INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   11 / 41

30K to 33K   out of 122.8K words

yace"karaso mana" da kyar
yyinamijin kkri ya shiga dakin, ya rusuna ya
gaida abba don duk yau bai je gaisheshi ba
gashi har karfetara, ya juya ya gaida inna
ma sannan yace"abba gani,"
.
Dama fatima ce bata da lfya, shine nace a
kiraka ka dubata, abba ya fadi yana kallonsa,
Aliyu ya saki ajiyar xuciya, sannan ya maida
dubansa ga kangadon yana kallonta, idonta
a lumshe yake, duk da dae ba bacci take ba,
ya karaso kusa daita yace "meke damunki?"
tayi shiru kmr mae bacci, hkn ya bata masa
rai don yasan idonta biyu, a dan fusace
yace"kinajina xakiyi min banxa?" inna cikin
tsawa tace "kai mahaukacin wani gari ne,
baka ga bacci take ba yarinya tana fama da
kanta xaka dinga mata ihu," xainab ta
karasa kusa da ita tana bubbuga kafarta a
hankli tana kiran sunanta, ta bude ido tana
kalln xainab din, Aliyu ya juya yana kallon
abban nasa yace "ko dae a wuce da ita clinic
kawae abba" inna tayi karaf tace"wllh bbu
inda xa a kaita, gamu da likita a gida kace
xa a wuce da ita wani wajen, meye amfanin
ka" Aliyun ya dubeta rai bace yace "to ni din
Allahn musuru ne da xan san abinda yke
damunta," cikin tsawa inna tace "shiyasa
naga an kai fadila asibitida bata da lfya, don
ubanka ba kai ka dubata ba ka bata
magunguna da allurori ba kuma gashi nan
ta warke," Aliyu ya dubeta a walakance ya
kauda kai kawae, abba yace "shknan bari a
kaita asibitin ka iya tafiya" da sauri yace "aa
abba bance baxan dubata ba ae, guri nake
jira su ban na dubata," ya fadi yana
kallnsuinna, haisam ya shigo dakin da
sllmrsa ya karasa kusa da intisaar din ya
xauna cike da damuwa yana kallonta yace
"intisaar me ya sameki, dama jiya baki dalfya
baki yi magana ba," ta sunkuyar da kanta
kawae sae hawaye, nanya shiga lallashinta,
ya dube abba yace "asibiti xamu wuce
abba?" inna tace "asibitin lfya ga likita a
gida, ynxu xae dubata ae" sllmrsu hajiya da
umma ne yasa kowa yyi tsit a dakin, momy
ce kadae ta amsa masusuka shigo suna
cewa ashe abinda ya faruknan, momy ta
basu waje suka xauna sannan suka gaisa,
suka tambayeta mae jiki tace masu da sauki,
hajiya tace Allah sarki duk ta rame sae kace
warce tayi sati tana jinya, umma tace wllh
kuwa baiwar Allah, inna ta tabe baki tace
"ikon Allah" xainab ta girgixa kai cike da
takaici, ynxu har anje an barbada masu
shine suka kwaso jiki suka xo gulma,
kumatasan baxae wuce kursum ba ko
rahma, abba ya dubi gaba dayansu yace "to
ae kwa bashi waje yyi aikinsa de ko" hajiya
ta mike tana cewa"me xae hana, Allah dae
ya bata lfya yasa xakkan jikine," suka mike
gaba dayansu har da yaran xasu bar dakin,
Aliyuyace "to..to abba ya xa ayi treatin din
nata?" abba da har ya kai bakin kofa xae fita
ya juya yana kallonsa cikin rashin fahimta
yace "kmr ya fa?" yace"aa...dama...emm, to to
ae naga sae da magunguna da allurori xa
ayi treatn din nata, kuma ni...." sae kuma yyi
shiru yana kallon tagan dakin, abba
yyimurmushin takaici ya girgixa kai yace "to
nawa xa a baka?" inna ta mike ta saki salati
tana girgixa kai tace "ita intisaar din sae....."
