INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   28 / 41

81K to 84K   out of 122.8K words

ya fita safeena
ta bi bayansa da sauri, durkusawa yyi
gabanta yana kallonta, ta fashe masa da
kuka abun tausayi ta xube jikinsa muryarta
na rawa tace "don Allah ya Aliyu ka kai ni
gida, ni wllh na gaji ko ina ciwo yake min
wayyoo mutuwa xanyi," ya rungumeta cike
da tausayi xae yi magana safeena tace
"dear," ya juya da sauri yana kallonta,
kallonsa kawae ta tsaya yi bata ce komai ba,
ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Inteesar
yace "ke kuma mahaukaciyar wace gari ce
xakiyi ma mutane amai a nn, idan kina jin
amai ba sae ki shiga bathroom din ki ba,
wnn ae kaxanta ce," Inteesar ta daga kanta
tana kallonsa, da kyar ta shiga kkrin mikewa
daga inda take wani aman ya taso mata ta
shiga kwarara sa a wajen, kuka ssae ta
fashe da ta jingina jikin bango tace "wayyoo
Abbana," kallonta kawae ya tsaya yi ya kasa
cewa komai, ta rarrafa ta shiga dakinta ta
xube kan tile tana mayar da numfashi,
safeena da sae kallon inteesar take da
mugun mamaki lkci daya jikinta yyi sanyi ta
ma rasa tunanin da xata yi, a xuciyarta tana
cewa amae kuma? to me hkn ke nufi, ta
sauke ajiyar xuciya tana kallon Aliyu tace
"me ke damunta????
.
Aliyu ya mike tsaye yana kallon safeena yace
"bata jin ddi ne," bae jira me xata ce ba ya
bude dakinsa ya shiga sae ga shi ya fito da
mop ya gyara wajen aman, safeena ta koma
daki da sauri hannunta na rawa ta shiga
kiran uwarta, tana dagawa tace "momy wlh
ina ga fa kmr cikine da yarinyar nn," uwar ta
mike daga xaunen da take da sauri tace
"mene? Ke wa ya gaya maki," a rude safeena
tace "gashi nn tana ta amai," uwar tayi salati
tace "bari xan kiraki," ta katse kiran. Da
daddare Inteesar na kwance kan tiles ya
shigo dakin ya durkusa gabanta yana
kallonta yace "tashi ki sha kunu na karbo
maki a gida," ta kasa dagowa ya dagota
yana kallonta ya kauda kansa da sauri, ya
kai mata kofin baki, ta kauda kai da sauri
muryarta na rawa tace "xafi," ya girgixa
mata kai yace "ba xafi," ta maido da kan
jikinta na rawa ta daura hannunta kan kofin
taji ba xafi ta kai bakinta yana rike da kofin
ya shiga bata, da sauri ta cire bakinta tace
"baxan yi amai ba? ya gyada mata kai ya ci
gaba da bata, yunwa take ji ssae don hka
rabi tasha ta koma tayi kwanciyarta kan
tiles, yace "kin koshi ne ta gyada masa kai
tace ruwa xan sha, yace "aa baxa ki sha ba,"
bata ce komai ba ya dago ta mayar kan
gadon duk abinda suke safeena na lekensu,
ta koma da sauri daki har da hawayenta ta
kira uwarta tace "kai ni momy wllh na gaji,
gashi can wajenta yana lallabata yana bata
koko," uwar tace "yi shiru safeena, daxun
nn na dawo daga wurin mutumin, ca yyi
wae duk abinda xa muyi masa a kantabaxae
taba tasiri ba sbda yana mugun son cikin nn
dake jikinta," safeena ta dafe kirji tace "ynxu
