Addininmu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Love

Chapter   5 / 37

12K to 15K   out of 109.2K words

ganinn irin shigar da tayine yabashi damar kafeta da ido, yana jin sonta har zuciyarsa. Bai ankaraba yaji tana cewa "Yaya ɗin AJ bayanann kunyi saɓani yanzu ya fita, amma in yadawo zance masa wannan da yazo jiya yazo neman sa. Tana kaiwa nann ta juya zata koma ciki.

Cikin sauri salis ya ce "Ji'mana, bagurin sa nazoba gurin ki nazo. Ta ɓangare ɗaya kuma yana tinanin meyasa bata riƙe sunann saba. Cikin mamaki Nana ta nuna kanta da cewa ni?.

Duk da uban fankoki da asi da suke aiki a palorn hakan bai hana AJ jiƙewa da zufaba. Cikin rikicewar ya ce "Hajiya aure fa kikace? Kuma dani!?... gaskiya bazan iya ba, yazanyi da salis wanda agirme. Ya girmeni kuma abokina wanda yake temakamin a komai, amma na auri uwarsa!!? Ina Hajiya dan Allah kibar wannan zancen Please. Ya ƙarasa yana kallon jakar kuɗin da yasan in har ya mallakesu to tabbas shida talauci har abada.

Salis ya ce "Yes gurinki nazo. Nana ta juya tana neman wacce salis ɗin ke magana da ita, domin kuwa tanada tabbacin bada ita yakeba, domin kuwa babu haɗin kwanda da gula. Kayanda kejin sama tasan ba na ƙananan yara bane, bare motar da yake jingine a jikin ta. Cikin mamaki ganinn yanda take ta dube-dube ne salis ya ce "Keɗayace a gurinan, kuma dake nake...kamata yayi a ce kiyi maraba da zuwana domin da alkairi nazo....📝



_
*PAGE* 👉7️⃣

............... Kallon jakar kuɗin yakeyi yana aiyana abun da zai faru in ya mallake su. Cikin ransa yace "Anya kuwa in nabar wannan garaɓasar ban cutuba!?. Zuwa wani lokaci ya ɗago ya kalli Hajiya Babba sannan ya ce "Yanzu dan Allah hajiya meyasa kikeso ki aureni?. Hajiya Babba tayi dariya sannan ta ce "Banice zan aurekaba kaine zaka aureni...Kuma ba wai in ka aureni shikenan bazaka sakeyin wani auran bane, a'a zaka auri wacce kakeso, amma kafin nan zan baka labarin abin da yasa zanyi aure.

Cikin gamsuwa da abunda ya ce Nana ta ce "Ok tom barka da zuwa. Salis ya gyara tsayuwar sa sannamallak "Barkade...da fatan dai ba dole namikiba? Nana ta ce "kusan dai hakan...yanzu dai kafaɗi abunda ya kawoka tunda kace gurina kazo, kafin innah ta fito nemana?. Cikin dariya Salis ya ce "Afito nemanki fa kikace kamar wata ƙaramar yarinya?.

"Eh dama ai ƙaramar yarinyar ce baka gani bane?. "Dan Allah karki ƙara kiran kanki da ƙaramar yarinya, kallekifa kin isa aure amma kice wai yarin ya ceke?. "Cikin jin kunya Nana ta rufe fuskarta haɗi da cewa... Please dan Allah zan tafi gida.? Salis yace "Muga wayar ki?. Ya mata wannan tambayar ne ganin wayar a hannuta. Ita kuwa Nana tinda a ka bata wannan wayar haryanzu bata barta ta hutaba.

Hajiya Babba ta ce "Nakasance tin ina yarinya Allah ya ɗoramin wani irin ciwo, wanda tin kafin na kai mizanin aure a kamin. Na kasance daga cikin mata harijai wato masu mutuƙar sha'awa. Hakanne yasa iyayena sukayi saurin aurarr dani, aurena uku (3) zan faɗa maka abun da yake rabani da mazajena. Har Allah yayi na auri mahaifin su Laɗifa, shima ɗin dan Allah yayishi jarimin gaske ne, shiyasa zamanmu yakai har lokacin da Allah ya amshi abinda.

Lokaci ɗaya AJ ya zaro ido waje jin abunda Hajiya ke faɗi. Ya ce "Hajiya menene harija? Hajiya tayi murmushi tana jin wani matsananci sha'awar yaron na ƙara taso mata a duk lokacin da yayi magana.

