Author : Khaleesat Haidar Category : Romance
da ake bata sani
ba, bacci mai nauyi yyi gaba da ita. Aliyu
kam ya kasa ce da inna komai sbda
mutanen da ke wajen sae binta yake da ido
tana ta xuba masa rashin mutunci, can dae
ganin abun nata gaba yake ba baya ba yace
"ke wllh baki da maraba da tsofaffin
yarbawan lagos, dama can cikinsu kika je
kika xauna da yafi maki alkhairi, haba
mutum bashi da aiki sae masifa da fadan
rashin gskya, wnn wllh duk halin tsofaffin
yarbawa ne," nn fa Aliyuya sama ma kansa
lfya, don xube wa inna tayi gun ta dinga
rusa ihu wae jikanta ya hadata da kafurai
yace mata tsohuwar bayerabiya, hehehe
gidan Bukar dae ya tashi daga gidan biki ya
koma gidan comedy, hmm bari kawae mu
tsallake nn wajajen sisters. Karfe takwas aka
gama walimar da Anty Nafisa da kawayenta
suka shirya don kmr yanda Aliyu yace baya
son ko wani irin party, Abba bae bari anyi
komai ba duk da Anty Nafisa ta so ko dinner
ne ayi, ynxu kam intisaar ta daina kukan da
take yi sae dae ta xama kmr wata gunki ga
muguwar ramar da tayi duk tayi wani irin
sanyi tun bayan nasihar da Alhaji mukhtar
yyi mata daxu da wani abokin abba, karfe
tara aka fara shirye shiryenwucewa da
amarya don abba yace ranar xa a kaita, inna
ta shigo dakin rike da kofi tana wangale
baki tace "maxa ki shanye wnn jikalleta,
shine na karshe," sae ka rantse kace ba
innar daxu bace.Anty Nafisa ta dago intisaar
tana kallonta tana murmushi bayan matar
da ta kawo musamman dongyaranta ta
gama tsantsara mata kwalliya na fitan
hankali bayan ta gama mata gyaran karshe,
lace ne mai laushi da shegen kyau, shi ba
milk colour ba, kuma ba light brown ba, da
ratsin orange colour a jiki sae daukar ido
yake, fuskar nn tata tasha cool make up, ga
design din lallenta da yyi ma fara fatar ta
kyau sae sheki yake, Anty nafisa ta dago
fuskartatana kallon idonta, ta girgixa mata
kai hade da bata rai ganin hawaye makale a
idonta suna neman xubowa, ta dauki
hankerchief ta goge mata hawayen, snn ta
dauki babban mayafinta fari ta yafa mata a
ka,
.
ta dauko mata takalminta shi ma farin ta
saka, snn ta ja ta tayi bangaren Abba da ita
yan rakiyarsu na biye dasu a baya, Nasihar
karshe abba xae mata, fuskarta a rufe yake
Anty Nafisa tayimata jagora har cikin falon
Abba, ta xaunar da ita har lkcn fuskarta a
rufe yake tana hawaye duk da Nafisa bata
san kuka ma take ba, kamshin turaren Aliyu
ta dinga ji a gefenta hkn yasa gabanta ya
shiga faduwa, ta juya da kyar ta kalli gefenta
taga Aliyu xaune shima kansa a kasa, yana
sanye da shadda ruwan kasa yyi masa kyau
sosai, cikin dubara ta dan matsa ganin kusa
kusa suke,"fateemah" taji abba ya kirata
cikin nutsuwa, ta amsa da dashashiyar
murya tace "Na'am Abba," abba yyi
murmushi yace "kin san abinda nake so
dake," ta girgixa kanta ba tare da ta dago
ba, nn daeabba ya dinga mata nasiha tun
tana daure wa har ta kasa ta fashe da kuka
sosai, hkn yasa Abba ya kyaleta ya juyo kan
Aliyu, shi ma dae har Abba ya gama bae
dago kai ba, sae maganar abba ta
karshegareshi ne yasa sa dago kai yana
kallon abban,"kuma Ali idan ka cutar min da
fateemah bana tunanin xan iya yafe mka,"
*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.thn.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > tophausanovels@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Top Hausa Novels
Twitter: Top Hausa Novels
Telegram: Top Hausa Novels
Watsapp Group: https://chat.whatsapp.com/BRN8VEA8BczD61ZGjoOUod
********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
Aliyu yyi wani kasaitattcen murmushi tare
da maida kansa kasa, Abba ya sa masu
albarka snn yace su tashi suje Allah ya basu
