tun kafin ya buɗe palon, ka na kallon sa kasan ya na cikin tashin hankali mara musaltuwa. Laɗifa da Samuel da Sarah da Muhammad su na zaune a palon suka ji wannan kiran na Salis. Ya na shigo wa palon ya ɗauketa da wa ni mari, kafin ta yi magana ya ƙara ma ta. Daddy Muhammad da Samuel su ka yi saurin ta shi su na kamo shi ganin ya na shirin ƙara ma ta wani marin. Cikin ihu da zafin rai ya ke magana "Mai ya kaiki gidan su AJ? Mai kika je kika ce ma sa a kaina? Wato saboda ke Allah ya yi mara kunya shine ki ke tunanin kowa ma haka ya ke? To Nana na keso kuma sai na aureta ko ki na so ko bakya so. Da ga cikin ɗaki Momy ta ji kamar a na faɗa-faɗa a cikin gidan, cikin rashin sanin abunyi ta miƙe ta na nufar palon domin jin muryar Salis.
"Kai Salis ba magana na ke maka ba? Jin Muryar mahaifin na sa cikin fushi ya sa ya tsaya da maganar ya na kallonsa dai-dai Momy Hajiya Babba ta ƙaraso gurin. Tsabar mamaki da rudanine ya ha na Laɗifa kuka, ta ri ƙe kuncinta sai bin Yayan na te da kallon mamaki ta ke yi. Wannan shine karo na farko da hannunsa ya taɓa ta da niyar duka, ku ma wai a kan AJ, sanan ita batama san akan mai ya ke bayani ba.
"Mai ya ha ɗa ku? Cewar Muhammad cikin ɓacin rai?
Salis ya ce "Daddy gidan su yarinyar da zan aura ta je ta yi halinta na rashin mutunci wanda ya sa Yayan yarinyar ya ce ba zasu ba ni ya rinyar ba.
Muhammad ya ce "Su ne su ka ce maka ita ce ta je gidan?
"Daddy ita kaɗai na sanarwa ina son yarinyar, sannan ko a lokacin da na sanar ma ta ba ta nuna min a'min cewar ta ba, sannan kuma yarinyar ba yar kowa ba ce , hakanne ma yasa ta je gidan ta ci mutuncin su domin kar su ba ni ita. Ya ƙara ya na jin wani ɗacin abun da AJ ya masa har cikin ransa, sannan ya na jin a kan Nana zai iya fafatawa da koma waye ba AJ ba.
Sai a lokacin Hajiya Babba ta gano kan maganar. Duk da ta na cikin damuwa amma kuma ba ta so ya ranta su ga no halin da ta ke ci ki, sai ta sunkuyar da kai ƙasa ganin irin kallon da Muhammad ke yi ma ta.
"Ƴar gidan wa ye? Kuma wa ni gida ne? Hajiya Babba ta tambaya cikin ɓoye ta ta damuwar, ta yi wannan tambayar ne domin sasanci amma batasan tambayar itace silar wargatsewar komai ba.
Nan ta ke Salis wanda dama ɗazu yazo gurinsu da niyar sanar musu da wacce ya keso, am'ma bai samu da ma ba, yanzu kuwa ya na jin da ma ta samu ya fara maga cikin da kiya da nuna cewar tabbas ya na son abunda ya ke faɗa ɗin.
"Ba ƴar gidan kowa ba ce, ƙanwar AJ ce Nana sunanta, kuma mun dai-dai ta da juna tun ba yanzu ba, ta na sona nima kuma ina sonta, amma yanzu na je gidan na su AJ da kansa ya ke korata da ga gidan su, Laɗifa mai kika ce masa a kai na? Salis ya ƙara sa idonsa na cikowa ya na nu na Laɗifa wacce har yanzu kallonsa ta ke yi. Ta na jin wa ni irin tsanar AJ a zuciyarta, ta na jin cewar wallhi da ga yau ba zai ƙara zuwa cikin gidannan ba, ku ma tinda dai ya sa Salis ya da ke ta, to walhi sai ta je har gidan ta ci masa mutunci.
