Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   26 / 37

75K to 78K   out of 109.2K words

tare. Ita dai a zahirin gaskiya tana sonsa shi kuma a da yana sha'awar ta ne kawai, yanzu kuwa sai yaji duk babu koɗaya kodan ita ɗin jininsace. Hakanne yasa a zaman da sukayi bai wani sake da itaba sai Usha ne ma yake ɗan janta da hira, shi kuwa gaba ɗaya hankalinsa yana ga surarr jikin Hadiza. Sarah da laɗifa a ɗaki ɗaya suka kwana hakanne ya ba Laɗifa damar gano komai dake tsakanin ta da AJ domin kuwa ta bigi cikinta. A wannan lokacin Laɗifa ta sake yarda da cewar AJ kawai yana bin ƴaƴan masu kuɗine ya na manne musu kuma daga yau idan ta ƙara ganinsa a gidansu walhi sai ta wulaƙan tashi.

Washe gari bayan sun gama breakfast wanda Hajiya Babba ta kasa cin komai kasan cewar ta tashi da ciwon kai, ga kuma abincin da bata son ganinsa kamar zatayi a'mmai. Bayan sun gama ne Hajiya Babba ta kalli Salis ta ce "Zaka rakani gidan su AJ domin zan kai masa gudun mawa kaga abun da ya sameshi shi bai kamata a barshi haka ba ko? Cikin sauri Salis ya ce "Ok Tom Hajiya amma Abba ya ce zan rakashi gidan abokinsa ki bari idan mun dawo sai na kaiki? Da sauri Sarah ta ce "Na san gidan zan rakata? "Muhammad ya ce "Hajiya bazaki bari ki sake hutawa ba? Ko dai zamu koma asbiti ne? Naga yanayin jikin naki ,ko a kira Dr yazo? Ta ce "No karka damu yanzu zan dawo kuma ba wani ciwo da nakeji. Hajiya Babba da ta ke jin cewar bazata iya cikekken minty biyar batare da sun haɗu da AJ ba ta yi saurin ce wa da Sarha "To ba damuwa idan har zaki gane gidan ai sai mu tafi. Laɗifa kuwa da take takaicin wannan abun ganin Sarah tayi hakane domin taga AJ, shi kuma Salis yayi hakane domar har ya dawo ya je yaga wannan shegiyar ƙanwar AJ ɗin da ya ce yana so. Ai kuwa a zuciyarta ta ce "Yau dai zan sai naga wannan yarinyar kuma naga shi AJ ɗin a ina ya ke, daga nann kuma na ci masa mutunci.

Da sauri ta ce "Hajiya nama zan rakaku? Hajiya Babba da bata son a sirinta ya tonu ta ce "No Auta ki zauna a gida yanzu zan dawo? Laɗifa ta ce "Haba mana zan iya takawa fa ƙafar bata ciwo yanzu na warke fa? Muhammad ya ce "A'a auta keda Samuel ku zauna a gida har mu dawo domin kuna buƙatar hutu, ga Anty Titi tana tare da ku kinji? Jin haka yasa ta ce "To amma ku dawo da wuri Pls?. Salis da Muhammad da Umar da Usman suka tafi gurin abokin Muhammad wanda shiɗin malamine domin nemo hukuncin auransa da matarsa shin auran yana nann ne tinda bata ƙara wani auran ba, ko dai sai an gyara auran duba da an daɗe ba'a tare. Bai sanar dasu abunda zaijeyi ba shi kaɗai ya barwa kansa hakan.

Hajiya Babba da Sarha ne a bakin gidan su AJ da safe. Hajiya ta ce da Sarah "Shiga ki ce ana sallama da AJ? Sarah ta kalleta ta ce "Ok i'm Coming. Ƙarasawa gurin mai shayin unguwar ta yi ta ce da yaron da yazo siyan shayi yazo ta aike shi. Gaba ɗaya ƴan gurin suka zuba mata ido domin kuwa turanci tayi. Yaron da bai san me take cewa ba ya ce "Mai shayi ana maka magana wai zata siya shayi? "Gaba ɗaya suka kwashe da dariya mai shayi ya ce "Hajiya na nawa kikeso? Sara ta ƙara Mai-maita abun da ta ce sai akayi sa'a wani ya gano abunda ta ke nufi shikuma ya sanarwa da yaron. Ai kuwa take yaron ya tafi kiran AJ ɗin. Suna tafiya kuwa sabuwar hira ta ɓarke a kan taiburin mai shayi. Wasu na yaba irin kyun da yarinyar ke dashi, wasu kuma suna zaginta saboda arniya ce, wasu kuma na gulmar me tazo yi gidan su AJ domin dai basu ganeta ba, kuma basu manta irin tashin hankalin da ya samu gidan su AJ ɗinba a kan idonsu.

