Author : Khaleesat Haidar Category : Romance
na xaune falon inna
tana cin tuwa da lafiyayyan miyan vegetable
da inna tayi mata yaji
nama da kifi da ganda, sae tura abunta take,
ga farfesun kayan ciki
da na kai gabanta ga fura mae sanyi shima
duk a gabanta, inna ko
na xaune gefenta tana tayi mata hira tana
kyalkyala dariya, inteesar
dae hankalinta na kan abincinta har ta
manta rabon da ta ci tuwo
sae indomie kmr mayya kullum, tun safe da
inna ta ja ta tayo sashin
ta da ita bbu wanda yaga fuskar xuwa ya
samesu har Abba, Aliyu
kam Abba ne ya hanasa xuwa don yasan
halinsa, Haisam ma baram
baram suka yi da inna daga yaxo yi ma
inteesar fada, ransa a bace
ya bar falon, sallamar faruuq yasa inteesar
ta jawo hijabinta da sauri
don daga ita sae yar shimi, suka amsa masa
sallaman inna na washe
baki ya nemi guri ya xauna ya gaida inna ta
amsa cike da jin ddi ta
mike ta kwaso masa lemo a fridge dinta,
inteesar ta gaishesa tana
murmushi ya amsa ba tare da ya kalleta ba,
tace "ya faruuq Zainab
fa?" yace "tana lfya," ta ci gaba da cin
tuwonta inna nata yi masa
hira mara tushe sae binta yake da uhm, sae
da ya jira don kanta tayi
shiru snn ya hade rae yana kallon inteesar
yace "inteesar wajen ki
naxo," ta dago tana kallonsa hka ma inna,
yace "am vry disappointed
in yhu inteesar, never knew yhu 2 b
foolish...." da sauri inna tace
"meye wnn kke cewa, ka fada wanda xanji
mana," ya juya yana kallon
inna yace "Haba inna, ynxu abinda inteesar
tayi ta kyauta knn da ba
ki son a mata fada, rae biyu fa ta hallaka dan
wauta irin nata, kuma
ace baxa a mata magana ba" a fusace ya
karasa maganar, inna ta
dafe kirji kmr xata yi kuka tace "rae biyu fa
kace, dama yan biyu ne
knn?" faruuq yace "au ke da duk abinda ake
baki sani ba inna," inna
tayi narai narai da ido tace "ni ina nasani,
ynxu yan biyu ta xubar
faruuq, ko daya bae rage ba," ta juya tana
kallon inteesar dake ta
tura tuwanta abunta fuskarta a daure, can
ta juyo tana kallonsa tace
"to hka Allah ya kaddara sae a dau na
annabi, yarinya dae bata gama
mallakar hankalinta ba bare ace xa a mata
fada ynxu, kawae sae dae
ace Allah shi kyauta, su kuma Allah ya ji
kansu," faruuq don takaici
kasa cewa komai yyi, can dae yace "meyasa
xaki dinga cewa hka
inna, inteesar din ce yarinya ynxu," inna ta
hade rae tana kallonsa
tace "naga dae alamar kaima ka fara xama
munafuki, tashi ka ban
waje idan har wnn maganar ce ta kawo ka,
to jefar da ita kuke son
nayi kome, dama Allah yyi yaran baxa su
wuce wata uku a cikinta ba,
don hka ku shafa ma jikata lfya" faruuq ya
mike ransa a bace yace
"to inna, Allah ya baki Hkuri ni xan koma,"
tace "eh Allah ya kiyaye,"
ya juya ya fice daga falon, inna ta ja dogon
tsaki tace "munafukan
bnxa kawae, ci ki koshi kije ki kwanta ina
fatan dae jinin ya tsaya
gaba daya ynxu." Da daddare inteesar na
kwance gefen inna duk da
fankan dake aiki a falon tana tayi mata fiffita
suna hira, Abba yyi
sallama, inteesar ta mike xaune da sauri
tana kallon inna, inna tace
"tsaya tsaya kar ka shigo min," ta juya tana
kallon inteesar murya
kasa kasa tace "maxa tashi ki shiga daki," da
gudu inteesar ta shige
daki ta rufe kofa, inna ta rungume
hannuwanta tana sakace hakori
tace "yauwa xaka iya shigowa" Abba ya
shigo dakin da sallamarsa ya
xauna ya gaidata yana kallonta, ta amsa bbu
yabo ba fallasa, yyi
