INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   29 / 41

84K to 87K   out of 122.8K words

tabe baki
jin wakan da ke tashi dakin safeena, sae da
ta huta na kusan minti goma snn ta mike ta
dauki purse dinta ta fita daga dakin, dakin
Aliyu ta bude a hankali ta shiga ta bude
drawer din da taji yace Safeena ta bude ta
dauki kudi ranan, taji ta a kulle, tace "na
shiga uku," ta mike ta fara kalle kallen cikin
dakin kmr xata yi kuka, to ina xata samu
kudin xuwa asibitin ynxu, drawers din
dakin ta dinga bubbudewa gaba daya ko
xata ga kudi amma bbu, duk ta gaji sae haki
take, tuni ta fara kuka tana cewa "Allah ka
taimakeni in ga kudi" ta bude lst bedside
drawer din taga wani babban book an
rubuta my diary a gaba, tayi tsaki ta ajiye ta
mayar da drawern, ta mike ta isa wardrobe
din da yake ajiye kayansa na sawa ta bude
ta lumshe idonta sakamakon wani kamshi
me ddi da ya bugi hancinta, ta gama
bincikenta nn ma ba ta ga kudi ba ta rufe ta
xube kasa ta daura hannu a ka tace
"wayyoo Abbana wllh ni na gaji," ko ina ta
bude daga taga Allura sae taga magunguna
da dae kayan asibiti kmr tsiya wnn wace
irin jaraba ce, kmr ance ta mike ta daga filo
taga dubu daddaya karkashin filon har da
Atm dinsa ta wara ido tace "wayyo Allahna,"
ta kwashi kudin ta shiga kirgasu da sauri
hannunta na rawa taga dubu sha biyu ne, ta
dan marairaice fuska to xae isheta taje
asibitin ma kuwa, tayi tsaki ta bude purse
dinta ta xuba kudin snn ta juya xata fita
daga dakin taje dakinta ta sha ruwa don
mugun kishi take ji don tsabar son taje ta
cire cikin ta nemi xaxxabin dake tattare da
ita ta rasa sae kasala kawae, har ta isa bakin
kofa ta dawo da sauri tuna baxae rasa ruwa
a dakinsa ba da tayi ta bude fridge dina ta
ko ga ruwa ta dauka ta bude ta sha snn ta
rufe fridge din ta dauki sauran ta fita daga
dakin, duk wnn abinda take safeena bata
sani ba, tana daki kwance tana ta shan kida
cike da jin ddi, jiran jin ihun Inteesar kawae
take a ko wani lkci, Inteesar kam har ta fita
daga gidan rike da purse dinta cikin Hijab,
mai gadi dae bae ce mata kala ba ta bude
gate ta fice abinta sae da ta isa bakin titi
snn ta tsayar da tricycle tayi masa
kwatancan asibitin da Aneesah ta gaya
mata yace ta bada dari biyu, ta shiga tace
mu je. Wasa wasa asibitin shegen nisa ne
da shi, yyi parkin dae dae gate din asibitin
ya juyo yana kallonta yace "mun kawo
Hajiya," ta fito tana kare ma asibitin da ma
anguwar kallo, ta bude purse ta ciro dubu
daya cikin kudin ta basa kudin ya rage dubu
sha daya, ya bata canjinta ta karasa cikin
asibitin gabanta na faduwa, wnn dae da
ganin asibitin nn ba na talakawa bne, anya
kuwa xasuyi mata abortion a dubu sha daya
kuwa ta dan karyar da kanta abun tausayi,
da Addu'arta ta shiga asibitin, babba ne
ssae ta karasa cikin reception ta xauna
ganin patients dayawa a xaune, ta shiga
kare ma reception din kallo, ta kai kusan
minti talatin a xaune ba a xo kanta ba duk
ta gaji, taji kwanciya kawae take son yi ga
amai dake taso mata, ta daura kanta a cinya
taji kmr ta rusa ihu duk ta rasa ina xata sa
ranta, wata nurse ce ta dafa ta ta dago da
sauri tana kallonta, Nurse din tace "yhur
card nmbr Madam," inteesar ta shiga kalle
kalle xata yi magana taji yawu ya cika
bakinta, nurse din ta lura da hka ta nuna
mata bayin dake kasan reception ta karasa
ta xubda yawun ta kora ruwa snn ta dawo,
nurse din ta debo vitamin c ta mika mata ta
sa a baki tayi mata gdya ta karba, tana
kallon Nurse din tace "i dnt have a card in
here," Nurse din tace "to dole sae kin yanki
kati," Inteesar tayi shiru snn tace "nawa ake
yankan katin," nurse din tace "family card
dubu biyar, na mutum daya dubu 2 da dari
5," inteesar tayo waje da ido tana kallonta,
ganin xata bata ma nurse din lkci ga kuma
patients dayawa suna jira yasa tace "to ki
yankar min na mutum daya," nurse din tace
"ok" snn tayi gaba, a hankali inteesar tace
"na shiga uku, to ai kudin ya kare," ba ajima
ba nurse din ta fito daga wani dan daki ta
mika mata katin snn wata nurse ta
daddubata ta duba har da weight dinta tayi
rubutu a file tasa nurse ta rakata bayi aka
xuba mata ruwa a kanta don temperature
dinta yyi sama, ita dae binsu kawae take, a
xuciyarta tace ko da yake basu san me ya
kawota ba shiyasa suke bata lkcnsu, ita dae
ynxu likita kawae take son gani, wata nurse
ce ta gwada mata office din doctor din da
xata shiga a sama, tana rike da file dinta ta
haura sama da kyar ta karasa office din tayi
knock.
