Author : Khaleesat Haidar Category : Romance
kunnen intisaar, intisaar
dae
hadiye dariyarta kawae take don bata ma
san me
inna ke cewa ba ta dage sae mutsu-mutsu
take
mata a kunne, ita a dole xata ba Aliyu
haushi,
kallonsu kawae yake ta madubi, intisaar ta
lura
da hkn sae ta shiga taitayinta, yyi tsaki
kawae ya
kara volume din wakar dake tashi a motar, a
hankli intisar ta matso kusa da inna take
nuna
mata hanyar gidansu faruuq cikin murya
kasa
kasa take magana, inna ta bude murya tana
cewa
"Allah sarki yaron Arxiki" brake Aliyu ya taka
da
karfi, inna ta saka salati a rude tana cewa
"lfya?"
ya fito da sauri ya bude bayan motar, da
gudu
inna ta fito tana cewa "fito intisaar yau mun
shiga uku me ya faru?.
A rude inna ta dinga tambayrsa me ya
sami motar bayan intisaar ta fito, bai ko
kalleta
ba ya shiga kwaso masu ledojin tsarabarsu
da
saurinsa, inna ta dada rudewa tana cewa
"purse
dita na ciki akwae kudade da yawa fito min
dashi
da sauri wllh har da daham dina a ciki, ya
ciro
purse din ya ajiye kan ledojin da yake ta dire
su a
gefen titi, inna ta kin ki me abinta da sauri
tana
lekar motar a tsorace, "to wae me ya samu
motar?" inna ta tambaya tana jan intisaar su
matsa daga kusa da motar, bai ko kalleta ba
har
sae da ya tabbatar ko tsinkesu bai bari a
cikin
motarsa ba sannan ya rufe motar, ya juyo
yana
kallonsu fuska daure yace "ku nemi motar
haya
da xae kai ku inda xaku, don baxan bata lkci
na
na bar abinda ke gabana na dauko ku a
mota ku
dinga min iskanci a cikin motar tawa ba."
Yana
kai wa nan ya shige motarsa ya ja ta ya bar
su
tsaye a wajen, inna ta xabga salata tana
girgixa
kai tace "amma wannan yaro na Bukar anyi
tantirin dan iska, ynxu xubar damu yyi a
dajin
Allahn nan ya wuce?" sae kuma ta fashe da
kuka
tana cewa "wannan masifa da me yyi kama
ni
Rahmatu" intisaar ta dinga tuntsire dariya
tana
karewa inda ya ajiyesu kallo ita dae bata ga
alamar daji ba a wajen amma inna tace daji
ne,
sannan ga motoci na ta wuce wa abinsu,
har da
mutane ma nata harkokin gabansu a wajen.
kukan da inna ta dinga rusawa ne ya fara
jawo
hanklin jama'ah wajen, intisaar tace "kai
inna don
Allah kixo muje mu hau mota mu wuce,
dube
yanda kika janyo ana ta kallonmu," cikin
kuka
wiwi inna tace "wllh baxan hau motar haya
ba
don ubanki, hka kawae dan nawa na da
motoci
sae na buge da hawa ta haya" intisaar ta
kulu
matuka ita kam da ta sani bata bi inna ba,
wannan disgrace din har ina? Taruwa
mutane
suka fara yi a kansu ana tambaya lfya? Nan
inna
ta dinga surutu ratata akan abinda jikanta
yyi
mata, intisaar ji tayi kmr ta nutse a wajen
don
kunya, da sauri tayi gaba ta barta a wajen
cike
da takaici, ita ba kudi ta fito da ba bare ta
hau
mota ta koma gida, ta juya daga nesa tana
kallon inna da mutane suka gama
kewayewa, ko
me take gya masu oho. Da kyar mutane
suka
lallaba inna ta hau adai-daita sahu, tana
gunjin
kuka ta shiga tana cewa "Allah dae ya isa
tsakanina dashi," sae kuma ta fara
kwadawa
intisaar kira tashigo su wuce, kasa xuwa
wajen
intisaar tayi sbda mutanan da suka taru a
