Author : Khaleesat Haidar Category : Romance
da sauri
tana kallonsa tace "gida?"yace "yea," ta
daure fuska tace "kmr ya na kwana
dakinka," ya daura kansa kan kirjinta yace
"kmr hka," ta turasa da sauri, ya kashe mata
ido yace "am serious fa" tayi shiru gabanta
na faduwa ga haushinsa da ya cikata, ta
dago kai tana kallonsa wani mugun
tsanarsa na yawo a xuciyarta, lalle ma ya
rainata, lst thing da xata so a rayuwarta knn
wae Aliyu ya kusance ta, Allah ya kyauta,
ganin amsar ta yake jira ne don ya tsura
mata ido yasa ta dan marairaice tace "to ka
bari muje gidan yau mana, idan yaso da
daddare idan mun dawo sae na kwana
dakinka," nn da nn ya rikice mata "ki rantse
fateema," ta dan fara kame kame, can dae
taga meye to, axumi ne dae guda ukukuma
xata iya, ta gyara xama da kyau tace "wllh
wllh," ya rungumeta ta turasa da karfi don
tsanarsa kara yawa yake a xuciyarta idan
yana hada jikinsa da nata, ta mike tsaye tace
bari naje na shirya.
snn ta shige cikin gidan ya bi ta da kallo,
shikam baya son ya kara forcin dinta ya
kwana da ita. Yana tsayebakin motarsa yana
jiranta don tuni ya gama shirinsa, ta fito
sanye da shadda brown colour am mata
dinki riga da skirt ya sha aiki, tayi daurin
dankwalin nata kmr headtie, tayi mugun
kyau, ta rike handbag dinta brown colour,
snn ta yafa mayafi light brown, flat shoe ta
saka don ita bata sa heel sbda tsayinta, tun
fitowarta Aliyu ke kallonta har ta karaso
kusa da motar, ya tabe baki ya kauda kansa,
bata burgesa ba kam, shi ma shaddar ce a
jikinsa brown colour, intisaar bata ji ddin
hkn ba, shima taga alamar bae ji ddi ba, ya
shige motar, ita ma ta shiga gaba, snn yaja
motar suka bar gidan. Karfe sha daya suka
isa gida, har wani bari jikinta yake yi tun
kan ya gama parkin din motar, ya fixgota ya
hade rai yace "bana son hauka, don kika yi
provokin dina wllh sae na juya motar nn,"
bbu ko alamar wasa a tare dashi, nn da nn
ta kame kanta suka fito daga motar, suna
fitowa kuwa ta kwasa a guje tayi cikin
gidan Aliyu ya bi ta da sauri amma tuni ta
shige gidan, hknyyi mugun basa haushi yyi
kwafa ya bi bayanta, intisaar na shiga kan
momynta ta fara daura idonta,ta fito daga
bangaren inna, tayi 'yar karar farin ciki ta
karasa da gudu da murnarta ta rungumeta,
momy tayi mamakin ganinta sosae, ta dago
kanta tana kallonta tace "meye hka fateema,
daga ina hka" tayi dariya tace "daga gida
mana momy" shigowar Aliyu yasa momy ta
turata gefe ta fara wucewa abinta, ta juya
tana kallon Aliyun har ya karaso inda take ta
kauda kanta, ya riko hannunta yace "can xa
mu fara xuwa," ya fadi yana nuna
matabangarensu,
.