Tasaye suke a jikin motar su, Hajiya Babba na jin kamar ta shiga gidan tsabar ruɗewa.

Sanye da jallabiya fara ya fito ƙafarsa ko ta ƙalmi babu, yana fitowa ya ci garo da Sarah domin itace ta farko jikin gidan nasu, sai kuma ya ga Hajiya Babba. Da mamaki yake kallonsu, sai kuma ya kawar da mamakin nasa domin kuwa yasan dama doke ta nemeshi . Lokaci ɗaya ya kafe Sarah da ido wacce itama shi take kallo idonta har ya fara cikowa da hawaye. A hankali ya ƙaraso kusa da ita wanda yayi dai-dai da ƙamshin tirarensa na fashion ya shiga ƙofofin hancinsu dukkansu. Take Sarah ta lumshe ido, ita kuwa Hajiya Babba tsabar damuwar da take cikima sai taji bata son wannan ƙamshin turaran nasa, take tashin zuciya ya fara zuwar mata. Kallon juna sukayi ita da shi sannan ya ce "Kinsan Sarha ne? Yayi tambayar ne cikin mamaki? Domin shi dai bai san asalin komai ba.

Ta ce "Eh amma ba wannane ya kawoni ba, ta faɗa tana mai jin a'mai na ƙoƙarin zuwar mata? Ya ce "Eh dama nima ina son muhaɗu domin kuwa a kwai ma tsala? Kallon Sarah Hajiya Babba tayi sai AJ ya mata a lama da bata jin Hausa. Hajiya ta buɗe baki ta ce.....📝




[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*



*S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

_*Bansan da wani irin alƙalami zan rubuto muku ɗinbun godiya da irin addu'o'in ku a gareniba, tabbas LITTAFIN ADDININMU yana samun yabo sosai a gareku makaranta ina godiya sosai da sosai.*_


_*PAGE3️⃣6️⃣*_
..........Ta ce "Bana son wannan ƙamshin tiraran naka pls kaje kacire wannan rigar kazo muyi magana? AJ ya kalli jikinsa sannan ya kalli Hajiya Babba sannan ya dawo da kallonsa izuwa ga Sarah wacce tunda ya fito ta kafeshi da ido ko rin tsawa batayi. Juyawa yayi ya koma cikin gida ya cire rigar ya sako wata jallafiyar sannan ya fito. Yana fitowa bai ce musu komaiba ya ƙarasa jikin motar ya na cigaba da kallon Sarah. "Ta ce ina wayarka? Kuma me ya kaika gidan Comanda Daniyel? Hajiya Babba ta watso masa wannan tambar. Acikin jimilla ɗaya ya bata amsar tambayoyinta. "Babu ruwanki wannan bai damekiba faɗi abunda ya kawoki? Shima ya bata amsa cikin tsananin jin haushin halin da ta jefashi. Da mamaki Hajiya Babba ta kalleshi sai kuma ta kawar da kai gefe tana danasin abunda ta aikata, yanzu wannan ɗan yaron shine har na yarda ya sanni a matsayin ma ce! Inalillahi wa inna i'laihim raji'un! Ta furta a zuciyarta kafin ta koma serus ta ce....

