INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   16 / 41

45K to 48K   out of 122.8K words

da gudu
bata lura da ruwan dake cikin bucket da
take mopping ba tayi ball dashi ya kife a
wajen tsantsi ya kwasheta tun kan ta kai ga
fadawa kan centre table din dake gabanta
don kansa ta ga take shirin fadawa ta fasa
wani ihu, cikin ikon Allah bata wani buge
ba, amma taci wahala ledar da Aliyu ya ajiye
kan table dinma sae da ya fadi kasa, duk
kayan dake ciki su ka xube cikin ruwan da
ya malale ta ko ina a falon, intisaar duk ta
rude ta mike da sauri tana rike da cikinta ta
haye sama har tana tuntube ta bude dakinta
ta shige.Tana shiga daki taji ya bude kofar
dakinsa ya fito, takoma gefen gadonta da
sauri gabanta na faduwa ta rakube ta dinga
yarfe hannayenta tana hawaye, xuciyarta
kmr xae shige cikinta don tsoro, yau kam
tasan tata ta kare in ta shiga hannun Aliyu,
tayi kusan minti goma a hka amma bata ga
Aliyu ya banko kofar dakinta ba don ita
jiransa kawae take ya xo yaci ubanta kafin
hankalinta ya kwanta, ta mike tsaye da kyar
jikinta na rawa, taji an bude kofa
downstairs snn aka rufe, tayi kusa da
window dinta da sauri ta dan bude curtain
din tana lekan compound din,
.
tafiyar nn tasa yake ta kasaita yana sanye da
shadda fara yyi mugun masa kyau, har ya
isa kusa da motarsa dake ajiye a garage
don bae fiye fita da ita ba kuma da alamar
shigowarsa gidanaka wanke motar, taga
wani mutumi ya mika masa makullin motar
a ladabe snn ya juya ya bar gidan, ya bude
motar ya shiga ya tada ta maigadi ya bude
masa gate ya fice ta bi motar da kallo cike
da mamaki anya kuwa Aliyu ne wnn, sae a
lkcn ta tuna ashe ma ranar jumma'ah ce,
don da safe kananan kaya ta ga a jikinsa da
ta leko ta window don indae taji fitansa
daga gidan to sae ta lekosa ta taga tun kan
ya shiga mota, jikinta a sanyaye ta sauko
downstairs, barnar da tayi yana nn yanda
yake sae dae ya kwashe ledan magunguna
da allurorinsa da suka xube cikin ruwan, ta
dauki mop ta fara share ruwan da ya malale
ko ina na falon, ba karamin gajiya tayi ba da
aikin falon don sae kusan karfe uku komai
na falon ya dawo dae dae, ta dauko turare
ta feshe a falon snn taje tayi wanka a sama.
Karfe biyar xainab ta kawo mata abinci tace
ba dde wa xatayi ba don sauri take amma
bari ta bata waya su gaisa da inna don
kullum cikin mita take an hanata xuwa
wajen jikokinta kuma an ki barin ta ta
kirasu su gaisa, intisaar ta karbi wayan da
murnarta suka gaisa da inna kmr xatayi
kuka wae kullum ta kira Aliyu ya bata sae
yace tana bacci, intisaar tayi yake tace eh
hka ne inna, sun dde suna hira da inna
daga bisani xainab ta kwace wayarta ganin
suna nema su cinye mata kati tace "ke ma ai
sae ki ce da mijinki ya siyo maki waya tunda
baki taho da taki na da ba," intisaar dae
bata tanka mataba sae murna take yau taji
muryar innarta, xainab tace "daxu fa ya
Aliyu ya xo gida," intisaar bata ce mata
komai ba hkn yasa ta mike tace kinga sae
da safe, intisaar tace Allah ya kai mu, gobe
kice ma inna dan wake xata min, xainab tayi
mata bnxa ta fice abinta
.
