min Anty ne? "Ya buɗe baki zaiyi magana wayarsa ta sake yin ƙara a karona ashirin da huɗu.
Kallon Nana yayi wacce ke fama da figar kajin da AJ ya kawo ɗazu wai sune abincin dare haɗida dankalin turawa. Ya ce "Idan ban dawoba kisaka min nawa a ɗaki komai dare zan zo na ci. Nana ta ce "to yaya amma dan Allah karka daɗe kaji...kuma ka gaida minda Anty na.ta faɗa tana dariya. Jin wayarsa ta sakeyin ƙarane yasa ya amsa da cewa zataji, sannan ya bargidan.
SARAH kuwa iya ƙuluwa yau ta ƙulu hakanne yasa tayi alƙawarin saita nuna masa fishinta. Kallon sa takeyi cikin mantawa da laifin da yamata ganin irin wani kyu da yayi. Da sauri ta rungume shi tana mai jin cewar ko ina zasu iya shiga dashi ba wanda ya isa ya raina mata saurayi. Yau kan A.J ya ajiye komai a gefe ya kama hannun ta suka nufi gurin da a ke gabatar da birthday ɗin.
Cikin dare misalin ƙarfe 12 Daddy ya dawo gida. Yana zuwa ya nufi ɗakin sa, sai yaga ɗakin a buɗe, hakanne yasa ya nufi ɗakin Mommy yana kiran sunan ta. A'leza! "Da sauri Mommy ta fito aɗaki domin kuwa itama barci ya gagareta, tinda SARAH ta fita bata dawoba, shi kuwa Samuel dama yasaba. Cikin yarunsu na tibi Daddy ya ce "Nace ki rufemin ɗaki lokacin da zan fita amma na dawo naga ɗakina a buɗe? Ya ce gaba da cewa...Shin kunsan irin kuɗin da na ajiye a cikin ɗakin! Kuma kinsan kuɗin waye? Lokaci ɗaya fuskar Daddy ta koma ta asalin sojojin da ransu ya ɓaci. Ya ce "Oyaa muje ɗakin mu duba.
Tin daga bakin ƙofar ɗakin sukaga kuridon kuɗin a buɗe, cikin sauri Momy ta ƙarasa zaro kuridon kuɗin. Mommy ta ce "Samuel Samuel Samuel! Sai kawai ta rusa ihuu!. Amma sai taga Daddy na murmishii ya ce "Koma waye yanzu zamu kamashi. Mommy ta ce "Ban gane ba? Daddy ya ce "Tin lokacin da akamin satannan na ƙarshe naga abun yayi yawa shine na faɗawa wani abokina shikuma yabani shawarin nasaka CCTV camera aɗakin zan kama kowaye. To hakane yasa na bar ɗakin abuɗe tin da rana.
Cikin mamaki Mommy ta ce "Ar You serus? Daddy kuwa cikin murmushin da yazama na ɓacin rai ye ce "Yes. Nann take ya ɗauki computer ɗinsa da yayi connektin da shi ya buɗe.
Kallon abun sukeyi har a kazo lokacin da SARAH ta shiga. Kallon juna sukayi cikin mamaki, basu ƙarasa mamaki ba saida sukaga ta ɗebi kuɗin sannan zata fita, saikuma sukaga tashiga ƙarƙashin gado. Saiga Samuel shima ya shigo, shima bayan ya ɗiba sai ya shiga toilet...haka dai suka cigaba da kallo har lokacin da Daddy ya shiga, har SARAH da Samuel suka fita.
Lokaci ɗaya Daddy ya koma tamkar bashiba tsabar ɓacin rai! Ita kuwa Mommy kasa yin mgn tayi tsaɓar tsoro domin kuwa tasan yaude mai hana Daddy karya Samuel da SARAH sai Allah, cikin muryasa ta mazaje ya ce "Ina SARAH? Mommy ta ce "Ba ba ba ta ba "cikin ihuu ya ce "Ina SARAHHHHHHHHH!!!!!!!!!!!!!!? Mommy ta ce "Bata dawoba....📝
*PAGE* 👉1️⃣0️⃣
.... *ABDALLAH.* Cikin tsananin mamaki yake kallon address ɗin gurin da zata gabatar da taron nata, tabbas unguwar sune, sannan kuma ƙofar gidan maƙofcinsa, kenann hakan nanufin yau zatayi rawa da waƙa a ƙofar gidan sa!. Afili kuma ya ce "Jiya taje bikin abokina har ta samu damar cin mutuncina, shine yanzu ma take son ta ƙara samun damar yi a karo na biyu ko!. Kallon sunan sabuwar ƙasidar da tace zata sake a gurin taron yayi, afili ya karanta sunann waƙar. *BUƊAƊƊIYAR WASIƘA.* Take ya saki dariya sannan ya kashe wayar yana mai aiyana cewa kodai shi takeson tama martani.
