Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   10 / 37

27K to 30K   out of 109.2K words

zaka biya. Kekuma tinda shi wanda kike kaiwa kuɗin musulmi ne, kuma shege to miliyon uku zai biya harda dubu ɗari biyar, idan ba hakaba wallhi saide karya dawo Benue.

Haka Mommy ta goyi bayan sa, domin kuwa Momy ta tsani musulmai fiyeda Daddy. Haka kuwa a kayi, Samuel da Sarah a ka turasu a wani ɗakin da babu komai a ciki saide hasken gulob guda ɗaya. Kuma ɗakin haɗe yake da toilet.

Ɓangaren su Nana da Innah kuwa tunda a ka turasu sell babu ko mutum ɗaya da yazu domin dubasu, harzuwa wannan lokacin Innah batayi maganaba sai hawaye dake bin fuskarta. Tun safe har qarfe biyar na yamma babu abunda a ka kawo musu da niyar suci. Nana kuwa tin tana kuka harta fara tunanin dalilin me a ka kawosu. Ta kalli Inna ta ce "Innah Kodai yaya yana sata ne? Batayi tunanin Innah zata bata amsa ba ganin tin ɗazu tana mata maga bata um bata um-um.

Sai a lokacin inna tayi magana cikin muryar tsufa da kuma yunwa da damuwa haɗida fargaba ta ce "Nana babu shakka Abdul jabaru sata yiyi, domin kuwa in ba sataba baza'a mana irin wannan cin mutuncin ba! Tana faɗa hawaye na wanke mata fuska, Nana ta ce "A'a Innah Walhi yaya baya sata saide ko shari a ka masa.

Cikin kuka Innah ta ce "Nana a'i'na ya samu kuɗin da yake mana komai? A ina ya samu kuɗaɗen da ya siya mana wayoyi? Shin ya taɓa faɗa miki cewar ga irin san'ar da yakeyi? Wani lokaci ma nama kawai zai ce muci, muba ƴaƴan kowaba. Idan na tambaye kekan ki kinji abunda yake cemin...

Ni bana sata. Bana bin mata bana shaye-shaye bana komai!! !!!!!!!!! Ina ta ƙarasa tana cewa haka yake cemin, ashe kuɗi yake sata shine yanzu ya tafi ya barmu da masifar!!! Ta share hawaye ta ce "Tabbas yasan da haka shine yasa ya gudu ya barmu!!!

Nana tayi shiru tana tunani. Can ta ce "Tabbas Innah yaya yana ɓoye mana wani abun, ranar da zai tafi ya bani kuɗi, wato jiya, masu yawa na tambayeshi yace min wai ƙara tambayarsa.

"Inna ta ce "Yanzu da zaitafima munce ina zaije, yamana ƙaryar banza, gashi tunda ya tafi bai kiramuba, shikuma idan an kira bata shigaaaaa. Inna ta ƙara fashewa da wani kuka mai ƙarfi wanda yasa ɗaya daga cikin ƴan sandan daka musu wata tsawa wacce tunda suka shigo yake zaginsu da aibatasu wai suna mata amma suna sata, kasan cewar shima ba musilmi bane. Haka yake musu tin ɗazu. Shiru sukayi suna haɗewa a guri ɗaya domin har sun fara tsoran sa....📝




?
*PAGE1️⃣4️⃣*

......Police ɗin ya kallesu cikin ƙas-ƙanci da cin mutuncin ya ce "Idan baku rufe mana baki a'nan ba sai na gyara muku zama yanzunnan, kodan kunci sa'a tunda kukazo babu wanda ya taɓaku shine har kuke samun damar cika mana kunne da surutu, to karna ƙara jin tarinku agurin nann idan ba hakaba kuma...babu ruwana da ku matane cin ubanku zanyi tunda ai ku ɓarayine. Cikin tsananin tsoronsa Innah da Nana suka ƙuntse kukansu suna takurewa a guri ɗaya. Haka Innah da Nana suka wayi gari a cikin seel ɗinnan babu ci babu sha, sannan babu wanda ya zo garesu. Misalin ƙarfe 8 nasafene Nana ta ce da Innah "Innah yunwa nakeji bazan iya ba a kwai kuɗi a gida da yaya ya bani zanje na ɗauko sai mu dinga siyan abinci.

