Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
tsaidasu Karku bari su gudu kafin nazo" Angama y'an sanda suka Fad'a suna ganin Arman ya fito daga motar ya shiga ciki suka maza sukaje sukasa k'usa suka sace tayar motar Arman ko baisan wainar da ake toyawa ba yana shiga ciki ya samu Aira Inda ya barta "Sorry dia ya fad'a yana zama " murmushi tayi ta ce "Amma kayi Sauri yaya " murmushi yayi tare da fito da wata had'ad'd'iyar zoben gold ya matuk'ar tsada mai shegen kyau kama hannun Aira yayi tare da saka mata zoben yace ga zoben alk'awari murmushi Aira tayi tare da fito da zoben dake hannunta azurfartace tun tana Yarinya take jikinta dak'yal ta cirota itama k'aramar yatsar hannunshi ta kama tare da saka mashi tace "nima ga tawa ta alk'awarin" murmushi suka sakarwa juna tare Sosai Aira taci abinci saboda yanzu Hankalinta ya d'an fara kwanciya Arman Shima ya samu yaci Waje ya bata ya ce ta sauya kayan yana fita Aira cikin Sauri ta cire na jiya ta sanya doguwar rigar d'aya kawo mata bak'a tana gama sawa ta d'ora hijab d'inta pink ta jiya yana shigowa kallonta yayi yace"Koda yaushe Kyanki karuwa yake cutie "murmushi tayi ta ce " kamar kai kenan"A nan suka bar kayanta na jiya hannunsu mak'ale Dana juna suka fito Bayan Yaje ya saki d'akunan da suka kama Aira tunda suka fito kanta yake a k'asa saboda ganin yanda ake kallonsu ga kuma gabanta dake fad'uwa Suna isa Inda Arman yayi parking sosai yayi mamakin Ganin tayoyinshi Duka a sace cike da mamaki yace "yanzu fa lafiya qalau na bar motar nan cutie " Cike da tsoro Aira tace "ko wasu suka sacemaka su Yaya nidai tsoro nakeji muyi Sauri mubar wajen nan Tab'i suka jiyo daga bayansu raf RAF Raf saurin Juyawa sukayi a tare Wara idanu Aira tayi cike da firgice ganin...........✍🏿
*Ni da yaya Arman it's not free it's for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*
*_Miss Hajo ce_*
[6/23, 10:04] Hajo hajo: 🅿️........*57&58*
......Wara idanu Aira tayi cike da firgice ganin Abba tsaye bayansu yana tab'i tare da jami'an tsaro Sosai ta firgita ba itaba hatta Arman saida ya tsorata Rugawa Bayan Arman Zatayi Abba yayi Saurin Fard'o hannunta Tare da d'auketa da gigitaccen mari rumtse ido Arman yayi ji yayi kamarshi Aka Mara cike da b'acin rai Abba ya k'ara wanketa da wani Marin Wanda yafi na d'azu durk'ushewa a wajen tayi tare da fashewa da kuka Kamar Wanda aka tsunkula haka ARMAN ya zabura tare da Fard'o Aira ya boyeta bayanshi idanunshi harsun fara sauya launi tsabar masifa cike da b'acin rai Abba ya ce "Kai harka isa ina yiwa y'ata hukunci ka boyeta Dan ban waiwayo kankaba "cike da b'acin rai Arman yace " na b'oye ta d'in wannan ai zalinci ne Idan ka daketa a Bayan idona wannan ban ganiba amma gaban ido na baka isa ka daketa na zuba ido ina kallo ba "cike da b'acin rai Abba yace " Tabbas ka haifu kome kamun bazanji ciwo ba saboda baka da tarbiya bacin b'atawa y'ata tarbiya da kayi shine har zaka nuna mata hanyar da zaku gudu to Allah ya Toni asirinku y'an iskan banza y'an iskan hofi sannan ya nuna Aira dake mak'ale a bayan Arman ba abunda take inba kuka ba ya ce "Ke kuma zaki gani zakisan ja da iyaye ba Abu bane me kyau y'an sandan ya juya yace " ku kama mun ita "Daya daga cikinsu yazo Zai kama Aira dake Bayan Arman wani irin bak'inciki da ya tunkarowa Arman Ai baisan sanda ya d'aukeshi da Mari ba cike da masifa ya ce " zanga ubanda ya isa ya D'auketa wlh duk