NI DA YAYA ARMAN Lokacin da So Ya Zama Laifi by Hajara L Sadeq

Author :  Hajara L Sadeq Category :  Romance

Chapter   48 / 54

141K to 144K   out of 160.7K words

lafiya Bayan anyi bishshar kudi Mummy ma sosai ta taka rawar gani a sunan Haidar Wanda Daddy ma ya bata gudummawa mai tsoka da zata taho tare da twins sosai suka sha gayunsu nan aka shiga musu hotuna da dare Aira na kwance saboda hayaniyar mutane ya sanya kanta tsananta ciwo Mummy Ce tazo da kanta Tare da mik'ar da ita ta bata magani ta sha su Aysha tayiwa magana akan a barta ita kadai ta huta Haidar ma daukeshi Mummy tayi tare Madarar da aka fara basa ta ce "Shima bari mu kwana dashi Jinin naki ina ganin har yanzu yaki sauka kodai sai mun koma asibiti" girgiza kai Aira tayi ta ce "a a a Mummy ina ga hayaniyar mutane ce zuwa safe na kwanta zai sauka " saida taga kwanciyar ta tukwana Mummy ta mik'e tare da rufo mata dakin.
Washegari koda ta tashi ciwon kan da sauki Bayan Angama soye soye y'an uwan Mamy da Mummy duk suka wuce Bayan ancikasu da Abubuwan arziki Arman ko yana Abuja Dan ya koma kan aikinshi Ganin irin jimawar da yayi bayanan kuma lafiya qalau komai nashi a normal ya sameshi hakan yasa bai samu daman lekowaba washegari dukda hankalinshi na kan Aira Cikin kwana biyu su Aysha Da Ummy suka koma Wanda Aira saida suka sha kuka da zasu tafi su Mummy ma sun tafi danma an bar Nihal taki bin Mummy yasa Tadanjin saukin kadaici Da dare tana kwance tana chat Inda Rahama tayi mata voice ta ce "nayi ta Kiranki bata shiga daughter kuma baki hawa online " voice Aira ta tura mata ta ce "Sorry momcy kinsan bani da layin nan Shiyasa bansamu na kira ba kina raina kuma albishirinki muna ma garinku anyima su twins k'ani shekaranjiya akai suna kunyi Aliyu Haidar" kasancewar rahma na online "cikin farinciki ta ce " wow congratulation daughter Allah ya raya kai amma wlh baki kyauta mun ba kina ma garinmu ashe turoman address din Inda kike gobe insha Allah gani nan zuwa "nan Aira ta tura mata address din gidan Wahshegari ko Aira na kwance akan sopa Mama Halima na rigima da Nihal Dan kullum saisun yi rigima Aira na Dariya Haidar ko na hannun Hafsat tana liliyarshi Suka jiyo knoking Mikewa Hafsat tayi da Haidar a hannunta tana bud'ewa turus tayi ganin kawarta Rahama da suka gama KASU tare " wara idanu tayi ta ce "Friendy kece yau a gidan namu ko gizau" itama rahamar mamaki tayi ashe gidansu Hafsat ce ma Aira ta sauka "Dariya tayi ta ce " muje ciki"suna shiga har kasa Ta duk'ursa ta gaishe da Mama ta amsa cikin mutuntawa Rungume juna sukayi da Aira sunajin farincikin had'uwa Barin d'akin Mama tayi Rahama ta kalli Aira ta ce "Kai daughter a fili kinfi kyau kin ganki kuwa" Dariya Aira tayi ta ce "Ai momcy kema a fili kinfi kyau kinganki kuwa " Dariya sukayi "Ganin Nihal Kallon Aira tayi ta ce " Takwarace ko uwar fad'a kinsan bana gane su daban daban "Dariya Aira tayi ta ce " takwararce "Wara mata hannu Rahama tayi ta ce " yaudai gani ga takwara da Oum twins fad'awa jikinta Nihal tayi tana Dariya kamar ta Santa daman"Hafsat ce ta ce "Wai ina kikasan juna nan Aira ta fad'a mata Inda suka had'u tukwana itama Hafsat din ta fad'a mata kawartace " D'aukar Haidar tayi ta ce 'masha Allah shi kuma kama da mom d'inshi yayi kenan Allah ya raya manasu"Ameen Hafsa ta fad'a Bayan an kawo mata kayan makuleshe Nihal ko duk ta hahhayeta Nan ta fito da uwar sayayyar da