Gaskiya nan ina da ma aikata ina da mai gadi da masu bawa flowers ruwa driver ne kawai nake nema Wanda zai dinga kai iyalaina unguwa kai kuma banjin ka iya tuk'i " Cikin Sauri Arman ya d'ago ya ce "Alhaji ai na iya tuk'i" Kallon rainin wayau Alhaji yayimai ya ce "Kai dinne ka iya tuk'i ina ganinka a haka" wallahi Alhaji na iya tuk'i a aikace aikacen da nayi nayi driver kuma idan kana kokonto zaka iya gwadawa"Shidai Alhaji mamaki yake yaza ayi Ace buzu dayazo daga rugage ya iya tuk'i Dan son tabbatarwa mik'awa Arman key d'in motarshi yayi ya ce "Amshi ga mota ta Chan a parking space fiddomun ita ka kawo ta nan" Amsa ARMAN yayi yana hamdalar ya taka nasarar matakin farko cikin Sauk'i haka ko akayi yanda Alhaji ya fad'a haka ya fito da motar"Cike da farinciki Madugu ya ce "Eh Gaskiya ka iya tuk'i gashi cikin nutsuwa daga yau na d'aukeka Aiki duk wata zan dinga biyanka dubu talatin " Kasa da kanshi ARMAN yayi ya ce "Saidai wani hanzari ba gudu ba Alhaji bani da wajen kwana " karka damu akwai BQ zansa a share maka d'aki nan zaka dinga kwana"to nagode Alhaji Allah Kara budi"Arman ya fad'a zuciyarshi na mashi zafi "Karka damu yaro ai na yaba da hankalinka yanzu bari naje na fito da mutanen gidan na gabatar musu dakai sosai gaban Arman ya fad'i amma ya fisge Alh Yusuf na shiga gida ya shaidama su Hajiya saude ya d'aukar musu driver suje su ganshi Laila hada tsallen murna a lokacin Aira na mata kalaba Mikewa tayi ta ce " Sis taho muje Tare"B'ata fuska Aira tayi ta ce "kuje kawai ni basainajiba" Mama saude ce ta ce "a a a kema fa saikinje ai hakkin kine " Saude Da Alhaji saida suka fita tukwana Laila ta mik'ar da Aira suka fito Hakanan Aira tajita yanayinta ya sauya kallon Arman Hajiya saude ta yi ta ce "Alhaji ai wannan yayi nutsuwa Saidai naga kamar ba buzu ba kamar yafi kama da bafullatani" Gaban Arman ne ya bada daram Alhaji ne ya ce "inbanda abunki saude meye maraban buzu da Fulani sannan ya kalli Arman ya ce " wannan itace uwargina "Juyawa yayi ya kalli su Aira dake Tunkarosu tare da cewa " wad'anchan kuma Y'ata ce tare da Amarya"gabanshine ya bada daram daidai lokacin da ya d'ago idonshi ya sauka akan na Aira da itama shid'in take kallo karaf idanunsa suka sartse Dana juna" Rumtse idonshi Arman tare da budesu ya k'ara saukesu a nata jin abun yake tamkar mafarki sosai yaga ta k'ara mishi kyau Saidai kuma ta rame Aira ja tayi turus ta tsaya Inda take bugawar zuciyarta ya tsananta Ji take kodai mafarkine idan ba idon tane ya gane mata ba daidai ba Arman take gani da shigar buzaye gabanta Nunashi tayi da yatsa tana son magana mamaki ya gama cikata Duk kallonta suka tsayayi da mamaki sukace kin sanshi daman "Rumtse idonshi Arman yayi ya ce " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un shikenan Aira zaki ruguzamun plane da na jima ina shiryawa............โ๐ฟ
*Tofa ya kenan Fans Ga Aira ga Arman Me kuke tunanin zai faru nan gaba karfa Aira ta kwafsamai ta ruguzamai shiri*๐๐พ๐๐พ๐๐พ๐๐พ๐๐พWarrrrrrrrrr๐๐พ
_*Miss Hajo ce*_
[7/5, 17:12] Hajo hajo: ๐
ฟ๏ธ...........*81&82*
...Ruguzamun plane d'in dana jima ina shiryawa "sauke hannunta Aira tayi tare da rumtse idonta ta ce " wai meyake neman damuna karfa na haukace Yaya Arman gizau yake mun mema zai kawo Arman gidan nan meya had'ashi da buzanci kuma "duk cikin zuciyarta take maganar nan" Laila ce ta dafata ta ce "Yadai ko kinsanshi ne" Bud'e idonta Aira ta sakar mata murmushi ta ce "a a a bansanshiba Yadai yimun kama da wani Wanda na tab'a ganine sai yanzu na lura bashi bane" tana gama fad'a ta Juya Dan batason k'ara had'a ido da Buzun mutumin nan zuciyarta neman tarwastewa take "Da kallo suka bita har ta wuce" Arman ko wata nauyayyar Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Alhamdulilla Allah na gode Maka Amma yayi mamakin yanda Aira ta kasa ganeshi gashi da farko dai Ta nuna ta ganeshi ko meyasa kuma ta nuna bata sanshiba " Aira tana komawa d'akinta ta nufa saboda tsananin sara mata da kanta yayi Gado ta haye tare da rumtse idonta ta ce "Ya Allah Arman harya faramun gizau to meyasa da Chan bana kallon mutane a matsayinshi sai wannan buzun da sak yaya Arman d'ina nake gani,tsaki taja ta ce " Lallai na fara haukacewa Ma me zai kawo Arman gidan nan " a haka tayi ta sake sake akan buzun nan a cewarta.
