Author : Khaleesat Haidar Category : Romance
wanke mata baki ya
dauketa ya maidota cikin dakin ya kwantar
kan gado ya rufa mata bargo yana kallonta
sae rawan sanyi take, ya koma ya gyara
bathroom din, snn ya dawo gefenta ya
xauna yana kallonta duk ya ma rasa wani
tunani xae yi, ya jinginar da kansa jikin
bango a hankali ya lumshe idonsa "no! Wnn
me shegen rakin baxata iya rainon ciki ba
ynxu, nd bae tashi haihuwa da ita ba tukun,
da ma safeena ce wnn kam takuran da yake
samu a gida a kanta xae kara yawa ne ma,
to ma wani moranta yyi har xata dauki ciki
ynxu" yyi tsaki ya bude ido yana kallonta
bacci take amma da gani ba me ddi ba sae
juye juye take, ya girgixa kai ya mike ya fice
daga dakin, makullin motarsa ya dauka ya
sauko falo, safeena da ta fito daga kitchen
knn bayan ta kashe gas din da Inteesar ta
kunna tace "me ya sameta Dear," ya galla
mata harara yace "ban sani ba," ya fice, ta bi
sa da kallo, ita kam halin Aliyu ya isheta a
gidan nn, gashi sae bata kudinsu suke a
banxa a kansa, amma abu sae kara gaba
yake, tayi kwafa ta haura sama, yana shiga
motarsa ya kama hanyar asibiti, bae damu
da gaisuwan da nurses ke masa ba har ma
da patients ya haura sama kawae ya wuce
office dinsa, ya bude glass din da
magunguna suke ya shiga xaban wanda ya
kawosa, tabs kala biyu ya dauka da ruwan
allura daya ya rufe glass din ya fito ya rufe
office din, ya sauko kasa xuwa reception,
sae a snn ya shiga amsa gaisuwan patients
din da ke gaishesa, yyi murmushi ganin
matar da yyi ma theatre kwanakin baya da
yaranta da babansu, ya karasa kusa dasu
yana kallonsu yace "madam me ya sami
twins" matartace "wllh tari suke doctor, ya
aiki?," ya karbi dayan yana masa wasa yace
"aiki Alhmdllh anyi attend din maku ne," tace
"A'a ynxu dae xa a duba mu, madam fa," yyi
murmushi yace "tana lfya," tace "to a gaida
min ita, yau kana wkend ko," yace "wllh
kuwa, Allah ya sauwake, i wil b on my way,"
ya ba mijinta hannu suka yi sllma snn ya
juya, yana isa kofar fita sai da ya juya ya
sake kallon kyawawan yan biyun da suka
girma ssae, ya dauke kansa da sauri ya fice
ya shiga motarsa ya bar asibitin.
.
Aliyu na shiga gida ya tarda Safeena kwance
a falo tana kallo, ta bisa da kallo har ya
haura sama snn ta mike xaune tana
bubbuga kafa a hankali ta shiga maganar
xuci "lallai its high tym she wake up frm her
slumber, ya kamata ta tashi tsaye daga
xaunen da take ynxu, Aliyu ya gama kawota
bango, xata cire sonsa ta ajiye gefe guda
tayi abinda uwarta ta dde tana son tayi taki
yi sbda so ya rufe mata ido, ita kuma
inteesar ynxu suka sa kafar wando da ya da
ita" tayi murmushin mugunta ta mike ta
haura sama xuciyarta na tafarfasa. Aliyu na
shiga dakin ya tarda ta tana bacci ya xauna
gefenta yana kallonta ya ciro magunguna da
alluran da ya dauko a asibiti yana kallonsu,
snn ya juya yana kallonta tayi wani irin
haske ta kuma kara kyau, yyi murmushi ya
shafi gefen fuskarta ya mike ya dauko
syringe a dakinsa ya dawo ya shiga hada
alluran, sunansa yaji ta kira, ya juya da sauri
yana kallonta ta sake maimaitawa "ya Aliyu,"
sae kuma yaga tayi murmushi ta juya, ya
ajiye alluran hannunsa ya dawo dab da ita
ya xauna yana shafa labbanta da yatsa yace
"fateema," cikin baccin ta amsa "na'am," yyi
murmushi ya daura mata kiss a bakinta,
murmushin yaga ita ma tayi, yyi still yana
kallonta, to wae meyasa yake son xubar da
cikin nn, shi dae yana son yara kuma xae so
yaga kyakkyawan bbyn da xata haifa masa
mai kama da ita, ya dauke kansa ya daura
hannu a goshinsa kan na juya masa, y?