gun,
har kusa da ita tricycle din ya tsaya sannan
inna
tace "maxa shigo intisaar, Allah xai saka
mana,"
fuskarta daure tashiga, mutanen wajen
suka bisu
dacewa " Allah ya saukeku lfya Hajiya, Allah
ya
kiyaye, ya ja da ranki" inna ta ding a
washale
baki tana gdya tare da daga masu hannu,
shi
kanshi mai tukin dariya yake yi. Sae da suka
yi
nisa sannan inna ta dube intisaar tace
"kinga
mutanen arxiki koh, har biya mana sukayi,
Allah
yyi masu albarka dae" intisaar bata ko
kalleta ba
bare ta tanka mata. Har bakin gate Napep
din ya
ajiyesu, inna ta dinga gdya ya fiffito masu
da
kayansu, intisaar ta dauki wanda xata iya ta
shiga cikin gidan inna na biye da ita a baya
tana
cewa "to ynxu bayan duk wlkcn da yyi mana
ba
gamu a gidan ba. Nafisa tayi murna da
xuwan
mhaifiyar ta ta sosai,'ya yanta duk suka xo
gaida
kakar tasu dayake ranar asabar ce suna
gida,
sae da inna taci ta sha sannan ta soma
xayyano
wa Nafisa irin abinda Aliyu yyi masu a kan
titi,
Nafisa tace "amma wllh Aliyu bai da
mutumci ko
kadan inna, kinsan kuwa tunda na dawo ko
sau
daya bai taba xuwa gaida ni ba ko yi min
sannu
daxuwa, amma haisam xuwansa biyu
knan," inna
tace "ranar da ya kawosu xainab bai shigo
ba?"
Nafisa tace "xan masa karya ne inna?" nan
inna
ta kwadawa intisaar dake dakinsu maryam
kira,
dayake maryam din sa'arsu ce da xainab,
suka
shigo tare da maryam din, inna tace "ranar
da
Aliyu ya kawoku gidan nan dama bai shigo
ba?"
intisaar tayi jim don dae ba Aliyu bane ya
kawosu
motar haya suka shiga amma da suka koma
gida
basu ce kin kai su yyi ba, da sauri tace "eh
bai
shigo ba" inna ta galla mata harara tace
"munafukan bnxa kawae amma ca kuka yi
min ya
shigo da na tambayeku," intisaar tace "uhm
ae
xainab ce bni bace" nafisa tace jeki kawae
abinki,
kika san ko yy masu gargadi akan kar su ce
bai
shigo ba, bala'i inna ta dinga yi tana cewa
"wllh
yaron nan mugun shaidani ne, amma xai ci
ubansa bari na koma gida dae" intisaar ta
fice.
The end of book one.
INTEESAR BOOK 2
Intisaar ta xaro ido a tsorace tace "nashigauku, wllh bn san...." buga mata baki yyi dakarfi sannan ya tura ta fuskarsa a murtuke
yace "wat do yhu fink yhure tryn 2 do?
Seducin me or wat?" da sauri ta juya ta bar
palon tayi hanyar dakin momy da gudunta,
yyi ajiyar xuciya sannan ya buga tsaki ya
nemi kujera ya xauna. Maryam ta shigo tace
"lah, ya Haidar kai ne a gidan namu yau" yyi
murmushi yace "yea kanwata, ykk?" ta
xauna gefensa tana dariya tace fyn uncle ya
aiki?" yace "alhmdllh, momy fa?" ta yi hanyar
bedroom din tana cewa bari na kirata " ko
da ta isa dakin momy na rubuce rubucenta
ne, tace "momy uncle haidar fa ya xo?"
momyn ta watsa mata harara tace to uban
me xan masa?" maryam tayi murmushi tace
"yana dae palo fa shi daya" momy tace
"manta dashi kawae" maryam tace "intisaar
fa?" momy tace "ta shiga wanka," maryam
ta koma palon tana murmushi tace"uncle
gata nan xuwa," yace"yauwa kanwata ya
karatu?" tace"muna tayi uncle," sannan tayi
hanyar fridge ta dauko masa ruwada lemo
ta dire masa a gabansa yana mata gdya."