ita dae bata ce komai ba ya ja ta har suka
isa sashinsu, yyi sallama snn suka shiga
falon, ihsaan ta fito daga daki tana ganin
yayarta ta rungumeta tana mata oyoyo da
murnarta, ya nemi kujera ya xauna, ita ma ta
xauna rungume da kanwartata tana
kallonta tace "momy fa ihsaan," ihsaan tace
ta kwanta a daki, ta juya ta sace kallon
Aliyun, shi ma yadan kalleta snn ya jawo
ihsaan yana mata wasa, intisaar ta mike
jikinta a sanyaye ta shiga dakin da sallama,
ta karasa kusa da momyntata dake kwance
tace "momy ki fito ku gaisa da ya Aliyu,"
uwar ta galla mata harara tace"fice min a
daki," jikinta a mace ta fito daga dakin,
taxauna gefensa ta kirkiro murmushi xata yi
magana ya riga ta, "momy na bacci ko," ta
gyada masa kai kawae, yyi murmushi yace
"to xo muje gun inna, ltr sai mu dawo," bata
ce masa komai ba ya jawo hannunta yana
rike da ihsaan suka bar falon, ita kam bata ji
ddin abinda momy tayi ma ya Aliyu ba, suna
tafe ne gabanta na faduwa kar su hajiya su
gansu, don tasan su kursum duk sun tafi
islamiyya sae karfe daya, ya lura da ita yyi
dariya yace "ae su hajiya basa nn sun tafi
biki kaduna tun friday, ammayau xasu
dawo," hkn yasa ma ya sami confident din
kawo ta gida, ita dae bata ce masa komai ba
har suka isa sashin inna, tana gaban TV a
xaune kmr xata shige ciki wae nn kallo take,
intisaar ta fixge hannunta daga na Aliyu ta
fada falon da gudunta, har sae da ta tsorata
innar, ta fasa ihu "innata kina ina," inna ta
mike da sauri tana mitsike ido, sae kuma ta
fashe da kuka ta xube kasa tana cewa,"ashe
dae xasu kawo min ke 'yar nn, kullum sae
na xubda hawaye a kanki a gidan nn da
daddare, ga Bukar gantalalle yaki barin a kai
ni gidan shi da 'yar banxan yarinyar nn
Nafisa,
.
intisaar ta kankameta tana tuntsira dariya,
ita ma ta fasa dariyan suka dinga yi, ihsaan
na taya su, Aliyu kam jingina yyi jikin kofa
yana kallonsu yana murmushi, can inna
tadago tana kallonsa tana washe baki tace,
karaso mana jikalle,shigo ka xauna, ni anya
ma akwae abinci a gidanka kuwa Aliyu,
naga duk yarinya ta fiffige kmr kaxa," ya
galla mata harara yace "to ki siya ki kai min
mana," snn ya harare intisaar din yace "nn
da minti talatin ki shirya xamu wuce," inna
ta mike a fusace tace "ku wuce gidan
ubanwa, dagaxuwan yarinya xata shirya ku
wuce, ae in kaga fitarta a gidan nn sha
biyun dare ne yyi wllh" ta koma ta xauna
tana huci, ya girgixa kai, ya fice ya bar mata
falon, nn inna ta sa ta gaba bayan ta hadata
da fura mai sanyi tana mata tambayoyi,
cutar ki yake yi a gidan ko, da gske ne bbu
abinci a gidan nasa ko, to me kike ci ni
Rahmatu, ynxu ma nasan kila Bukar ne yace
ya kawo ki nn ko, to wae a ina gidan yake
sun ki gaya min da na ringa xuwa kullum da
kaina, intisaar ta fara tarin karya ta buge
innar tace "kae inna ae gashi kinsa har ina
kwarewada wa innan tambayoyin naki, inna
ta koma gefe da sauri tace "yi hkuri to gama
tukunna," hka intisaar suka dinga cafter da
inna dake ji kmr ta maida ta ciki har su
Zainab suka dawo gidan, duk suka yi
murnar ganinta sosae suka sa ta gaba sae
kallo suke, kursum tace kai kinga yanda kika
yi wani fresh da kyau intisaar, intisaar ta
galla mata harara tace "a inda bbu fresh din
da kyau ba," duk suka dinga dariya, ita
kanta tasan tayi kyau sosae, ramewa kadae
ne tayi, inna tace "ku rabu da ita ciki ne da
ita" nn da nn intisaar ta hade rai tana kallon
innar, suko sae tuntsira dariya suke, inna
kuwa ko a jikinta sae tauna goranta take,
suna xaune a hka Aliyu ya shigo falon duk
suka yi tsit bayan sun gaishesa bnda
intisaar dake ta xuba abinta bata kara kallon
inda yake ba, ya daka mata tsawa yace"kina
jiran abba yaxo ya same ki a nn ne, kafin ki
gaida shi," ta mike da sauri tace "lah na
manta," ta ja gyalenta tabi ta gefensa ta fice
daga falon tayi bangaren Abba, ya bi ta a
baya, su xainab suka kwashe da dariya inna
na taya su.