A hankali Inteesar ta tura kofar bayan an
mata ixinin shigowa office din, cak ta tsaya
daga bakin kofa tana kallon likitar, doctor
din ma ta mike tsaye tana kallon Inteesar da
mamaki tace "fateema," inteesar ta kirkiro
murmushi gabanta na faduwa ta karaso
office din a sanyaye, ta nuna mata kujera ta
xauna, doctor din tace "daga ina kike hka
fateema, me ya kawo ki nn," ta rasa karyan
da xata mata, da kyar bakinta na rawa ta
ce"banda lfya ne," doctor din ta hade rae
tace "shi Aliyun fa," inteesar ta rasa me xata
ce ga xuciyarta sae tashi yake, likitan ta
dawo kusa da ita tana kallonta ta dago
kanta tana kallon cikin idonta tace "ciki gare
ki fateema," inteesar tayi shiru bata ce
komai ba, doctor din ta ciro wayarta ranta a
bace ta shiga neman layin Aliyu, da sauri
inteesar ta dakatar da ita gabanta na
faduwa tace "A'a don Allah doctor kar ki
kirasa wllh ya sani kuma yana dubani nice
dai bana son shi ya duba ni, Allah yana kula
dani doctor kawae ni ce bana so, idan yaji
na xo nn xae bata min rae don bae sani ba,"
doctor din tace "haba fateema, to ma don
me xaki fita ba tare da ixinin mijinki ba,
kuma meyasa baki son ya duba ki," inteesar
ta fashe da kuka tace "wllh ni bana sonsa
doctor," doctor din ta tsaya da mamaki tana
kallonta snn tace "sbda me fateema, gashi
har rabo ya shigo kice baki son mijinki,"
Inteesar ta sunkuyar da kai tana hawaye,
doctor din tayi shiru tana kallonta, can ta
koma sit dinta ta xauna ta shiga yi mata
nasiha kan cewar ta rungumi mijinta ta cire
duk wani rashin sonsa a ranta, ita dae bata
ce komai ba sae kukan da take a hankali,
Doctor din tace "yyi maki scan ne?" inteesar
ta girgixa kanta tace "A'a nace masa bana
so," doctor din ta harareta tace "to karki
sake yi ma mijinki musu baki san aljanarki
na karkashin kafarsa ba," inteesar ta dan
tabe baki kanta a kasa ba tare da ta bari
doctor din ta lura ba, doctor din ta yagi
wani takarda ta danyi rubuce rubuce snn ta
danna bell wata nurse ta xo da sauri, ta
mika mata takardar tace "scan xa ayi yi mata
sisterna ce," doctor din ta kalli Inteesar tace
"tashi ki bita," inteesar ta mike a sanyaye ta
bi bayan nurse din har sun kai bakin kofa ta
juya tana kallon doctor Maryam tace "don
Allah doctor kar ki kirasa wlh xae bata min
rae,"doctorn tayi murmushi tace "baxan
kirasa ba ki kwantar da hankalinki" bayan
kusan awa daya inteesar da nurse din suka
shigo da sakamakon a hannun nurse din, ta
mika ma doctor maryam ta fita, doctorn ta
bude takardar tana dubawa, inteesar dae
kallonta kawae take ranta a hade, ba shiri
taga doctor maryam ta mike tsaye da sauri
tace "waw Ahmdllh, twins 4 Aliyu, Allahu
akbar," ta rungume inteesar tace "Allah ya
raba lfya kanwata, kinga ma yan biyu ne"
inteesar ta sunkuyar da kanta da sauri
hawaye ya cika idonta, hka doctorn ta dinga
mata surutu cike da murna kmr ita xata
haifa ma cikin, ita dae bata ce mata komai
ba daga karshe ta hada mata magunguna,
