Author : Khaleesat Haidar Category : Romance
har ya fita, ya
fita da minti biyar momy ta shigo, xani ne
kawae jikinta, kunya ya kamata ta rufe ido
da
sauri kmr me bacci. Kullum sae Aliyu ya xo
sashinsu da safe da dare, ya kan siya masu
fruit ko nama, duk da ko kadan momy bata
sake masa, sae dae yyi ta xamansa a falo
idan ta fita sae ya shiga dakin, laulayin
inteesar ya dawo sabo kullum cikin wahala
da
amai take yana mugun tausayinta har mmki
abun yake bata, duk da tasan duk sbda
cikinsa ne, wani lkcin idan ya shigo gidan
sae
karfe sha daya yake wucewa duk da bbu
wanda yasan yana xuwa har inna, idan
kuwa
tayi bacci me ddi to a jikinsa ne, don yana
xuwa ya rungumeta bacci yake xuwa mata,
wani lkcn ma sae dae ya kwantar da ita
kawae yyi ma momy sallama ya wuce, duk
dare Abba ma na shigowa dubata hka
Haisam, inna kam bata san ashe jarababbun
yara na makale jikin inteesar ba, su kansu
Hajiya basu sani ba. Yau ta cika sati biyu gun
mamanta, momy na kula da ita ssae kuma
tana tausayinta ganin yanda cikin ke bata
wahala, karfe hudu na yamma Aliyu ya shigo
gidan ranar yaci sa'a bbu kowa tsakar gida
ya
nufi sashinsu inteesar, xaune ya tarda ta da
momy a falo ta sata gaba sae ta shanye
kunun da ta dama mata don bata cin komai,
ya gaida momy tayi kmr bata ji sa ba ta fice
daga falon, ya dawo gefen inteesar ya shiga
lallabata yana bata kunun har ta sha rabi,
snn
ya ajiye ya rungumota jikinsa yana buga
mata
baya kar tayi amai, tayi lamo tana sauke
ajiyar xuciya, a hankali yace "fateema," ta
dago tana kallonsa ya mayar da kanta
kirjinsa yace "gida nake son tafiya dake
fateema, nasan sae da amincewarki Abba
xae
yarda na daukeki, ki tausayamin plss my
wife"
.
Inteesar ta kwace kanta daga rungumar da
yyi mata tana
masa mugun kallo tace "waye wife din taka?
Sae yau da kaga
ciki a jikina kasan ni wife dinka ce, to ni ba
matarka bace wllh,
bari ma kaji abinda baka sani ba ya Aliyu,
wllh bana sonka
bana sonka, tun ynxu nake son mu ajiye
yarjejeniya da kai a
kan cikin nn," yyi shiru yana kallonta
xuciyarsa na tafarfasa,
tunanin me yake hka har ya kai sa ga
kiranta da wife dinsa, ya
rike temper dinsa yana kallonta bbu yabo
bbu fallasa yace
"yarjejeniyar me," tana masa wani irin kallo
tace "na farko ina
haifa abinda ke cikina xaka bani takardata,
na biyu kuma ni
baxan shayar da danka ba tun ynxu ka sani,
idan ka yrda da
deal din nn, to na yrda xan bar cikin nn,
idan kuma akasin hka,
to wllh wlh xan sake komawa a cire min
cikin kuma baxa ku
sake gani na ba," ya sauke ajiyar xuciya
yana kallonta, ransa
yyi mugun baci, amma da yake yaransa
kawae yake so, sae
yace "ok na yrda xan baki takardarki kuma
baxa ki shayar da
su ba," tace "ka rantse da mahaliccinka," yyi
shiru yana
kallonta snn yyi wani irin murmushi yace
"na rantse," tace
"kuma ni daga ynxu ka daina xuwa gurina
na yafe maka,"
yace "ok ngdd," snn ya mike ya fice ba tare
da yyi mata
sallama ba ma, ta mike ta koma daki da kyar
ta kwanta kan
gado ta lumshe idonta dake cike da hawaye,
yes hkn kadae ne
mafita a gareta, Aliyu bae cancanci ta xauna
da shi ba ko
kadan, idan yana shisshige mata hka xata
iya canxa ra'ayinta.