tayiwa twins hada Haidar sosiau Aira tayi mamakin kirkin Rahama Godiya tayi mata sosai ta ce Bakomai ai ana tare sai yamma Rahama ta tafi Wanda dak'yal Nihal Aka Bambareta jikinta Dan cewa tayi sai ta bita Bayan tafiyar ta Mama Halima taja kunnen Nihal ta ce "Mutane na zuwa kina cewa zaki bisu saina zaneki ko suna baki abu kina amsa ki bisu uwar kwadayi ja'ira a haka idan mugaye ne har a sace ta " Kuka Nihal tasa "Aira ko dariya tayi " Mama ta ce "Gaskefa ku dinga hanata wlh kwanaki haka y'ar wata nan k'asar layin mu Daga ganin wani a hanya ya bata sweet ta like mai Saita bishi a banza mutumin nan ya lalata musu y'a karshe sai gawarta aka kawo musu karkiga ba kyan Gani y'ar shekara shidda " Sosai Aira ta tsorata ta ce "wayyo amma duniya ba Gaskiya wlh insha Allah Mama zamu hanata daman itace Naila bata da likewa mutane " Aira sosai take samun kulawa daga wajen Mama Halima Wanda suke zuwa Asibiti akai akai har aka samu jinin nata ya sauka yanzu ciwon kan ma ta daina sosai Rahama ma kawarta me kirki tana zuwa akai akai Arman ko fashin kwana daya yake yau yazo gobe bai zuwa Mummy ko duk sati sai tazo wannan satin tazo zata tafi Nihal ta ce itama binta zatayi daman ba wasu kaya gareta ananba Mummy tace suje zasu shiga mota juyowa tayi ta dagawa Aira hannu ta ce "Cutie mom bye" Sannan ta kalli Hafsa ta ce "Aunty bye " Dariya Mama Halima tayi ta ce "Ni baza ayimun bye d'inba " Turo baki tayi tare da Harararta ta ce "Ke ai fad'a galeki ba ruwana dake ke da dad en Cutie " sosai kowa dake wajen ya kwashe da Dariya musamman Mummy kama hannunta tayi tana Dariya cikin zolaya ta kalli Mama Halima ta ce "Kinji yarinya k'arama ma tasan halinku na fad'a " Dariya Mama Halima tayi ta ce "y'ar yayatu ce Ai gwara kuje Chan ku karata Wannan iyayen Surutun " duk Dariya sukayi washegari Arman yazo dayake barin musu palourn ake idan yazo Suna mak'ale da juna kamar kullum Haidar na hannunshi yana mashi wasa yana Kallonshi yana Dariya Aira na mak'ale jikinshi marairaicewa yayi ya ce "Cutie yaushe zaki koma gidan ni d'aya ba dadi duk a takure nake "marairaicewa tayi ta ce " Uhm nima bansaniba hero gashi Mama batamayi zancen ba "cikin damuwa ya ce " Yanzu saura kwana nawa ayi arba'in d'in "Juya idanu tayi saikuma ta ce "yau dai satinmu hud'u "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " saura kwana goma kenan"gyada mashi kai tayi "cewa yayi Allah ya kaimu"daganan suka sauya Tasha sunjima suna Abu d'aya kafin Arman ya Mike ya tafi Bayan yayiwa su Mama bankwana Aira ko ciki ta koma tayi wanka tayi alwala tayi sallah Dan tun last week ta fara salla batason Arman ya sanine Dan karya dameta ".
Inna koda ta dawo daga kauye aka bata labarin abunda ya faru sosai ta shiga Surfa ruwan masifa a gidan Inda ta shiga ba tanan take fita ba hada kukanta a lokacin Su Abba na wajen a palourn gidan ta ce " y'an jikokin nawa da nafiso su suka tsolewa mutane ido akewa sharri duk wani masifar mutum kansu ake dorawa to ta Allah ba ta mutum ba Kuma abunda akaso suyi din Alhmdllh basuyi ba mutum Saidai ya mutu Sannan kai kuma habu ka jima baka kori Hajara a gidan nan ba Ai ba wajen zama zata rasa ba Aikin banza aikin hofi sosai ta dinga bala I da masifa Shidai Abba bai tanka mata ba haka kowa dake wajen Mamy ko sosai taji dad'in yanda Inna tayiwa Abba Dan ko magana basayi dashi ita kwanciyar hankalinta ma da yanzu aka San Inda y'arta take.