da allurori a office dinta ta xuba mata su a
leda da takardar scan din tace "to maxa
tashi ki koma gida sae ki kai masa takardar
scan din, sae ya fada maki yanda xaki sha
magungunan yyi maki alluran," Inteesar ta
mike da sauri kmr jira take tace "ngdd ssae
doctor," har gate doctorn ta rakota snn tayi
mata sallama bayan ta kara jaddada mata ta
hakura ta xauna da mijinta, ita dae inteesar
sae gdya take mata har ta koma ciki snn ta
kama hanyar titi inda xata samu tricycle, a
cikin wani flower ta watsar da magungun
da injectns din dake cikin ledar dake
hannunta ta bar takardar scan din kawae, ta
isa titi xuciyarta na suya, ta tsayar da tricycle
tace "malam don Allah idan kasan ko wani
asibiti a nn wajajen ka kai ni," yace "to
shigo muje akwae wani can gaba," ta shiga
da sauri ya ja machine din suka kama
hanyar asibitin, ae ko yan goma ne a cikinta
ba yan biyu ba sae ta xubar da su yau wllh
.
Wani babban Asibitin aka kuma kawota, ta
fito tana kare ma asibitin kallo snn tace
"nawa xan baka," yace "ki bada ko nawa
ne," ta ciro dari biyu ta mika masa tayi
hanyar gate din shiga asibitin, gabanta ya
shiga faduwa ganin asibitin bana wasa
bane don har yafi wanda taje da xu, tana isa
reception bata tarar da patients da yawa ba
aka xo kanta, nurse din tace "yhur card
nmbr madam," Inteesar tace "i dnt have a
card in here, nawa ne katin," nurse din tace
"family card dubu biyar, na mutum daya
dubu uku, na Anti natal, dubu biyu,"
Inteesar ta ciro dubu uku ta mika mata,
matar tace "sunanki fa," inteesar tace
"Fateema Aliyu," matar tace Address fa? Da
date of birth, Inteesar ta bata fake address
da date of birth dinta, matar ta juya ta wuce,
ba ajima ba ta dawo ta mika mata katinta
snn aka dubata wata nurse ta rakata da file
dinta a hannunta xuwa office din doctor,
yana xaune yana ta rubuce rubuce farin
glass a idonsa, sae da gabanta yyi mugun
faduwa don sae taga kmr ya Aliyu barin
yanda ya hade rae da tsukekken bakinsa,
shima kyau kam ba a magana, ta karasa
office din xuciyarta na ci gaba da bugawa ta
ajiye masa file din a gabansa ta xauna kan
kujera a sanyaye tana kallonsa, yana ta
rubuce rubucensa har lkcn bae dago ba,
hkn yasa ta dan marairaice a hankali kmr
me shirin kuka tace "doctor," sae a snn ya
dago yana kallonta yace "srry ina dan abu
ne," ya jawo file dinta gabansa ya bude,
tana kallonsa a sanyaye tace "don Allah don
annabi taimako naxo ka min doctor," ya
dago yana kallonta yace "taimakon me fa,"
nn da nn hawaye ya cika idonta ta rasa me
xata ce, yace "tok 2 me mana yan mata,
taimakon me kike nema, baki da kudine
kika xo a dubaki," ta girgixa kai ta fashe
masa da kuka tace "A'a," ya kauda kansa
yace "ni karkiyi min kuka a nn, ki fadi
abinda ya kawo ki, mijin ki fa?" a hankali
muryarta na rawa tace "ni banda miji," ya
wara ido yana kallonta yace "wat? Amma
kin san kina dauke da juna biyu kuwa," ta
fashe da matsanancin kuka tace "ka taimaka
min ka tausaya min ka cire min don Allah
