INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   30 / 41

87K to 90K   out of 122.8K words

ranar da daddare har tayi
bacci don ido Aliyu ya sa mata, washegari
sunday yana gida yana xaune dakinsa
na'ura gabansa, safeena ko na daki kwance
abun duniya ya isheta, inteesar ta gama duk
abinda xata yi da kyar don xaxxabi ne ssae
tare da ita, ta rufe dakinta da makulli ta ciro
maganin da likitan ya bata jiya ta debo ruwa
a bathroom don har lkcn ba ruwa a dakinta,
ta xauna kusa da gado, ta fiffito da
magungunan daga kwalayensu ta daddauki
yanda yace mata, ta tsura ma kwayoyi
shiddan dake hannunta ido, ita bata ma
taba ganin irinsu ba, ta rumtse idonta ta
xuba su a bakinta ta kora da ruwa da sauri
ta hadiye su.
TAMMAT ALHAMDULILLAHI.


INTISAAR BOOK4

Inteesar tayi shiru a dan tsorace bayan ta
hadiye maganin tana jiran jin me xata fara ji
a jikinta, har na kusan minti goma bata ji
komai ba hkn yasa ta mayar da hankalinta
ga TV dake ta aiki shi kadae tana kallo, taji
ta fara jin bacci amma har lkcn bata ji ko da
ciwon kai a jikinta ba, hkn yyi mugun daga
mata hankali, tace na shiga uku kar dae
cikin baxae xube ba, ta dauko magungunan
ta shiga balla su kuma xata sha yanda ta sha
daxu hankalinta a tashe, ta ciro su knn ta
jawo kofin ruwanta xata sake korawa taji
wani matsanancin ciwo a mararta da bata
taba ji ba, tayo waje da ido a tsorace
gabanta na faduwa, a hankali cikinta ma ya
fara ciwo ya hade da na maran, tunda take
bata taba jin irin wnn ciwon a jikinta ba,
kankame cikinta tayi ta shiga mutsu mutsu
daga xaunen da take tana buga tiles da
hannunta, taga xama ya gagareta ta kwanta
kasa tana rike da cikin tana juye juye, ita nn
tana ga xata iya jure ciwon har ya gama
cikin ya fita, da marar ta yyi wani irin murda
mata ta daura hannu a ka taji kmr
mutuwarta ce ta xo, bata san lkcn da ta fasa
wani axababben ihu ba tana rike da cikin,
lkci daya ta hada xufa, ta shiga kwala ihun
axaban da take ji a gigice, a tare Aliyu suka
fito da Safeena ya karasa kusa da kofar a
rude ya murda yaji a rufe, bubbuga kofar ya
shiga yi yana kiranta, ta fashe da wani
matsanancin kuka da kyar tace "wayyo
mutuwa xanyi ya Aliyu," ya koma daki a
rikice ya shiga neman spare key, safeena
kam da gudu ta koma dakinta ta dinga
tsallen murna shknn ta sha ruwan, ya
karaso jikin kofar jikinsa na rawa ya bude
kofar ya afko cikin dakin yana kalle kallen
inda xae ganta, can kusa da gado ya ganta
kwance tana juye juye ya karasa gabanta da
sauri ya durkushe ya dago ta a rude yana
tambayarta me ya faru, kasa cewa komae
tayi sae juye juyen da kawae take a