Meyasa yake son xubar da bbynsa gudan
jininsa, ya girgixa kai yace "No," da sauri
yaga ta mike xaune ya kamo ta ta fara
turasa xata sauka yaki sakinta yana
tambayarta mene, amai ta shiga kwarara
masa a jiki yana rike da ita har lkcn, sae da
ta gama snn ya dauketa ya shiga da ita bayi,
sae kuka take tana cewa ita ya kaita gida,
wanka yyi mata ya nannadeta cikin towel ya
fito da ita ya cire xanin gadon snn ya
kwantar da ita, shima wankan yyi don duk
ta bata masa jiki ya saka xanin gadon cikin
washn machine da shirt din jikinsa snn ya
fito daure da towel, ranar ce rana ta farko
da ta taba ganinsa daure da towel don ko
singlet Aliyu bae yrda ta gansa da shi bare
short nicker, ta rufe idonta da sauri, shima
bae ce mata komai ba ya kwashi
magunguna da alluran da ya hada ya fita da
su, dai dai lkcn da Safeena ta fito daga
dakinta, ta bi sa da kallon mmki shi kam ko
kallonta bae yi ba shiga dakinsa. Alluran da
yyi mata bayan ya tilasta ta sha tea ne ya
tsayar mata da aman, amma duk da hka sae
da ta gwammace dama aman ta dinga yi taji
ddi, don rasa inda xata sa ranta tayi sae
kuka take tana juye juye, ya rungumota cike
da tausayinta yana lallabata tayi bacci, da
kyar ta samu baccin ya dauketa, yyi shiru
yana kallonta duk ta rame lkci daya, da
yamma wajajen karfe biyar ya fita pharmacy
siyo mata magunguna da drips din da xae
sa mata.Yana fita ko minti goma ba ayi ba
Zainab ta shigo gidan ko kallon safeena
dake ta busar da gashinta da hand dryer
bata yi ba ta wuce sama, safeena ta bi ta da
kallo snn ta ja dogon tsaki, bacci ta tarar
Inteesar ke yi ta shiga tashinta da xolaya
tana cewa "ke kasa kinyi bakuwa maxa
tashi" inteesar ta shiga juye juye ta mike
xaune da kyar tana kallon Zainab, Zainab
tace "hmm lbri na xo maki da mai ban
kunya," inteesar xata yi magana taji yawu
cike bakinta, ta mike tsaye da kyar ta shiga
bayi ta xubar da yawun ta dauraye bakinta
da freshner ta dawo, Zainab tace "meye
hka," Inteesar ta langwabe da kyar tace
"bana jin ddi ne," Zainab ta bude baki "iyye
kar dae bby xa a samo mana," inteesar tayi
shiru da mamaki tana kallonta snn tace "bby
kuma, wani bby," Zainab tayi dariya tace
"lalala kinga yanda kka yi wani irin haske da
kyau kuwa, shknn xa a sama ma yayana
bby," inteesar ta hade rae xata yi magana
taji yawu kuma a bakinta ta mike da sauri
taje ta tofar wnn wani irin jaraba ce, ta
tambayi kanta, kuka ta fashe ma Zainab
ganin Zainab ta kuke sae murna take xa su
samu bby, tace "ni fa bana son hka Zainab
wllh bani da komai," Zainab tace "ki daina
wllh, ga signs a jikinki," kuka ssae take tana
cewa na shiga uku ni Zainab ki bari bani da
komai yarinya da ni xaki ce ina da ciki,
Zainab tayi dariya ssae tace "tunda ko kina
kwana daki daya da yayana ai ke ba yarinya
bace," dai dai nn Aliyu ya shigo yana ma
Zainab mugun kallo yace "ke wae wace irin
mutum ce, ban hanaki shigowa gidana ba,
xo ki fita," cikin daga murya ya karasa
maganar ta mike da sauri tana xumburo
baki ta dauki mayafinta ta bi ta gefensa ta
fice ya kai mata rankwashi, inteesar ta hade
kanta da gwiwa tana kuka, ynxu ciki ne da
ita yar yarinya da ita, to da wani ido ma xata
kalli su inna, ae Allah ma ya kyauta kuma ya
rabata da haihuwa ynxu kuma ma wae dan
Aliyu. Ta mike da sauri tun kan ya shigo
dakin xata yi hanyar bathroom jiri ya debeta
ya shigo dakin da sauri ya kamota ta fada
kansa suka xube kan gado, ya fada gefenta
da sauri ganin ynda take mayar da
numfashi ya dagota ya rungumeta yana
mata sannu, cikin kuka tace "wllh ka cire
min cikin nn bana so," ya toshe bakinta da
sauri yana kallon cikin idonta yace "ni ina
son abu na
.
