Author : Hajara L Sadeq Category : Romance
abunda Abba yayi musu ba har suke ce masa mugu Saida ya biya yayi musu sayayyar kayan ciye ciye Dan su kwantar da hankalinsu tukwana ya wuce dasu gidan wani abokinshi kasancewar akwai yara a gidan Tuni suka wartsake suka hau wasanninsu yinin ranar Aira Haka ta yini a sume.
Washe gari ma.koda ta farka bata iya tuna komai saidae tabi mutane da ido ganin Abun nata Yana neman zama tab'in hankali ya sanya Mamy buk'atar a basu sallama Dan Aje kawai a dinga mata rokon Allah likitan bai musa ba ya basu sallama ranar Suka wuce gida Da ita Sosai Mamy tayi mamakin Abba da bai ce komai ba A.lokacin Aira bata ma cikin hayyacinta Abu saiya Zamewa mutanen gidan biyu da Jimamin mutuwar Inna ga Rashin lafiyar Aira Arman kasancewar bayanan aka bada sallamar koda Mummy ta fad'a masa an sallamesu an Wuce gidansu da ita sosai ya shiga f'ada Inda ya shiga ba tanan ya ke fita ba Ya ce "Akanme za a kaimun mata Chan bada izini na ba sanadin a kara bata mata rai ne Me yasa ba a kiraniba Ko so ake sai an k'ara wulakantamun ita tukwana hankali zai kwanta" Cikin fad'a Mummy ta ce "Kai baka da hankali ma to tatafi chandin kainan gani kake har kafi iyayenta sonta to ko su da kaga suna mata haka ba Dan basa sonta ba koshi mahaifin nata Yana son y'arshi daurewa ce yake ka duba kai soyayyar da kakeyiwa yaranka to haka ko wani uba yake yiwa y'ay'ansa Dan an kaita gidansu shine zakazo ba kunya kana kumfan baki to ankaita din kuma bazata dawo ba sai ta samu lfy" Shiru Arman yayi batare da ya k'ara cewa uffan ba Daga asibitin Mummy gida ta wuce ita da twins shi kuma Arman ya wuce Guest house d'inshi ko ya rage haushin da yakeji har a ranshi yaji haushin tafiya da Aira akayi gidan su Dan Ko kare ya cinye zuciyarshi bazai tab'a taka gidansu ba Dan ko zaman makokin Inna da akayi a Farfajiyar gidanta akayi bai lek'a ko bangarensu ba to shi yanzu ya zaiyi sun tafar mai da mata gashi baya ma da tabbacin Abbanta zai amsheta Da wannan tunanin ya yini zuciyarshi chunkushe duk ba dadi Aira ko bangarensu Sosai Aka baza malamai aka dinga mata rokon Allah Dan ta firgice ta zama kamar wata mahaukaciya a haka Aka samu take shan rubutu ko magana batayi Yayinda Mamy ta yaye Haidar ganin halin da mahaifiyarshi ke ciki Ga kuma ciki da Dr yace tana dashi madara da Abinciccikan yara aka shiga bashi y'an gidan sosai suke Son yaron lokaci guda suka shaku dashi abun tausayi Aysha Da Ummy ko kullum suna gidan Mama Halima da Aunty Maryam Bayan anyi sadakar Bakwai suka tafi gidajensu Yaya Omar ma ya koma wajen aikinshi Bayan Kwana goma da rasuwar yan uwan mummy ma da na mamy duk sun zazzzo gaisuwar daga garuruwansu har bappa da goggo sunzo sunyi gaisuwa ranar suka juya gidan ya rage sauran yasu yasu Aira ko har yanzu sauki Saidai na Allah Arman Kullum da damuwar abun yake kwana yake tashi gashi idan ya kira wayarta Saidai Amma ta d'auka a wajen amma nema yake sanin halin da ake ciki yau yana zaune a daki kadaici duk ya isheshi gana Aira ga na kewar twins ga mutuwar Inna duk ya rame kiran Daddy ne yaji ya shigo Wayarshi da mamaki ya d'auka "Nan Daddy Ya shaida masa yana nemansa a gidansa yanzu" Cikin Sauri Arman ya Mike tare da d'aukar key bai zarce ko ina ba sai gida Inda yana zuwa ya samu twins Gefen Daddy Alamun Kuka ma suka gama suna ganinshi suka Ruga da gudu tare da Fad'awa jikinshi suka sanya kuka Lallashinsu yayi tare da zaunawa kan