Tun daga ranar Aliyu bae sake xuwa
sashinsu ba duk da tasan
yana xuwa gidan, yau kusan sati knn tayi
forcin din kanta
xuciyarta taji hkn da yyi yafi burgeta yafi
mata ddi amma ta
kasa, baccin kirki gagaranta yake duk da
ynxu laulayin nata da
sauki cikinta ma ya dan fara fitowa, in kaga
yanda inna ke ji
da ita da cikin sae ka rantse kace ba ita ke
jinjina mata xubar
da cikin da tayi kwanaki ba, tunda ta gane
ciki na nn
maimakon a ga inna ta bata rae ko
makamancin hka sae aka
ga ta buge da murna har da rawanta,
kullum ita ke ma
inteesar girki safe da yamma wae don yaran
suyi karfi, su
Hajiya ma ba karamin girgixa suka yi ba da
kursum ta gaya
masu ae ciki na nn kuma har ya fara fitowa,
umma tace "tab,
wllh ki san abun yi tun wuri Hajiya," Hajiya
da abun duniya ya
isheta tace "to umma ya xanyi ni wllh duk
jikina ma ya mutu,
taya xa'ayi Aliyu ya hada xuriya da marasu
asali kuma
mugaye, umma ta tabe baki tace "ki shigo
anjima da daddare
ina da shawara da xan baki," Hajiya taji ddi
ssae tace "to
umma naji ddi amma, xan shigo anjiman"
Yau lahadi inteesar
na xaune tsakar gida da inna da yamma
wajajen karfe biyar
suna ta hira tana cin gyada kursum na
kwance kan tabarma a
gefensu tana danna wayarta, ynxu kam bbu
laulayi sae shegen
kwadayi kmr xata ci bbu, sae nauyi da
jikinta yyi mata don
cikinta ya fito ssae watan shi na biyar knn,
duk da tana tattare
da damuwar da bata san dalilinsa ba sae
kyau take karawa
abunta kmr ba ita ba ga wani haske da ta
kara a kan nata,
cikin ya amsheta ssae yyi mata das das a jiki
gwanin
sha'awa, ta mike knn xata dauko ma inna
tsintsiya ta tattare
bawon gyadan da suka ci don kursum tace
baxata tashi ba
tunda bata ci gyada ba, suka ji an bude
gate, gaba daya suka
maida hankalinsu ga gate din, Aliyu ne ya
shigo gidan safeena
na biye da shi a baya, kallo daya tayi masa ta
dauke kanta tayi
gun inna rike da tsintsiyar a hannunta, ya
kasa dauke idonsa
daga kanta sae binta da kallo yake, ya sauke
idonsa kan
cikinta ya sauke ajiyar xuciya, muryar inna
ne ya dawo dashi
cikin tsawa tace "su waye wa innan xasu
fado mana gida kmr
tsofaffin arna ba sallama," safeena da ta
kasa daina kallon
Inteesar ita ma xuciyarta na harbawa ta
maida kallonta gun
inna tana mata wani shegen kallon rainin
wayo, Aliyu ya
harari inna yace "ke dae kin banu wllh, ae
randa xaki mutu a
gidan nn sae na xuba ruwa a kasa nasha," a
fusace inna tace
"karyanka yaro kuma sae ka riga ni
mutuwa," inteesar ta juya
da sauri tana kallon inna tace "kai inna,"
inna ta mike tana
gyara daurin xani tana huci tace "ku fita ku
ban waje, kar na
walakanta ku ynxun nn," Aliyu yyi dariya
yace "to mai gidan,"
safeena ta tabe baki tayi bangaren Hajiya
inna ta sha gabanta
tana huci tace "ina kike tunanin xaki
mahaukaciya," inteesar ta
mike da kyar tayi sashinsu Aliyu ya bi ta da
kallo har ta bace
