INTISAAR Ramuwar Kaddara By Khaleesat haidar

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Romance

Chapter   19 / 41

54K to 57K   out of 122.8K words

kuyi fa, kin juyowa tayi sae da ya sake
kiranta snn ta dawo ta xauna tana kirkiran
murmushi, Aliyu ya mike ya bar falon yana
mata wani irin kallo, ko lura da hkn ma tayi,
faruuq ya dago yana kallonta yace"kinyi
mamakin gani na ko," bata ce komai ba yyi
murmushi yace "ya amarci," nn ma shiru
tayi, "yace common fateema, baki yrda da
kaddara bne, ki tuna fa matar mutum
kabarinsa," ta gyada masa kai kawae, yace
"cheer up kanwata," tayi murmushi kawae,
yace "yauwa ko kefa," nn dae intisaar ta
sake suka dinga hira da faruuq din kmr ba
komai, Aliyu ya sauko ya xauna falon shi dae
bae sa masu baki ba sae dae yyi murmushi,
intisaar tace "yayanain xubo maka abinci
to?" faruuq yace "haba dae sae kace jaki
daxu fa muka ci da Aliyu," ta juya tana kallon
Aliyun ya harareta ya dauke kai, faruuq bae
bar gidan ba sae kusan maghrib, har bakin
kofa ta rakasu da yake shi da Aliyun xa su
fita kuma, tace"yayana ina da magana da kai
fa," ya juya yana kallonta yace "ina jin ki
kanwata," ta harare Aliyu daya xuba masu
ido tace "ba da kai nke ba," yyi murmushi
yyi gaba, faruuq yyi dariya yace "to ina
ji,"tace "yayana dama nace don Allah don
annabi, tunda Allah yyi ni ba matarka bace,
to ka nemi 'yar uwata mana," ya juyo da
sauri yana kallonta yace"wa?" tace "zainab,"
ya harareta da wasa ya juya xae wuce tace
"haba yayana, abinda yyi zainab shi fa yyi ni,
ni da xainab daya ne" yace "haba dae, da
gske?"
.
ta lura yana son shashantar da maganar ne,
ta dinga masa magiya kmr xatayi kuka, daga
karsheyyi murmushi yace "shkkn kanwata
xanyi shawara,"ta ce "haba yayana kasan fa
ba talarta nake mka ba,tana da manema
dayawa, kawae dae xumuncin mu nake so
yyi karfi kuma...." yyi dariya yace "to shknn
fateema, ngd da kulawarki sae da safe," ya
juya da sauri ya bar wajen, tayi dariya ta
daga masa hannu ta koma cikin gida. Bayan
kwana biyu da xuwan faruuq intisaar na
daki a kwance tana ta game da wayar Aliyu
da ta mayar nata don har lkcn bata gansa
ba bare ta sa ran xae mata maganar wayar
tasa, hkn yasa ko da yaushe cikin kiran inna
da Zainab take su yi ta hira don akwae kudi
sosai a wayar, momy dai sau daya ta kirata
suka gaisa, abun da ya bata mamaki bae
wuce na rashinganin kiran safeena ba don
jira kawae take ta kira tayi mata rashin
mutunci amma har lkcn bata kira ba kuma
bata yo tex ba, sau dayawa kiran
abokanansa da 'yan mata kan shigo amma
ko sau daya bata taba dagawa ba, ta goge
duk hotunan haukan da sukayi da safeenah
dake cikin wayar, snn tayi deletin tex din
safeenar da na mata da dama a wayar,
karar bell taji downstairs ta mike a dan
tsorace don Aliyu baya dannabell, ita tun
ranar ma da ya fita raka faruuq bata sake
ganinsa ba, kar dae Hajiyarsa ce ta dawo
don ita tsoran matar nn take, a tsorace ta
sauko kasa cikin sanda ta isa bakin kofar ta
dan leka ta glass taga Anty Nafisa ce, ta
bude kofar tare da doka tsalle ta rungumota
tana mata oyoyo cike da farin ciki, Anty
nafisa tayi dariya tace "ni kar ki karya ni,"
suka shigo falon intisaar na tambayarta