nan ta xauna suka dinga hira amma momy
taki fitowa, ya dube maryam din da ita ma
bata ji ddin yanda uwartata tayi ba yace
"wae halan fushi momy take yi dani ne?"
maryam tayi yake tace "ina ga dae wani
abun take yi amma tana xuwa," yamike yana
murmushi yace "bari dae naje ciki na
sameta nasan fushi ake yi dani," har
bedroom dinta yyi sallama ya shiga, can ciki
ciki ta amsa masa ya yi dariya ya nemi gu ya
xauna yana cewa "dama ashe uwa na fushi
dadanta," ta galla masa harara tace"kaji
dashi dae" yyi dariya yace "toam srry mum,"
kun shigo Nigeria lfya? Wllh ayyuka ne suka
sha gabana," ta tabe baki tace "gskya ne
mara mutunci kawae" don tasan ba don
Allah yaxo gidan nata ba kila Abba ne yyi
masa tatas shine ya kamo hanyar gidanta
yau, don inna bakinta ba shiru xai yi ba,
dariya kawae yake yi yana bata hkuri har
daga karshe ta dan sake, suna hira intisaar
ta fito daga bathroom sanye da hijab ta fice
daga dakin xata wuce dakin maryam ta
kimtsa, momy ta kira ta tace "kin gaida
yayan naki ne,? Tayi yake tace hnkli na ne
baya wajen, "ina kwana yaya?" ya daga kai
yana mata wani irin kallo, sannan yace"lfya,"
ita kuma ta fice da saurinta.Karfe daya Aliyu
ya wuce masallaci xae yi sllh, nafisa tayi tayi
dashi yaci abinci amma yaki wae ya koshi,
tace "to yyi kyau ae"yyi yar dariya yace "to
ku ajiye min idn na fito masallaci xan xo
naci sae na wuce gida," tace "um um fa
Aliyu," yace "serious anty xan dawo wllh"
tace "to sae ka dawo," har gate maryam ta
rakasa suna ta hira cikin raha, intisaar kam
tunda tashiga dakin maryam dama bata fito
ba, tayi mamakin yanda Aliyu kewa maryam
dariya, ashe dae yana dariya hka, a bakin
gate ya hadu da kannin maryam din sun
dawo daga makarnta suka rungumesa suna
murnar xuwansa yace su shiga ciki anjima
xae dawo idan yyi sllh. Bae shigo gidan ba
sae wajajen karfe uku har momy ta fidda rai
da xuwan nasa sae gashi, tace "ca nake
halin naka kayi min ae" yyi dariya yace "to
ina abincin sauri nake yi" nafisa tace au a
dole ma xaka ci abincin knan?" yace "hva de
wane ni" a dae kawo min abincin, momy ta
kira intisaar ta xo ta kawo masa abinci,
gabanta na faduwa ta dire masa abincin a
gaba, momy ta mata umarni da ta xuba
masa a plate, jikinta na bari ta shiga
budekulolin, muryarsa taji yana cewa"no ta
barshi kawae anty" ta mike da sauri ta bar
wajen ba tare da tabari sun hada ido ba.
Wajen karfe hudu da rabi yyi ma momy
sllma xai wuce bayan ya hada ko wani yaro
da dubu biyu a gidan, maryam kuma ya bata
dubu goma, momy tace to ita intisaar din
fa? Yyi yake yace "ta bari a gida xan bata
nata," momy tace"aa wllh ka bata a nan
kawae muna gani" ganin momy da gske
take ne yasa ya kirgo dubu biyar ya mika ma
shaheed ya bata, momy tace "aa ita ma
goman xaka bata wllh" anty duk wata fa ina
basu, ko sati biyu ba ayi ba ma da na basu a
can gida fa" momy tace "to shknan ka wuce
dasu tunda gida xaka, su ma gidan xasu
wuce yanxu," yace wa? Momy tace intisaar
din da maryam mana, ya kirkiro murmushin
dole yace "ae ba gida xani ba yanxu," eh ka
ajiyesu sae ka wuce inda xaka din," ya rasa
yanda xai yi ya ce aa, don hka kawae yace
mata to su sameni wajen mota a waje,
sannan ya fice bayan ya mata sllma yana
kokrin boye bacin ransa. Yana cikin motar
suka karaso wajen, intisaar duk jikinta yyi
sanyi.