Ranar dae har tayi bacci bata ji shigowar
Aliyu ba, washegari asabar ma bata ji fitarsa
ba hkn yasa ta gane bae kwana gidan ba
knn, karfe biyar da rabi zainab ta kawo
mata abincindare, tuwon shinkafa ce da
miyar ganye sae farfesun kifi, intisaar ta
tabe baki tace "to ynxu ni canayi ma inna
ina cin kifi," xainab tace " iyye samun waje,
ba laifinki bne, kuma ni da kaina xan xuga
inna nace tunda kinyi sati kawae ki fara
girki," intisaar tayi dariya tace "ke kin isa ki
shiga tsakanina da innata, ae ta dinga kawo
min girki knn har sae nayi shekara," xainab
tace gskya ne matar yayanmu, snn ta hada
mata wani tsumi da inna ta bata ta kawo
mata tace "gashi nn inna tace ki sha wnn,"
intisaar ta yatsine fuska tace "na meye,"
xainab tace "yana sa mutum yyi fresh, yyi
kyau," ganin yanda xainab tayi serious
kuma taga har da madara ta xuba ciki yasa
intisaar ta yarda ta jawo ta fara sha, xainab
ta danyi murmushin intisaar wawiya ce, snn
ta bata turarrukan da inna ta bata takawo
mata kusan kala uku, tayi mata sllama tayi
gaba abinta. Karfe takwas intisaar ta gama
kallon tasharta ta Mbc bollywood ta kashe
kayan kallon snn ta kwashi kwanukan da ta
ci abinci tayi kitchen dasu xata wanke, ta
gama wanke wanken tana dan goge
kitchen din da ruwa taji shigowar motar
Aliyu, gabanta yyi mugun faduwa ta kife
kwanukan da ta wanke da sauri har tana
xubar da ruwa kitchen din don har wani
bari jikinta yake don tsoro, ta kashe tap ta
fito ta rufe kofar kitchen din ta haye sama
da gudunta ta shige daki ko me ya dawo da
shi da wuriyau don tasan ba lkcn
dawowarsa bne ynxu. Tana jiya bude
dakinsa ya shiga, ta kashe wutan dakinta
snn ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta
fara shafe shafenta gaban madubi, ta dauki
turaren da xainab ta kawo mata ta shafa
kamshin turaren yyi mugun tafiya da
imaninta, dama ga ta gwanar son kamshi, ta
lumshe idonta ta bude cike da jin ddi, ta
tsura ma kanta ido a madubi tana kallo, ta yi
murmushinta mai kyau snn ta mike ta dauki
wani kayan barcin ta pink colour mai
hannun singlet tsayin iya cinyarta sae
wando da shima da kadan ya wuce cinyar
ta saka, tana ji Aliyu ya bude kofar dakinsa
ya fito ya sauka downstairs, ta san coffee
kila xai je hadawa a kitchen,

shi ko yana shiga kitchen tsantsin ruwan da
ta xubar kan tiles ya kusan kwashe sa kasa,
yace "subhanallahi,"yyi stilla wajen baki
bude yana kare ma kitchen din kallo ransa
yyi mugun bacewa ya juya a fusace ya bar
kitchen din ya haye sama kmr wani zaki yyi
hanyar dakinta.Yana hawa sama yyi hanyar
dakinta a fusace ya sa kafa ya buga kofar
dakin da karfi, tun da aka kawo ta gidan
ranar ce rana ta farko da Aliyu ya shigo
dakinta, tana xaune gaban madubi tana
kokarin saka gashinta cikin net snn ta
kwanta, ta mike a raxane ta yo waje da ido
tare da dafe kirji muryarta na rawa tace " na
nashiga uku ya ya Aliyu," bai ko damu da
halin da ta shiga ba yyi kusa da ita yana huci
cikin tsawa yace "don uwarki karya ni kike
son yi a gidan nawa duk da fita harkarki da
nayi da xaki xubar min ruwa a kitchen kiyi
gaba," jikinta ya dau bari tana kallonsa,