.
Da fara'arta ta shiga falon Abba ta
rungumesa tana dariya tace"Abbana ina
yini," shima yyi dariya ya amsa yana kare
mata kallo snn yace "baki da lafiya ne
fateema," ya juya ya hade rae yana kallon
Aliyun da ya nemi kan tiles ya xauna yace
"bata da lafiyane," ya fara kame kame kmr
munafuki yace "Abba lafiyarta qlau ka
tambayeta," abba yace wae hka fateema,
Aliyu ya gyada mata kai da sauri yana
kallonta, ta galla masa harara, snn ta
mairaice murya tace "ni Abba makaranta
nke son na koma lkci yana ta
wucewa,"Haiydar Abba ya juyo yana kallon
Aliyu yace, "amma lst tym da ka xo nn nai
maka maganar karatunta me kace min,"
Aliyu aka fara kame kame da shafa kai "No
Abba dama fa, dama tun lkcn nayi mata
magana tace min ba ynxu ba tukun shine
yasa ma ban sake mata maganar ba," Abba
ya juya yana kallon intissar da ta tsaya kallon
Aliyun da mamaki, yace"wae hka ne
fateema" Aliyu ya shiga gyada mata kai wae
tace hkne, ita kam ta rasa dalilin da yasa
taga Abba da Aliyunsa kmr basa shiri kmr
da, don dae tasan duk iskancin da Aliyu
yake da wuya abba yace masa komai sae
dae yyi ta kallonsa, yau kumataga ya hade
masa rae kmr wanda yyi masa babban laifi,
ta kalle Abba tace "ehh abba ya taba min
mgna sau daya," Abba yace "ok, wni
makarantar kike so," tace "bayero Abba,"
"medicine kika ce xa kiyi ko," ta gyada ma
Abba kai, Aliyu yace"ke din ce xaki iya
medicine? Abba baxata iya ba" abba ya galla
masa harara yace "kai din da kayi kai goma
gare ka?" Aliyu bae ce komai ba ya kauda
kansa, Abba yace "sae kaje kayi abinda ya
dace, ta fara karatu vry soon, idan nace vry
soon, i mean vry soon" ba tare da ya kalle
abban ba yace "to abba," intisaar ta mike
tsaye tace " Abba sae anjima, ngd" abba
yace "yaushe xaku koma gida," ta dan sace
kallon Aliyu tace "aa abba ni kwana xanyi
dama" Aliyu ya juya da sauri yana kallonta,
amma bae ce komai ba, abba yace "to
shiknn nima fita xanyi sae na dawo, ina da
magana dake " tayi ma abba Allah ya kiyaye
snn ta fice daga falon.