xaman lfya, intisaar na gaba yana binta a
baya mutanen da suka rakota falon suka
rufa masu baya, anty nafisa kuwa ta tsaya
don tana son magana da yayan nata kafin ta
fita, sae ga inna ta shigo tana murmushi
tace "Bukar Bukar, wae da ca nayi don Allah
ko xan iya binsu na koma can da xama, don
gskya gidan nn naka duk ya fitar min a rae
barin da xasu barni ni kadae, dama ga
matanka ba gani na da gashi suke ba gaba
dayansu, can ko kaga muna tare gaba daya
snn suna gani na da mutunci, idan ya so
duk bayan wata biyu sae na dinga kawo
maka xiyara nn ko ya ku ka gani....." abba ya
juya cike da takaici yana kallon Nafisa da ta
kauda kanta, ya mike tsaye rae bace yace
"ae saeki bi su to" snn ya shige bedroom
dinsa, Nafisa ta mike ba tare da ta kalli
uwartata dake nn tsaye kmr gunki baki
bude ba ta fice. Momy ta kasa ce da intisaar
dake durkushe gabanta tana jiran tata
wordof advice din kan xamantakewar aure
komai, Nafisa dake kan su a tsaye tace "kiyi
magana mana maman ihsaan lkci fa na
wuce wa," momy tayi murmushi tace "Allah
ya basu xaman lfya, kuma ya albarkaci
aurensu, shi knn abinda xan iya cewa knn,"
anty Nafisa tayi murmushi ta dago intisaar
dindake kuka sosae tace "mamanki ta maki
addu'a fateemah, kice ameen,"
.
intisaar ta xube jikin uwartata tana kuka
sosai tace "momy ni bna son nabarki baxan
iya ba, don Allah kice su bar ni, bana son
naje ko ina," da kyar Anty nafisa da kawar
momy suka fitar da ita daga falon don
haukace masu tayi, momy duk iya dauriyarta
sae da ta xubdama 'yar tata hawaye don taji
tausayinta sosae, kuma sae gashi Allah bae
sa tayi dacen miji ba, da har su Anty nafisa
xasu kai ta wajen inna tayi mata tata
nasihar aka ce masu ae fa inna na can tana
ta rusa ihu, ba shiri suka saka intisaar a
motar ita da kawayen nata, wato su zainab,
Anty nafisa ma ta shiga motar suka kama
hanyar gidan Aliyu dake can Hotoro, su
Hajiya da umma dama tun da rana suka
kulle kofofinsu kmr bbu kowa a ciki, don
cikin lodin jama'ar da suka xo bikin bbu
dangin hajiya ko daya bare kawayenta hka
ma umma.karfe goma da kusan rabi motar
da ta taho dasu tayi parkin cikin gidan Aliyu
bayan mai gadi yabude gate din, abokinsa
ne Mujaheed yyi drivin din, gida ne babba
mai kyan gaske ya kawatu da shuke shuke
ta ko ina masu daukar hankali, ginin tsarin
duplex ne, dakuna uku da bathrooms a ciki
each, sae babban falo da bathroom da toilet
a ciki daga downstairs don sae ka hau
stairs xaka tafi dakunan,kitchen din babba
ne sosai sai kuma store dake cikin kitchen
din, stairs uku xae yi lead dinka xuwa
dinning din da aka xagaye da labule snn
akwae kawatattcen garden dake ta bayan
gidan, Anty nafisa ta fito da intisaar daga
motar fuskarta a lullube suka hau stairs na
balconyn, Anty Nafisa ta fadi mata adduar
da xata karanta a kunne kafin ta shiga
gidan kuma ta tabbatar da kafar damanta ta
shiga gidan, sun tar da mutane da dama
cikin gidanmasu jiran kawo amarya, har
bedroom Anty nafisa da yan rakiyar suka yi
ma intisaar jagaro suna guda, ita dae
intisaar ji take kamr ba ita ba binsu kawae
take kmr wata gunki, Aminiyar inna ta
xaunar da ita gefen gadon tana ce ma
mutanen da suka shigo suka cika dakin su
fita su bata waje xatama intisaar magana,
duk sae da ta koresu dakin ya rage daga ita
sae Anty nafisa da xainab, maganganun da
intisaar bata yi xato ba masu nauyita dinga
gaya mata ga anty Nafisa tsaye, xainab
dama tsum tsum tayi ta fice daga dakin, ita
dae fuskarta a rufe yake, daga karshe ta
dada mata nasiha sosai, Anty nafisa na
tayata, kuka sosae intisaar ke yi tana
tausayin rayuwarta don tana da tabbacin
kila farin cikinta ya gama karewa a duniya,
.
