INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   23 / 41

66K to 69K   out of 122.8K words

da mamaki kadda cikin dakinta
aka yi ma safeena jere, ta juya tana kallon
Aliyu da ya fito daga dakinsa yana kallota
yace "Abba ne ya ba kansa wahala ya bata
kudinsa shi me 'ya," ya sauka kasa ya barta
nn, sababbin funitures masu rae da lfya
wanda suka fi na da ne a dakin nata, ashe
su Anty Nafisa abinda suka xo yi knn, ta
karasa cikin dakin a sanyaye, bbu abinda ba
a canxa ba a dakin. Tanaxaune gefen
gadonta bayan ta fito daga wanka ta sa
kayan bacci tayi jigum ta ma rasa abinda ke
damunta ya shigo dakin ya ajiye mata ledan
abinci ya fice. Ranar friday da yyi dai dai da
Ana gobe daurin auren Aliyu da safeena
ranar da kuma xa suyi dinner, Inteesar na
kwance a daki da rana duk ta rasa kanta
kmr wata mara lfya, rabonta da Aliyu tun
ranar da ya ajiye mata abinci ya fice sae dae
taji shigowarsa da fitarsa, Zainab da kursum
kadae ke xuwa debe mata kewa, taji an
bude kofar dakinta a xatonta su ne, Aliyu ya
shigo dakin ya xauna gefen gado yana
kallonta yace "mantawa nayi jiya bamu je
party da ke ba" bata ko kallesa ba bare ta
basa amsa, ya tabe baki ya ajiye mata dan
box karami irin na jewelries yace "tunda
kince ba kya son kaya ga wnn, don banso in
shiga hakkinki," ta juya tana kallon box din
ya bude mata, Zinari ne dan kunne da sarka
har da xobunaye biyu, tayi tsaki tace aikin
bnxa me xanyi da wnn gantalin kadae je ka
kara mata don wanda ubana ya sa min a
kayana ma ba damuwa nayi dasu ba bare
wnn, ku wnn ya dama" ya mike tsaye
fuskarsa daure yace "ni kike gaya ma
magana," ta fashe da kuka tace "an gaya
maka din wlh ka fitar min a daki," yyi
murmushi ya dauki box din ya fita daga
dakin, tasulale kasa tana kuka ssae da bata
san dalilinsa
.
ba, karfe bakwae suka shigo gidan da
abokanansa suka shirya suka wuce dinner.
Har
Aliyu ya shigo gidan karfe daya idon
Inteesar biyu,
ta kasa bacci, hka kawae ta samu kanta da
fashewa da kuka har da shessheka, har
kusan
karfe biyu tana xaune bbu alamar bacci a
tare da
ita, taji an tura kofan dakinta a hankali ta
juya da
sauri suka yi ido hudu da shi ta kauda kanta
da
sauri ta mike xata shiga bathroom yyi
hanxarin
rikota ta fashe masa da kuka ya rungumeta
.
