INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   38 / 41

111K to 114K   out of 122.8K words

hawayenta, ganin ta fara cin
nasara yasa tace "to shknn Alhaji kila kai
kadae kasan dalilinka na rashin son gaya
mana, amma kayi hkuri ka barni naje na
dubota don Allah don Annabi," yyi shiru na
kusan minti biyar snn daga karshe yace "to
shkknn kya iya xuwa, suna india amma
ynxu hka," ta dafe kirji da alaman jimami
tace "ohh ni yar nn, wnn wace irin fitina ce
ga ciki" sae kuma ta fashe da kuka Abba
yace "ba kuka xakiyi ba, addua'a xakiyi
mata, amma bana son maganar nn ya fita
daga nn ki bar shi a cikin ki kawae har Allah
yasa ta samu lfya," Hajiya na share
hawayenta tace "to Alhaji in son samu ne ko
xuwa jibi na tafi tunda ina da visa," yace "to
shknn," ta mike tace "Allah ya shigemana
gaba" snn ta fita daga falon Abba xuciyarta
fal murnar xata je ta dawo da danta.
Vidyasagar institute of mental health and
neuro sciences, shine asibitin da su Aliyu
suka sauka a new delhi, babban asibitin
mahaukata ne na india, kuma basu samu
wata matsala ba aka karbesu
.
Kwanansu hudu a asibitin Hajiya ta iso, ynxu
kam haukan inteesar da sauki tunda ta
daina buge buge sae dae kawae ta xauna ta
tsura ma abu ido tana kallo, da yamma
Hajiya ta shigo asibitin bbu wanda bae yi
mmkin ganinta ba barin Aliyu amma bae
nuna ba, kuka ta fashe masu da tana jijjiga
kai tace"ashe abinda ya samu inteesar knn,
bbu dae wanda ya tanka mata ita kuwa
inteesar dama bacci take, ganin sae fa tayi
da gske yasa ta kama hotel nn indian ynda
kowa xae saki jiki da ita yyi xaton jinya ta xo
ganin dari dar ake da ita, duk safiyya da
yamma take xuwa duba inteesar da kayan
fruit, Anty Nafeesa da Aliyu a asibitin suke
kwana wajenta, Faruuq da Haisam kuma
hotel suka kama, likitocin suka mayar da
hankali ssae a kanta sbda cikin da ke jikinta
don at an ytym xata iya haifesu, suna xaune
da yamma ranan Aliyu na bata abinci tana
karba, Faruuq na xaune yana kallonsu Anty
Nafeesa taje hutawa a hotel din da su
Haisam suke, Hajiya ta shigo rike da ledan
fruits dinta da lemo, ta xauna, Aliyu ya
gaisheta hka ma Faruuq, ta amsa tana
tambayar jikin Inteesar, ta mike ta dauko
kofi tayi waje kmr taje daurayewa ta bude
maganin da take yawo da kullum a bakin
xaninta ta xuba kadan, snn ta koma ciki ta
bude juice tacika kofin ta dauka ta mika ma
Aliyu tace "dubi yanda ka rame son, nasan
baka cin abinci yau ma bn ga alamar kasa
komai a cikinka ba ga lemo ka kora kaji
son," ya rufe abincin da yake ba inteesar
ganin takikarba kuma ya dagata sama yace
"ni naci abinci ae," snn ya ja ta suka sauka
xuwa kasa don yawanci a kasa suke wuni
gun pool ko flowers. Shi kansa Faruuq bae ji
ddin abinda Aliyu yyi ma uwartasa ba yace
"kawo ni na sha mum," da sauri tayi
murmushi tace "A'a bar shi kawae," faruuq
ma yyi murmushin jikinsa dae yyi sanyi ya
mike ya sauko ya samesu a kasa, bakacewa
hauka inteesar take ynxu duk ta nutsu ssae
sae in tayi wani abun ne wani lkci xaka
gane har lkcn haukan na jikinta, kusa da
ruwa ya samesu a xaune, faruuq ma ya