Zaro ido waje Nana tayi ta ce "Mezakayi da wayana? Salis ya ce "kinga rufe bakin kar..."ai kafin ya ƙarasa ta rufe fuskarta tsabar kunya. Haka ta ciro wayar ta bashi, domin kuwa babu fuskar masa musu, domin kuwa ya mata kwarjini sosai. Bayan ta bashi sannan ta zuba masa ido domin ganin mai zaiyi da ita. Hoton ta da AJ ne a gaban wayar. ganinn yanda sukayi kyau ne yasa ya ce "Kunyi kyau sosai kamar ba keba ya ci gaba da cewa "Badan AJ ya girmekiba da sai ace ko ɗin ƴan biyu ne. Dariya tayi tana jin daɗin yanda ya yabesu.

Number sa ya saka mata sannan ya ƙwada kira ko tanada kuɗi, aikuwa sai gashi ta shiga, yayi seveng number sa da (my sweetheart) sannan ya nuna mata. Haɗi da cewa wannan number nane zamu dinga gaisawa.

Hajiya Babba ta ce "Karka damu duk zan sanar dakai. Taci gaba da bashi labari. Yanzu haka shekarar Alhaji huɗu da rasuwa, kuma tun baya ya rasu yarana suka hanani yin wani auran, kuma sunsan da cewar addinmu bai hanaba amma duk wanda yazo sai sun korheshi. Jiyama sun koriwani, shine yasa nayi amfani da kai domin cimma wani burina, inaso ka yarda babu abun da zai faru, domin kuwa ADDINIMU bai haramta ba.

Zamuyi aure na shekara ɗaya, Sannan zan baka miliyoyin hamsin da gida harda mota... sannan babu abun da zai shiga tsakanina da kai har muyi wannan shekara ɗaya ɗin, abin da nakeso shine Karka sanarwa da kowa, harda kakarku domin kuwa nasamo labarin ka gaba ɗaya, iyayenku sun rasu, daga kai sai ƙanwarka sai kakarku, to banaso susan da labarin, da so samunema wata ƙasar samu tafi mufara yin wats ɗaya kafin mudawo, kokuma kawai zan cewa su Salis na ɗaukeka a matsayin yaron gidana, zaka dinga zuwar min aike da cefane. Kaga kassmu damar shiga ɗakina duk lokacin da na kiraka koda kuwa kana inane?.

Nana bata tsaya karanta abun da yayi seveng number ba, domin ita duk a tinanin ta kawai yasa number ne bai ajiye taba. Hakan ne yasa ta karɓa tana cewa "Tom zan shiga gida? "To sai kinga kirana. Batace komaiba ta shige gida, shikuma ya tsaya yana Kallon ta har ta shiga gidan. Sannan shima yayi murmushi ya huce gida. Yana hanya yana tinanin hirarr da sukayi.

A.J. Ya ce "Shekara ɗaya kawai? Hajiya ta bashi amsa da cewa "Eh shekara ɗaya. Amma bazan baka kuɗin gaba ɗaya ba, zan baka miliyoyin biyu yanzu, bayan shekara ɗaya kuma zan baka sauran, amma gidan da nace shima zan baka, motarma saboda gudun tambaya da zan baka, amma yanzu itama motar sai bayan aure.

"Waiyoooo daɗin kasheni AJ ya furta a zuciyarsa sannan ya ce "Hajiya na yarda, amma ki bani miliyoyin biyun yanzu, sai kuma ki kaini gurin gidan nawa. Hajiya ta ce "wannan duk mai sauƙi ne, amma ai ban gama kafa maka sauran sharuɗan da suke cikin auran ba?. AJ ya ce "i'najinki.

Hajiya ta fara bayani kamar haka...."In na fara karkace komai sai na kammala sai kayi tambayar ka? AJ ya ce "Kede Hajiya muje bayani.

"Duk lokacin da na nemeka to ko a i'na kake ko me kakeyi zaka bari kazo?. Sannan wasu lokutan a gidana zaka kwana kuma a ɗakina, zan sanarwa da mai gadi cewar in kazo yabuɗe maka koda cikin dare ne. Ba kai ba kula wata macen ko wacece harsai auranmu ya ƙare. Karwani yasan wannan labarin koda kuwa Salis ne, ko abokanka, ko ƙanwarka, koma de waye. In kayarda gobe inada gurin da zamuje a ɗaura auran.