daga shi sae three quatre ko singlet bbu, ta
fasa ihu ta haye kan gado a rude ta koma ta
daya side din har tana faduwa cikin kuka
tadinga cewa "wllh wllh wanke wanke nayi
ya Aliyu kayi hkuri don Allah," ko sauraranta
bai yi ba ya xaga yana kkrn cafketa, tana
ganin hka ta sake fasawani ihun " wayyo
nashiga uku xae kasheni, ya Aliyu don
darajar iyayenka kar ka dokeni wllh
baxansake ba," idan akwae abinda ya
fahimta game da intisaar bae wuce na
rashin son a taba lafiyarta ba, tana da
tsoran duka sosai tun tana karamarta, ganin
bbu inda xata bi ta gudu ne yasa ta dinga
tsalle tana ihun kar ya doketa don Allah, hkn
ya dada tunxurasa sosai ya karasa gabanta
ya fincikota da karfi fuskar nn tasa bbu
alamar rahamaya take mata kafa da tasa
kafar, wani raxanannen ihu ta saki tare da
kankamesa ta saka kanta kan yalwataccen
kirjinsa jikinta na rawa "kayi hkuri ya Aliyu
nace maka baxan sake shigar maka kitchen
ba daga yau" cak ya tsaya, yaji wani yarr tun
daga kansa har yatsan kafarsa, mutsu-
mutsu ta dinga yi a kirjin nasa tana kuka
hade da rokan kar ya doketa don Allah, ji yyi
kafarsa ta kasa daukarsa, ya shiga turata
daga jikinsa amma sae dada kankamesa
take da karfi,
.
jikinsa duk ya mace, cikin muryar da ba tasa
ba ya samu kansa da cemata "cikani," cikin
kuka tace "Aa wllh dukana xakayi, kayi min
rai ya Aliyu wllh baxan sake shigar maka
kitchen ba nace"numfashinsa ya dinga fita
da kyar snn ga wani mayen kamshi dake
neman xautar dashi ba gashinta ba ba
jikinta ba, bae san lkcn da ya saka fuskarshi
cikin gashin nata ba shima ya kankameta da
karfi har sae da tayi yar kara, to fa, nn ya
Aliyu yashiga sumbatarta ta ko ina kamr xae
cinyeta, a tsorace ta fara kkrin kwace kanta
ganin hkn tana cewa "meye hka ya Aliyu, na
shiga uku don Allah ka bari," cikin kuka
sosai kuma a gigice take masa magiyan,
maimakon Aliyu ya sake ta taga sai gaba
abin nasa yake dada yi, kokuwa ta shiga yi
dashi da karfinta tana cewa "wllh xan cije
ka idan baka sakeni ba, wayyoo momyna na
shiga uku, ka rufa min asiri ya Aliyu, wllh
xan maka ihu," bata ankara ba taji ya ja ta
sun xube kan gado, duk ya gama fita
hayyacinsa, duka ta shiga kai masa da cizo
da sauran karfinta don duk jikinta ya mace
itama, wani gigitattcen mari ya kai mata
hade da danneta da karfi snn ya soma
rabata da kayan jikinta, ganin da gske yake
yasa ta dinga ihu tana kiran duk sunan da
yaxo bakinta tana kokuwa dashi, amma duk
a bnxa dn karfinsu ba daya ba,
.
wannan dare kam intisaar baxa ta taba
mance shi a rayuwarta ba don kaca-kaca
Aliyu yyi mata tana ji tana gani, tun dagakan
gado har suka sauko kasa, tai ihun tai ihun
har ya kai ga muryarta ya daina fita, tai kuka
tai kuka har ya kai ga bata iya kukan, tayi
rokan har ta rasa wani iri kuma xata yi, Aliyu
bai bar ta ba sai da yagata daina motsi, ya
jima gefenta a kwance snn ya mike da kyar
don shima ta bashi wahala sosai, wajen
karfe biyu ya bar dakin ba tare da ya bi ta
kanta ba duk da yasan suma tayi, yana
komawa dakinsa ya shige bathroom yyi
wanka duk jikinsa bakwari snn ya kwanta
ya ja bargo duk da yasan ba barcin xa yi ba.