xauna yace"gskya she's respondin 2
treatment a nn Aliyu naga improvement,"
Aliyu ya dan yi shiru snn yace "hka ne, but
lkcn haihuwarta ya kusa faruuq a hkn xata
haihu bbu hankali tare da ita,"Faruuq yace
"muyi ta Addua frnd kila ma haihuwar ne
xae yi sanadiyar dawowa da hankalinta,"
Aliyu bae ce komai ba sae kallonta yake cike
da tausayi. Yau suka cika sati daya aIndia,
Hajiya kam ta rasa yanda xata yi Aliyu ya sha
maganin da su safeena suka bata, ynxu
xuwanta xae xamo a bnxa knn tayi, da
yamma ne misalin karfe hudu saura Aliyu na
xaune da inteesar kusa da babban pool din
dake cikin asibitin, ga mahaukata da suka
fara warkewa xaxxaune a wajen kowa nata
harkan gabansa, tun safe ya lura inteesar
bata jin ddi, yasan lkcn Haihuwarta ne ya
lura nakuda take duk da bata nuna tana jin
komai ba, shima duk hnkalinsa ya tashi
faruuq kadae ya gaya ma, faruuq ya fita siyo
abubuwan da ya kamata,Anty Nafeesa ta tafi
hutawa a hotel, Haisam jiya ya koma Nigeria,
Hajiya kuwa ta fita yawon xaga gari
xuciyarta fari tas don tana tunanin yau ce
xamansu ta karshe ita da Aliyu a indiadon ta
lura da abinda yake sha a asibitin wani lemu
ne kadae abincinsa ta xuba masa maganin
ciki snn ta bude fridge a ward din da
inteesar take ta ajiye masa hkn yasa taje
xaga garikafin ta tafi anjima idan taga ya
sha, xamowa inteesar tayi daga kan kujeran
da take ta xauna kasa ya lura duk axaban
ciwo ne kesawa tayi hka, shima ya dawo
kasan yana kallonta da damuwa yace "ina
ke maki ciwo fateema," bata ce komai bata
dauke kanta, suna nn xaune a hka har na
kusan minti sha biyar ya juya yana kallonta
yaga robon ruwan wasu mutane kawae
take kallo, ya kamo hannunta yace "xaki sha
ruwa ne inteesar" kai ta gyada masa ya
koma baya da mamaki yana kallonta, da
sauri ya mike yace "ina xuwa bari na kawo
maki kinji bata sake cewa komai ba yyi
hanyar stairs da sauri yana waiwayota
xuciyarsa na bugawa ya haura sama dauko
mata ruwa, tsam ta mike ta fara kalle kalle ta
bi hanyar da taga mutane na bi, da sauri
take tafiyar kmr ana turata, har ta isa gate
masu gadi suka bita da kallo don bbu
uniform din mahaukata jikinta, ta fice tayi
hanyr hagu duk da tafiya ce mai shegen
nisa tana ta tafiya har ta daina hango
asibitin, Aliyu ya sauko rike da ruwa da kofi
a hannu ya ga wajen wayam bbu fateema,
kalle kalle ya shiga yi a rude bae ga alamarta
ba, ya hango faruuq ya karasa gunsa da
sauri yace "fateema fa," faruuq yace "wace
fateemar ba nn na bar ku tare ba," ya dafa
faruuq ganin kafafuwansa sun kasa
daukansa yce "wlh nn na barta naje dauko
mta ruwa" cikin tsawa faruuq yce "wat?
Don me xaka barta ita kadae" tare suka
shiga xaga asibitin suna nemanta ta ko ina
amma basu gnta ba sune har gate duk Aliyu
ya birkice kmr wani xautattce, sae ga Anty
Nafeesa ta shigo asbitin rike da abinci da
mamaki ganin yanda suka tara jama'ah tace
"me ya faru" faruuq yy karfin halin cewa
"bamu ga fateema ba" kmr kar faruq ya fadi
hka sukaji Aliyu ya saki wata irin kara ae sae
da asibitin ya dauka sae kawae suka ga ya
sulale wajen.