da sauri abba ya katse ta yace "aa baaba ae
hakkinsa ne bari a basa" nawa ne kudin
treatment din gaba daya? Abba ya tambaya
yana kallonsa, cikin bacin rai haisam yace
"abba ka bari na wuce da ita asibiti kawai,"
abba yyi saurin cewa "aa haisam ka bari xae
dubata," abba ya sake tambayrsa nawa xae
basa, yyi shiru kmr me lissafi sannan yace
ba tare da ya kalli abban nasa ba "dubu
takwas da dari biyar gaba daya," abba yyi
murmushi, haisam cike da takaici yace "to
yyi kyau, ka dubatani xan baka," da sauri ya
juya yana kallon haisam din rai bace yace
"to da baki na xan siyo kayan ne koya? Ko
kuma ina da kudin xan tsaya cewa abba ya
bani," inna cikin ihu tace "Allah ya babbake
mae krya sannan ya tsinemasa," Aliyun ya
juya ya galla mata harara sannan ya dauke
kansa, haisam ya ciro dubu biyar daga
aljihunsa ya mike xae fita abba yace ina
xaka, yace xan dauko kudi ne,abba yace
nawa ne a wajen ka ynxu, yace dubu biyar,
abba ya ciki dubu hudun haisam ya mikawa
Aliyun ya karbe yana kirgawa, duk wannan
abinda akeyi a kan idonsu hajiya ne, hajiya
taji kmr ta maida dan nata ciki don murna,
sae murmushi take yi, umma kuma ji tayi
kmr ta tsine ma haisam da bai yo hali irin ta
Aliyu ba, shekaranjiya tace ya bata dubu
goma yace bai da, amma sae gashi ynxu ya
kirgo har dubu biyar ya bada don a duba
wata bnxa ita kam bata san irin dan da Allah
ya bata ba, momy kam sunkuyar da kanta
tayi tana jin duk abinda sukeyi cike da
takaici, intisaar kuwa idonta ta rufesbda
axabar da take ji ko ina na jikinta ciwo yke
mata barin ma kanta sannan kuma ga
ciwon mara shima ya kunno kai, abba kam
tuni ya fice su hajiya suka bi shi a baya a
xuciyarsu suna fatan Allah yasa cikita yo,
don rahma ca tayi masu amai take ta
kwararawa, Aliyu ya dube inna yace"a bata
tea kafin na dawo, xan je siyo abinda ya
kamata," ya fice haisam ya bisa a baya da
sauri, sai da suka kai tsakar gidan sannan
yace "canjin nawa xaka dawo da knan?"
Aliyu yace kmr ya, haisam yace eh ae dubu
tara aka baka, kuma dubu takwas da dari
biyar kace, Aliyu yyi masa wani irin kallo
sannan yace "to da kafa xanje siyo
magungunan?" sannan yyi tsakiya wuce
yana cewa "dn ma kun samu xan bata lkcn"
.