masa, snn ya maida dubansa ga inna dake
fada safeena na
fada, bbu tonan sililin da inna bata yi mata
ba, yace "ke
safeena," ta juya ranta a bace tana kallon
Aliyu tace "ka ja ma
tsohuwar nn kunne ta fita harkata don ni
nafi karfinta wllh," ya
daka mata tsawa yace "tunda tace ki fita ba
sae ki fita ba,
sa'ar kakarki ce aka ce maki wnn" safeena
ta shiga hawaye
tana kallonsa, yyi tsaki ya karasa gun inna
yace "kiyi hakuri
inna, bata cika hankali bane yarinyar," inna
tana wage baki
tace "ae naga alama maxa ta fitar min daga
gidan dana,
sannu da xuwa Aliyu ina ta cigiyarka" yyi
murmushi yace "ae
gani innata," tana dariya ta ja sa suka yi
sashinta, shi ko sae
murmushi yake don yana da dalilin yin
abinda yyi
Safeena ta juya tana kukan takaici ta bar
gidan, da sauri Hajiya da umma dake leke ta
taga suna kallon duk abinda ke faruwa suka
fito, Hajiya tabi bayanta tana kiranta cikin
lallashi tace "kiyi Hkuri safeena ki kyaleni da
shi, wancan kuma me ya kai ki musanyar
yawu da ita baki san mayya bace," Safeena
tace "ae kam naga alama Hajiya, amma ni
dae wllh nafi karfinta" ta karashe maganan
tana kuka, Hajiya ta ja suka yi sashinta
umma na biye dasu a baya suna lallashinta,
kursum ta tabe baki ta mike tace "lallai wnn
jaka ce mara xuciya," fura inna ta shiga
dama ma Aliyu yana kwance kan dogon
kujera suna hira, yace "ae idan yarinyar nn
ta haihu ke xaki je mata xaman jego," da
sauri inna na wage baki tace "haba," yace
"eh mana," tace "wayyo amma naji ddi wllh,
Allah yyi maka albarka," ya dan tabe baki
yace "Ameen, to ma taya xaki je xaman
jegon tana nn," inna tace "yo ba sae ta
koma ba," ya danyi murmushi yace "to kiyi
mata magana, don tafi jin maganarki kan na
kowa a gidan nn" inna tace "to bari na aika
a kira min ita na gaya mata ynxun nn ma, yo
ae wnn ba wani abu bne," dae dae nn
khadija ta shigo, ta gaida yayanta snn tace
"inna an aiko ni wajen ki," inna tace "waye,"
khadija tace "wae mamata tace naxo na
amshi dari biyar din da kika ara hannunta
kwanaki," inna ta bude baki tace "lah ku ji
min mata, ki je kice mata taxo ta danne ni ta
kwata, naga dae gun dana take samun
kudin kajin min fitsararriyarkawae," khadija
ta juya xata fita Aliyu ya kirata ya ciro dubu
daya ya mika mata yace "gashi ki kai mata,"
inna tace "ae da ka kyaleni da ita Aliyu, ita
don bata da kunya don na amshi wani
shegen dari biyar a hannunta kusan
shekara daya knn sae ta aiko a karba, maxa
kice kuma ta baki canjin dari biyar ki mayar
min," khadija har ta fita inna ta kwalo mata
kira ta dawo fuskarta a daure tace "wae
meye ne inna," inna tace "kije ki kira min
inteesar ynxun nn," ta fice daga falon Aliyu
ya daka mata tsawa baki ji me tace maki
bne "ta leko tace naji ae," snn ta wuce,
bayan kmr minti goma inteesar ta shigo
falon tana rike da kugunta daga bakin kofa
tana kallon inna tace "gani inna," Aliyu dake