Abun da Hajiya Babba bata saniba shine...duk wannan bayanin da takeyi, shi AJ kuɗin kawai yake hange, amma abu ɗaya ya tsaya masa a'rai, wato kwana a gidanta. Tayaya!? AJ ya tambaya? Hajiya ta ce "Karka damu duk wannan mai sauƙine, nidai karka bari Salis da laɗifa suji wannan zancen? AJ yace "ya yarda. Nann take Hajiya ta ce "bani acont number ɗinka yanzu na tura maka?.

Nann take miliyoyin biyu suka shiga acont ɗin A.J. kallon message ɗin yakeyi, tamkar ya ƙwala ihu tsabar daɗi. Haka ya tashi ya fita, tsabar ruɗewama ya manta da maganar gidan. Hajiya Babba kuwa, duk abinda yaron keyi sake ɓurgeta yakeyi, badan tana tsoran saɓon Allah ba, kuma tin tana yarinya batayiba, da babu abun da zaisa bata zuba masa magani a ruwa don tayi amfani da yaron ba. Tabbas tana buƙatar na miji kuma, yaranta sun hanata, akan ta je ta aikata haram ƙwara tayi haka, tinda ADDINIMU bai haramta ba. Tawani ɓangaren kuma tana ganinn tsan-tsar son kud'i da ƙuruciya da suke damun AJ.

A.J. Yana fita sukayi karo da Laɗifa zata shiga palorn. Shi AJ tsabar rikicewane yasa bai gantaba. Ita kuma laɗifa tsabar zuciyarta ce take suya tsabar halin da take ciki. Tabbas yau tayi gamo, tana tafiya tana tinanin abun da yafaru tsakanin ta da shi, wanda tanada tabbacin ba musulmi bane. sai kawai taji tayi karo da mutum.

Kallon-kallo sukewa juna, yayinda laɗifa kejin kamar ta zabga masa mari. Aikuwa cikin rashin iya magana da wanda suka girmeta ta ce "Wannan wani irin wawancine da dabbanci!!, kana tafiya baka kallon gabanka!?. Kafin ya bata amsa ta sake cewa...waima uban me ya kawoka gidannan da ranar Allah?( Kasancewar yanzu 12 miyu da mintin 4).( 12:0,4)) Kodan naji Hajiya Babba ta ce tana neman ɗan aiki ko? To Allah yasa dai aikin waje kasamu bana shiga cikin gidaba...dan Allah kalleka har wani tsami kakeyi waikai a hakan saurayi, yanzu haka wannan kayan sunkai kwana uku a jikin ka, koma sunfi haka...bari dai naje naji wani aiki Hajiya tabaka, wallahi badan Salis ba wallhi baka kai ka shigo gidannan ba, nonsense.

Abin da Laɗifa bata saniba shine A.J yafita baki, sannan a yanzu yana ganinn dai-dai yake da shugaban ƙasa ma ba itaba, saboda miliyoyin biyun da suke tare dashi, saboda haka ya barta ta gama maganar ta sannan yaga zata tafi ya ce "Yaro man kaza...kalleni da kyu nafi ƙarfin kimin wulaƙanci, domin nibadake zanyi saidai nayi da wanda yafiki, saboda haka kisan da wanda zaki dinga magana, AJ nake bana ɗaukar nonsense. Take ya juya yabar gurin yana jin kansa a sama, domin kuwa yanzu jinsa yake yana dai-dai da uban kowa harda uwar kowa a duniyar nann dan yanada miliyoyin hamsin, yanzu kuma ga biyu a hannusa, afili ya ce "kai wallahi sabuwar waya ma alherice, daga siyan waya yau har tafara ganinn irin wannan message na kuɗi haka, kai Allah ya sakawa Sarah da albarka, dole yau na ɗauketa muje clop domin itama aci wannan banzan da ita. Haka ya tafi gida cikin farin cikin da yafi na jiya.

Ita kuwa Laɗifa tsayawa tayi tana Kallon ikon Allah. Ɗan aikin gidan sune zai faɗa mata magana son ransa!! To wallhi an fasa ɗaukar sa aikin, nann take ta nufi cikin gida gurin Hajiya Babba.

*ABDULLAH* *POV*

Cikin ɓacin rai Mommy take masa magana. "Yanzu Abdalh kana cikin haiyacinka kuwa?! Yanzu da ka il'latata a wani gurifa!? Bakasan mace bace, macan ma budurwa wacce takai ta zama matar wani... ban sanka da irin wannan halin ba sabada haka karka fara, dukan mace!....hakan ya nuna cewar ko aure kayi haka zaka dinga ɗikar ƴar mutane ko?. Abdalh ya ce "Ayi haƙuri Mommy bazan sakeba, Amma fa Mommy rawafa na samu tanayi agidannan harda ƙawayen banza, sun kunna waƙa sai rawa sukeyi.