hannunsa, a rikice ya shiga cewa "don Allah
kiyi min magana fateema me ya same ki,"
duk da mugun axaban da take ji hannunta
na rawa ta shiga tura kwalin magungunan
karkashin gado tana mayar da numfashi da
kyar wae kar ya gani, ya lura da abinda take,
ya rike hannunta da sauri yana kallon
kwalin yace "meye wnn," girgixa masa kai ta
shiga yi tana neman xamewa daga jikinsa
ya daga kwalin tabs din yana kallo baki
bude, a rude ya jefar ya shiga cewa
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un meye wnn,"
wani ihun ta kuma fasawa ta kankamesa
tace "wayyoo ya Aliyu, cikina, mutuwa xanyi
wllh," yana jijjigata cikin tashin hankali ya
shiga cewa "ki gaya min shi kika sha
fateema?" kasa cewa komai tayi sae jujjuya
kanta da take cikin axaba, ya ga farar
takardar scan din dake gabanta ya dauka da
sauri hannunsa na rawa ya bude, jefar da
takardar yyi ya fixgota cikin mugun tashin
hankali yace "wayyo fateema ki gaya min
magungunann nn kika sha? Plss kiyi min
mgna," a rude yake maganar, ita ko da kyar
ta shiga gyada masa kai tana jawo
numfashi kmr me shirin suma, ya dafe
kansa yana kallonta yace "nashiga uku, oh
my God," saketa yyi da sauri ya fice daga
dakin, ta dinga ihu tana birgima cikin
axaban ciwo tana kiran Abbanta, ya dawo
dakin da sauri rike da allura, kwance ya
ganta cikin jini, yyi wani kara a rude ya jefar
da alluran hannunsa ya karaso kusa da ita
da sauri yace "ya salam, innalillahi wa inna
ilaihi raji'un, fateema fateema" kuka take
ssae tana juye juye kmr ranta xae fita jini
sae malala yake ta kasanta, ya dagota ya kai
mata wani wawan mari a gigice ya shaketa
yace "kika kashe min yarana, yhu kill my
kids" ta kankamesa tace "wayyo mutuwa
xanyi na shiga uku," wani marin ya kuma
kai mata ya dagota ya buga ta da bango,
tunda take bata taba ganin yanayin da Aliyu
ya shiga ranan a tare da shi ba, idonsa ya
kada yyi jajur muryarsa na rawa yace "ki
gaya min ubanwa ya baki maganin nn, wani
asibiti kika je," ya wurgar da ita ya buga
bango da hannayensa biyu yace "ya salam,"
juyowa taga ya sake yi ta fara kkrin fita
daga dakin ya fixgota ya shaketa yana huci
yace "me yarana suka maki kika kashe su
fateema," ta rike hannayensa biyu cikin
kukan tashin hankali tace "no plss kayi min
rae ya Aliyu cikina xae kasheni," bugata yyi
da bango da karfi ya fice daga dakin tasan
be gama da ita ba, tayi karfin hali ta rarrafa
ta fito daga dakin da kyar tana neman inda
xata safeena ta fito da sauri ta ja ta suka
shige dakinta ta rufe kofar da sauri, inteesar
ta xube kasan dakinta tana mayar da
numfashi har lkcn jinin dake xuba jikinta
bae tsaya ba
.