shiru na kusan minti biyar snn yace "baaba
fateema fa" inna ta hade
rae tana kallonsa tace "ya aka yi," cikin fada
Abba ya fara magana
"haba baaba, ni ynxu kina gwada ma yaran
nn bani da iko da su ne
kome, ya yarinya tayi laifi irin wnn nasa a
kawo min ita gida ki
kunshe ta a daki bbu wani bayani, kuma ke
ba yi mata xaki yi ba,
ynxu kina gwada mata abinda tayi tayi dai
dai knn kome," inna ta
marairaice ganin yanda ransa ya baci tace
"to wae Bukar maganar nn
bata wuce bane ko me, naga dae ya ya ba
dawowa xasuyi ba," Abba
ya shiga kiran inteesar a fusace "fateema
fateema," kmr munafuka ta
fito da hijab har kasa, inna se ca take baxata
fito ba koma inteesar,
Abba yace "maxa ki wuce falona ki jira ni," a
fusace yyi maganar don
hka bata saurari inna ba ta fice kmr
munafuka gabanta na faduwa,
inna tace "to wllh sae na bi ku," bae tanka ta
ba ya fice, ta fixgi
gyalenta da sauri ta fice ta bi bayansu,
gaban inteesar yyi mugun
faduwa ganin su Hajiya da ma momynta har
ma da Anty nafeesa da
ta bi ta da harara a falon ashe ta xo gidan,
ko inna ma bata sani ba,
inteesar ta saci kallon Aliyu dake xaune
gefen Haisam, ta rasa inda
xata xauna don kowa haushinta yake ji a
falon, Abba ya shigo ya
xauna yana kallonta ta sunkuyar da kanta
har lkcn tana tsaye, cikin
ikon Allah sae ga inna ta shigo falon tana
haki, tana kallon Hajiya
tace "ke tashi ki ban waje in xauna," Hajiya
bata yi musu ba amma in
ranta yyi dubu ya bace, ta mike inna ta
xauna tace "xo xauna nn
inteesar," inteesar ta xauna gefen inna,
Hajiya kuma ta nemi wani
wajen ta xauna ranta a bace. Inteesar ta
daga kai a hankali ta saci
kallon Aliyu taga kallonta yake, duk ya koma
kmr wani mara lfya, ta
dauke kanta da sauri shima hka
.
A nutse Abba ya kira sunanta "fateemah," ta
dago a hankali tana kallonsa, ya sauke ajiyar
xuciya yace "ko da yake ma bari na fara ta
kanki baaba," inna na kallonsa tace "eh ina
ji," yana kallonta yace "Baaba kar ki fara
magana nn ba tare da ance kiyi ba, duk me
xaki ji a nn don Allah karki bude bakin ki,
idan ana bukatar cewar ki xa'a sanar da ke,
don Allah dae nace," inna ta tabe baki tana
girgixa kafa, ya maida dubansa ga Inteesar
da ta sunkuyar da kanta yace "fateema,"
wnn karan kasa dagowa ta kallesa tayi, bae
damu ba ya ci gaba "Ashe ke dama mara
hankali ce bansani ba," inna tayi karaf tace
"kmr yaya," Abba ya hade rae yana kallonta,
ta daga hannu da sauri tace "to nayi shiru,"
Abba na kallon Inteesar yace "ynxu abinda
nake so dake shine kawae ki gaya min
asibitin da kika je," Hawaye ya cika idonta ta
kasa cewa komai, cikin daga murya Abba
yace "ba magana nake maki ba," a hankali
Aliyu yace "ae Safeena ce tayi mata jagora
wae," a fusace inna tace "ga magana nn
xaku tsaya kuna wani lauyewa, ni dae nasan
jikata baxata iya aikata wnn danyan aikin da
kanta ba" Abba yyi shiru yana kallon Aliyu
snn yace "kae wa yaga maka hka," Aliyu
yace "ita da bakinta ta fada," inteesar ta
watsa masa harara tace "ni ba muyi hka da
kai ba, kuma safeena bata yi min ko wani
jagora ba ni da kaina na tafi inda naje,
hasalima bata sani ba," Aliyu ya yo waje da
ido da mamaki yace "kika ce me?" ta xaro
masa ido tace "ehh" ya dafe kansa yace
"innalillahi wa inna ilaihi raji un, kika sa naje
na ba yar mutane takarda ashe sharri kika
mata" Abba yace "takardar ka kai mata?"