abinda ya kawo ni knn," yace "kina da
hankali kuwa ca aka maki ana xubar da ciki
a nn," cikin kuka tace "nasan ka iya doctor,
ni taimakona nake son kayi don Allah," ya
girgixa kai yace "me ya aike ki kanwata,
meyasa kika xabi ki..." da sauri ta katsesa
tace "rapin dina aka yi, kuma har yau ba a
sani ba a gida," yace "innalillahi wa
inna'ilaihi raji'un, to don me baki fada ba a
gida" tana kuka tace "ba yrda dani xasu yi
ba wlh," yace "to waye yyi maki," tayi shiru
kmr me tunanin abinda xata ce nn kuma
amai ne ke taso mata, ta daure tace
"saurayina ne," yyi shiru yana kallonta,
mikewa yaga tayi da sauri shima ya mike,
yaga ta toshe bakinta ya bude mata bayi da
sauri ta shiga ta fara kwarara amai, yana
tsaye gefenta tausayinta ya rufesa ganin
yanda take aman kmr xata shide amma bae
taba ta ba har tagama ya bata ruwa ta
wanke bakinta ta xuba ruwa a wajen ta fito
da kyar ta xauna kan kujeran ta kifa
kantakan table dinsa abun tausayi, yace "to
sae mu ce ma Allah me, wllh ban taba xubar
ma mace ciki ba kanwata," ta dago tana
hawaye tace "plss ka taimakeni kuma ka
fadi nawa xan baka ko ba yau ba xan biyaka
don kudin hannuna ya kare," shi dae yyi
shiru bae ce komai ba, har dae daga karshe
ya mike ya fito gabanta yana kallonta yace
"takardar meye a hannunki," ta kalli
takardar snn tace "na scan da nayi ne," ya
karba yanadubawa snn yace "Mrs Aliyu
kuma aka sa," kmr xata yi kuka tace "kunya
nake ji, ace bani da miji kuma gani da ciki,"
bae ce komai ba ya maida idonsa kan
takardar yace "ya salam, yan biyu ne ae," ta
gyada masa kai tana hawaye, ya koma ya
xauna ya dafe kansa, yace "anya kuwa xan
iya taimakon nn kanwata, rae biyu fa kuma
har kusan 2mnth," ta fashe masa da wani
sabon kukan tace "don Allah ka rufa min
asiri," ya mike shima da ganin sa kasan
jikinsa yyi sanyi, ya bude wani show glass
din magunguna ya shiga xaban wasu
magani har kala uku, snn ya dawo yana
kallonta rike da maganin yace "amma xan
maki allura a nn," kai kawae ta gyada masa
tana kallonsa ya hada alluran ya juyo yana
kallonta tace "ni ba kai xaka min ba ka ba
nurse su min," yana kallonta yace "ok ni xan
rufa maki asiri, ke kuma ki tona min nawa
ko," da sauri tace "A'a wllh," ta bude
cinyarta yyi mata snn ya dauko
magungunan ya bata ya gwada mata yanda
xata sha, tayi ta masa gdya har da kuka, nn
dae yyi mata nasiha ssae akan matsalar da
ta tsinci kanta a ciki, ya nuna mata ita ce me
babban laifi, ita dae hawaye kawae take har
yyi mae isar sa, yyi shiru, a hankali tace "to
nawa xan biyaka doctor," yyi shiru yana
kallonta snn ya sauke ajiyar xuciya yace
"bana bukatan komai tunda ba aiki me kyau
nayi ba, kawae dae nmbrki xaki bani don
Allah," da sauri tace "to xan baka amma a
kashe yakesae na koma gida na kunna," ta
basa tsohon layinta, snn ta dada masa gdya
ssae ya rakata har gate, ya koma, ta shiga
ticycle xuciyarta fari tasa kmr an mata
albishir da aljanna ta kama hanyar gida da
magungunanta.
.