Aliyu ya mike yyi masa sallama shima ya fice,
da sauri ya bi bayanta,amma tuni har ta
shige falon inna, ya shiga falon shima ransa
a hade yace "wllh xuwa karfe shidda
kishirya kafin na dawo," ya fice daga falon,
ta tabe baki, tana kallon inna da ta bude
baki tana kallon bakin kofar da ya bari,
intisaar tayi dariya tace "innarufe bakin,"
inna tace "ae abun ne kmr wani
mahaukaci," ynxu irin xaman da kuke yi knn
intisaar, intisaar ta tabe baki tace "wae don
nace xan kwana shine wae baxan kwana
ba," inna tace"to uban me xaki masa a
gidan, manta dashi kawae ai in kin koma
gidan nn ke da kanki kika ce xaki koma,"
intisaar ta dinga dariya da jin ddin abinda
inna ta ce mata, nn suka dinga hira har dae
intisaar tace ma inna bari taje wajen momy,
snn ta yi bangarensu. Bayan sllhn isha'i Aliyu
ya shigo gidan,intisaar har ta fidda rai da
ganinsa ta yi xaton ya hkura ne, ya tsaya
masu kmr soja a bakin kofa wae ta tashi su
tafi, intisaar ta yi kmr bata gansa ba tanata
kallo abinta, kiri kiri inna tace bbu inda xae
je da ita, kwana da kwanaki xata yi a gidan,
sae ta gaji don kanta tace xata koma, ya
hade rai yana ta kallon intisaar din dake
kwance kan kujera tana taunar cingam, ko
kallon inda yake ma bata yi ba, yasauke
ajiyar xuciya tare da kwantar da murya
ganinba ihunsa xae sa inna ta basa intisaar
ba yace "don Allah inna ki bari, akwae fa
inda xamu ynxu," ya kalle intisaar din yace
"kiyi mata bayani mana fateema, wllh xuwa
nxt wk sunday xan kawo ki kiyi sati ma idan
kina so," intisaar ta tabe baki tace "ka dae je
kawae nxt wk sunday din sae ka xo
daukata," snn ta mike ta shige bedroom, ta
barsa nn a tsaye, inna tace "to ka dae ji,"
snn ta kashe wutan falonta tace "Allah ya
bamu alkhairi nima kwanciya xanyi, sae da
safe," snn ta shige dakin ita ma ta kullo
kofar.aleesat HaiydarAliyu ya kasa cewa
komai sae kofar dakin da ya tsura ma ido,
ya dde wajen a tsaye, can dae ya juya ya fice
daga falon ya rufe kofar, inna na jin fitarsa
tace "munafuki kawae, ki kwantar da
hankalinki, ke da barin gidan nn sae ran da
kika ce xaki tafi," intisaar ta gyara
kwanciyarta don dama har tayi shirin bacci
tace "kin ma san mene inna, bari na yake ni
kadae fa kmr mayya a gidan, kuma bae ma
san ci na da sha na a gidan ba, sae nayi sati
ban gansa ba ma," inna ta bude baki tana
kallonta "ke 'yar nn da gske," ta tabe baki
tace "uhum ke dae barikawae, wllh kuwa
inna," inna tace "to ni ae ca nke ciki ne da
ke," intisaar ta galla mata harara tace " kaji
ana mgnar arxiki wnn tsohuwar wae ciki,
cikin lafiya, ni bnda komae" inna tace "ikon
Allah, kina nufin har ynxu bbu abinda ya
shiga tsakaninku intisaar" intisaar tayi mata
bnxa ta juya mata baya snn ja bargo ta
gyara kwanciyarta, inna xata yi magana
wayarta ya shiga ruri,
.