BQ aka sharewa Arman tare da samashi Katifa a ciki da niyyar gobe zai fara aikinshi Koda
Ya kwanta bacci k'auracewa idanunshi yayi Kallon d'akin yayi tare da Inda yake kwana Wanda gaba d'aya gidanma yana da dukiyar da zai rabawa sama da mutum d'ari irinshi ba tare da dukiyarshi ga girgiza ba "Murmushi Yayi tare da sanya hannunshi a baya ya had'esu ya d'ora kanshi ya ce " So kenan" washegari tunda Safe ya tashi Ya kai Laila school ya dawo a lokacin Aira ta lek'o kenan ta window shi kuma yana fitowa murza idanunta Aira tayi ta k'ara budesu tsorata tayi da ganin shi d'inne da gudu ta Ruga ta koma d'akinta tana ta karanto duk addu'ar da tazo bakinta Kardai Gamo ne take tayi.
Arman ko sosai yaso had'uwa da Aira A lokacin amma ya gagara da Yamma yaje ya d'auko Laila daga school Wanda tun a hanya sai iyayi take yimashi shidai shiru yayi yanajin haushin ta da tsananta Dan Duk abinda ya shafi mutumin nan ya tsaneshi musamman yarinyar da yaga sai shishige mai take Laila ko tana dawowa bata iske Aira ba A palour bedroom d'in Aira ta nufa tana zuwa ta isketa tana salla saida ta jira ta gama da zumud'i ta ce "Wai kinsan Me sis?A a saikin fad'a " Lumshe idanunta tayi tare da murmushi ta ce "Wlh sabon driver d'in nan ya had'u ke saima kinji muryarshi zazzak'a da ita har so nake yayi magana saboda karkiga yanda muryarshi ke rikitani" Gaban Aira ne ya fad'i saurin fisgewa tayi ta ce "Uhm Laila kenan to ya school d'in kunyi text d'in kuma" Dan son barin wancen zancen "tab'e baki tayi ta ce 'wlhko munyi Ai lecturer nan baida mutunci Da banjeba fa da na fad'i " Daga nan suka cigaba da hirar makaranta Wanda Aira Duka hankalinta na kan buzun nan Da daddare Bayan isha'i Aira kasa daurewa tayi Dan so take ta tunkari buzun nan Dukda fargabar da take Dan a zatonta Aljanine yake mata suffar Arman d'inta Hakanan tayi shahada ta fito saida ta lek'a ko ina taga bamai ganinta kuma taci sa a palourn ba kowa cikin Sauri ta nufi BQ d'in gidan Dan Laila ta fad'a mata Chan aka saukeshi tana sanda haka harta isa d'akin da tagani bud'e da labule ya tabbatar mata da nan yake a hankali ta tura kofar tare da Yin bismilla tana shiga ta ganshi kwance yana d'an latsa waya Arman jin shigowartata kawai yayi cikin Sauri ya Mike daga kwancen da take Da mamaki yake kallonta Cike da farinciki ya ce "My Cutie" Wara idanu Aira tayi jin ya ambaceta da sunan da Arman d'inta kad'ai yake kiranta dashi cike da tsoro ta ce "Dan Allah kai D'in mutum ne ba aljaniba meyasa kakemun suffar mutumin danafi k'auna a rayuwata " murmushi Arman yayi tare da wara mata hannu Alamun tazo gareshi ya ce "Ba aljabi bane my cutie nid'in ne dai Arman d'inki" Cike da mamaki Aira ta ce "Yaya Arman Me ya kawoka nan kuma" Murmushi yayi mata tare k'ara wara mata hannuwanshi ya ce "So my cutie soyayyarki ta kawoni" Da gudu Aira ta Ruga tare da Fad'awa jikinshi ta fashe da kuka mai cin Rai"wace nutsuwace ta dirarwa Arman Ajiyar zuciya ya sauke "Jin abar K'aunar tashi a jikinshi Dadddabata ya fara kamar yanda yake mata a baya ya ce " is okay my Cutie ba kuka ya kamata kiyi ba farinciki ya kamata kiyi"Lafewa Aira tayi tana shakar daddad'an k'amshin turarenshi da bazata tab'a mantawaba dashi a rayuwarta ba Irin salon yanda yake daddab'a Bayan nata ya k'ara tabbatar mata da shi d'inne lumshe idanunta tayi ta ce "Yaya da gaske Kaine please Idan mafarkine nake ya Allah kada ka tasheni daga wannan mafarkin Ka dawwanar dani a cikinsa har k'arshen rayuwata" Shafa bayanta yake a