Kuka ssae Inteesar ta shiga rera masa, shi
kam saekallonta yake yana murmushi, ta
fara kkrin mikewa xata sauka daga kan
gadon ya riketa da sauri yace "ina xaki,"
cikin kuka tace "wllh sae ka cire min cikin
nn bana so," ya rufe bakinta ya hade rae
yace "kar ki sake cewa na cire maki bbyna,
sae kace wani kaya," ta buge masa hannu,
ya harde kafarsa cikin nata tayi yar kara, ya
rungumota yana kallonta ya shiga shafa
mata cikinta yace "me xaki ci, dubi fa yanda
kika rame tun kan ba mu je ko ina ba, a hka
xa muyi rainon cikin kika san ma ko yan
biyu ne kanwata," ta fashe masa da kuka
tana kiran Abbanta, ya rankwashi kanta
yace "ki daina min kmr ihsaan a nn, ke baki
san kin girma ba tunda ga bby nn cikin cikin
ki" bata san lkcn da ita ma ta rama
rankwashin ba tana kukan da xa a iya
kiransa da na shagwaba duk da har ga Allah
ba shagwaba take ba, ya wara ido yana
kallonta, ta koma baya da sauri nn da nn ta
tsorata ya lakaci hancinta ya ja kunnenta
yace "kin ci sa a bbyna na jikinki da yau na
maki shegen bugu, ya Aliyu kike rankwashi
" bae jira me xata ce ba ya kwantar da itaya
mike ya fita, ta mike xaune da sauri ta hade
kanta da gwiwa ta fashe da wani sabon
kukan ynxu wae ciki ne da ita da gske yar
yarinya da ita, ba a dau lkci ba ya dawo
dakin rike da kofin tea yace "maxa tashi ki
sha na saka maki ruwa aman ya tsaya,"
kallon tean kawae tayi taji xuciyarta na tashi
ya kai mata baki ta mike da sauri sae cikin
bayi ta shiga kwarara amae, ya isa kusa da
ita ya durkusa ya dafata yana kallonta yana
mata sannu, sae da ta gama snn ya gyara
mata jiki ya maidota cikin dakin, a hankali ta
kamo hannunsa tana hawaye tace "don
Allah ya Aliyu ka tausayamin ka cire min
cikin nn bana so," ya galla mata harara yace
"wllh idan kika sake gaya min wnn maganar
sae na bata maki rae, ki cire ynxu na gani
mana," tayi shiru tana kallonsa xuciyarta na
tafarfasa, ita ko ta fi sa iskanci xae gani
kuwa, ta juya tayi kwanciyarta tana mayar
da numfashi, tean da bata sha ba knn har
bacci ya dauke, sae kusan sha daya na dare
ta farka yana gefenta a kwance, shima amai
ne ya farkar da ita, ya cire mata ruwan dake
hannunta ganin a gigice ta farka tana
neman sauka ya raka har bayin ta shiga
kwarara amae, gashi dae ba komai cikinta,
ya xuba mata ruwa a kai ya fito da ita, daga
ita har shi ranan basu yi baccin kirki ba,
jikinta yyi xafi ssae ta rasa inda xata sa
ranta sae kuka take masa yana rungume da
ita, da kyar bacci mai nauyi ya dauketa
kusan asuba. Washegari monday bae je aiki
ba sbda ita, tana kwance jikinsa bayan ya
lallabata ta sha tea kadan yyi mata
allurorinta wajen karfe goma safeena ta
kwankwasa kofar tare da sallama, yace ta
shigo, ta bude kofar ta shigo sae da
xuciyarta ya kusan harbawa yanayin da ta
gansu, shi singlet da 3qtre ne jikinsa, ita
kuma rigan bacci iya cinya, ta kirkiro
murmushi ganin allurori a bedside drawer
tace "Ayya bata jin ddi ne dear," ba tare da
ya kalleta ba yace "eh, ya akayi?" tace "Allah
sarki, Allah ya sauwake fateema sannu,"
inteesar ta dago kai da kyar ta watsa mata
harara, ta mayar da kanta, safeena ta dauke
kanta da saurixuciyarta na tafarfasa tace
"yauwa dear Momy ce ciwonta ya tashi
shine xanje ynxu, amma ba ddewa xanyi ba
dan da sauki," yace "ita kuma kullum ciwon
nata ke tashi, baku da abinci ne a gida, ae
yunwa ce ke kawo ulcer " tayi shiru tana
kallonsa ya tabe baki yace "Allah ya