.
Sanyin tiles hade da na A.C snn da sanyin
ruwan da aka tsula daren ranar suka taru
suka farfado da Intisaar, tayi kkrin jawo
rigarta ta rufe jikinta amma ta kasa daga
hannun, bata sake yunkurin yin komai ba
sae hawaye mai xafi da ya dinga saukowa
bisa kuncinta, Aliyu ya cuceta, ya walakanta
ta, yyi raping dinta, wayyo Allahnta, kuka ta
dinga yi sosae da dashashen muryarta da
ko fita baya yyi, sbda cikin sanyin da ta
kwana, tana ji aka yi sllhn Asuba amma ta
kasa ko motsi daga inda take, duk jikinta yyi
tsami sosai snn ya mata nauyi, ta kara
yunkurin tashi amma ta kasa, ga wani
rawan sanyi da take yi, kuka sosae ta saki
tana kiran Allah a xuciyarta, kofar dakinta
taji an tura a hankali, gabanta yyi mugun
faduwa, ya karaso kusa da ita ya durkusa,
karkarwa ta shiga yi cikin dashashiyar
muryarta take rokansa "ka rufamin asiri ya
Aliyu, kasheni xakayi, don Allah don annabi
don....." ganin ya dago ta ne yasa ta kwala
ihu a tsorace har sae da muryarta ta fito
don axaba, daukarta yyi ya daura kan gado,
hade da rufe mata bakicikin sanyin murya
yace "bbu abinda xan maki, amma kar ki
sake min ihu," kai kadae ta gyada masa
jikinta na rawa tana hawaye, ya mike ya
shiga bathroom ya samu ruwa a heater ya
hada mata ruwan xafi ya saka dettol sosae,
ya maida wani ruwan a heater snn ya fito,
tana nn yanda ya barta, kuka kam yinsa take
kmr ranta xae fita, daukarta yyi ya shiga
bathroom din ya saka ta cikin ruwan, ta fasa
masa ihu "wayyo nashiga uku wllh da kwae
xafi sosae yaya," cikin kuka take masa
maganan sakamakon wani axababben
radadi da taji bayan ya saka ta cikin ruwan,
ya riketa ganin tana neman tashi yace"xae
daina maki xafin rufe idonki," ba shiri ta
kulle idon tana kuka, ruwan ya dinga ratsa
ta, ya daura kanta bisa kafadarsa, sai da ya
tabbatar ya gasa ta sosai, kuka kam tayi shi
har ta gode Allah, don ita tun da take bata
taba wahala hka ba, ya dauko tooth paste
da tooth brush ya taimaka mata ta wanke
baki, da kansa ya wanketa, snn ya taimaka
mata tayi wankan tsarki ya nannadeta a
towel ya fito da ita,
jikinta ya dau xafi matuka, ya kwantar da ita
bayan ya cire xanin gadon ya sa bargo ya
lullubeta ganin yanda take rawan sanyi, sae
da ya fara moppin din kasan tiles din dakin,
snn ya dawo gefenta yana kallonta ya ga
bacci take, hkn yasa ya dauki makullin
motarsa ya fita siyo magani da allurori don
bae da komai a gidan. Bayan kmr minti
ashirin ya shigo gidan, sae da ya fara shiga
kitchen ya hado mata tea snn ya hau sama
ya shiga dakin wajen karfe bakwae da rabi,
ya dago ta yace "ta shi ki sha tea fateema,"
da kyar take numfashi, jikinta kmr wuta, ya
shiga lallabata ta sha tea taki, ita kam kukan
bakin ciki take kawae, yyi lallashin amma a
bnxa hkn yasa ya rungumeta yana cewa
"bna son kukan nn fateema," lamo tayi a
jikinsa tana ajiyar xuciya cike da tsanarsa,
kofar dakin da aka murda yasa ya dago da
sauri, ita ko ta fara kkrin kwace kanta daga
rungumar da yyi mata don tasan xainab ce,
da sllmarta ta shigo dakin tana cewa "wllh
yarinyar nn kina ma yayana abinda kika ga
dama a gidan nn, kamshin dettol har waje
don ba ke kike siya ba ko," turus tayi a
bakin kofar ganin yayan nata rungume da
intisaar.Zainab ta juya xata bar dakin, Aliyu
ya kirata da sauri, ta juyo ba tare da ta