Inteesar ta shiga turasa yaki sakinta, har
suka isa kan gado ya xaunar da ita shima ya
xauna yana kallonta ya dago kanta a hankali
yace "me ya hanaki bacci har ynxu," ta
dauke kanta har lkcn tana hawaye ta mike
xata bar wajen ya rikota, a hankali ta shiga
rera masa kuka ya rungumeta yace "ina son
jin kukan ki har wani ddi nake ji idan naga
kina kuka," ta turasa da karfi xata mike ya
rike ta gam yace "not until yhu tel me y yhu
re cryn," ta fashe masa da wani kukan abun
tausayi ya daga ta ya kwantar da ita kan
gadon ya kwanta gefenta ya rungumota
snn ya kashe wutan dakin, ajiyar xuciya
kawae take, a hankali yace "don xanyi aure
shine kike kuka," xata yi magana ya rufe
bakinta da sauri, yace "warce xata haifa
mana 'yan biyu xan auro, kinga sae kiyi ta
raino tunda kina son su," bata ce komai ba
ya daura bakinsa kan gashinta yana kissin
dinshi, a hankali ya kai hannunsa kan
cikinta yana shafawa kmr mae mata rada
yace "xaki iya na baki yan biyun ynxu?" a
tsorace ta rike hannunsa da sauri tace "A"a
wllh baxan iya ba," a hankali yace "plss,"
muryarta na rawa tace "No plsss" ita kam
1st nyt dinsu kawae take tunawa da irin
wahalar da tasha har da suma har abada
bata fatan ya sake kusantarta, ya kankameta
murya can kasa yace "to yi baccin ki," suna
nn a hka har bacci ya dauke ta, ranar dae a
hka suka kwana tana jikinsa kuma ranar ce
rana ta farko da ya kwana a dakinta,
washegari da yyi dae dae da ranar daurin
aurensu da safeena, da asuba ya kwantar
da ita a hankali ya shiga bathroom dinta yyi
alwala, ko da ya fito ya tarda ta xaune kan
gadon tayi tagumi, ta mike ba tare da ta
kalleshi ba ta shiga bayin ita ma tayi alwala
ta fito ta tar da shi yana jiranta, a tare suka
yi sllhn, rana ta farko knn da ta bude baki da
safe ta gaishesa ba tare da ta kallesa ba
yana murmushi ya gyada mata kai kawae, ta
mike xata bar dakin ya kamo hannunta yace
"ina xa ki," ta sunkuyar da kanta bata ce
masa komai ba, ya saketa ta fita, falo ta
sauka ta shiga mrnin duties dinta, ba ita ta
koma sama ba sae kusan karfe tara,ta tarda
shi kwance yana bacci, wanka ta shiga ta
fito ta gama shirinta ta fita daga dakin ta
koma downstairs, bata ba kanta wahalan
hada breakfst ba don bae taba cin girkinta
ba, tayi kwanciyarta a falon don neman
yunwa tayi ta rasa, karfe sha daya taji mai
gadi ya bude gate ta mike ta isa jikin kofa
taga ko waye ya shigo, motoci biyu ne suka
shigo gidan abokanansa kusan su biyar
suka fito, da yake kofar a bude yake
komawa kawae tayi ta kwanta, suka shigo
gidan da sallamarsu duk suna sanye da
fararen shaddodi, ta kara volume din Tv ta
mayar da hankalinta kan TV, tsokanarta
suka shiga yi suna dariya "uwar gida ke
kika rike ango har ynxu yaki fitowa kuma
kika sa ya kashe wayoyo ko to ayi hakuri a
sakar mana shi muje gun daurin aure," bbu
yabo bare fallasa tace "ku dae tambayesa
wanda ya rikesa," ta mike fuskarta a daure
ta haura sama ta bar su nn falo, a step duka
hadu da Aliyu ya galla mata harara, don me
baki tashe ni ba, ita ma ta galla masa
hararan tace "sbda baka isa ba," tayi gaba ta
bar sa nn tsaye, ya sauko suna ta
tsokanarsa wae tsoron uwargida yasa ya
makara, dole suka jirasa yyi wanka snn ya