sopa Ya ce "Ina yini Daddy " Lafiya qalau Daddy Ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya "Shiru Arman yayi Ya rasa abun cewa ga twins dake masa kuka Jin Shima Daddy yayi shiru ya sanyashi Dagowa a hankali ya Kalleshi tare da Kallon Mummy da itama shid'n take kallo Da ido tayi masa sing da yaba Daddy hakuri Kallon Daddy yayi tare da Saukowa daga kan kujera ya Dirar da gwiwowinshi har k'asa cikin ladabi ya ce " Daddy Dan Allah ina neman yafiyarka akan abubuwan da nayi maka Kayi hakuri ka yafe mun badan niba Dan girman Allah"Ajiyar zuciya Daddy Ya sauke ya ce "Ka tashi Arman na jima da yafe maka Allah yayi maka albarka ya yafe mana baki d'aya Arman wani sanyi yaji cikin zuciyarshi Mikewa yayi tare da zuwa kujerar da Daddy yake ya ce " Nagode Daddy Allah ya saka Alkhairi ya k'ara girma hakika kaid'in ka cika uba na gari mai mahimtar iyalanshi Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana"Cikin murmushinshi na manya daddy ya ce "Ameen my son Tare da Rungumeshi yanajin soyayyar yaron nashi na k'ara ratsa shi ta bangaren Arman ma haka yaji sosai soyayyar mahaifin nashi na k'ara fisgarsa.........✍🏿
*Ni da yaya Arman its not free its for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*
_*Miss Hajo ce_*🤙🏿
[7/23, 23:37] Hajo hajo: 🅿️..........*123&124*
Sosai soyayyar mahaifin nasa ke Kara fisgarsa Mummy ko hamdala tayi tare da d'aga hannu ta godewa Allah da ya nuna mata wannan babbar ranar da ta jima tana tsumayi "Bayan sun tsagaita Daddy Ya kalli Arman ya ce " Naji ance Ita Matar taka tana gidansu Kaje kaga jikin nata"A a a Daddy Banje ba Banajin zanje"shiru Daddy yayi bai Kara cewa uffan ba Mummy ko ta lura akwai magana a bakinsa ya kasa furtawa ne kawai twins ne sukaje wajen Mummy Naila na hawaye ta ce "Mummy ki kaimu wajen mom asibiti mu ganta" Nihal kuma ta ce"Mummy ki kaimu wajen cutie Mom da Haidar bata da lafiya karta mutu"shiru Mummy tayi tana Nazarin yanda zatayi da Yaran nan wata dabara ce ta fad'o mata ta ce "Mamanku ta warke tana London Ita da Haidar sunje suyi maku sayayya "shiru twins sukayi kamar masu nazari basu Kara cewa uffan ba Mummy ko tana so taje taga jikin na Aira Tana tunanin Daddy Dan ya hanata shiga gidan saboda ko zaman makokin Inna da Akai bakinsu part din inna Batace uffan ba Daga ranar ARMAN ya dawo gidansu da zama Wanda Bayan sati guda Daddy Ya ce " ya koma kan Aikinshi Ba dan ya so ba ARMAN ya koma Ba abunda ke damunshi irin. Kewar cutie d'inshi da Rashinta a kusa dashi gashi har yanzu idan ya kira amma Saidai tace masa bata magana Twins ko sunkoma makarantarsu Inda yanzu basu da walwala irin ta da Dabara Mummy tayi musu tace Aira ta koma Abuja tare da Dad d'insu Idan sukace ta kira musu ita sai tace Wayarta ta lalace a haka take musu dabara.
Tsawon wata biyu kenan Aira na kwance ba a gane kanta dan likita ya ce "ta dan samu loosing memory ne sai a hankali zata dawo daidai insha Allah Kullum Mamy saitayi mata kuka ga cikinta da ya fito sosai yau ma tana kwance idonta bud'e Mamy na gefenta Amma na goye da Haidar tana jijjigashi Kallonta Mummy tayi ta ce "Ki tashi kici abinci Aira tun jiya rabonki da abinci ?juya kanta Aira tayi tare da rufe idonta " Girgiza kai Mamy tayi tare da zubo abincin nan ta tirsasata taci Saida tayi hawaye ganin halin da y'artata take ciki ta zama kamar wata mai tabi nan ta bata rubutun da ake yo mata Tasha tukwana ta gyara mata kwanciyarta.