"Kaman yanda mukayi wannan auran ba tare da kowa ya sani ba to haka nakeson yanzu-yanzu ka sakeni na baka kuɗinka kuma karka sake ne ma na, sanan duk wata alaqar da ke tsakanin ka da Salis itama inaso ta yanke daga yanzu, zan baka kyutar gida kubar wannan unguwar domin bana son wani abu ya ƙara shiga tsakanina da kai har a bada. Da ɗan mamaki AJ ya ce "Ai dama a cikin sharuɗanmu harda gida a ciki saboda haka ba kyuta zaki baniba hakƙinane, sannan kuma nima nafi son hakan, amma kinsan fa a tsarin Addinin Muslunci dole sai an ɗaura muku wani auran kafin zamanku ya halarta keda shi mijin naki, kenan ya zakiyi? Hajiya Babba da gaba ɗaya kanta ya ɗau zafi, ga kuma taga kamar yanason yin amfani da wannan damar ya raina mata hankaline ta ce "Wannan ba damuwar ka ba ce, kaidai ba damuwar ka kuɗi ba? AJ ya ware hannu haɗi da karkatar da wiya alamar yes. Ta ce "Ok yanzu nawa ne sauran kuɗin naja? Ya ce "Gidaa nafi buƙata a yanzu, sannan kuma kuɗi inaso ki bani miliyon hamsim idan kinga zaki iya ? Ya faɗa yana haɗe fuska kamar yanda tayi.

Cikin tsawa ta ce "Kai ɗan matsiyata walhi kai baka isa ka iya tonamin asiriba kayi kaɗan, kaiɗin banza miliyon goma zan baka ai bamu gama cika watannin da muka yankeba, saboda haka idan kaga dama ka amsa idan bakaga danaba ka barshi aurene dai ya ƙare tunda mijina ya dawo? Hajiya Babba ta ƙarasa maganar tana buɗe gaban motarta ta ciro wayarta ta ce "Bani account numbar ka yanzu na tura maka, suma ta kardar gidan nazo dasu, inaso daga nan ƙarna sake jin labarinka. Cikin jin jewar shawar da zuciyarsa ta bashi tayi ya ce "Idan har kina son saki daga gareni kuma nayi nisa dake har abada to inada sharaɗi? "Sharaɗinkan na banza, walhi yaro sai ka sakeni kuma yanzu idan ba hakaba walhu sai kayi da kasanin sanin Aisha Salisu.

AJ ya ce "To shikenan tinda kince haka, zaku iya barin ƙofar gidannan yanzu kafin na tara muku jama'a kuma ki sani auranmu zai baiyana ga duniya, kuma zaki bar gidanki kidawo gidana ki tare, badai sai na sakeki za'ayi auran ba to muzuba mugani? Yana faɗa ya juya zai shiga gida. Ai da sauri Hajiya Babba ta kamo hannunsa ta yi ƙasa da murya cikin sanyin rai ta ce "AJ karkamin haka ka tuna cewar aurannan fa dama munyishi a cikin kuskurene kaga rabuwar shine mafi dacewa, kokai bazakaso ace kaine mijin uwar abokinkaba, kaga Salis bazaiji daɗiba pls kayi haƙuri kafaɗi sharuɗan naka? Hajiya Babba ta ƙarasa maganar da muryar roƙo kamar zatayi kuka. AJ yayi shiru yana tunano irin dukiyar da ta mallaka, sannan yana tunano irin wahalar da yasha kuma duk itace, sannan ya tunano su Innah yanajin cewar wahalarsu ta ƙare a rayuwa, ya tuno lokacin da take bashi umarni kuma tace a cikin sharuɗan auransune. Afili ya kalli gurin da Sarah ta ke yaga har yanzu su take kallon ko magana batayi, take yaji gabansa ya faɗi ganin irin kallon da take masa, lokaci ɗaya yaji wani tausayinta sai kawai ya lumshe ido yana son sanin alaqar Hajiya Babba da ita ɗin. Ya ce "Sharuɗa na guda ukune? Idan kin yarda yanzu zan rubuta miku saki na baki idan kema kin bani nawa? Hajiya Babba ta haɗiyi wani yawu muƙut ta ce "Ina jinka?

*SALIS POV*

Gaba ɗaya hankalinsa kacoƙan ya tattara izuwaga Nana ya na son yaje yaga a wani hali suke, shin bayan da suka fito daga gidan ƴan sanda ina sukaje? Anya kuwa lfy? Gashi numbar ta ta daina aiki. Har sukaje gidan abokin Daddy suka dawo bai daina tunaninta ba. Afili ya ce "Yanzu lokaci yayi da Hajiya zata san da magar aurane tunda Daddy ya dawo, kokuma na fara sanar da Daddy. Haka dai ya keta saƙe-saƙensa shi ɗaya, ya bari a kan zaije gurinta da yamma.