Tunda Muryar Salis ta ambaci sunan AJ Hajiya Babba ta sanƙare a gurin, duk wasu gaɓobin jikinta suka tsaya chak, ta ma rasa wani irin tunani za ta yi, sai kallon Salis ta ke yi kamar yau ta fa ra ganinsa. Muhammad da har ya gano komai domin jin sunan AJ, kuma ganin yanda Hajiya ta yi suman zaune, ya kalli Hajiya Babba ya ce "To Alhamdu lillh! Muna godewa Allah da yasa abun ya zo ta ha ka, sannan dukkanku ina so ku ba ni aron hankulan ku domin ku fahim ce ni da kyu.
Ya fara da cewa "Da farko dai ba Laɗifa ce ta je gidan su AJ ta ci mu su zarafi ba. Hasalima shima AJ ɗin da ya ma ka haka ba'a son ransa ba ne duk borin kunya ne, sannan idan har bai maka haka ba to baisan da wa ni ido zai kalleka ba, kasan halin yaron da shegen son kuɗi. Hajiya Babba ta kurma wa ni uban ihuu ta na ce wa "Idan ka ƙaunaci mahsifan ka karka ce komai , ni na san yanda zan yi, Please And Please? Muhammad ya da ka mata tsawa ganin yanda ta ke abu kamar wa ta yarinya ya ce "Yau sai kowa yasan komai, wai i'na hankalin ki ya tafine? Kina abu kamar ba musulna ba, kamar baki yarda da ƙandara ba, ke bazaki godewa Allah ba ma da yasa kika bi hanya mai kyu?
Sarah da Samuel sai kallon ikon Allah su ke yi, ita kuwa Sarah sai ta hau mamaki jin saboda ha ka Hajiya ke kuka, ita duk a tunaninta a addininsu Hajiya Babba ɗin yin haka ba kuskure ba ne ganin kowa ya ƙi cewa komai, ashe dai babu wanda ya san da zan cen sai yanzu. Kasan cewar Muhammad ba kwarewa ya yi a Hausa ba, ya sa idan zaiyi magana sai ya haɗa da turanci. Suma kansu su Salis ɗin idan har za su yi magana da shi to sai su na haɗawa da turanci.
"Sakamakon kuskuren da kuka ai kata na hana mahaifiyar ku yin aure ya sa ita kuma ta ga bazata iya jurewa ba, kuma ta na tsoron faɗawa halaka, sai ta yi aure ba tare da kun sa ni ba, ba tare da ma kowa ya sa ni ba. Salis ya yi tsit, Laɗifa ta kalli Hajiya Babba wacce ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na karanto addu'o'in da ta samu ta wawaso. Wa ni irin abu Salis ya ji ya ratsa tsakiyar kansa, sai ya ɗaga kai ya kalli Hajiya Babba domin shi sam bai yarda ba, domin kuwa, yaushe har ta yi auran, bayan da ga shi har Laɗafi a cikin ƙasar nan sukayi karatu, kuma a cikin gidannan su ke ta re da ita, sannan a iya saninsu itama ba ta taɓa yin nisan da har zai kaita ga yin aure ba. Itama Laɗifa tunani ta ke yi kenan, yau she har suka taɓa yin nisa tsakanin su da ita da har za ta yi aure ba su sa ni ba am'ma ta kasa tunowa.
Cikin rashin yarda da komai ya sa Salis ce wa "To Hajiya saboda kinyi auranne ya sa kike kuka? Ya yi tambayar ne ba dan ya yarda da cewar ta yi aure ba, sai domin ya ji dalilin kukanta, domin kuwa ya na da tabbacin cewar ba auranne ya sa ta ke wanan kukan ba. Hajiya ta kasa magana sai ta sa ke fashe wa da wani kukan. Kana kallon Hajiya Babba sai ka tausaya mata, ganin yanda ta ke kuka kamar wacce ta aikata haramun, yawu da majina duk sun haɗe mata, idanuwanta sun ja zirr kamar mai ciwon ido, hakan yasan Salis yin wannan tambayar domin sanin dalilin hakan, shi kansa Muhammad sai yanzu ya ke ƙara tausayin matar tasa domin yasan duk gudun kunyar yaranta ta ke yi, domin kuwa tasan ba haramci ta ai kata ba amma kalli irin kukan da ta ke yi.