*MARYAM.* Wani ihuu tayi haɗi da kwashewa da dariya irin dariyar da kana gani kasan ta muguntace. Da gudu tazo gurin Mommy sannan ta ce "Mommy albishirin ki? Tayi tambayar cikin dariya. Mommy ta ce "Lafiyar ki kuwa? Kinzo sai dariya kikeyi kamar wacce ta zauce?. Tsabar dariya Maryam ta kasa magana sai kawai ta miƙawa mommy wayar tana cewa... "Mommy karanta kiga Ikon Allah.
Bayan Mommy ta gama karantawa ne ta ce "Na gani za'a ayi walima ne a unguwar su yayanki kuma shine abun dariya? Maryam ta ce "To ai Zainab Ambato ce zata gabatar da waƙoƙin ta a gurin, kuma kalli wannan sabuwar waƙar kigani, itamafa agurin zatayi, kuma Allah daga jin sunann waƙar zatayi sweet. Tafaɗa haɗi da cewa ai kuwa baza'a barni a bayaba, dama bamu taɓa haɗuwa da itaba saide daga nesa, yau kan har ƙawance zamu ƙulla. Cikin mamaki Mommy ta ce "Amma ai yayanki ya hanaki shiga lamarinta ko? To saboda haka ban yarda kije ba. Maryam ta ce "Mammy kirabu dashi ni nasan komai, shimafa Allah yana son ƙasidun yarinyar kawai dai..."kafin ta ƙarasa Mommy ta kai mata duka tana cewa ai zai nado mara kunya kawai. Ita kuwa Maryam cikin dariya ta je domin shiryawa.
*ZAINAB. POV*
Kallon taron al'ummar dake gurin takeyi wanda kusan rabunsu basu taɓa ganinn taba. Cikin farin ciki da ƙwanar mosoyan nata take takowa izuwa gurin da a ka ware domin ta. Gurine wanda a ka masa ado da hotunan Shehu Ibrahim inyasa da dai sauran shehunan su, kowa burinsa ya gaisa da ita, yayinda matakan tsaronta da mai gidan da ya gaiyatona ya haɗasu da ita domin bata kariya, sai tare mutane sukeyi. Ita kuwa Zainab faɗuwar gaban da takeji tin a gida sai ƙaruwa yakeyi.
A haka ta ƙaraso gurin sanan ta samu guri ta zauna tana sakin murmushi, halifan ta guda biyu mace da namiji, sune suka zauna a kusa da ita, can zuwa wani lokaci kuma ta tashi ta shiga bin layin duk wani malami dake kurin saida ta gaida shi. Saida malamai suka buɗe taro da addu'a kafin aka fara wa'azi a kan aure. Saida malamai biyu suka yi kafin a ka bata. Manyan malam gurin sai binta sukeyi da ido, daga mai aiyana cewa yau zai gabatar da kansa sai mai cewa yayiwa yaran kamu, sai masu jin cewar wannan ai irin tasu ce.
Cikin muryarta mai tsaki wajan yabon Annabi Muhammad S a w. Ta fara da addu'a sannan ta shiga gaida manyan malamai da dai sauransu. Nan fa aka saki kiɗa tafara yin wata ƙasida mai taken.... *INDAI KAASONI BANI DA FAR GABA, ANNABI NA BIKA BAN BI WANIN KABA* Nann fa al'ummar gurin suka ɗauka harda malamen dake gurin.
*ABDALLAH* kuwa yana cikin gidansa, yana jin duk abundake faruwa, damuwarsa ta saki wannan waƙar domin da ita zai yi amfani wajen kamata da hujja. Har cikin kunnuwansa muryar ta ke shiga wanda ya nutsu yana jin abun da take cewa a cikin waƙar. Saida tayi waƙoƙi guda uku, izuwa lokacin kowa nason jin wannan sabuwar waƙar, ai kuwa take aka kunnata. Kasancewar babu wanda yasan ƙasidar sai gurin yayi tsit ana sauraron ta.