Hajiya ta shigo asibitin rike da kayan
tsarabar da tayo ma yan Nigeria barin
safeena da uwarta tana dan rera wakarta,
jikin wani ward taga Nafeesa tsaye tana
kuka ssae ga wani likita da alamar dan
Nigeria ne yana lallashinta, da sauri ta
karasa kusa da ita tanakallonta tace "me ya
faru Nafeesa," da kyar Anty Nafeesa na
girgixa kai tace "bamu ga inteesar ba,"
Hajiya tayi shiru tana kkrin boye murnar ta,
can kmr warce ta tuna abu da sauri tace
"Aliyu fa," Anty Nafeesa ta kasa cewa komai
sae kuka, Hajiya ta juya a rude tana kallon
likitan dake gaban Anty Nafeesa tace "ina
da'na," da sauri ta bude ward din da
inteesar take mai xata gani, Aliyu yana
dambe dalikitocin dake kansa sae Fateema
yake kira, hajiya ta fito a guje tayi kan Anty
Nafeesa a rude tace "me ya samu Aliyuna,"
likitan ne ya bata amsa "suma yyiya farfado
a hka shima ana ga kmr ya samu matsala a
kwakwalwa," Hajiya ta fasa ihu tace"hauka
Aliyu yake yi hka," kuka ta fashe da a rude ta
ciro wayarta ta shiga danne danne tana
gunjin kukasae rawa hannunta yake ta kara
a kunne, "hello salame kina jina maxa ku je
ku karya asirin nn da kuka yi ma inteesar ya
koma kan dana wllh," ta katse kiran a rude
tana rusa kuka sae kallonta Anty Nafeesa
take da mamaki, cikin kuka tace "wlh
Nafeesa safeena ce da uwarta suka
haukatar da inteesar su suka haukatar da
ita suka gaya min," Anty Nafeesa ta dafe kirji
ta kasa cewa komai ta fashe da kuka tayi
waje, Hajiya ta bita ita ma tana kukan kmr
mahaukaciya, Faruuq ya shigo asibitin a jike
don anyi ruwa ssae, bbu inda bae xaga ba a
india amma bae ga inteesar ba, ynxu ma
daga gidan talabijin da redio yake, duk ya
xama kmr wni mara lfya, ganin inda su Anty
Nafeesa ke kuka yasa da kyar yace "Aliyu fa,"
cikin kuka Hajiya tace "wllh ya haukace
faruuq ku ceci rayuwar da'na ku nemo
inteesar, ina inteesar ta shiga don Allah a
nemota," ta fashe da wani matsanancin
kuka ta xube wajen, sae kallonsu ake
gwanin ban tausayi, faruuq ya dafa bango
ya kai minti kusan biyar a hka da kyar ya
haura sama ya shiga ward din da inteesar
take, duk alluran da suka dinga yi ma Aliyu
bae nutsu ba don hauka karara ya dinga
gwada masu, duk aka fita aka kulle dakin
aka barshi shi daya ya dinga buge buge
yana jijjiga kofar abun dae ba ddin ji,
likitocin suka hana faruuq shiga ya jingina
jikin bango hawaye ya cika idonsa da kyar
ya ciro wayarsa ya shiga neman layin
Haisam, muryarsa na rawa yace "Haisam
abu ya baci Haisam inteesarta fita daga
asibitin, Aliyu baya cikin hankalinsa shima
brain dinsa ta samu matsala, ka sanar da
Abba baxan iya gaya masa ba" bae jira me
Haisam xae ce ba ya katse wayar sae
hawaye. Inteesar kamnata tafiya abunta sae
dae idan taji kmr an mintsileta a mararta ta
xauna ta huta snn ta ci gabada tafiya ko ina
tabi sae an kalleta, hadari ya hadu garin
ssae tana ta tafiya abunta kowa nata kkrin
ganin ya isa gidansa, har daga karshe ruwa
mai karfi ya sauka ta xauna kan wani dakali
ruwan ya dinga dukanta amma bata damu
ba, har ruwan ya tsagaita bayan kmr awa
biyu, ta mike da kyar ta ci gaba da tafiya
tana rawan sanyi, kasa ci gaba datafiyar tayi
dae dae wai babban plaza ta dalilin wani
mugun ciwo da taji mararta da kugunta
nayi a tare da kyar ta ja kafa ta samu wani
gefen mota ta durkushe gaban plazan tana
rike da kugunta sae rawan sanyi take tana
yarfe hannu alamar axaba, indiawa sae
kallonta suke suna wuce ta, don su dama
basu gaji taimko ba ko a tsakaninsu, kuka ta