"Wanda ta aura ɗin ne bai kamata ba shine ya sa ta ke kuka? Cewar Muhammad cikin sanyin murya.
"Waye cewar Salis cikin sauri, domin zuwa yanzu gabansa ya tsananta faɗuwa. Hajiya Babba ko dai-dai lokacin numfashi ta ya yi ɗaukewar ƴan daƙiƙu kaɗan tsabar kunya da far gabar abun da zai faru. Ita kanta izuwa yanzu Laɗifa ta fara sakin kuka ganin irin kukan da mahaifiyarta ke yi. Sarah ma kukan ta ke yi cikin tausaya mu su. Shi dai Samuel baima fa himci komai ba, sai dai shima ya ji tausayin Hajiya.
"AJ abokinka kuma Yayan budurwarka wan da ka ce kaje gidansu yanzu ya koreka to shine wanda Hajiya Babba ta aura, kuma da yardar sa da yar darta harda rabon ci ki......📝
*Ikon Allah sai kallo! Wai ni Hajiya Babba ko dai ta manta da cewar Aure ta yi ba zina ba ne irin wannan kuka?*
*Comments ɗinku shine abun alfaharina*
*Ƴan fexxbookk ina ganin saƙonninku*
*S REZA ✍️*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*Duk abinda Allah ya tsara to tabbas ba makawa sai ya faru, fatammu a kullum shine Allah yasa mucika da imani, Allah yasa mu cika acikin addininmu wato addinin Musulunci addinin gaskiya. Amin²*
*PAGE4️⃣1️⃣*
......Shiru palon yayi tamkar babu ko wa a cikin sa, ko wa sai nazarin maganar yake yi, zuciyoyi na harbawa da sauri da sauri. Tabbas da gaske Daddy ne yake sanar da su cewar Hajiya tayi aure, auranma wai da AJ! Salis ya kasa magana sai kallon Hajiya Babba yake yi wacce ita kuma ta sun kuyar da kai ƙasa tana zubar da hawayen da na sani. Da ƙarfi Laɗifa ta ce "Wallahi ƙaryane babu wanda ya isa ya ce haka! AJ ɗin banza Wallahi na tsaneshi! Ƙarya yake yi dan uwar da ta haifi uwarsa, kuma yanzu zanje gidan na su yazo ya faɗa a gabana idan ya cika tsinane. Kana kallon yadda take yin maganar kasan ta fita a hayyacinta tsabar tashin hankali. Daddy ya ce "Sai dai idan nine nake miki ƙarya domin ba AJ bane ya sanar daku ba nine? "To koma waye bazan yardaba, wallahi bazan yardaba wanan ma ai cin fuskanne da rainin hankali! Kamar AJ!... Sai kuma ta dawo da kallonta izuwa ga Hajiya Babba tana cewa "Hajiya wai da gaske ne? AJ kika aura bayan duk irin tsaron da muka saka a kan ganin hakan bai faru ba? Da ƙarfi Hajiya Babba ta ce ...
"Eh nayi aure kuma na auri AJ sanan yanzu haka ina ɗauke da cikin sa? Hajiya ta faɗa cikin miƙewa tsaye sannan tana jin wani kwarin gwiwa na zuwar Mata. Shima Salis cikin fushin da yazo masa tun ɗazu ya meƙw ya ce "Nooooo! Dan Allah Momy bana son ji dan Allah ki daina faɗin wannan abun kunyar Please and Please na roƙeki Momy? Ya durƙusa har ƙasa a lamar roƙo ga kuma hawaye a fuskarsa. Sarah da Samuel dai izuwa yanzu sun fara tsorata da lamarin nasu.