ciki ne da ita da gske ina xaune momy,"
uwar tace "ki tsaya ki saurareni mana,"
safeena na share hawaye tace "to ina ji
momy," uwar tace "yauwa, to ynxu ca yyi
dole sae an lalata cikin in har muna son
muga aiki yyi mugun tasiri a kansa, ynxun
ma ba wae bae yi tasiri bane, don xae dinga
lallaba ki kuma sae abinda kika ce masa xe
yi, sae dae fa hankalinsa gaba daya na
gunta sbda wnn shegen cikin, kuma fa baki
isa ki hanasa xuwa gunta ba amma, don
hka kawae ki kwantar da hankalinki jibi ki
xo mu koma kauyen yace yana jiranmu, ciki
kuma kmr ya bare ne," safeena ta share
hawayenta xuciyarta fal murna tace "to
ngdd momyna," ta katse kiran tana
murmushin mugunta. Da safe Aliyu ya bae
ma safeena i.v din bikin Zainab, ta tabe baki
tana hararansa tace "to ca nayi maka ban
sani bane," yyi shiru yana kallonta snn yyi
murmushi yace "to Allah ya baki hkuri
bbyna, amma ni dae ban san me nayi maki
ba kika canxa min kwana biyu," ya mike ya
karasa kusa da ita ya xauna yana shafa
gashinta yace "haba yan matana," ta
hararesa tare da buga masa hannu tace "ni
ka rabu dani," ya rungumeta yace "haba
bbyna," kmr xata yi kuka tace "to ba kai bne
ba baka ma damu dani da lamarina ba a
gidan ba," yace "inji wa yace maki hka,"
kakarin Aman inteesar yaji, ya saketa da
sauri ya mike tsaye ya fice daga dakin,
safeena ta bi sa da kallo xuciyarta na mugun
kuna, kasan dakin ya tarar da ita tana ta
amai ya kamata har ta gama snn ya gyara
mata jikin ya gyara dakin ya kwantar da ita
kan gado, ta rikesa muryarta na rawa tace
"sanyi nake ji yaya," ya lulluba mata bargo
snn ya dauki I.v din da ya ajiye gaban
madubinta xae fita ya juya yaga kallonsa
take, ya dawo yana kallonta yyi murmushi
yace "kina san wani abu ne," ta girgixa
masa kai yace "kinsan bikin Zainab saura
kwana goma ko," ta mike xaune da sauri
tace "da gske yaya, ni ba a gaya min ba to,"
ya kamo hannunta yace "ae sun san baki da
lfya, ki bari nxt wk sae mu tafi gidan kafin
nn jikinki ya kara kwari," ta marairaice kmr
xata yi kuka tace "to ba kila xuwa tayi ranan
ta gaya min ba ka koreta," yace "ba ta ji ne,"
tace "to yaya wa xata aura" yana kallonta
yace "faruuq," ta wara idonta ta fada kansa
cikin jin ddi tace "don Allah da gske yaya, kai
amma naji ddi wllh, ka bani nmbr ya faruuq
din" yace "to anjima xan baki, xanje gida
ynxu me xan ce inna ta girka maki?" tayi
shiru sae kuma ta bata rae ita da ba ma son
cikin take ba, yace kinyi shiru, tana
hararansa tace "kace mata ina da ciki ne," ya
daga hannayensa da sauri yace "A'a" yana
girgixa kai, ta koma ta kwanta tace "dan
wake nake so ni," yace "to, sae na dawo, kar
ki sha ruwa kar amai ya takuraki," bata ce
masa komai ba yayi hanyar kofa, duk wnn
abinda suke safeena na labe tana jinsu, tana
jin xae fito ta bar wajen da sauri ta shige
dakinta tana murmushin mugunta, yana
fitowa ya shiga dakin safeenar
.