ta mike da sauri ta dauko tana cewa "ina
xan danna ke," intisaar tace"kai inna
shekararki nawa da wnn wayar amma har
yau baki san ina ake dannawa ba," inna tace
"aa wani lkcn rudewa nake yi ne wllh," da
kanta tayi pick din wayar dan intisaar kin
mikewa tayi, ta doka uban sllma tana
tambayar wanene, can kuma tace"A'a Bukar
ne, lfya? Ayyo na ba fateema, to ga ta nn,"
inna ta mika ma intisaar wayan, intisaar
gabanta yafadi ta amsa a sanyaye tace
"Na'am Abba," murya can kasa tace "to
Abba," snn ta kashe wayan, sae tafashe da
kuka, inna ta rude "ke lfya me ya faru?" cikin
kuka tace "kina ganin inna hada ni da abba
yaje yyi ko," inna ta hade rae "to uban me
Bukar din yace maki ynxu," ta goge
hawayen idonta tace "waenaje yana
nemana," inna tace "to bbu inda xaki je yi
kwanciyarki, ni nn Rahmatu nace bbu inda
xaki je, idan Bukar din ya isa yaxo ya
tunkareni" intisaar ta mike tsaye ta dauki
hijab har kasa tasa tace "ba dani ba xa ayi
wnn ba inna, Abbana na kirana xanje na
amsa kiransa," snn ta fice ta bar ta nn a
tsaye. A hankali tayi sallama falon abba ta
shiga, suka yi idohudu da Aliyu dake xaune
falon a kasa gefen abba, ta nemi guri ta
durkusa ta gaida abba, ya amsa yana
kallonta yace "ki shirya maxa ku wuce gida
fateema," a sanyaye tace "to abba" don bata
iya ma abba musu, abba yace "ynxu meye
naki a wajen inna, xainab taje ta dauko
maki," ta girgixa kai tana kkrin maida
hawayen idonta tace "bbu komai, kawae
jakata ne, wani lkcn xan dauka," Abba
yace"yauwa fateema, maxa tashi kuje kuyi
ma momyntaku sllma, ku kama hanya ku
wuce gida," ta mike tsaye ba tare da ta bari
abba ya ga hawayen da take yi ba ta fice
daga falon bayan tayi masa saeda safe ,
Aliyu ya mike shima yyi masa sae da safe, ya
bi bayanta, bae ce mata ba, ita ma bata ce
masa ba har suka isa sashinsu, falo suka
tarda momy, ya nemi kujera ya xauna ya
gaidata kmr wani munafuki, ta amsa batare
da ta kallesa ba, ita dae intisaar tv kawae
take kallo, suka dde a falon a xaune momy
na gyara ma ihsaan gashi na xuwa sch
gobe, ganin har karfe goma ya wuce Aliyu
ya kasa tashi ne yasa intisaar ta mike tana
kallon momyn tace "momy xamu tafi sae da
safe," tace"Allah ya kaimu,
.
*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.thn.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > tophausanovels@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Top Hausa Novels
Twitter: Top Hausa Novels
Telegram: Top Hausa Novels
Watsapp Group: https://chat.whatsapp.com/BRN8VEA8BczD61ZGjoOUod
********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
Aliyu ma ya mike tsaye yyi mata sae da safe
tayi kmr bata ji sa ba, ya ajiye ma ihsaan
dubu biyar ta sha ice-cream snn suka fice,
ita kam bata ga laifin momy ba. Har suka isa
gida bbu wanda yyi magana tsakaninsu, shi
dae ne ke ta waya da safeenah suna
soyewa, yana parkin ta bude motar ta fice
tayi cikin gidan da sauri, ya bi bayanta tun
kan ta hau sama ya risketa ya fixgota, yace
"direct bedroom dina xaki shiga, ba sae kin
shiga naki ba," ta turasa tana masa wani
irin kallon raini, "nayi maka uban me," bata
rufe baki ba ya dauketa da mari, ta fasa ihu
ta durkushe wajen, ya bita da sauri, ya
rikota, kuka ta shiga yi tana ihu, dukya
gigice ya rungumota yace " don Allah kiyi