Wanda ya k'ara attempting tab'ata zaku San asalin waye ni stupid kawai mararsa Aikinyi"Sosai y'an sandan sukayi luk'ui ba Wanda ya k'ara yunkurin tab'ata cike da b'acin rai Abba ya nunashi da yatsa ya ce "Harni ubanta?Harkai d'in Arman ya fad'a cikin k'unar rai" D'aukeshi Da mari Abba yayi Dagowa Arman yayi tare da rik'e kumcinshi yace "Ni ka Mara?An mareka d'in marar mutunci ko ramawa zakayi" Suka tsinkayi Muryar Mummy"duk kallonta sukayi musamman Arman dake mamakin me ya kawota wajen nan "Abba ko sosai ranshi ya b'aci cike da b'acin rai Mummy ta ce " ka basu y'arsu Arman kafin ka fuskanci fushina"Mummy Auren dole fa yake shirin yi mata mutumin nan baida tausayi ki barmu Mummy babu ruwanku munason junanmu koma ina zamu babu ruwanku"cike da b'acin rai Mummy ta ce "Arman Yayan mahaifin naka kake fad'awa haka?Shima Arman d'in cikin b'acin rai ya ce " shi Mummy baisan da hakan ba baisan da wannan alak'arba abunda yakemun ko Wanda bamu had'a komai dashi ba bazaiyi ba me yasa bazaku ganeba Mummy munason junanmu amma mutumin nan ya tsaneni baku tunanin irin halin da zamu shiga rabamu ba alkhairi bane"Cikin b'acin rai Mummy ta ce "nace ka basu y'arsu kai wani irin mutum ne y'ar ko ta gwal ce baka hak'ura da ita ba na fad'a maka ka rabu da ita me yasa baka da zuciya Arman " Kallon Mummy Aira tayi cikin kuka ta ce "Mummy please karkice haka Allah inasonshi Karku rabamu" Hawaye ne suka zubowa Mummy tamaza ta Goge ta ce "Kiyi hakuri Kibi umarnin mahaifinki zakifi ganin da kyau Aira ku hakura Da juna sannan ta dakawa Arman Tsawa ta ce " bazaka saketa ba baka ganin hankalin mutane duk yana Kanmu ko so kake sai mutane sun fara daukarmu "Cikin b'acin rai Arman ya saki Aira tare da kama hannunta ya wullata wurin Abba ya ce " ga y'ar taka nan idan ka tashi ka kasheta Sannan baka burgeba idan baka Aura mata Duka mazan duniyar nan ba"Rik'e hannunshi Aira tayi tana kuka Ya fisge hannunshi tare da barin wajen kamar zai tashi sama cikin Sauri Mummy ta bishi Dan tasan halinshi idan yana cikin wannan halin kome zai iyayi ruk'oshi tayi dak'yal ta samu ya shiga motar da sukazo da ita tare da escort d'inta Suka bar wajen Aira ko cikin b'acin Rai Abba Shima ya kama hannunta Tare da wullata cikin mota ya zagaya ya shiga ya tada motar Mutane harsun fara taruwa wajen danma y'an sanda sun rufe ba kowa ya fahimci abunda ake ba Aira harsuka isa gida tana kuka kamar ranta zai fita suna isa Zagayowa Abba yayi tare da Fiddota ya wullota nan ya hau ball da ita tsakar gida cikin b'acin rai masifa kawai yake ya ce "kin nunamun ban isa dake ba ,ni zaki wulakanta a idon duniya Kibi namiji hotel ku shirya guduwa Y'ar iska wulak'antatta marar mutunci biye biyen maza ne kika fara hotel hotel koshi D’an iskan naki nafi karfinshi bare ke " Sosai Aira ke kuka y'an ciki ne duk suka fito Jin hayaniyar Abba da kukan Aira dak'yal manya suka kwaci Aira daga hannun Abba ba k'aramun Duka yayi mata ba Mummy ko ko lek'owa batayi ba tana ciki ta na kuka Yayyinta da d’iyan yayyinta da suka zo daga agadez su suka dinga Lallashinta akan tayi hakuri ta fawwalawa Allah komai Aira ko Bayan ankwaceta d'akinta Mama a kayi da ita ba abunda take In banda kuka tana cewa "Dan Allah ku barshi ya kasheni wlh bana k'aunar rayuwar nan mutuwa ta kawai nake buk'ata Duk Wanda yaganta saiyayi mata kuka Cikin kuka Aysha taje ta duk'ursa gaban Abba tace " Dan Allah Abba kayi