fito shima sanye da farar shaddar, ba
karamin kyau yyi ba don ko hmm bari dae,
ya shiga dakin Inteesar tana xaune gaban
madubi, kallo daya tayi masa ta madubin ta
dauke kanta yace "kinyi break," tayi bnxa da
shi, ya daga kafada yace "sae na dawo kiyi
mani adduar Allah yasa ayi a sa'a," ya juya
xae bar dakin ta fashe da kuka ba tare da ta
shirya ba, ya juyo yana kallonta, ya karaso
cikin dakin yace "an maki wani abu ne ko
kawae jin ddin kukan ne ke damunki," bata
tanka sa ba, ya tabe baki ya juya ya fita, suka
fita gaba daya da abokan nasa suna masa
mitan ya bata lkci dayawa ko mantawa yyi
yau ce ranar daurin aurensa da sahibarsa
shi dae bae ce masu komai ba har suka
shiga mota suka bar gidan, suna fita daga
gate yace "kun san wani abu ku je kawae
gani nn xuwa, ina son na kai fateema can
gida daga can sae na wuce," namesake
dinsa yace "wae meye hka kke yi ita bata
san hanyar gidan ba sae an kaita baka
ganin saura yan mintoci," Aliyu yace "ni dae
kuje kawae ina nn xuwa, ya bude motar ya
koma cikin gidan," suka yi tsaki kusan gaba
dayansu suka yi gaba, yanda ya barta hka ya
dawo ya tarar da ita, ya dauki hijab dinta ya
mika mata yace "tashi to na kai ki gida,"
bata yi musu ba ta mike ta karbi hijab din
tasa takalminta suka fita, motarsa ya fito da
ta bude sit din baya ta shiga, bai ce mata
komai ba ya ja motar suka bar gidan, suna
isa gida bata jira ya gama parkin ba ta bude
mota ta fice, ya dakatar da ita da sauri ko
kallonsa bata yi ba ta shige gidan da gudu
sae sashin inna, hkn yyi mugun bata masa
rae kuma yasan da mutane cikin gidan shi
yasa bae bi ta ba, ya ja motar kawae yyi gun
daurin aure, mutanen dake tsakar gidan har
da su Hajiya suka bi ta da kallo murna fal
cikinsu, umma ko ta dinga tuntsira dariya
tana guda kawayen Hajiya na taya ta.
ta xube jikin inna ta fashe mata da kuka, a
rude
inna ta shiga tambayarta "meye faru, ke da
waye," ta kasa cewa komai, inna ma ta bare
baki
ta fashe da kukan, Anty Nafeesa ta fito daga
daki
da sauri tana kallon Inteesar tace "wa ya
kawoki,"
inteesar tayi kkrin tsayar da kukanta tace
"shi ya
kawo ni," Nafeesa tace "ynxu kuwa muke
shirin
tafiya can gidan, kukan meye hka kike yi, ke
dae
baki ji ddi ba wllh," a fusace cikin kuka inna
tace
"ban son iskanci ke uwar wa yyi maki
kishiya,"
inna ta mike ta daga inteesar tana share
hawayenta suka shiga daki tana cewa "ki
rabu da
shi, bbu abinda xaki koma gidan nn kiyi,
kuma
bbu uban da ya isa yace ki koma tunda nace
baxa ki ba, ina nn ina jiransa daga shi har
ubansa," Anty Nafeesa tayi murumushi ta bi
su
cikin dakin. Gida ya cika fal da yan uwan su
Hajiya da umma da abokanan arxiki ana ta
shagalin biki har da su Dj a gidan, inna na
daki
xaune gefen Inteesar da ta kwanta tana
bacci
tana mata fiffita ita ma tana gyan gyadi, jin
kide
kide yasa inna ta farka ta fito da gudu har
Anty
Nafeesa da wa inda ke falonta suka tsorata
suka
dinga tambayar lfya, ko kallonsu bata yi ba
ta fita
xuwa tsakar gida da gudu, Anty Nafeesa ta
ma
xaci abu ne ya sami Inteesar suka shiga
dakin da
sauri suka tarar baccinta take, wasu kuma
suka
bi inna da sauri a baya suna tambayar wae
Hajiya
mai ya faru, inna na isa tsakar gidan cikin