Bayan kwana biyu safeena ta samu ta lallaba
Aliyu wae xata gun wata yar uwarta, ya ko
barta har da bata kudi da makullin mota
dayake ta iya drivin tana ta murna a
xuciyarta tana cewa lallai sae yanda tayi da
Aliyu, ynxu kam ta yrda yana tafin hannunta
amma dae ba duka ba, tunda bata isa ta
hanasa xuwa gun Inteesar ba, amma komai
ya kusan xuwa karshe, ta fada a fili tana
murmushi, cikin kwanakin nn Aliyu na da
aiki ssae a clinic don hka ya gwammace da
ya bar Inteesar kadae a gida gwara ya
dinga tafiya da ita don tana bukatar kulawa
ssae, hka ko ya dinga yi kullum shi xae
shiryata da safe yyi ma safeena sallama su
wuce asibiti, hkn yyi mugun tada ma
safeena hankali to ta ya xa'a yi ta aikata
abinda suka sha wahala kafin su samu
bayan baya barinta a gida., ita kam Inteesar
ko kadan abinda Aliyu ke mata baya burgeta
don dai dae da second daya bata son cikin
jikinta, kuma tasan sbda cikin yake mata
hka, wani mugun tashin hankali ke xuwa
mata idan ta tuna cikin Aliyu ne jikinta, Ana
saura kwana uku bikin Zainab ya kai ta gida
duk da ba a son ranta ba don bata son su
san tana da ciki, amma ashe duk ya gaya
masu uwarsa ce kadae be gaya ma ba sae
umma, inna duk ta rikice masa wae cutar
jikarta kawae yake gashi duk ta fige ba kyan
gani, shi dae bae tanka ma inna ba ya fice,
Inteesar dae na kwance falo sae mayar da
numfashi take don da kyar ta iya karasowa
cikin gidan bayan sun sauka daga mota,
kuma da asibiti ne baya barinta ta taka da
kanshi yake daukarta su shiga ciki, inna tace
"to wae wani irin jarababben cikine wnn
dake neman kashe min ke," ta mike xaune
tana hararan inna kmr xata yi kuka tace
"wae ni nace maki ciki gareni ne," bata jira
me inna xata ce ba ta shiga daki tayi
kwanciyarta, inna duk ta daga hankalinta
ganin irin laulayin da Inteesar take mai
tsanani, bbu wanda bae san ciki ne da ita
ba a gidan, ko da yaushe cikin amai da
kasala take, ko maganan kirki bata son yi
sae in Aliyu na yasa ta gaba ko yana
tambayarta me take so, duk tausayinta
kawae yake, Hajiya da hankalinta yyi mugun
tashi bata ga fuskar da xata ma Aliyu
magana ba da ya shigo da ya fice daga
gidan, tab aiko gwara ta nemo yanda xa ayi
da cikin nn, ynxu Aliyu dama sae ya iya
kwana daki daya da yarinyar nn duk cika
bakinsa, hka aka yi biki hankalin inna rabi
na gurin Inteesar rabi na gun bikin, duk aka
yi abubuwa masha Allah, amma inteesar na
kwance tana fama da kanta, safeena ma ta
xo ranar bikin tana daddaga hanci ita matar
Aliyu inna ta kunyatata gaban lodin jama'ar
biki su kursum dariya kmr xasu shide, ko
minti daya bata kara a gidan ba tayi gaba ba
shiri jikinta a sanyaye har ga Allah tsoran
tsohuwar nn take, ran Hajiya yyi mugun baci
amma bbu yanda ta iya da inna, washegarin
ranar da aka kai Amarya da daddare Aliyu ya
shigo falon inna bae ko kalli innar ba ya
durkusa gaban inteesar dake kwance
idonta biyu, ya daura hannu a goshinta yace
"amma yau bakiyi amai ba ko," a fusace inna