.
Motar ya bude ya fito yana kallon intisaar
din ransa a hade, yyi mata wani irin kallo
yace"hope ba wannan motar kike
shirinshiga ba?" ta kauda kanta da sauri
gabanta na faduwa ta gyadamasa kai
sannan ta dau hnyr da xae kai ta babban titi
inda xata samu mota ta hau. Maryam tayi
sororo tana kallon Aliyu, yace shigo mu
wuce kanwata, ta hade rai tace "hva uncle
me yasa xakayi hka, ita din ba kanwarka
bace?" ya tabe baki yace "idan xaki ki shigo
mu wuce kawae" ta juya ranta a bace tace
"kaje kawae ni na fasa xuwa" yyi dariya ya
shige motarsa ya wuce. Maryam na shiga
gidan ta gyawa momynta abinda Aliyu yyi
ma intisaar, momyn tace "maxa bita ki kira
min ita," maryam ta fice da saurinta, amma
bata ga intisaar ba, ta dawo ta gyawa
uwartata, kiranta momy tayi a waya, bugu
uku ta dauka tace ita tama kusan gida,
momy tace to idan kin saukaxan kiraki
intisaar kiyi hkuri ki kyaleni da dashi, bake
yyi wa ba ni yyi ma, intisaar tayi murmushi
tace ba komai momy, amma ae maryam din
xata xo ko? Momy tace "aa ita ma ta fasa
xuwan saesati mai xuwa," intisaar bata ji
ddin hkn ba amma kawae tace "tomomy
ngd sae anjima. Intisaar naxaune a bakin
kofar palonsu ita da xainab dake fere wa
momy doya dan shi xata girka da rana da
yake kowa girkinsa yake yi daban da rana
har ma da safe, sae dae idan kayi ka kai ma
inna, na dare ne kawae akeyi gaba daya,
intisaar ta ajiye nail cutter din dke hannunta
tana kallon xainab din tace "ki bni na karasa
mana, ko ku baxa kuyi girki bane yau?"
xainab ta tabe baki tace"ohon masu ni dae
doya xanci" intisaar tayi dariya tace "ni dae
nasan da biyu kike fere doyar nan" momy ce
ta fito daga palo ta karbe kayanta tace "ku
tashi ku bni waje ni don Allah, awa nawa xa
ayi ana fere doyan nan" takun da suka ji ne
yasa gaba daya sukajuya suna kallon wanda
ke xuwa, Aliyu ne yana tafe yana danna
wayrsa, gaban intisaar ya fadi to me yaxo yi
a sashinsu, xainab ma sae da taji tsoro
sosae, to me sukayi kuma, momy kuwa cin
gaba da aikinta kawae tayi, ya karaso wajen
yana kallonsu da daddaya da daddaya, daga
xainabdin har intisaar baki na karkarwa
suka gaida shi, yau kam suit ne a jikinsa yyi
kyau sosai, ko daga inayke oho, bai ko
damu da gaisuwarsu ba ya dubi intisaar
fuskarsa a tamke yace "wae da jira kke naxo
na sameki kafin ki bni kudina ne?" intisaar
ta firfito da ido tace "ni?" ya daka mata
tsawa yana cewa "yhu re vry stupid,
tambayata kike yi ko waye?" a tsorace tace
"Allah ni bngne abinda kke nufi ba...." ya
gallamata wani mugun harara yace"fito min
da dubu biyar dina" ta xaro ido tace "lah ni
na mnta wllh kayi hkuri" sannan ta mike da
sauri ta shiga ciki, sae gata ta fito dasu, ta
mika masa ya fixge ya kirga sannan yyi
gaba. Xainab tace "an shiga uku," momy dae
bata ko kallesu ba ta dauki doyarta tayi
hanyar kicin, intisaar tace "uhmm ni har na
manta ma wllh" xainab tace "amma yaya
Aliyu bai yi ba a lyf wllh, Allah ma yaso baki
taba kudin ba" intisaar tayi dariya tace "me
xae kaini dama, ni wllh har ma na mnta da
kudin, tun fa ran sunday gashi yautuesday"
xainab ta tabe baki tace"Allah ya kyauta toh"
yauwa na mnta ban gya maki ba jiya faruuq
ya bni dubu biyu wllh, intisaar tace "Allah
sarki, ihsaan ma ya bata" ni kuma dubu