Innah ta ce "Nana addu'a kawai zamuyi in ba hakaba bamuda kowa in ba Allah ba, sannan kike maganar zuwa ɗauko kuɗi yaushe yayan naki ya baki kuɗin? "Ranar da zai tafine kuma sunada yawa, zasu ishemu harda Berlin kanmu, bari na ƙwada zuwa ko Allah zaisa ya barni. Innah ta ce "Nana daga yau har zuwa lokacin da zan mutu a cikin wannan gurin to wallhi bazan ƙara taɓa komai na Abdul jabaru ba, indai shine zai fitar dani, kokuma kuɗin satar da ya saba samowa to na ƙwammace mutuwa a haka, saboda haka nidai babu ruwana da komai da ya shafi Abdul jabaru, tunda har zai iya jawo masifa ya gudu ya barmu, to haƙura! na haƙura!!! Inna ta ƙara maganar ƙirjinta na mata wani irin zafi, ga hawaye da ya wanke mata idanu.

Nana ta ce "Haba Innah dan Allah karkici haka, shima yanzu ai bakisan halin da yake ciiiba dan Innah ki yarda da yaya bazaiyi abunda kike tunaniba, Please ina ki yafe masa dan Allah!? Itama ta fashe da kuka tana faɗawa jikin Innah wacce kana ganita kasan bata cikin haiyacinta. Inna ta kasa magana sai kuka takeyi tana shafa gadon bayan Nana. Nana ta ce "Innah yunwa wallhi ina jin yunwa zan mutu! rabona da abinci tun jiyafa! Please ki yarda naje na ɗauko kuɗin dan Allah Innah ta? Tafaɗa tana ɗagowa daga cinyar Innah tana riƙe ciki.

Domin itama yunwar takeji kamar ta yi ihuu amma haka ta danne ta ce "Nana idan har zasu barki kije to kije ki samowa kanki amma nidai ƙwara na mutu yau ɗinnan, tashi kije Allah yasa ya saurareki. Nana ta ce "Amin. Bakin sell ɗin tazo tana kallon ƴansanda da suke kaiwa da kawowa a gurin, shikuma mai jiran nasu yana tsaye da wani alamar dai wata maganar sukeyi. Sai ta rasa me zatace masa domin ya sauraretNa, ai kuwa ta tuna ba Hausa ya keji ba, domin tunda sukazo bataji yayi Hausa ba.

Ta tsaya a bakin gurin ta ce "Am am am yalla'bai". Bai jiba. Sai ta ɗaga muryar ta ce "Oga. Nan ma baijiba alamar dai zancen nasu ya ɗauki hankalin sa. Sai ta sake cewa "Ogaaaa! Da ƙarfi wanda yasa dukkanin yan sanda seda kowa ya juyo yana kallon ta.

*LAƊIFA. SALIS. POV*

Haba Umar meyasa baka sanar dashi ba? Cewar laɗifa tana waya da Umar tana sanar masa da cewar ta kira number Samuel amma ba'a ɗagawa, shikuma yana sanar mata da cewar ai Samuel baya ɗaga baƙuwar number. Yanzu ina zamu haɗu domin zuwa gidan nasu?, cewar Laɗifa? Umar ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "Bazai yiwu muje gidansu yanzuba amma dai ki tsaya zan kirashi zuwa gobe domin ina tunanin bai dawo bane?

Cikin muryar da kana ji kasan tayi zurfi cikin soyayya ta ce "No Umar please yanzu nakeso muje, wallhi ina son ganin sa, idan ban ganshiba a kwai matsala? Umar ya ce "Ok tom kisameni a unguwar mu sai mu tafi yanzu. Ai kuwa cikin sauri ta ce "Tom jost minti goma.

Haka da yamma Salis ya koma gidan su Nana ko an sakesu amma yaga har yanzu basu dawoba. Nan fa hankalin sa ya tashi domin zuwa yanzu yasan babu lafiya sosai. Haka ya zauna a gurin har zuwa wani lokaci kafin ya bar gurin cikin rashin kwarin gwiwa. Washe gari ma da safe ya kira number Nana amma no amsar, haka ya koma gidan ya sake ganinn sa a rufe kamar yanda ya rufe jiya, domin farkon zuwansa a buɗe ya samu ƙofar Shine ya rufe.

Yana tunanin kamar ya shiga gidan amma ya tsoro, yana cikin hakane wani tsohon abokin AJ yazo hucewa, wanda ganin Aj yana abota da yaran masu kuɗine sukuma yana ja baya dasu yasa suka rabu da yaron, amma har zuwa wannan lokacin suna gaisawa da yaron mai suna kamal.