tace "kaji gantalalle wani irin bata yi amai
ba, ae hanjin cikinta ne kadae bae xaxxago
ba yau har tsorata nayi nace to ko su ne ke
shirin fitowa" Aliyu yyi mata mugun kallo
yace "to ke kuma wa ya somo bakin ki nn,
iyayi kawae," sae abun ya ba Inteesar dariya
ya dago ta yana kallonta yace "Abba na
neman mu, xaki iya ko na daukeki," ta
marairaice tace ynxu, ya gyada mata kai, ita
mugun kunyan Abba take ji har ma da
momynta, duk shigowar da momy take ta
gaisheta kar inna ta xaxxageta tace taki
xuwa, Inteesar yi take kmr tana bacci, inna
ta mike tsaye da sauri tace "bari kawae na
kama hannunta mu je," Aliyu ya bude baki
yana kallonta yace "wae meyasa kike son
shiga tsabgar da ba taki ba ne," bae jira me
xata ce ba ya harareta ya sa ma Inteesar
hijab dinta ya dauketa suka fice, inna tayi
kmr xata yi kuka tace "ni ban san meyasa
yaron nn ya rainani da tsufa na da furfurata
ba," a hanya ya ajiye ta dalilin rokansa da ta
dinga yi ya ajiyeta suka karaso falon yana
rike da hannunta, da kyar ta iya bude baki
ta gaishe da Abba kanta a kasa, ita kawae
kunyarsa take ji, yace "ya jikin fateema,"
kanta a kasa tace "da sauki Abba," yace "to
Allah ya sauwake, kina son komawa dakin ki
ne ko xaki xauna nn gun inna sbda
condition dinki" ta dago kai a hankali tana
kallon Aliyu, shima kansa a kasa yake, tayi
shiru ta rasa me xata ce don ita kam bata da
burin cikin nn ya kara girma a jikinta, Aliyu
yace "Abba da dae na tafi da ita xan fi kula
da ita a can kuma ba gida ma nake barinta
ba tare da ita nake xuwa clinic, nn ko xae yi
min nisa kuma xan takura kaina," Abba xae
yi magana inna ta fado falon, ashe tana labe
tana jin duk abinda suke cewa tana huci
kmr xata yi kuka tace "amma munafurcinka
dayawa yake Bukar, hka muka yi da kai? To
ni Rahmatu nace bbu inda yarinyar nn xata
je aje a kashe min ita da abinda ke cikinta a
banxa a hofi a barni da wayyo Allah, don
idan an kashe su ma ni nayi hasara ba ku
ba".
.. Aliyu ya dan yi tsaki ya kauda kai, Abba
kam shiru yyi yana ta kallon inna, ita ko ta
tsaya masu kmr soja a bakin kofa, can dae
Abba yace "to ki hada kayanki sae ki bi su,"
tayi kwafa tace "ko da naji," snn ta juya ta
fice da sauri, Abba ya girgixa kai yace "tashi
ka dau matarka ku tafi," Aliyu ya mike yana
kallon Inteesar, ita ma ta mike tsaye suka
ma Abba sallama snn suka fita, yana rike da
hannunta yace "mu je mu gaida momyn
ihsaan ne," tayi kmr bata ji sa ba shima bae
sake ce mata komai ba har suka fita ya bude
mata mota ta shiga shima ya xaga ya shiga
suka kama hanyar gida, ko da suka isa tayi
bacci ya fito da ita daga motar yana rike da
ita kmr bby, safeena na kwance falo ta bi su
da kallo ya sakar mata murmushi yace
"bbyna," tayi tsaki ta dauke kanta tacigaba
da kallonta, sae da ya kai Inteesar sama ya
kwantar da ita snn ya sauko ya sameta, ta
mike tayitsaki ta haura sama ta bar sa nn ya
bita da kallo snn yyi mmrshi yabi bayanta.