shiga yi ganin ta kasa daure ciwon Abbanta
ta shiga kira tana juye juye jikin motar da
take taji an bude motar ta koma baya da
sauri, da ganinsu matada miji ne, matar na
kallonta da yaran india tace "keme kike yi a
nn," kai ta daga tana kallonsu bakaken fata
ne kmr ita amma da gani xasu Haifeta, ta
mike da kyar tana rike da kugunta xata bar
wajen matar tace "amma ke yar Nigeria ce
kuma bahaushiya ko,"ko kallon matar bata
yi ba taku daya biyu ta xube wajen tana
wayyo cikinta, matar ta juya tana kallon
mijinta dake tsaye kmr wani tsoko yana
kallonsu tace "Abbanmu kalli fa yar uwar mu
ce ga kuma alamar bata da lfya mu taimaka
mata," bata jira me xae ce ba ta karasa kusa
da inteesar da sauri ta dago ta tana kallonta
tace "sannu kinji yan mata daga ina kike
hka," inteesar bata ce komai ba sae girgixa
kai da take don axaba, matar ta dagota da
sauri ta saka ta bayan mota ita ma ta shiga
tace"mu je Abbanmu," ya shiga motar ya
tada suka bar wajen, ihu ta dinga masu a
mota duk ta rikice jin axaba na neman
kasheta matar na rike da ita tana tofa mata
addua, mijin ma duk ya rude yace "asibiti
xamu ko," tace "A'a muje gida kawae xan
karbi haihuwar," babban gida ne ssae,
matar tace "ka taimaka min mu fito da ita
Abbanmu," ya xagayo yana kallon inteesar
da ta gama fita hayyacinta ciwo ya ci
karfinta, tace "help me mana Abbanmu," ya
koma baya da sauri har lkcn yana kallon
inteesaryace "baxan iya ba, bari na kira
maku yan aiki," yyi cikin gidan da sauri sae
gashi ya fito da yan aiki suka taimaka mata
ta shiga ciki da inteesar
.
.. Da taimakon matar Inteesar ta Haifo
santala santalan yaranta maxa biyu, ba
karamin wahala ta ci ba, matar ta tausaya
mata ssae, babban likitace don hka tayi
mata duk abinda ya kamata snn ta kaita
bedroom dinta ta kwantar da ita kan ta
hado mata tea har tayi baccin wahala, mai
gidanta kuwa kasa xaune yyi har sae da
inteesar ta haihu, snn hankalinsa ya kwanta,
matar ta gyara yaran ta kaisu gefen uwarsu
ta kwantar dasu gashi gaba dayansu basu
da lfya, inteesar bata farka ba sae can tsakar
dare matar na xaune gefenta rike da dayan
yaron dake ta kuka ta kwantar dashi tana
mata sannu, kai kawae inteesar ke gyada
mata, ta kira yan aiki su kawo mata tea,
suka kawo suka ajiye, matar tace maxa ki
sha ki basu nono yunwa suke ji kuma duk
basa jin ddi, inteesar bata ce komai ba
matar ta taimaka mata tamike xaune snn ta
mika mata tean ta shiga kurba a hankali,
maigidanta ya shigo ya xauna yana kallon
inteesar yace "sannu baiwar Allah ya jiki," ta
dago kai tayi shiru tana kallonsa, wata
yarinya ce da baxata wuce shekara goma
sha biyu ba ta bude kofar ta shigo ta karaso
kusa da inteesar da harshen hausa tace
"Sannu Anty," inteesar tayi murmushi tace
"na gode" yarinyar ta xauna tana kallon
bbies din, ba karamin kama suke da
inteesar ba iyayen sae kallonsu suke, daga
karshe Abbanmu ya mike ya bar dakin,
inteesar ta ajiye tean hannunta matar tace
"har ya isheki," ta gyada mata kai tace "na
koshi," matar tace "bari a kawo maki abinci
ki ci kinji," inteesar bata ce komai ba matar
ta mike ta fita, inteesar na kallon yarinyar
tace "ya sunanki," yarinyar tace "sunana
Zainab," inteesar tayi murmushi tace "nyc
name, wa ya kawo ni gidan nn,"yarinyar
tace "mum nd dad ne suka kawo ki daxu,"
inteesar tace "wani gari ne nn," yarinyar
tace"india," inteesar tayi shiru bata ce komai
ba gabantana faduwa ranta a dagule, india
kuma, me ya kawota india
.