Zaune suke a cikin motar Laɗifa Umar ya sanar mata halin gidan su Samuel a kan iyayensa basa son musilmai, ko shima da suke abota iyayansa sunyi dashi amma yaƙi, kuma har yanzu idan abban su ya gammu tare saiya kusa karyashi, nima idan nasake ya kani ubana zaici, kuma babban soja ne. Laɗifa ta sauke a jiyar zuciya sannan ta ce wannan duk mai sauƙine, indai zan samu ganin sa. Umar ya ce "nima bansan meyasa baya ɗaga min wayaba (Umar baisan an kama Sameul ba)

SALIS ya ce "Salamu alaikum? Kamal ya amsa da "w slm.

"Dan Allah ko kasan ina a ka kai masu wannan gidan?

Kamal ya ce "Walhi nima tin lokacin da abun ya faru bansan ina a ka kaisuba, na je duk police station ɗin dake kusa damu amma shiru shine na haƙura.

"Yauwa ko ka san wani soja ne a kace yazo ya tafi dasu? Ko kasan gidan sa?

"Kamal da yasan komai tsakanin A.J da Sarah tin ba yanzuba. Ya ce "No ban san gidan sa.

"Salis ya ce " Ok yanzu amma ai kasan yaron gidannan ko?

"Eh nasan shi abokina ne sosai.

"Ok tom zaka biyoni zuwa gida ka rakani mu shiga cikin gari neman inda a ka kaisu?

Kamal ya ce "Ok ba damuwa. Domin kuwa yaga alamar Salis ɗin ba wanda zai tsaya yiwa musu bane, gakuma yaga kamar a rikice ya ke.

Bayan sun je gida ya ɗauki motarsa ne suna cikin tafiya yaji wayarsa na ƙara, yana dubawa yaga Hajiya Babba. Bai ɗagaba saida ya samu gefen titi ya tsaya kafin ya fito da wayar. Saiga wani kiran ai kuwa yana ɗagawa ya ce "Please Hajiya ina A.J? Abun da yaji Hajiya Babba na cewane yasa ya tsaya da maganar tasa yana mai sauraron ta har tagama. Ya buɗe baki zaiyi magana ta ce "Ku kula da kanku bazan daɗeba ka kula da laɗifa. Kutttttt yaji ta kashe wayar.

Dafe kansa yayi yana jin wani ɗacin abunda yake faruwa daga jiya zuwa yau. Yaso ya sanar wa da Hajiya Babba cewar ya samu wacce ya keso, amma yanzu gashi babu Nana itama Hajiya Babba tana zancen sai tayi sati ɗaya ko fiye da haka. Salis bai kawo komai tsakanin Hajiya da AJ ba kawai suka cigaba da tafiyarsu shida kamal. Saida sukayi yawo sosai kafin a hanyar dawowarsa suka ga wani police station kamar dai ba'a aiki a cikin sa. Kamar bazasu shiga amma kamal ya ce "Su shiga su tambaya ko Allah zaisa a dace.

Suka shiga ciki suna raba idanu. Wani ɗan sanda suka gani shi kaɗan a bakin mushigar gurin, ya tambaye su wa suke nema? Kamal ya masa bayanin abunda ya kawosu, ai kuwa ya ce "ba nann a ka kawosuba. Salis zaiyi magana police ɗin ya haɗe girar sama da ta ƙasa, ya ce ba nan bane. Ganin kamar dai suna ciki sai Salis yasa hannu a aljihun sa ya ciro kuɗi masu yawa ya kama hannun plec ɗin ya saka masa. Ai kuwa ya washe baki yana sanar musu da cewar suna ciki.

*GIDAN SOJA*. *POV*

Kaman yanda Daddy ya ce sau ɗaya zai dinga basu abinci haka a kayi, tin jiya har yanzu sau ɗaya ya basu abinci, amma kowa nasa. Sannan bai baiwa Sameul wayarsaba sai yau, ita kuwa dama Sarah ya ce bazai bataba. Washe gari Daddy yasa a ka buɗesu ya shiga ya baiwa Sameul wayarsa yana ƙara faɗa masa cewar kar kuɗinsa ya huce kwana shida. Yana kallon Sarah jikinta duk yayi sanyi ga har yanzu kuka takeyi amma ya kawar da kansa ya bar ɗakin sanan yasa a ka rufesu. Ai kuwa Daddy na fita Sarah tayi wajan Samuel tana cewa "Please Samuel call A.J for me please?