xaune yana shan fura ya juya yana kallonta,
inna tace "to bakin kofar xan xo in same ki,"
inteesar ta shigo ta xauna gefenta da kyar,
sae bin ta da kallo Aliyu yake, tace "me xan
maki inna bacci fa nake, inna tace "kai haba,
to shiga ki kwanta in kin tashi ma yi
maganan," inteesar ta mike xata shiga daki,
inna tace "lah baki ga Aliyu bne, naga baki
gaidashi ba," inteesar ta juya tana kallon
inda yake, har lkcn kallonta yake, yyi
murmushi ya ci gaba da shan furarsa yace
"ni na isa ta gaishe ni," inteesar ta dan yi
tsaki ta shige daki abinta, inna tace "to Allah
shi kyauta," hira Aliyu ya kwanta gefen inna
yana mata tana biye masa muryarta har
waje, sae ka rantse kace ba Aliyu bne, duk
inteesar na kwance a daki tana jinsu, rabon
da Aliyu ya tsaya suyi hirar arxiki da inna
har an manta, yace "ni fa inna yunwa nake ji
kin wani hada ni da fura," tace "lah me xaka
ci toh," yace "jollof rice nake so da farfesu,"
da sauri tace "to bari in je in maka," ta mike
tsaye tana gyara dankwalin kanta tace "yo
nayi ma wasu bnxa ma bare kai," ta fice
tana kwala ma kursum kira taxo ta hura
mata gawayi, don bata gane gas acewarta
bata lkci ne. Aliyu ya juya yana kallon kofar
dakin kmr ya shiga ya fasa, yana ta danne
dannen wayarsa amma lkci lkci yakan juya
ya kalli kofar dakin, inteesar taji shirin yyi
yawa, wata xuciyarta tace ta leka taga ko
yana falon, a hankali cikin sanda ta isa bakin
kofa ta dan bude labulen a hankali tana
lekensa, shima ya juya knn yana kallon kofar
dakin xuciyarsa na son ya shiga, suka hada
ido, ta sake labulen da sauri yyi murmushi
bae dae ce komai ba, ganin xuciyarsa ta
kasa hakura da shiga dakin kuma baya so
ya shiga yasa ya mike da sauri ya fice daga
falon yyi sashinsa. Ko da inna ta shigo falon
tana kiran inteesar ta fito ta ci abinci da
xafinsa, da sauri ta fito kmr jira take, taga
inna kadae ne xaune falon, tace "wae ni
kika ma girki," inna tace "aa Aliyu nayi ma,"
inteesar tace "to ina yake," inna tace "ae ni
da kaina na kai masa yana kwance a
dakinsa yaron kirki." inteesar bata ce komai
ba ta dauki furan da ya rage ya rufe ta shiga
sha, inna tace "ke dae kin banu da kwadayi,
naki ne," ko kallonta inteesar bata yi ba ta
shanye ta ajye kofin, snn ta fara cin
abincinta, ta gama cin abinci knn, khadija ta
shigo dakin tace "wae ina furan ya Aliyu"
inna tace ahaf gata nn ta shanye khadija
tayi tsaki ta juya ta fice. Karfe tara inteesar
tayi ma inna sae da safe tayi sashinsu, har ta
wuce bangarensu Aliyu ta dawo tana lekan
ko yana nn ko ya tafi, ita dae bata ga alaman
ya tafi ba kuma bata ga alaman yana nn ba,
ta karasa bakin kofar a hankali da yake basu
kunna bulb din wajen ba ta durkusa tana
lalube ko xata ga takalminsa, dae dae nn
aka bude kofar Haisam ya fito, daga ita har
shi sae da suka tsorata. Ashe Aliyun ma na
kallonta daga bayanta ya fito daga
bangaren Hajiyarsa knn.
.