Maryam fa, meyasa har ynxu bata xo ba,
Anty nafisa tace sun fita waje da abbanta ai,
intisaar tace Anty mu hau sama mana, Anty
nafisar tace "ina fitsararren mijin naki,"
intisaar tace "uhm baya nn," snn ta mike ta
kawo mata lemo a fridge ta dire mata a
gabanta tana tambayr ya su shaheed da
ummi, Anty Nafisa tace suna nn lfya, snn ta
mike ta hau sama tana cewa "bara naje
naga dakin amarya," intisaar ta bi ta a baya
tana dariya, hira suka dinga yi da Anty
Nafisa tana bata lbarai, duk da anty nafisar
taso jin irin xaman da suke yi da Aliyun,
amma intisaar ta dinga shashantar da
batun, karfe sha biya tace bari taje ta daura
girki tunda yini Anty Nafisar xata mata, Anty
Nafisa ta mike tana inspect din dakin tace
"duk da dae nasan ke ba kaxama bace
intisaar bari dae na dudduba ko ina, don
randa naje gidan fadila duka ne kadae ban
mata ba, gskya mijinta na kkri don fadila
muguwar kaxama ce ta karshe," intisaar
dae tayi dariya ta sauka kasa don ita kam
tun tana karamarta take da kyankyani, kuma
ko a gida ma inna na yaba tsaftarta, ko
shakka bbu tasan Anty nafisa baxata ga
datti ko kadan a dakinta ba, dama ko ina na
gidan, lafiyayyar jollof rice da plantain sai
farfesun kaza ta shiga girka ma Anty nafisa,
ta dan hada mata cream salad kadan, snn
tayi ginger drink, gidan ya kauraye da
kamshin girkinta, tana jerasu a faranti don
sama xata kai mata taji an rungumota ta
baya, ta tsorata sosae xata fasa ihu ya juyo
ta yasaka bakinsa cikin nata, ta turasa da
karfi tana maida numfashi, "meye hka," ta
tambayesa tana hararan sa
yace "ni kika yi ma girki?" tayi masa wani
irin kallo tace "kai a su wa," ya tabe baki
yace "kinga ina cin ko wani girki? Ae wnn
kaxanta ce kika hada," bata kara ce masa
komai ba ta gama jera abincin a faranti ta
dauka xata bar kitchen din, ya fixgota, saura
kiris farantin ya fadi daga hannunta, ta xaro
ido tayi saurin ajiye farantin kan table, "wae
meye hka don Allah," ta tambayesa kmr
xatayi kuka, yace "to dibar min nawa," ta
galla masa harara tace "ban yi girki da kai
ba, kai da ba ko wani girkikke ci ba," yace
"to kuwa baxa ki bar kitchen din nn yau ba
knn," ta ce " Anty Nafisa na jirana fa a
sama," ya dan wara ido yace "Nafisa?
metaxo yi?" muryar Anty Nafisar suka ji tana
cewa "wae store din kitchen din kike girka
min gaba daya e intisaar, wnn ae sae
yunwar ta galabaitar dani," da sauri har
yana neman faduwa ya shige bayan kofar,
intisaar bata san lkcn da ta kwashe da
dariya ba har da xubewa kasa, Anty nafisa
ta shigo kitchen din tana cewa "ohh dariya
ma na baki, ai gskya ne," intisaar tace"na
gama anty ynxu dama xan kawo maki," ta
dauki farantin, Anty nafisa tace "to ina na
mijin naki fa," intisaar ta girgixa kai tace "ae
shi ba ko wani girki yake ci ba Anty," nafisa
ta tabe baki tace "sae irin na uwarsa Aisha
yake ci knn," intisaar ta dinga dariya, Anty
nafisa ta karbe farantin tace "ni bani kar ki
xubar min da abinci, ae gskya na fada," suka
bar kitchen din a tare suka wuce sama, ae
ba karamin farin cikin saukowar Antynafisar
intisaar tayi ba, kuma tunda ya shige bayan
kofa baya son ta gansa tasan bae da gskya
ne. Ni kam koma wacece ke ci min gaba da
lbri gskya bn yafe mata ba, Inteesar....