hakuri ka janye Auren nan wlh Aira na cikin wani hali"D'auketa da Mari Abba yayi ya ce "kika Kara zomun da makamanciyar maganar nan sainayi miki lilis bar ganin kinyi aure cikin y'ay'ana babu Wanda yafi k'arfina" Cikin kuka Aysha ta koma ciki rik'e da kumcinta da tasha Mari wajen Aira ta nufa ta Rungumeta Itama ta fashe da kuka cikinsu bamai Lallashin wani itama amma rungumesu tayi tana kuka Dak'yal aka samu suma wata yayar Mamy ta rabasu Ta dinga basu hakuri a ranar za ayi walima walimar da ba ayita ba kenan Dan gidan ya koma kamar gidan makoki wajen isha'i Abba ya shigo ya cewa Aunty Maryam a palour maza na baki minti goma kije ki amsomun wayar da suke communication dashi idan ta Bari kuma naje na amsa da kaina tasan sauran" "To Abba" Aunty Maryam na zuwa tace "Aira ki kawo wayarki idan akwaita a kaiwa Abba yace ya shigo ranki zai b'aci " cikin kuka Aira tace tana d'akinmu cikin kayana dukansu ki kaimai"ta k'arasa fad'a tana kuka"Aunty Maryam na zuwa Inda Aira ta fad'a mata nan ta samu wayoyin tana zuwa a palour tace "ga su Abba" Kallon wayoyin Abba yayi tare da amsa ya kalli Mamy ya ce "kalli wayoyin da take rikewa a boye ke da kike d'aure mata dukanku harke zanyi maganinku" Sannan ya tarwatse wayoyin sukayi ratsa ratsa "Mummy ko tsaki taja batare da tayi magana ba abun duniya duk ya ishi Mamy Abba na fita ta tashi ta dauki mayafinta tare da ficewa ta dauki mota kai tsaye gidan Yayanta Wanda ya rik'eta ta nufa tana kuka ta ce "Dan Allah Yaya kaje ka samu Alhaji ka mashi magana kila kai yaji maganarka Dan Allah kar a d'aura Auren nan " Yayanta Alhaji Safiyanu dattijone Shima Dan zai wuce sa annin su Abba ba kamarsu daya da mamy shima dukda ya fara manyanta ya ce "Gaskiya zan fad'a maki Rahama kiyi hakuri mijinki ya dau zafi baki saniba ni kaina na sameshi munyi magana dashi ta fahimta Duka ya fad'amun abubuwan da take da kuma dalilinshi na Aurar da ita a Gaskiya ko nine iya hukuncin da zan yanke mata kenan Aurar da ita y'arki batajin magana Rahama Duka abubuwan da tayi bana kyalewa bane kawai dai Auren tsohon ne ba dad'i amma tunda shi mahaifinta ya yanke hukuncin da ya yanke me zaisa bazaku hakura ba Kuyi mashi biyayya tunda dai shine mahaifinta ku mata kuna da matsala wlh ku kuke d'aurewa y'ay'anku gindi suke lalacewa sai abu yazo yafi k'arfinku kuzo kuna kuka da idanunku kuna sharrin shed'anne bayan y'ay'annakune shaid'anun kuzo ana lik'awa k'addara tabbas akwai k'addara amma kaddara tana tarda hali Allah yace tashi in taimakeka ko saikije ki aje kud'inki a kasuwa ki tafi ki barsu kice Allah zai tsare to kamar hakane ku da kanku ya dace ku dinga tsawatarwa y'ay'anku idan sunyi ba daidai ba yana da kyau y'ay'anku ya kasance suna shakkarku to nidai indai na isa dake karki k'ara daga maganar nan ki sanyawa Auren nan Albarka kawai kinji abunda na fad'a maki" cikin kuka ta ce "Yaya ni ban d'aurewa y'ata gindi ba maganar gaskiya ce yaya tana da wanda takeso suna san junansu kuma d'an uwanta ne yaya kasan komai fa yanzu haka fa yau inbanda Allah ya taimaka dafa sun gudu wani hali kake tunanin zasu jefa kansu da ace sun gudu d'in" d'aga mata hannu yayi ya ce "duka nasan komai Ya fad'amun ba a hotel aka gansu ba ni kaina na so ace d’in wanda take so d’in aka bata amma tunda mahaifinta yace bayason alak'arta dashi me yasa bazasu hakuraba tayiwa mahaifinta biyayya kika sani kila sanadin biyayyar da tayi mashi