hkuri fateema, am vry srry," ko sauraransa
bata yi ba taci gaba da rusa kukanta, ya
dauketa cak, ya hau sama yyi bedroom
dinsa da ita, duk irin yanda yaso intisaar ta
basa hadin kai kin yrda tayi, don kuka ta
dinga masa sosai tana rokansa yyi hkuri
bata so, hkn yasa ya kyaleta kawae yyi
kwanciyarsa bayan ya lallasheta yace tayi
baccinta baxae mata komai ba, ta jima bata
yi bacci ba sbda tsoro, gnin kmr Aliyun yyi
bacci ne yasa ta dan kwantar da hankalinta
ita ma ta fara baccin, duk da kuwa idonsa
biyu ba baccin yyi ba, yana ganin ta fara
bacci kuwa ya mike ya bar mata dakin ya
kohaleesat HaiydarDa asuba Aliyu ya shigo
dakin yin alwala, tayi shame-shame hankali
kwance tana bacci, kallo daya yyi mata ya
dauke kansa ya shige bathroom, yana
fitowa ya bude fridge ya dauko ruwan gora
mai sanyi ya bude ya xuba a hannunsa ya
watsa mata, ta mike xaune a firgice tana
kalle kalle, ya juya ya fice daga dakin ya
wuce masallaci, ta yi tsaki, a xuciyarta tace
Allah ya isa na, snn ta mike tsaye ta shige
bathroom tayi alwala, tana idar da sallah tayi
jigum a dakin, can dae ta mike xata fita
idonta ya sauka kan wayarsa da yyi haske a
gaban mirror, ta dan kalli bakin kofar snn ta
karasa ta dauki wayar, taga msg ne, ta bude
taga na safeenahne, ta tabe baki bata damu
ta karanta ba ta fita daga inbox din kawae,.
ta xauna gefen gadon wayar a hannunta ta
shiga hotuna, duk hotunansa da na safeena
ne, wasu yana rungume da ita, wasu tana
kwance jikinsa, wasu suna kiss, gasu nn
dae ba kyan gani, duk da ba son Aliyu take
ba sae da taji baddi, wani bakin ciki ya
dinga yawo a xuciyarta, tana nn a hka har
Aliyu ya shigo dakin tayi saurin boye wayar
cikin hijab dinta, ya galla mata harara
yace"fice min a daki kar nayi ball dake," ta
mike ta fice daga dakin ba tare da ta kallesa
ba wayar tasa a hannunta, yyi kwafa yace
"xaki gane kuranki ne yarinya," har Aliyu ya
fita ranar bata ji yyi mata maganar wayarsa
ba, gabanta kuwa sae faduwa yake kar yaci
ubanta. Da yamma wajen karfe biyar tana
kwance a daki tana kallo, aka bude kofar
dakin ta mike xaune a dan tsorace tana
kallonsa, daga bakin kofar yace "ina jiranki a
falo, kuma kar ki fito min da shigar nn na
iskanci," ta tabe baki ta ci gaba da kallonta
kawae, bayan kmr minti goma ya sake
dawowa, ta mike a dan tsorace yace "kina
hauka ne,me nace maki," ta hararesa tace
"gani nn xuwa," yyi murmushi ya juya ya
wuce, ta dauko hijab dinta har kasa tasa ta
sauko falon, dama tasan bako na falon
tunda har ya kira shigar ta ta iskanci, da can
da take sa wa bae san na iskanci bne, ta
karaso falon ta xauna tare da gaisuwa "ina
yini," ya dago yana kallonta yyi murmushi
yace "lfya fateema, ya gida ya amarci," komai
nata ya tsaya cak ganin faruuq, ta kasa
dauke idonta daga nasa, shi kansa
yanayinsa ya canxa duk da yyi kkrin
boyewa, yyi yake yace "kai wnn kallon kmr
kin ga dodo intisaar,"ta dauke kanta da
sauri ta kasa cewa komai ga hawayen da
taji na neman cika idonta, Aliyu yana danna
wayarsa duk da hankalinsa na kanta yace
"kikawo masa ruwa mana" da kyar ta mike
jikinta a sanyaye tayi hanyar kitchen ta
dauko faranti da cupta daura juice da ruwa
a kai ta dawo falon ta dire gabansa, yyi
murmushi yace "thank yhu fateema"
.
tajuya xata bar falon Aliyu yace ina xaki, hira
yaxo