.
Karfe biyar saura anty nafisa ta fara shirin
wucewa gida, intisaar duk sae taji wani iri
tayi jigum tana kallonta kmr kar ta tafi, Anty
nafisa tayi dariya tace "kar ki damu
daughter, xan dinga xuwa a kai a kai ina
duba ki, tunda dae ke Allah bae sa kinyi
sa'an miji ba," dae-dae nn Aliyu ya shigo
dakin da sallamarsa, nafisa ta xuge handbag
dinta ta sakale a hannu tana kallon intisaar
din fuskarta atsuke tace "daughter ni na
wuce sae wani lkcn," snnta yi hanyar kofar
ba tare da ta kalle inda Aliyun yake ba, da
sauri ya shige gabanta yana dariya yace
"haba momy, ina kika taba jin uwa na fushi
da danta," ta galla masa harara tace "da'alla
wuce ka ban waje malam," ya karbe
handbag din hannunta yace "ina! Ai yau nn
xaki kwana momy," tun tana gintsewa har
ta fara dariya ganin yanda Aliyu ya maida ta
kakarsa, ta koma ta xauna tace "sae ka fito
da kudin mota tunda Allah ya kawo ka,"
yace"tab, ni ban da kudin mota sae dae na
kai ki a motata," dole anty nafisa ta tilastasa
ya bata dubu biyar kudin mota snn ya
maidata gida a motarsa, bayan fitansu
intisaar duk sae taji ba ddi ta xauna ita daya
a daki tana rera kuka. Ranar friday daya
yyidae-dae da sati daya da xuwan Anty
Nafisa gidan kuma hkn yyi dae dae da wata
biyu da sati daya da kawo intisaar gidan
Aliyu, tana daki da daddare ta gama shirin
bacci wajajen karfe tara, Aliyu ya shigo
dakin nata ya tsaya bakin kofa, ta juyo tana
kallonsa, ransa a hade yace "ki shirya xamu
fita," snn ya juya ya fice daga dakin, ta dde a
tsaye bakin madubinta tana tunanin to ina
xasu je da daddaren nn, can dae tayi tsaki
tayi kwanciyarta a xuciyarta tace bbu inda
xani, can bayan kmr minti sha biyar ya
dawo dakin, ya daka mata wani raxannen
nn tsawa "wat?
.
Ina wasa da ke ne ko kin fara hauka ne?" ta
mike a tsorace don har ta manta rabon da
yyi mata irin wnn tsawar tun suna gida,
jikinta ya dau bari ganin bbu alamar wasa a
tattare dashi ta mike tsaye muryarta na
rawa tace "kayi hkuri, ni bn ji ka da kyau
bne," "baki ji ni da kyau ba?" ya tambayeta
yana mata wani irin kallo, ta girgixa masakai, yyi kwafa ya fice, ba shiri ta dauko
dogon rigarta na material ta saka snn ta
dauki hijab dinta har kasa ta sa, ta feshe
turare ta fito falon a sanyaye, yana tsaye ya
dafa kujera yana jiranta, ya dauki makullinsa
ya fita ta bi bayansa, suna fitowa ya rufe
gidan yyi hanyar garage ya bude motar ya
shiga, ta xaga ita ma ta bude ta shiga, ya ja
motar suka fita daga gidan, sun yi nisa
sosae, intisaar gabanta sae faduwa yake
don bata san inda xae kaita ba gashi bata
ga fuskar tambayrsa inda xasu ba, taga yyi
park gefen titi, ya juyo yana kallonta
fuskarsa a daure ya fara magana a hankali
"kina jina," ta gyada masa kai a dan tsorace
"wllh duk tambayar da xa a maki idan har
kika nuna baki san komai a kan tambayar
ba, xanyi gunduwa gunduwa dake, idan
kuma kin yi tunanin am jokin dare me,"
gaban intisaar ya shiga faduwa sosai ta
dinga gyada masa kai a tsorace...