Ɓangaren su Muhammad da Umar da Usman kuwa, izuwa yanzu sunce sumafa sun matsu da son zuwa gida suga iyayensu, domin kuwa dukkansu babu mai aure. Hakan yasa Muhamd ya yanke cewar suyi haƙuri zuwa gobe sai su tafi. Sunyi yawo sosai a cikin gari, duk gurin da Muhamd yaje indai ansanshi sai kowa yayi mamaki. Lokacin da sukaje gurin abokin nasa kuwa yana ganinsu ya fara Ambato sunayen Allah cikin tsoro. Sai da yaji yayi maga kafin ya nutsu.

Bayan yaji duk abunda ya faru ne ya shiga mamakin rashin imanin Daniyel, a ce ka ɗaure mutum kusan shekaru har ashin(20) saboda kawai ya koma addinin Allah. To walhi sai anyi masa hukumci ai samun matsayi ba hauka bane. Malam fa ya shiga surfa faɗa yanajin abunda a kaiwa abokin nasa babu daɗi, domin kuwa ko bayan abotar dake tsakanin su ai shiɗin musulmine, musulmi kuma ɗan uwan musulmine. Da ƙyar dai Muhammed ya taushi Malam har yayi shiru, sannan ya ce "Ni Walhi na yafe masa duniya da lahira, in de domin abunda yaminne za'a masa hukumcin to walhi na yafe. Cikin mamaki Malam ke jijjiga kai ya ce "Eh laillai kam kaci sunanka Muhammad domin kuwa wannan shine irin halin mai sunanna, kuma haka yayi mana nuni da muyi, rama kairi d
ga wanda ya aikata maka shirri yin hakan imanine, haƙiƙa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama zaiyi alfarahi da kai, kuma wannan halin naka shine ya kamata adinga yin koyi dashi. Malam ya ci gaba da cewa ..."A kwai wani maƙofci da Manzon Allah ya taɓayi wanda ba musulmibane baya ƙaunar mudulmnci da kuma musulman gabaki ɗaya, tsabar ƙiyayarsa da manzan Allah, kullum idan yayi shara a gidansa sai ya tattara ya watso gidan Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, shi kuma idan ya watso sai ya kwashe. Sai Manzon Allah yaga kwana biyu wannan kafirin bai watso masa sharaba sai ya tambaya ko lafiya kuwa kwana biyu baya jin ɗuriyar maƙofcin nasa? Sai a ka shida masa cewar ai bashi a ke binsa kuma bai biyaba shine a ka kamashi a ka kulle. Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama sarkin tausayi Sarkin adalci ya bada wannan kuɗin masu yawa a kaje a ka fito da wannan mutumin. Bayan ya fito ya tambaya cewar waye ya fito da shi?

Sai a ka ce masa Muhammad Rasulullah. Sai ya ce "Shiɗin ne ya bada kuɗin da a ka fito da Ni? A ka tabbatar masa da haka. Ai kuwa take kafirin ya miƙa wiya ya musulunta. Take su Muhammad da Umar da Usman da Salis suka ce Allahu Akbar! Malam ya ci gaba da cewa "Haƙiƙa Muhammad kaiɗin masoyin manzan Allah kuma da yardar Allah bazaka taɓa wulaƙanta ba, daga kai har zuri'arka.

Nan dai malam ya masa bayani game da matarsa cewar idan har tayi wani auran to zata zaɓane ko shi ko waccen mijin nata, idan kuma batayi wani auran ba to auransu yananan kawai dai zasu cigaba da zamantakewar su a matsayin ma'aurata ne. Muhammad yayi godiya sosai sannan ya tambayeshi labarin malamin su wato shek Kabir kabuga. Malam ya sanar masa da cewar yana nan lafiya, kwanan ma zai aurar da yaransa mata guda biyu. Muhammad ya ce "Ikon Allah malam har zai aurarr da yara. Sun daɗe a gurinsa ya ƙara jaddadamusu cewar suma su Umar da Usman so je gida domin a sanar cewar sunraye.