Aliyu ya kasa cewa komai sae kallon inteesar
da yake, a rude Hajiya tace "kana da hankali
kuwa Aliyu, ka saketa fa kace?" Abba yace
"saki nawa kayi mata," Aliyu ya sauke ajiyar
xuciya yace "daya," snn ya ciro pen daga
Aljihunsa ya mike ya shiga dakin Abbansa
duk aka bi sa da kallo ya fito rike da farar
takarda ya isa study desk ya duka xae yi
rubutu Abba yace "meye hka kke yi Ali," ya
dago bbu yabo bbu fallasa yace "ita ma
rubuta mata nata xanyi Abba" Abba ya daka
masa tsawa "kana da hankali kuwa, a
gabana don baka da kunya xaka dauko
takarda kana gaya min maganar bnxa,"
cikin daga murya Abba yace "dawo nn ka
xauna," Hajiya tace "kambu, ae wlh baka isa
ba Alhaji, ita wancan din da ya saka ance
maka gata ne bata da, ae ita ma Wllh sae ya
rubuta mata nata, na rantse," Abba ya mike
a fusace yace "fice min a falo Aisha, nace ki
fita," ta mike tace "ae ko baka fada ba fita
xanyi, amma wllh kmr yanda tayi makirci
tasa ya saki matarsa ta arxiki ita ma sae ya
saketa, ae dama idan bata xama makira ba
sae Allah ma ya tambayeta, abu a jini," ta fice
tana huci, inna tace "shegiya yar wahala, ae
in Aliyu ya saki Inteesar yau duk kuma sae
nasa dana ya rubuta maku takardarku wllh
wllh," inteesar ta fashe da kuka tace "Abba
ni ka bar shi ya rubuta min takardata don
Allah don Annabi," Abba ya daka mata tsawa
a fusace "rufe min baki, stupid" Anty
Nafeesa kam kasa cewa komai tayi sae
kallon inteesar take, momy dama hankalinta
na kan TV, Abba yyi shiru na wani dan lkci
snn yana kallon Aliyu yace "sae kaje ka
mayar da matarka," Aliyu bae ce komai ba
sae da har lkcin kansa a kasa yake da
ganinsa kasan ran maxa ya baci, Abba ya
hade rae yana kallon inteesar yace "ynxu
dalilin cire cikin jikinki kawae nake son ki
gaya mana gaba daya mu ji," hawaye ya cika
idon Inteesar tayi shiru kanta a kasa, har
sae da Haisam ya daka mata tsawa, "ba
magana ake maki ba," a fusace inna ta mike
tace "ohh ni yau naga tsiya xasu kashe min
jika, kuma sun hanani magana " ta fashe da
kuka xata bar falon, Abba yace "haba baaba
ki dawo muji daliin da yasa tayi hka, ae bbu
wanda yyi mata wani abun a nn," da kyar
aka lallaba inna ta dawo ta xauna tana
share hawaye, Abba yace "muna jin ki
Fateema," inteesar ta dago kanta a hankali
tana kallon Aliyun, taga shima kallonta yake,
ta kauda kanta tace "sbda bana sonsa
shima kuma baya sona yasa nayi hkn Abba,"
ta fashe masu da kuka ssae tace "Abba
tunda na taso ya Aliyu ke cutata a gidan nn,
tun ban san kaina ba, ban san me nayi masa
ba ko dan ba gidan ubana bne, ya tsaneni
kuma baya son bude ido ya gan ni cikin
gidansu, ko uwar da ta haifeni ma bae bari
ba, idan an manta randa ya daga hannu xae
mareta to ni ban manta ba, kuma har gobe
baxan manta ba, ban san me muka yi masa
ba, duka bbu wanda ban sha a hannun
Aliyu ba, idan ba a manta ba wani rashin
lfya da nayi na kwana da kwanaki shi shine
sanadin sa, amma ban fada ma kowa ba,
har ka hada mu aure Abba, kuma tunda ka
hada mu abba ko sau daya ban taba jin
ddin xaman gidansa ba, sae nayi sati biyu
ban daura idona a kansa ba, bae san ci na
ba bae san sha na ba, kullum a wahale nake
cikin gidan, to a hka yake son na haifa masa
yara, wllh Abba bana sonsa ka taimakeni
kasa ya bani takardata ynxun nn, biyayya
kawae yyi maka yake xaune da ni gida daya
a matsayin matarsa," ta fashe da
matsanancin kuka takasa ci gaba, tun da ta
fara magana Aliyu ke kallonta baki bude.