karfe sha daya bakin suka watse gida ya
rage daga Anty nafisa sae xainab don har ta
kawayen amarya ma sun tafi, su ma suna ta
shirin wucewa ne, dama Anty nafisa ta ajiye
mata kayan baccin da xa ta saka snn ta
nuna mata turarrukan da xata shafa kafin ta
kwanta, ta tambayeta tana jin yunwa ne,
tace A'a, ta fita kitchen ta hada mata wani
tsumi ta bata ta shanye gabanta, lkcin da
xasu tafi kuwa intisaar rungume anty nafisa
tayi tana kuka sosai wae kar su tafi su barta
don Allah tsoro take ji, sae da xainab tayi
kuka don tausayin intisaar don gigicemasu
tayi, da kyar Anty Nafisa ta lallabata bayan
tayi assure dinta cewar yanxu su Aliyu xasu
shigo don ta kirasa yace suna hanya da
frndx dinsa kuma gobe in'sha Allah xata xo
da safe snn ta samu suka bar gidan don
mijinta na busstop yana jiranta, gidan ya
rage daga intisaar sae halinta, kuka take
sosae kamr ranta xae fita, ta kasa xaune ta
kasa tsaye don tashin hankali, yau ga ta ga
babban makiyinta xasu kwana gida daya,
duk tabi ta takure kanta waje daya tana
rawan sanyi tsoro. Karfe kusan sha biyu taji
shigowar motar Aliyu, xumbur tamike a
tsorace ta daura hannu a ka tace "nashiga
uku ni fateemah," ta koma ta gefen
madubinta ta tsaya jikinta na bari tana
hawaye sosae, tana ji ya shigo gidan ya rufe
kofofin, tun kan ma ya hayo sama ta dinga
jin kamshin turarensa da ya shiga tada mata
xuciyarta don tsabar tsoro. A hankali taji
yana taka matakalan benen yana hayowa
sama, xuciyarta ya tsananta buga wa, ta
rumtse ido cike da tashin hankali tana yarfe
hannu hade da shesshekar kuka, can kuma
sae taji tsit kmr ba mutum a wajen, ta bude
idonta a hankli tanakallon kofar dakin a
tsorace, taji an bude kofa, saurakiris ta saki
ihu jikinta ya dau rawa, kafanta suka kasa
daukarta ta durkushe wajen tana maida
numfashi kmr warce tayi gudu, a hankali taji
an rufekofar da aka bude.
ba dakinta ya shigo ba ta fadi a xuciyarta
tana kkrin maida hawayen dake neman
saukowa a idonta, ta xaune kan tiles din
dake shimfide a dakin ta jingina jikin
gadonta kanta a kangadon, kmr xata fara
sabon kuka kuka, to ta tabbatar baxae
shigo din ba, tayi jigum ta xuba ma kofar
ido tana tunanin irin abinda Aliyu xae mata
indae har ya shigo dakin nn, kila ma jefar da
ita xae yi ta tagan dakin gaba daya, tunda
wanda ya iya bude mota ya wurgota waje
ae komai ma xae iya yi. A hankali intisaar ta
bude idonta jin haske da ya addabi fuskarta,
ta fara waige waige a tsorace tana kallon
inda take, har lkcn tana jingine jikin gadon
nea xaune, sun ray ne ya shigo dakin ya
sauka kan fuskarta, ta mike da sauri tana
kallon agogon dake manne a dakinta taga
karfe bakwae, ta xaro ido hade da dafe kirji
don ko sllh bata yi ba,ita bata ma san
yaushe baccin ya dauketa da har gari ya
waye ba, budewar gate din da taji ne ya sa
ta xuwa kusa da window ta bude curtain
dinta a hnkli tana lekan ma xa ayi, Aliyu ta
gani cikin motarsa yana gaisawada mai
gadi snn ya ja motar ya fice daga gidan mai
gadi ya kulle gate, intisaar ta sauke ajiyar
xuciya ta jingina jikin wall din dakinta tana
tausayin kanta, ganin hkn ba shine gabanta
ba yasa ta shige bayi tawanke bakinta tayi
alwala ta fito, tana idar da sllh tashiga gyara
bedroom dinta ta tabbatar komai yyi mata
yanda take so ta feshe dakin da turaren da
anty nafisa ta nuna mata xata dinga sawa a
daki ta hada da room freshner snn ta shiga
wanka tana gama wankan ta wanke
bathroom dinta tsaf ta feshe ko ina da
freshner snn ta fito dakin, tana cikin fito da
kayan da xata saka taji an bude kofar, ta
juyaa tsorace tare da sakin abinda ke
hannunta a gigiceta fasa wani raxanannen
ihu tace "wayyoo Abbana nashiga uku,"
Zainab ta tsaya baki bude da mamaki tana
kallon intisaar, a hankali intisaar ta sulale
kasa ta xauna tare da dafe kirjinta da ya
kasa daina bugu da sauri,ta galla ma zainab
din harara duk da taji dadin ganinta tace "
dubeta don Allah, baki iya sallama bne
malama xaki tsorata mutane," zainab tayi
dariya tace "xa ma ki fadi gskya ne, wae ta
tsamman angonta ne, shine xata wani
wayance ma mutane" intisaar ta galla mata
harara da wasa tace" angon bnxa, meye
hadina dashi, " zainab ta tabe baki tace "
kya ji dashi dae," snn ta karasa cikin dakin
ta ajiye basket din dake hannunta da leda ta
shiga fiffito da kulolin dake cikin basket din
da flask,intisaar ta xauna gaban madubinta
tana shafa mai zainab ta dago tana kallonta
tace "kin tashi lfya amaryarmu," tayi kmr
bata ji ta ba, zainab tayi dariyar tsokana tace
"kice sae ynxu ma xakiyi sllhn, ina yayana,
nasan kin sa shi makara yau da gani,"
intisaar dae bata kara kallon inda zainab
take ba ta gama shafa mai ta shiga sa
kayanta wani material mai kyau orange n
milk colour,
.