Cikin rashin kunya Maryam ta ce "Wallahi Mommy ba waƙa mukejiba, ƙasidar Zainab Ambato cefa, kuma yabon Annabi Muhammad s a w suke..."kafin ta ƙarasa Mommy ta bige mata baki, tana ƙarasa cewa Sallallahu alaihi Wasallama. Kafin ta ce "Yanzu Maryam ban hanaki ana magana kina saka bakiba?, to ai gaki gashi zan barku tinda kinga kema kinkai ko?. Ai kuwa dama Maryam abu kaɗan take nema ta ɓare baki. Nann take tafara ihu!! "Waiyo bakina waiyoooo bayana Mommy kin fama min ciwo, kuma kin fasa min baki, waiyoooo Allah Daddy. Haka Maryam ta dinga ihuu! Har su sadiya da Nusaiba harda Nura wanda shigowar kenann daga makaranta, suka zo gurin da gudu.

Cikin ɓacin rai ABDULLAH ya ce "Wallahi in baki rufe mana wannan ƙaton bakin nakiba zan fasa shi da gaske. Nann take tayi tsit sai jan numfashi takeyi kamar wata me shirin haɗiyar zuciya. Abdalh ya ce "Wallhi Mommy in har na sake ganinn ta tana jin waƙoƙin nann sai ta gane, In ba haka a ke mataba yarin yarnan wallhi saita gagari kowa a gidannan. Mommy ta ce "nima naga alama amma bana son duka, ka ja mata kunne dai. Sannan Mommy tamasa faɗa. Bayan ta kori su Maryam. Sannan ta masa nasiha a kan ya daina nuna ƙiyayyarsa ga mawaƙannan domin itama kakanta wanda ya haifi mamanta ɗan ɗariƙane. Amma Abdullah ya ce " Ai da ba haka ɗariƙar takeba yanzu sun ɗauki abun fiyeda yanda nada sukeyi, suna baiwa wani ɗan adam ɗin matsayin, wanda ni da ke da shi duk mutanene amma suna kaishi matsayin da Allah bai kaishiba, wasumafa har Allah suke kiran sa, in kamusu magana suce wai ƴan haƙiƙa, dan Allah mene haƙiƙa a ADDININMU?

Cikin sauri mommy ta ce "Abdalh kaji tsoran Allah yaushe ka taɓa jin sun kira wani da Allah? Shiya kullum nake maka faɗa akan ka dinga iya bakinkan a kan mutanann ka daina faɗar abun da kasan baka da tambas akai. Haka Mommy ta masa faɗa sosai, kafin Daddy yazo, ya masa maganar auran da ya ce masa, amma basu sanar dashi dukan da yama Maryam ba.

*A.J* Da sallama ya shiga gida, bayan ya biya ta bank ya ciro kuɗi. Geme take bugawa a wayarta hakanne yasa bataji sallamar saba. Hakanne yasa ya ƙarasa gurin ya kafce wayar daga hannuta haɗi da cewa "Sabon shiga ɓarawo da sallama...ba sabobba ɗan Fulani yayi a gogo. "Haba yaya gashi kasa ammin Game ovar. Nana ta faɗa cikin shaƙwaba, haɗi da turo baki.

AJ ya ce "yazu tun safe dana fita abun da kiketayi kenann ko?

Ai kuwa kamar yasani, domin kuwa tin kafin Salis yazu har yanzu ya tafi ta cigaba da game ɗin ta, babu yanda innah batayi da itaba akan tazo tayi aikin gida amma sai ta ce ina zuwa innah. Kafin tayi magana innah ta ce...

"Maraba da zuwa Abdul jabaru, tinda yanzu ta ganka ai tazo muyi aikin, yarinya tinda tayi waya kuma bata moruwa, ni kaga tawama tinda na ajiyeta bambi ta kantaba har yanzu.

AJ yace "Nana kafin na baki wannan wayar me nace miki? Nana tayi shiru. Ya ce "Bani wayar? Nana kuwa da yanzu-yanzu ta saba da wayar ta ce "yaya dan Allah kayi haƙuri wallhi na daina..."Tsawar da ya daka matane yasa ta kasa ƙarasawa sannan ta ciro wayar danufin miƙa masa.

Dai-dai wayar ta shiga rabin hannun sa, rabi kuma tana hannuta saiga kira ya shigo cikin wayar number an rubuta my sweetheart.....📝



_
*NASIHA*
_ka tarbiyyanci kanka da karatun alƙur'ani, sannan ka saka soyayyar Annabi S.A.W a zuciyarka, sannan ka saka soyayyar iyalan gidansa za ka rabautu duniya da lahira_.