Yau Arman yazo daga Abuja yana isowa twins suka tareshi da murna ya d'aukesu d'aya Bayan daya Yana musu Dariya Waiwaye suka fara suga ina Aira amma basu ganta ba Kallonshi sukayi suka ce "Hero ina cutie?Gaban Arman ne ya bada daram Dan daman abunda ya kawoshi kenan Dan hakurinshi ya k'are Gwara a bashi matarsa ya nema mata lafiya Dan kwanakinnan duk cikin 'kaya ya yisu Mummy ce ta Kalleshi dake tsaye ta ce " Yaran nan Dan Allah a kaisu suga mamansu ni wlh tausayi suke bani"Ajiyar zuciya ARMAN ya sauke ya ce "Bari idan na huta na kaisu amma ki fara tambayar Daddy idan ya yarda " murmushi Mummy tayi ta ce "Zan tambayesa dukda nasan bazai hanaba saboda na lura tundaga mutuwar Inna dad d'inku baida walwala yayi sanyi duk ya sauke wani Abu dake kanshi" Bayan Arman ya huta Mummy ta shirya twins da sai murna suke yau zasuga mom d'insu Mummy koda ta tambayi Dad cewa yayi akaisu suga Mahaifiyarsu tunda ma weekend ne su yi kwana biyu a Chan"Bayan Arman ya shirya misalin hud'u na yamma ya d'auki yaranshi a mota Inda saida ya biya ya jibgo uwar sayayya su Malta cartoons madara,Custard, Juice kala kala Da sauransu saida aka cika boot din motar da kaya Tukwana ya nufi gidan su Aira suna isa Kallon Twins yayi ya ce "Ku shiga to kuga mom din taku gobe zanzo na Daukeku" Naila ce ta zaro ido ta ce "Hero mom ai bata nan dad enta da mukaje ya kolemu" Danne zuciyarshi Arman yayi ya ce "Ku je tana ciki yanzu bazai kore ku ba" ya fad'a yana fitowa tare da kama hannunsu Ya kaisu Har bakin Kofar gidan saida yaga shigarsu Yana musu bye bye tukwana ya koma Almajirai ya samu suka shiga da kayan cikin gidan dafe ganshi yayi dake mugun saramai ji yake kamar shiga ta fito da matarsa da yaronsa dake gidan Wayarshi ya lalubo tare Danna kiran layin Aira Amma na d'auka ya ce "Fitomun da Haidar Ina kofar gidanku" To ta fad'a A lokacin da twins suka shiga palourn gidan Sosai akayi mamakin ganinsu Aysha ta taryosu ta ce "oyoyo my twins yau kune a gidan" Shiru sukayi suna kalle_Kalle So suke suga Aira amma basu ganta ba Mamy ce ta fito ta ce "Ah yau manya garemu a gidan kenan " Duk shiru sukayi basuce komai ba sai waige waige da suke "Mama ce ta ce " Yau ba a y'an maganar kuke ba kenan?Naila ce ta fara hawaye tare da Kallon Mamy ta ce "Mom ena cutie " Nihal kuma ta fara kuka ta ce "Ina mom d'inmu" kama hannunsu Mamy tayi tare da kaisu d'akin da Aira ta ke Inda suka sameta kwance da gudu Suka ruga Wajenta tare da hayeta suka fara girgizata suna mom ki tashi"Hayaniyarsu ta tayar da Aira Kallonsu ta dingayi da ido su kuma Rungumeta sukayi suna murnar ganin maman tasu "Mummy na tsaye a kansu Amma ce ta fito daga toilet Bayan tayiwa Haidar wanka ta shirya shi Kallon Mamy tayi ta ce " Mamy babanshi ya ce na kaishi Bari na kaisa"ARMAN dinne ya kawo yaran kenan"Eh Mamy "Bazai shigo ba kenan" Girgiza kai tayi ta ce "Wlh bansaniba" Ki kai masa shi "Mamy ta fad'a " Su mamy nan sukaga ana ta shigowa da uwar sayayya suna gani suka san arman ne ya aiko Fita amma tayi da Haidar a hannunta da yake ta zillo a gaban mota ta samu Arman Inda ta