Su twins ko sosai suke samun kulawa daga wajen kakannin nasu Dan duk wani meeting da za ayi na manya dasu mummy take tafiya sosai manyan mutane suka San jikokin na excellency Wanda sosai ake musu kyaututtuka ganin Suna zaune a haka ya sanya Daddy nema musu makaranta me kyau wacce tafi ko wacce tsada da koyawa ya sanyasu sannan ya nema musu Tahfex sosai Kuma yaran suke ganewa da fahimta Dan sun tsaida hankalinsu waje d'aya Saidai Rashin ji fa akwaishi musamman Naila da Ake shan fad'a da ita a school y'an ajinsu duk tsoranta suke Nihal cema miskila Dan Yanda take daddagewa yara saikace wata babba wai ita ala dole Jan aji ne kar a rainata Sosai Malaman makarantar keson yaran kasancewarsu masu kyau da kokari gashi kuma jikokin governor guda hakan yasa ake nuna musu kulawa a school kuma hakan yasa sukeson zuwa makarantar har so suke su tafi.
Aira ta na gama arba'in da sati Mama Halima ganin irin Rashin kunyar ARMAN tayi yawa yanzu kullum Yana nan kuma ya gwada matarshi yakeso ya sanya hada musu kayansu ta runkutasu ta ce Allah ya raka taki gona hakan ko sosai yayiwa Aira da arman dad'i ranar da ta koma suka bud'e sabon shafin soyayya suka dasa daga Inda suka tsaya Danma yanzu Arman na zuwa wajen Aiki ba kamar Lokacin da suke London ba kawarta maman noor da suka had'u a jirgima Tazo tayima Aira barka Dan jininsu ya had'u ranar yini tayi mata tana tambayar ina twins Noor Kullum saitayi zancensu"murmushi Aira tayi ya ce "Ai suna kano twins ina ma tunanin sun koma Chan da zama wajen kakanninsu " jinjina kai Mom noor tayi ta ce "Amma kinyi kokarifa sis kinganninan noor ta girma ma amma ban iya barinta ta tafi da kwana daya ma ai bazan iya bacci ba" Dariya Aira tayi ta ce "nikam Kinga banajin komai Saidai ma wani Karin ne nakejin kewarsu " Ai Dan kunsamu wannan shiyasa da ace ba kowa zakiji fin kadaici"eh kuma hakane noor ma Dan ita kad'aice shiyasa "Mik'a mata Haidar Mom noor tayi tare da Aje mata 20k ta ce " gashi mom twins ba yawa Ai bansaniba da har suna munje Allah ya raya"amsar Haidar tayi tare da ajeshi kan gadon shi Dan yayi bacci ta ce "Haba mom noor Dan Allah ki barshi sunyi yawa" Girgiza mata kai tayi ta ce "a a a kawata baza ayi haka ba sainaga kamar bakison kyauta daga waje na ne Ai anzama daya Dan Allah ki amsa" Badan Aira tasoba ta amsa ta ce "Angode har bakin get Inda tayi parking motarta Ta rakata tana mata Godiya sannan ta ce " insha Allahu duk ranar da su twins sukazo zasuzo tare "Bayan ta koma Daga mata rakiya ta samu missed call d'in mamy a sabon layinta na 9ja dayake suna waya " kiranta tayi Inda suka sha hirarsu sosai nan Mamy take fad'a mata irin fad'an da Inna tayi murmushi Aira tayi ta ce "Allahsrk my Inna inasonta sosai wlh Allah yabar mana Ita inason ganinta amma ba hali".