Haisam yace "me kike yi a nn Inteesar," ta ji
kmr ta nutse wajen don kunya ta fara kame
kame, Haisam yyi dariya yace "to ae baya ciki
ya fita sae dae in xaki shiga ki jirasa," kmr
xata yi kuka tace "wayyo ni ya Haisam abu
na
ne ya fadi nke nema," bata jira me xae ce ba
ta juya da sauri xuciyarta a dagule xata bar
wajen ta kusan cin karo da Aliyu dake tsaye
har lkcn yana kallonta, gabanta yyi mugun
faduwa, tabi gefensa da sauri xata wuce ya
rikota, Haisam dae yyi gaba abinsa yana
dariya, ta buge masa hannu ta daure fuska
tace "meye hka malam," dariyarsa mai kyau
yyi snn yace "me kike bukata daga gare ni
da
kika biyo ni," ta fashe da kukan takaici tace
"waye ya biyo ka, Allah ya isa na, da'alla ka
sake ni na wuce don naxo neman abu na
shine na biyo ka," dariya ya dinga yi har da
buga bango yace "ae nine abun naki, ni kika
xo nema 4 sure na sani," ta fixge hannunta
xata bar wajen yyi saurin rikota ya bude
kofar
falon ya ja ta suka shiga, kuka ssae take yi
kuma na takaici, ka kyaleni ya Aliyu bana
son
hka, yyi murmushi ya rufe kofar falon da key
ya karaso bayanta ya tsaya a hankali yace
"am srry fateema, i also feel...." sae kuma yyi
shiru ta juya tace "ka bude min kofa in fita
nace maka," bae ce mata komai ba ya
dauketa
sae bedroom yace "ki bari in gaisa da
yarana,"
kuka ta dinga yi tana jin haushin kanta ita
kam har ga Allah ganinta kawae tayi a bakin
kofar bata san ya aka yi ba, ya rufe kofar
dakin ya xaunar da ita kan gado yana
kallonta ya durkusa gabanta yace "its High
tym mun fahimci juna fateema," cikin tsawa
tace "wace fahimta kuma, ka bude min kofa
in
fice daga dakin nn" yyi murmushi ya kauda
kansa yace "ok," snn ya mike ya bude mata
kofar dakin da sauri ta fita, ya bi ta baya ya
bude mata na falo ma ta fice, snn ya mayar
da kofarsa ya rufe. Ko barin wajen bae yi ba
ta fara buga kofar da sauri, ya bude yana
kallonta ta shigo falon da sauri tace "momy
xata gan ni" yace "a ina," tace "wucewa
take,"
bae ce komai ba ya xauna kan kujera, ita ko
tana tsaye bakin kofar sae leke leke take, ta
kai minti kusan goma a hka snn yace "to ki
xauna mana," ta juya ta galla masa harara
tace "ina ruwanka da tsayuwata," yyi
murmushi ya dauke kansa bae sake cewa
komai ba har ta gama tsayuwarta ta bude
kofar ta fice, ya sauke ajiyar xuciya, shi kam
baxae iya tsayawa rokan karamar yarinyar
nn
ta koma gidansa ba ta ci gaba da raina sa
ba,
duk da abun yana damunsa but ya
gwammace yyi ta damunsa din. Kullum sae
Aliyu ya xo gida da daddare duk dan sbda
inteesar amma baya nunawa, ita kuwa idan
bata gansa ba har bata jin ddi, tayi ta
sintirin
xuwa gun inna knn, ta rasa me ke damunta
kan Aliyu, gashi ko sun hadu kallon arxiki
bata yi masa bare gaisuwa, shi kam sae dae
ya bita da kallo, tun ran da inna tayi mata
maganan komawa gidanta ta balbaleta da
masifa bata sake yi mata ba. Cikinta ya shiga
wata na shidda amma bbu me yi mata
maganan komawa gidan mijinta, Yau tana
xaune falon inna ya shigo da daddare, inna
na
bakin famfo tana wanke robobinta, ya
xauna
yana kallon inteesar dake xaune tana shan
watemelon, kallo daya tayi masa ta dauke
kanta, ya sauko gabanta ya xauna yana