gaisheshi Ya amsa cikin mutuntawa Mik'a masa Haidar tayi ta ce " Gashi yaya"Amsarsa yayi ya ce "Nagode Sis Ya jikin cutie din da sauki" da sauki yaya yanzu tana samun sauki bazakaje ka ganta ba?Girgiza kai Arman yayi ya ce "Allah ya bata lafiya Dan Allah ku dinga kula da ita sosai ga twins nan zasuyi kwana biyu shi kuma Haidar ki cewa Mamy na tafi dashi yayi mana kwana biyu Idan nazo daukarsu saina Maidosa ki gaishe da y'an gidan to amma ta fad'a tare da yiwa Haidar bye bye Dan sosai ta shaku dashi a Rashin lafiyar da Aira tayi ita ta zame masa uwa twins sosai suka lafe jikin Aira wacce ta kasa daga baki tayi musu magana ganin tayi shiru ya sanya Nihal shafa Fuskarta ta ce "Mom bazaki mana magana ba ko munyi miki laifi kiyi hakuli bazamu sake ba" Naila ce ta fara hawaye ta ce "Mom kiyi magana" Saida Mamy ta Goge hawayen tausayin yaran "Magana suka dinga mata wanda hakan yasa aira taji kanta ya fara juyawa saiji sukayi ta fasa.k'ara tare da sulalewa wajen summammiya Sosai y'an gidan suka nufo d'akin hankali tashe twins ko kuka suka sanya suka hau jijjigata suna mom.ki tashi karki mutu ki tashi mu tafi Abba ne da ya shigo duba jikin na Aira dan yajiwo ihunta ya samesu a haka suna ganin Abba Suka rude suka hau jijjigata suna cewa " Mom ki tashi Ga dad enkinan Ki tashi mu tafi karya dakeki ki tashi mu koma gidanmu"Mamy ce dak'yal ta samu ta banbaresu daga jikin Aira suna kuka Naila Abba ya yunkura ya d'auka Dan baiji dadi ba har ranshi yanda yaran suke tsoronshi sosai Naila ta k'ara yiwa kukanta volume Lallashinta Abba ya fara cikin sigar Lallashi da kwantar da hankali "Harya samu tayi shiru ta lafe a jikinshi Nihal ko kuka ta ke ta kalli Mamy ta ce " mom en Cutie a kaita hospital karta mutu"Kallon Abba Mamy tayi ta ce "Ko Asibiti ake kaita Abbansu?Shiru Abba yayi kamar mai nazari sai kuma ya ce " Bari na kira dr din yazo ya duba ta a gida haka ko akayi Dr d'in har gida yazo Inda ya duba ta Sosai sukayi jugum jugum yana gamawa Ya juyo Ajiyar zuciya ya sauke tare da Yin hamdala ya ce "Alhamdulilla Ta dawo daidai ne data tashi Insha Allah zata dawo yanda take Saidai a dinga Lallashinta Sannan kar a dinga tuno mata da Abubuwan da suka wuce Dan Gaskiya a tunani na ba tension din mutuwar nan kawai ya sanya ta samu matsalar nan akwai damuwa sosai a tattare da ita Wanda a age d'inta kwalwarta bazata d'auka ba Allah kiyaye gaba " Hamdala kowa ya sauke Sukace ameeen sosai suka yiwa dr din Godiya Abba ne ya ce "Yanzu zuwa yaushe zata farka" ?zuwa gobe zata iya farkawa a barta ta huta kar ayi hayaniya a kanta "Godiya duk sukamai Abba ya ce Duk a firfita a barta ta huta Shi ya fita da twins da suke kuka ya lallashesu Bayan ya bawa Haidar ya sayo musu choculate Aiko nan suka D'are Abba Suna murna Take suka waske suka fara masa surutu Sosai hakan yawa Abba dadi koba komai dai yanzu yaran sun daina tsoronshi dukda har yanzu baisan ta yanda aka samun yaran nan har Ukku ga cikon na hud'u "