Bayan sun dawo gidane Salis ya shiga wannan tunanin nasa. Ya na cikin haka Muhammad ya shigo ɗakin nasa ya na cewa yazo suje su siyo kayan siyayyar da su Umar ɗin zasu tafi dashi. Tashi tayi suka tafi duk su huɗun. Samuel da Laɗifa da Usha kuwa hira suka sha sosai daga nan Usha ya bar gidan itama Titi ta shiga cikin tadomin ɗora musu abinci. Samuel ya taso daga kujerar da yake yazo kusa da ita ya ce "Laɗifa wannan shine gidan Uncle Solomon? Ta ce "Sunansa Muhammad from today or call him Daddy? Samuel ya ce "Ok Daddy. Laɗifa ta ƙara matsowa kusa dashi sosai ta ce "Yes gidanmune munada irinsu sama da goma a cikin garinnan sannan kuma munada camfanunuwa guda takwas biyu a nan biyu a Abuja uku a kano sai ɗaya a Lagos, amma na Abuja da Lagos sune manya-manyan. Samuel yayi shiru yana tunani sai ya ce "Waye ya baki kuɗin da kika kai gidanmu ranar?

Ta ce "Nawane ai inadasu a account ɗina? Ya ce "Waye yake baki? Ta ce "My Momy And my brother. Bai san lokacin da ya ce "I love U so mouc my lovelly Sister. Itama ta ce "Me too my brother. Sai kawai yaji shikenn kaya ya tsinke a gindin kaba. Ya riƙe hannunta yana kallon ƙwayar idonta, yana son yayi amfani da wannan damar ya karya mata tata zuciyar, ai kuwa ya samu nasara domin kuwa take tayi ƙasa da kanta tana mai jin wani yanayi. Ya ce "Ar you serus You love me? Ta yi ƙasa da kai tana jin faɗuwar gabanta na ƙaruwa. Bata an karaba taji ya ɗago kanta ya saka bakinsa a cikin bata. Ido ta zaro tana kallon idonsa da yayi jaa. Da kyar da ƙwace bakinta ta na ce wa "Pls Samuel babu kyu a Addinimu karka sake?

Ya ce "Sorry tsabar son da nake miki ne yasa amma kiyi haƙuri bazan ƙaraba. Haka dai ya dinga mata zantukan soyayya wanda yasa Kaɗifa jinta a duniyar sama, har ta saki jiki dashi sosai. Soyayyar gur-gwaye kenann.

*AJ POV*

AJ ya ce "Idan kin yarda zaki bani miliyon hamsim da gida haɗida takardun gidan, kuma karki bani wanda yake kusa da ku, in da sosamunema ba'a cikin garinnan ba. Idan kinyi haka sai kuma... ki samu wani daga cikin yaran aikin ki yazo gidanmu a matsayin shine ogana, ya sanarwa da Innah ta cewar shine ya bani wannan gidan, sai ya bani takardun gidan a gaban ta, a haɗo da mota sabuwa, idan har kin yarda to yanzu zan rubuta miki saki ko nawa kikeso daga kan ɗari har zuwa ɗaya. Hajiya Babba ta ce "Matsiyaci kaine talaka wanda baisan mutunciba kuma in sha Allah sai ka wulaƙanta. AJ ya ce "Walhi kika sake yin magana to sai dai milion sittin? Cikin jin tsanarsa ta ce "Idan uwarka da ubanka sun isa sai suzo su kwatar maka, wawa ɗan talakawa dama Laɗifa tana cemin kaiɗin ba ɗan arziƙi bane amma naƙi yarda kuma zakagani. Ya ce "To farashi ya ƙaru sai kin bada sittin Walhi! Hajiya dai baki bai mutuba tana jin duk itace ta jawa kanta.lokacin da zatayi aure yaranta sun hanata taƙi hanuwa, ta ɗauki Wannan tsinanan yaron aiki Laɗifa ta hanata amma taƙi.

Ta ke ta turawa AJ miliyan hamsin ɗinsa, shi kuma ya ce "Walhi bazaiyi sakiba har sai ta ƙara wannan goman. Haka dai tana zaginsa har ta tura masa. kasan cewar bashida waya yanzune yasa baya ganin message sai har ta nuna masa daga wayarta, ai kuwa saida yaga tabbacin shigarsu sannan ya ce "Ki turo Salis gobe da motar tawa sai ya karɓa miki sakin?ya faɗa yana ɓiye dariyarsa.

"Hajiya Babba tana jin kamar ta zabga masa mari ta ce "Na faɗa maka babu kai babu yarana walhi idan

26 / 37