kallonta, tayi kmr bata san da shi ba tana ta
shan kankananta, ya shafi cikinta ta buge
masa hannu tace "meye hka," bakinsa ya
daura an nata yana kallon cikin idonta,
gabanta yyi mugun faduwa ta rufe idonta
da
sauri ya shiga kissin din wuyarta, tayi baya
xata fadi ya tallabota da sauri snn ya
kwantar
da ita a hankali ya shiga shafata ta kasa
hanasa, ganin idan ya ci gaba da hkn baxae
iya hkura ba yasa ya dago ta yana kallonta
da kyar yace "fateema," ta daga kai tana
kallonsa ita ma da kyar don gaba daya
yanayinta ya canxa, ya kauda yace "meyasa
kike walakantani hka ne kike cutata," tayi
tsaki bata ce komai ba, ya ci gaba "kiyi hkuri
ki koma dakin ki, ni nayi maki alkawarin
baxa
a sake jin kan mu ba," tace "ae bani kadae
bace matarka da xaka damu kanka a kaina,
kuma ni bana sonka" yyi murmushi yace
"karya kike yarinya ga sona nn ina hangowa
cikin idonki, ni dae ne bana sonki i only
need
yhu badly, amma xanyi kkri naga na koyi
sonki sbda kids dinmu" ta fashe da kuka ta
mike tsaye tana kallonsa tace "ka yaudari
kanka idan kayi tunanin ina sonka, uwar me
xanyi da wanda baya ganin mahaifiyata da
gashi ma dae tukun, i hate yhu Aliyu," ta
juya
da sauri ta shige dakin inna tana kukan
takaici, wae he only need her dama tasan
kawae don ya dinga biyan silly bukatarsa
yasa yake son ta koma gidansa. Ya sauke
ajiyar xuciya ya mike ya fita daga falon, inna
tace ina xaka" yace ina xuwa inna, sashinsu
inteesar ya nufa, yyi sallama can kasa ihsaan
ta amsa ya bude kofar ya shiga falon, momy
na xaune tana feed din ihsaan, ya nemi gu
ya
xauna kansa a kasa ya gaisheta, ta amsa da
"qlau," yyi shiru na kusan minti biyar tana ta
harkan gabanta, a hankali ya fara magana
yace "wajen ki na xo momy," ba tare da ta
kallesa ba fuskarta a daure tace "ni kuma
.
Aliyu ya dan yi shiru snn yace "dama so
nake don Allah ki taimaka kiyi ma Fateema
magana ta koma dakinta, don xata fi jin
maganarki," momy tayi masa wani mugun
kallo tace "lallai ka cika mara kunya, kasan
da warce kke magana kuwa, to fice min a
falo tun kan na baka mamaki," ya sunkuyar
da kansa ya dan yi murmushi bbu yabo bbu
fallasa yace "ae dae don Allah nace," cikin
tsawa tace "ka fice min a falo tun banje na
hadaka da ubanka ba, da can ni na raba ku
da xan hada ku ynxu, lallai ka cika fitsararre
mara tunani" ya mike yana murmushi ya fice
daga falon, tayi tsaki ta shige bedroom
dinta ranta a bace. Sashin inna ya koma,
inna na xaune da inteesar tana shafa mata
bayanta wae xuciyarta na tashi, daga bakin
kofar yana kallon inteesar yace "in har kika
koma gidana to baki cika yar halak, kiyi ta
xama gidanku, cikin ma in kinga baxa ki iya
ba kya iya xuwa ki xubar da shi ynxu," ya ja
dogon tsaki ya sake labulen ya juya yyi gaba,
inna da ta kasa rufe baki ta mike da sauri ta
bi shi tace "ka dawo ka bata takardarka don
uwarka, idan ba kaddara ba me xae kaita
auren mahaukaci," ya juya yana kallon inna
yace "sae dae in ku ne ke hauka," yyi gaba
abunsa. Inteesar da komai nata ya tsaya ta
kasa cewa komai sae hawayen da take, inna
ta shigo tace lah meye abun kuka, ki rabu
da dan iska wllh na kashe aurenku ynxun
nn, ya ya kuma