Arman daga gidan su Aira wani mall ya biya ya jibgowa yaron nashi sayayyar kayan sawa da kayan wasa gidan Mummy ya wuce Amsar Haidar Mamy ta yi ta ce "Lale marhaban mai Gidan har gida" zaunawa Arman yayi tare da sadda kai ya dafe kanshi"Kallonshi Mummy tayi ta ce "Lafiya dai son"? d'agowa yayi ya ce " Mummy wai yaushe zasu bani mata ta?Shiru Mummy tayi ta ce "Inason naje ma naga jikin nata wlh amma bari anjima muyi magana da Dad dinka in ya bari jibin sai naje na ganta Ka bar maganar dawowarta Arman ka bari ta samu sauk'i kuma tunda mahaifinta ya fara Saukowa ka bari su sasinta da mahaifinta kamar yanda ka sasinta da mahaifinka muyi mata adalci itama Mu bari iyayenta suma suyi iko da y'arsu tunda wancen lokacin munyi musu haka koni kaina sainaje na nemu yafiyar mahaifinta saboda bamubi yanda shari a ta tanadar ba a aurenku mu samu mu warware matsalolin nan Inajin a jikina komai yazo karshe" Ajiyar zuciya Arman ya sauke Tabbas maganar Mummy Gaskiya Ce soyayyar da zai nunawa Aira a yanzu ita ce Ta sasinta da mahaifanta da dare Mummy ta samu Daddy da maganar zataje taga jikin Aira cewa yayi zata iya zuwa amma akayi mata wulakanci ba ruwanshi cewa Mummy tayi ta yarda tunda dai ya amince taje din da sauki.
Washegari kamar yanda Dr ya fada tunda safe y'an gidan suka sanya Aira gaba Suna jiran farkawartata har Naila dake jikin Mamy Suna wajen Abba ma yana d'akin Nihal na jikinshi Dan tun jiya ta like mai A hankali ta fara bud'e idonta da sukayi mata nauyi harta k'arasa budesu saukesu tayi akan y'an gidansu kowa Ajiyar zuciya ya sauke Sukace alhmdllh Naila da Nihal da gudu sukaje suka Fad'a kanta sukace "Mom kin tashi" Kallonsu Aira tayi d'aya Bayan daga abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata a kwalwa rumtse idonta tayi tare da budesu wasu zazzafan hawaye ne suka shiga zubo mata kallon Mamy tayi ta ce "Mamy wai da gaske ne Inna ta mutu?Kama hannunta Mamy tayi ta ce " Hakan da kikayi ayra ba soyayya bace kike nuna mata Shi mamaci a koda yaushe addua yake buk'ata bawai Dan anyi mutuwa ka shiga tashin hankaliba Wannan din kamar Rashin tawakkaline karfa ki manta mutuwa na wuyan kowa kuma muma bamu wuce ta d'auke muba a kowani lokaci kema Da mu jiranta muke addua zaki mata ba kuka ba kinji"hawaye ne suka zubowa Aira ta Goge ta ce "Allah ya jikanki Inna yasa kin huta ked'in kinyimun komai a rayuwa halinki na gari ya biki Tabbas nayi Babban rashi Inna shakuwarmu da mukayi shekara da shekaru shikenan yanzu kin tafi kin barni" Rungumeta Mamy tayi ta ce "Is okay kukan ya isa Haka kiyi mata addu'a kinji" Saida Aira tayi kuka sosai jikin Mamy kafin ta hakura tayi shiru Dagowa tayi ta kalli Mamy ta ce "har an binneta mamy"?,Yanzu watan Inna Biyu da rabi Ayra tunda ta mutu kika zautu sai yau Kika dawo hankalinki " Sosai Ayra tayi mamaki Ace wata biyu kenan da rasuwar Inna ji take kamar yau ne duba jikinta tayi taga ciki jikinta ya fara girma sosai tayi mamaki ita dai ko lokacin nan bata San tana da ciki ba "Nihal da Naila ne sukaje Wajenta suka Rungumeta suka Ce "Sannu mom " Rungumesu Aira tayi tare da Kallon Mamy Dan bata lura da Abba dake dakinba ta ce "Mamy bari muyi Sauri mu tafi kar Abba ya dawo ya samemu Ta