INTEESAR BOOK 3

Aliyu bae sake ce mata komai ba sae gudun
bala'in da ya dinga yi kmr xae tashi sama,
hankalinta yyi mugun tashi ta ma rasa mae
xata ce masa don tsoro, ta dake daga
karshe da kyar Muryarta na rawa tace "wae
ni ya Aliyu ina xa ka kai ni ne don Allah," ya
taka brake yyi arkin da sauri yana kallonta
cikin tsawa yace "kika ce me?" ta tsorata
ssae ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba,
yyi mata wani mugun kallo yace "sayar da
ke xanje nayi," bata dago kai ba bare tace
masa komai yyi kwafa ya ja motar suka bar
wajen, lkci daya hankalinta ya kwanta
ganinsu da tayi anguwansu, yana gama
parkin kuwa ta bude kofa xata fita da sauri
yyi hanxarin fixgota yana hararta yace "kin
dae ji me na ce maki, kuma wnn hawayen
bana son ganinsa a fuskarki" ta fixge
hannunta ta fice da sauri daga motar snn ta
watsa masa harara hade da jan tsaki tace
"ban ji ba," tana fadin hka tayi cikin gidan
da gudu ya bita da sauri, tana isa gate cikin
rashin sa'a tayi tuntube tayi gaba xata fadi
yyi saurin rikota ta fado kansa, ta marairaice
fuska a tsorace tace "don Allah kayi hkuri ba
da kai nake ba," bae ce mata komai ba ya
shiga janta kmr wata dabba tana biye da shi
a baya har suka iso falon Abba, sae a snn ya
juya yana kallonta fuskarsaa murtuke yace
"Allah ya baki sa'a ki ki yin abinda nace
maki, wllh sae na kusan sumar dake a gida
yau," bata ce komai ba ya ja ta suka shiga
cikin falon, Abba na xaune remote a
hannunsa yana canxa tasha, Aliyu kadae ne
yyi karfin halin yin sallama ita kam inteesar
kasa wa tayi ji tayi hka kawae gabanta na
faduwa, ta xauna Aliyu ya xauna gefenta
snn ya gaida Abban nasa ba tare da ya
kallesa ba, Abba ya amsa bbu yabo bbu
fallasa snn ya kalli Inteesar da ta kirkiro
murmushi tana gaishesa ya amsa da
fara'arsa yana tambayarta ya gidan, ta
sunkuyar da kai tace lfya lau Abba, murya
can kasa Aliyu yace "ga ta nn Abba na kawo
ta," ko kallonsa Abba bae yi ba ya fara
magana kmr hka "tambayace kawae xan
maki Fateemah, amma gskya kawae nake
son ki gaya min kar kiyi min karya ban san
ki dakarya ba," tayi shiru gabanta na
faduwa tana kalln Abban, ya dan dau lkci
snn yace "wae da amincewarki Aliyu xae
kara aure?" ji tayi komai nata ya tsaya ta
kasa dago kai bare ayi expectn amsa daga
gare ta, nn da nn taji hawaye na neman cika
mata ido, Aliyu ya kamo hannunta ya hade
da nasa a boye, ta gane abinda yake nufi,
suka ji muryan Abba na cewa "magana nake
fateema kin yi shiru, sharri yyi maki ko?" da
ganin Abba kasan ransa a bace yake, da
kyar ta iya bude baki ba tare da ta kalli
Abban ba tace "eh hka ne Abba da sanina,"
Abba ya girgixa kai yace "karya kike," tayi
kkrin boye hawayenta tace "da gske Abba
na sani ni ce nace yyi," Abba yyi shiru yana
kallonsu gaba daya daga bisanni yace "to yyi
yau, baxan hanaka kara aure ba Aliyu kuma