goma ya bni har ynxu ma yana wajen inna,
xainab tace "bawan ALLAH, shine ake
neman a maki tijara kan dubu biyar ynxu,"
suka kwashe da dariya gaba dayansu. Suna
sashin inna gaba dayansu yau amma bnda
khadija da rahma, intisaar na tsife ma
kursum gashi,xainab na kwance suna kallo
sukaji hayaniya a tsakar gidan, da sauri
suka fiffito har da inna dake binsu a baya
da gudu, fadila suka ga ya Aliyu ke duka da
belt yana ball da ita, ita kuwa bakinta bai
mutu ba yana dukanta tana xaginsa, hajiya
da umma na ta masa ihun ya rabu da ita,
inna ta karaso da gudu tana yarfe hannu
tace "an shiga uku, wae kai Aliyu wani irin
shaidani ne, ynxu me tayi mka kke neman
kasheta?" cikin xafin nama Aliyu ya kaita
kasa ya dinga xuba mata belt din tana ihu,
"ae wllh sae ta gya min gidan uban da take
xuwa yau, idan ba hka ba na rantse sae na
sumar da ita," "ayyo ynxu naji bayani, ae
fadila ana kiran sllhn farko take barin gidan
nan ba ita xata shigo gidan nan ba sae
karfe sha dayan dare," inna ta fadi tana
kallon su hajiya da kamar su shake ta, hva,
nan inna ta dinga xuga Aliyu ya dinga
dukanta kmr xae kasheta, ita kuwa bakin ta
yaki mutuwa sae xaginsa take tana ihu, inna
ta dauko wani katako da gudu ta kawo
masa tana cewa "muka mata wannan Aliyu,
wa yasani ma ko karuwanci take fita yi,
tsinannun iyayenta sun xuba mata ido,"
haisam ya shigo gidan, inna ta tsiri yi masa
bayani shima yasa kafa ya kwasheta ta xube
kasa hka suka dinga dukanta inna na xuga
su, kmr xasu kasheta, umma da hajiya ba
baki tunda inna na wjen sae matsar kwalla
suke, intisaar da su xainab duk jikinsu yyi
sanyi ganin yanda akayi ma fadila, xainab
tace "ae gwara suyi mata hka kila ta nutsu
wllh"
.
Momynta tashiga kwada ma kira tana bata
hkurin ta bude mata kofar tana kuka,ta juya
taga ya kusa iso inda take, tasa tafin
hannunta ta rufe fuskartata dinga ihu tana
bubbuga kafa tana cewa"wayyo kayi hkuri
ya Aliyu wllh tllh ni ina xuwa makaranta naje
kitso ne yau shi yasabnje ba yau, don Allah
ka rufa min asiri kar ka dokeni, ina
rokanka," kuka take yi sosae hannunta a
fuskarta tana tsalle-tsalle sae kace ihsaan.
Shiru bata ji an kamata ana duka ba, ganin
shirun yyi yawa ne yasa ta xamehannunta a
hnkli daga fuskarta jikinta na rawa, wayam
taga wajen ba kowa, ta fara waige-waige
tana gwalo ido amma bata ga kowa ba a
gun, a hnkli ta dinga kuka tana kallon kofar
palon nasu, takai hannu ta bude, taji shi a
rufe gam, jikinta a sanyaye tayi bangaren
inna tana goge hawayen fuskarta, xaune
taga Aliyun kan dakali kusa da wani flower
yana ta tuntsira dariya kmr mahaukaci,
haisam dake kan kujera yyi tagumi yana ta
kallonsa, gabanta yyi mugun faduwa xata
juya ta koma da sauri, haisam yace"intisaar
wa ya saki kuka?" tsit Aliyu yyi ya sha mur
kmr bashi ke dariya ba ynxu, ta girgixa kai
tace"ba kowa," sannan ta maxata bar
wajen. Xainab na xaune a palonsu intisaar
suna kallo intisaar na kwance, wayan
xainab yyi kara, ta daga,masifar da take tayi
ne yasa intisaar ta mike xaune tana ta
kallonta har ta gama ta kashe wayan,
intisaar ta tambayeta wanene,
cikinfushitace "wannan gantalallen da na ke
gya maki ne, tun ranar yake sintirin xuwa
gidan nan, nace ya rabu dani bana yi yaki
saurarana, wannan wani irin jaraba ce?"