Aliyu ya fito kmr wani mahaukaci daga
dakinsa ya shiga nata a rikice bae ganta ba,
ya fito ya shiga buga kofar Safeena da karfi
ganin trace din jini tun daga kofar Inteesar
har nata, alamar nn inteesar ta shiga, cikin
tsawa yace "baxa ku bude min kofar ba"
cikin sanyin murya Safeenah tace "haba
dear ka sa ma xuciyarka ruwan sanyi mana,
so kke kayi kisan kai, ka bar ta da halin da
take ciki mana xaka dinga dukanta kuma,"
ya daka mata wani raxanannen tsawa yace
"na rantse da wanda numfashina ke
hannunsa idan ban hada dake ba kada Allah
ya bani abinda yake nema, baxxa ki bude
min kofa ba" ya karasa maganar yana huci,
ta bude baki da mamaki tana kallon kofa,
A'aaah lallai abun babba ne yau, to fa, ta dan
tabe baki tace "to ni ko sae dae kar ya baka,
don baxan tsaya hka kawae ina ji ina gani
ka kashe yar mutane gabana ba," bae sake
cewa komai ba ya juya da sauri kmr xae
tashi sama ya koma dakinsa yana huci,
inteesar kam na durkushe dakin sae kuka
take tana juye juye kmr ranta xae fita, kila
karshenta ne ya xo yau, gashi har lkcn jini
bae tsaya mata ba sae bulbulowa yake, duk
kayan jikinta ya baci da jini hka ma dakin
safeena, safeena ta dauko Zaninta da sauri
ta mika mata a xuciyarta tana cewa "yau ai
sae dae jininki ya tsiyaye ki mutu yarinya
baxan bude kofar ba bare ya taimaka maki,"
inteesar ta kasa karban xanin, sae cewa
take mutuwa xanyi, safeena tace "baxa ki
mutu ba," key suka ji Aliyu ya saka a kofar,
Inteesar ta fasa ihu jikinta na rawa taji kmr
ta sume ynxu ta samu saukin abubuwan
dake faruwa ynxu "wayyo kayi min rae ya
Aliyu wlh yau mutuwa xanyi, don Allah kaji
tausayina" ya afko dakin rike da kwalin tabs
din da ta sha yana huci, idonsa ya koma
jajur kmr gauta, kanta yyi ya fincikota da
karfi ya dago ta, muryarsa na rawa yace
"wllh wllh baki gaya min wanda ya baki
magungunan nn ba, sae na kashe ki kema
yau," jikinta na rawa ta shiga girgixa masa
kai hawaye na bin kuncinta, ya shaketa da
karfi, cikin tsawa yace "baxa ki gaya min
ba," ta yo waje da ido a tsorace, da kyar
muryarta a shake tace "xan gaya maka," ya
watsa mata mari yace "uban me kike jira," ta
fashe da wani matsanancin kuka ta juya
tana kallon safeena tace "ita ce ta kaini aka
bani," Safeena ta yo waje da ido ta dafe
kirjinta tace "na shiga uku yarinya xata min
sharri, a ina kika ganni," cikin kukan Axaba
Inteesar tace "ita ce ya Aliyu, ka tausaya min
cikina kasheni xae yi wllh," a hankali Aliyu ya
saketa ta sulale kasa ya juya yana kallon
safeena da ta xama kmr mara gskyar gske,
duk ta rude, sae rawa bakinta yake ta kasa
cewa komai, ta fashe da kuka tace "wllh
wllh sharri tayi min Aliyu, a ina ta gan ni yau
da har xan kai ta a bata magani," wani kara
yyi ya karasa kusa da safeenar kmr xaki ya
shaketa hawaye cike idonsa yace "ku ka
kashe min yarana, me suka maku safeena,"
bae jira me xata ce ba yyi wani irin buga
kanta da bango ya saketa yana huci, sae ga
jini, a hankali ta sulale kasa ta fadi
sumammiya a wajen, juyawa yyi bae sake
ganin Inteesar ba a dakin
.