ni kam bbu abinda xan ce maka da ya wuce
Allah ya taimaka, snn abu na karshe da nake
son na gaya maka shine ka tabbatar kafin
kayi auren naka 'ya ta ta fara karatu tayi
settle dwn idan ba hka ba wllh sae na
wargaxa komai, ka tashi ka ban wuri" bbu
ko dar bare damuwa Aliyu ya mike yace
"ngd Abba," ya sace kallonta, ita ma kallonsa
take hawaye cike idonta da ganinta ta shiga
wani yanayi da baxa a iya fassarawa ba ya
galla mata harara snn ya fice, Abba yyi
shiruyana kallonta snn a hankali ya fara
magana"kiyi Hkuri fateema, nayi dana sanin
hadaki daAliyu da nayi, kuma ni ban isa
hana shi kara aure ba, snn baxan ce kar ki
bi mijinki ba amma idan har kin ga baxa ki
iya xama gidan ba bayan auren nasa ni nn
nace ki tattaro ki dawo gida," kai kawae
take gyada ma Abba tana hawaye yyi mata
nasiha ssae yana kwantar mata da hankali
daga karshe yace ta tashi tashiga cikin gida
amma kar ta ce da inna komai tukun, ta
mike jikinta a mace tayi masa gdya snn ta
fita falon tayi bangaren inna tana kuka ssae,
tsaye ta gansa alamar ita yake jira, yana
ganin tayi bangaren inna ya daka mata
tsawayace "c'mon gida xa mu wuce ina kike
tunanin xa ki," ko kallonsa bata yi ba ta saka
gudu tayi sashin inna ya bi ta shima da
sauri, Kursum da ta fito daga gun inna knn
ta bi su da kallo baki bude, saura kiris ya
kamata ta afka falon inna tana mayar da
numfashi ta fasa ihu tare da xubewa
tsakiyar falon, inna dake daki ta fito da
gudu tana salati tace "me ya faru?? Daga ina
hka?" shi ko ya fixgota a fusace ya shake ta
hade da hada ta da bango yana huci yace
"don ubanki ina wasa da ke ne?" inna tayo
waje da ido snn tayi waje da gudu ta saki
kuka cikin daga murya tace "jama'a yau
naga ikon Allah xae kasheta gabana, Bukar
Bukar ka taho kaga abinda dan ka ke shirin
yi da daddaren nn"
.
Haisam ya karaso da sauri yana kallon inna
yace "me ya faru inna," tana kuka wiwi tace
"wllh Haisam ina daki na je ajiye kayan da
kursum ta gama goge min naji ihu kmr xa a
xaga falona, fitowar da xanyi wae sae ganin
Aliyu nayi shake da Inteesar yana duka yana
buga ta da bango, duk yyi mata kaca kaca
ko motsin kirki wllh bata yi yanxu ban san
ya ake ciki ba ka taimaka ka kira mun Bukar
don Allah," tana kai wa nn ta fashe da wani
kukan har da durkushewa kasa, Haisam ya
girgixa kai ya shiga falon innar da sauri dai
dai bakin kofa ya hadu da Aliyun rike da
hannun inteesar yana janta tana kuka tana
cewa "wllh ka kyaleni bbu inda xa ni," ya
buge mata baki Haisam yace "wae kai wani
irin mutum ne Aliyu 4 heaven sake" Aliyu ya
watsa masa wani mugun kallo yace "da'alla
can get out malam kar na buge ka," inna
tayi cikin gida da gudu tana rusa kuka lkci
daya tana kwala ma Abba kira, da sauri Aliyu
ya ja inteesar suka fice daga gidan tana
nonnokewa ya bude mota ya jefata ciki snn
ya shige motar ya tada ta, dae dae nn inna