intisaar ta tabe baki tace "ae duk hka suke
kmr mayu," sannan ta mike ta dauke cup
din da kanwarta tasha corn-flakes ta fita
dashi tana taya xainab mita. Tana fita tayi
hanyar gate, ta ko gansa a tsaye tayi
masaiso har wajen inna, tayi sallama inna ta
amsa daga can kuryar daki, ta shiga tana
cewa "inna bako kikayi," inna tace "hva don
Allah, daga ina? Gani nan xuwa" intisaar na
'yar dariya tace "saurayin xainab ne," inna ta
sake kabbara daga cikin dakin tana cewa
"gani nan xuwa, ya shigo don Allah,"
intisaar na dariya ta juya xata fita tayi masa
iso xuwa palon, suka hada iso da Aliyu dake
gefen kujera a xaune yana danna laptop,
wani mugun faduwar gaba ya xo mata, ita
bata ma gansa ba, wani irin kallo yyi mata
yana girgixa kafa, ya hade girar sama da ta
kasa,jikinta a sanyaye tace ma bakon ya
shigo, ya shigo yana gdya, ya mikawa Aliyu
hannu suka gaisa Aliyun ya dan saki
fuska,inna ta fito ta dinga wangale baki
tana masa sannu daxuwa, kusan duka
lemukanfridge dinta ta dire masa a gabansa
sannan ta xubo masa cin-cin da alkaki, tana
cewa "ci ka koshi yaro nan ma gidanku ne,
ae xainab jikata ce, ni na haifi ubanta, kmr
an baka ita an gama kaji ko," gdya ya dinga
yi shima yana murmushi, intisaar kuwa
dama tuni ta nemi lungu ta xauna tana
satan kallon Aliyun da shi din ma satar
kallon nata yake, suna hada ido ya galla
mata harara, ta mike jiki a sanyayexata bar
palon, inna dake ta faman xuba da
Abdurrahman, tace "aa ina xaki," takirkiro
murmushi tace "xainab din xan kira, inna
tace "yauwa maxa kije ki kira min ita yar
kwal uba, ashe dama tana da santalellan
yaro kyakkyawa hka taki gya min, maxa kira
min ita," ta fice da sauri tana yake, Aliyu ya
mike inna tace "ina xaka malam bayan kaga
munyi bako," ya kirkiro murmushi yana
kallon Abdul din yace "ina xuwa ynxun nan
ae xan dawo," sannan ya juya da saurinsa
ya fice, shit, ya fadi da karfi ganin har tayi
kwana, bae san ta fisa wayo ba, dama tasan
sae ya biyo ta don hka da gudun ta tayi
sashinsu, tana shiga palon nasu, xainab tace
"ina kika je ina kiranki tun daxu kixo ki ga
abu," intisaar ta tabe baki tace "kicin na tafi,
inna tana kiranki fa." xainab ta kalleta tace
"a ina kikaga inna?" tsakar gida tana neman
ki, intisaar ta fadi ba tare da ta kalle xainab
din ba, xainab ta mike tayi sashin innar,
intisaar ta dinga dariya bayan ta wuce, ita
ma ta rama abinda xainab din ta mata ranar
da faruuq ya fara xuwa gidan. A hanya taga
ya Aliyu ya watsa mata harara ta kauda kai
tare da xumburo baki tayi gaba da sauri, yyi
kwafa tare dacewa "xakuci ubanku gaba
daya ae, ke mai saurayin da me