Washegari sae da safeena ta sa ya makara
xuwa office, wanka kawae yyi ya shirya ya
dauki makullin motarsa ta rakasa tanai
masa shagwaba ya manna mata kiss ya ja
motarsa ya bar gidan, ta sauke ajiyar
xuciyan jin ddiyau dae ya manta shegiyar
gaba daya, ta koma cikin gida murna fal
cikinta, tana shiga daki ta fito da kullin
maganin da aka basu su sa ma Inteesar a
ruwan sha ta tsura ma maganin ido tana
murmushi,dukiya fa knn a hannunta, ruwan
fridge ta kwashe gaba daya ta bar guda
biyu ta xuxxuba maganin cikisnn ta rufe
fridge din ta koma sama, ta lura kasa
Inteesar ke saukowa shan ruwa bbu ruwa a
dakinta kuma bata ga alamar an siyo ba,
tana ta kwance a daki tana jiran jin
saukowar Inteesar amma shiru, ita ko tana
kwance daki ta rasa inda xata sa ranta sae
juye juye take ga yunwar da take ji tun safe
ta gane Aliyu ya bar gidan hkn yasa ta daure
ta mike ta sa ma kofar ta key, kishin ruwa
duk yabi ya ishetagashi ba karfin sauka
kasa, da kyar ta rarrafa ta shiga bathroom
ta bude tap ta sha ruwa ta dawo tayi
kwanciyarta kan tiles. Washegari ma abinda
ya faru knn Aliyu bae shigo ya ga halin da
take ciki ba ya bar gidan da sassafe, duk da
jiya don ita ya dawoda wuri amma safeena
ta gusar masa da hankalinsa ya manta me
ya dawo da shi, ganin yunwa na neman yi
mata lahani yasa ta dinga daurewa tana
hada tea a nn dakinta da ruwan sanyita sha,
shima tana sha ta amayo, duk ta kara
xabgewa bata da aiki sae na kuka ita daya a
daki, wani lkcn sae taji kmr ta dauki waya ta
kira inna kawae sae ta fasa don bata ga
amfanin kiran ba don rabuwa kawae take
son yi da cikin, ita safeena bbu abinda yafi
daga mata hankali irin yanda taga ruwanta
na nn ajiye ba a taba ba, hkn yasa da
daddare da Aliyu ya dawo ranan tace "anya
kuwa kana shiga duba baiwar Allahn nn
dear, gashi ita bafitowa take ba, na kan
shiga na dubata wllh, amma ba ddewa nake
ba kar ace xan yi mata wani abun ne" Aliyu
ya mike da sauri kmr an tsikaresa yyi hanyar
stairs ta bude fridge ta dauka ruwan da
sauri ta bi sa tana cewa "gashi ka kai mata
ruwa naga kmr jiya ruwan dakinta ya kare
na fanfo take sha, ni kuma kar na kai mata
ta xata wani abun ne," ya karba ya haura
sama ya bude dakin ya shiga rabon da ya
ganta yau kwana uku tun ranar da
sukadawo daga gida, ya karaso gabanta ya
durkusa yana kallonta a hankali yace "ya
jikin fateema, kin daina aman," tayi tsaki ta
juya abinta, ya bude fridge dinta ya ajiye
mata ruwan yace "me xaki ci," tayi bnxa da
shi, yyi shiru yana kallonta, ta juya cikin kuka
tana kallonsa tace "wllh tllh idan baka cire
min wnn shegen cikin ba...." bae jira ya
karasa jin maganarta ba ya xuba mata mari,
"don uwarki kika sake min maganar cire
ciki sae nayi mugun saba maki kina ma da
hankali kuwa, to ki je ki cire tunda ke
mahaukaciya ce," ya mike a fusace ya fice
daga dakin ta bisa da kallo dafe da kuncinta.