Zainab ta sauka kicin ta dauko plates da
cups ta dawo dakin tana kallon intisaar
dake gyara fuskarta gaban madubi tace "
wae yaya fa?" intisaar ta baxa mata hannu
alamar ita ma bata sani ba, xainab tace
"joke apart intisaar da gske baya nn,"
intisaar tace " Allah ni ban gansa ba ma tun
jiya, daxu dae naji fitar motarsa" zainab ta
tabe baki tace "to Allah ya kyauta, kice jiya
ma baki ci 'yar kazar nn da madara ba"
intisaar ta sauko kasa ta xauna kusa da
xainab kmr xata yi kuka tace "inna fa?"
xainab tayi dariya tace "ke dae bari, ai yau
karfe 5 duk muka tashi a gidan nn wae xa
tayi maku waina kuma a murhu xatayi, snn
xata dama kunun gyada ta dafa muku
ruwan lipton hadadde, ae mun aikatu yau,
har da su farfesun kaxa da kayan ciki, duk
ga su nn" intisaar tayi dariya sosai tace
"Allah sarki innata, amma de ba yanxu xaki
tafi ba ko xainab?" xainab ta galla mata
harara tace "to uban me xan maki, ni de
daukokuloli ki juye abincin nn don dasu xan
wuce gida , kuma islamiyya xan wuce,"
intisaar ta kamo hannunxainab din hawaye
ya cika idonta tace "Zainab ni kadae ce a nn
tsoro nke ji wllh," zainab tayi dariya tace
"xaki saba ne ai, kuma naga ai yaya na
dawowa da yamma," intisaar ta goge
hawayen idonta tace " aa ni dae ki bari
anjima ki tafi don Allah," xainab tace to naji
je ki dauko abu na juye maki abubuwan nn,
intisaar tace "ni ban san ina ne kitchen din
ba ai," xainab tayi dariya tace "yaya bai xaga
dake gidan ba knn," intisaar ta harareta
tace"wnn yayan naki mutum ne," xainab ta
dinga dariya ta ja ta suka sauka falo suka
xaga ko ina na gidan, intisaar dae bbu
abinda ya burgeta game da gidan hasali ma
ita tsanar gidan tayi, dakinsa kadae taki
shiga duk da irin tilasta mata da xainab ta
dinga yi tace baxata shiga ba, xainab din
dae ta shiga ta fito.sae kusan karfe goma
suka karya da xainab, ta dinga ji kmr xainab
ta dawo gidan da xama kwata kwata. Karfe
sha daya xainab ta tattara ina ta ina taxata
tafi gida intisaar ta dinga kuka wae don
Allah kar ta tafi, xainab tayi ta kwantar mata
da hankali tare da assure dinta ae xata
kawo mata abinci da yamma.
.