daga
murya tace "nashiga uku uban wa ya
gayyato wa
innan shaidanun gidan nn" ta fadi hkn a
fusace
tana nuna masu Dj da kayan kide kiden
nasu, aka
kashe wakar dake tashi, Umma tace "to
naga dae
yau ranar farin ciki ne inna kuma dae daga
yau ba
sake ganinsu xa ayi ba," inna tace "kin ci
ubanki
mai dattin hula, kaji min rubabbiyar
yarinya," ta
karasa kusa da masu dj tana huci ta shiga
bubbuga speakers din tana cewa "ku fitar
min
dasu kar na babbake su, gidan da na ba
gidan
yan iska da shaidanu bane" ba shiri Hajiya
tasa
aka shiga kwashe su a barrow ana fita
dasu, hka
ma canopies din duk sae da tasa suka fita
dasu
tana jaraba an cika gidan dan'ta da tarkace,
hka
mutane suka dinga kallon inna wasu na
dariya
can ciki ciki, "kuma duk shegen da ya xauna
kusa
da flawowin da na ban yafe masa ba duniya
da
lahira tunda dae ba shi ya dasa masa ba, ko
tsinke kuma kar a wurgar a tsakar gidan
nn," ta
fadi tana huci kmr kirjinta xae fashe, Hajiya
dae
shigewa daki tayi kunya kmr ta nutse, wae
juyawar da inna xata yi sae ganin momy tayi
xaune suna hada salad, ta saka salati kmr
xata yi
kuka tace "Allah ya wadaranki Zainabu, ynxu
uban me ya kawo ki cikinsu idan ba
shisshigi da
neman suna ba, ca suka yi maki yi suke
dake
mara xuciya kawae wahalalliya, ni dama
nasan
tun ba yau ba kika tsani yarinyar nn kike
son
ganin karshenta, idan ba hka ba taya xaki
kwaso
kafafuwa ki taho nn cikinsu, wllh daga yau
kar ki
sake nuna kin san Inteesar, ita ma bata
sanki ba
wllh, shi yasa ma da ta xo daxu bata nufi
inda
kike ba dan tasan ba sonta kike ba" ta
karashe
maganar da kuka ssae har da tari, ta bar
wajen
tana cewa "kuma yau bbu ubanda ya isa ya
bar
min tsakar gidan da' na hka, duk sae an
wanke
shi an goge wllh," dariya wasu har da
xubewa
kasa, ranar dae a dari dari su Hajiya suka yi
shagalin bikinsu, jefi jefi inna kan fito taga
ko an
xauna kusa da flowern da tace kar a xauna,
bbu
wanda yyi gigin xama kuwa. Da Magrib
bayan
kowa ya watse inna ta tasa su Hajiya gaba
sae
da suka wanke tsakar gidan su Zainab da
kursum
da Maryam din Anty Nafeesa dariya kmr
cikinsu
xae fashe, dama momy tun daxu ta shiga
ciki
amma sae da inna taje ta fito da ita wae har
da
ita yar bakin ciki maxa su gyara ma dan ta
tsakar
gidansa, sae da taga sun kusa gamawa snn
ta
koma sashinta tana cewa "wahalallun bnxa
kawae" karfe takwas abba yyi kiran Inteesar
falonsa, ta karasa falon a sanyaye tayi
sallama ta
shiga, Zaune ta tarda Aliyu a falon yana
sanye da
shadda brown colour, ta nemi gefe ta xauna
tana
kallon Abba tace "ina yini Abba," Abba ya
amsa
yana kallonta yace "ya gidan," ta sunkuyar
da kai
tace "lfya Abba," Abba ya nisa yace "ranar da
nace ku taho da Zainab don me kika ki bin
ta," ta
daga kai tana kallon Aliyu dake kallonta,
Abba ya
gyada kai yace "to yyi kyau, kuma har ynxu
baki
fara karatun ba ko?" a hankali tace "Abba na
kusan farawa," Abba yyi shiru yana kallonta
snn
yace "to Allah yasa, ki tashi ki bi mijinki, a
cigaba
da hakuri, Allah yyi maku albarka" Aliyu ya
mike
yana kallon Abba yace "nagode Abba," ko
kallonsa Abba bae yi ba, Inteesar ta yi shiru
kmr
xata yi kuka tace "Abba inna tace ba
ynxu......."