kallesu ba tace "ina kwana yaya," yace "lfya
lau daga ina hka," tace"emm dama inna ce
ta ce na kawo ma intisaar abincin break," ya
gyada mata kai yace "cum in," ta karaso
cikin dakin kanta a kasa ta durkushe
gabansu ta ajiye basket da flask din dake
hannunta,yace "meye a nn," tace " kunu ne
da wainar shinkafada miyar taushe, sae
dambu da kosae," yyi murmushin da bae
shirya yi ba yace "yyi kyau, je dauko plate ki
dibar mata wainar," tace "to" snn ta mike ta
bar dakin, ya dago intisaar yana kallonta
yace "me xaki ci fateema," ta kauda kanta da
sauri, ta fara kkrin mikewa duk da yanda
take jin jikinta kmr ba nata ba, ya rikota
yace "ina xa ki," ta kwace hannunta snn ta
mike tsaye, lkci guda ta fasa ihu tare da
durkushewa kasa, sakamakon wani
axababben xafi da taji a kasanta, ta kife
kanta kan tiles, ya durkusa gabanta ya dago
ta yace "menene,"bata ce komai ba sae
hawayen dake xuba a idonta, ya dagota ya
maido kan gadon, xainab ta shigo ta
yiabinda yace mata snn tace xata tafi, yace
"ok gyara mata bedroom sae ki wanke
bathroom din tukunna,"tace masa to, ya
mike tsaye ya dauka intisaar din kmr wata
bby ya fita da ita daga dakin ya kaita
nasabedroom din ya xaunar da ita kan
gado, da kyar ya lallabata ta dan ci abincin
da kunu, snn ya bata magani yyi mata allura
shima da kyar, bbu abinda take yi sae aikin
kuka, ya kwantar da ita tare da lullubeta nn
da nn bacci ya dauketa, yana kwance kan
kujera yana danna wayarsa xainab tayi
sllma yace ta shigo, ta shigo tace yaya dama
na gama ne xan tafi, yace mata ok snn ya
bata dubu daya tayi kudin mota ta amsa
tare da gdya ta fita,
.
lallai xa ayi ruwan sama da kankara yau,
wae ya Aliyu ne har da bata kudi ta hau
mota," tayi dariya sosae bayan ta fita, lallai
intisaar ta gama mata da yaya jiya. Yinin
ranar Aliyu bae fita ba yana gefen intisaar,
duk wani motsi da xata yi a kan idonsa,
dukda xxabin ya bar jikinta amma ta kasa
sukuni don sae juye juye take, yasan ciwo
ne ke cin ta, karfe biyar da wani abu ya fita
siyo mata chips ganin taki cin duk abincin
da xainab ta kawo mata (ko ya akayiyasan
intisaar na son chips oho ma Haiydar) yana
fita kuwa xainab ta shigo gidan da abincin
dare, ta kasa shiga dakunan ganin level ya
canxa a gidan, hkn yasa ta dinga rafka sllma
amma shiru, ta sauka kasa ta samu maigadi
ta tambayesa ko mutanen gidan na ciki,
yace oga dae ya fita daxun nn, ta koma cikin
gidan tayi hanyar dakin intisaar ta bude a
hnkli bata ga kowa a ciki ba, hkn yasa tayi
hnyar dakin yayan nata, xaune taga intisaar
kan gado, ta kife kanta bisa gwiwwowinta,
ta karasa dakin ta xauna gefen gadon tana
kallonta, a hnkli intisaar ta dago kai tana
kallon xainab din da idonta da ya gama
rinewa alamar ta ci kuka, xainab ta girgixa
mata kai ganin kukan take son fashewa da
kuma ta rungumeta, ta ko fashe da kukan
sosae cikin shassheka tace "xainab ya Aliyu
mugune, ya cuceni,ya..." da sauri xainab ta
rufe mata baki tace "sshii.. Ya isa hka, wnn
sirrinki ne tsakaninki da mijinki," kuka
sosae intisaar ta dinga yi xainab na
lallashinta, suka ji an bude kofar Aliyu ya
shigo dakin "wat," ya daka ma xainab tsawa
yace "uban me ya kawo ki nn kuma," ta
mike tsaye da sauri, ya daka mata tsawa ba
da ke nke ba, ta xunburo baki tace "abincin
dare na kawo maku," ya nuna mata kofa
"xoki fita,"
.