Da yammar kuwa Zainab ta kawo mata
tuwan shinkafa da cous-cous sae dan
fankasau da miya kusan kala uku, sae
farfesun naman rago, intisaar tace " xainab
na safen da kika kawo fa na nn har ynxu, ya
xanyi da wa innan kuma" xainab ta harareta
tace "to shi kuma yayan fa, ai ba ke daya
inna ke yi ma ba, ke dashi ne," intisaar ta
tabe baki tace "to ai sae ki jira randa ya
dawo sae ki kai masa," xainab ta girgixa kai
tace "intisaar knn, baki san ke mace bace
kece xaki jawo hankalin mijin ki gare ki, duk
wani tsoro da fargaba ki ajiye sa gefe ki
daure....." intisaar ta dakatar da ita a fusace
"kinga idan baxa ki min maganar arxiki ba
kiyi shiru, ni fa ban dauke ya Aliyu matsayin
mijina ba fa, yanda aka tilasta masa aurena
nima tilasta min akayi, wllhwllh bana sonsa,"
xainab ta mike tace "to ai yyi kyausae kuyi ta
xaune a hkan, kinga tafiya ta sae da safe."
intisaar bata ce mata komai ba duk da bata
ji ddin tafiyartata ba har ta fita daga dakin,
karfe goma tana kwance kan gadonta rike
da littafin hisnul muslim tana dubawa taji
shigowar motar Aliyu, gabanta ya fadi ta
mike xaune ta kashe wutandakin gaba
daya, ta takure gefe daya xuciyarta na
mugun bugu, har taji ya hayo sama ya bude
dakinsaya shiga ya rufe. Ta sauke ajiyar
xuciya ta koma kangadon tayi kwanciyarta
ta lullube da blanket. Washegari tana kan
darduma tana tilawa bayan ta idar da slln
asuba taji fitan Aliyu da motarsa daga gidan,
a xuciyarta tace ae indae irin xaman da
xasuyi knn baxae dinga cin ubanta ba
Alhamdulillah.Yau kwanan intisaar hudu a
gidan Aliyu, amma ko sau daya basu taba
haduwa dashi ba, in ya fita tun bakwae na
safe baya sake waiwayo gidan sae
karfegoma wani lkcn ma har sha daya na
dare, ko kadan hkn bae taba damunta ba
don ita gaba ma ya kai ta, ita kam bata taba
tunanin Aliyu xae bar ta ta kai har wnn lkcn
a gidansa ba tare da ya cuceta ba, sae daefa
bai san cin ta da shan ta ba. Yanxu kam ta
fara kwantar da hankalinta a gidan ta fara
sabawa da xaman kadaici, dama yana fita
xata fito ta gyara ko ina na gidan ta share ta
goge snn tayi moppin, ta fito da kwanukan
da taci abinci a daki ta wanke a kitchen ta
gyara kitchin din ta tsaftace ko ina, ta kanyi
mamakin inda Aliyu ke cin abinci safe da
ranadon tasan shi ba gwanin cin abinci a
waje bane da daddare kuma yafi shan tea
ko coffee, indae ta shigo kitchen da safe ta
kan ga mug din da yasha coffee da daddare
sae ta wanke ta maida inda yake.
Duk safe da yamma inna na ba xainab
abinci ta kawo mata wani lkcin zainab ta
dan tsaya taya ta hira wani lkcin kuma tace
sauri take duk da tafi tsayawa ma da
yamma, don da safe tana xuwa islamiyya,
intisaar ta sa zainab ta kawo mata novels na
turanci dayawa don ita bata fiye karanta
littafin Hausa ba kuma kallo ishenta yake
don wani lkcin sae ta yini bata kunna tvn
dakinta ba, karatun da take yi yana matukar
taimakonta don yana debe mata kewa
sosai, wani lkcin idan ta gaji da karatun ta
kan tafi garden tayi xamanta tana kallon
tsuntsaye, yau ma kmr kullum intisaar na
falo tana goge gogenta da ta saba, wajen
karfe karfe sha daya na safe ne don Zainab
duk ta bata mata lkci ta cika ta da surutu da
ta kawo mata abinci da safe bata barta tayi
aikinta ba don bata fi minti goma da barin
gidan ba intisaar ta fara gyare gyaren gidan
har lkcin kuma kayan barci ne jikinta,
muryar Aliyu taji bakin kofa yana waya duk
da bae shigo falon ba amma ya bude kofar,
gabanta yyi mugun faduwa ta mike a
tsorace tayi bayan kujera da gudu ta
durkushe a wajen tana xare ido, taji ya
karaso cikin falon tare da rufe kofar, bata
kara jin takunsa ba ko ina yyi tsit, ta rasa
inda ya shiga, a hankali xuciyarta na
bugawa ta dan leko daga bayan kujeran da
take ta gansa tsaye kmr mai naxari yanabin
ko ina na falon da kallo, ta maida kanta da
sauri tare da toshe bakinta gudun kar ta
fasa ihu jikinta ya dau rawa, can dai taji
yana hawa stairs har taji ya bude kofar
dakinsa ya shige, ta mike tsaye da sauri
jikinta na rawa tayi hanyar stairs