*A.J. SARAH.*
Kallon mamaki sarah kebin A.J dashi ganin irin abubuwan da yake sawa a kawo kan teburin su, bata tashi ruɗewaba saida taga wasu daga cikin abokansa yaran masu kuɗi sunzo sun zauna a teburin, kuma suma yace su karɓi duk abun da sukeso. Nan fa sarah ta shiga zare ido, domin kuwa tasan abubuwan da a ka kashe sun fi ƙarfin kuɗin ta. Bayan an gama abun da za'a yi ne, kowa ya kama budurwar da yazo da ita suka fara aikata abunda ke kaisu gurin. Hannusa ta kama ta miƙar dashi sannan ta jawoshi izuwa gurinda ake rawa. kallon ta yakeyi ganin yanda take shafa shi ta ko ta ina, nann shima ya fara mayar mata da mar tani. Tin suna shan bakin juna har A.J ya jawota gefe, suka faɗa kan ɗaya daga cikin do kwayan gujerun gurin. Cikin fitar tunanisa ya fara kai hannusa izuwa ƙirjinta, wanda hakan ya bata damar ƙara tura masa ƙirjin nata, bata an karaba taji hannuwansa a fatar ƙirjinta, ya zame rigar maman ta ya sa hannunsa. Tin da AJ yake a duniya bai taɓa shiga irin wannan yanayin ba, haka ya dinga jinsa kamar ba a wannan duniyar yakeba.
Sun kai minti ashirin a haka suna shafar juna yana taɓa ko ina a jikinta kafin ya fara ƙoƙarin zame mata riga, bata hanashi ba har saida ya rabata da rigarta, sannan ya shiga ƙoƙarin cire ɗan gajeran wandon da tasa, yana ƙoƙarin hakane, yaji alamar tana cire masa wando, saida ta cire belt ɗin ta fara jan wandon sai kawai taji ya riƙe wandon sa. Lokaci ɗaya ya miƙe yana kiran sunan Allah, kallon gefe da gefen sa yayi yaga kowa harkar gaban sa yakeyi babuma wanda yasan sunayi, ya mayar da Kallon sa izuwa gurin ta, yaga ƙirjinta duk a waje, da sauri ya jawo rikarta yana kare mata jiki shima ya ɗaure wandonsa, ya ce "Tashi kisa kayanki, yayi maganar ne yana juya mata baya. Cikin kasala da mutuwar ji ta miƙe tsaye tana jin baƙon yanayi na sake shigarta, har ta gama bata ko iya magaba. Saida yaji shiru sanan ya juyo, aikuwa ya ganta tsaye tana kallon bayansa, idonta yayi jaa. Ya ce "Mu tafi? Haka ta ɗau jakarta, suka nufi gurin biyan kuɗi. Cikin mamaki taji ance ai abokansa sun biya dukka. Haka suka fito babu mai magana acikin su sai tinanin abun da ya faru sukeyi.
A.J ya ce "Sarah kiyi haguri bansan mai ya kaini harna aikata haka a garekiba, ba halina bane, kuma addinmu ma bai halarta haka ba, kuma ina so na sanar miki da wani ab..."Bai ƙarasa ba ta ce "Karɓa wannan kuɗine nazo dasune domin wannan abun amma basuyi amfani a nann ba, kuma idan na je dasu gida za'a iya kamani, saboda haka kawai ka karɓa kayi amfani da su. Kallan kuɗaɗen yayi yana aiyana cewar ai yanzu yafi ƙarfin su.
A.J yayi dariya sannan ya kalleta cikin ido ya ce "SARAH yanzu kece kike buƙatar wannan kuɗin baniba, sannan inason na sanar miki cewa gobe zanyi tafiya zuwa Maiduguri, zanyi wata ɗaya, kuma i'naso ki bani acont number ɗinki, idan na tafi zan sake layi ba lallai mu yi wayaba har mu dawo.
Cikin Muryar ta da tun tuni take rawa ta ce "Me zakajeyi? Idan kuɗine ai nace zan dinga kawo maka, Please karka tafi ka barni, bazan iya jurewa ba...tana kaiwa aya kuka ya kufce mata, tana jin kamar ta rungumeshi ko zataji sanyi. Ya ce "Sarah ki daina kuka ba zama zanyiba zan dawo, Please kije gida kar Daddy ya gane baki dawoba. Haka yayi Sa'a ta tafi amma ta ce ba gida zatajeba gidan su Usha zata kwana, hakanne yasa ya rakata har ƙofar gidan sannan ya ciro kuɗi masu yawa ya ƙara mata, ya ce ta ɓoye har yadawo.