Samuel kuwa ko kallonta baiyiba yasa buɗe wayarsa yana kallon tarin miss call da aka masa, domin kuwa Daddy bai kashe wayar ba. Number Umar ya fara kira, ai kuwa kira ɗaya Umar ya ɗaga haɗi da cewa "Haba Samuel ina ka shigane muna ta kuranka amma no amsar?

Samuel ya ce "No yanzu babu lokaci, nann ya kwashe komai ya faɗawa Umar. ai kuwa Umar ya zaro ido yana cewa "harda Sarah? Sameul ya ce "Please yanzu meye abun yi? Umar ya ce "gaskiya kuɗin da yawa, amma ina wannan yarinyarr da kace zaka sameta? Samuel ya ce "Ka haɗu da itane?

Umar ya ce "ai jiya tare da ita muke nemanka. Nann Umar ya kwashe komai ya sanar masa.

Take Samuel ya saki wani ajiyar zuciya ya ce "Good! Aikinka na kyu, yanzu ka kira ta ka sanar mata da komai sai kawai tazo ta fitar dani?

Umar ya ce "kai haba da huri haka? Ai sai kasa ta renaka, bari kawai nasan me zan ce mata, zatazo ta fito da kai.

Haka sukayi sallama yayinda Umar ya ƙara mamakin daddyn su Samuel gaskiya baida kirki, ƴaƴan samafa kenan bare ƴaƴan wasu, kai gaskiya zuciyar kafirima batayiba. Haka dai ya cigaba da tsorata da lamarin mutumin, sannan yana tausayawa Sarah Sosai. Sarah ta ce dan Allah ya kira mata A.J? Cikin tausayin ta da ya faraji tin jiya ya kalleta ya ce "Please Sarah waye Aj?

Sarah ta ce "His my boyfriend.

"Like Haw?

Sarah ta kwashe komai tsakanin ta da AJ ta sanarwa yayan nata sannan ta ɗora da cewa...i love him so much, please Dan Allah kiramin shi. Haka ya bata wayar tasaka numbar AJ ta Kira, amma bata shiga haka ta dinga kira amma babu alamar zata shiga. Samuel ya ce "Haba Sarah wai wai!! Meyasa zaki yarda dashi? Yanzu haka kuɗi yayi ya gudu ya barki. Yanzu ga halin da kike ciki....✍️



I'
*PAGE1️⃣5️⃣*

......Kinsan ba'a yarda da musilmannan domin basu da kirki burinsu kawai su cuci mutum su gudu su barshi saboda haka nifa dama bana yarda dasu, ko Umar da kike ganinmu tare nasan irin zaman da nakeyi dashi, amma ke kin ɗauki yarda kin baiwa wanda baya ƙaunar ADDINIMU, nasan shi baya sonki kawai yayi amfani da kene ya biyawa kansa buƙata ya ware. Kuka Sarah takeyi tana tunanin maganar da A.J ya mata ranar da zasu rabu! Cikin zuciyarta ta ce "kenan da gaske A.J ya tafi bazai dawo ba!? Wani irin kuka ta sake tana mai jin ƙaunar AJ ɗin na ƙara mata yawo a duk sass-sassan jikinta...

Tabbas ta yarda da AJ kuma tasan zai dawo gareta, domin tasan yana sonta. Sai kuma ta tsya cak tana tunanin tunda suke tare ya taɓa cewa yana sonta kuwa!? Bama wannan ba, shin mema yace min ranar da na bashi kuɗinnan!?

"Kiriƙe wannan kuɗin domin yanzu kece kike buƙatar su, sannan ki bani acont number ɗinki zan turomiki wasu. Tabbas haka yace mata. Kenan da gaske yayi kuɗi ya gudu!? Gashi ya bar gidan iyayensa! To dama haka halin musilmai yake! Haka sukeyi!. Sai kawai ta fashe da kuka wanda yasa Samuel kamota yana rarrashin ta. Sannan ya ce "Yanzu a ina zaki samu miliyon biyu? Sarah ta ce "idont no. Kafin Samuel yayi magana wayarsa ta fara ƙara hakanne yasa ya ɗaga yana kwantar da Sarah a kan cinyarsa yana cewa Hello.