. Su Aliyu na fita inna ta mike tana tambayr
intisaar din me xata ci, ta girgixa kai alamar
ba komai, xainab tace"to ki daure kisha tea
din" inna ta dauki kofin ruwan shayin ta isa
kusa da ita tana cewa "tashi ki sha kafin ya
dawo to" intisaar ta girgixa kai murya can
kasa-kasa tace "wanka xan fara yi," momy ta
shiga bathroom ta hada mata ruwan
wankan sannan ta mike da kyar jiri na
kwasarta ta shige bayin, ko da ta fito rawan
sanyi ta dinga yi, inna ta lullubetatana cewa
"ikon Allah, ciwan lkci daya ya kwantar da
ita," ya haisam ya shigo dakin yana tambayr
ko Aliyun ya dawo,inna tace "ina fa! yana
can yana sokwanci" haisam ya girgixa kai
yace "ni dae wllh inna nafi son a kaita
asibiti," inna tace "wae ni kuna bani mamaki
wllh, ga likita a gida kuyi ta kiran asibiti,"
haisam yace "to shknan, ni xan wuce kd ne
ynxu ina da wani aiki a can amma yau xan
dawo in'sha Allah," inna tace "to Allah ya
kiyaye" yace "ameen" sannan ya karasa kusa
da intisaar yana kallnta yace "Allah ya
sauwake kanwata kinji" tayi murmushi, a
hnkli tace "ngdyayana" yyi ma momy ma
sllma sannan ya fita. Da kyar inna ta lallabata
tasha kunun da ta dama mata, xainab sae
fama kallon agogo take yi dn har sha daya
ya wuce, tun kusan karfe goma da Aliyu yaje
siyo magunguna har ynxu bai dawo ba, tuni
bacci ya dauke intisaar din bayan inna ta
bata paracetamol kafin Aliyun ya dawo,
amma har karfe sha biyu bbu Aliyu bbu
lbrinsa, "kai jama'a ko dae wannan yaron
bata yyi ne" inna ta fadi tana kallon momy
da xainab dake dakin bakinta a bude, momy
dae bata ce komai ba, xainab ta tabe baki
ita ma bata ce komai ba, wasa-wasa har
karfe biyu bbu Aliyu, inna na idar da sllh
tana xaune kandarduma cikin ihu tace
"amma wannan anyi tsinannan yaro," daga
momy har xainab sae da suka raxana sbda
irin bude muryar da inna tayi, momy tace
"kai inna, kika san uxurin da ya tsayar
dashi," a fusace inna tace "yaci ubansa shi
da uxurin," ku bni waya na kira bukar,
momy tayi ma xainab ido alamar kar ta kira
mata abban, inna ta mikawa xainab din
wayar tana cewa "maxa kira min uban
nasa" xainab ba don ranta yaso ba tace ma
inna baya xuwa bayan ta kara wayr a kunne
kmr me kira, don ita da momy ta barta kiran
abban xatayi, ita kam bata san irin yayan
nata ba, basu san tuni abba ya kira momyn
yana tambayrtajikin intisaar din ba tace
masa da sauki sosae, yace Aliyun ya bata
duka magungunan tace masa eh sannan
sukayi sllma, xagi kam Aliyu ya sha shi a
wajen inna ba adadi, har da dan hawayenta,
"ni da nasan abinda tambadadden yaron
nan xae yi knan da asibiti kawae na bari
muka wuce, gashi ynxu yrnya na ta shan
axaban ciwo ba magani, shi kuma bukar na
rasa uban me xae sa ya dinga kashe
wayarsa ni kam, ynxu wa xae kai mu
asibitin gashi haisam ba ya nan," daga
momy har xainab bbu wanda ya tanka
mainna, intisaar kam jikinta yyi xafi sosae
kmr wuta, hka inna ta ishesu da mita tana
hawaye, wajen karfe uku da rabi wayan
intisaar yyi kara xainab ta dauka tana kallon
me kiran, faruuq ne, da har xata ajiye don
bacci intisaar din take yi sae kuma ta fasa ta
daga, suka gaisa ya tambayeta intisaar din
fa, tace "bacci takeyi wllh, bata da lfya," cike