Ita dai zara sai kallon sa takeyi tana tinanin kode yayi kuɗine!, sannan tana jin cewar kamar in ya tafi bazata sake ganin saba. Haka ya juya yabar gurin yana mai jin tausayin ta domin kuwa yasan sun rabu kenan har a bada. Haka itama ta shiga gida cikin rashin kwarin gwiwa. Yana shiga ɗakinsa ya fito ya shiga bayan gidansu ( toilet) wanda ke tsakar gida, yana wanka yana aiyana cewa yanzufa daga yau na daina wanka a irin wannan bayan gidan, wanda kana wanka ƙasa na hawa ƙafafunka. Har ya gama ya fito yana aiyana abubuwa da yawa. Saida yazo saitin ɗakin Nana zai huce yaji kamar ana magana, hakanne yasa ya dawo da baya ya kara kunnansa, tabbas magana akeyi amma baya jin me a ke cewa, amma idan anzu gurin yin dariya dariyar tana fitowa.
Saida yayi kamar ya shiga ɗakin amma ya fasa yana mai tinanin kodai kallo takeyi, haka dai ya bari a kan da safe zai tambayeta. Yana shiga ɗakinsa yaga abincin sa, ya buɗe yaga namane sai dankali ɗan kaɗan naman kazar ya fishi yawa, sai kawai ya ɗau cinyar kaza ɗaya yasa a baki yana taunawa yana kallon lokacin da bakinsa dana Sarah ke haɗuwa, tashi yayi ya fita ya ɗaura a laula ya gabatar da magariba da isha.
Nana kuwa Salis ya samu nasarar shawo kanta, yayinda suna gama waya zata goge number sa, idan ya kira kuma saita ga ba kowa take ɗagawa, kokuma suyi wayar dare, tabbas ta yarda da shi har zuciyarta,. Yau kwana biyu kenann amma taɗan saki jiki dashi ganin da gaske sonta yakeyi.
*WASHE GARI. HAJIYA BABBA POV*
Tin misalin ƙarfe 8 na safe ta gama shirya komai da za'a buƙata na ɗaurin aure, tin daga kan waliyan ango da kuma waliyanta, gamida gaiyatar mutanan da basu santaba.
Ta gama tanadar komai, yayinda ita yayanta wanda suke uba ɗaya shene wanda zai jagoranci auran, shi kuma AJ wasu iyayen bogi aka samo. Misalin ƙarfe goma na safe Hajiya Babba ta kira yaranta Laɗifa da Salis. Kallonsu tayi sannan ta ce "Kamar yanda na sanar daku cewa yau zamuje Abuja domin tabbatar da in gancin ma'ai katan da a ka ɗauka a kamfanin ku, da banyi niyar zuwaba amma na samu kira yanzu wai dole sai naje. Saboda haka zan tafi, amma yau zan dawo. Cikin sauri laɗifa ta ce "Haba Mommy yanzu kece zakiyi tuƙi tin daga Benue har Abuja? Mommy ta ce "No tare zamu tafi da AJ.
Kafin Laɗifa tayi magana SALIS ya ce "Tom Mommy amma fa dan Allah karki kwana Please ku dawo da wuri. Laɗifa ta ce "Yanzu Mommy wannan yaron har ya iya tuƙin da zai jaki har Abuja? Gaskiya nidai ban yardaba. Hajiya ta ce "To kizo ki kaini? na ce kizo kikaini, tindade bakison ya kaini, waima dan Allah menene yaronnan ya mikine? Kafin Hajiya Babba ta rufe baki Laɗifa ta ce
"Zaginafa yayi yana matsayin ɗan aki amma kice wai me yamin. Salis ya ce "Hajiya dan Allah ki rabu da ita, idan kin shirya kawai muje mu rakaki mota.
Hajiya Babba ta ce "Nagode Salis Allah ya maka albarka, bari yaron ya ƙaraso domin shima yanzu tafiyar ta sameshi. Salis ya ce "Kekuma bari kiji na faɗa miki, dama kinsan tin jiya ina tunanin zancen da kikamin ko? To ki cire idonki a kan A.J idan ba haka ba Allah ranki zai ɓaci. Cikin mamaki da rashin kunya Laɗifa ta ce "Yanzu kaima yaya kana goyan bayan wannan yaron? Har kana cewa zaka ɓatamin rai, cikin kuka tayi sama ɗakinta tana cewa ita walhi saide duk abunda zasu mata suyi amma Walhi saita kori wannan yaron daga gidannan.