"Wannan ba abun kunya ba ne Salis, domin aure na ce muku nayi ba zina na aikataba, wannan ma kawai ba abin farin ciki bane ace mahaifiyar ku tayi aure kuma harda c"...."Ya isa haka Momy ya isa ya isa bana so bana so? "Yanzu auran AJ shine abun alfahi a gurinki? Abin farincik? Shin Momy ko dai kin manta da waye AJ ne? Yaro ne fa ɗan ƙarami, na girmeshi sosai ma kuwa, amma kije ki aureshi? Wahy! wahy! Momy mai yasa zaki aikata mana haka? Shin kin manta da cewar kinada yara a gabankine? Ya ƙarasa yana sake sakin wani kukan. Laɗifa ta ce "Wannan tsinanan yaron ai ko nu zan gyarmeshi wallahi, amma wai Momy har kike iya cewa kin aureshi?
Cikin sanyi rai da a'lamar kuka a muryarta ta ce "Shin Salis lokacin da na ce muku zanyi aure kukaƙi saurarata a wannan lokacin ba kwa tunanin komai? Shin a wannan lokacin ba kuyi tunanin halin da zan shigaba? Har kuka nake yi ina roƙonƙu akan ku barni nayi aure amma ko nayi niya zaku ɓata? Ni kuma na kai adadin da bazan iya jurewa ba shine nayi aure, shin da ba aure nayi bafa!? Hajiya ta faɗa kan kujerar dake bayanta tana sake fashewa da kuka. Kallon mahaifiyar tasu yayi sai kuma ya kalli Daddy wanda ya zuba musu Ido sai ya sunkuyar da kai yana furta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Yana kaiwa nan ya tashi da niyar barin gurin.
Itama laɗifa miƙewa tayi zata bi bayan sa amma Daddy ya tsayar dasu. "Ku dawo ku zauna? Kamar bazasu zauna ba haka suka dawo kowa ya zauna rai a ɓace.
Muhammad ya ce "Salis?
"Na'am". Ya amsa.
"Laɗifa?
"Na'am Daddy? Itama ta amsa kamar bakinta na ciwo.
"Duk wanan abin kune kuka jawo, domin kuwa mahaifiyarku ta ce zatayi aure amma kunce bazaku yardaba shin wace hujja kuke da ita na hanata yin wani auran? Sanan shi yaron da ta aura ɗin yayi ƙaramine kokuma dai yaya? Idan har yayi ƙaramine to mai ya hana kubarta ta auri babba? Addininmu bai hana auran da tayi ba, hasalima taraya sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne! Saboda haka dan Allah inaso kozo muhaɗu mu rufawa junanmu a'siri, dan Allah Salis da Laɗifa kudawo cikin hankalinku, ita kanta sai yanzu take da tasanin yin auran, kuma tayi ƙoƙari zama babu miji harna tsawon shekaru masu yawo, ya kamata mu ɗaya hannu mu godewa Allah da yasa aure ne ya samar da wannan cikin.
Salis ya ce "Nagane Daddy kuma na fahimta na gamsu, amma kuma Daddy naji ka ce harda ci ci....sai kuma ya kasa faɗa yana jin ɗacin abin da zaifaɗa ɗin. "Eh harda ƙaruwa na ciki, amma kusa hakan a ranku cewar Allah yayi sai tayi koda bada AJ ɗin bane, saboda haka kuyi amfanin da tawakalin da a kasan musulmi dashi, ku ɗauka cewar haka Allah yaso. "Amin Daddy amin. Salus ya miƙe ya nufi gurin Hajiya.
"Ɗago ta yayi daga sunkuyan da take sai ya rungumeta yana sakin kuka itama haka. Laɗifa na ganin haka ta miƙe ta bar palon cikin kuka tana zagin AJ. "Kiyi haƙuri Hajiya naga ne cewar duk laifinmune, munyi kuskure kiya fe mana mun tauye miki hakinki da Allah ya halarta miki. Jin haka yasa Hajiya Babba ta ƙara rungumo yaron nata tana kuka ta kasa cewa komai sai ɗan dukan bayansa da takeyi. Sarha da Samuel suma kuka sukeyi ganin yanda suke kuka, take wani irin imani ya shigesu ganin yanda suka warware matsalolinsu cikin sauƙi da min dokokin addininsu. Sarah ta kalli Samuel sai ta miƙe tsaye shima ya bita.
*HOSPITAL (ASBITI)*
Bayan wani lokaci Innah ta farka, aikuwa ta samesu a tsaye a kanta dukkanninsu cikin tashin hankali. Da sauri AJ yazo kusa da ita yana kiran sunanta "Innah? Dan Allah kiyi magana yanzu muna sonki?