Ganinbbu wanda ya iya cewa komai a falon dondukjikinsu yyi sanyi ya sa inteesar ta tsagaita
kukan
da take ta cigaba "snn Abba ni bada
yardana ya
sake aure ba, hasalima ni ban san xae yi
aure ba
sae ranar da ya kawo ni gunka da daddare
kke
tambayata ko nasani, to a nn ne ma nasan
aure
xae yi, kuma dama tun a hanya yyi threatn
dina
kan cewar ko me xaka tambayeni nace
nasani,
kuma Abba har yau yaki daukar batun
karatuna
da muhimmanci da nayi magana sae ya
dinga
hantarata wae baxan iya course din da nace
nake so ba, kuma Abba da yake cewa na
xubar
masa da ciki a tambayesa ko kula dani da
cikin
yake, Abba sae nayi kwana uku ban gansa
ba
gashi bbu abinda nake iyawa kullum a
wahale
nake kwana nake yini a gidan ga kuma
yunwa,
tunda ba iya girkin nake ba," tayi shiru tana
share
hawayenta snn a hankali tace "lastly Abba
kayi
hakuri ba rashin kunya nake maka ba,
amma ka
tausaya min kayi masa magana ya sauwaka
min,
don baxan koma gidansa ba wllh na gama
aurensa," Aliyu ya mike yana mata wani
mugun
kallo yana huci yace "munafuka,
makaryaciya
kawae, ki xo ki shake ni na baki takardar
taki
kuma wllh sae kinyi da kin sanin xubar min
da
ciki," ya juya xae bar falon Abba ya dakatar
da
shi a fusace, inteesar ta fashe da kuka tace
"wllh Abba kace ya bani takardata bana
auren
kuma, bana sonsa," Abba yana kallon Aliyu
yace
"dawo ka xauna," ya kai minti kusan biyar a
tsaye kmr baxae xauna ba, sae da Anty
Nafeesa
tace "ba magana ake maka ba ka tsaya ma
mutane kallon rainin wayo," ya juya ya
kalleta,
snn ya koma inda yake ya xauna yana ma
inteesar wani irin kallon, da ganinsa kasan
ran
maxa ya gama bacewa, Abba yace "cikin
maganganun da Fateema tayi a nn akwae
wanda
xaka karyata," ya kauda kansa bae ce komai
ba
sae huci da yake, Abba yace "gud, dama tun
ba
yau ba nasan halinka, na kuma san xaka iya
aikata duk abinda fateema ta lissafo a nn,
kai
kam ban san wani irin mutum bne Aliyu,
kuma
gwara da Fateema ta gaya min abubuwan
da ta
dde tana boyewa a cikinta tana cutar
kanta," ya
juya yana kallon Inteesar yace "amma
fateema
ke abinda kika aikata a ganin kinyi dai dai
knn,
me xaki ce ma mahaliccinki, ashe dama
karamin
tunani gare ki ban sani ba" inteesar dai
kanta na