AJ kuwa tin safe Hajiya Babba ta kirashi a kan ya shirya domin goma da rabi zasu tafi, hakanne yasa tin safe ya shirya ƙaryar da zaiwa inah da Nana. Bayan sun gama karyawane shida Nana, ita kuwa Innah sai fama takeyi har lokacin. Ya kalli ƙanwar tasa sai ya kejin kamar idan ya tafi wani abu zai samesu. Cikin sanyin rai ya ce
"Nana?.
"Na'am ta amsa tana jin yanayin muryar da yayi mata maganar.
"Inah. Ya sake kiran sunan innah wacce ke tura naman kaza a baki.
Itama ta ɗago ta ce "Ya a kayi Abdul jabaru?
AJ ya ce "Innah zanyi tafiya yau, kuma zanyi kwana uku kafin na dawo shine nake tinanin idan na tafi kaman wani abu zai sameku?
Cikin sanyin murya innha ta ce "Ina zaka kuma me zakaje yi?
Cikin irin ƙaryar da ya shirya musu ya ce "Inna ai dama nace miki na samu aiki, to ogan gurin aikin namune ya zaɓomu mu biyar akan zamuje wani aiki. Kuma Innah muna dawowa shikenan mun zama manya a gurin aikin. Inah ta ce "To Abdul jabaru wannan wani irin aikine haka? AJ ya ce "Innaaaaah!! Haba mana irin wannan tambaya kamar yar jarida, kinsan dai bana sata bana shaye-shaye bana... "Kafin ya ƙara sa ta ce "Naji, ba sai ka ƙarasa ba, ta ci gaba da cewa... kai yanzu badama na maka faɗa sai kamin wannan zance? To sai mutum yana yin sata da shaye-shaye zai jefa kansa a damuwa? To Walhi Abdul jabaru na gaji da irin wannan ɓoye-ɓoyen da kakemin, yanzu komai fa a gidan nann yazama na masu kuɗi, hatta ruwan da
muke sha, kuma nace wacce sana'a kakeyi kace kai baka sata baka shaye-shaye kuma..."Kai inann haba dan Allah!, ni har kin fara sakamin ciwon kai, yanzu gashi har nafara makara, nidai kimin addu'a kawai inah ta. Ya faɗa yana kamo mata hannu alamar wasa.
Ita dai innah haka ta bishi da ido har ya tashi zai fita, ita dai jikinta na bata kamar AJ na ɓoye musu wani abune, saida ta ga zai fita kafin ta iya buɗe baki ta ce "Allah ya dawo da ku lfy. "Amin my amarya ko kefa. AJ ya faɗa domin ganinn ya kawar mata da kokwanton da ke ranta. Aikuwa tayi murmushi tana cewa, kaide Abdul jabaru halinka sai kai, sai kuma wannan mara kunyar ƙanwar taka mai kama da ifiritai. Nana tayi dariya ta ce "Ooo innah, yanzu ni mai kuma namiki da kike haɗani da jin sin aljannu? AJ ya ce "Nana tashi muje ki karɓo muku saƙo. Haka suka fito yayinda innah ke faman surutu ita kaɗai.
P .O .S .Sukaje shida Nana ya ciri kuɗi dubu hamsin (50,00) Kafin ya ce mata "Wannan kuɗin bance ki nunawa innah ba, ki barsu a gurinki, duk abunda kuke da buƙata kawai ki siya. Nana ta ce "Wai yaya zaka daɗene haka? Kuma waye ya baka wannan kuɗin? Ni dai gaskiya nimafa kafara bani tsoro kamar inna!? AJ ya ce "Bana son dogon surutu, kede kiyi abun da nace miki. Haka ta ƙarɓa ta tafi, yayinda takeda tarin tambaya da zata masa idan ya dawo, sannan itama jikinta na bata cewar idan ya tafi bazai dawoba. Koda tazo gida haka ta ɓoye kuɗin batare da innah ta ganiba.
A.J kuwa yana shiga gidan, Hajiya Babba da Salis suna fitowa daga cikin palorn gidan. Cikin fara'a Salis ya ce "Babban yaya har ka iso kenann?
A.J ya ce "babban yaya kuma!? Salis ya waske da cewa ka iya mota kuwa? "Cikin wannan surutun nasa ya ce "To ai ni saide mota ta iyani, nida nayi aikin gidan biredi, kuma