Washegari Aira na yiwa Haidar wasa yana y'ar dariyar k'uda Arman ya shigo da Fara a fuskarsa " Mikewa tayi tare da tarbarsa ta ce "Yadai honey yau ka shigo cikin fara'a kama hannunta yayi ya ce " kin tuna promise d'in da nayi maki na haihuwar twins ?jujjuya idanu tayi sai Chan kuma ta ce "Na tuna hero " yawwa to muje ga tukucinki na farko "suna fita Aira taga dalleliyar mota Ja mai masifar kyau da d'aukar hankali wacce a k'alla zata haura 10 millions"batagama santin motar ba Taji ya mik'o mata makullin mota a hannu ya ce " ga motarki cutie ta iso"wara idanu Aira tayi ta ce "Hero kana nufin motar nan tawace " Gyara mata kai yayi yana murmushi "tsallen murna Aira ta daka tare da Rungumeshi Ta fashe da kukan farinciki ta ce " Thnks yo hero Thnks you so much ka gamayimun komai a rayuwa Allah ya saka da alkhairi ya k'ara budi"murmushi kawai Arman yake ya ce "Komai nayi maki ban isa na biyaki kwatar abunda kikayimun ba cutie kece kika gamayimun komai a rayuwa kika bani farincikin da babu wanda ya tababan kwatankwacinshi Komai nayi maki kin chanchanci fiye da hakan banason Godiya Da ni da duk abunda na mallaka naki ne keda yaranki ko kin manta" murmushi Aira tayi tana farinciki ta ce "Hakika kaid'in haskene a cikin duhu Mijina Da babu kamarsa a fad'in duniyar koda ina cikin bakincikin wani abun idan na tuna Da baiwar da Allah yayimun na mallakamun mijin da yafi na kowa so da k'auna da tattalina uwa uba kyauwun hali da kyawun fuska sai Naji dadi a raina Naji waccen damuwar ta gushe nagode mijina aljannata Allah ya barmu tare har a badan Abadan....✍🏿

*Ni da yaya Arman it's not free it's fore sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*


*_Miss Hajo ce_*
[7/22, 19:01] Hajo hajo: 🅿️........*119&120*




Har Abadan Abadan sosai Aira ta shiga Jerawa mijin nata adduo i Dan sosai ya sanyata farinciki marar musaltuwa a ranar Ta shiga ta tuk'a mota Inda yana gaba Rike da Haidar Dan yaga yanayin tukin nata kuma masha Allah komai na tafiya normal Saidai Sam barka sosai masoyan nan suke rayuwarsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Sai fargabar su d'aya kawai Rashin daidaaito tsakaninsu da mahaifansu Anyi hutun school Wanda Mummy ta sanya aka kawo twins Dan suyima iyayen nasu Hutu da misalin Sha biyun rana Arman na wajen Aiki Aira na d'akinta tana gyara kayan Haidar da twins suka lalata shi kuma ta barshi a palour cikin net Twins da suka gaji da wasansu Wajen Haidar suka nufa tare da Fara liliyarshi suna mashi wasa Nihal ce ta ce "Naila bari kiga na iya d'aukar Haidar yalinya " Wara idanu Naila tayi ta ce "Mu daukeshi mom bazatayi fad'a ba " Eh mana ai bata nan "a tare suka had'u suka Chunkumeshi Jin damkar manya yaro ya kwala Kuka Wanda shi ya fito da Aira daidai suna shirin kadashi da gudu da ruga ta warceshi Cikin fad'a ta ce "Dan gidanku ban hanaku Tab'amun yaro ba kashemunshi kukeso Kuyi mugaye waye ya ce Ku daukarmunshi " ta fad'a tana jijjigashi tsuru tsuru sukayi Naila ta ce "Cutie Nihal ce ta ce Mu daukeshi" Cikin masifa Naila ta hayayyakowa Nihal ta ce "Munafuka Ba ke kikace mu daukeshi ba shine zakimun sharri" Harararta Nihal tayi ta ce "kece dai Munafuka muguwa kawai " Kallon Aira Naila tayi ta ce "Mom kinganta ko "? harararsu Aira tayi tana danna wayarta tana chat ta ce " Kuka k'ara sako suna na ma zakuyi mamakin abunda zan muku koba fad'a ba ku kashe kanku"sosai Naila