tayi hnyr kofar ba tare da ta kallesa ba tace
inna tace ta fara girki daga gobe," yace"taji,"
snn xainab ta fice.. Cikin kwanaki biyun nn
intisaar ta sami kulawa a wajen Aliyu sosae,
don ynxu kam jikinta yyi sauki sosai, kuma
duk wnn abinda yake mata baya bari su
hada ido, ita kuwa dari dari take dashi don
bata yrda Aliyun da ta sani bne wnn ga
wani mugun tsanarsa da take ji a xuciyarta,
sae dae kuma har lkcn bata iya takawa, yyi
yyi ta bari ya dubata amma kememe taki,
hkn yasa ya kira wata Dr Maryam warce
suka yi karatu tare ta xo dubata, ya fita ya
bar masu dakin, ita ma dae da kyar intisaar
ta yarda ta dubatan. Bayan kmrminti talatin
ta fito tana ma Aliyun wani irin kallo, yyi
murmushi yace "ya akayi Dr," ta girgixa kai
tace"amma wllh ka bn mamaki Dr, kai da
kanka, kai da xaku dinga ba wasu
shawarwari shine..." yyi dariya ya katse ta
da sauri "gskya ne maryam, but tel me d
truth don Allah, is it dat critical" ta galla
masa harara tace "wnn kuma ya rage naka,
though it's nt, idan na fita ynxu xan turo
maid dita da drugs da injections da
prescription dinsu sae ka mata, snn kadinga
sa tana shiga ruwan xafi da dettol sosae, i
will b on my way," yace "ok, bill dina fa Dr,"
ta hararesa tace " ae ba kai nayi ma wa ba,
kanwata nayi ma, xan lekota xuwa jibi," yyi
dariya yace "to ngd maryam," ta tabe baki
tace "mugu kawae," snn ta fice, sunyi
soyayya sosae da maryam suna sch, kuma
lkci daya ya gujeta duk da irin son da take
masa, shi kuma yana da dalilinsa nayin hkn.
Ya haye sama ya shiga bedroom dinsa ya
xauna gefenta yana kallonta, tana kwance
idonta a lumsheduk da ba bacci take ba,
shima kuma yasan ba barcin take ba.
Cikin kwanaki ukun da intisaar tayi dakin
Aliyu ta sami kulawa sosae daga gareshi
don komai shi yake taimaka mata tayi, harta
abinci shi da kansa yake bata, duk da tana yi
tana dan noke masa, kullum da yamma sae
Dr maryam taxo dubata har dae ta warware
sosae tana iya yin komai da kanta, yana
ganin ta warke kuwa ya fita harkarta ya
daina tarairayarta kuma, snn yaki barin ta ta
bar dakin nasa, tsakaninta da shi sae dae ya
siyo mata abincin ya ajiye mata gabanta in
ta

16 / 41