Allah ya daidaita tsakaninshi da d'an uwanshi ko kuma ya sanya ya hakura kinsan dai ba ayiwa iyaye biyayya a tab'e Bansan ki k'aramun maganar komai Rahama y'arki bata da gaskiya abubuwan da take ba daidai bane ga al'adar mu mu hausawa harma a musulunce dan haka Aure shi yafi dacewa da ita Tsohonma idan yaro ya gagareka wanda ya fishima saika Auramai da dai d'a ya daukomun magana hukuncin mahaifinta yayimun daidai kawai inda bai Kyauta ba da baya bin komai a hankali fushi ne kawai matsalarshi ‘’Goge hawayenta Mamy tayi tare da tashi Ta ce " saida safe yaya " Kinji Haushi na dan na fad'a maki Gaskiya ko Rahama"girgiza kai tayi ta ce "a a yaya zantafi ne nabar bak'i "girgiza kai yayi ya ce" sannan itama Hajarar ki yi mata nasiha kinji gobe idan an d'aura Auren zanshigo na ganta"To"tafada tare da saurin ficewa daga palour duk Haushi ya kamata yayannata ma da take tunanin zai huce mata takaici shima ga abunda yake fad'a Cike da takaici Mamy ta koma gida sannan kuma tana nazarin maganganun Yayan nata.
Arman har suka isa gida jin zuciyarshi yake kamar zata rabe gida biyu dak'yal Mummy ta samu ya shiga gida cikinsu babu Wanda ya kuma yiwa magana Ranar kamar wani zararre haka ya koma ba um ba um um ga wani zazzabi da ya rufeshi lokaci guda Sosai Mummy ta shiga tashin hankali Kwantar dashi tayi a d'akinshi lallashi da nasiha ba irin Wanda Mummy batayi ba Amma a banza ko tanka mata baiba wajen karfe goman dare ganin har yanzu Arman yaki magana ya sanya Mummy fashewa da kuka ta ce "ya kakeso nayi Arman karka sanya rayuwarka cikin wani hali please kaikad'ai nake dashi " Shima fashewa da kuka yayi tare da Rungume Mummy ya ce "Shikenan Mummy yanzu ya rabamu Mummy me yasa kikaje wajen me yasa zakice na bar mashi ita su tafi Mummy why ina sonta sosai itad'in rayuwata ce Mummy ko kema kin daina sona kamar Daddy duk Wanda ya rabani da Aira mak'iyina ne Mummy na tsani Abbanta bana kaunarshi ya rabamu.....ya k'arasa fad'a yana rushewa da matsanancin kuka Itama mummyn kuka take ta ce " ka nutsu son ina sonka sosai kawai Inajin takaicin irin wulakancin da ake makane a sabo da ita shiyasanya nace ka rabu da ita nafi kowa sonka tare da ita Arman Amma tunda mahaifinta bayaso ka hakura da ita shi yafi Allah zai musanyama da wacce ta fita Alkhairi a lokacin da naje wani D’an sanda ne ya kirani yace nazo ba lafiya shiyasama harka ganni “Mummy babu wacce tafi Aira a duniyar nan ki daina fad'ar haka ni ita kadai nakeso kuma ita kadai zan iya rayuwa da ita Mummy mutuwa zanyi ya k'arasa fad'a yana rushewa da kuka Mummy Lallashinshi sosai Mummy ta shigayi amma ya dinga mata sabbatu Daddynshi ta kira ta fad'a mashi halin da ake ciki tsaki yaja yace "ki rabu dashi indai akan mace ne yake wannan haukan ni kaina mahaifinka bazan tab'a yarda ka aureta ba baka isa ka aurarmun jinin Rahama ba duk na kyale kane ka gama haukan naka kuma yayimun daidai da ya rabaku kuma zai mata Aure Kamar yanda mahaifinta ya isa da ita zai mata Aure to haka nima indai na isa dakai Bazaka k'ara sati biyu ba batare da na maka Aure ba " yana gama fad'ar haka Daddy yayi waje Arman sosai ya k'ara burkicewa Mummy ya zame mata kamar wani Mahaukaci dak'yal ta samu ta kira family doctor d'insu yayi mishi allurar bacci Saida bacci ya daukeshi hankalin Mummy ya d'an kwanta gefenshi ta zauna tana hawaye tayi tagumi sosai ta tausaya halin da tilon d'an nata yake ciki.