ta kulu Aiko shako Nihal tayi nan suka hau Dambe Aira na jinsu ta musu banza ganin ihunsu ya isheta ma earpiece ta sanya Arman ne yashigo Ya ga twins na fad'a D'aya ta hau kan d'aya cikin Sauri ya shigo Tare da rabasu nihal dake Kuka tana saita rama Dakyal ya samu ya raba su Kallon Aira yayi da Hankalinta na kan waya ya ce "Ke yanzu Kina ganinsu suna fad'a bazaki raba su ba Saima zama kikayi kina Danna waya to idan d'aya ta jiwa d'aya ciwo fa kice me?Dagowa Aira tayi tare da turo baki ta ce " To Hero Akanme zan damu kaina Kaida kasan halinsu sarai barinsu nayi su gwada karfi nan gaba wacce taji jiki bata yarda su Kara fad'an ba Dan basu isa su doramun hawan jini da yarintataba "tana gama fad'ar haka ta sab'i Haidar tayi ciki girgiza kai yayi tare da d'aukar Nihal dake birgima take kuka ya ce " sorry my angel kiyi shiru idan ba haka ba Kuma na fasa kaiku wajen wasa"Lokaci guda ta Goge hawayen tace "hero da gaske" eh mana kuje Yanzu mom ta shiryaku anjima zamu fita sannan kice itama ta shirya kafin na shirya "Cikin Sauri Nihal tahau tsalle tare da Kallon Naila ta ce " Naila taho muje muyi Sauri mu shirya kinji dad zai kaimu wajen wasa"kama hannunta Naila tayi Ta ce "Nihal kiyi hakuri Bazan sake Dukanki ba kinji kema ki daina Jana" Gyada mata kai tayi ta ce "Nima nadaina" tukwana suka Ruga a tare d'akin Aira "murmushi Arman yayi yana jin soyayyar iyalan nashi tun suna yarinta ya lura zasu taso cikin Had'in kai da k'aunar juna danma Mummy Sun kwafsa musu sun amshe Su Gashi bazai iya amsar su daga wajen iyayen nashi ba Suna zuwa Suka samu Aira kan Gado Naila ta dareta ta ce " Cutie mom dad yace ki shiryamu kema da my boy ku shirya zamu fita unguwa Shima shiryawa yake"To aku sarkin surutu ta fad'a tana Mikewa "Dariya Nihal tayi ta ce " Mom yaushe zamuje naga takwarata"Harararta Naila tayi kamar wata babba ta ce "Ke baki da zuciya me zamuje muyi a wannan gidan Ai dad en Cutie mugu ne bazamu sake zuwa ba" Ta fad'a tana murguda baki"kallonta Aira tayi tare da hade rai Ta ce "magulmaciya Abban nawane mugu na k'arajin kin fad'a haka saina Bata maki rai Munafuka" Turo baki Naila tayi ta ce "To ai mugun ne tunda baya sonki nima bana sonshi kuma bazan sake zuwa gidan ba Har mom En takima bazanje naganta ba Tunda bata tab'a zuwa gidan muba shi kuma dad enki da bindigata zanje na harbe sa" Sakato Aira Tayi tana kallonta ji take kamar ta shakota Ja mata kunne tayi ta ce "Uban kine mugun ba uba na Dan Ubanki ubana sa ankine karki Kara zuwa gidan mana wani yace yanason ganinki yarinya sai shegen surutu to gobe_goben nan zaku tattara kubar mana gida Tunda Isgilallu ne ku munafukai" ta fad’a tana Kara ja mata kunne k'ara ta saki tare da fashewa da kuka Arman da ya shigo yaji suna dramar nan Dariya yayi tare da saurin zuwa ya d'auki Naila da take rafka ihu ya ce "Sorry momcy Yaudai kinjawa babanki zagi Kiyi shiru karna karajin maganar nan a bakinki"tana ihu tana kuka ta ce " Ance mugu ne "Tasowa Aira tayi da niyyar bugunta Arman ya ja gefe yana Dariya ya ce " Sorry mana my beautiful wife ayi mana hakuri bazamu sakeba "Naila dake Kuka ta ce " Dad saina sake mugu ne Ai "Cikin fad'a Aira ta ce " ka bari hero na daki yarinyar nan wlh ta rainani Kanaji ina fad'a tana fad'a ga sa'arta(Ohni su Aira manya)Dariya Arman yayi sosai Ya ce "To ai halinkine tayo na kafiya kinga ko idan ka tashi Gado ai linkawa kake"

48 / 54