da damuwa yace "subhanallahi, me ya
sameta" xainab ta yarfe hannu tace "wllh
bamu sani ba, tace dae ciki da kantake mata
ciwo," yace "tun yaushe?" tun jiya da
daddare wae,yace "ya salam! kunje clinic
ne?" tayi shiru ta rasa me xata ce, yyi saurin
cewa "ohk... Gani nan xuwa," ya kashe wayr,
inna tace "faruqu ne?" xainab ta gyada mata
kai kawai, cikin minti goma sha biyar faruuq
ya iso gidan, hanklinsa ya tashi sosae, momy
da ta bar masu dakin ya rage inna daxainab
kawae, ta tashi xaune tana kallon faruuq din
da ya sata gaba yana tambayrta inda ke
mata ciwo, cikinta t.a nuna masa da kai,
yasa hannu ya danna cikin nata ta xaro ido
tace "waii! ciwo yake min" me ya buge ki a
nan ya tambayeta yana taba goshinta da yaji
xafi sosae, ta girgixa masa kai kawae sae
hawaye, duk ya rude ya shiga lallashinta
yace "dama kina ciwon kai ne," ta girgixa
masa kai kawae, ya mike yana kalln inna
yace "bari ina xuwa yanxun nan inna," inna
tace "to dan albarka, wannan shaidanin
yaron aka ba kudi ya siyo mata magunguna
bamu sake ganinsa ba " bai tanka wa inna
ba ya fice da sauri, ko minti talatin bae cika
ba ya dawo dauke da kayan magunguna da
allurori sae ledar ruwa dan karami da xae sa
mata, ya ce wa xainab ta hado mata tea mai
kauri ta kawo mata, shi da kanshi ya shiga
bata, amma ta karba tace xata iya sha, yana
ta hada allurorin da ruwa har ta sha rabi ta
ajiye tace "ta koshi," yace "ae baki ma ci
komai ba tukunna, tuwo xa a kawo maki
kici ynxun," inna ta mike tana cewa "gskya
ne, bari naje da kaina ma xan mata ynxun
nan," da kyar ta yrda yyi inject din ta sannan
ya sakamata ruwan ya bata wasu daga cikin
medicines din tasha ta kwanta, ya xauna ya
xuba mata ido yana kallonta cike datausayi,
xainab dama tuni..
Faruuq na xaune har ruwan da yasa mata
ya kare da yake karamin leda ce, ya cire
mata don bacci ma takeyi, yana gama cire
mata ta bude ido tana kallnsa, yyi mata
murmushi yace "ya jikin kanwata," ta tashi
xaune tace "da sauki," ba tare da ta kallesa
ba, ganin tana kkrin mikewa tsaye ne yasa
yace "ina xaki kuma kanwata," murya can
ciki tace masa "2 ease my self," ba tare da ta
kallesa ba, ya taimaka mata ta tashi tsaye dn
jikinta ba kwari dukda taji ta garau ynxu,
tuwon da inna ta kawo mata ya shiga xuba
mata, ta fito ta nemi gefe ta xaunatana
kallonsa kmr xatayi kuka, ya dago kai yana
kallnta yace "kici abinci ki sha sauran
medicine dinki kanwata, kusa da ita ya
durkusa yana kallonta yace "ya dae
kanwata, cikin na maki ciwo har ynxu ne,
naga yhu re restless" ta girgixa masa kai
kawae bata cekomai ba "say somethin
mana kanwata, ina ke maki ciwo kuma?"ya
tambayeta cike da damuwa, itakam kunya
take ji tace masa mararta ke mata ciwo, don
hka tace "ni bbu inda ke min ciwo," sae
kuma ga hawaye, nan da nan ya rude ya
shiga lallashinta yana cewa "plss kanwata ki
gya min mene mana, kan bai daina
bane?,"ganin yanda duk ya bi ya daga
hanklinsa ne yasa tace "cikina ke ciwo," ba
tare da ta kallesa ba, yace "ciki kuma, ba kin
ce ya daina ba, to wae me ya buge ki a cikin
ne" a hankli tace ba shi bne, yyi shiru kmr
me naxari sannan yace "on yhur Period?"