Ranar bata yi bacci da daddare ba, kawae
Allah Allah take gari ya waye, gari na
wayewa ya shigo dakin kafin ya tafi aiki, tea
me kauri ya hada mata ya ajiye matagefenta,
snn ya dauko goran ruwan da safeena ta
basa jiya ya ajiye mata gefenta safeena ta
shigo dakin tana murmushi tayi ma Inteesar
ya jiki ko kallonta inteesar bata yi ba suka
fice tare da mijintata rakasa ya shiga mota
ya manna mata kiss snn yaja motar ya bar
gidan, safeena ta koma gidan xuciyarta fari
tasa ganin goran ruwan da ta ba Aliyukusa
da inteesar yau dae xa ayi ta ta kare, ta
shige dakinta tana dariya. Inteesar ta mike
tsaye ta dauki Hijab dinta ta saka, duk irin
wahalan da take sha ko sau daya wanka
bae taba wuce ta da safe ba dole sae ta
daure ta shiga tayi, ta fito tana ganin jiri mai
gadi ya tsaya xae mata maganar bnxa ta
fixgo gate din ta fice abinta ta barsa nn
tsaye, gidan Aneesah ta shiga, tana xaune
tana ba shakur Indomie, tana shigowa ta
kwanta kan kujera tana mayar da numfashi,
Aneesah tace "lah daga ina hka Inteesar
daxun nn nagama xancenki a xuciyata wllh"
Inteesar xata yi magana taji yawu bakin ta
mike da kyar taje bathroom ta xubar
Aneesah tace "A'aah kice oga yyi aiki"
.
Inteesar ta harare Aneesah snn tayi tsaki
tace "ni don Allah taimako naxo kiyi min
Aneesah," Aneesah tayi dariya tace "to
kawas ina jinki amma cikin nn na baki
wahala gskya, kinga yanda kika rame
kuwa," Inteesar ta dawo kasa kusa da ita
tace "don Allah don Annabi Aneesah kinsan
inda ake abortion?" Aneesah tayo waje da
ido da mamaki tana kallonta snn tace "kina
da hankali kuwa inteesar," inteesar ta
jinginar da kanta jikin kujera hawaye ya
cika idonta, Aneesah tace "kinyi shiru,"
inteesar ta share hawayen idonta tace "wllh
xubar da cikin nn xanyi kin dae ji na rantse
in ma xaki gaya min ki gaya min," Aneesah
ta gyada kai tace "to tashi ki fita a gidana, ni
bana hulda da maras tsoran Allah," inteesar
ta juya tana kallonta tayi shiru snn ta mike
tayi hanyar fita daga gidan, Aneesah ta bita
da sauri ta kamo hannunta tace "haba
inteesar bafa kiyi kama da jahila ba," kuka
inteesar ta fashe da tace "baxa ki gane ba
Aneesah wllh bana sonsa bana son cikinsa,
bae damu dani ba sae wahala nke ta sha,"
Aneesah ta xaunar da ita tana kallonta da
tausayi tace "ni na tabbatar maki kina haife
wnn cikin xaki ga tsantsan so gun mijinki,
ni banga rashin son da mijinki yake maki ba
inteesar nafa ga abinda yyi ma kishiyarki
ranar sbda ke, don me xaki walakanta
kyautar da Allah ya baki yar uwa," inteesar
tayi shiru tana ta sauraran Aneesah tana ta
wa'axinta da nasiha, har ta kai Aya snn
inteesar ta kirkiro murmushi tace "to ngdd
Aneesah, ta dauki shakur tana ta wasa da
shi yana mata dariya, tace "amma a gida
kika haife yaron nn ko Aneesah," Aneesah
tace "me kika gani," inteesar tayi yake tace
"aa kawae tambaya ce nayi don ni dae ina
tsoran Haihuwa," Aneesah tayi dariya tace
"A'a a asibiti na haifesa," inteesar tace "wani
asibitn?" Aneesah tace "A'a tender care na
haifesa, ai kin san asibitin bbu wani nisa,"
Inteesar tace "A'a" Aneesah ta gaya mata
inda asibitin yake kuma dama abnda kawae
take son ji knn, ta mike xuciyarta fal murna
ta bar gidan.
.
Inteesar na fita daga gidan Aneesah ta
koma gida cike da jin ddi ta shiga dakinta
tana haki kmr warce tayi gudu, ta

28 / 41