kasa tana hawaye ta kasa cewa komai, Abba
ya
ci gaba, "a nan kin nuna kmr rashin kulawar
da
yake nuna maki ne yasa kika aikata abinda
kika
aikata, to Fateema baki san hanyar gida bne,
ko
in kin xo akwae wanda xae ce maki don
me" a
hankali tace "Abba banyi wnn tunanin ba,"
Abba
ya girgixa kai yana kallon Aliyu yace "to
malam
rubuta mata takardarta, Allah ya hada kowa
da
rabonsa, ni nayi kuskure tun farko na baka
auren
fateema duk da ka nuna min baka sonta"
Aliyu
ya juya yana kallonta, ita ma kallonsa take,
ya
maida dubansa ga Abbansa yace "srry ba
rashin
kunya nake mka ba Abba, amma taxo ta
shake ni
ta kwata, ko kuma ta saki kanta da kanta,"
yana
kai wa nn ya mike yana huci xae bar falon,
Abba
ya daka masa tsawa yace "don uwarka ni
nayi
maka magana ko fateema" Inna ta mike a
fusace
tace "yau naga tsiya, yarinya tace bata son
aurenka ka sallameta mana ko ana yi dole
ne, ae
ba rasa manema tayi ba, ko gobe ta fita titi
santalelen yaro me katuwar mota wanda ya
fi ka
komai ne xae biyo ta wllh, yo tsami gaye da
kai
idan ba tsautsayi ba ma me xae kai ta
aurenka
sai tsayi ba hankali kmr bishiya," abun
dariya
abun takaici, a walakance Aliyu na kallon
inna
yace "ae sae ki rubuta mata sakin ki bata, ko
kuma ku hadu ku shake ni ku karba," yyi
tsaki a
fusace ya juya xae fita Abba yace "kar ka
kuskura ka fita daga falon nn, kanka rawa
yake
Aliyu, ita mahaifiyar tawa kke gaya ma
magana"
inna ta fashe da kuka tace "yo sabon abu ne
wnn, ae sae Allah ya mana hisabi da Aliyu"
Haisam ya mike ya fice daga falon, hkn ma
Momy, ran Abba a bace kuma a nutse yana
kallon Aliyu yace "bani takardar Fateema
ynxun
nn Ali kar na nuna maka d odza side of me,"
cikin tsawa ya karasa maganar, Aliyu yyi
shiru
yana kallonsa yana huci, inna tace "ba
magana
ake maka ba salubabbe kawae," ya juya
yana
kallon inna tace "daina kallona Munafuki
kawae,"
inteesar dae kanta na kasa, ya juya ya kalleta
snn yyi huci me xafi ya ciro takardar da ke
Aljihunsa da pen ya daura takardar kan
hannun
sofa, snn ya duka ya fara rubutu a jiki.
Inteesar
ta dago a sanyaye tana kallonsa hawaye na
bin
kuncinta, Abba ma kallonsa yake ko kiftawa
baya
yi, hka ma Anty Nafeesa, inna tayo waje da
ido
ta dafe kirji tace "lah rubutawa xae yi
Bukar"
.