Inteesar na fita daga dakin dama falo ta
sauko tayi hanyar kofar fita waje da sauran
karfinta don dk jikinta yyi weak, tana isa
tsakiyar falon jiri ya debeta ta xube kasa ta
kasa tashi kuma, dae dae nn shima ya sauko
kmr an hankadosa ta fasa wani gigitattcen
ihu ta fara kkrin mikewa tsaye amma ta
kasa cikin kuka ta dinga cewa Noo plss ya
Aliyu ka tausaya min," ganin ya yo kanta ne
yasa ba tare da ta shirya ba ta sulale wajen
sumammiya, ya xube gabanta ya kife kansa
kan tiles cikin tashin hankali yace "Nooo" da
kyar ya dago kansa yana kallonta hawaye
kwance fuskarsa, ya dagota ya rungumeta
muryarsa na rawa yace "y fateema, meyasa
xaki min hka, me yaran nn suka yi maki kika
gwammace ki kashesu, y?" ganin har lkcin
jini bae tsaya mata ba yasa ya dauketa da
kyar ya haura sama da ita ya bude dakinsa
ya kwantar da ita yana tunanin me xae
mata, duk wata baseera ta bace masa kmr
ba likita ba ya rasa yanda xae yi da ita sae
bincika ruwan allura yake ya rasa wanne ma
ya kamata yyi mata, da kyar ya jawo
wayarsa jiki ba kwari ya shiga neman nmbr
wani abokinsa doctor yaji a kashe, ya kira
Dr maryam ma yaki shiga, hkn yasa ya kira
nmbr faruuq bugu daya ya daga, da kyar ya
iya cewa "plss faruuq ka taho gidana ynxun
nn i need yhu help," ya katse kiran ya ajiye
wayar har lkcn inteesar na jikinsa, ko minti
sha biyar bae cika ba faruuq ya iso gidan
don a xatonsa Aliyun ne bae da lfya, yana
shiga compound ya kira Aliyu yace gashi nn
ya xo, Aliyu yace ya shigo falo ya hayo sama,
bbu abinda ya daga ma faruuq hankali illa
ganin jini da yyi ta ko ina a gidan, kasa
karasa cikin dakin yyi bayan ya bude dakin
Aliyu, har lkcn kuma yana rungume da
inteesar jikinta duk jini, da kyar faruuq ya
iya cewa "meye hka Aliyu, me ya sameta,"
Aliyu ya kasa cewa komai sae girgixa kansa
da yake, faruuq yyi karfin hali ya karasa
cikin dakin yana kallon Inteesar xuciyarsa
na bugawa, da kyar 4 d second tym ya sake
cewa "me kayi mata Aliyu," Aliyu yyi karfin
halin cewa "Abortion tayi faruuq, she killed
my children," hawaye ne ya biyo bayan
maganr tasa, Faruuq yace "innalillahi wa
inna ilai'hi rajiun, ix she alryt, suma tayi ko
me, she's still bleedn" ya karaso gabansu da
sauri ya durkusa ya daga hannunta yana
feel din pulse dinta, ya sauke ajiyar xuciya
snn ya karbeta daga hannun Aliyu ya
kwantar da ita, yace "kana da kayan aiki ne
a gida," Aliyu ya nuna masa inda komai
yake, ya shiga hada alluran da xae mata da
sauri, da kyar ya samu jinin nata ya tsaya,
shi dae Aliyu kallonsu kawae yake yana gefe
xaune, faruuq yace "ka gyara mata jiki sae
ka mayar da ita kan gado, bari naje xan siyo
drip din da xan hada mata," Aliyu bae ce
masa komai ba ya fice da sauri, da kyar Aliyu
ya iya tashi ya tafi dakinta ya dauko mata
wani kayan da abubuwan da ya kamata, ya
koma dakinsa ya shiga gyara mata jikinta
har ya gama ya sauya mata wani kayan ya
dauketa ya kwantar kan gado, snn ya shiga
aikin goge gogen jini a gidan, a hka faruuq
ya dawo ya samesa, faruuq ya gama mata
duk abinda ya kamata snn ya fito yana
tambayar Aliyu safeena fa, Aliyu dake xaune
ya takure a falo xaxxabi na neman rufesa
dakyar yace ka duba nxt room din i thnk ita