Daren ranar Aira bata rintsa ba kwana Tai tana kuka tana jin daman mutuwa tayi ta huta washegari koda ta tashi batayiwa kowa magana ba ko kukan ta daina Dan tuni ta sik'e duk yanda akayi da ita tayi magana takiyi kowa yazo Saidai tayi mishi banza wajen k'arfe Goma da wani Abu yayar mamanta Fadila ta shigo Tare da farfesun Kaza a plate da tasha had'i zaunawa tayi tare da Kallon Aira ta ce "maza maza y'ata ki cinye wannan kinji Wai Yama za ayi Ace Amarya ba gyara ba dilka ba komai har yau d'aurin Aure Amshi ki cinye wannan muje na had'o maki ruwan wanka " Wani irin banzan kallo Aira ta wulla mata Tare da Amsar Farfesun ta watsa mata shi a jiki dukanshi ga zafi"Fadila saida tayi ihu Dan sosai zafin ya shigeta cikin tashin hankali ta mik'e tana yarfe hannu Tace "Aira ni zaki k'ona koma nace kika k'ona tsaki Aira taja tare da tashi tayi hanyar waje Aunty Maryam ce dake d'akin tace " waike Baki da Hankali yayar mahaifiyartaki zaki yiwa wannan wulakancin"itama harara Aira ta galla mata tare da Jan tsaki tabar d'akin Fadila koda ta koma sosai yayyun Mamy suka shiga yi mata Dariya Aunty ramlat tace "daman wa ya kaiki in banda kinibibi irin naki" Dariya Mama Halima tayi ta ce"Ai saida nace ki rabu da ita wannan kiyi waje kawai ki ajeta Muma ido muka zuba mata Aira tana barin d'akin daman dakin Mama ne Chan ta kwana Dakinsu ta koma Tare da buga uban tagumi K'arfe d'aya da wani Abu aka d'aura Auren Hajara Abubakar tare da Angonta Alhaji Yusuf Madugu sokoto Wanda ya samu halartar manya_manyan mutane Dan Alh Yusuf Shima ba k'aramun attajiri bane haka Abba a masallacin Juma a aka D'aura Auren Arman na kwance Bayan ya tashi lokaci guda harya rame Mummy ta sanya mishi pillow a bayanshi tana bashi tea a baki Wanda dak'yal ta samu yakesha saida tayi kuka ta samu ya fara sha a plasma din dake manne a d'akinshi tashar da suke kallo suka ga An nuno D'aurin Auren Inda d'an jaridar yake cewa "Alhmdllh a yaune Ranar Juma a aka d'aura Auren Alhaji Yusuf Madugu Shahararren d'an kasuwar nan tare da Amaryarshi Hajara y'a ga Former Senate Alhaji Abubakar Umar.......ai Arman bai k'arasa jin sauran maganganun ba ya nemi numfashinshi ya rasa Mummy na bashi tea taji ya fara tari da wani irin Abu kuka ta fashe dashi tace " na shiga ukku me zan gani haka Arman "Kafin ta k'arasa maganar sai gani tayi jini yana fito mai ta hanci ta baki wani uban k'ara Mummy ta saki tare da rugawa tayi waje cikin tashin hankali ma aikatan gidan suka taryeta tare da Daddy da ya shigo ta kasa magana sai d'akin da Arman yake take nuna musu Cikin kid'imewa Daddy suka nufi d'akin sosai suka shiga tashin hankali ganin halin da Arman ke ciki gudajen jini kawai ke fitomai shi kanshi Daddy cikin rud'u dukda nauyin Arman haka ya sungumeshi cike da tashin hankali Mummy Da Abba sukayi waje Driver Ya fiddo mota tare da Security Aka nufi Asibitin