. Ba karamintashin hankali kowa ya shiga ba
rashin ganin Inteesar har na kwana biyu,
barin ma Abba don shi ba ma ta Aliyu yake
ba, ta yar mutane yake, Hajiya dae ta dage
kowa ta gani tace su safeena ne suka yima
inteesar asiri ta haukace ita ma dae ta xama
kmr mahaukaciyar, idan ta gaji da gantalin
don bbu wanda ke kulata kowa abinda ke
damunsa yafi karfinsa sae ta dawo ta xauna
bakin kofar inda Aliyun yake tayi ta rusa ihu
tana kuka har aka fara tunanin ko ita ma
haukan xata yi ne, Aliyu kam ya xama abun
tausayi ba shi da aikin yi sae na kiran
fateema duk ya xama wani iri haukan nasa
ma sae yafi nata shi dae a bashi fateemar
shi, kullum sae an xubar masa da hawaye
don tausayi, gashi kullum su Faruuq sae sun
xaga india neman inteesar bayan sanarwar
da suka bada gidan talabijin da sauransu,
Bbu abinda yafi daga ma Abba hnkli irin
ynda xae tunkari momy yace basu
gainteesar ba ba a ma maganar inna da ta
dage xata xaman jego, hka kowa ya xama
kmr mara lfya a asibitin bbu me xama yaci
kwakkwaran abinci, inteesar kam na xaune
hankali kwance gidan bayin Allahn da suka
tsinceta ita da yaranta, sae dae fa yaran duk
basu da lfya kusan kullum allura ake masu
barin hassan din, duk da rashin lafiyar tasu
hkn bae hanasu ci ba kmr me, shegen ci ne
dasu ssae basa koshi ko kadan ko da
yaushe bakinsu motsi yake, suna mugun
takura inteesar gashi ruwan nonon ma bae
wani cika ba, hkn yasa matar tasa Abbanmu
ya siyo masu madaran jarirae take dama
masu ta basu, shknn inteesar ta samu
kwanciyar hankali, ko kadan ba ita take
rainonsu babarin ma ba iyawa tayi ba,
matar ce take masu komai nata kadae ta
basu nono, nonon ma ita ta koya mata
yanda xata dinga basu, kuma suna sha tana
ihu wae xafi take ji, ba karamin dariya take
ba matar ba, matar tace "amma ke yar fari
ce ko," ranarda suka cika kwana biyar ne
Abbanmu da matarsa da suke cema Anty
suka sa inteesar gaba suna tambayarta me
ya kawota india, inteesar tayi shiru ta rasa
me xata ce tunda ita ma ganinta kawae tayi
a india, a hankali ta fara magana "wllh Anty
nima bansani ba kawae na gan ni ne a nn
bn san wa ya kawo ni ba," duk suka yi shiru
suna kallonta da mamaki, Anty tace "a
Nigeria wani state kike to" inteesar tace
"kano," Anty tace "to mai gidanki fa?" tace
"shima a can yake," duk suka yi shiru suna
kallonta, Anty tace "kin tabbata gskya kike
fada mana inteesar," inteesar kmr xata yi
kuka tace"Allah gskya nake gaya maku
Anty," matar tace "to shknn bari ki kara
kwari sae mu kai ki gida," inteesar dae bata
ce komai ba, Abbanmu ya dauki Hussaini
yana kallonsa yace "wnn kmr Husainin
muko Antynmu," Anty tace "wllh kuwa baka
ganin ita ma inteesar kmr su kusan daya da
Zainab, Allah mai iko," duk suka yi dariya
Abbanmu yace "baki da nmbr kowa can
gida ne kada hankalinsu ya tashi dayawa,
koma dae kuna da yan uwa a nn india ne?"