sauwake, ki duba side drawer can bedroom
dina ki dauki dubu goma," tana murmushi
tace "to ngd dear," snn ta juya ta fice tana
murmushin mugunta. Da yamma safeena ta
shigo gidan, har lkcn Aliyu na dakin
Inteesar, lkci lkci yakan yi tunanin ko dae
kawae ya rabata da cikin nn ne ta huta
shima ya huta, don ba karamin wahala yaga
take sha ba tun kan cikin ya kai ko ina, ynxu
ma da kyar ta samu bacci ya dauke, irin
masu shegen laulayin nn ne me wahala, ya
dan yi tsaki, ita ma ragwancinta ne kawae
yyi yawa, duk ta fige lkci daya sai kace
wacce tayi wata tana ciwo, safeena ce ta
bude dakin ta shigo ya daga kai yana
kallonta, tayi murmushi tare da lumshe ido
tace "Aliyu so nake kaje duba mum dita
ynxu, kuma ka tafi mata da wnn maganin
nn da ka bata ranan nn wae taji ddinsa," yyi
shiru yana kallonta,snn taga ya sauke ajiyar
xuciya yace "wae ynxu?" ta dan yi fari da ido
murna fal cikinta, amma ta hade rae tace "to
da yaushe kke tunani," yace "ok," snn ya
kwantar da Inteesar dake jikinsa ya mike
tsaye ya juya yana kallonta bacci take, kan
yace komai safeena tayi saurin cewa "to
kaxo ka wuce," ya juya ya fice daga dakin, ta
bisa da kallo tana murmushi, dakinsa ya
shiga ya shirya snn ya fito da makullin mota,
tana hararansa tace "to haka xaka je mata
hannu rabbana," ya koma ciki sae gashi ya
fito da kudade, ta rakasa har jikin mota snn
ta manna masa kiss a baki, yyi murmushi ya
lumshe idonsa yace "sae na dawo bbyna,"
snn ya ja motar ya fice daga gidan, ta doka
uban tsalle tashiga kiran layin uwarta cikin
murna tace "wayyoo mum, saura naki gashi
nn xuwa.
Aliyu na fita gidan ya wuce wani babban
super market ya yayiwa mum din safeena
siyayya bata wasa ba akalla ya kashe kusan
50k. Ya fito ya shiga motarsa ya dau hanyar
gidan mum xuciarsa duk a cushe ya rasa
dalili,gashi yana son kiran inteesar a waya
ta wayar sa dake hannunsa amma ya kasa a
haka dai ya cigaba da driving har Allah ya
kai shi lpy. Yana isa gidan su safeenar
maigadi ya bude masa get yana washe baki
kasancewar aliyu na hannun damansa ne
yana da yawan kyau,ko kula da gaisuwar da
me gadi yake yi masa bai yi ba ya mika masa
2k aiko maigadi ya hau godia da kiraki
hannu kawai ya daga masa yai hanyar
parkin shade dinsu ya ajiye motarsa ya
duba seat din baya cikin magungunan daya
ajiyewa a a first aid box dinsa ya dauki na
ulcer ya jefa a cikin ledar magunguna da
safeena ta bashi. Sallama yayi cikin nutsuwa
ya shiga falon dai dai lokacin mum ta fito
aiko ganin aliyu yasa ta dan yatsina fuska
shiko jiki na bari kamar yayi gamo ya sauko
dg kan kujera yana kwasar gaisuwa,fuska
ba yabo ba fallasa suka gaisa yai mata ya jiki
sannan ya mika mata ledojin hannunsa ya
mike xai mata sallama kenan tace "aliyu
baxaka tsaya ko ruwa kasha ba?" Sai ya
tsinci kansa ya kasa yi mata musu alhalin bai
taba cin komai na gidan ba. Komawa yai ya
xauna xuciarsa na cikin dumuwa yana
buqatar ya duba inteesar kuma ya san by
nw ta tashi dg baccin da ya barta tanayi.
Tunanin haka yasa ya ajiyar xucia tare da
fesar da iska mai xafi hade da lashe
labbansa da suka bushe. Mum ce ta shigo
riqe da jug a akan tray da cup da roban
ruwan c'est bon,ta tsiyaya masa xobon ta
mika masa ya kai hannu biyu tare da yin
godia.... zai kai bakin shi kenan wayarsa tai
ringing hakan ya dakatar dashi da sauri ya
ajiye xobon ya karkace ya xaro wayar dg
aljihun jeans dinsa duk a tunaninsa ko
inteesar ce ta kira shi...