ma suman tayi" faruuq ya tsaya kallonsa ya
kasa cewa komai, ya juya ya shiga dakinta
ita ma yyi mata duk abinda ya kamata ya fito
yace Aliyu yaje ya mayar da ita kan gado. Har
dare inteesar bata farfado ba, safeena kam
an farfado amma bata yi gigin fitowa ba ba
karamin fashewa kanta yyi ba ta dinga kuka
ita daya a daki faruuq ya shigo gidan bayan
sllh magrib ya shiga ya duba inteesar ya
sauko yana kallon Aliyu yace dole sae an
kara mata jini, Aliyu bae yi masa musu ba
suka tafi asibiti aka diba jininsa don dai dai
ne da nata, shi dae komawa yyi kmr wani
mara lfya suka dawo gida faruuq ya sa mata
jinin, ko da faruuq ya bude dakin safeena
bae ganta a ciki ba, ya sauko kasa yana gaya
ma Aliyu, Aliyu yace "tafita knn," ita ko tana
jin fitarsu dama tayi gidansu ba shiri. A
daren Aliyu ya tafi gida, yasa Abbansa a
gaba kmr wani karamin yaro yana hawaye
ya gaya masa abinda inteesar tayi, Abba
kasa yrda yyi, hka ma Haisam dake falon duk
jikinsu yyi sanyi, Abban yace "ita fateemar,
innalillahi wa inna ilaihi raji'un" frm no
where suka ji muryar inna tana salati
tashigo falon Abba da gudu kmr an jefota a
rude tace "Bukar Bukar wae ji nayi ance
Inteesar ta xubar da cikin jikinta," duk suka
yi tsit suna kallonta, a fusace tace "kuji min
mutane kmr kurame, wae ba magana nake
maku ba xaku mayar dani yar iska" Abba ya
sauke ajiyar xuciya yace "nima ynxu Aliyu ya
xo yake sanar min," inna ta fasa ihu tare da
fashewa da wani matsanancin kuka ta
daura hannu a ka tace "wayyo na shiga uku
ni Rahmatu, amma wnn anyi gantalalliyar
muguwar yarinya, don ubanta dan nawa ta
xubar, tasan burin da na ci akan dan nn,"
Aliyu ya mike da kyar yana kallon Abba
muryasa can kasa yace "sae da safe Abba,"
inna na huci tace "maxa muje ka kaini
wajenta ynxu" Abba yace "A'a baaba, gobe
ya taho min da ita ko.
Karfe goma da rabi Aliyu ya shigo gida, ya
kulle gidan ya haura sama a sanyaye ya
bude kofar dakinsa ya shiga, kwance ya
tarda ita idonta biyu, ledan jinin hannunta
ma kiris ya rage ya kare, kallo daya yyi mata
ya dauke kansa, ya cire shirt din jikinsa da
dogon wando, ya rage daga shi sae singlet
da gajeran wando, ta dauke kanta a hankali
ta lumshe idonta, bae taba tsayawa gabanta
hka ba sae sau daya, ya karasa kusa da ita
ba tare da ya kalleta ba cire mata alluran
hannunta ya soka jikin ledan jinin ya xaga
yyi kwanciyarsa can karshen gadon ya juya
mata baya, ita kadae tasan me take ji a
jikinta, ko ina na jikinta ciwo yake mata,
gashi har lkcn marar ta bae dena damunta
ba, ga mugun yunwar da take ji, don
rabonta da abinci tun safe, a hankali ta fara
kkrin sauka daga kan gadon ko tea ta hada
ta sha don yunwar yafi karfinta, jiri ya
debeta ta xube kasa, ya juya da sauri yana
kallonta sae kuma ya dauke kansa, ta fara
kkrin mikewa amma ta kasa, a hankali
muryarta na rawa tace "yunwa nake ji ya
Aliyu," ya juya yana kallonta kmr ya rufeta da
duka ya girgixa kansa xuciyarsa na suya,
cike da takaici yace "ta kasheki," snn ya juya
yyi kwanciyarsa. Da rarrafe ta fita daga
dakin ta shiga nata ta hada tea jikint a na
rawa, amma duk yunwan da take ji sae ta
kasa shan tean, hka ranan ta kwana a
wahale. Washegari monday bbu yabo bbu