"Abduljabaru?
"Na'am Innah ina jinki? Kimin magana dan Allah?
"I'na Salisu?
"Innah bayanan" ya bata amsa yana matsowa
"Abdul baka ɗaukeni a matsayin komaiba, idan ka ɗaukeni da daraja bazan maka magana acikin mutane amma kayi banza daniba...yaronnan ya taimaka mana nida Nana lokacin da ka tafi kabarmu, amma yanzu na fito na samu kuna faɗa dashi har na maka magana amma Abdul kayi banza dani...to ni dai bazan maka bakiba, abin da zance maka shine Allah ya shiyamin kai yasa ka daina wannan halin naka na taurin kai, sannan Nana ta sanarmin cewar yace yana sonta kuma na amince ko bayan raina Salis shine mijinta, kai kuma kaje kayi abin da zakayi domin kafi ƙarfina, kodan kayi kuɗine to, sannan yanzu ka gama zama maƙaryaci yanzu idan nace maiya haɗa ka da Salisu bazaka sanar dani gaskiyaba kuma nasa"..."A'a Innah wallahi na shiryu na daina komai, sanan shima Salis ɗin bansan lokacin da hakan ya faruba, ki daina cewa dan nayi kuɗine walhin na shiryu . Inaah ta ce "To shikenan Allah ya muku albarka, ka dinga rage zuciya Abdul, sannan ka rage son kuɗi da yawa Abdul, domin wani lokaci ko ka samu kuɗin idan ka rasa wani abun naka zakaji dama Allah bai baka wannan kuɗin ba ya barka da wannan abin da ka rasa.
"Dan Allah Innah ki daina faɗin haka banaso jikina na mini wani iri idan kina faɗin haka? Cewar Nana tana durƙusuwa kusa da Innah. Suna cikin haka Dr ya shigo.
A ranar a ka sallamesu Dr ya ƙara jamusu kunne akan a daina ɓata mata rai. Ai kuwa suna dawowa AJ ya ce zai ƙarasa kwashe komai da sukeso na gidannan zaikai sabon gidansu domin daga yau bazasu ƙara kwana a gidan ba. Ita dai Innah bata ce komai ba, haka suka shigar da ita ɗakinta suka kwantar da ita, suka fara fitar da kayan da zasu amfana i zuwa cikin mota. Bayan ya tafi ita kuma ta shiga gyaran gidan. Bayan ta gama ta shigo ɗakin Innah tana cewa "Innah karfa kiyi barci kinga magariba tayi? Jin kamar har ta fara barcinne yasa ta ƙara cewa "Innah!!!!!! Ki tashi!? Nam ma taji shiru, Sai taje harkusa da ita ta ɗagota tana cewa "Kinsan barcin yamma babu kyu amma yanzu-yanzu har kin fara? "Cikin ɗan barcin da ya ɗauke ta ta ce "Nana barni na ɗan kishingiɗa ko zanji barcin nan ya tafi? "A'a fa Innah ai kinsan ba kyu. Haka dai dole saida Innah ta miƙe.
A cikin daran AJ ya gama kaiwa koma nasu, gobe saide kawai su tare a sabon gidan su. A cikin daran Nana ta tambayi AJ abin da Salis ya masa, amma ya sanar mata da cewar babu komai kawai dai yayi tunanin ko zai ɓata mata rayuwane. Badan ta yardaba tayi shiru, shima ya tambayeta tsahon yaushe suke tare? Ta ce "Tin kafin yayi tafiya zuwa Niger. Yayi mamaki sosai amma ya ce "Kuma kina sonsa? Ta ce "Ai shi yana sona" AJ yayi dariya yana tausayin Nana domin yasan idan har Hajiya taji wannan zancen bazata yarda Salis ya auri Nana ba, ko shi Salis ɗin idan yaji bazai auretaba. A ranar a Restaurant sukaje suka sayo abinci, yauma kowa kazarsa da bam ga kayan sha, Nana kam warewa tayi ta zaɓi duk abin da takeso ta sayowa Innah ma nata.