A gajiye Inteesar ta shiga gida bayan ta biya
mai adai-daita sahu kudinsa, xaune ta tar da
Safeena a falo tana cin Ayaba da gyada tana
kallon American film sae kyalkyale dariya
take ita daya kmr tababbiya, bata ko kalli
inda safeena take ba ta haura sama da sauri
gabanta na faduwa kar ta biyo ta ta ci
ubanta, don mugun tsoranta take idan su
biyu kadae ne a gida, in ko Aliyu na nn
fitsara sae wanda bata tuna ba, dat was
den, lkcin da take da lafiya knn, ynxu kam ta
kanta take ba ta tsiwa ba, Safeena ta bi ta
da kallon mamaki baki bude, dama yarinyar
nn bata gidan ashe, shine take ta xaune kmr
yar iska tana jiran jin ihunta, to ina ma taje,
ranta yyi mugun baci ta kasa cin ayaban
gabanta, tunawa tayi cewar tunda ta kwaso
rana 1st abinda xata fara bukata shine
ruwa, hankalinta ya kwanta tunanin hkn da
tayi, to amma Allah yasa a fridge ruwan yake
kar taga abinda ke ciki don inda sanyi
baxata taba lura da komai ba, inteesar kam
na shiga daki ta ajiye magunguna da
takardar scan dinta a kan gado, katunan
asibitin dama tun a hanya ta watsar da su,
ta bude fridge dinta da sauri tana haki xata
dauki ruwa ta sha taga bbu ruwa, ta yarfe
hannu kmr xata yi kuka to ynxu ya xata yi
ga wancan mayyar a falo taje tayi mata duka
a bnxa, ta juya xata shiga bayi tasha ruwan
ganin bata da wani alternative ta hango
goran ruwan da safeena ta ba Aliyu ya
kawo mata a bedside drawer, ta karasa da
sauri ta dauki ruwan taji shi kmr ruwan
dumi, bata damu ba ta kai bakinta xata sha
taga abubuwa na yawo a ciki kmr an xuba
kasa, idan ma baka kura ido ba baxa ka lura
da hkn ba, ta dauki dayan ma tana kallon
kasan ruwan ta gansu kwance ta girgije ta
ga suna ta yawo, ta yatsine fuska ta isa
bathroom dinta ta tsiyaye duka ruwan guda
biyu a bath tub snn ta koma daki ta dauko
cup ta dibi ruwa a famfo ta sha ta koma ta
kwanta a gajiye, a hka bacci mai nauyi ya
kwasheta ba tare da ta shirya ba, shafa
cikinta da taji ana yi a hankali ne yasa ta
bude idonta da sauri suka yi ido hudu da
Aliyu xaune gefenta ta shiga kkrin mikewa
xaune ya taimaka mata yana kallonta yace
"kin ci abinci kuwa don yau na xo duba
bbyna ne hope kin shirya?" ta juya ta kalli
agogo da sauri taga karfe takwas na dare,
mikewa tayi da sauri taje ta xubar da yawun
bakinta ya rikota yace "ina xa ki," ta buge
masa hannu ya saketa ta karasa bakin kofar
bayin ta juya tana hararansa,
magungunanta ta gani kan gadon kusa da
shi, ta yo waje da ido a tsorace da ganinta
kasan bata da gskya, ya tsaya kallonta yace
"me ya faru," sanin cewa xae juya ya kalli
inda take kallo ne yasa ta tofar da yawun
bakinta nn bakin kofa da sauri ta fasa wani
raxanannen ihu tana tsalle, har ya juya ya
kalli ledan kan gadon kuwa ya mike da sauri
ya karasa kusa da ita a rude ya riketa yana
tambayarta lfya, jikinta ya dau rawa ta fashe
masa da kuka tace "wayyoo cikina ke min
ciwo har da kaina," da mugun damuwa
yace "cikinki kuma" ta gyada masa kai
jikinta na ci gaba da rawa, ya daga ta xae
kwantar da ita kan gadonta ta fasa masa
ihu a gigice tace "wayyoo ni ka kai ni
dakinka, xafi nake ji," duk ta rikitasa ya
dauketa da sauri ya bude dakin ya fita, sae
kuka kuwa take jikinta na rawa, safeena
dake fitowa daga dakinta knn ta bisuda
kallo xuciyarta na bugawa "kai wayyoo ddi,
ta sha ruwan," ko kallonta Aliyu bae yi ba, ita
ko inteesar sae kuka take kmrgske, ya
kwantar da ita kan gado bayan ya kunna AC
yana kallonta yace "ina kika ce ke maki
ciwo," a hankali tace "ya daina, wanka
kawae xanyi da ruwan xafi," ya shiga
bayinsa da sauri ya hada mata ruwan, yana
shiga ta mike har tana tuntube ta fice daga
dakin da sauri suka kusan cikin karo da
safeena dake labe bakin kofa, safeena ta
koma baya a tsorace tayi xaton Aliyu ne,
inteesar ta watsa mata harara tace "an dae
ji kunya," tayi tsaki ta bude kofar dakinta da
sauri ta kwashe magungunan kan gadon ta
xuba su cikin handbag dinta jikinta na
rawa, tana xuba su ta fice da sauri taga
safeena tsaye har lkcn kwakwalwarta a
jagule to ko bashi tasha bane, inteesar ta
wuce ta ta shige dakin Aliyu, dae dae nn ya
fito ya tsaya kallonta da mamaki, xae yi
magana ta rigasa "ruwa, amm ruwa naje
sha," yana mata mugun kallo yace "get out,"
ta yi kmr xata yi kuka ya daka mata tsawa
"ni kike raina ma hankali ko, fitar min a daki
munafuka," tayi tsaki ta juya ta fice daga
dakin tare da sauke ajiyar xuciya. Bata samu
shan maganin ba

29 / 41