Abba ya hade rae yace "inna tace me, tashi
maxa
ki koma dakin ki, kuma bance ki shiga cikin
gida
ba," bata san tayi mugun ba Abba haushi
ranar
da ya aika Zainab kiranta taki xuwa ba, a
sanyaye Hawaye na kkrin sauko mata ta
mike
tace "Abba sae da safe," yace "Allah ya tashe
mu
lfya," Aliyu ma yyi masa sai da safe ya bi
bayanta
suka bar falon
.
.. Suna fita Aliyu ya kamo hannun Inteesar
da sauri ganin bata son jerawa da shi, ta
juya tana kallonsa yace "mu fara shiga na
gaida momynki," tayi masa mugun kallo tace
"ae ko baka fada ba dama momyta ce bance
taka ba," bai ce mata komai ba yana rike da
hannunta suka isa sashinsu, shi yyi sallama
ganin tsaya kawae tayi ta rike kugu, duk da
ita yaso tayi sallamar, Ihsaan ce ta amsa ya
shiga falon tana biye da shi a baya, suna
hada ido da momy ya kauda kai da sauri ya
nemi kujera ya xauna, ita ma ta xauna kusa
da ihsaan da ta kankameta, momy dae na
rike da assignment books din ihsaan, ba
tare da ya kalleta ba yace "ina yini," ita ma
tana neman page din da aka ba ihsaan bbu
yabo bbu fallasa tace "kalau," Inteesar ta
mike ta koma kusa da momynta tace
"assignment ku ke yi momy," momy ta
gyada mata kai, tace "bari nayi assistn dinta
momy," momy ta bar mata buk din, ihsaan
tace "Anty ae na iya," Inteesar tace "to xo
kiyi," ta mika mata buk din ta karba ta shiga
yi, momy ta mike ta shiga daki, inteesar ta
juya tana kallon Aliyu da ya bita da kallo, ko
kadan ba ta jin ddin yanda momy ke masu,
ta mike a sanyaye ta bi ta daki, shi kuma ya
dawo kusa da kanwartasa yana kallon
abinda take yi, tana ganinsa ta daina
rubutun, yana kallonta yace "y did yhu stop,"
tayi shiru taki cewa komai ya mike xae
koma inda yake taji tsoro ssae don ta xaton
dukanta xae yi, yyi murmushi yyi xamansa
yace "to na bar maki wajen," ta ci gaba da
abinda take, da Haisam ne jikinta na rawa
xata fada kansa, amma da yake shi ya koya
mata tsoransa shi yasa bae damu ba, to a
gidan nn ma waye baya tsoransa, yyi
murmushi tuno hka da yyi, yana nn xaune
har kusan karfe tara da rabi snn inteesar ta
fito bayan sun dan yi hira da momy, ta
xauna gefen kanwarta tana kallon abinda
take, murya can kasa yace "ki ce ma momy
xa mu tafi," ta mike ba tare da ta kallesa ba
ta shiga dakin, sae ga ta ta fito a sanyaye
tace "tace to," hkn ya sa ya gane baxata fito
ba knn, ya mike yana kallon ihsaan yace
"bby gud Nyt," ta kauda kanta bata ce komai
ba tana kallon inteesar kmr xata yi kuka tace
"Anty ni xan bi ki," Aliyu yace "je ki tambayi
momy to," ta shiga daki da gudu, sae ga ta
ta fito kmr xata yi kuka tace "tace a'a," yace
"je ki ce mata plss," ta koma da gudu sae ga
ta ta dawo da hawaye tace "tace xan je sch,"
yyi shiru yana kallonta snn yace "i promise
xan xo na dauke ki nxt wk kin ji, sae ki
dinga tafiya sch daga can," ta gyada masa
kai kawae ya ciro dubu biyar ya mika mata
tayi masa gdya snn ta daga masu hannu
suka fita daga falon Inteesar na murmushi,
da kansa ya bude mata gaban motar ta
shiga snn ya xaga ya bude driver sit ya ja