hankali ya ce "Ba mafarki bane cutie a zahirance d'in nine dai yaya Arman d'inki da Abba ya rabamu Allah ya sake had'amu" Tashi Aira tayi tare da Kallonshi Kamo hannunshi tayi cike da farinciki ta ce "my yaya da gaske Kaine dai na kasa gaskata mafarkinnan"murmushin da ya mance yaushe rabon da yayishi yayi tare da shafa mata fuska ya ce "nid'inne dai Arman yayanki kuma mijinki insha Allahu mai k'aunarki na har abada"Wara idanu Aira tayi cikin fara a ta ce " yaya Ya akai kazo wajen nan me yakawota nan gidan matsayin driver kuma ?murmushin gefen baki yayi ya ce "a saboda soyayya ba abunda bazan tab'ayiba a rayuwa Aira a saboda son da nake maki banajin bazan iya afkama ko wani hatsari ba a saboda ke soyayyarki daga Allah ne ked'in a jinin jikina kike Bazan tab'a iya jurewa rashinkiba a tare dani hakan yasa Bayan Naji sauk'i na yanke shawarar nemoki a duk Inda kike Wannan ce kawai nayi tunanin mafitar da zan samawa kaina ta hanyar aiki a k'ark'ashin mijinki...rumtse idonshi yayi yanajin kamar wani dutse ya tokare mashi zuciyarshi " Tuni hawaye sun gama wankewa Aira fuska Shafa fuskarshi tayi ta ce "Hakโikโa aya kaid'in ka cika masoyi na Gaskiya Wanda babu kamarsa a duk fad'in duniya Allah nagode maka daka had'ani da masoyin da babu kamarsa mai yimun soyayyar da babu irinta mai sona saboda kai ya Allah Sannan ta fad'a Jikinshi ta fashe da kuka ta ce " I love you yaya bansan irin kalar adadin Kaunarka a cikin zuciyata please yaya wannan dama ce muka sake samu please ka tashi kawai mu gudu muje muyi Auren mu?Shafa bayanta yayi yana goge hawayen da suka so zubo mata ya ce "Bazamu gudu ba cutie " Da mamaki ta d'ago hawaye jab'e jab'e a fuskarta ta ce "saboda me.yaya Bayan mun sake samun dama" Saboda da igiyar Auren banzan Chan a kanki ya sanya bazamu gudu ba harsai Ya sakeki"Cikin kuka Aira ta ce "Ni yaya Banajin a jikina ina da wani Aure ni ban daukeshi matsayin mijina ba kawai mugudu yaya" shafa kanta yayi cikin sigar lallashi ya ce "Komai ba ayinshi cikin gaggawa my cutie ba yanzu ba" Lafewa jikinshi tayi tare da turo baki ta ce "To sai yaushe" Lakutar kumatunta yayi cikin sigar zolaya ya ce "Sai sanda kika zama jawar da kud'in yaro" Bugunshi a k'irji Aira tayi tare da turo baki cikin shagwaba ta ce "Allah yaya zan sanya maka kuka " Murmushi yayi ya ce "I m sorrry my prince's d'ina ayi hakuri kar ayi kukan nan wasa nake" Murmushi tayi tare da kafesshi da idanu ta ce "I love you so much My buzuna" Murmushi yayi ya ce "I love too Matar buzu" Duka Dariya sukasa a lokacin jinsu suke cikin farinciki da annashuwa marar musaltuwa harsun manta da damuwar da suka shiga a baya Arman ne ya ce "Had'in kanki nake buk'ata cutie wajan ganin mun cimma burinmu karki sake ki nunawa kowa kin Sanni zamu dinga mu'amula da juna a sirri kingane "Gyad'a kanta tayi ta ce " to my yaya"Jinjina mata hannu yayi ya ce "Good girl " Amma wai ya akayi jiya kad'an ya hana ki kwafsamun"Murmushi tayi ta ce "Na d'auka gizau ne kakemun Ko kuma Aljanine ya kemun siffarka Dan Yaga ina mugun sonka zai tsoratani da kai" Dariya yayi ya ce "Lallai My cutie Aljanin nan da bai kyauta ba kice har yanzu ina ranki alk'awarinmu bai tafi a banza ba" Murmushi tayi tare da kama hannunshi ta murza hannunshi ta ce "Kar Allah ya kawo ranar da zan manta dakai my yaya da ranar tazo gwara mutuwa ta Alk'awarin mu bazaije ko ina ba ya na nan har abada" Sun tab'a Hira sosai Cike da farincikin da sun manta yaushe rabon da su shiga irinshi Wanda basu sani ba har