*HAJIYA BABBA. A.J*

Hannu takai tana son buɗe masa idon nasa wanda ganin ta tsirara ne yasa shi rufe idon, ganin yaƙi buɗe idonne yasa ta ɗauki shi cak tamkar wani ƙaramin yaro ta kaishi kan gadon tana kwantar dashi. Ai kuwa da sauri ya jawo bargo yana rufe tin daga kansa har ƙafafun sa. Hajayi tayi dari sanan ta ce "Angona lokacin sallah fa yayi ka tashi idan munyi sallah sai mu koma barcin.

Yana jinta amma yayi shiru yana jin cewar wannan matar ta gama dashi har a bada. Wankan tsarki tayi sannan ta ɗauro a laula kafin ta fito ta saka kaya sai murmushi takeyi, tana tunanin sauran mazajan da ta aura. Mijinta na farko. Ko sati basuyiba ya saketa domin kuwa har kuka saida yayi dukda lokacin tana ƙarama, idan ya fara kwanciyar aure da ita baya ko a'wa ɗaya zai gaji yayinda ita kuma a wannan lokacin batama san me a kayiba, hakanne yasa a ka raba auran.

Sai tayi dariya tana tuno mijinta na biyu. A daran farko. Bayan sun gama duk wasu sharuɗa da ADDININMU ya tanada ga duk wasu sabbin aure. Ya ɗauko kaza yana zumuɗi, haka ya dinga bata harsaida tagoshi kafin shima ta bashi. Ganin ita ɗin bazawara ce yasa bai tsaya yin wata-wata ba domin shima bazawarine, yana ganin ai sun san komai.

Haka cikin nuna zaƙuwarsa ya fara sarrafata. Ai kuwa itama Madam wacce dama takawo iya wuya, sai kawai ta fara mayar masa da martani. Bai kawo komaiba domin kuwa yasan ai dama ita bazawara ce. Haka dai ango ya shiga duniyar ma aurata yana ta aiki. Saideme? Aifa ango yaga duk abunda yakeyi baijin ihunta ko wani a lama da zainuna tana gamsuwa. Sai ya ƙara dagewa! Amma fa duk ɗaya. Saida ya gaji sosai amma yaga idon Madam Carr a kansa a lamar kafara ne kodai kana shirine? Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana. Ogafa ya fara raba ido yana mai haɗiyar wani yawu muƙut.

Haka Hajiya Babba ta jashi kan gadon ta cigaba. Nann fa ya fara kokuwar ƙawtar kansa amma ya kasa, ga kuma ya gama jigata domin kuwa babu wani ƙarfi a jikin sa. Itafa Hajiya tin tana jin yana magiya har yasaki baki yana ihuuu!. "Dan Allah kiyi haƙuri walhi zan mutu na gaji kibarni haka. A ta ƙaice dai, bawan Allah bai farfaɗo ba saida gari yawaye sosai sannan ya buɗe ido ya ganshi a gadon a sibiti. Aikuwa ba wata-wata ya saketa yace ba zai iyaba. Haka Hajiya Babba ta dawo gida ta cigaba da zaman zawarci har na shekara ɗaya da watanni kafin wani yazo.

Saida biki ya rage sati ya ce yafasa, alamudai yaji labarinta, haka wani baƙo wanda ba ɗan garin nasuba shima saida abu ya kusa aka zugashi shima yace ya fasa. Ai kuwa bata rufe wannan shekararba Allah ya kawo mata uban ƴaƴan ta. Dariya tayi bayan ta dawo daga tunanin, ta tuno da mijin ta mai iyawa da ita, bawai dan tana gamsuwa ba, a'a dandai yafi sauran. kafin ta tada sallah.

AJ kuwa yanajin ta har ta fara sallah yayi sauri ya shiga toilet, domin kuwa duk hankalin sa na kanta, yana kallo tanata murmushi. Yana shiga ya tsaya yana Kallon jikinsa daga sama har ƙasa kafin ya ce "Na shiga uku ni AJ!! Ina kuma sankuɗina ya kaini! dama haka a keji idan anyi aure? To meyasa wasu mazan suke cewa daɗi a keji!? Nidai wallhi matarnan kasheni tasoyi, idan ya tuno irin wahalar da yasha, domin kuwa abarsa har wani zafi take masa, tin tana iya tsayawa har ta lanƙwashe. Ya ce "kai wallhi bazan iya da wannan abunba, ni wallhi sai najima na tsani aure indai haka a keji mutum ya kusa mutuwa, amma fa da farko yaji daɗi. Take ya tuno da ranar da sukaje clup

10 / 37