yana kallonta, tayi shiru bata ce komai ba
kanta a sunkuye, yace "ohk ina xuwa
kanwata," ya mike ya fice. Ko da ya dawo
tana xaune a falo ita da momy da inna sae
kursum, tasa tuwo a gaba amma taki ci,
ynxu kam jkinta yyi mata sauki sosae, da
sllmrsa ya shigo falon rike da ledan magani
karfe biyar da minti goma na yamma, ya
gaida momy don tun xuwansa na farko bai
sake ganinta ba sae ynxun, ta amsa tanai
masa sannu da xuwa sannan ta mike ta bar
falon, xainab ta shigo ta xauna gefen
intisaar din tana mata ya jiki, tayi murmushi
tace "da sauki"maganin da ya xo da shi kala
uku ya dauki daya ya buda ya bata, ta karba
a kunyace xata ajiye yace tasha ynxun, inna
tace "ae hka nan take yarinyar nan bata san
magani, nayi mamakin ma da tasha wa inda
ka bata daxu," faruuq yyi murmushi kawae
yana kallnta har ta kora maganin da ruwa
sannan ya sa ta cin tuwon dake gabanta,
bude kofar da sukaji anyi irin ta mahaukata
ne yasanya su juyawa gaba daya, Aliyu ne ya
shigo dakin sanye da t-shirt fara kal da
wando three qtrshima farin, yyi kyau sosae,
hannunsa rike da leda da basu san ko meye
a ciki ba, intisaar ta sunkuyar da kanta da
sauri, faruuq kuwa kallo daya yyi masa ya
kauda kansa, kallonsu ya shigayi daddaya
da daddaya, inna tana sakace hkori ta tabe
baki tace "ae sae ka je ka tsis-tsira ma kanka
allurorin ka shanye magungunan don jikata
kam ta warke, dan arxiki wanda aka haifa
tsiya na bacci ya xo ya duba mana ita" Aliyu
ya yo waje da dara-daran idanunsa yana
kallon innar, wato shi aka haifa tsiya ido
biyu, ya juya yana kallon faruuq din da
intisaar, xainab ta labe bayan intisaar sbda
wani irin dariya dake cinta, hka ma kursum
da ta rufe fuskarta a jikin inna, Aliyun
yatsura wa faruuq din ido kmr xae shake
shi, faruuq bai ma san yanayi ba, ya dube
intisaar yace"kanwata kin ki cin tuwon ko
na taya ki ne?" ta kirkiro murmushi bata ce
komai ba, yace "au kar na taya ki?" a hnkli
tace "kaci mana" yyi murmushi yace ok,
sannan ya mike ya dauki ruwan goran dake
gabanta ya bi gefen Aliyun ya fita, Aliyu ya
bishi da kallo har ya dawo ciki sannan ya
xauna gabanta yace "to muci," a kunyace
tasa hannu cikin tuwon sannan shi ma ya
saka, inna tace "yauwa faruqu kila ma xata
fi ci idan taga kana ci," faruuq yyi 'yar dariya
ya dubi xainab yace "xo muci xee" xainab
tayi dariya tace aa ni naci nawa ae, inna ta
dubi Aliyu tace "to ka tsaya mana kerere a
ka kmr wani tsohon soja, da'alla fice ka ba
mutane waje su ga haske,gantalalle kawae
dogon bnxa, knka ka cuta ba mu ba " Aliyu
yyi huci mae xafi yana kallonintisaar din
dake cin tuwonta a hnkli ita da faruuq,"
juyawa yyi ya fuce fuuu, inna ta kyalkyale da
dariya ya dawo da sauri idon nan nasa ya
kada yace "kika ce me?" bata tanka masa ba
sae dariyar da take ta yi kawae, ya juya yyi
gaba yana cije lebensa. Kursum da xainab
suka dinga kyalkyale dariya inna na taya su,
faruuq kam murmushi kawae yke yi, intisaar
kam jingina kanta tayi jikin kujera tana
kallonsu.
.