*ADDININMU*
*PAGE* 👉8️⃣

............Kasan cewar lokacin misalin ƙarfe sha ɗaya zuwa sha biyune yasa A.J Baiga sunan mai kiran nataba, itama kanta cikin mamaki take kallon wayar domin kuwa har ta manta da cewar Salis ya saka mata numbar sa. A.J ya ce "Waye mai kiranki? Rikicewa tayi domin kuwa ta rasa mai zatace. "Badake nake mgn ba? Sai a lokacin ƙarya ta samu nasarar isowa bakin ta, ta ce "Ɗazu ne naje gidan su kaɗija na nuna mata wayana, shine tace nabata numbar na idan tasa kati zata kirani, to inaganin itace. Ta ƙarasa maganar kamar tayi kuka.

Kasan cewar A.J yasan halin Nana, kuma yasan bata kula kowa, sannan kuma yaga kwata-kwata ma yau wayar ta shiga hannun ta, sai kawai ya ce "Karna sake jin ance waya ta hanaki aiki, in ba hakaba Allah sai na ƙwace. Nana ta ce " I'm Sorry yaya bazan sakeba, sannan ta harari gurin da innah ke wanke shinkafa. Ai kuwa caraf suka haɗa ido. Inah ta ce "Eh ai da yake ni kika rena shi yasa, ga wanda ya miki faɗa amma ni kike harara, to wallhi ahir ɗin ki mara kunyar banza, ai Allah yasa Abdul jabarun baibar gidan ba.

A.J Kuwa yana shiga ɗakinsa ya fito da dubu hamsin (500) ɗin da ya ciro a bank, ya zuba musu ido yana aiyana cewa yanzufa yabar matsayin talaka ya zama ɗan ƙaramin mai kuɗi, wata zuciyar ta ce kai ai kafi ƙarfin ƙaramin mai kuɗi sai babba, take ya kwashi kuɗin ya watsa sama yana dariya, yana jin yanda kuɗaɗen ke sauƙa a kansa kamar ganye, sannan ya ciro sabuwar wayar da ta zama masa alkairi a cewar sa ya kira sarha.

*SARAH. SAMUEL* *POV*

Cikin ɓacin rai Samuel ya kalli abokinsa Umar cikin English ya ce "Umar ban taɓa jin kunya irin na jiyaba, saboda haka karka sake min haka. "Umar ya ce "Kai Allah nimafa naji kunya amma hakan shine mafita badan wannan yarinyar ba Allah sai munji kunyar da tafi wannan, amma fa yarinyar ta ɓurgeni. Yafaɗa yana kallon Samuel ɗin. Samuel ya ce "Yau zan biyata kuɗin da ta kashe mana, domin banason raini, kasan yaran hausann naku sun iya jisga mutum, yanzu a kan wannan abun da tamin saitayi tinanin ko muɗin matsiyata ne.

Umar ya ce "Yes nasan yarinyar batada kunya ga isa, kai itafa tsabar raininn hankalin ta, wallahi samari har tsoran zuwa gareta sukeyi. Samuel ya ce "Rely? Umar ya ce "Yes.

Samuel ya ce "Ai kuwa yau zan mayar mata da kuɗin ta, sannan sai na karya wannan record ɗin nata, ya ci gaba da cewa...kasan ni babu ruwana da yaran hausawa domin sam basu iya harkar wayewa ba, amma wannan karan sai na afkuwa wannan yarinyar, kuma sainayi nasara a kanta. Cikin mamaki Umar ya ce "Ban ganeba? Samuel ya ce "ina nufin zan huta da ita. Umar ya ce "Lallai kam bakan taba. Sameul ya ce "Ok nabaka kwana biyar sai ka ganta a gaban motana muna yawo cikin soyayya. Umar ya ce "kwana biyar dai? Samuel ya ce "Yes.

Haka suka rabu, yayin da Samuel ya shiga tnanin yanda zai sato kuɗi domin zuwa clop ɗin yau. Haka ya bari a kan cewar zai shiga ɗakin daddy tindade an'masa sharri, sannan ya rasa waye ya saci kuɗin wancan karan.

*SARAH* Kallon wani Afrikan Film ta keyi wanda ya ɗauke mata hankali har bata san shigowar Usha gidan nasuba. Zagayowa yayi ta bayan kujerarr da take kallon yayi,

5 / 37