.. Inna ta fashe da kuka ta mike tsaye tana
cewa "Bukar kayi shiru, kaga fa rubutawa
yake, lah ha ila ha ilallahu mahammadur-
rasulillahi sallallahu alaihi wassallama, Bukar
kayi wani abu mana" Abba kam kasa cewa
komai yyi sae kallon Aliyun yake, Anty
Nafeesa ta jinginar da kanta jikin kujera
tana kallon ikon Allah, har Aliyu ya gama
rubutunsa ya mayar da pen din cikin
aljihunsa yana kallon Abbansa yace "gashi
nn na rubuta mata," Abba yyi murmushin
takaici yace "to ka kyauta," ya dauke kansa
ya shiga linke takardar neatly yana kallon
inteesar dake kallonsa har lkcn tana
hawaye, ya karasa gabanta yana mata
mugun kallo ya jefa mata takarda snn ya
juya xae fita inna ta bi sa da gudu ta cakumi
kwalarsa tace "don uwarka jikartawa ka
mayar baxawara, to Allah ya isa bamu yafe
maka ba, sae Allah ya saka mana," Abba yace
"ki rabu dashi baaba," inna tace "naki din,
dama nasan har da hadin bakinka ae," ta
fashe da wani matsanancin kuka ta xube
wajen tana daddaga hannu sama, Aliyu yyi
yar dariya rainin wayo ya juya ya fice daga
falon, sae a snn umma dake xaune har lkcn
bata ce komai ba ta mike ta bar falon
xuciyarta fal murna don dama abinda take
jiran gani knn, kuma ta gani, ynxu kuma xa
taje tayi break din ma Hajiya gud News din,
Abba ya sauke ajiyar xuciya yana girgixa
kansa, Anty Nafeesa ta mike ta nufi gaban
inteesar ta dauki takardar da Aliyu ya jefa
mata ta koma ta xauna tana warware wa,
inteesar kam hade kanta tayi da gwiwa tana
rera kuka a hankali, Anty Nafeesa ta gama
karanta content din takardar ta ajiye kan
kujera kusa da Abba ta mike ta fice daga
falon, inna ta mike ta dago inteesar tace
"tashi mu je, sae me don ya sake ki, abinda
ynxun nn kina fita masu mota xa su biyoki,
uban waye xae kalleki yace kin taba aure
idan ba dan bakin ciki ba, ae gwanda da
kika kwabar da cikin don da ganin
jarababbun yara ne, mu je kawae Allah ya
isar mana" sae a snn inteesar taji sanyi ta
mike tsaye inna ta shiga share mata
hawayenta, Abba kam idonsa na kan
takardar da Nafeesa ta ajiye masa bayan ya
dauka, yana gama karanta cntent din ya
sauke ajiyar xuciya tare da jinginar da kansa
jikin kujera yace "gashi nn fateema," inna ta
ja hannunta xasu fita tace "rabu da shi
da'alla muje me xaki yi da shi su da suka sa
shi ya sake ki ae sae su cinye," Inteesar ta
kasa bin inna ta koma a sanyaye ta karbi
takardar a hannun Abba, Abba yace "kiyi
hkuri Fateema ni na ja maki komai," ta
kirkiro murmushi ta karbi takardar inna tayi
tsaki ta ja ta suka fice daga falon tana cewa
"yo idan bata yi hkurin ba ya ake son tayi
dama bayan an gama cutarta," inteesar dae
jikinta a mace suka isa falon inna, inna ta
karbe takardar hannunta da ta kasa
dubawa har lkcin, tayi michi michi da ido
tana kallon rubutun ita nn karatu take kmr
tasan me aka rubuta jikin takardar tayi tsaki
ta cukuikuye takardar ta jefar bakin kofa
tace "shege kawae rubutun ma kmr ta
agwawa," ta juya tana kallon inteesar da ta
xauna kan kujera ta kura ma TV ido tace
"maxa je ki kiyi wanka ki xo ki kwanta, kar
ki sa komai a ranki kinji" a sanyaye inteesar
ta mike ta shiga dakin inna tayi kwanciyarta
kan gado kawae don baxata iya yin wankan
ba.
.
Washegari da safe inna na share falo ta ga
takardar da ta jefar bakin kofa, tace "na
share
wn shegen takardar Inteesar," inteesar da
har
lkcn ke kwance a daki tayi shiru kmr baxata
ce
komai ba sae kuma tace "ki ajiye kawae kar
ki
share," inna na gama sharan ta hada mata
ruwan wanka ta kai mata bayi duk tana
kwance, inna tace "maxa ki tashi kije kiyi
wanka kadda ruwan ya huce," ta mike
xaune
da kyar ta fara cire kayan jikinta xata shiga
wankan inna tace "to me xan hada maki na
kalaci kan ki fito," inteesar ta dan yatsine
fuska
tace "ni waina kawae xa a siyo min," inna
tace
"yo ae