motar suka bar anguwar, bae ce mata ba
bata ce masa ba, suka yi nisa ssae snn taga
yyi parkin ya fita ta bi sa da kallo, tasan me
xae siyo ganin inda suka tsaya, ba a wani
dau lkci ba ya dawo rike da ledoji har biyu
ya bude motar ya shigo snn ya ja ta suka
bar gun suka kama hanyar gida, suna isa yyi
horn mai gadi ya bude ya shiga yyi parkin
snn ta bude motar ta fita shima ya fito ya
kulle motar ya bi bayanta suka shiga gidan,
kamshi ne mai ddi ke tashi a gidan, ta kalli
agogo taga karfe goma da kusan rabi ta
haura sama ta bude dakinta ta shige, ya dde
xaune falo snn ya mike shima ya haura
sama da ledojin a hannunsa yana kallon
kofar dakin safeena ya bude nasa dakin ya
shiga, ba a dau lkci ba ya fito sanye da
jallabiya ya bude kofar dakin safeenar ya
shiga, tana xauna sae taunar cingam take
tana kallo ta wurgar da mayafinta gefenta,
ya karaso yana kallonta yyi murmushi ya
ajiye ledar hannunsa yace "amarya bakya
laifi," ta galla masa mugun harara tace
"daga ina kke Aliyu xaka shanya ni nn, har
kawayena sun gaji da jira sun wuce," ya
xaune gefenta ya rungumota yana shafa
bayanta yace "Abbana ne ya bata min lkci
bbyna kiyi hkuri," ta dan marairaice kmr
xata yi kuka tana shafar fuskarsa tace "har
naji haushi wllh angona," yyi kissin din
goshinta yace "nasan kina jin yunwa bari na
kawo plate da cup na xuba maki chicken da
yogurt din da na siyo maki, tayi kissin din
lips dinsa tace "to mijina," snn ya mike ya
fita, dakin inteesar ya bude a hankali, tana
kwance kan gado ta tsura ma Ac ido, yana
kallonta yace "kinci abinci can gida ne," tayi
bnxa da shi ya karaso kusa da ita ya hade
rae "ba magana nake maki ba," nn ma taki
ce masa komai sae dae me, ya lura kuka
xata fara ta yanda tayi da fuska ya xauna
gefenta da sauri yace "wae ke wace irin
mutum ne da shegen kuka sae kace
marainiya," yyi tsaki ya ce "saura idan na
kawo maki abincin kar ki ci," snn ya fice, sae
da ya fara shiga kitchen ya dauko plate da
cups snn ya koma dakin safeenar, ita ma ta
fito daga bayi knn sanye da dogon hijab ta
xauna gefen gado, kaji uku ne taga ya ajiye
daya gefe da yogurt biyu, ta sauko tana
kallonsa tace "wnn fa dear," yana xuba mata
kajinta a plate yace "na warcan ce" ta
jingina jikinsa ta marairaice tace "xafi nake
ji bby," yace "to cire hijabin mana, a hankali
ta shiga cire hijabin tana masa wani
shu'umin kallo
.
Aliyu ya dauke kansa da sauri ganin wasu
shegun kayan baccin dake jikinta ya ci gaba
da abinda yake, har ya gama ya ajiye mata
nata snn ya dauki na Inteesar ya mike xae
fita ya kai mata, safeena da ta koma kan
gado ta xauna ta daura cinya daya kan daya
tayi yar kara ya juya da sauri yana kallonta
yace "me ya faru bbyna," kamr xata yi kuka
ta shiga nuna masa bayanta ya karasa kusa
da ita yana kallonta yace "me ya samu bayan
dear," cikin tsigar shagwaba tace "nima ban
sani ba," ya dafa ta ya dan duka yana duba
bayan da take nuna masa ta turasa da sauri
ya fada kan gado ya wara ido kan yace
komai ta fada

23 / 41