inteesar tace "nima ban sani ba," Antynmu
tace "ka bari Abbanmu nn da sati daya ae
xamu je Nigerian,"Abbanmu yace "to shknn
Allah ya kai mu," snn ya mike ya fita, Anty ta
shiga hada masu madara don sun fara
mutsu mutsun yunwa, kmr ba jarirae ba
yaran, Antynmu tace "yaran nn dae da
yunwa kike barinsu suna cikin ki, yara da ci
hka tubarkallah," inteesar tayi murmushi
bata ce komai ba ta tsura ma yaran ido,
farare ne ssae kmr ita amma bbu abinda
suka bari na Aliyu, idonsu, bakinsu
hancinsukomai nasu na Aliyu ne, yaran kmr
yaran larabawa ga lips dinsu pink gwanin
sha'awa, tayi murmushi ta kauda kanta, ko
wani farin ciki xae yi idan yaga ya'yansa
masu kama dashi, Antyn mu ta dauki dayata
shiga bashi feeder ita ma ta dauki dayan ta
daukinasa ta fara basa don ta fara koyan
yanda ake yi gun Anty, Anty na da kirki ssae
tunda ta haihu a bedroom dinta take, kayan
da suka dinga siya ma jariran sae ka rantse
kace sun taba saninta, komai nasu enuf a
gidan suma autansu yan biyu ne masu
shekara takwas, kusan duk yamma sae
Zainab ta shigo da frnds dinta daban daban
wae su xo su ga Antyn ta mai kama da ita.
Inteesar taji kmr tayi ta xama a gidan don
tana jin ddin xama da su ssae. Abba na
xaune abun duniya ya ishesa Anty
Nafeesana gefensa ita ma ba um ba um um
sae uban tagumin da ta rafka, wayar Abba
tayi kara ya fito da shi yana kallon mai
kiransa, inna ce, ya kasa dagawa har sae da
ya kusan tsinkewa, kmr xata fasa masa
dodon kunne yaji tace "helo Bukar ne," yace
"eh nine baaba," "to wae wnn wani irin
tafiya ce kayi Bukar kasan da cewar wnn ne
watan Haihuwar inteesar har yau an rasa
wanda xae kai ni, tun yaushe kace na hada
kayana amma kayi min shiru to ni ynxu xan
sa kursum ta raka ni gidan, ynxu hka ma a
bakin gate nake wllh da jakata" Abbaya
girgixa kai ya rasa me xae ce mata, da sauri
ya samo abun cewan yace "kiyi hkuri baaba
gobe xan dawo sae nasa a kaiki, kuma su
dinma ae basa nn suna lgs," tace "yo ae can
din dama xani," Abba yace "to shknn baaba
ina nn dawowa gobe ki koma ciki," ya katse
kiran ya dafe kansa cikin tashin hankali yace
"ban san ya xanyi ba Nafeesa,"

..Karfe tara na safiyar lahadi inteesar suka
sauka kano daga lagos, Antynmu na rike da
Hussaini ita tana rike da Hassan kmr yanda
suke ce masu, Zainab na rike da wani yar
jakan kayan abincin yaran don da ita aka
taho aka bar yan biyu a india gun yan

38 / 41