Sae da Aliyu ya fara xuwa asibiti ya dauki
maganin da xai kai ma mamar safeena snn
ya ja motarsa ya kama hanyar gidan jikinsa
a mace, ya na isa yyi parkin a waje, ya fito
da maganin yana kare ma gidan kallo snn ya
shiga, suka gaisa da mai gadin ya karasa
balcony ya danna bell, yar aiki ta bude masa
kmr jira take ya shiga falon ta nuna masa
kujeran da xae xauna da sauri shima kmr
wnda ake contrl ya xauna inda ta nuna
masa yana bin ko ina na falon da kallo, yar
aikin tayi sama kiran Hajiya, yana kallo
Hajiyar ta shigo falon ya dan dukar da kansa
ya gaisheta ta amsa da fara'a kmr gske snn
yyi mata ya jiki, ya bata maganin da ya kawo
mata, ta amsa tana gdya tana jujjuya
maganin, ya ciro kudin da ya dauko daxu ya
mika mata yace "ni xan koma Hajiya" ta
karba da sauri tana gdya ta mike tace to
bari na kawo maka ruwa kasha mana, yace
"A'a Alhmdlh ae daga gida nke," tace "to
bari na baka sako ka kaima safeena," yace
"to," ta mike ta yi sama, sae ga ta ta sauko
da dan wani parcel, ya karba yyi mata
sallama, ta rakosa har bakin kofa tana sa
masa albarka snn ta koma murna fal cikinta,
yana barin anguwar yaji hka kawae yana
son ganin abinda ke cikin parcel din, parkin
yyi gefen titi snn ya shiga budewa, wani
ruwa ne ya xuba jikinsa ya matsar da parcel
din daga jikinsa da sauri amma duk da hka
sae da ruwan ya taba kayansa da farko wari
yaji, ya yatsine fuska kawae kuma sae yaji
wni mugun kamshi me ddi ya xiyarci
hancinsa, ya rufe da sauri ya ajiye parcel din
ya ci gaba da drivin dinsa. Safeena ta kasa
xaune ta kasa tsaye sae kaiwa take tana
komowa a falo, wayar uwarta ya shigo nata
ta daga da sauri jikinta na rawa tace "ya
xauna kan kujerar mumy, kuma ya karbi
ledan," uwar ta kyalkyale da dariya tace
"wllh kuwa dota, ynxu fatanmu kawae Allah
yasa ya bude," safeena ta doka tsalle tace "
Alhmdllh amma naji ddi momy, budewa
kuma ba matsala bace ko a gida xan sa ya
bude bare ina da yakinin ma ya bude naji
sighn din da mutumin yace xan ji a jiki na,"
budewar gate din da safeena taji yasa tace
"wayyoo momyna ya dawo xamu yi waya
anjima," ta katse kiran tana murmushin
mugunta, shknn ynxu sae yanda tayi da
Aliyu," yana shigowa gidan ta karasa cikin
kissa ta rungumesa ya dagata sama ya
manna mata kiss a goshi yace "bbyna sae
kyau kike karawa kullum," ta hararesa tace
"sae yau ka sani," yace "A'a bbyna ina sane,"
kinsan me bbyna na dan maki barna wllh
momy ta ban turare na kawo maki da
karambani na na bude ya xuba jikina," ta
kankamesa ta rasa inda xata sa kanta don
murna, tace "da gske bbyna, wllh sae ka
biya ni," yyi hanyar stairs da ita yana cewa
"naji xan biya bby nawa ne," inteesar kam
na xaune ta jinginar da kanta jikin gado, ji
take kmr ba ita ba duk ta rasa inda xata sa
ranta taji ddi, ga alluran hana aman da yyi
mata duk ya bi ya dameta, tana neman yin
aman ma ko xata samu sauki amma ta kasa,
yunwa take ji ssae amma bbu abinda ke
ranta, ko wani abinci ta tuna sae taji amai
na taso mata jikinta yyi mugun xafi ga
kishin ruwa da take ji kuma tana tsoron
shan ruwa, ta sauko kasa da kyar ta kwanta
kan tiles din dakin ko xata ji ddin ranta,
kasa daure kishin tayi ta mike xaune tana
mayar da numfashi ta rarrafa ta bude fridge
dinta taga ba ruwa ciki sae lemo, tana
daddafa bango ta fita daga dakin ta sauka
kasa da kyar ta bude fridge ta dauki ruwa ta
sha, snn ta koma sama, dae dae kofar
dakinta taji amai frm no where ta xube
wajen ta shiga kwarara aman kmr ranta xae
fita, suna daki shi da safeena duk ta gama
rikitar da shi, ya turata da karfi ya mike
tsaye ya karasa kofa ya bude