fallasa ya shigo dakinta da safe yace ta
shirya xasu gida, gabanta ya shiga faduwa,
tana kallonsa daga kwancen da take tace
"baxan iya ba ya Aliyu" wani tsawa ya daka
mata yace "kada Allah yasa ki iya din, jahila
kawai, Allah ya baki sa'a na dawo naga baki
shirya ba," ya fice daga dakin, kuka ta shiga
rerawa a hankali, ta kasa tashi daga kan
gadon duk jikinta yyi tsami, cikin ikon Allah
ta mike da kyar ta shiga ta wanke baki ta
canxa pad, don bata da karfin wanka, ta fito
jikinta na rawa ta xura doguwar rigarta snn
ta saka hijab ta sauko yana falo yana jiranta
bae ko kalleta ba ya mike yyi hanyar fita
tana biye da shi a baya kmr iska xae kadeta
ta fadi, duk tayi mugun rama daga jiya
xuwa yau, a sanyaye ta bude bayan mota ta
shiga bae ko kalleta ba ya shiga driver sit ya
ja motar suka fita daga gidan, har suka isa
gida bae ce mata ba ita ma bata ce masa ba,
gabanta ya shiga faduwa don bata san me
xata shiga ta tarar ba, da kyar jikinta a mace
ta fito daga motar ta jira shima ya fito, bae
ko kalleta ba ya nufi gate xuciyarta na
harbawa da sauri da sauri ta bi bayansa
suna shiga gidan falon abba taga ya nufa,
ita dae tana ta biye da shi a baya kmr jela, a
bakin kofar Abba suka ci karo da momy
xata fito daga falon, inteesar ta koma baya
da sauri kuma a tsorace, momy ta bi ta ta
cafketa, ihu ta fasa a tsorace momy ta shiga
xuba mata mari tana duka kmr an aikota,
kuka ta dinga rusawa tana ihu a gidan Abba
ya fito da sauri yana kallon momy a fusace
yace "kina da hankali kuwa Zainab, meye
hka kike yi," ko kallonsa bata yi ba sae
jibgarta take tana tumble da ita, ita ko bata
fasa ihu da kukan da take ba, Aliyu ya dauke
kansa ya koma gefe ya tsaya ya lumshe
idonsa, su Hajiya da umma duk suka fiffito
daga dakunansu su Rahma duk sun tafi sch,
duk irin masifar da Abba ya dinga yi ma
momy ransa a bace kan ta sake inteesar kin
sakinta tayi, har sae da ta kai ta kasa, su
Hajiya da umma dae na tsaye sae murmushi
suke, Hajiya na cewa "to wnn abu dae idan
bakintsa mata aka yi ba taya yar mitsitsiyar
nn tasan wani cire ciki" daga nisa suka ji
Muryar inna tana tahowa da gudu tana
cewa "muryar waye nake ji hka kmr ta
Inteesar uban me ake mata," ta karaso tana
haki, tana ganin abinda momy ke yi ma
inteesar tayo waje da ido ta fasa ihu "meye
hka xan gani Zainabu, akuya kika samu ko
me? kashemin ita xakiyi don uwarki," sae a
snn momy ta saketa, inna ta fashe da kuka
tana kallonsu gaba daya tace "amma dae
Allah ya isa ban yafe maku ba, ynxu Bukar
har da kai aka taru xa a kashe yar mala'ikan
Allahn nn don ta xubar da wani wahalallen
cikin Aliyu dake neman aikata lahira, to duk
shegen da bae fasa dukanta ba bae haifu
cikin uwarsa ba " ta dago inteesar dake ta
rusa kuka ita ma tana nata kukan ssae tace
"Allah ya isar maki kuma ciki kin isa ne yasa
kika xubar da shi, mu je ga ruwa can na
daura xan maki wanka" taja ta tana dingishi
suka yi sashinta tana huci, Aliyu ya juya yana
kallon Abbansa da ya bi su da kallo shima,
snn ya girgixa kai kmr xae hadiye xuciya yyi
hanyar fita daga gidan Abba ya kirasa. Allah
sarki Babana Aliyu, but ol d same Allah shi
kara, na ma tuna ko waye kai da.
.
Inteesar

30 / 41