Gajiya tayi da tsayuwa taga ba sarki sae
Allah, tayi shahada, ta kusa kai cikin gate din
tana karanto duk addu'ar da taxo mata don
duk a rude take, a dai-dai lkcn shi kuma ya
mike tsaye xae bar gidan ya wuce masallaci
don maghrib ya kunno kai, duk gidan yyi
masa xafi, wata raxanan nan kara ta saki
ganin ya mike tsaye a dai-dae lkcn da ta
shigo gidan, don a nata tunanin dama can
ita yake jira yana ganintakuma ya mike, shi
kanshi sae da ya firgita da irin karar da tayi,
ta kuma juya a guje kmr mahaukaciya xata
bar gidan, yyi saurin fixgota da karfinsa
ransa a bace, bae an kara ba sae ganin
yarinya ta sulale kasa yyi, yyi hanxarin rikota
ta xube jikinsa sumammiya, ya durkushe
wajen yana kallonta cike da mamaki, yasan
suma tayi, jijjigata ya shiga yi a hnkli ya ma
rasa abinda xae yi ya fara waige-waige
gashi bbu kowa a tsakar gidan dan gari ya
fara duhu, ruwan goran da ya fitoda yasha
ya rage, ya dauko ya bude ya shiga yayyafa
mata ruwan, a hnkli ta bude idanuwanta ta
daura kan nasa idon da ya tsura mata a
fuskarta, kuka ta saki tana kkrin tashi daga
jikinsa tana cewa "don Allah don annabi ya
Aliyu ka daina dukana, ni bn maka komai
ba....." buga mata baki yyi yace "keep mute!"
ba shiri tayi shiru, ya turata daga jikinsa
fuska a hade yace "don ki kara ja min bakin
jini wajen abbana shiyasa xaki tsiri suma da
kin ganni ko" girgixa kai tayi hawaye na
sintiri a fuskarta, ya daka mata tsawa "tashi
a kaina kar nayi ball dake munafuka kawae,"
ta mike da sauri jikinta na rawa, shima ya
mike tsaye, tayi baya xata fadi, yyi saurin
tallabota, ta fada jikinsa ya turata da sauri
sannan yyi maxa ya riko hannunta dn
faduwa xatayi, ya fara fixgarta kmr wata
dabba tana binsa jikinta ba kwari sae jiri
dake kwasarta amma bae bari ta fadi ba, yyi
sashinsu daita, har bakin kofarsu ya kaita ya
bude kofar yana kallonta, duk a tsorace
take, ya tura ta ciki har tana faduwa yyi
gaba, momy ta taso da sauri ganin yanda
'yar tata ta fado falon tana cewa "lfya
intisaar,"
.
Karfe tara abba ya shigo duba intisaar, har
lkcn inna na falonsu bata tafi ba, abba ya
shigo mata da fruits da tsire a leda ya ajiye
mata yana tambayarta ya jikin, tace "da
sauki abbana" sannan ta mike ta shige
bedroom ta bar masu falon, abba ya dubi
inna yace "nan xaki kwana knan yau?" tace
"aa dama kai nake jira, kasan iskancin da
wannan dan naka yyi mana yau" abba yyi
shiru yana kallonta, ta tabe baki tace "wllh
bkayi sa'an da ba bukar, shanya mu yyi a
nan ya gudu da dubu taran da kuka bashi,
sae wannan yaron faruuq yaxo ya dubata
kmr xata mutu" abba ya tsura mata ido yana
kallonta ya kasa cewa komai, "wllh ko minti
goma ba ayi da fitan yaron ba ka shigo, tun
safe yaki barin gidan nan yana kanta, gashi
ynxu jiki alhmdllh, yaron mutunci ne wllh"
abba ya jinjina kai cike da takaici yace "to
shknan yyi masa kyau, hkn yaga yafimasa
alkhairi," inna ta mike ta tabe baki tana
cewa "ka rakani bangarena" yace "to
sannan yyi sallama da momy, ta rakosu har
bakin kofa tana ma inna sae da safe. Karfe
goma haisam ya shigo duba intisaar, momy
tace "kar dae ynxu ka dawo haisam" yace
"wllh kuwa momy," bae bar sashin nasu ba
sae kusan karfe sha daya, suna ta hira da
momy da intisaar da ynxu bata jin ciwo a ko
ina na jikinta. Da safe ita da ihsaan suka je
gaida abba, kmr ba ita tayi ciwo jiya ba,
Aliyu na xaune a falon kansa sunkuye bayan
abban nasa yyi masa tatas, intisaar ta nemi
gefe ta xauna ganin Aliyu duk sae jikinta ya
mutu, ta gaida abba ya amsa da fara'arsa
yana tambayarta jiki, tayi murmushi tace
abba da

11 / 41