ta fito kofar gidan Abba na biye da ita a
baya tace "maxa bi shi Bukar ya tada
motar," Abba ya girgixa kai cike da takaici
yace "kina ma Allah da annabi ki daina daga
min hankali a gidan nn baaba wnn wani irin
bala'i ne," bae jira mai xata ce ba ya koma
cikin gidan ransa a bace. Suna isa gida Aliyu
yyi parkin ya bude motar ya fito yana kallnta
har lkcin bata daina kuka da take ba ta hade
kai da gwiwa, cikin tsawa yace "ko sae na
jefar dake waje," taki dago kai bare ta tanka
masa, ya fixgota ta fasa masa ihu tana cewa
"wllh baxan shiga gidan nn ba ka mayar
dani gida," cak ya dauketa ya rufe motarsa
tana dukansa bae damu da hkn ba ya shiga
gida da ita ya haura sama ya bude dakinsa,
nn da nn ta saita kanta cikin muryar kuka
tace "ni ka ajiye ni," bae kulata ba ya isa kan
gado ya kwantar da ita ta mike da sauri ya
turata da karfi ta fada kan gadon snn ya
fada kanta, nn da nn ta hadiye kukan da
take xuciyarta na bugawa a hankali tace
"kayi hkuri ya Aliyu na daina kukan" ya dago
yana kallonta da ganinta kasan a tsorace
take, ta fara kkrin sauka daga kan gadon ya
rikota yace "bbu inda xaki yau nn xaki
kwana," kanta ce komai ya kashe wutan
dakin, ta fasa masa ihu ya buge mata baki
da karfi, ba karamin wahala ya bata ba, don
duk sae da ya jagwalgwalata, ganin irin
kukan da take da kuma yanda jikinta ke bari
duk da bae ma kai ga yi mata komai ba yasa
ya kyaleta tare da cewa "ki rufe min baki kar
na baki mamaki," ba shiri ta hadiye kukan
jikinta na rawa don duk ya tsorata ta, ya
rungumota ssae, snn ya dauki wayarsa yyi
dialin nmbr safeenah, kmr jira take yana
ringin kuwa ta daga, murya can kasa yace
"bbyna," ita ma a marairaicen tace "mijina,"
ya sauke ajiyar xuciya ya daura bakinsa kan
gashin inteesar da ta rumtse ido xuciyarta
na bugawa, yace "nayi missn naki ssae fa
bby, i need yhu safeena," ta danyi dariya
tace "matarka fa? Kaje ka sauke need din a
kanta mana," ya yamutse fuska yace "me
wnn take da shi da xata bani da ya wuce
wahala, naki nake so bbyna," tayi dariya
ssae snn tace "ka kusa samu dear na, ina
amaryartaka," yace "ga ki nn bbynah," nn
suka dinga xancen yanda 1st nyt dinsu xae
kasance bbu kunya bare tsoran Allah, a
hankali Inteesar ta shiga xamewa daga
rungumar da yyi mata, ya matseta da karfi
ta shiga kokuwa da shi, ya ki sakinta, ya
kunna wutan dakin yana kallonta, hawaye
ne kwance fuskarta, ta boye fuskar da sauri,
bbu yabo bbu fallasa yace "nayi maki wani
abu ne kike min kuka don munafurci?" tayi
shiru bata ce komai ba har lkcn hawayen da
take yaki tsayawa, ya dada rungumeta ya
kashe wutan ya ci gaba da wayarsa, suna
nn a hka yana ta hirarsa da safeenah har
bacci ya dauke Inteesar
.
Karfe sha biyu da rabi ya kwantar da ita a
hankali, snn ya shiga bathroom yyi wanka
ya koma wani dakin yyi kwanciyarsa.

19 / 41